document audiovisuel · Daarul Hadeethis Salafiyyah · 3 avril 2011 Citer
In an bugi jaki... Habaa shehi!!!? Rigiji gabji
- Type
- Enregistrement vidéo
- Créateur
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Editeur
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- Description
- en This video contains a message from Sheikh Albani Zaria to the Sheikh of Tijaniyyah Dahiru Bauchi. It shows the importance and meaning of the position of Islam and the meaning of Christianity and an explanation of who they are "Izala and their Sufs and an explanation of who the Christians are and their Sufs and an explanation of whether it is permissible for a Muslim to vote for an infidel if a Muslim is also competing.
- ha Wannan Video ne ta Qunshi Sako Da Sheikh Albani Zaria Ya Turawa Shehin tarikan Tidjaniyyah Dahiru Bauchi. Sheikh M.A.A Albani ya tunatar da mu irin matsayin musulunci da na’anar kiristanci, da bayani akan cewa suwaye “Yan izala da suffofinsu, da bayani akan cewa suwaye kiristoci, da suffofinsu da bayani akan cewa ko ya halatta musulmi ya zabi kafiri idan harda musulmi shima yana takara.
- Date
- 3 avril 2011
- numéro
- 1
- 2
- 3
- Est une partie de
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Importance matérielle
- PT243M
- Support
- DVD
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000012
- contenu
-
============================================================
[Part 1]
============================================================
[Segment 1/5 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yanzu da muke magana daren litinin ne da ya daidai da daren talatin ga watan na da shekara dubu daya da dari hudu da talatin da biyu daidai da uku ga watan April shekara ta dubu biyu da sha daya. Wannan lokaci da kake saurare a kuma wannan ainihin wato masallaci kana sauraran mu ne daga ainihin wato masallacin da kenan jihar Kaduna Nigeria. Ni ko mai magana suna na Abu Abdurrahman Muhammad Awwal Adam da aka fi sani da Albani Zaria. Yanzu da kake sauraran mu lokaci ne da ya kamata muyi karatun Sai dai wata ta ta burza ce wadda ainihin ta taso tsakanin al'ummar musulmin kasan na dangane da kataniyar siyasa da ainihin ake ciki. Sakamakon haka shi ya kai zan gabatar da wannan lacca tawa. Ina fatan wannan lacca tawa sabanin yadda na saba gabatar da laccoci masu taki musamman wannan in tsawaita wannan zan takaita ta kwarai da gaske. Dan haka abubuwa da dama wadanda ya kamata in bude in karanto su zan yi ishara su ko kuma in nuna wanda wannan ya isar da ikon Allah dangane da bukatan takaitawa a ainihin wato irin wannan hali. Bayanin farko wanda yake matashiya ce dangane da halin da muke ciki jama'a. An sa ranar zabe a jiya asabar amma sai aka samu ainihin matsaloli wadanda sakamakon wadannanLire le texte intégral — 34 807 mots restants Réduire le texte intégral
matsaloli shi yasa aka daga wannan ainihin zabe. Abun da muke fata shine al'ummar mu don girman Allah kamar yadda kuke ta mana biyayya da kuma ainihin saurare da jagoranci da muke muku dangane da menene ya kamata sannan menene kuma bai kamata ba. Ku taya mu addu'a akan Allah madaukakin sarki ya ya tabbatar da diga digan mu akan abubuwan da suke daidai. Sannan Allah madaukakin sarki ya tsare mu daga kurakurai. In kuma mun samu kan mu a wajen su diddabaka ko kuskuren aikata abun da ba daidai ba ku taimaka mana da nasiha kamar yadda muma muke taimaka muku da nasiha da ainihin fadakarwa. Hakikanin al'amari matsaloli ne suka faru wadanda yake shi shugaban hukumar zabe ta kasan nan da aka fi sani da Professor Attahiru Jega ya samu kanshi a tsaka mai wuya ne abun da bahaushe ke kira gaba kura bayan siyaki. Idan akai zaben nan ko da anyi zaben nan jiya to da an rugurguza shi kuma da an rusa ainihin irin manufofi da jama'a suke gani tattare da shi. Daga zaben kuma zai ja mishi zagi da zargi da zubar da mutunci. Wannan shine halin da ya samu kanshi sai ya lura Abubuwan guda biyu dukkan su barna ne. Ayi zabe zaben ya zama akwai magudi a cikin shi barna ce. Haka kuma ace ba ayi zaben ba wanda wannan zai rusa mishi mutunci da ganin cewa yana yi ne don wasu kafin a kai ga bayyana abun da yake gaskiya ko kuma fahimtar shi wannan ma zai ja mishi ainihin wato hakikanin zargi. Sai yaga cewa ya dauki zargi da zagi da suka tafi mishi sauki fiye da a zo a ainihin zalunci al'umma. Wasu abokan tafiyar shi ne wadanda babu yadda za'a yi hukuma irin wannan ta INEC sai an samu tana da manyan ma'aikata da kananan ma'aikata. Kuma kai kasan cewa babu yadda za'a yi tafiya irin wannan ta zama duk tattaruwar mutane ne na kirki wadanda manufar su gyara ce. Sakamakon haka aka samu matsaloli wadanda daga cikin matsalolin nan na cikin gidan shi ne suka ci amanar shi. Wanda wannan cin amana ya faru daga ainihin wasu jiggan ma'aikata na shi wanda daya daga cikin su ko kuma jagoran su komishina ne a cikin wannan hukuma na gudanar da ainihin wannan zabe. Yana daya daga cikin jagora jigga jiggan wadanda ainihin suka haifar da cin amana. Sai kuma wani na hannun daman shugaban kasa wani ainihin wato sanata wanda dukkan su sune suka hada baki suka so su abkar da wani mummunan magudi ta hanyar buga takaddun ballot paper wadanda suke 'yan jabu na karya. Ya aka yi aka iya ainihin wato gano irin ballot paper din da INEC kadai ta kadai ta dasu. Haka bai faru ba sai ta hanyar wadancan manya manyan munafukai na cikin gida. Allah ya tona asirin su kuma muna fatan Allah madaukakin sarki ya cigaba da tona asirin su. To babu shakka da anyi zaben nan da jama'a sunyi mamaki kwarai da gaske domin daga cikin abun da zai alamta muku gaskiyar wannan maganar da na fada itace a mafi yawancin mazabun kasan nan inda akai register mutun dari hudu ko dari biyar ko dari shida sai kaga takaddun zabe da za'a kawo musu baza su wuce guda dari ba ko tamanin ko cha sai. A mafi yawancin wuraren da ainihin wato aka zo za'a yi zabe ance za'a yi zabe ne na sanatoci da kuma 'yan majalisar tarayya sai kaga ballot paper na bangare daya ne cewa ko dai an kawo na sanatoci babu na 'yan majalisu ko kuma an kawo na 'yan majalisu babu ainihin na sanatoci da nufin za'a je ta ainihin wato kasuwar bayan fage a je ayi abun da ake so da wadancan ballot papers 'yan jabu. To Allah madaukakin sarki ya tona asirin su ko muna rokon Allah madaukakin sarki ya cigaba da tona wa al'umma asirin su. Kuma kada Allah madaukakin sarki ya basu nasara. Abun da muke fata shine Allah muna kai kuka zuwa gare ka ka gyara mana wannan kasa tamu yadda duk wani azzalumi wanda yake kokarin ya kai mulki ko ta wacce hanya Allah ka karya shi. Domin alamar ya kai mulki ta kowace hanya dalili ne akan cewa in ya kai mulkin zai mulki mutane ta hanyar duk da yaso ya fanshe abun da yake gani mutane ainihin sunyi mishi ko kuma ya fanshe kudin da ya dankawa ainihin wadanda ya danka dan haka muna rokon Allah madaukakin sarki kai ya bada nasara ga dukkan wani wanda manufar shi itace ya samar da zalunci ko kuma ainihin wato wata keta ko kuma kama karya a cikin al'amuran da suka shafi mulkin nan da ainihin ake nema. Sannan abun da muke kira kamar yadda mukai kira a baya zuwa ga wadanda suke jami'an tsaro ne da ma'aikatan hukumar INEC da duk wani mai kishin kasa ku bar abun da shugaban kasar ya fadi in dai da gaske ne muma mun yadda. Amma bamu yadda da ba bamu yadda cewa yadda aka ce duk namiji kuri'a daya duk mace kuri'a daya sannan kuma a zo ace mai ake nufi da bama anar ta ta hakika ba karamin yaro ake nufi ma'ana magudi ne za'a yi kenan wanda bai isa ya dangwala ba shima ya dangwala ba yadda da wannan ba. Mun karbi wannan kuma mun yadda da wannan ainihin babu shakka dangane da haka wannan itace matashiyar farko to matashiyar da nake so in jingina a jikin wannan yayin da aka hasaso cewa mu 'yan arewa mune muka fi ainihin yawa kuma alqiblar mu bana ta karkatu mafi yawancin mu kan mu ya hadu. In banda wadanda suka fan darewa dangi wadanda suke tsararu ne. Alqiblar mu ta hadu a wata nahiya wanda ba itace aka so ba. To shine sai aka ga cewa babban abun da za'a yi ayi amfani da ma'ana a dubi yaya tunanin dan arewa yake dan arewa so da dama yana da gajan hakuri da gajan dangana wajen jeka dawo. Yana da rashin hakuri da gajan dangana wajen jira ina zuwa. To dage zaben nan da akai babu shakka yana neman ya kashe wa wasu guiwa su ce gobe in ance za'a yi zabe baza su fito ba jibi in ance za'a yi zabe baza su fito ba asabar ta sama baza su fito ba wata asabar din ma baza su fito ba. Idan kukayi haka jama'a to duk kwazon da kukayi a baya gaba daya ya lalace kwarai da gaske. Kwatan kwacin mutun ya tafi aikin hajji ne abun da ya rage mishi gashi ga Mecca yana jidda sai yace tunda yazo nan ma nan ya ishe shi. Yana jiran a gama aikin hajji a dawo. A zo a tafi da shi babu shakka ya isa kasar amma kuma bai je yayi ibadar ba dan haka jama'a kuyi hakuri abun babu dadi amma kamar yadda jiya na dan yi tsokaci irin wannan babu shakka anyi wadannan abubuwa ne ba dan komai ba sai dan ainihin a rikita mana al'amura. Ana ganin cewa mutane in ance gobe litinin su fita baza su fita ba in ance jibi su fita baza su fita ba ba dan komai ba dan za'a ce in ma mun fita ga abun da za'a yi mana. Don girman Allah yanzu an sa litinin an zo an dage an sa asabar asabar din nan kasan cewa in ka tashi fita baza su ainihin wato zo da kayan aiki da wuri ba. Baza ayi duk abubuwan da ake fadi karfe takwas za'a yi kaza karfe sha biyu za'a ayi kaza karfe kaza duk za'a bi ayi ta ainihin wato wahalar da ku ayi ta galabaitar da ku yadda za kuyi fushi wannan fushin zuciyar muke cewa ku kara hakuri ku kara daurewa kar kuyi. To ana nan a cikin wannan hali jama'a sai ga wani dattijon malami na mai suna shehi Tahiru Usman Bauchi yayi wasu kalmomi wadanda kalmomin basu yi wa al'ummar musulmi baki daya dadi ba. Daga ciki hadda da yawa daga cikin ko mafi yawancin mabiyan shi mabiya Wadannan kalmomi nashi kalmomi ne wadanda suke sun shahara a karkashin haka na kirayi wannan lacca domin ainihin mu maida martani dangane da ita wannan magana shi kuma shehi muyi kira zuwa gare shi yayi marmari janya wannan magana domin bata dace da dattijo irin shi ba bata dace da malami irin shi ba bata dace da jagoran wata al'umma mai yawa irin shi ba. Wannan kalma babu shakka zata zub da mutuncin shi. Amma bari in dan yi wani tsokaci so da dama mukan hadu a wuraren tarurruka da dama da shi sheikh Tahiru Usman Bauchi misali mun hadu a wurin wani taro wanda a Kaduna kamar yadda muka sake haduwa a wurin wani taro wanda ainihin wata kungiya ta 'yan boko ta shiriya. A wadannan wurare guda biyu da kamar yadda aka sani a kafafen watsa labarai yana yawan magana yana kukan cewa yara suna yi mishi rashin kunya yara suna zagin shi yara suna cin mutuncin shi to abun da muke cewa babu shakka mu dai bamu daga cikin marasa kunya masu ainihin rashin kunya ga shehi bamu daga cikin masu zagi ko masu cin mutuncin ainihin shehi saboda dalilai kamar haka wadanda zan fade su a bisa mahanga shari'a da kuma mahanga ta ainihin tunani. Babu shakka shehi makarantun al'qur'ani ne da ya koya kuma yake karantar da al'qur'ani A wannan halin bai kamata ace a wulakanta shi ba don manzon tsira Muhammad wanda ya fi ku shine wanda ya koya al'qur'ani ya koyar da shi. Dan haka shehi kana da wannan daraja dan ka iya karatun al'qur'ani bayan ka koya kuma kana karantar da ainihin al'qur'ani din. Dan haka bama wulakanta ka in kuma kaji masu wulakanta ka to ba daga cikin mu bane. Na biyu kai abokin uban mu ne a sheikh Abubakar Mahmoud Gumi shi kuwa abokin uba to uba ne. Saboda martabar Abubakar Gumi ko kai ba malami bane a matsayin kai abokin uban mu ne baza mu wulakanta ka ba. Na uku kai dattijo ne da hakika juye ban kwarya ta a shekaru ka girme mu ka haife mu kana da 'ya'ya makamantam mu ko wadanda suka dare mu a shekaru to wadannan dalilan da kuma hadawa da cewa mu mun tashi gaban manya ne to bamu san mu wa ainihin babbar rashin kunya ba. Sai dai kuma fa dole duk inda babba yake da darajojin shi dole ne ya kiyaye mutuncin shi yasan maganar da zai fadi yasan inda zai sa hannun shi yasan inda zai sa kafar shi. Sannan girman mai girma da darajar mai daraja bata hana ayi mishi martani dangane da mummunan maganar da yayi ko kasassaba ko kuskuren da yayi. Domin Imam Malik yana cewa Ko wanne daga cikin mu da ka gani limaman musulunci a nemi mishi raddi kuma shima yakan yi raddi yakan yi raddi kuma akan yi mishi raddi yakan wayi gari wata ran ya ganshi a halin ya naima wani raddi wata rana kuma akan wayi gari shima ana mishi raddi sannan raddodi suna da yanayin da ke hukunta ayi su da kuma irin tsarin da ke ainihin hukunta ayi su. Dan haka shehi duk da darajar ka da girman mabiyan ka a Nigeria bazai hana in kayi mummunan magana irin wannan a fito a tara jama'a kamar yadda ka tara kafafen watsa labarai suka yada a jaridu da radiyoyi da kasussuwa aka saka a internet har wasu daga cikin wawayen mabiyan ka suke kare maganar suna yi mata ta goma shi suna bayyana sharhin ta suna jinjina maka babu shakka dole ne a tsaya a bayyana barnar da ke cikin wannan magana musamman a irin wannan hali da al'ummar musulmi suka fi bukatan su hade kansu fiye da kowane lokaci. Musamman a irin wannan hali wanda kai da makamantan ka kuke kira dangane da a dena kafirta musulmi kai da makamantan ka kuke kira akan musulmi su tashi su hada kansu musulmi su kauna ci junan su tsakanin ka da Allah shehi duk sanda kake wannan magana baka tunanin cewa wadannan mutanen da kai mummunan magana a kansu suma musulmi ne baka fatan cewa a hada kai tare da su baka ganin hadarin in ya zama sun koma gefe guda a irin wannan halin kai kanka taka manufar zata samu kaiwa ga matsala da cikas to dan haka na shirya ainihin wato wannan lacca tawa wadda na sa mata Haba shehi Yadda spelling ta zai kasance a rubutun ajamanci na turanci shine H A double B zaka yi double in kai B sai kai double A a gaban shi haba sannan sai kai dige dige ina fatan an gane sannan shehi shima sai kai dige dige sannan sai ka sa alamomin tambaya guda uku sannan ka zuba alamomin motsin rai guda uku wato question marks da kuma exclamation marks ka zuba su guda uku. Wannan kenan Allah madaukakin sarki ya taimake mu dan haka taken laccan tawa kenan haba shehi. Sannan abu na biyu da nake so zan tattauna akai in Allah yaso manufar wannan lacca wadda shine mayar da ainihin martani ga shehin darikar tijjaniya shehu Tahiru Usman Bauchi Allah ya shirye shi. Sannan sai maganganun shehi a murya da rahotannin jarida a nan na maida jaridar aminiya itace babban madogara dangane da maganganun da ainihin zan yi insha Allahu ta'ala. To a nan ne fa nake so in yi tsokaci dangane da fassara maganganun da shehi yayi da kuma irin munin da suke dauke dasu. Zan yi magana dangane da menene kristanci menene kristanci sannan menene asalin kristanci sannan suwanene kristoci sannan manyan dabi'un kristoci zan kawo su insha Allahu ta'ala don asan irin dabi'un kristoci da muke so a gwada su da dabi'un 'yan izala da shehi ya fifita kristoci a kansu sannan me cece izala menene asalin izala da tarihin ta waye ma dan izala shin gwamna Ibrahim Shekarau gwamnan jihar Kano a yanzu kuma dan takarar jam'iyyar A N P P a yanzu ko dan izala ne zamu yi magana akan wannan insha Allahu ta'ala. Sai kuma siffofi da dabi'un dan izala insha Allahu ta'ala zamu tattauna wadannan maganganu sannan daga karshe hukuncin zaben kafiri wanda ba musulmi ba zamu tattauna ainihin wadannan matsaloli insha Allahu ta'ala sannan matsayin mu mu 'yan izala dangane da da ace za'a tsayar da wanda yake dan darika takara gefe guda kuma ga krista me cece fatawar mu menene kuma matsayin mu mu 'yan izala insha Allahu ta'ala zamu yi magana dangane da wadannan matsaloli. Sannan sai maganar shehi akwai gyara kuma ta ja cece kuce zamu dibo wadannan gyare gyare daga ainihin jama'a wadanda ainihin suka yi a cikin jaridu mujallu da kuma tashoshi na ainihin internet kamar yadda nace wadanda suka saba saurare na yau da gobe don Allah sai suyi hakuri a irin wannan halin ba dan komai ba saboda ina so zan takaita kwarai da gaske fata nake gaba dayan wannan lacca ta kasance a cikin cassette daya wanda yake awa daya da rabi ne insha Allahu ta'ala. Kamar yadda nace taken laccan dai shine haba shehi manufar laccan kuma maida martani ne ga shehin darikar tijjaniya shehu Tahiru Usman Bauchi to sa'annan sai maganganun shi shehu Usman Tahiru Bauchi din wadanda nake son kasan cewa wadannan maganganu fa ba yanzu ne shehi ya fara yin su ba. Ya dade yana yin wadannan maganganu sai dai wadannan maganganu sun zo ne a wani yanayi wanda mutane kansu ya kara
[Segment 2/5 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
dangane da yawan sauraren ainihin wato rediyoyi. Daya kenan. Da yawan karanta jaridu. Da yawan bincike dangane da shafukan internet. Sannan wannan lokaci kuma ya kai mutane sun kara zabura da kara fadaka dangane da abin da ya shafi yawan ainihin wato shiga da kuma sanin me ke kaiwa da komowa dangane da harkokin siyasa. Kaji abin da ya ja kenan. In ba haka ba wannan maganar shehi yayi ta tafi shekara ashirin. Kuma ya dade yana nanata ta. Ya kuma yi maganganu wadanda suke sun mafi haka dangane da abin da ya shafi yan izala. To amma wannan lokaci ne kamar yadda nace al'amuran sun hada ana yawan karantawa da saurare ana kuma yawan shiga harkokin al'amuran yau da gobe dangane da abin da ya shafi ainihin wato jaridu. Allah madaukakin sarki ya taimake mu.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
To jama'a kun dai ji wannan bayani. Bayan nan insha Allahu ta'ala kamar yadda ya shahara wadannan abubuwan duk da shehi yayi su. Jaridun nan duk sun dauko rahotannin su. Zan karanto mana kadan daga cikin su kuma in yi ishara zuwa ga inda ya kamata ainihin wato aje ainihin a saurare su. Allah madaukakin sarki ya taimaka. Kamar yadda nace ainihin wato jaridar aminiya ta ruwaito wadannan maganganu wanda jaridar aminiya website din ta shine aminiya.com. In kasa www. aminiya.com itace jaridar hausa ainihin wato ta jaridar daily trust. Allah madaukakin sarki ya taimaka. Mallam kunna mana naka. Wannan wani yana ta kira na ya hana in abin nan in bude file din. Kamar yadda nace jaridar aminiya ta ruwaito wannan gashi a wani shafin ta na ranar juma'a 18 ga watan Maris na wannan shekara ta 2011. Gashi inda yasa garar Jonathan da shekarau. Kalmar da ita jaridar ta ruwaito kenan daga gare shi sa sheikh Dahiru Bauchi. Suka ce sheikh Dahiru Usman Bauchi na daya daga cikin malaman da Na'am? Bude kawai. A'a wannan maganar ta shi. Mun fahimta jama'a? Sheikh Dahiru Usman Bauchi na daya daga cikin malaman da suka taimaka wajen tallan mallam Ibrahim Shekarau a kasar nan. Musamman game da shirin sa na taimakawa shari'ar musulunci. Amma a yau aka wayi gari sheikh ya raba gari da gwamna Shekarau na jihar Kano. Inda har yayi barazanar cewa matukar Shekarau bai dena mu'amala da shi ba zai garzaya kotu. Domin jin ko me yayi zafi haka aminiya ta tattauna da shi kamar haka. Ina fata an gane? To ga ainihin abun a murya kuma ko? Ka kunna kunna shi. Kunna kawai. Ina fata an gane? Asalin audio clip din bashi da gara jama'a sai ayi hakuri. Amma abu ne wanda duk yake da hanset din ya kunna shi insha Allahu ta'ala zai ji shi. Daga cikin kadan daga dalilan da ya kawo kamar yadda muka ce a tattaikaice muke yi gashi nan dai jaridar ta ruwaito shi ainihin a tsanaki cewa na farko saboda dan izala ko yan izala basu yarda su yan darika musulmi bane. Na biyu in ku bari kawai shikenan. Na biyu idan dan izala ya samu suna sallah cewa zai aikin banza. Idan kirista ne kuwa cewa zai musulmi suna ainihin sallah har yace sorry sorry suyi hakuri. To na fara ainihin wato bayar da wata yar takaitacciyar amsa dangane da tunani irin wannan. Dan mutumin da yake ba musulmi ba ya amintu kai musulmi ne. Yo ya ka iya? Kamar kai ne da ka amintu shi kirista ne. Ya ka iya? Ka san addinin daidai yake ko ba daidai yake ba. Don haka bayar da shedar musuluncin ka shehi daga kiristoci ba dalili ne akan cewa musuluncin ka ya inganta a wurin su ba. Kuma ba dalili ne akan cewa su ne maka kallon kai mutumin arziki bane. Wanda gobe da zai tashi shi zai iya bada fatawar cewa kai kafi wani dan uwan shi da ke wata kungiyar. Koda tsakanin protestant ne kuwa da ainihin wanda yake dan Roman Catholic. Don haka wannan magana a cikin ta akwai matukar kuskure kwarai da gaske. Gashi daga cikin abubuwan da ita jaridar ta ainihin yanko sai yace don haka muka ce idan dan izala ya tsaya zabe da wanda ba musulmi ba aka rasa na uku sai dan izala to mu wanda ba musulmi ba zamu zaba. Ba dan komai ba saboda ya kafir tamu kuma yana saboda bara kafir tamu shi wanda ba musulmi ba kenan. Kuma yana cin yan kan mu. Kuma baya zagin iyayen mu da malaman mu. To shi yasa zamu zabi kirista mu bar dan izala. Don bata mana suna da cin mutuncin mu da suke yi suke kafir tamu. Anan zan iya dauko wata amsa da mallam Abubakar Ikaru Allah ya gafarta mishi a taren can namu na Kaduna da muka je ya baiwa shehi dangane da wadannan irin maganganu. Cewa shehi dan menene zaka tsargo ka damu akan ana yawan kafir taku. Sai yace domin mu idan dukkanin al'ummar kasan nan zasu tattaru da malaman su da wadanda suke masu wa'azozin su su ta jawo na soshi suna cewa mu kafirai ne yan izala. Mu ran mu ba zai baci ba. Ba zamu damu ba. Ba zamu tsargo ba don mun san mu ba kafirai bane. Yo me yasa in har kai ba kafiri bane don ance kafiri kaza ko dan ance mai akida kaza kafiri ne don menene zaka damu? Sannan shehun takar shehu Dahiru Bauchi ta kai kamar shehun takar sheikh Sharif Salihu ne bata kai ba. Me yasa sheikh Sharif Salihu baya damuwa akan dan an kafirta masu irin wadannan akidojin da ake tuhuma? Domin duk sanda aka ce wanda ke kaza kafiri ne sai ance saboda yana da akida kaza saboda yana da akida kaza saboda yana da akida kaza me yasa shehi ba zai duba ya ga shin yana da wadannan akidun ne? Idan yana da su to lallai maganar da shi ake. In kuma bashi da su ashe ba da shi ake ba. To me yasa sheikh Sharif Salihu shi baya damuwa in an fadi ire ire wadannan maganganu? Don haka shehi ya koma yayi nazarin ainihin wato ire ire wadannan kalmomi wadanda kullum yake dogara da cewa ana kafirta malaman su ana cewa kaza ana cewa kaza. Shin siffofin da ake fadi shehi kana da su ne? Ko da gaske ne an taba kama ka kana gudun daji za'a tafi wani taro na sufaye shehi ko da gaske ne kana da kwarakware a wannan zamani wadannan wasu mas'aloli ne da aka yi wa'azi a kan su yau shekara 30 da ta gabata. Wanda muyi wa'azi dan bana bakwai dan shekara 20 ko 25 har dan shekara 30 din ma baka san lokacin da aka yi wannan gogarmayar ba. Wadannan abubuwan su suka ja a lokacin shehi yace ana zagin shi. Shin ita maganar ta farkon da ta biyun karya ne dangane da hakkokin ka? Idan karya ne dan menene zaka damu? In kuma gaskiya ne ko kana da dalilin da za'a ce za'a je taro ka kama hanyar da kowa yake bi ka ki sai ka kama hanyar daji kana son ka isa kafin jama'a su isa don ace shehi yana da wata karama har mafarauci ya kamo ka ya kamata a binciki wannan magana. Sannan ko a wannan zamani akwai yiwuwar ace ga namiji yana da kwarakware mata amma babu yadda za'ayi a iya samun bayikar ti maza. A wannan lokaci jaridun gaskiya tafi kobo da jaridun amana sun ta dauko wadannan rahotanni suka bi malaman kasan nan kaf da na izala da na darika da wadanda ma ba ruwan su da dayan kungiyoyin ko dari ungu da biyu aka ji ra'ayoyin su wanda ra'ayin wadannan malamai gaba daya a lokacin ya hadu akan cewa duk wanda ya da'awar yana da bayi a wannan zamani to sai ya kawo hujjar da aka yayi ya iya samun bayi. Domin wannan zamani ne da babu inda zaka je ka ga kasuwar da ake sai da bayi. Kuma duk bayin da jama'a suka mallaka shekaru 100 da ta gabata da kan su sun amince sun yantar da su ko kuma sun siyar da su ga wadanda suka yunkurin yantar da su. Ta wace hanya ake iya samun bayi mata wadanda a yanzu ba'a iya samun bayi maza wadanda maza ya kamata a fi samu a matsayin bayi domin su ne suke mubasharantar harkar yaki. Idan yaki ya karye su za'a fara kamawa. Me yasa shehi bai iya bada wannan amsar ba shekara 30 da ta gabata jaridar amana wanda ake bugawa anan Daga ce ita ta dauko ainihin wadannan rahotanni. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. To wadannan su ne kadan daga ainihin wato cikin ire ire maganganun wadanda kamar yadda nace jama'a wadanda suke karatun jaridu suje su ainihin wato samu jaridar aminiya don bayan da shehi yayi wannan magana akai ta rade rade shin maganar gaskiya ce shehi yayi ta ko ba gaskiya bace? Yan jaridu suka ziyarci gidan shi daga ciki akwai ainihin tashar muryar Amurka ta sashin hausa da suka ziyarce shi suka je suka zauna da shi suka tattauna suka ji ainihin daga gare shi kai tsaye ya tabbatar da wannan magana aka sake sa wa jama'a. Wannan yan jaridar aminiya gashi hira ce mai tsawo suka dauko da shi suna yi mishi tambaya daya bayan daya. An buga ta ainihin a dukkanin jaridun da suka biyo bayan tun waccan tattaunawa da ainihin aka yi da shi a murya Amurka. Duk wanda yake da jaridun yaje ya samu ya karanta. Wanda bashi da su muka ce kaje ka buga www.aminiya.com kaje zaka sauke jaridun baki daya ka zabi wanda kake so kayi printing. Gashi yanzu yanzu nan da yamma nan nayi printing din su daga internet. Kaima kana iya yi. Kana iya karantawa. Kuma ai har yanzu shehi bai fito ya karyata wannan magana ba bayan duk da aka yada ta. Musamman an samu ainihin wato bugun jaridar aminiya na 24 ga watan da ya wuce watan March. Inda sai da suka buga hoton shehu Sharif Salihu da hoton shehu Dahiru Bauchi da shehu hoton ainihin wato sheikh Sa'ido Alhasan a jingir shugaban izala duk sai da aka buga su suka tabbatar da kurakurai da katobarar da ke cikin maganganun da shi shehi Dahiru Bauchi yayi. A karkashin wannan da sai aji shehi ya dawo yace shi ba haka ya fada ba. Ko kuma maganar shi sam shi bai fadi wata magana mai alaka da wannan ba. Amma shehi ya amince da wannan magana kuma ya ja baki ainihin yayi shiru. In muka dawo magana ta gaba da muka ce zamu tattauna akai cewa menene kiristanci? Sannan me ce ce izala? Wanene kirista? Sannan wanene dan izala? A gwada wadannan mutane guda biyu ta hanyar addinan su da akidojin su a bisa hasken biyayya ko kuma rashin biyayya ga Allah da ma'aikan shi tsira da amincin Allah ya tabbata ainihin su tabbata a gare su. Hakikanin al'amari ya kamata mai saurare na kayi kokarin gane cewa kiristoci ba su ne daya da nasara ba. Ba kuma su ne daya da masihiyuna ba. Masihiyuna su ne mabiya annabi Isa alaihis salatu wassalam almasihu na gaskiya wadanda basu canza ba basu sauya ba basu yi bidi'a ba basu kirkiro ba dangane da abin da Allah ya aiko annabi Isa da shi. Wadannan su ake kira nasara su kuma ake kira masihiyuna. Kiristoci kuwa su ne wadanda suke bin jabun addinin da aka dangantawa annabi Isa ta hanyar ainihin manzo Bulus wanda Bulus din nan ba yahude ne. Yayi barna tsawon fiye da shekara a ru a ru dangane da mabiya annabi Isa alaihis salatu wassalam ta hanyar kashe su da wahalar da su da haifar musu da yaƙoƙi na ƙare dangi. Duk da ya gama wannan baki daya amma ya kamata kasan cewa bai ga annabi Isa ba kuma shi ba sahabi annabi Isa bane. Daga baya ya dawo yace ya bayyana tuban shi zuwa ga ainihin mabiya annabi Isa. Dayawa su kayi tawaye suka ce ba zasu karbe shi ba don sun fahimci makirci ne kuma ya kullo. Bayan ya gama wa addinin ƙare dangi kuma zai zo ya lalata addinin. To amma sai aka samu tattawa irin su Barnabe wanda aka fi sani da Barnabas. Sai ainihin ya nuna cewa a karbe shi. Tunda ya tuba ai Allah na karban laifi da duk mutum yayi ya tuba. Amma matasan tafiyar daga duk wanda yayi laifi ya tuba Allah yana karban shi. Matasan tafiyar daga cikin mabiya annabi Isa irin su Mathew sam basu amintu da ainihin wannan tuba ta Paul ba ko kuma Bulus. Don haka haka aka ci gaba da wannan tafiya Barnabas kamar ya amintu da shi amma Mathew bai amintu da shi ba. Ana nan ba'a dade ba sai aka ji yace yayi mafarki ya ga annabi Isa alaihis salatu wassalam kuma annabi Isa yace mishi ya tashi ya rubuta Injila cikin jerangiyar almajiran annabi Isa da ke rubuta injiloli. Sai aka ga ga Injila ya rubuta ta amma tana ɗauke da cewa Isa Allah ne. Isa dan Allah ne. Allah yana da ɗa Maryamu ƴar Allah ce. Mala'ika Jibrilu ma Allah ne. Aka samu wadannan akidoji sun fanjama a cikin littafin da yayi da'awar cewa annabi Isa ne ya bashi umarnin ya rubuta. Bayan da ya gama ainihin wato rubuta wannan ya fito da shi ga jama'a mabiya annabi Isa suka yi tawaye. To amma ya riga yayi raraka a karkashin kasa wanda ya kama hankalin dayawa daga ainihin mabiya annabi Isa wadanda ba zama suka yi da annabi Isa ba. Suna bin karantarwar ne. Kafin a fadaka ya riga ya samu mabiya. Don haka lokacin da wadancan suka yi tawaye cewa karya ne sai ga wasu mabiya masu ɗinbin yawa a cikin tafiyar sun miƙe suna mara mishi baya. Cewa ai mafarki yayi kuma a cikin addinin annabi Isa akwai halaccin kayi mafarki kaga annabi Isa ya fada maka magana ka rubuta ta azo a karbe ta ba tare da anyi wani bincike ba. Don haka shima yayi mafarkin haka. To ashe dan kwangila ne tsakanin yan uwan shi yahudawa da kuma sarki Constantine na kasar Constantineya wato kasar Turkiya ta yanzu. Wannan sarki shi kuma bama guje ne mai bautar allolin bauta dayawa. Sakamakon haka suka sha alwashin sai sun ɓata addinin annabi Isa alaihis salatu wassalam. Tabbas suka dakko wannan kwangila suka ɗanka wa shi Bulus. Da yazo ya kawo wannan rikici da rikici yayi rikici sai yace to a samu wani wanda bayida addini akai mishi ƙarar wannan ƙadiyya. Suka ce kamar wa sai yace kamar sarki Constantine. A cikin rashin sani sai suka amince. Da aka tafi sai sarki Constantine duk ya tattara duk wata Injila da ke hannun su yace za'a samu wani ƙaton kwano a lulluɓe wadannan injiloli. Idan gari ya waye duk wanda aka samu a sama da wannan ainihin wato kwano saura suna lulluɓe to itace ta gaskiya jama'a kun yarda suka ce sun yarda. Wannan na daga cikin matakin farko na makircin sauya addinin annabi Isa alaihis salatu wassalam. Aka dakko ainihin wato aka wayi gari sai aka ga wannan Injila mai cewa Isa Allah ne. Mai cewa Maryamu Allah ce. Jibrilu Allah ne. Allah yana da ɗa. Alloli guda uku ne sai aka ga itace a sama. To Barnabas da shi da Mathew da suka ga haka sai suka ce to wannan itace ranar farko ta tarihin lalacewa addinin da annabi Isa ya aiko yazo da shi. Don haka baza su tsaya su ga wannan ɓarna a idon su ba. Sai suka kama hanya sai zasu yi gudun hijra a daji aka gane ga wa'awakin su an daddafa musu makamai da ake zargin in ma Bulus da sarki Constantine ne suka aika aka bi bayan su aka hallaka su. In ma wasu yan ta'adda ne suka hallaka su. Iya ƙarƙarshen labarin Barnabas da Mathew kenan dangane da abin da ya shafi riwayar wannan littafi na Baibul da aka fi sani da littafi mai tsarki. An hallaka su sakamakon ɗayan wadannan abubuwa guda biyu da ake tsammani. Sai aka dawo cikin gari duk wadancan injiloli sai aka hallaka su. Sai abin da Allah ya tsiratar na daga Injilar da a yau aka fi sani da Gospel of Barnabas. The Gospel of Barnabas itace Allah ya kuɓutar da ita. Don haka a yanzu wannan ainihin wato Injila da yadda take a asalin rubutun hannun ta tana nan a Barnabas square a cikin ainihin wato ƙasar Italiya a Rome. Sun kewaye ta da ainihin wato wani gilashi na ainihin kwalba wanda yake shokin baka isa kaje ka taɓa ba domin an jajje fa su ta ita har ta fara cin wuta sai wani yazo ya fusge ta yayi gudu da ita. Itace yau tarihi ya ajiye ta tana nan ainihin The Gospel of Barnabas. Shine aka samu wani mutumin Pakistan ya samu kaiwa gare ta tun kafin ayi mata wancan gatan. Tun a wancan zamunna ya ainihin ƙafo ta shine ake buga ta. Dayawa zaka ga kiristoci suna inkarin ta saboda sunayen annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama a ƙarara ya bayyana ainihin a cikin ta. Amma kuma babu shakka itace Injila mafi kusantar gaskiya daga ainihin injilolin duk da suke hannun kiristoci da Afokrifa a yau ɗin nan. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Don haka jama'a kun ji wannan shine addinin kiristanci. Kenan yanzu wannan addinin shine asalin addinin da Barnabas ya tsarawa mabiyan annabi Isa
[Segment 3/5 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
a karshen zamani suke bi. Sai suka dawo suna ainihin wato daukar wannan suna ainihin ratayawa a wuya. Ratayawa a wuya da suke yi shine sai yahudawa su ne musu ainihin wato makri, su ne musu ba'a suna zargin su cewa wato masu bautar masu bautar masu bautar wanda aka gicciye. Toh da zamani yayi tsawo sai su da kansu suka anshi wannan suna suma sun amshi cewa suma kiristoci ne. Don haka jama'a in ka fahimci wannan takaitaccen tarihi kenan kana iya gano ashe addinin da ake bi a yau da sunan ba shine addinin annabi Isa ba. Wani abu ne daban ake bi daga cikin shawarar sarki bama guje da kuma wanda yake shi kuma bayahude ne wanda ya shigo cikin addinin domin ya ainihin bata addinin. Shi Paul bayahude ne daga cikin manya manyan 'yan kungiyar asiri da aka fi sani da Kaje ka saurari lacca ta da nayi ta awa hudu na sa mata mun yi bayani dangane da ainihin wannan kungiya. Toh shi Paul dan wannan ainihin kungiya ce. Yanzu kaga wannan ya bayyana maka menene kiristanci? Menene asalin addinin kiristanci? Toh kaga ya sha bambanda ainihin abin da aka sani na addinin Ba zaka yi mamaki ba in baka san wannan tarihi ba da zaka ji aya al'qur'ani tana cewa Allah ya tsine wa bani Isra'ila Ba zaka yi mamaki Allah ya tsine wa bani Isra'ila a bisa harshen annabi Dauda da harshen annabi Isa Annabi Isa shi kanshi ba Isra'ili bane, shi kanshi bani Isra'ila ne. Me yasa Allah zai tsine musu? Shine Allah ya tsine wa wadannan ne masu manufar lalata addinin da Allah madaukakin sarki ya turo annabawa da shi. Wannan ainihin wato tarihi kamar yadda kaji na kawo shi a takaice haka yazo ainihin a cikin Sa'annan an samu daga cikin malamai wadanda suka zauna suka bincike suka ainihin rubuta wannan tarihi a nan kasar mu ta Najeriya. Akwai wani bawan Allah mai suna Gashi ya rubuta wato na gaskiya dangane da tarihi. A cikin wannan littafi zaka samu gamsassun bayani da zasu banbance maka tsakanin wato annabi Isa na gaskiya da kuma ainihin wanda aka kirkira da sunan a bata addinin. A cikin wannan littafi zaka ga tarihin gaskiya na injila wanda ya sha bamban da tarihin wannan littafin a yau wanda ake rike da shi mai suna ainihin Don haka wani abun mamaki su da kansu kiristoci wadanda suka yi bincike suka zurfafa game da ainihin bincike sun gano cewa wannan littafi dake rike a hannun su a yau ba dukkanin shi ne daga annabi Isa ba. Da suna boye wannan hakikar amma sai suka ga zamani na bincike da wayewar kai dangane da tantance bayani ta kai matukar da babu sauran a cigaba da saka ya wannan. Don haka suka zo suna buga wani irin bible da gashi nan a hannu na wanda irin wannan bible din sai ka ga sun sa Wato bible mai haruffa da jan biro. Me ake nufi da wannan maganar? Mafi yawancin duk inda zaka gani zaka ga an rubuta shi da bakin biro. Abin da suke nufi wadannan san ba maganganun annabi Isa bane wadanda ya samo su daga Allah. Maganganu ne da aka kirkire su aka danganta su ga annabi Isa sannan zuwa ga Allah madaukakin sarki. Don haka ka ga mafi yawancin nan duk da ake budewa kashi casa'in da biyar na bible gashi duk sun rubuta shi da bakarta wa da wanda ke ishara akan cewa kaf babu maganar Allah a ciki nan wanda aka samo daga annabi Isa. In ka taho can karshe karshe shine zaka dan fara ganin wasu wurare 'yan hikwanna na 'yan kadan daga cikin wadanda zaka rinka ganin su an sa su da jan biro. Wadannan wuraren 'yan kadan din su ne kiristoci wadanda sun amince cewa wannan littafi ba daga Allah yake ba. Suka ce iya inda aka rubuta da jan biron nan nan ne kadai daga Allah. Wannan shine littafin da kiristoci suke bi a yau. Dukkan kirista kuma yayi imani da wannan in ba wanda ya butsare daga ainihin cikin dangi ba. Toh kenan wadannan suna bin wani addini ne wanda kamar yadda Allah ya fadi yace Allah yace mutanen nan da basa imani da Allah basa bin addinin gaskiya ku yake su har basu imani da ranar lahira ba. Abin da Allah ya halatta basa halatta shi. Abin da Allah yace haramun ne basa haram ta shi. Daga cikin kiristoci da yahudawa Allah yace ku yake su har sai sun shiga kaskancin da kowannan su zai bada jizya a halin kaskanci da wulakanci. Qur'ani wanda yazo bayan littafin Allah injila ya sauka bayan masu ainihin canje canje irin su bulus da makamantan su sunyi canje canjen da suka yi al'qur'ani ya sauka. Don haka kullum al'qur'ani yana kiran littafin da cewa an sauya shi. Sannan Allah madaukakin sarki kullum yana zargin su da cewa masu sauya littafin Allah. In ka karanta al'qur'ani tun daga farkon shi har karshen shi inda duk Allah yake magana a kansu sai ya zarge su da cewa Allah yace gwalalan azaba ya tabbata ga wadanda suke rubutun littafi da hannun su sannan su ce wannan daga Allah ne domin su samu 'yan kudi kadan. Yace azaba ta tabbata gare su game da abin da suke rubutawa. Azabar Allah ta tabbata gare su dangane da kudin da suke samu na wannan danyen aiki. Qur'ani ya bayyana mana komai game da wannan. Shehi a matsayin ka na babban mahardaci alaranma gangaran ka kamar yadda kakan kira kanka kakan ce kana da digirori inda digirori za'a bayar a hadda irin taka. Wadannan ayoyin baka san su bane? Kasan su ka haddace su, ka haddatar da wasu, ka fassara su tare da haka kake cewa dan izala bai kai wadannan irin mutanen wadanda wahayi ya sauka a kan Allah ya bayyana lalatattu ne addinin su lalatacce ba. Kana da aya kwaya daya da Allah madaukakin sarki ya ainihin fadi 'yan izala akan a yake su sun chanza addini sun kawo kaza sun kawo kaza sun kawo kaza. Kana da aya akan cewa 'yan izala suna rubutawa da hannun su suna cewa daga Allah ne amma kana da aya dangane da danyen aikin wadannan mutanen. Shehi ka dawo cikin taitayin ka ka auna wadannan abubuwa. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Don haka jama'a kunji kiristoci kuma kunji kadan daga cikin abubuwan da Allah madaukakin sarki ya fadi dangane da su. Na daga cikin siffofin su da suka shahara shine me? Shine kafirce wa Allah. Allah madaukakin sarki ya nanna ga wannan magana a wurare da dama in kana son ganin inda Allah yafi ko ina fedewa game da kiristoci ka karanta suratu Ali Imrana. Allah madaukakin sarki ya shiga ya fita game da dabi'un su gaba daya babu abin da ainihin ya boye suna da kafirci, suna da kin gaskiya, suna da hassada da kiyayya, suna da bin son zuciya sannan sun fi kowa jahiltar abin da Allah yake saukar wa da annabawan shi. Sannan suna da kirkiro bidi'a su mayar da ita ita ce asalin addinin Allah. Wadannan su ne kiristoci su wanene kuma 'yan izala? Me ce ce izala? Wadannan siffofi ne ake gane 'yan izala da su. Ita kalmar izala kalma ce ainihin wato ta larabci wanda duk ya karanta harshen larabci yasan ina ne ta samo asali amma menene take nufi a jimlance duk inda aka ganta a larabci gusarwa. Don haka za'a ga a cikin fikihu zaka ji sun ce babu babun gusar da najasa. Toh abin da ya faru wani gwarzon malami ne kuma mai suna Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi. Bayan ya karanci addinin musulunci gashi dan boko gashi hafsan sojoji ya zauna yayi nazari ya shiga ya fita dangane da tarihin yadda addini yake a kasar sai ya ga cewa ba daidai bane. Yana da kakin sojan shi ya fara wa'azi. Yana bayyana cewa abubuwa kaza da ake ba daidai bane, kaza da ake shi ya kamata, kaza da ake akwai gyara a ciki sai ainihin aka fara zargin cewa yana son ya kawo rudani. Idan kai dan ba na bakwai ne an yi wadannan tattaunawar baka nan har zuwa Kaje a cikin Akwai jaridun gaskiya tafi kwabo. A lokacin su suka yi tarwaito wadannan duk tattaunawa da karar da aka rinka kaiwa zuwa ga shugaban sojoji na wannan nahiya da dauko maganganun shi ana kaiwa Abubakar Gumi ana cewa ga wani yaron mu na soja yana maganganu wadanda muna ganin akwai tada hankali a ciki. A wannan lokaci da al'amari yayi al'amari har sai suka fara gaya mishi cewa yana da kakin soja ba dole ya fadi abin da yake so ba in ba ga tsoro ba ya cire kakin sojan mana. Ya sanya farin kaya ya shigo cikin su yaga zai iya fadi? A wannan makon ya rubuta takardar Yayi Yab bayyana a matsayin farin kaya ya cigaba da wa'azin kuma babu abin da ya same shi. Toh a wannan lokaci sai gwamnati ta rinka kama shi ana cewa yana yin wa'azi bashi da kungiya. Me ce ce sunan kungiyar shi? Ina rijistar shi? Su wanene suke tare da shi? Shine sai yayi shawarar toh bari ya kafa kungiya ya sa mata Al'ummar da ke gusar da bidi'a sai ya tafi neman tabarruki wurin sarkin musulmi sa Abubakar na uku a Sokoto. Da yaje ya gaishe shi ya fada wa sarkin musulmi sarkin musulmi ya ce mishi yaro bazaka iya wannan aiki ba. Muna fadi ne a tarihin ce ba dan wai yaron bane amma a wurin sarkin musulmi shi yaro ne. Yace bazaka iya wannan aiki ba za'a kashe ka. Yace ya yarda indai akan addinin Allah ne. Don haka malamin yace abin da nake so ranka ya dade ka sa min albarka a cikin wannan aiki yace Allah ya albarkace ka. Har ya tashi ya fita sai ya ce mishi dawo. Yace zasu kashe ka. Gusar da bidi'a a wannan kasa ka bar mutane su je su hadu da Allah wanda Allah ya soyewa gafara yayi wa gafara wanda Allah ya so yayi wa azaba yayi wa azaba amma gusar da bidi'a a wannan kasa tana da wahala. Don ta zama ita ce addinin su, ita ce mu'amalar su, a cikin ta aka haife su, a ciki suka tashi. Kace zaka gusar da ita yace a wurin Allah nake neman taimako. Sai yace toh in har haka ne kayi kuskure in ka gusar da bidi'a baka tsai da sunna ba. Me yasa bazaka kara sa da sai ya karba. Da nan ne yaje yana kiran kungiyar Al'ummar da ke gusar da bidi'a kuma su dasa sunna. Sai sarkin musulmi yace toh kaga tayi daidai da In an rusa shirka sai a tabbatar da tauhidi. In an rusa bidi'a sai a tabbatar da sunna. Wannan shine tarihin wannan kalmar da ake cewa izala a kasar nan da kuma tarihin dan izala da kuma cewa 'yan izala. Ma'ana mutane ne da suka fito suka ce zasu gusar da bidi'a zasu tsayar da sunna. Wadannan siffofi ne siffofin wadannan mutane. Kaga dai siffar su ta farko sun yarda Allah kadai ake bautawa bashi da abokin tarayya. Sun yarda manzo Muhammad daga Allah yake Allah ya aiko shi. Suna kaunar Allah, suna kaunar manzon Allah suna kaunar sahabbai suna kara mutuncin su. Ba dan komai ba saboda sahabbai su ne waliyan farko bayan annabi Muhammad Don haka waliyan farko bayan annabawa su ne mabiyan su. 'yan izala gaba daya suna so basu taba zagin wani daga cikin ainihin manya manyan waliyan Allah daga cikin annabawa da sahabbai da wadanda suka biyo bayan su da kyautatawa irin tasu har tashin alkiyama ba. Wannan ita ce ainihin siffar su. Sa'annan daga cikin siffar su suna son gaskiya da kuma yada ta. Sannan kuma suna bin gaskiya da kuma tsayayya a kan ta. Sannan suna kare gaskiya ba tare da sunyi kara dangane da kare gaskiyar ba. Sannan kuma suna da watsi da bidi'a da kuma rashin kirkiro bidi'a da rashin goyon bayan bidi'a sannan basa yi wa bidi'a kara don ba abin da ya hada su da su rukuntaka da ita. Ina fatan an gane? Suna koyon karatu da ilimi kuma suna yada shi kuma suna bin sunna annabi bayan sun tace ingantacciya daga cikin ta sannan sai suyi watsi da wanda take ainihin ribabbiya ce. 'yan izala su ne wa iyaye biyayya tukuru suna girmama manya da kuma sanin darajar na gaba da kuma bin ainihin wato na gaba a bisa gaskiyar da na gaba yake a kai. Wanda duk bai san 'yan izala ba wadannan su ne 'yan izala. Mu kuma da muke maganar nan mu ne 'yan izala. In baka taba jin maganar 'yan izala ba toh yanzu da kake jin wannan maganar muryar dan izala kake ji kuma 'yan izala 'yan izala ne da kansu suke magana yanzu. Ba wani ne yake ruwaito maganganun su ba. Don haka wadannan su ne 'yan izala. Toh dan girman Allah shehi da duk wanda ya yarda da waccan magana ta shehi ya dauki wadannan siffofi na 'yan izala ya gwada su da wadancan siffofi na kiristoci. Tsakani da Allah baka yi adalci ba shehi gaskiya saboda Allah. Kuma kayi awo da ma'aunin kuskure ba dan komai ba tun da ake a tarihi ba'a taba inda aka dauko wanda yake musulmi ne musulmi ne saboda ana da banbancin wani abu a fifita shi a lokacin da musulmi suka shiga hadari irin wanda al'umma suka shiga kansu a wannan kasar ba. Ba taba samun wannan aিনিhin ba jama'a. Don haka shehi kayi ka tobara kuma kayi kuskure abin da muke fata kayi marmaza ka janya wannan kuskure ba dan komai ba kana daga cikin jagororin da ke kiran a zo a hada kai. Wannan maganar ta raba kan al'ummar musulmi baki daya har cikin masallacin ka har cikin almajiran ka kan su ya rabu a kan wannan maganar da kake fadi. 'yan darika duk inda kuke ku bani amsa. Kun yarda da maganar shehi? Ku bani amsa. In kun yarda toh kuna daga cikin jagororin wargaza kan musulmi. Idan kuma baku yarda da wannan magana ba ku fito ku bayyana wa shehi kuskure da ka tobara da ke cikin wannan magana musamman a irin wannan lokaci wanda ake fatan kowa ya daure yayi karfin hali ya cire son zuciya da son duniya ya tsaya wa gaskiyar da 'yan uwan shi al'ummar musulmi suke a kan ta. Jama'ar musulmi wadannan su ne takaitattun bayani dangane da abin da ya shafi siffofin kirista da siffofin ainihin dan izala. Toh sai magana ta gaba ita ce shin gwamna Ibrahim Shekarau na jihar Kano a yanzu kuma dan takarar jam'iyyar ANPP game da shugabancin kasar nan Najeriya shin dan izala ne? Toh idan ka fahimci hakikanin abin da ake nufi da dan izala shine mai son gaskiya mai bin Allah mai bin annabi mai biyayyar iyaye da tsayawa gaskiya mai bin sunna da yakar bidi'a wanda baya cin amana. Idan ka kira gwamna Ibrahim Shekarau cewa dan izala ne a karkashin wannan maganar bakayi kuskure ba. Domin gwamna Ibrahim Shekarau musulmi ne mai son bin daidai musulmi ne mai sanin darajar Allah da annabi mai sanin darajar waliyai wanda ke kiyaye mutuncin sahabbai wanda ya san darajar iyaye ya san darajar na gaba. Idan ka kira Shekarau a karkashin wadannan siffofi na 'yan izala cewa Shekarau dan izala ne kayi daidai. Kenan a karkashin wannan duk wanda yake da wadannan siffofi shine abin da ake kira izala. Don haka zaka ga wadanda suke amsa sunan 'yan izala ne suna da yawa dayawancin su kuma basu shiga cikin kungiyar ba domin ya bayyana cewa abin da ake nufi da izalar gusar da bidi'a da tabbatar da sunna. Kai ka isa kana cikin taitayin ka kace baka gusar da bidi'a? Kai ka isa kana da hankali ba motsuwa kai kace baka son tsai da sunna? Don haka a karkashin wannan maganar idan ita ce ta sa shehi ke nufin cewa Shekarau dan izala ne gaskiya ne amma in yana nufin cewa Shekarau ya shiga kungiyar izala Shekarau bai shiga kungiyar izala ba. Shekarau dan boko ne malamin makaranta ne daga baya ta juye yazo ya zama dan siyasa amma ba abin da ya hada shi da za'a ce izala. Kuma shehi ka manta irin sadakoki na musamman da Shekarau yake aika maka da su?
[Segment 4/5 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
Tsakani da Allah. Ka manta irin yadda shekaru yake zuwa yana neman tabarukinka? Ka manta irin yadda shekaru yake neman duk sanda kai ka ziyarci Kano kaje ka samu mishi albarka? A karkashin wannan ne nace shehi yayi butulci. Shehi yayi butulci amma me ya ja shehi yayi wannan butulci? Nace wa da shekaru Gwamna Jonathan. Me ya ja shehi ya fada haka? Shine Jonathan ya bashi kudi. Jonathan ya baiwa shehi lambar girmamawa. Iyakarta kenan. Shi kuma shehi dama babban abun da yake so shine a bashi kudi kuma a bashi girma ko ta kaka ne. Toh tunda Jonathan yayi mishi haka dan haka Jonathan yafi shekaru. Allah wadaran naka ya lalace.
[Speaker seg4-spk:1]
Amin.
[Speaker seg4-spk:0]
Dangane da abun da ya shafi hukuncin zaben kafiri kuwa pau pau pau bai halatta ace ga kafiri ga musulmi sun tsaya kayi neman wato zabi wanda yake kafiri bane. Sam bai halatta ba. Amma game da yan uwan mu musulmi da suka samu kansu a kasar Amerika da Australia da Canada wanda za'a fito ana takara dukkan su kafirai ne. A lokacin sai su dubi wanene zai tsare wa musulmi yancin su. A wannan halin malaman mu sun bada fatawa akan cewa anan musulmi in ya zabi wanda yake krista ai ba ya fifita krista akan ainihin musulmi bane. Sai dai ya zabi yayi zabe ne daidai da halin wurin da ya samu kanshi a ciki. Wannan kenan a irin wannan halin da muke ciki a yau a kasar wace fatawa ce daidai? Ita ce bai halatta a zabi wanda ba musulmi ba. Ita kenan fatawa bayan ta babu ainihin wata. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Sannan ina matsayin mu mu yan izala game da zaben dan darika inda zai tsaya takara da krista? Idan da krista zai tsaya takara gefe guda dan darikar Tijjaniya mai carbi dan sha bakwai ne ko dan sha hudu ya tsaya takara zamu saka wa dan darika kuri'a ne. Ba zamu zabi krista akan dan darika ba kuma ba zamu yi fatawa akan ya halatta a zabi krista a bar dan darika ba. Kuma ya kamata a sani hatta Buhari da muke cewa shi za'a zaba sam Buhari ba dan izala bane ko miskalar zarratin. Buhari ba dan izala bane amma abun da muka shaida shine Buhari yana cikin al'ummar musulmi kuma musulmi ne don haka wannan ya ishe mu ba sai ya shiga kungiya kaza ba sai ya karbi darika kaza ba. Buhari yana musulmi yana cikin al'ummar musulmi shine musulmi suka fifita saboda wannan dalili. Don haka matsayin mu mu yan izala gaba dayan mu a Najeriya Idan da dan darika irin Dahiru Bauchi zai tsaya takara tare da Jonathan toh Dahiru Bauchi zamu zaba. Shehi kai zamu zaba mu ba zamu zabi Jonathan ba duk da wannan kasassabar. Idan da zaka tsai da danka a Bauchi takara da wani arne na sayawa daga garin Tafawa Balewa danka zamu zaba shehi ba zamu zaba arnan garin Tafawa Balewa ba. Wannan mu shine matsayin mu yan izalu gaba dayan mu. Ina fata an gane. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Dangane da maganar shehi akwai gyara kuma ta jawo kace nace zanyi amfani da abubuwan da mukayi ta gani ne wasu matasa suna tattaunawa akan internet sai muka ga cewa mu tunda shekarun mu ya fara ja bari mu bar su yan shekara ashirin da biyu ne zuwa talatin. Suka rinka mai da martani ga shehi daga cikin su kuma har da yan darikar Tijjaniya akan ainihin website na Yahoo, Facebook in ka karanta zaka yi ta gani. Don haka kadan daga cikin wadannan maganganun sai an yanko maganar shehi tukunna sannan sai a kawo irin maganganun da wadannan matasa suka yi. Gashi shehi yace ga ra Jonathan da shekaru inji sheikh Dahiru Bauchi sai matashin farko mai suna Jibril Muhammad Yusi daga garin Bajoga ta ainihin wato jahar a'a jahar eh daga jahar Gombe. Website din shi shine abun nan email address din shi shine gm y u c at yahoo dot com gm y u c at yahoo dot com yace a'uzu billah. Gaskiya bana ganin ya isa dalili da za'a ce ga ra Jonathan da shekaru amma a cigaba da karanta labarin dan mu kara fahimtar sa sosai Allah ya saukake. Abun da wannan matashi na farko ya fadi kenan yace duk dalilan da shehi ka bayar kaji jikan ka nema wannan. Yace Allah ya saukake yace har yanzu yana ganin baka kawo dalilan da zaka iya kara kan ka ba. Saurayi na biyu da aka kawo maganar ga ra Jonathan da shekaru sheikh Dahiru Bauchi shi kuma yana da email address dake m fatuhu m fatuhu 313 at yahoo dot com yace haba malam har yaushe zamu yi ta zama malaman nan na amfani da sunan addini suna cutan mu. Kaji abun da shi kuma yace maka shehi haba yaushe za'a zauna kuna ta amfani da sunan addini kun karbo kudi da lamba c c o n eh kuna ainihin eh eh kuna ainihin wato cewa a zabi ainihin kaza kaza toh saurayi na biyu kenan na uku guda aka kawo ga ra Jonathan da shekaru sheikh Dahiru Bauchi yace sai shi wannan mai suna Muhammad Adamu dash m a g at yahoo dot com Adamu dash ina fata an gane m a g at yahoo dot com sai da yace ga ra Jonathan da shekaru inji sheikh Dahiru Bauchi sai yace a'a wannan Dahirun ba na Bauchi bane sai dai Dahirun Ebele eh ba na Bauchi bane shi abun da yace wannan Dahirun ba na Bauchi bane a'a su basu saba jin Dahirun Bauchi ya fadi wannan ba wannan na Ebele ne. Toh jama'a a takai kunji wadannan maganganu wanda dama sune ainihin na tsaro na rubuto su na yo mana isharorin su ba dan komai ba domin ainihin wato in fadakar da mu a wannan majlisi da muka zauna don haka ina fatan maganganun da na fadi sun isa su zama ainihin fadakarwa da matashiya ga duk wani wanda ya rodu kuma maganganu irin wadannan bai halatta ayi shiru ba ko muna fatan cikin maganganun da muka fadi bamu yi wa abokin uban mu rashin kunya ba bamu yi wa tsiwa ba bamu yi cin mutunci ba sai dai ita maganar kasassaba ce kuma katobara ce don haka shehi bamu yadda da ita ba kuma muna cewa wannan dalili ne dake nuna anya shehi ka gama tafsi ka gama fahimtar tafsirin kur'anin nan da kake kuwa? Mutumin da ya karanta al'kur'ani tun daga suratul Fatiha da bakaran Shahanasi yazo yana fifita masu irin wadannan maganganu dake zagin Allah anya shehi kaje ka sake karatun ka da tisa ainihin tilawar ka ta Ali Imrana da Ma'ida da suratul Nisa'i ina fatan shehi ya koma ya karanta daga cikin littattafan malaman mu na ahalus sunna irin su Ibn Taimiya da su Ibn Kayyim wadanda shehi ya sha ce musu wahabiyawa yana sukar su ya ga matsayin mu dangane da abun da ya shafi addinin christianity daga ciki akwai littafin Ibn Taimiya da ya rubuta ya sa mishi Gamsasshi ya amsa ga wanda ya sauya addinin almasihu ga fassarar shi na turanci gashi sannan sai gashi almajirin Ibn Taimiya Ibn Kayyim ya rubuta sannan professan musulunci professa Bilal Philips shi kuma ya rubuta shehi duk kana bukatar ka karanta wadannan littattafai in ba haka ba yayan ka yan boko su karanta maka dan kayi kyakkyawar fahimta amma kawai an dauke ka an kai ka Abuja an kunna maka iya condition din da wuta bata daukewa shehi kazo kana kasassaba irin wannan a karkashin haka ne cikin masu wadannan comment din nan fa wani matashi yace toh tsohon nan fa ya fara rudewa sai ainihin wato a fara taka tsantsan da abubuwan da yake fadi kenan wadannan maganganun nashi sun ja a koma ayi waiwaye dangane da sauran maganganun ma da ya saba fadi ba dan komi ba saboda me? Saboda ire iren wadannan maganganun suna nan zankame a cikin ainihin wato maganganun shi saurare abun da Aliyu Sabo yake cewa da ya kawo wannan maganar yace ga ra Jonathan da shekaru sheikh Dahiru Bauchi sai yace tsufa yayi gaddama wannan mutumin fa ba yau ya fara tubka da warwarewa ba da sunan addini dukkan masu sauraren wannan tsoho a kafafen yada labarai sun san haka. Jama'ar musulmi wadannan kadan daga cikin maganganun da jikokin shi yan shekara ashirin ashirin da biyar zuwa talatin suka fadi kenan duk akan internet maganganun suna nan. Abun da muke cewa jama'ar musulmi gaskiya saboda Allah muna nan ainihin a matsayar mu ba gudu ba ja da baya sannan dukkanin wani dan takara yaji tsoron Allah dangane da wannan kara da yan uwan shi suka tsaya suke mishi ya san cewa karan nan in kaci amana ba irin amanar da ta wuce bace amana ce da tsoron Allah amana ce da sunan addini amana ce da sunan al'ummar musulmi kuma Allah madaukakin sarki ba zai sassauta maka ba ko kadan. Sannan jama'a dan girman Allah dukkanin zabuka da zasu biyo baya kar ku sake ku ainihin ja da baya saboda kunji an sanar da kaza anmur da kaza ku ce toh zabe na gaba ma ko mun fito a'a ku fito kuyi abun da yake daidai a kowane yanayi domin bayan zabukan gaba daya akwai abubuwan da ta iya yiuwa su biyo baya toh in akayi na farko aka kashe muku gwiwa da magudi ya baku damar kuka ki fitowa a na biyu toh anan kuma kune kuka sarayar da a kayar da kuka yauwa ta hakika. Don haka jama'a ku daure an daga zabe cewa babu zabe gobe kar ka damu kuma shi jega ku taya shi addu'a ita kasa kuma ku taya ta addu'a kamar yadda akayi zabe lami lafiya a kasar Nijar toh haka za'ayi zabe lami lafiya a Najeriya kuma Allah ya tabbatar wa da mai gaskiya gaskiyar shi na daya kenan na biyu dukkanin wanda yake tunanin cewa zai shiryo yan daba da yan iska wadanda zasu zo su tada hautsini toh irin abun da muka fadi a mciya muna sake fadin shi kai ko limami ne ranar zabe an yafe maka sa doguwar riga kasa jamfa in kai liman ne in kuwa gayu ne dama shi yana da t-shirt da t-shirt saboda in wani ya suru a kwati ya kamata ku bishi sai an dawo da akwatin. Duk wani magun magun da za'ayi jama'a kar ku amince sannan jami'an tsaro kuji tsoron Allah ku sani da cewa da makaman ku da barazanar ku a 2007 akayi abun da akayi me ya kai shugaban ku Tafa Balogun? Toh sa'annan wadannan mutane ba yan amana bane kamar yadda na fara fadi ajiya wanda duk ya san abun da shugaba Obasanjo yayi a kasar nan game da wadanden da su suka dakko shi suka yi mai wankan tsarki suka sanya mishi riga ta mutunci da takalmi gogagge sai da yayi bima fi yawancin su ya zuba su a kurkuku sai da yayi bima fi yawancin su ya wulakanta su na karshe karshen nan shine Bode George. Bode George din nan wani tsohon aminin Obasanjo ne wani tsohon abokin harkar shi ce tunda ga ta harkar gwamnati da kwangila da harkar kasuwanci da abun da ya shafi mulki amma yau sai ga Obasanjo ya dauke shi ya jefa shi a kurkuku har ya sauka ba'a sake waiwayar Bode George ba sai mako uku da suka wuce ne sannan aka sallamo Bode George da shi da wasu mutane amma a farkon mulkin Obasanjo jeka kofar gidan Bode George ka gani motocin gwamnoni ne suke goslo duk wanda yake da wata bukata a wurin Obasanjo in ya tafi wurin Bode George Bode George zai daga waya ne kawai ya buga wa Obasanjo shikenan wannan matsalar takwaran yi amma sai da Obasanjo ya dauke shi ya jefa shi a kurkuku don haka mutanen nan yan cin amana ne in ma kuna ganin sun baku kun ansa toh zasu ainihin ci amanar ku a halin kuma mutanen ku kun ainihin ci amanar su. Matasa da aka dauka daliban jami'o'i da wadanda aka dauke su n n y s c masu hidimar kasa kuji tsoron Allah kar ku sake saboda dubu biyar ko dubu goma da za'a baku kuyi murdiya ko kuyi rashin gaskiya ku sani da cewa babu abun da zai cigaba da zaunar da kasar mu lafiya sai gaskiya da adalci da kuma barin gaskiya da adalci su guda na sannan ka sani da cewa duk lokacin da kaje ka tsaya a wurin zabe aka fusatar da kai kayi fishi ka tafi toh dama an ci ribar fusatar da kai din da aka yi amma duk yadda aka fusatar da kai in ta kama kuyi committee a wurin duk lokacin sallah a zahar yayi wani ya muku sallah a gurin amma kar ku sake ku bar gurin idan kuka sake kuka bar gurin babu shakka wadannan jami'an tsaran hukumar a a ina a a Ainek in ma ayi corrupting din su ko kuma afi karfin su duk an shirye wadannan magudin toh wai dan menene mutani zasu shekarar goma sha suna mulki amma har yanzu suna son komawa sai sun koma ta karfi da yaji me yasa wannan yana tabbatar da cewa basu yi wa mutane abun da ya kamata ba. Sa Abubakar Tafawa Balewa lokacin da suka yi mulkin farko da zasu yi tazarce fitowa yayi gidajen rediyo da jaridu yana cewa yaku yan Najeriya ku zabe mu saboda duk abun da mukayi muku alkawari zamu yi munyi yanzu babu sabon alkawari domin wanda yayi alkawarin farko ya cika a karo na biyu da aka san shi baya bukatar sai yace zai yi tsakani da Allah me yasa bazaku ce yaku yan Najeriya ku zabe mu saboda munyi muku ba sai dai ku ce ku zabe mu zamu gyara wutan lantarki wutan lantarkin da kuka samu akan mulki ta ragu daga adadin da take ku zabe mu zamu gyara game da ruwan pamfo ku zabe mu zamu gyara game da harkar security ma'ana kullum a cikin gyara ake kuma wancan mokacin haka kuka ce a yafe muku a zabe ku zaku gyara toh sannan na yo wata magana a cikin wancan kaset da nayi a mciya wanda nake so in maimaita ta ya kamata ku kuma talakawan kasa ku san cewa su fa wadannan mutanen da ake gwagwarmaya akan zaben su Buhari kadai muka sani shine kadai gaskiyar shi ta bayyana sauran sunzo sun shiga albarkacin Buhari ne ba'a san ina suka dosa ba ba'a san me cece manufar su ba ba'a ma san ko yan aikin su wane da su waye bane a karkashin wannan su suji tsoron Allah zargi da tsoron da ake game da su kai ya bayyana sannan ku kuma talakawa wallahi ku sa zuciyar ku a sanyi babu mai iya gyaran Najeriya sai Allah shi kan shi Buhari in ya hau irin yadda ya samu kasar ada gwal gwale sai yaci shekara hudu tukunna bai san ina ne clutch da birkin da zai taka ya kara mata giya tayi gaba ba ba dan komi ba saboda rudanin tattali da siyasa da addini da zamantakewa da halaye da kasar take ciki amma mu abun da muke fata shine mutane irin su in sun hau zasu hana barna ta cigaba toh matukar aka samu barna aka tsai da ita daga inda aka same ta toh in Allah ya so an sanya dan ba dangane da gyara ana sa rai gyara zai biyo baya domin idan gobara ta kama wuta a gida me ake fata? Ayi marmaza a kashe ta kafin ta raunata gidan idan ta raunata gidan in aka zo baki dayan kayan gidan sun kone gidan kuma sai an sake gina wani idan ko iya abun da taci taci in aka tashi gyaran da za'ayi kadan ne daga inda ta tsaya toh abun da muke fata kenan bawan Allah nan in Allah shi ya dauka yayi ba mu sai mun taya shi da addu'a sai kuma mun taya shi da hakuri kuma mu sani da cewa ko shi din ne sai an shekara da shekaru wutan kasar nan bata gyaru ba ruwan harkar kasar nan bai gyaru ba saboda na daga cikin matsalar hukumomin kasar irin nefa da wata board shine wasu tsofafin kuraye ne da wasu tsofafin jiragen ruwa wadanda sun ribe a gabar teku su ba'a janye su ba su kuma in Sabo yazo zai sauke kaya bazasu bashi guri ba toh kaga za'a dade ba'a sauke kaya ba saboda haka ya kamata mutanen kasar nan su fadaka babu shakka hukumar nefa tana cike da wasu tsofafin kuraye ne wadanda jiya i yau duk sanda aka zo su din ne suna nan don haka idan har ba revolution za'ayi na tace wa da tantance duk wani tsohon burgu da duk wata tsohuwar kura da duk wani muzuru mai ci ba bismillah ba wallahil azimi kasar bazata gyaru ba saboda haka al'ummar mu kusan haka don kada gobe ku dawo kuna zargin mu cewa ai su malam ne suka ce mu zabi su wane ga su nan mun zabe su har yanzu basu tsina na komai da komai ba toh sa'annan su kuma yan takarar da suka dogara da wasu matasa wadanda zasu ainihin yi musu satar
[Segment 5/5 | 01:20:00–end]
[Speaker seg5-spk:0]
Akwati abinda nake cewa wadannan matasan kai canku kuma kalubalen ku. Me yasa wannan dan takarar bai dibo kannen shi da yayan shi ya saka a cikin ku ba? Me yasa ranar zabe ke kwashe yayan shi da matan shi su bar anguwar? Me yasa ba zaku yi tunani akan haka ba? Ko kun san cewa duk barnar da take faruwa ta hanyar sata akwati da tayar da hayaniya wasu matasa ne wadanda abinda ake basu baya wuce naira dari biyar. Abinda ake basu baya wuce dubu biyu. Wasu masu aiki ne da bai wuce a basu dubu biyar ba. Wasu shuwagabannin wasu hukumomi ne da jami'an tsaro wadanda basu wuce ace an kai musu dubu hamsin ba. Daga karshe kuma wahalar kowa ya shata bakwa fatan akalla kasar mu ta samu gyara kamar yadda kasar Ghana ta samu gyara shekara talatin da ta wuce ana wahala a kasar Ghana. Yanzu kasar Ghana muke diban yayan mu muna turawa suje suyi jami'a. Bakwa tunanin cewa muna son kasar mu ta samu gyara kamar yadda sauran kasashen duniya suka gyaru. Bakwa ganin cewa komai game da al'amarin kasan mu daga shekara talatin zuwa yanzu babu abinda ya gyaru. Bakwa ganin cewa hatta na'urar nan ta GSM rashin gaskiyar masu mulki ya hana ta tafiya lafiya. Bakwa ganin cewa galibi a credit da kuke sakawa na kudi ana yanke wani kwandala yayi ana zuba wani mai mulki a cikin account din shi. Bakwa fuskantar haka? Yaushe kasan mu zata gyaru? Idan kai soja da dan sanda da DPO da OC da area commander da IDIN wato wanda yake shugaban yan sanda IGI na kasa da commissioner din sanda in baku ji tsoro ba Allah ba. Yaushe kasan nan zata gyaru idan malamai da masu wazo zoi baku ji tsoron Allah ba. Idan masu saka kuri'a baku ji tsoron Allah ba. Sannan kai da akace ba'a son ka angaji da kai dan menene ba zaka hakura ba? Ka bada wuri mana. Daga baya in kana da alheri mutane zasu gani su nemi dawo da kai. Kuje kuga gwamna Kwankwaso mana a Kano. Ance ba'a son shi. Da akace ba'a son shi. Na sama da shi sun bada damar za'a murde kuri'a a tabbatar mishi yace baya so. Tunda ance ba'a son shi baya so. Ranar da yazo zai miya ka mulki sai yace yana rokon duk wanda ya batawa ya yafe mishi. Ashe kenan in ka koma Kano yanzu kaje kaga wanene kanawa suka fi goyon baya. Kwankwaso suka fi goyon baya. Ashe asali talakawan kasar ba jam'iyyar PDP suke ki ba. Amma zaluncin da akai musu da sunan jam'iyyar aka kasa gyarawa shine ke musu ciwo. To shine yanzu talakawan sunce suna son canji ne. Dan haka a bari canji ya faru. A bar musu abinda suka zaba. Duk abinda suka zaba koda anyi taro anga bai dace ba su sunga wannan ne ya dace da su. Domin gubar wani shine abincin wani. San da kuke ganin wane bai dace shugabanci ba masu kada kuri'a sunce shi ya dace ku kar ku basu guri. Idan ta rikice kuna da passport da visa sai ku gudu ku barwa wadanda suka zabi wadanda suke so kasar su ci wahalar abinda suka zaba. Amma dan menene zaku ce sai kun zaban musu na gari. Kuma nagarin nan ku ne. Saboda Allah. Jama'ar musulmi wannan shine ainihin sako na wanda yake maida martani ne zuwa ga shehin darika shekh Usman Dahiru Bauchi akan wannan kasassaba da yayi. Dan haka shehi hatta yan darika muna fatan su fito suyi maka bara'a suce ba ruwan su dangane da wannan maganar da ka fadi. To sa'annan sai yan shi'a. Yan shi'a suma yaya yaye ne ga ire iren wadannan mutane na yan dariku wadanda sun fito karara a bisa harshen kattaginsu shine Ibrahim Yakubu Zazzaki. Sun tabbatar da cewa babu dalilin da ya fifita zaban musulmi akan wanda ba musulmi ba. Kamar yadda babu dalilin da ya fifita a zabi wanda yake ainihin wato musulmi ne ace ba za'a zabi wanda yake ba musulmi ba. Haka aka samu wasu kananan kwari daga cikin yan dariku da suka fara tsurowa a Kaduna. Wai suma sun fara goyon bayan wannan saboda an dauki yan mukamai an basu duk wata ana sa musu dubu dari a ainihin cikin account. Wannan lalata ce wanda yake wallahi tallahi sai kun dawo kun fi kowa na dama a kanta. Kuma wannan yake nuna ashe da'awar da su Zazzaki suke suna cewa azo a hada kai. Babu wadanda suka ki a hada kai sai yan izala. Ashe asalin wadanda ke raba kan musulmi sune yan shi'a su Zazzaki da yan darika su Dahiru Bauchi sune suke raba kan musulmi. In ba haka ba kashi casa'in da biyar na al'ummar musulmi na arewacin kasan nan gaba daya alkiblar su guda daya ce itace gabas. Amma su sun dawo sunce a'a ba nan ba yamma. Gaba dayan al'ummar kasar musulmi sunce a fuskanci inda Allah daya yake. Su kuma sunce a'a inda Allah uku yake nan za'a fuskanta. Wannan shine matsayin yan shi'a da matsayin yan darika. Sannan mu kuma musulmi yan izala wannan shine matsayin mu. Sannan kuma wannan ke tabbatar mana da cewa ashe kafirtar da musulmi da ake zargin yan izala sunayi ashe yan darika ma wannan ainihin harkar hajar su ce. Dan in ba haka ba ya zaka yi kace wanda ke cikin musulunci wanda ke fadin la ilaha illallah wanda kai kake cewa a dena kafirta mai la ilaha illallahu. Mu yan izala muna cewa la ilaha illallahu muna cewa muhammadu rasulullahi mun yadda da waliyan Allah muna zikiri muna aikin hajji muna hadda alkur'ani amma ace lalacewar mu a wurin ku ku yan darika har tafi ainihin kristoci to wace irin kafirtawa ce kenan baku mana ba. A karkashin wannan shehi bamu yadda da maganar ka ba ko kadan kuma muna kiran al'ummar kasan nan su fito kaf din su suyi Allah wadare da ainihin wannan maganar. Jama'ar musulmi kamar yadda muka ce ayi hakuri a tattaunace kwarai da gaske muka gabatar da wadannan bayanai wadanda fadakarwa ce nusarwa ce kuma muna fatan in sha Allahu ta'ala zamu cigaba da yin ire iren wadannan bayanai a wuraren karatuttukan mu wadanda zasu cigaba da zuwa. Kuma yanzu mun sanya duk ranar Alhamis a kiyaye duk ranar Alhamis za'ayi karatun Bukhari a wannan guri. Sannan a dawo kuma ayi ainihin ranar asabar da lahadi din. Hakikanin al'amari ba tare da mujamala ba mun kara ranar Alhamis ne a karatun Bukhari saboda daddatsutsa kiyarmakon da zamu rinka fadakar da mutane dangane da zaban da za'a rinka yi ranar asabar. Dan haka duk ranar Alhamis kasaro Bukharin ka ka tawo nan karatun Bukhari za'ayi. Sannan kuma sai a gaya maka Menene ake ciki al'umma ina ne aka bullo muku ina ne zaku kauce. Don nan muke cewa
============================================================
[Part 2]
============================================================
[Segment 1/5 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yan uwa masu kallon mu da sauraron mu na kusa da na nesa da wadanda zasu ji mu su kalle mu ta kafofin yada bayanai na zamani. Kuna sauraron mu da kallon mu ne kai tsaye daga masallacin mu dake nan muciya sabon garin Zaria jihar Kaduna a Najeriya. Mai suna Masallacin da aka fi sani da masallacin Albani. A yanzu daren asabar da ya daidai da ainihin wato ashirin da takwas ga watan Na da shekara dubu daya da dari hudu da talatin da biyu daidai da daya ga watan ainihin wato April shekara ta dubu biyu da sha daya. A yanzu mun zauna ne domin mu cika alkawaran da mukayi wa jama'a na cewa in Allah madaukakin sarki yaso a wannan dare na juma'a in Allah yaso wato daren asabar zamuyi musu wa'azi dangane da al'amarin da baturan yau ke kira Wato me ake ciki a yau? A yau din da muke nufi ba yau ta juma'a ko yau ta asabar ko yau ta litinin ba. Ma'ana wane yanayi ne muke ciki yanzu dangane da tarkatarkar siyasa. Sannan wacce alqibla ya kamata al'ummar mu ta musulmi su fuskanta dangane da wannan tarkatarka ta ainihin wato siyasa da ainihin ake ciki. Ba dan komai ba hakikanin al'amari rudanin siyasa da rudanin yan siyasa ya kai matuka matuƙar da talakawan ƙasan nan gaba daya a ruɗa suke basu san alƙiblar da ya kamata ainihin su fuskanta ba basu san wanene ya kamata su ainihin marawa baya ba basu san wanene ya kamata su amintu da shi a matsayin in ya tsaya da sunan addini ko ƙabilanci ko yanki ko yare ko wani abu daban da ake kirarin siyasa da shi a wannan zamani wanene ba zai basu kunya ba. To insha Allahu ta'ala wannan wa'azi nawa zan gina shi kamar yadda muka saba a ƙarƙashin ainihin wato alƙur'ani da sunnar manzon Allah ingantacciya. Don haka wa'azin zan taƙaita shi ƙwarai da gaske domin ina son in bada dama ga manufofin da nake so in tattauna su in tattauna su din insha Allahu. Sannan kamar yadda ka sani Albani duk duniya ba yaron kowa bane don haka wannan wa'azi ba'a zo ayi shi dan a goyi bayan kowa ba ko wanene. Abin da Albani ya amince da shi tunda yake a wannan teburi da kake gani a ƙalla yau shekara ashirin ana irin wadannan tattaunawa da karantawa a wannan kujera da wannan lasifika a wannan majlisi wanda tun kafin a sa lasifika yau shekara talatin da daya kenan kowa yasan cewa abin da zuciya da akidar Albani ta amince kadai shi yake faɗi game da addini ne game da siyasa ce game da rayuwa ce game da tattali ne wannan abun yayi maka daɗi ko bai maka daɗi ba don haka Albani bai san wata ƙabila da zai goyi bayan ta balle wata jam'iyya balle wasu tarin mutane ba domin kamar yadda nake faɗe din ba yaron kowa bane ni ban ci tuwon kowa na girma ba sai na uba na kuma bana rayuwa a ƙarƙashin inuwar ko wacce jam'iyya bana rayuwa a ƙarƙashin inuwar ko wacce ƙungiya kuma duk duniya ni ba ma'aikacin ko wacce gwamnati bace don haka babu wata masarauta duk duniya da nake wa aiki sai masarautar da mamallakin ta yake burbushin al'arshi.
[Speaker seg1-spk:1]
Allahu Akbar.
[Speaker seg1-spk:0]
Sarki da daukaka sun tabbata ga Allah. Don haka zan fara da ainihin wato wannan wa'azi nawa wanda ainihin insha Allahu ta'ala sai tafiya tayi tafiya tukunna za'a ji taken wa'azin saɓanin yadda aka saba
[Speaker seg1-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:0]
Zan fara da jawo hankalin mutane dangane da amanar da Allah madaukakin sarki ya danƙawa duk wanda ya ɗora shi a matsayin shugabanci. Ga wani hadisi a cikin littafin Hadisi na dari takwas da casa'in da uku Wannan hadisi Imam Bukhari yayi mashi sharar fage da wasu fatawoyi da tattaunawa dangane da halaccin yin juma'a a ainihin wato wasu alƙaryu da kuma wasu birane bayan da ainihin Ibn Shihabin ya gama bayar da wannan fatawa sai ya ɗaure fatawar da hadisin manzon Allah wanda ya samo shi daga malamin shi mai suna Salim. Salim ya bada labari cewa lallai mahaifin shi Abdullahi dan Umar ya kasance yana cewa yaji manzon Allah yana cewa Dukkanin ku masu kiwo ne kuma dukkanin ku sai kowa Allah ya tambaye shi game da kiwon da ya bashi. Wannan kulliya ce ma'ana ce kowa ya ɓata zai sha duka haka suka ce har da mangari. Tafi dandalin wasan yara zaka ji fassarar ta. Ma'ana duk wanda Allah madaukakin sarki ya danƙa wata al'umma a hannun shi annabi ne manzo ne limami ne malami ne mai gida ne shugaban ƙasa ne gwamna ne komishina ne fam sek ne a din shi ko wanene sai Allah madaukakin sarki ya tambaye shi game da nauyin wadannan mutane don haka in muka koma cikin al'qur'ani sai muje Allah yana cewa Sai mun tambayi wadanda aka aika wa da annabawa kuma sai mun tambayi susuwa su manzon nan sai an tambaye su. Jama'a mun ji wannan da kyau ko? Sai an tambayi al'umma sai an tambayi kuma annabawan da aka aika wa al'ummar. Kun fahimta jama'a? To wadannan na soshi jama'a suna gargadi ga duk wani wanda yake ƙwaɗayi da ƙwalamar mulki ya shirya ranar da Allah madaukakin sarki zai tattaro su shugaban ƙasa ne kai mataimakin shugaban ƙasa ne gwamna ne kai mataimakin gwamna ne limami ne shugaban ƙungiya ne babban malami ne kai ka shirya ranar da Allah madaukakin sarki zai tarkato ku mala'ikuna kaɗa ku sai anzo sai ya ce Ku tsaya da su za'a tambaye su tukunna akwai magana. Shine Sayyidina Ali yake cewa Yace da ace in mun mutu sai a tafi lahira shi ai sai kenan aka rufe mashi ba ba matsala ba tashin kiyama ba aljanna ba wuta da sai a ce mutuwa ta zama hutu yace amma matsalar ita ce in mun mutu an rufe mu to akwai matsala dangane da tambaya a cikin ƙabari akwai tambaya ranar lahira in aka tashi akwai tambaya ko ina sai anyi maka tambaya sai dai in ka shiga cikin aljanna. Duk wanda yake ganin cewa abu ne mai sauƙi kawai dan yana da digiri ko masters ko PhD ko diploma ko kuma ya fito a tsaya da shi takara yana da kuɗi sun tara suna da ƙarti masu sata akwati suna da yadda za'a yi suna da yadda za'a yi Ka shirya tambayoyin da za'a yi maka tun daga ƙabari har ainihin dandalin alƙiyama to wannan hadisin abin da yake cewa kowa za'a tambaye shi duk wanda ya zan akwai wasu jama'a da Allah madaukakin sarki ya bashi kiwo. Don haka Sayyidina Umar da yake yayi wadannan na soshi kyawawan fahimta yace abu duk inda gwamnatin shi take duk inda kwalbati ya ruguje da duk inda gada ta karye aje a gyara ayi daƙali a gyara ayi siminti a sa gada yace dan kar a ɗora wa jaki mangala yazo zai ƙetara saboda babu gada ya afka ciki ranar kiyama Umar ya shiga uku. Jaki kenan duk ƙabilan duniya in in aka ambaci jaki ƙaskantacciya halitta ce a cikin su amma Umar yana ganin jaki da ya sha matsalar hanya zai iya ja mashi matsalar shiga aljanna. Ka kewaye sabon garin local government Ka kewaye titunan Najeriya ka ka gani. Yaya titunan suke? Billions nawa aka narkar Ina ma'aikatar zirga zirga ina ina ina suke ina kuɗaɗen da ake narka musu? Dukkan mu mun tashi in zaka tafi Legas ta birnin gwari ake bi yanzu hanyar birnin gwari bata biyuwa ita ta Abuja Okene da ake bi je ka ka gaya take. Ina kuɗaɗen da ake narkawa? Tunda muke karatu daga shekara ta dubu biyu da shida har yanzu da muke karatu jama'a har yau bamu yi karatu da wutan nefa ba a Zaria.
[Speaker seg1-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:0]
Yau shekara nawa? Yau shekara biyar duk inda kaji karatun mu duk wani kaset da kaji duk wani wa'azi da kaji duk wani CD ko DVD da kaji da generator muka ɗauke shi da generator mukayi aikin babu wutan nefa saboda ba zata iya ba da an fara zata ɗauke da ta ɗauke kuma aikin zai lalace kaset goma sha bakwai da mukayi na ƙarshe a rayuwar mu a masallacin nan da mukayi su da wutan nefa da gayya mukayi su kaje kaji su na karatun mu Ana cikin yin sai wuta ta ɗauke sai a dawo da ita sai inyi habaici inyi gatse inyi baƙar magana duk ta shiga cikin kaset din domin tarihi ya irin halin da muka samu kan mu a ƙasar kenan ma'ana bamu taɓa samun awa daya da rabi lafiyayya muna karatu ba a ɗauke wuta ba a wannan masallacin kenan. Kaset goma sha bakwai suna nan. Ina kuɗi da aka danƙara wa hukumar wutan lantarki tsawon shekarun nan ina naira biliyan goma sha daya ko biliyan goma sha shida da tsohon shugaba ƴar'aduwa yayi aka ɗauke akaje aka kasab ta aka ɗibi mutane aka kai su kurkuku bayan wata guda sai gashi an fito da su kuma suwanene suka tafi belin su sarakunan mu masu alfarma wane mai martaba wane mai sandawa wane mai abin nan kaza su suka je suka yo belin su. To duk wadannan za'a yi musu tambayoyi a ranar alƙiyama kuma su shirya amsawa don haka ba wai neman shugabancin ba amma ka shirya zaka iya bada jawabin abin da ya shiga da abin da ya fita to sai annabi ya fara fassara wadanda mas'uliyya take a kan su mai nauyi sai ya ce Shugaba mai kiwo ne kuma abin a tambaye shi ne game da abin kiwon shi anan kafin ka fassara shugaba anan da shugaban sallah ko shugaban gida shugabanci ake magana anan na jagorancin al'umma a siyasance domin jagorancin al'umma a siyasance ita ce babbar tutar da ta mamaye ko babban laimar da ta lilliɓe duk wani shugabanci a ƙarƙashin ta. Da liman da gwamna da shugaban ƙungiya da shugaban ƙaramar hukuma da kowa yana ƙarƙashin shugaban ƙasa in aka sake yo ƙasa ƙasa dukkan su suna ƙarƙashin gwamna in aka sake yo ƙasa ƙasa dukkan suna ƙarƙashin chairman to duk wanda yake shugabancin ƙasa ko gwamna ko kuma ya zama minister a ma'aikata ko komishina a wata ma'aikata ko kuma shine chairman a wata ƙaramar hukuma ko shine sarki a wata masarauta annabi za'a tambaye shi game da talakawan shi daga cikin talakawan nan har da jaki har da doki har da kare har da akuya da duk wani abu da ya rayu a ƙarƙashin mulkin ka duk sai ka bada jawabi. Wannan shine na gaskiya kenan ma'ana a tsaya ayi bincike na gaskiya sai ranar alƙiyama. To wannan shugabanci da annabi yake maganar cewa wanda yake ɗauke da shi za'a ayi mashi tambaya game da jama'ar shi a ranar alƙiyama zaka zo kaji wasu abubuwa ne wadanda matuƙar shugaba ya kula da su in Allah yaso ranar alƙiyama yana da jawabi da zai faɗi amma matuƙar aka samu cikas akan abu daya to wuta zai yi daga nan. Don haka duk sanda kake ƙwaɗayin shugabanci to sai ka sauraru wadannan mas'alolin da zamu zo mu ambata zaka iya kiyaye su ko kuma da kai shugabancin a baya ka iya kiyaye wa jama'a su sai ya ce Haka nan mai gida ma kiwo yake game da iyalen shi kuma za'a ayi mashi tambaya zai yi jawabi dangane da iyalen shi. Yaka koya musu addini yaka tsare musu mutuncin su yaya rayuwar su take yaya shiga da ficen su menene ya shiga gidan menene ya fita menene ake kaza me baki daya wannan gaɓar nayi sharhin ta a wata lacca da mukayi a ainihin jihar Niger a garin Mina a wata semina da mukayi daga cikin abubuwan da nayi tsoƙaci a wannan lokaci cewa wannan waya ta hannu da ake kira GSM a yanzu da matar ka take da ita ko ƴar ka take da ita ko ɗan ka yake da shi kasan cewa wake bugo musu waya kasan cewa wane irin text ne a cikin box din ƴar ka ɗan ka kasan da wa yake yaya akai ƴar ka ta iya mallakar wannan handset ta wacce hanya take bi take iya sanya wannan handset kuɗi har yau ba'a yi blocking din shi ba ka ƙaddara nawa kake bata da an kai lokacin dan mutum yazo ya tsaya ƙofar gidan ka yana jiran ƴar ka ta fito zaka zo kayi baraza zaka kore shi yanzu an wuce wannan zai hada handset ne ko da mai arhanin na naira dubu biyar ko dubu goma kawai sai ya danƙa mata. Lokacin duk da yake buƙatar ganin ta kawai shi kenan waya zai yi text zai yi haka za'a ainihin text din nan yazo ya wuce ta gaban ka kana nan ƙofar gida kana jan carbin ka kana fankama cewa ba wanda ya isa ya taɓa mutuncin ƴar ka ba wanda ya isa kaza sai ga ta zo ta wuce da hijabi da niƙabi da safa hannu da ta ƙafa da ta wuya duk ta maƙalƙale ko ina sai ga ƴar ka kamila ce mukammila mumina ce saliha ce nan ko anyi appointment ne zata je hotel mai ɗaki na kaza kaza kaza kaza kai kana ganin zata je wurin haddani. Jama'a kun fahimta? To sai anyi maka tambaya game da duk wadannan abubuwan ka taɓa zama ka ɗauki jakar ɗan ka na makaranta ko jakar ƴar ka ta makaranta ɗan bai sani ba ƴar bata sani ba ka zazzage jakar ka ga mai ke ciki ƴar ka tana da laptop kasan ina ta samu laptop din ka taɓa karɓan laptop din ka zaunar da laptop din a wurin ka ka duba email box din ta kaga cewa waye da waye yake corresponding da ita wake turo mata wasiƙu wadanne irin ko tunana video da menene menene yaya wadanne iri ne a ciki me take kallo ka taɓa ƙwace wayar ɗan ka wayar ta ƙwana hudu a hannun ka ko uku in an bugo waya ka san wake magana da shi akan me wake turo wa ƴar ka text wadanne irin abubuwa amana ce Allah madaukakin sarki ya baka kuma sai ya tambaye ka haka nan annabin tsira haka nan matar aure ma a gidan mijin ta kiwo aka bata kuma za'a bincike ta za'a tambaye ta game da kiwon da aka bata amana aka bata ku samu lacar da mukayi ba da jima'a wannan ba a garin Gusau ta jihar Zamfara wadda sai da mukayi sharhi dangane da yaya sippofin mace ta gari yake Allah ya ce mata na gari mace ta gari ita ce tana kula da sallah farilla tana kula da nafila tana kula da azumin farilla tana kula da nafila tana da gaskiya tana da amana tana da kula da kaza tana da kula da kaza game da haƙƙin Allah bata wasa. Wannan darajar da Hafsa ta samu kenan wataran annabi har ya sake ta ta kama hanya ta ta
[Segment 2/5 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
gidan su, sai mala'ika Jibril yazo yace mishi ka dawo da ita, Allah yace ka dawo da ita, kayi haƙuri da ita. Tana yawan azumi, tana yawan ƙiyamul laili, taci albarkacin biyayyar Allah, Hafsa saliha ce. Wannan hadisi sahihi ne Abu Dauda ya ruwaito shi. Shin ke kina daga cikin matan da za'a saka ki cikin masu ibada tukuru? Amanar da Allah madaukakin sarki ya baki game da mijin ki. Yaya kike game da ita? Dukiyar mijin ki. 'Ya'yan mijin ki. Mutuncin mijin ki. Alfarman mijin ki. Darajar surukan ki. Darajar 'yan uwan mijin ki. Wa'yannan duk suna daga cikin sifofin da mace zata kiyaye ta samu sassaucin tambaya a ranar alƙiyama. Amma in kika yi sakaci game da wa'yannan abubuwa, akwai matsala akan ki ya ke baiwar Allah. Sannan sai yace Hakanan yaron da uban gidan shi ya ɗora shi akan wata dukiya, shima wannan yaro kiwo aka bashi, amana aka bashi, kuma za'a mai tambaya dangane da wannan amana. Kala mai riwaya yace Ina tsammanin ma yace Haka ɗa da uban shi ya ɗauko shi ya ɗora shi akan dukiyar uban. Shima amana aka bashi kar ya ɗauka cewa tunda dukiyar uban shi ce bari yayi sama da faɗi yadda yake so, ai yana da haƙki a ciki, ya manta dukiyar ba tashi bace. In yace yana da haƙki, ya manta akwai wasu 'ya'yan masu haƙki a kai. Don haka duk ɗan da uban shi ya amince da shi ya aza shi akan wata dukiya, dole ne ya kula da wannan dukiya, ya kula da wannan amana, ba don komai ba Ranar lahira sai an mai tambaya game da wannan dukiya ta mahaifin shi. Annabi ya sake maimaita maganar don ya ƙarfafa ta da kyau yace Don haka dukkan ku jama'a kiwo aka baku, kuma dukkan ku sai anyi muku tambaya dangane da kiwo. Hadisi yazo sahihi a cikin littafin Annabi yace baki, hanci, kunne, ido, farji, azakkari hannaye wa'yannan gaɓoɓi in gari ya waye baki ɗaya sai su tattaru sai su samu ɗaya daga cikin su sai ya zama sai yayi magana a madadin su, yace wa ainihin harshe, yace wa baki, to bakin mu ɗaya fa gaba ɗayan mu. Amana aka ɗanka a hannun ka. Don haka idda kai da mu nan zamu yi don haka kaji tsoron Allah game da mu. Gaɓoɓi abun da suke cewa baki kenan. Domin Baushe yace baki shike yanka wuya. Shi zai faɗi kaza, shi zai ce kaza, shi zai ja kaza, shi zai ja kaza. Kaga kenan koda zaka ce kai saurayi ne kuma kai baban ka ya mutu ma ba wata dukiya ko baban ka talaka ne ko kai, ma'ana kana ƙoƙarin ka kaucewa wannan hadisi na Abdullahi ɗan Umar cewa kai bazaka shiga tambaya ba. Sai aka ce kai co, ai an baka hannu da ƙafa. Ai kana da ido. Kana da azakkari. Ai kana da baki, ai kana da ƙafa, ai kana da kaza, duk wa'yannan abubuwan gaba ɗaya za'a yi maka tambaya game da su a ranar alƙiyama. Kun ga aikin bai ƙare akan kowa ba ko?
[Speaker seg2-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg2-spk:0]
To jama'a wa'yannan sifofi baki ɗayan su malamai suka ce duk in aka kai aka komo a duba na farko ɗin nan da Annabi ya faɗi shi yafi kowanne mahimmanci, shine wanne? Shine shugaba. Shugaba yafi kowanne mahimmancin shugabanci. Domin shugaban ƙasa ko gwamna ko sarkin musulmi ko mai martaba ko mai alfarma ko mai karama ko dagaci ko hakimi ko mai unguwa ko wanene. Shugabancin da yake ɗauke da shi ya mamaye shugabancin mai gida. Ya mamaye shugabancin matar aure. Ya mamaye shugabancin yaro dake kula da shago. Don haka mas'alar tafi ƙarfi akan shi. To malamai suka ce dole ne duk shugaba kafin a kira shi adilin shugaba sai ya kiyaye wa mutane abubuwa guda biyar zuwa shida. Abu na farko addini. Sai ya kiyaye wa mutane addinin su. Ina ma'ana addini? Yasa ido yaga wanne irin addini mutane suke yi. Don haka a musulunci babu Babu Babu Babu Ace ba ruwan gwamnati da addini, wannan fito na fito ne da Allah. Duk gwamnatin da tace ba ruwan ta da addini wannan gwamnatin ko ta musulmi ce ta yanke alaƙar ta da Allah. Domin alaƙa ƙwaya ɗaya ce tsakanin bayi ko halittu da ubangiji. Shine addini. Duk sanda kace ba ruwan ka da addini to ka datse wannan igiyar. Saboda haka ka ɗoɓara ta farko shine a samu hukumomi su ce ba ruwan su da addini. To amma kuma abun mamaki duk zaran an taho lokaci irin wannan musamman a yanayi irin wannan na siyasa, don ba'a taɓa siyasa irin siyasar bana a tarihin Najeriya ba, tun daga jamhuriya ta farko har ta biyu ba'a taɓa yi ba. Siyasar da ta fito ƙarara addini ce zalla, yanki ne zalla, ƙabilanci ne zalla ake yi, sai wanda ya fandare daga cikin dangi. In ba wanda ya fandare daga cikin dangi ba, duk inda ka samu kowa yasan gidan uban shi dama haka babban ɗan siyasa ya faɗi. Haka ne ko ba haka ba? To duk wanda ya fandare daga cikin dangi shikenan sai ya gan shi ya kwana a daji. Don haka a irin wannan lokacin jama'a sun ce ba ruwan su da addini amma kuma sai kaga wa'yancan sun yi cuci wa'yannan sun taho masallaci. To yanzu sun zo ne addinin da ba ruwan su da shi kuma suke so yayi ruwa da su. Rannan wani babban ɗan siyasa duk jaridun Najeriya suka ɗauko rahoton shi. Yaje cuci yana cewa to shi fa ya dogara da su ne dangane da ƙuri'a. In basu fa in ba ƙuri'ar su fa babu shi. Bazai tazarce ba, bazai je ba, bazai kaza ba, bazai kaza ba. Kuma abun takaici jama'a wa'yannan kalmomin da ake faɗi mu kaɗai ne bamu da wayo akan su. Mu kaɗai ne in mun faɗe su da gaske muke. In kaji musulmi yace ba ruwan shi da addini saboda giyar mulki ta buga shi da gaske yake ba ruwan shi da addini. Su wa'yancan ko sun ce ba ruwan su da addini wallahi ƙarya ne. Mun ga wani irin yanayi a jihar Adamawa yau shekara shida ko bakwai da ta gabata. Mataimakin shugaban ƙasa ya fito daga yankin. Yana ƙyamar raɗanganta shi ga addini har ya fito dukkan kafafen yaɗa labarai yace a daina ce mishi Alhaji. Amma sai kuma gashi ɗin nan a wannan halin ya ɗauko wani ɗan tsakon kirista busar shi ya saka shi ya zama gwamna. Shi kuma wannan sai da ya zama cuci ko ta ƙasa ce sai da aka rushe ta a jihar Adamawa aka yi mata ta sumunti. Yana ta gina mutanen shi yana ta gina addinan su. Shi kuma can na ƙololuwa yace ba ruwan shi da addini. Don haka in kaji wannan kalmar daga bakin wa'yannan mu take fitowa kuma suyi aiki da ita, su can basa yarda su faɗa. In kuma sun faɗa abun da suke nufi ba ruwan su da addinin musulunci. Don a daidai lokacin da yake faɗi zaka ga cross a wuyan shi. A daidai lokacin da yake faɗi in aka ce za'a yi addu'a sai kaga ya cire hula ya rufe ido. Amma in aka ce za'a yi addu'a namu kunya yake koda ya ɗaga hannu. Kunya yake koda ya bayyana da wata siffa cewa wannan addu'ar irin tasu ake yi. Bana an shiga wani hali wanda yake dole ne kowa ya bayyana ina yake. In ba haka ba munafuncin mutum ya bayyana. Ina fata an gane. To dole ne mai mulki ya kula wa mutane game da addinin su. Wa'yannan irin aƙidoji ake yaɗawa. Wa'yannan irin malamai ne suke wa'azi. Menene suke karantarwa? Wa'yannan irin darajoji ake faɗi da suka dace ga Allah. Wa'yannan iri ne ake faɗi da basu dace ga Allah ba. Dole ne mai mulki ya sa ido game da wannan. Haƙƙi na farko kenan da zai kular wa mutane. Domin Allah madaukakin sarki cewa yake Allah bai umarci mutane suyi komi ba sai suyi addini su tsarkake addinin ga Allah. Don haka Addini shine babban jali kai riƙo da shi. To dole ne mai mulki ya kular wa mutane game da addini. Abun da muke cewa wa'yannan mutane da suka zo suna lallashin mu yanzu suna cewa ayi haƙƙuri zasu gyara. Wai su kullum a cikin ban baki suke? Tsawon shekarun nan kaje ka saurari jawabin sa Abubakar ta fawa balewa. A lokacin da ya fito takara 'yan alƙauran da yayi 'yan kaɗan ne amma masu nauyi ne. Yace zamu yi muku kaza, zamu yi muku kaza, zamu yi muku kaza in kun zaɓe mu. Sai tattara takardun shi sai ya bar gurin. Jawabin shi ma na mulkin karɓan mulkin kai duka duka minti biyar ne. 'Yan siyasa na gaskiya basurutu suke da yawa ba. Aiki ne yake fassara maganganun su. Ina fata an gane. Duk ba ita bace ajanda nawa kaji a tarihin Sardauna? Amma ka kewa duk arewacin ƙasar nan da Sardauna ya zama shugaban ta sai da taga wani haske na cikin abun da Sardauna yayi na ilimi. Nan anyi musu jami'a, can anyi musu can anyi musu can anyi musu can anyi musu kaza, can anyi kaza. Duka a shekara nawa Sardauna yayi wannan aikin? Saboda haka abu na farko a kular wa mutane da addinin su. Shin daga shekara goma zuwa yanzu a nan ƙaramar hukumar sabon gari da nan jihar Kaduna da kuma ƙasa baki ɗaya wace hukuma ce aka kafa ta wadda ta tsaya tayi gwagwarmaya game da gyarawa mutane addinin su. Babu. Mu 'yan sabon gari ne. Mu 'yan jihar Kaduna ne. Mu 'yan Najeriya ne. Babu wata hukuma wadda ta tsare wa mutane mutuncin addinin musulunci. Sai yanzu ne an tsaya takara za'a biku malaman islamiya saboda kune wa'yane wai ana kawo muku ƙawa'idi da ahalari. Ƙawa'idi da ahalari. Nawa nawa ne ƙawa'idi da ahalari? Naira talatin talatin ne. Sai a kawo muku katan guda ko katan goma. Ana shigar da su gidan malamin islamiya an sa kamera ana ɗaukar hoto. Yana cewa ai gashi nan kuɗaɗe ne ko kuma katan katan ɗin sukari ne aka kawo ma malam. Nan ko ƙawa'idi ne da ahalari. Dukka dukkan an haɗa su biyun naira hamsin ne, wannan naira ashirin, wannan naira talatin. Me yasa da ba'a kawo muku ba? Sannan ya za'a yi malaman islamiya ku zama ku zama wautar ku tayi yawa wai har ace wai wani ɗan takara yazo ya same ku a islamiya wai yanzu ne za'a ɗauki lambar waya a baku. Wai ace wai inda matsala wai ku bugo mana waya. Yanzu sai ace a ba matsala sai an gama zabe, zamu buga muku in an gama zabe. Me yasa baku iya faɗin magana? Me yasa baku iya zama maza? Sai ka zama kaine malamin islamiya ka zauna ka ta kwarkwashe haka kawai wani wawa yazo yana hayaniyar banza a gaban ka kafi shi fasaha, kafi shi albarka. Baiwar da Allah yayi maka yafi tashi. Domin a cikin hadisin Usman da yazo Bukhari da Muslim Annabi cewa yayi Wanda duk ke karantar da alƙur'ani ya koyi ƙur'ani yake karantarwa yafi kowa, yafi gwamna, yafi minista, yafi darekta, yafi shugaban ƙasa, yafi mai martaba sarki, yafi sarkin musulmi, yafi kowa. Sai dai in wa'yannan suma sun koyi ƙur'ani suna karantarwa. Amma matuƙar basu koya suna karantarwa ba, mai karantar da al'qur'ani yafi su darajar duniya da lahira. Wannan hadisin manzon Allah ne Amma ya zaku zauna su maida ku wa'yane? Don mai zasu maida ku wa'yane? Idan har sun zo wurin ku me yasa bazaku tsaya kuyi magana da su? Maganganun da zasu dafa musu ƙwaƙwalwa ba. Ba'a ganin bana 'yan siyasa sun ji tsoron zuwa wurin mu? Mun ce ƙofa a buɗe take duk wanda zai zo yazo. Amma fa ga Ga Ga a wai su abun da suka ɗauka wai kawai zasu je su samu wa'yannan ne kawai su faɗa musu maganganun da zasu faɗi kawai shikenan a ɗan kawo dubu ashirin a ajiye, Allah ya tsine wa dubu ashirin ɗin da za'a baka a wulaƙanta ka albarka. Me haka ya kai dubu ashirin? Me zaka yi da dubu ɗari biyu? Me zaka yi da miliyan biyu? Me zaka yi da miliyan ashirin? Akan 'yancin ka. Ace jama'a lokaci yayi wanda zaku tsaya yanzu ku kwatar wa kan ku 'yanci. Amma an maida ku wawaye. Wa'yannan saƙonni ne muke isarwa tun daga malaman islamiya da malaman masallaci masu karantarwa da asuba da masu yi tsakanin magariba da isha, kuje ku faɗakar da mutane kuma ku wayar da kan su. Kan ma giya waye, babu sauraren ace wai sai yanzu ne wai 'yan takara wai zasu fara bin ku, wai suna baku wai lambar waya. Ace komai dare Allah gafarta malam ka bugo. Wai kai kuma sai kayi ta tsuma, aima kunga har sun bani lambar wayan su. Nawa suka baka? Ka rinƙa zuba kredit. Jama'a kun fahimci wannan? Yanzu wannan tsakani da Allah ba raina hankalin mutane bane? Allah madaukakin sarki ya kiyaye. To addini shine abu na farko da za'a kiyaye wa mutane. Tunda ake a Najeriya ba'a taɓa samun sanda addini ya rikice fiye daga shekara goma zuwa bana ɗin nan ba. Addini ya rikice, ya lalace saboda ba ruwan kowa, addini bashi da Bashi da wani wanda ke kula da shi. Kowa ya faɗi abun da yaso, ya aikata abun da yaso kuma ba abun da zai same shi. Saboda kawai wasu mutane ne wa'yanda yake basu da manufa aka murɗa mulki kawai aka dasa su a kai. Kuma malamai anbi duk an shafe bakunan su gaba 1 ba wanda zai iya fitowa. Wasu ma yanzu sai suka fito da salon wai ai ai an hana ayi magana akan masu mulki. Mai mulki na zalunci. An hana ayi magana akan shi. Kaje malamin da ya koya maka manhajin salafiyanci kace ya sake rafiun karatun shi da wanda ya biya maka, bai iya ba. Yo me yasa aka ɗora su Imam Malik? Imam Malik duka aka yi mai sai da hannun shi ya ƙage har baya iya ɗora hannun shi a kirji. Za'a tambaye shi yace Ya karantar da ƙawa'idi ne sarki yadda kai? Kofar rilan alwala. Yayi magana ne game da masu mulki sunyi zalunci. Ibn Taimiyya ɗaurin da ya sha ya sha ɗauri ne akan kawai ya fassara Yace Allah a sama yake, akan wannan ne kawai ya sha ya ɗauru. Yayi magana dangane da masu mulki. Idan har malamai basu yi magana game da zaluncin masu mulki ba wanene zai yi magana dangane da zaluncin masu mulki? Musamman wa'yannan masu mulkin da zaka nemi a so ɗari baka samu ban ance je ka kai musu nasiha. Kuma matuƙar yau kaje kai nasihar abun da za'a ɗauka yunwa ce ta kawo shi. Ku bashi dubu ɗari. Shi ko in yaga dubu ɗari gaba ɗaya rikicewa zai yayi faɗa toilet. Yana tunanin cewa ita ce hanyar fita saboda bai taɓa ganin dubu ɗari ba. Gaba ɗaya sai ya zare. Yana fita sai ya ga yana dariya. Kuje ku tambayi yadda ya rima ya rinƙa musu a Zamfara. In ya ba malamai kuɗi sai shiga suna ta faɗa sai ya fita yana dariya shi da komishinoni shi yace gasu can suna ta faɗa. Sai gasu can sun haɗa kai izala da ɗariƙa suna bin juna sallah yace saboda na miƙa musu kuɗi. Sun maida ku 'yan coɗa baku da dabara, baku da hikima, baku da wayewar kai. Bazaku zama kuna tsaye da kan ku ba? Yo ba dole ƙasa ta lalace ba in ya zama malamai sun rikice sun kasa sanin alƙibla? Allah madaukakin sarki ya kiyaye. Don haka dole ne mai mulki ya kula da mutane addini. Sannan annafsi rayuka. Duk mai mulki dole ya tsare wa mutane rayuka. Yanzu jama'a muna zaune ɗin nan 'yan bindiga daɗi na iya shigowa duk su harbe mu. Saboda me? Babu Babu tsaro, babu aminci. Kana cikin gidan ka a tsorace kake. Ƙofa a buɗe kana tsoro, ka rufe ƙofa, kasa ki, ka datse, kasa mabuɗin a aljihun ka amma hantar ka na ma ƙyarƙyata. Ya aka yi? Kana tafe akan hanya kana tsorace. Dubi ƙaramar ƙasa ce irin Nijar gata nan da daddare ake kawo ma hanya ana tafiya. Biliyoyin dukiyoyin Najeriya ta Nijar suke shigowa. Su shiga su shigo lafiya lau tun daga motoci har shaddoji, tun daga ta kalma har suturu ta Nijar suke shigowa. Amma suna cikin amincin da babu a nan. Ƙaramar ƙasa ce wadda duk dukkan ta bata wuce wata jihar ba a ƙasar nan. Amma suna cikin amincin da bamu cikin shi. Jama'a kun fahimci wannan da kyau? Sannan a kama 'yan fashi da makami kaje kaga anyi belin su. Aje kotu a zaunar da ɗan fashi da makami ko ɓarawo da ɗan ɓanga akan kujera ɗaya. Ƙarshe a sake shi ɗan fashin yana gargadin ɗan ɓangan ai zamu haɗu ne. Ba dai ƙarshen ta kenan ba anzo nan kaga an sallame mu. Jama'a kun fahimci wannan da kyau? A da in kaji anyi kuwar ɓarawo sai ka fito a guje ka kai ɗauki. Yanzu in kaji maƙocin ka yayi ihu
[Segment 3/5 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
barawo sai ka kara duba kofar ka, ta rufe da kyau. a Niger Delta, a garin Patakort jama'a da loudspeaker yan fashi suke fashi zasu zo su kafa loudspeaker a tsakiyar anguwa karfe biyu na dare sai su ce kowa ya bude gidan shi ya bude kofa ya fito da abun da yake da shi ya zauna ya jira mu sai ka tashi ka bude kofa da kai da matar ka sai ku ajiye kudi akan table ku zauna kuna salati in kiristoci ne kuna halaluya duk ku gama rintsa rintsa idon ku su shigo domin wanda duk ya sake sai anyi wahalar karya kofa an shigo to a bakin ran shi bayan kudin shi a Patakort a Niger Delta yanzu yan Niger Delta sun bazo Abuja karfe bakwai na magariba suke kwace mota kwace motar ka ayi maka tsirara a bar ka suntur dan haka sanda zasu sake ka ta kanka kake ma ka samu ka buya duk inda kai sai mutane su gan ka mahaukaci ne dan haka sai kayi awa uku baka fara kuwa ba, in ma aka ji kana ihu sai a ce ga wani sabon kamu chan ba haka bane tsirara za'a hadu da kai a kwace motar ka, a cire wandon ka, a cire rigar ka, a cire dan dress din ka, a bar ka tunki in kayi ihu barawo da an kalle ka a ce kaga wani sabon kamu chan abun da yake faruwa yanzu a cikin Abuja abun da yake faruwa kenan a cikin Abuja ko kwana bakwai ba akai ba, yau kwana hudu na je na yi wani jaje a gidan shi anyi mai haka karfe bakwai ya fito zai yi rakiya, karfe bakwai na magariba jama'a inda ya zama babu aminci gama da rayukan mutane rashin amincin ya kai har masu mulki yau ne ke da hannu dangane da kife wa jiragen sama daawa dan tsafi tsakani da Allah a fito muku da rahoto na gaskiya gama da hadarin jiragen sama da akai ta yi shekaru uku hudu da suka wuce a fito muku da menene dalili a fadi dalilai na gaskiya har yau ba'a fadi dalilan hadarin jiragen sama ba, jirgin sama ko duk inda ya hadari jama'a sai an gano dalilan gaskiya na hadarin shi kuma dalilan duk in ka samu wani kwararren masani cikakken mechanical engineer abun da zai ce maka 99.9% na hadarin jirgin sama shine human error ne ganganci ne daga dan adam da gangan aka rinka barar da mutanen dan ayi tsafi da rayukan su, ayi tsafi da jinin su, a nan kasar mu dan haka ba wanda ya fito da rahoton gaskiya me ya faru ya za'a ce jirgi daga dagawa ya kama da wuta nan take kowa ya kone a ciki babu aminci sannan gidajen yankan kai duk wata karamar hukuma da ka sani yau a Najeriya akwai gidan yankan kai in ba haka ba akai inda ake tarawa ma'ana tashar da za'a tattara wadanda aka sata a kai su ma yanka ta kusa yanzu da zabe ya fus ya kusanto kowa ya san al'amari yayi kamarin da hatta gidajen rediyo sai da suka fito karara suka rinka kawo irin rahotannin abubuwan da aka rinka yi musamman a jihar Jigawa yan siyasa gashi nan sun sa ana ta satar yara duk wanda ya bace yanzu karma ku kai filin cigiya da batarwa ku fara ainihin addu'a kawai Allah ya nufe fito da shi ya fito da shi amma yana chan za'a yi tsafi da shi saboda za'a ce wane a in fa kana son tazarce ba zai yiwu ba sai ka sha ainihin jinin kokunan mutane da gwargwadan shekarun da kake so kayi ko wace shekara daya tana da kwana 360 to sai ka sha jinin mutanen da suka kai 360 sau hudu mutane nawa za'a kashe sannan lokacin da wannan mutum guda kenan wancan ma haka yake so wancan ma haka yake so saboda haka babu aminci muna kanana a garin nan a Club Street ko a yau menene wajen Independence Road wajen layin Sulima a Rex Cinema aka kama babban gidan yankan kai ga sa hannu da hotunan manya manyan gari nan amma haka aka danna maganar ta tafi sannan yanzu ku je ku binciki anguwanne anguwanne ire iren wadannan anguwanne da ake cewa layout, quarters, GRA da sauran su akwai gidajen da ba'a bude su sai karfe uku na dare karfe hudu da rabi zuwa karfe biyar shikenan sai ka ji motoci na fitowa an tashi daga taro akwai bakaken motocin da ba'a ganin me ke cikin su su suke shiga su suke fita da wa suke shiga da wa suke fita duk wadannan na daga cikin hakkin gwamnati ta kiyaye wa mutane rayukan su sannan sai annasal annasal a nan ko al'ir abun da ya shafi mutuncin mutane mutuncin mutane ko kuma salsalar mutane abun da ke da alaka da lafiyar su abun da zai tsare musu nasabar su a hana zinace zinace wadanda ta hanyar haka za'a samu yayan banza yan ta gaban Fatiha yan iska wadanda basu da uba wadanda zasu waye gari basa jin maganar kowa lallai sai an tsare nasal sai an tsare yaya ne ake shiga da fice dangane da aure da auratarwa yaya wanda da aka sake ta ya tabbata ta gama idda ta gama takaba da mijin ta ya rasu wannan yaya da za'a daura mata aure bata yawan banza bata da ciki balle ta kai dan wani ga wasu al'umma da ba nasu ba dole sai an tsare wa mutane wannan sannan al'ird mutunci dole ne hukuma ta tsare wa mutane mutuncin su duk hukumar da bata tsare wa mutane mutuncin su yan iska zasu waye gari suyi abun da suke so yanzu ko waye kai limami ne kai ko dagaci ko hakimi dattijon anguwa ne kowane iri ne kai baka wuce yan iskan anguwa suyi maka dariya ba baka wuce su ci mutuncin ka ba a nan anguwan nan tsakanin muciya da cikaji aka samu yan iskan yaran da sai sha daya na rana na dare tayi zasu je su kwankwasa maka kofa su ce ka fito da ƴar ka wancan da suka sani ka basu sai bayan sun yi mata ciki wata biyar wata shida sai su dawo ma da ita, a daidai irin wannan lokaci na tsakar dare ce ga amanar da suka karba nan sun kawo maka sun dawo maka da ita sun yi kace kace da ciki an san su a cikin anguwanin nan amma ba yadda aka iya da su a nan babban titin muciya yara suyi samun dan karamin babur su cire salan sa su su sheko tun daga farkon titi har karshe su doke duk wanda zasu doke an rasa yadda za'a yi da su iya abun da za'a iya musu wai sai dai ayi kabarin mai ta tsine in sun yi tsalle su fadi amma babu wata hukuma da zata iya tsawatar musu amma wai wadannan hukumomin ne da mun san za mu yi sallar juma'a karfe tara a nan shikenan sai a ce wai za'a yi tashin duniya sallar juma'a karfe tara shine abun da na gaya wani jami'in yan sandawa taron da yayi min waya na ce salla tana da mai gida ne a Najeriya addinin musulunci addinin bashi da mai gida sai an zo za'a yi kaza sannan ku ce kaza ina ruwan ku kun ce ba ruwan ku da addini
[Speaker seg3-spk:1]
na'am
[Speaker seg3-spk:0]
sai na gaya wani na ce yanzu idan mutum ya daina salla akwai wata hukuma ne da aka tattala a kasar zata tsawatar mashi to in yace zai salla karfe tara harka ta nake yi ta gine gine ina kammala gine gine makaranta na dawo limanci ni ne limamin masallaci gaba dayan sallar karfe tara za'a maida ita
[Speaker seg3-spk:1]
Allahu Akbar
[Speaker seg3-spk:0]
ya rage in kana da iko ka rubuta saman bakwai cewa kar a karba iya inda zaka yi kenan amma a hukumance ba shegen da ya gina mana masallacin nan duk duniya
[Speaker seg3-spk:1]
na'am na'am
[Speaker seg3-spk:0]
masallacin mu ne namu ne waye gina mana ba gwamnati ta gina mana ba ko fenti da ake bayar wa masallatai mu bama karba fentin banza in in zinare ake narka a shafa a masallaci muna da kudin da zamu shafa a masallacin mu amma haramun ne in ba haka ba wallahi sai mun shafa
[Speaker seg3-spk:1]
na'am na'am
[Speaker seg3-spk:0]
za'a siyo generator a kawo mana ne miskinan masallata ne mu da wani matsiyaci zai siyo generator ya kawo mana generator dubu ashirin da takwas akan haka za'a yi determining kuri'ar kuwa zaku jepawa saboda haka ya kamata ku tsaya ku fahimta ba abun da ya hada su da harkar addini ko harkar kura da lafiyar ku ko rayuwar ku ko mutuncin ku ko ƴancin ku ko komai naku yan fashi zasu shigo cikin gidan ka su maka dukan tsiya a gaban matar ka sai ka galabaita tsaf kana kwance kana nishi sai ka ga wani sargame man kato ya danna matar ka a gaban ka yana zina da ita tana ihu ba abun da zaka ce dan kana cewa za'a dana maka bindiga a kunnen ka a fasa kwakwalwar ka ka gaya min wannan shine cin mutunci na karshe da za'a yi wa duk da na miji a kasar nan a nan arewacin nan yan fashi suka shigo suka datse da sai yayi zina da uwar shi kawai abun da suka zo kenan sai yayi zina da uwar shi wane cin mutunci ya wuce wannan babu tsaro amma biliyonsa nawa ake kashewa a tsaro duk in kaga yan sanda suna barazana operation yaki ne operation flush out duk barazanar su a nan cikin gari ce fita dogarawa kace ran ka ya dade ga yan fashi chan da ƙyar na sha kace musu su je su karasa ba ance operation yaki ba su je suyi yakin a chan amma sai sun shigo nan ne suke wa talakawa muzurai muzuran bashi da amfani ga inda zaka je chan kayi kuma in kai namiji ne jefar da bindigar mana in ka shigo cikin garin ba ga ƙarti nan suna zaune suna shan rake ba to jefar da bindigar kana dauke da bindiga wane bai da bindiga dan kayi ma zurai bakai ma zurai bakai ba namiji bane jefar da bindigar ga inda za'a bada tsaro chan yan fashi sun datse hanyar suna kashe mutane suna wulakanta mutane yan fashi suna bi gida gida suna fashi da ka buga musu waya sai su ce basu da kayan aiki basu da kayan aiki amma ya za'a yi da rana su cika cikin gari suna takurawa mai bos mai bos yana sabon garin muciya cikaji daurawa tsamiyar kunu yana neman ya samu yadda zai samu abun da zai rufa asiri operation yaki su kama shi suyi mai dukan tsiya wannan ne security dan ta'adda ne ya fito neman abinci ne ga yan ta'adda chan in ku da gaske ne tsaran ne dan haka wadannan jami'an tsaro da suka cika cikin gari ba ada bukatan su dan wadannan kananan yan iska yan cikin gari dogaran dagacin anguwar ku ma sun ishe su ba'a bukatan sai operation operation kamata yayi su tafi daji su tsaya in aka ce patrol team ne su kuma su rinka kai da komowa suna zarya amma sai kazo wucewa da motar ka wai sai a ce wai gilashin ka ya fashe yau gilashin ka da ya fashe kwalbar idon mahaifiyar ka ce ya fashe balle kace bata gani daidai ko kun fahimta jama'a ba wannan ne ake bukata ba abun da ake bukatan ku samar wa da mutane ƴanci a daidai lokacin da aka fara demokradiyan nan jama'a galibin yan kasuwan da ke kasuwanci tsakanin Bauchi da Kano sai da jalin su ya kare wannan rahoton a rediyo Najeriya Kaduna muka ji su saboda fashi da makami yayi yawa a wannan tsurkuki zasu tare ku su tatake ku wanda duk aka gani da draft wato ya kai kudin banki zai je Kano ya karba sai su sa bindiga su harbe shi ƴaƴa nawa aka mayar marayu jama'a kun fahimci wannan da kyau to gaskiyar lamari abun da muke gaya muku jama'a hukuma ba zata zama hukuma ta gaskiya ba sai ta kiyaye mutane wadannan sannan almalu dukiyar ka tafi kasashe da ake kasashe na gaskiyar demokradiyar irin Amurka da Ingila ba wata ma'aikata da za'a ga mai gadi za'a inda za'a ga bogula yanzu dube abun kunya wai nan masallaci ne dakin Allah amma anyi mai bogula ma'ana har dakin Allah za'a shigo ayi wa Allah sata saboda babu security ka tafi America ka ga gida nawa zaka gani da window nawa da bogula ma'aikata nawa zaka gani da mai gadi ba mai gadi sai get man da rana in kazo ya bude maka kofa in ka shiga ya rufe in an tashi an rufe an sa kwado kowa sai ya tafi ba inda zaka ga mai gadi a America wai ya ya tsuguna wai yana gadin wata makaranta ko wata hukuma ko wata railway ko wata NTC ta baku babu mai gadi saboda mai an samar da kkyakkyawan tsaro ne ga dukkan kasar amma yanzu sai kowa ya daukar wa kanshi mai gadi a gidan shi sannan mutanen anguwa sai sun hadu sun samar da yan banga me yasa ina jami'an tsaro ina kudaden da ake kashewa sannan a hir kai kuskure kaje kace kaji labarin za'a yi fashi da makami sai yan fashi da makamin su sun zo sun danne ka sun yanka ka domin wadannan da kaje ka gaya wa a cikin su akwai wakilan yan fashi zasu koma su ce wane ne ya kawo labari gama da ku so da haka kowane talaka yanzu dar dar yake in yaga ana wata rashin gaskiya sai ya kauce in ance ya kai rahoto ya ce ba ruwan shi saboda in ya kai rahoto bai san me zai je ya dawo ba sannan sai al'akal dole ne duk hukuma ta kiyaye wa mutane hankulan su shaye shaye ganye da duk wani abu da zai birkita kwakwalen mutane dole ne a kula da su jama'a wadannan abubuwan da muka fadi guda biyar ko guda shida tsakani da Allah hukumomi da gwamnatocin da muka zaba ko aka zaba mana muka zaba ko aka dora mana muka zaba ko aka kakaba mana su daga shekara goma zuwa yanzu sun kular mana da wadannan abubuwan to basu dace a sake zaban su ba chanji muke bukata kawai dan haka maganar a fara cewa ma zaban kafiri ko ba zaban kafiri ba asalin wannan ajendan ma ba akai gare ta ba yanzu ana magana akan ajendar tukunna abun da suka ce zasu yi tukunna sun cika dan haka basu cancanta su sake komawa ba ko wannan ya ishe mu shiyasa maganar wane za'a zabe shi baza'a zabe shi ba a'a an gaji da ku ne yanzu kawai chanji ake bukata chanji ake bukata wannan na daya daga cikin matashiyar sakonnin mu chanji muke bukata kuma yanzu kamar yadda Abubakar Ladan ya fadi yau kusan shekara arba'in yace jiniyar ƴanci yau ta koka a kudancin nan yau na Africa to jiniyar ƴanci yau ta koka a Najeriya lallai ne yanzu ƴanci ake bukata domin chanjin nan ya faru a kasar Tunisiya me ya ja wannan chanjin a kasar Tunisiya adalci ne yawa da jin dadi amma shugabancin wa yake shi jikan annabi ne Zainul Abidina Ibnu Ali cewa yake shi sharifi ne jikan manzon Allah amma da yayi zalunci an kawar da shi ko ba'a kawar da shi ba to balle wanda ba jikan uban kowa ba ko kun fahimta jama'a jikan manzon Allah ne a Tunisiya Zainul Abidina kuma babu shakka sharifi ne jinin manzon Allah ne jikan manzon Allah ne amma zalunci yayi ya kakaba wa mutane dokokin da basu yi daidai da na hankali ba balle na addini kuma menene ya kawo karyewar zaluncin zaluncin ya kai matuka matukar da ta kai me yalon bella ne yana gungurawa a kura ta nan yake samun abinci amma aka zo aka kifar da yalon bella aka zuba a kwata shi yalon bella bashi ya ciyo zai je ya siyar abun da ya samu ya dora riba ya je ya ci da ƴaƴan shi an je an kifar a kwata saboda zaluncin hukumomi shine ga da wace fuska zai kalli mai bashin in ya shiga gidan shi da wace fuska zai kalli matan shi shine ya barbada wa kanshi petrol ya kona kanshi abun da yayi ba daidai bane a addini amma ka sani da cewa ya ga wace wace mafita ce ta rage zalunci ya gama kaiwa zalunci dan haka ya ga cewa bari ya hallaka kanshi daga haka ne jama'ar kasar kowa ya fisa ta yau shekara hudu muna gaban ka'aba da wani mutumin kasar ina magana akan zaluncin da ake a kasar sai yace don girman Allah a rufa mashi asiri na ce ah muna nan ka'aba ba'a ka cikin aminci yace wallahi bani cikin aminci kaga wannan maganar da muke ina iya dira filin jirgin sama kasar mu ana zuwa a kama ni a ce ranar kaza ga watan kaza ka hadu da wani bakar fata dan Najeriya kayi hira kaza na ce mala'iku ne ke bin ka yace dan Allah ka rufa min asiri an gama birkita su gaba daya wallahi a gaban ka'aba cikin watan azumi ana dab da za'a sha ruwa wani malami to wai jiri ya gama tafsiri muna hira zalunci a kasar Tunisiya ya kai ga yau aure in zaka yi sai ka gaya wa matar ka in ta yarda to in ba haka ba sai ta kai ka kotu amma kuma an yarda tunda an takura ka akan mace daya ta aure to a waje kuma yan matan ka ko guda nawa ne shikenan dan haka aka samu wani kwallon shege yayi aure da yayi aure sai matar shi ta kai shi kotu da ta kai shi kotu ta gabatar da hotuna da bidiyo da menene duka shima ya je da lauyan shi na ce to matar ka ta kawo karanka ka kara aure bata yarda ba dan haka ga hotunan biki ga kaza ga kaza shine ya tashi yace ba haka bane amma lauyan shi zai karasa jawabi lauyan shi yace to client dina wato mutumina abokina ba aure yayi ba party yayi da shi da wata budurwa ta shi shine wannan daren aka yi holewa hotunan da aka dad dauka kenan ina shaida an daura aure sai matan ta sun kuyar da kai karshe ita ta tafi gidan maza ta kai karashi ne akan yaya aure kara
[Segment 4/5 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
aure laifi ne. Shi ko yace a'a, karuwar shi ce fa sukai fati. To kuma gwamnati ta yadda kai fati da karuwar ka, amma matar aure an haramta. Wannan jikan annabi ne dake da'awar wannan abu. Amma kuna ga Allah ya karya gwamnatin shi. Sannan mubarak husni mubarak wani irin zalunci da kama karya ne ba ya kasar shi ba. Kun ga yadda Allah yayi mishi. Ga Abdallah Salihu can a kasar Yemen. Sannan ga Gadafi nan. Wani irin fasikanci da fajirci da kafirci ne Gadafi baya yi a kasar shi. Yau wadanda suka daure mishi gindi yake wannan yau sun taso shi a gaba. Suna son sai sun ga bayan shi. Abinda Shehu Dan Fodio yace Allah yana zaunar da gwamnati ko da kafiri ne ke shugabancin ta inda adalci. Amma Allah na karya gwamnati ko da musulmi ne ke shugabancin ta idan akwai zalunci a ciki. Me Dan Fodio yake so yace? Zalunci shine ke karya mulki. Jama'a a Najeriya akwai wutan lantarki? Babu wutan lantarki. Yanzu da muke magana generator mu ne. Generator mu ne. Ba wutan lantarki bace. Sai abinda ya shafi ruwa yanzu a jihar Kaduna, wacce gwamnati ce tun daga lokacin da aka karbi mulki a hannun soja har zuwa yanzu bata yi da'awar ana nan ana aikin ruwa ba. Amma ruwan nan har yanzu ba'a ganshi ya digo ba a duk inda ba'a dashi. Amma fa ance ana nan ana aikin. Kuma mun san ana nan ana aikin ba ba'a yi ba. Amma muna sa ido nan da shekara 30 ruwa yazo. Bamu ce ba'a aiki ba, ana nan ana yi. Amma muma muna nan muna jin kishi fa. Amma miliyan nawa aka kashe? To sa'annan issue na security. An ce an dauki security, an sa operation yaki. Amma yau operation yaki in suka shigo anguwar ku, zaku gan su a kofar gidan Alhaji Wane. Zai kawo abinci ya basu, zai kawo kudi ya basu. Idan har bai kawo ba fa to gobe baza su sake shigowa ba. Don haka sun shigo anguwar mu sau daya sun shigo sau biyu, sun shigo na uku. Shikenan sai suka daina shigowa, suka ce wai suna shigo anguwar mu, ba'a basu kudi, ba'a musu kaza. Nace to ai duk 'yan boko ne sun fi kusan kudi ma, 'yan wadanda ke aljihun ku ma da zaku miyo mana amshe wa zamu yi. Dan boko zai ce tausayin ka in ka kana dan sanda ina ruwan shi da kai? Baya jin tausayin ka. Amma zasu je gyalle su. Zasu zo muciya, zasu je dogon Bauchi. Nan duk unguwar ni ne na 'yan kasuwa, 'yan cirani. Wadanda in suka dauka suka ba dan sanda ma murna suke suna gonin ta. Amma Dan boko ko tara aka ci shi sai yace a bashi receipt, in ba bashi receipt ba ba zai biya ba. Baka ganin da sun tare ka ka fara turanci ka fara turanci sai su ce Mr Lawyer come out, come out. Wai kai lawyer ne? Ka cika turanci da yawa wuce wuce zaka bata musu harka. Jama'a gaskiya saboda Allah kamar yadda na fada tun a tudun wada da muke sanar da wannan wa'azi. Hakikanin al'amari mun so mu bayyana wa al'ummar mu ina ne aka dosa. Babu shakka ana mulkar mu a wannan kasar tamu, da wannan karamar hukumar, da wannan jihar, da sanatoci, da ainihin 'yan House of Assembly da House of Reps. Amma mu abinda muke cewa don girman Allah muna so da dukkanin tsarkin zuciya ku nuna mana ribar demokradiyya da ake cewa. Ni dan muciya ne gaba da baya. Anan aka haife ni anan na haifa. Ba abinda ban sani ba, babu wani lungu da ban san shi ba san ni ba a anguwar nan. Daga shekara 40 zuwa yanzu babu wata kwata a muciya da ta chanza daga yadda take. Me ya chanza? To gaskiya mun gaji. Kuma bama so. Muna son mu ga sa babban fuskokin da bamu saba ganin su ba. Kuma muna son muji muryoyin da bamu saba jin su ba. To amma anan ina so zanyi wasu tsokaci wadanda wadannan tsokaci sune zasu bani damar yanzu a ji taken wannan wa'azin nawa wanda tun farko na saka mai sunan shi. Abinda nake so in in ja hankali anan shine taken wa'azin nan shine in an bugi jacki to a bugi taiki. Babu shakka chanji muke so. Amma bari in gaya muku. Kun ga shi Buhari nan da ake gani shugaban chanji ne to a cikin tawagar tafiyar shi shi kadai ne muke iya wa taskiya cewa da gaske yake fadin abinda yake fadi. Bayan Buhari bama sukar kowa cikin su amma bama yabon kowa. Amma Buhari muna da yakini in Buhari ya karba yayi mun gani. Buhari shi kadai ne ya rage irin sassar dauna a kasar nan. Sardauna har ya mutu bashi da gida a jiya a Kaduna. Bai mallaki gida ba, baya da fili a Kaduna ko kwaya daya. Gidan shi da yake da shi tun kafin ya zama abinda ya zama a garin su Sokoto shi yake da shi har ya mutu. To ire-iren wadannan mutane su muke bukata. Haka Buhari har yanzu Buhari bai mallaki gida a duk wadannan wurare da manya manyan mu ko kuma account na kasar waje ko kuma na ciki ba. To in muna da yakinin Buhari zai iya tafiyar nan to sauran wadannan da suka zo suka tsaya suke son su ci albarkacin Buhari bamu fa da yakini a kan su. To amma da yake chanji muke so eh muna son muga sabuwar fuska da sabuwar murya. Mun kafe akan sai so din da suke tare da Buhari ya rage. Su kuma suji tsoron Allah kar su bamu kunya. Domin dukkan kunya mu dai mun shata. Yau shekara uku da ta wuce akan kujerar nan muka zauna muka ambaci sunan wasu da jam'iyyar su muka roki mutanen garin nan arziki ko mutanen garin nan sukai mana arziki nan suka zabi mutanen nan amma mutanen nan suka bamu kunya suka ba mutanen garin nan kunya. To muna fatan ku din nan da kuka fito yanzu bamu san ku ba bamu san halin ku ba amma saboda mun gaji da wadancan wadancan kuma sunyi tuban mu zuru sun koma sun ce sun tuba 2003 suka sake koma 2007 suka ce wallahi sun tuba suka sake koma don haka baza a karbi tuban su ba wannan karon. Kada wanda ya saka musu kuri'a. Ya ka cin magana kenan. To sannan murdiya karan nan babu zuwa kotu. Eh babu zuwa kotu. Amma akwai sharadi daya wanda kuma bazai yiwu ba. Inda za'a nado wani mala'ika shine mai shari'a to za'a je kotu in anyi zalunci don haka talakawa ku sake a zalince ku. Ku saka ku tsare duk wani mita uku mita 30 a'a kowa ya tsaya gindin akwati. Ba wani mita 30 ko mita 300 a'a kowa ya tsaya gindin akwati. Duk yadda za'a yi ko kai liman ne karka fito da doguwar riga don gudu zai iya kamawa. Ina fata an gane eh gudu zai iya kamawa. Tsalle zai iya kamawa zaka iya sufa in an chafa ka chafe kaga doguwar riga zata ja matsala. Don haka ko liman ne kai ranar zabe karka fito da doguwar riga. Ina fata an gane. Dole ne kifa wannan jama'a wallahi ku tsaya ku tare 'yan cin ku. Amma wallahi in kuka sake abinda akai mana a sabon garin local government 2007 wallahi in kuka sake aka sake muku wallahi karya kuke gobe mu sake wa'azi irin wannan bazai yiwu ba. Wallahi bazai yiwu ba. Saboda lokacin nan sun ga sun ci 20 sun murde ba abinda akayi. Mutanen da ko a kofar gidajen iyayen su basu ci kuri'a ba ya za'a yi a ce sun ci kuri'a a kan su 20s irin wadannan. A kofar gidan uban da aka haife ka a ce baka ci kuri'a ba kuma a zo a ce wai kaci kuri'ar yankin gaba daya. Kuma jama'ar sabon garin ku fito kuyi shiru mun ce muku kuyi kona kona ba. Amma yadda za'a jajirce shi wanda zai sata akwatin ba mala'ika bane. Mutum ne ko? To mutane su hana shi satar. A tsaya a kirga a sanar a gaban ku a manna in kuma aka chanza a ce ba'a yadda ba. Ya ka cin ta kenan. Sannan kuma kowane gari akwai filin su kuwa. Filin su kuwa kuma yana da purposes yana da manufofi da dama da irin wannan filin su kuwa ne mutanen kasar Misra suka kwatarwa kan su 'yan ci. Suka fita suka ce ba kasuwanci, ba asibiti, ba noma, ba makaranta sai Mubarak ya sauka saboda haka in akai murdiya abinda ya kamata kenan. Amma wallahi babu wata kotu domin 2007 sai da shugaba 'yar aduwa da kanshi yace ku rufa min asiri in sauka suka ce baza mu yadda ba bazaka sauka ba. An fito da gaskiyar iya gaskiya ya ga cewa ya fadi. Yace ku taimake ni in sauka. Suka ce a'a in ka sauka mu muna so. To kuma tun da kai ne akai dole ka zauna don mu mu ci. Na daga abinda ya kara wa bawan Allah nan hawan jini da bala'o'in da suka saka shi a ciki saboda su suke cin moriyar abu. Aka zo alkalai suka tabbatar da cewa gaskiya ne. To sai aka ce shikenan yanzu akwai ta a kowane irin law civil law ne, canon law ne, wanene law ne, wanene law ne shine in alkalai sukai sabani sai a ce abinda babban su ya hukunta kawai babban su ya hukunta cewa baza a ba Buhari shugabancin ba shikenan. Amma a shar'ancan an tabbatar to wadannan sune irin kotunan da muke da su. Don haka babu maganar zuwa kotu. Abinda ya rage jama'a ku tsaya ku kara kuri'ar ku. Kuma indai da gaske ne a barwa jama'a wanda suka zaba ko kare ne. Amma waya ce wai ya za'a bar musu wane ai bai chanchanta ba. Su shi ya chanchanta a wurin su tun da shi suke so a bar musu mana. Baku ganin kasa a America? Bakar fata wanda sune kaskantattun halitta a kasar. Amma kuma da yake shi mutanen suka ce yanzu kasar bata zauna lafiya? To yaya za'a yi mu a rinka kaka ba mana mutanen da bama so. Saboda haka mun gaji da ku. Bama son ku. Ku hada ina ku ina ku ku tafi. Domin kuri'a dai an yanke shawarar baza a saka muku ba don duk inda kuka je ba wanda ke mobilizing jama'a jama'a da kansu suke mobilizing kansu suke korar ku. To bama bukatan ku. Sannan sauran 'yan takara sauran 'yan takara tsakani da Allah bamu yadda da ku ba gaba daya. Bamu yadda da Nuhu Ribadu ba. Sam bamu yadda da shi ba. Don haka tsintsiyar shi ta share shi da shi da wadanda ya jawo su tafi. Bama bukatan su. To hakan nan shekaru shima bamu yadda ba baza mu zaba ba. Don haka jama'a al kiblar mu guda daya ce. Iya kar al kiblar mu da muka fitar kenan. Jama'a kai tsaye jam'iyyar Buhari itace zaku zaba. Al kiblar mu kenan jama'a. Amma kuma ku sani Buhari ba ya da kudi. Don haka duk wanda zai aiki a madadin Buhari to kada ya sa rai za'a bashi ko kwabo. Kada kuma ya sa rai in an fara mulki za'a zo ayi mai fenti a gida. A'a don bari in gaya muku. Buhari ko ya samu kasar nan bazai iya gyara ta a shekara hudu ba. Abinda muke fata matakin farko in Buhari ya hau shine barna ta tsaya. Eh barna ta tsaya. Abinda muke fata kenan a yanzu muna neman kadar kwan da za'a jefawa barnan ne ta tsaya. Yanzu ba maganar gyara ake ba. Ya kamata talakawa ku gane wannan. Irin wannan yunwa Buhariyya da akai akai ta cin garin kwakin nan to kowane talaka ya shirya. Eh sai anyi irin ta. Saboda gyara za'a yi. Eh gyara za'a yi ya kamata mutane su gane don kada mutane su zo su ce malam ku kuka ce mu zaba mutanen nan gashi ana yunwa a'a yunwar za'a yi irin ta 'yan Ghana ne. Kaje ka samu duk mutumin Ghana sun sha yunwa da Jerry Rawlings ya hau an sha wuya amma yanzu gashi nan ta gyaru. Yanzu duk inda kaga dan Ghana a ko ina a duniya yana zaman ganin dama ne. Amma 1980s sai da 'yan Ghana suka cika kasar nan tamu. Sai da suka cika ko ina saboda yunwa da kishiruwa a lokacin wani dattijo yazo yana bada labari duniya na kwance 1980 yace kishirin miya na sule ake siya a Ghana. Ana ta mamaki sule gishirin miya sule. Saboda rayuwa tayi kunchi kamar yanzu a ce ne gishirin da za'a sa a miya sai an sa na naira dubu daya. Miyar kullum sai an sa mata gishiri na dubu daya. Wace irin miya ce wannan? Haka Ghana ta zama. Amma yanzu Ghana ta gyaru ko bata gyaru ba? Daga cikin gyaruwar da Ghana tayi jama'a yanzu duk Africa in ka cire South Africa babu kasar da matsayin ilimin su ya gyaru irin Ghana. Sannan harkar tsaro babu kamar Ghana. Yanzu ga Ghana sun samu man fetur. Ghana sun samu man fetur sannan don girman Allah kaje ka zauna a Ghana ka ga dauke wutan da za'a yi. Ba Ghana ba kwata na nan kwatano. Kaje kaga ana dauke musu wuta suna rasa ruwa a kwatano. Nijar nan ba'a dauke musu wuta amma fa mu muke basu wutar. Mu mu bayar amma tamu ta mutu. Amma su suna can suna shan haske. Abinda nake so in gayawa talakawan mu shine jama'a eh ko kun zabi Buhari zaku taya da addu'a ne. Matakin farko kasar wallahi Allah ya azurta mu. Amma anyi wawurar da in Buhari ya hau hatta shi kanshi abinda yake tunani na za'a shake wasu marasa gaskiya a amayo yana da wahala abinda mu muke fata a tsai da zaluncin. In aka tabbatar zalunci ya tsaya sannan sai a fara shawaran ya za'a yi a ci gaba. Saboda sunyi kache kache da kasar. Duk mutumin da ya rike mulki kwana bakwai sai ya azurta kanshi arziki da in zai shekarar dubu 70 bazai ainihin talauci ba. Zai wawura ya wawura yaje ya adana. Ya wawura ya wawura yaje ya adana. Kuma adanawar in ya tashi zai zubar inda ba'a tunani. Yanzu kasar Switzerland da zasu dawo mana da kudin mu da aka sata aka kai musu ajiya sai dai kasar su yi gudun hijira su kansu. Gaba dayan Switzerland a karkashin kudin ajiyar Najeriya suke rayuwa. Don haka da aka je kwato kudin wani barawo da ya sata sai suka ce ina in suka dawo da wadannan kudin ma'aikatu da yawa zasu tsaya a kasar su. Kaga da ba'a sata an kai ba da kasar bazata kai wannan matsayin ba. Ma'aikatu nawa ne suka kwanta dama a cika ji? Suna dewa. Cika ji bayan cika ji duk industrial area ce. Duk wurare ne na masana'antu yau duk ina suke? Sun kwanta dama. To chanji muke bukata. Abu na daya kenan abu na biyu dewa wadanda ke tare da Buhari su kansu they are corrupt personals. Su kansu na daga cikin abinda ya faru shine rikicin Kano da Katsina da yake faruwa. Wasu ne zasu je da sunan Buhari su karbi miliyan 25 wurin wannan dan takara a sake karban 25 wurin wancan dan takarar. Daga karshe me zai faru? Sai a ce ga wanda jam'iyya ta zaba amma ga wanda sunan shi ya fito. Yaya ake haka? A wannan kanin matar Buhari ne a wannan kanin kaza ne na Buhari sai ya je ta karban kudi a wurin wane ta karban kudi a wurin wane. Saboda haka su din wadannan da ake gani suke kewaye da Buhari to an san cewa babu shakka ba irin su daya da Buhari ba. Kuma wasu su sun zo ne irin yadda wasu suka takure tsawon lokaci a gindin Abubakar Gumi. Shi bazai ci ba to su sa ci da sunan shi. To sa'annan na uku. Wadannan sa babban fuska na 'yan takara to suji tsoron Allah game da mu. Nayi mamaki a ce wai sai yau ne dan takarar gwamna na jam'iyyar Buhari wai zai zo mu zauna domin tattaunawa. Amma wallahi saboda Buhari yana da mutunci a fuska ta. 12 na rana aka bugo min waya ga dan takarar gwamnan CPC nan zai zo zaku zauna. Sai nace madallah ni da kai na na zauna na shishirya inda za'a mu zauna. Amma bai zo ba. Har lokacin kwanciya ta bacci bayan sallar juma'a naga na fara jinjiri sai shikenan sai nayi kwanciya ta. Sai can na tashi sallar la'asar sai naga miss call. In buga wai sai suka ce wai sun zo ne an ce baza su samu gani na ba nace a'a baku zo lokacin da aka ce ba. Nace kuma ku da kun girmama wannan zuwa da ya kamata in san zaku zo don in zaku je wurin mai martaba sarki Wane a kalla bazai yiwu a ce karfe takwas na safiyar ranar bai san zuwan ku ba. Amma kun ga da yake kun dauka malami bashi da aikin yi. Kawai ko yaushe kuka zo marhaban biko. Saboda haka kawai sai da kuka kamo hanya ne sannan sai kuka ce a gayawa malam ga ku nan tafi. Daya kenan sannan na biyu haka 'yan jam'iyyar shekarau basu tashi tahowa ba suma sai lokacin da aka ji na fara magana a Markaz at tudun wada. To nayi mamakin wannan abu. Yanzu tsakani da Allah idan dai an taho ne wurin Albani mutumin da aka san yana da manufa da tsare tsare tsakani da Allah baza a taho ba sai ya rage kwana daya zabe me za'a tsara? Kawai an zo ne a fada mai abinda ake so a fada shi kuma kawai yazo ya fada abinda ake so. To ku 'yan jam'iyyar Buhari kun ci albarkacin Buhari ne kawai. Iya kar abinda za'a mu ce muku kenan. Amma in ba haka ba bamu san ku ba bamu taba ganin ku ba, bamu taba mu'amala da ku ba, kuma bamu da garantin ma ku bawa
[Segment 5/5 | 01:20:00–end]
[Speaker seg5-spk:0]
lan wadancan bane. Wannan na daga cikin matsalolin da ke damun mu. Sannan bamu da tabbas. Allah yasa ku ba wato ba yan siyasa ne da suka jarabtu da son mulki ba. Don haka yanzu sun zo ne dan su ci albarkar Buhari in an tafi an kada kuma me zai biyo baya? Ana cewa basu ci ba ko an murde ko anyi kaza sai su koma wurin wadancan. Yanzu ku dubi mutanen da yau shekara uku da ta wuce muke wannan gogormayar da su jama'a yau sune a waccan jam'iyya. Wasu in su har kama su akayi aka tafi da su ofishin SSS. Ni na dibi lauyoyi muka tafi fa muka je muka fanso su. Amma yau kuma sun koma wurin wadancan saboda me saboda suna sa rai wadancan mutanen zasu basu mulki. Kuma kowa yasan irin goyon bayan da muka nuna wa Hon. Kuye. Amma kowa yasan me ya faru daga baya? Da aka murde ya kasa daurewa ya koma cikin su. Yau duk wannan jam'iyya ba wanda ake wa makirci irin shi. Makircin karshe shine wanda akayi mai jiya. Aka ce shari'ar ma an kore ta. Tsakani da Allah da ya tsaya a inda ake tafiyar nan ta gaskiya kuna jin yau bazai zama shine dan takarar mu ba? Koda jam'iyyar in yamutsa ce Abga. Ko ba haka ba jama'a?
[Speaker seg5-spk:1]
Haka ne.
[Speaker seg5-spk:0]
Toh abinda muke magana shine Allah yasa wadannan yan takara ba bane wato yan siyasa ne wadanda kawai sun jarabtu da mulki. Don haka in sunji bazasu samu nan ba zasu koma can. Kana ga wancan mai tsintsiya da yana nan sai ya koma can yana ganin zata share ko? Wallahi ba inda zata share shi da yake dauke da addu'ar bayan Allah ma a kan shi. Ba inda zata je. Amma maganar da muke dai jama'a kunji alqiblar da muka dora ku akai?
[Speaker seg5-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg5-spk:0]
Toh ku tsaya a kan ta. Sannan ku kuma matasa qarti da aka dauke ku a kan ku zaku yi sata a kwati. Ka duba ka gani a cikin kungiyar ku ta masu sata a kwatin nan dan takarar yayan shi guda nawa ya kawo? Sannan a cikin ku guda nawa ne suke da digiri? Sannan a cikin yayan shi guda nawa ne basu da digiri? Toh ku auna ku gani. Ana can ana taro da ku yanzu ana baku adda ana fada muku wadanda zaku sara. Ana baku kwayoyi ana fada muku yadda zaku yi ku hadiye su. Amma abin cewar shine sun zubo yayan su a cikin wannan abu. Toh daga nan zaku gane cewa su zasu koma su zauna ne a tsare su a tsare yayan su. Idan mulki ya tabbata ta hanyar murdiya da zaku yi me zai biyo baya? Sai a gan su a sama. Abinda ya faru kenan tsakanin yan Niger Delta da Obasanjo. Obasanjo ya ringa diban makamai trailer trailer yana kai musu. Haka suka ringa fitowa suna fadi cewa sai mutum yazo ya samu kauye guda sai ya harbe su ya kashe su. Dan bindiga jama'a a ce yan ta'adda an kai musu treloli na bindigogi a zube musu a tsakiyar gari a ce su diba. Don haka yanzu suka tashi su ba wai murda akwati suke ba zasu je ne su samu mutanen kauye guda duk su harbe su sai su kwashi akwatinan. Kunji abinda yasa ta rikice tsakanin yan Niger Delta da Obasanjo. Shi yasa sulhun bai yiwu ba sai da lokacin yar aduwa yazo ya nemi ya sulhu tsakanin su da su. Amma sun ce ba sulhu tsakanin su da Obasanjo dan me ya basu makamai sun kashe iyayen su da kakannin su. Amma tunda yaci zabe ya gaba basu sake ganin shi ba. Toh saboda haka gaskiya matashin duk da aka dauki adda ko wani makami aka bashi aka ce ya datsu wani matakin farko an maida shi wawa. Mataki na biyu kuma ya tsaya yayi nazari. Shikenan a matsayin bawa dan daba ina yayan wannan mutumi ko bai da yaya ko bai da kanne sa'o'in ku? Me yasa bai sa su ba? Toh sannan daga karshe jama'a ina son in nuna muku wallahi Najeriya babu wani mutum daya da zai iya gyara ta kaf babu kuma wasu tarin mutane da zasu iya gyara ta. Babu kuma wata jam'iyya da zata iya gyara ta gyaran Najeriya wallahi sai Allah. Allah kuma yana da babban ka'ida itace addu'a da tsarkin zuciya. Amma kasa ta riga ta baci. Abinda muke fata jama'a a yau din nan kowa yayi shafa'i da witri ya rokan mana Allah cewa ya Allah wannan hali da za'a fuskanta daga gobe Allah ka sa shine wahala ta karshe da zamu fuskanta a kasan nan. Amma jama'a duk inda ake wahala wallahi mun wahaltu. Kuma muna cikin wahaltuwa da yunwa da fatara da rashin tsaro da rashin damuwa da komai ya kare a kan mu. Duk wani alkawari yanzu da za'a zo ayi mana mu ce ba shi ya dame mu ba. Abinda ya dame mu shine me muke so? Chanji kawai muke so. Duk abinda zaka fada a ce ka fada eh anji amma ba'a son ka ne ka koma kawai. Yakarta kenan kawai ba'a son jam'iyyar ku kawai abinda ake so kenan. Jama'ar musulmi kamar yadda na ce ina so in takaita sakon nawa kwarai da gaske. Wadannan sune sakonnin nawa da karshe ina fatan Allah ya gyara mana al'amarin mu. Kuma ina rokon Allah madaukakin sarki Allah ya mana zabi na gari. Ina rokon Allah duk wani azzalumi Allah ya sa wayewar garin gobe itace karyewar shi da karyewar alkadarin shi har qiyama ta tashi. Allah ya sa dangwala kuri'a da talakawa da al'umman Najeriya zasu yi gobe shi zai kawo karshen zalunci da mugun halin da muke ciki. Sannan malamai malamai ku ji tsoron Allah. Malamai ku ji tsoron Allah. Sannan manyan mu na arewa da manyan mu musulmi ku sani bahaushe yace da safe ake kama fara. Jama'a mutanen nan suna da na duk abinda suke yi wallahi. Amma mu a arewa bamu da wani Mu al'ummar mu ta musulmi bamu da wani Mun zauna wani taro a Kaduna yau kamar wata biyar jama'a. Da na dube mu taron an ce Taron an ce Daga masu digiri daya daya sai biyu sai uku daga lauyoyi sai injiniyoyi sai wadanda suke likitoci ne. Sai naji ana maganar ina za'a dosa yanzu sai naji na sace. Ma'ana sai lokacin ne za'a fara maganar ina za'a dosa? Kamata yayi a ce a yanzu da muke magana muna da din mu yaya za mu bullo wa Sannan wallahi al'ummar mu wajibi ne su fadaka. Yaushe za'a ce jama'a mutanen nan suna da dan takara daya muna da uku. Suna da daya muna da hudu. Sannan yaushe za'a ce hudu nan idan Allah suke wa a irin siyasar ba na wadda ta bayyana addini da addini kabila da kabila yanki da yanki. A ce kowa an nemi ya janye yace sam shine manzon da Allah ya turo ya kwaci mutane. Wadannan mutanen dan Allah suke yi? Ba dan Allah bane. Na daga kukan mu ayi cewa wadannan an turo su ne dan su karkatar da Don haka duk wanda ya dangwala musu toh yana daga cikin masu karkatar da ajanda mu. Saboda duk sanda muka cika mota za mu tafi Sokoto kowa yasan daga Zaria hanyar samuru za mu kama. Haka ne ko ba haka ba? Idan ka matsa mu kama hanyar Kaduna toh ba shakka za mu kai Sokoto amma za mu yi zagaye. Haka ne ko ba haka ba? Babu shakka idan kuka sake kuka chanza ko wasun ku suka chanza daga wannan alqibla toh abinda ake nema a samu an samu shine dama idan ba zaka iya hanawa bara ba kan su Yanzu jama'a dukkanin maqiyan mu sun tattaru gefe guda kaf sun koma gefe guda haka ne ko ba haka ba? Toh amma mu kuma fa an dargaza alqiblolin mu. Toh hikimar wannan wa'azin dama itace samar mana da saiti da kuma alqibla guda daya. Don haka don girman Allah kar wanda ya sake gobe gari ya waye a zo a baka naira dubu ashirin da biyar a karbi kuri'ar ka. Kar ka sake kuma kar ka sake a zo maka da wata takarda a ce kawo wannan kuri'ar kaga wannan takardar da kaje in ka nuna zaka saka kuri'a kai bazaka bi layi ba ma. Duk wannan yana daga cikin makircin da suke bi. Sannan masallacin ma da ba'a wa'azi gobe da asuba a fara a samu wani mai fasaha ko malamin islamiyya ne ya mike yayi maganganu karara ire-iren haka cewa jama'a ga alqiblar babu laifi yazo da ballot paper ya nuna wa jama'a kunga inda zaku dangwala kar ku dangwala kasa kar ku tafi can kololuwa zaku fado ga inda zaku dangwala. Ina fatan an gane? Ya kamata duk masallatan garin nan toh sannan bari ku ji. Kamar yadda in aka fara azumi bahaushe zai ce goma ta farko goma ta wuya goma ta daukin sallah ko toh ana neman ayi mana haka. Kunga yanzu kowa ana daukin zaben toh in kuka sake baku tara karfin ku wuri guda ba kuka samu faduwa a abubuwan da zasu faru a gobe toh abinda zai biyo baya shine zabe na gaba jikin ku zai sanyi. Toh kuma zabe na gaba shine tukullimar shine qashin bayan shine ke komai da kowa. Saboda kar ku sake kuyi abinda nan gwiwoyin ku zata yi sanyi game da zabe na gaba na biyu. Don girman Allah matasan nan da suka taso suka fara yin wa'azo zi'an guwanni toh su sani yanzu shine lokacin da aka fi ko yaushe bukatan wa'azo zi. Dan in baku sani ba
============================================================
[Part 3]
============================================================
[Speaker spk:0]
Anyi amfani da masallatai da dama. Wajen yaki da abin da jama'a basu yarda da shi ba. To mutanen nan fa na daga cikin manufar su. Ba za su sake barin a sake samun wannan damar ba matukar suka kai labari. Don haka ka kaddara mutum ne da wuka sharbebiya budaddiya. Ka tabbatar in ya danne ka kasa. Yanka ka zai yi. In ka shaki makogoron shi. Akwai kalmar da zai fadi da zaka sassauta?
[Speaker spk:1]
A'a.
[Speaker spk:0]
To duk abin da za a fada muku. A fada. Amma wallahi tallahi ba ja da baya. Amma in kuka sake kanku ya rabu. Wallahi tallahi za ku ga makircin da baku taba tunani ba. Akwai makwautan kasashe irin su Chadi da Kamaru. Ku je ku bincike su su baku labarin me ake ciki. Sinariyon iri daya ne. Yanzu lallashin ku ake. Gobe za ku zo kuna lallashi ba za a saurare ku ba. Don haka kuri'an nan da za ku tsaya gobe. Ka daure. In ma kun zo karfe takwas din an ce sai sha biyu za a fara tantancewa. Kar ku tafi gida.
[Speaker spk:1]
Na'am.
[Speaker spk:0]
Mutane suna cewa wai in an tantance za su koma gida. Sha biyu za su dawo. Ko sallah kuyi jam'i a wurin.
[Speaker spk:1]
Na'am.
[Speaker spk:0]
Ko sallah kuyi jam'i a wurin.
[Speaker spk:1]
Na'am.
[Speaker spk:0]
Kuma jam'in ma in ya kama kuyi jam'in tsoro. Hamsin suna sallah hamsin suna gadin akwati da masu akwatin. Wallahi kuyi sallar tsoro. In baku yi haka ba kuna can kun yi sujuda Wallahi sun gama kafin kuyi uku. Sun gama. Don haka hamsin suna sallah hamsin suna gadi. In an idar wannan hamsin su dawo bakin daga wannan can hamsin su yi sallah. Rana daya ce. Kuma uzuri ne. Amma ku karanta littafin Babu shakka. Babu shakka jama'a. Wallahi. Duk abin da za a gaya mana na a yaudare mu game da wadannan al'amuran. An riga an makara. Kuma mun riga mun kama alkiblar mu. Amma abin da muke roko Allah madaukakin sarki ya bamu nasara.
[Speaker spk:1]
Amin.
[Speaker spk:0]
Wadanda suka zo daga garuruwa. Ba za mu tsawaita ba don girman Allah kada wanda ya kwana garin nan yau. Saboda in ka kwana garin nan sakon ba zai isa garin ku ba yau. So muke ka ci dare duk inda zaka je. Tun daga nan ka isa birnin Kebbi. Sakon duk da zaka fadi a cikin minti biyar ko minti bakwai. Amma gaskiya jama'a. Idan muka sake. Muka wayi gari kawunan mu a rarrabe. Jama'a tafa bayyana fa. Bamu yi kuri'an nan da yawa ba fa amma ta bayyana mun fi yawa. Bamu yi kuri'an ba fa Amma ta bayyana mun fi yawa. Don mutum daya zaka samu yana da mata biyu. Yana da 'ya'ya goma sha biyar. In ya dade a duniya yana da jikoki hamsin. Can ko zaka samu mutum daya da 'ya'ya biyu. Jikokin kuma duk shegu ne suna can Ina fata an gane.
[Speaker spk:1]
Na'am.
[Speaker spk:0]
Saboda haka tsakani da Allah. Idan fa a wannan yawan namu muka sake aka kai mu aka baro. Aka yi mana cikin da babu uba. Wallahi bamu da asibitin da zai karbi haihuwar shi. Jama'a wannan shine sako na. Kuma kamar yadda na ce malamai na cewa Maganar da tafi kowace ita ce wadda ta nusar. Kuma ta biya bukata. Amma fa wadannan sakonnan ba za mu dena fadan su ba. Kullum muna da karatun Bukhari jama'a. Ranakun asabar da lahadi ko? To yanzu karatun mu na Bukhari jama'a za mu rinka dauko shi tun daga ranar Alhamis ne. Alhamis juma'a asabar. Lahadi har sai an gama zabe. Alhamis juma'a asabar lahadi haka za mu rinka dauko karatun. Don haka insha Allahu ta'ala. Idan muka wayi gari gobe jama'a babu karatu ko ina. Amma akwai karatu jama'a. Akwai karatun Bukhari da daddare. Akwai karatun Bukhari da daddare. To kuma haka za mu cigaba da wadannan karatuttuka insha Allahu muke cewa Allah ya kai kowa gida lafiya.
============================================================
[Part 4]
============================================================
[Segment 1/3 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yanzu da muke magana daren juma'a ne daidai da daren sha biyu ga watan jumada al ula hijira annabi na da shekara dubu daya da dari hudu da talatin da biyu daidai da sha hudu ga watan April shekara ta dubu biyu da sha daya. A daidai wannan lokaci da jama'a suke tsammanin zamu yi karatun hadisi karatun littafin Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi. Kamar yadda sanannan abu ne ga duk wanda yake bibiyar da'awar mu kai tsaye ko kuma ta kafofin yada bayanai na zamani cewa mu 'yan darul hadisis salafiyya dake nan Zaria a Najeriya muna da ruwa da tsaki game da harkokin yau da gobe da suka shafi addini, siyasa, tattali, rayuwa da al'amuran da suke shiga da wadanda suke ainihin fita. Musamman in suna da alaka da mu kai tsaye ko da wasu 'yan uwa ko suna da alaka kai tsaye da addinin musulunci. Sanannan abu ne dukkanin daren lahadi da daren litinin sune dare rakin da muke karatun ainihin ma'ana ranakun asabar da lahadi yau kusan shekaru uku kenan da su ya gabata. Amma a irin wannan hali da wannan zabe na shekara ta dubu biyu da sha daya ya kakkauto sai muka dage karatuttuka da muke yi ainihin wato a dare rakin lahadi wato ranakun asabar sai muka jawo su baya suka koma dare rakin juma'a wato ranakun Alhamis ba dan komai ba domin mu rinka fadakar da al'ummar mu muna wayar da kansu muna nusar da su zuwa ga abun da ya dace da kuma abun da bai dace ba na daga harkokin da al'ummar kasar mu suka samu kansu a ciki na harkokin siyasa wanda ke da alaka da addini wanda ke da alaka da tattali da rayuwa da kuma harkokin yau da gobe. Hakikanin abun da yake faruwa shine al'ummar mu musamman a nan arewa muna cikin dimuwa da rudani sakamakon maganganun da nayi a cikin kasusuwan da suka gabata na makonnin baya wadanda na ainihin yi maganganu dangane da harkokin siyasa din. Wannan dimuwa da rudani mun shiga cikin ta ne a arewacin Najeriya saboda mun karya karin maganar da Bahaushe yake cewa ba a fafe gorara na tafiya. Baki daya shirin al'umma dangane da ina mafita ina ta tinkara yaya za a yi dangane da al'amarin siyasa kaf a arewa bai wuce wata tara ba a yayin da wasu suke da shi shekara tara da ta gabata. Wannan dole ne ya saka mu a cikin dimuwa tun daga malamai har 'yan siyasa harda tawa har sarakuna balle dangin mu talakawa wadanda ke yawo a kwararo kwararo jaridu da kafofin yada labarai suna ainihin wato buga kawunan su. Dan uwa mai kallo da saurare kaset din da kake kallo da saurare a yanzu taken shi shine rigiji gabji an cire shugaban 'yan sanda saboda zabe a Zaria kaji matsalar da zamu tattauna mai suna Alhaji Kabiru Ibrahim me ya faru kuma me yasa. Sannan sai ziyarar manya manyan 'yan siyasa da suka ainihin wato yi zuwa gare mu. Sannan me ya kawo ainihin wato gigicewar da wasu 'yan siyasa da tsoro da fargaba me ya kawo musu irin ainihin wato wannan gigicewa da fargaba sakamakon ainihin wato gabatarwa ta zabubbuka. Insha Allahu ta'ala a wannan ainihin fagen zamu yi addu'a ta musamman ga jami'an tsaro na ainihin wato yankin Zaria dake wayan ta wato lardin Zazzau da suka shafi kananan hukumomin sabon gari da Zaria. Sannan na biyu shugaban 'yan sanda na kasa da shugaban INEC da kuma ainihin wato na kasa sannan da bayani dangane da shugaban 'yan sanda na nan ainihin Zaria mai suna Alhaji Kabiru Ibrahim Allah madaukakin sarki ya taimake mu.
[Speaker seg1-spk:1]
Amin.
[Speaker seg1-spk:0]
Jama'ar musulmi zasu yi mamaki musamman wadanda basu san yadda Albani ke gabatar da da'awar shi ba sai suce duk wadannan abubuwan da aka ji ya tattauna a kai sunyi kama da harkokin 'yan jaridu. Me ya kai shi yana malami mai wa'azi kuma bin tafarkin 'yan jaridu. To gaskiya saboda Allah dalilai ne guda biyu kwarara dalilin farko na komawa zuwa ga alakar wadannan matsalolin da mu kai tsaye. Dalili na biyu kuma karka yi mamaki ni dan jarida ne gaba da baya Allah madaukakin sarki ya taimaka.
[Speaker seg1-spk:1]
Amin.
[Speaker seg1-spk:0]
A kashin gaskiya abun da ya faru jama'a a daren shekaranjiya ko kuma yammacin shekaranjiya 'yan sanda suka je anguwar Dogarawa dake sabon garin Zaria a nan jihar Kaduna suka je suka afka ainihin wato suna bincikar wani malami mai suna Malam Yahaya Al Likori wanda daya ne daga cikin daliban darul hadisis salafiyya fiye da shekara ashirin da suka gabata. Suka je suna bincikar shi da zimmar cewa labari ya iso gare su cewar a gidan shi akwai wato akwai takardun dangwala zabe wadanda aka ce ana nan ana dangalawa domin ainihin ayi magudin zabe shi ko wannan malami Malam Yahaya ya bayyana karara yana tare da ainihin jam'iyyar Bahari wato CPC. To wadanda suka kai karar karar ba tare da sakayawa ba sune 'yan jam'iyyar PDP da wata mata da kuma wani gardi yaron su sune ainihin wadanda suka kai wannan kara. Da aka ainihin shiga sai aka samu amma na na misali wadda kowace jam'iyya takan yi ta nuna inda za a dangwala mata dan kai a kuskure. To kaga wannan abun mamaki ba bane ma. Ba abun saka zabe bane abun misali ne kowace jam'iyya tayi jam'iyyar tayi CPC tayi PDP ma tayi duk wata jam'iyya tayi don in taje sai tace wa jama'ar ta kunga inda zaku dangwala. Ba dan komi ake haka ba zaben da aka yi wanda a wannan lokaci ni shine farkon zaben da nayi a rayuwa ta a Najeriyar nan. Zaben su Shagari da aka yi na 'yan a wannan lokaci wannan zaben abun da ya faru jama'a sun rinka yin kuskure bayan duk an nuna musu ga abun da ya kamata su yi abun mamaki musamman mata a nan arewa in ance in kinje ga abun da zaki danna zaki danna gida da masara ko zaki danna dan mabudi wadanda wadannan jam'iyyun a lokacin sune jam'iyyun arewa. Ko dai ki zabi ko ki zabi ita ce take da alamar dan mabudi ita take da alama ta ainihin wato gida da masara. Idan mata musamman suka je sai suka ga hoton jam'iyyar wadda take da hoton 'yan yara sai kaji tace Allah sarki mu masu 'yan yara bari mu dangwala a nan. To shikenan sai suka yi ta danna wa jam'iyyar inyamurai ga su su kuma Hausawa ne 'yan arewa. To sai aka ji tsoron irin haka shi yasa daga wannan lokaci duk sanda zabe yazo sai a rinka kowace jam'iyya wata ma jam'iyyar in ta tashi hoton nata kawai zata yi da sunan nata da hoton ta da komai sai ta sa dangwala hannu makeki yadda za a gani sai a ji wannan cewa kunga inda zaku danna. To irin wannan kowace jam'iyya tayi kuma babu wata doka ta kasa ko dokar wata jam'iyya ko dokar hukumar zabe da ta hana haka. Dan haka iyakacin abun da 'yan sanda suka samo a gidan Malam Yahaya kenan. Aka taho da shi har zuwa To dan haka zo da shi shugabannin 'yan sanda suka duba suka gani sai suka ce to ai wannan ba wannan ai wannan hoto ne wannan kwatance ne. A karkashin wannan su basu da dalili da alfarmar da zasu tsare shi balle su tuhumce shi. Dan haka abun da za a yi ya koma gida idan ya koma gida gari ya waye to sai yazo sai a ji yadda za a kara cigaba da bincikar magana. To shikenan sai da safe da ya tashi dawowa sai ya dawo tare da ainihin dalibai da malamai da dattawan gari gaba daya da aka dawo a wannan lokaci shikenan to na daga cikin kuskuren da suka fara yi in nace su su su Malam Yahaya da dukkanin ustazan sai suka boye mana maganar wai suna ganin boyewar suna da nunan niyyar kwakwalwar da zasu iya wadannan kurdawan baku yi karfi da zaku iya da su ba duk abun da ya faru ku rinka fada mana mune tsofaffin zabi wadanda munfi karfin a watsa mana ainihin tsakuwa a kama mu baku nuna ba kuyi hakuri ustazai da sauran lokaci muma sai da muka bi kafar wasu tukuna muka goge sannan kuka ga muke iya tinkarar su da haka dan haka in abu ya faru yana faruwa ka fadi menene ya faru me yiwuwar wani abu ne wanda kai baka san shi ba ya bayyana gare ka ne da ka fada sai a ce a ga tushen abun. Saboda haka watan nunanniyar magana ce tun su basu san da ita ba mu kuma da muka kashe ta muka ja baki muka yi shuru to kunga ashe da ace sunyi wa kansu adalci da tun da daddaren sun fada da tun da daddaren muka bi muka kashe maganar. Amma sai suka ga cewa zasu iya to daga karshe dai su wadancan wadanda suka kai magana sai suka ga cewa shugaban 'yan sandan nan fa ya ki musu abun da suke so domin a sun samu shugaban 'yan sanda na Zaria wato ya rinka yi musu duk abun da suke so duk umarnin da suka bayar in ba wani umarni kwaya daya ba wanda insha Allahu ta'ala a yau zan shine kadai basu bi ba sakamakon wannan menene ya faru. Sai aka ce to shugaban hukumar 'yan sanda na jihar Kaduna gaba daya yana neman da aje da Malam Yahaya can Kaduna to a lokacin ne da ta tabar zata yi yawa sai suka ga tasha kansu sai kuma sai suka bugo muni. To a lokacin ne sai nake cewa a'a ya tabbata ana tuhumar shi da laifi in ana tuhumar shi da laifi a rubuta takarda rubutacciya sannan a hada da shi da takardar da kuma duk jama'ar shi magoya bayan shi a tafi da su Kaduna. Idan kuwa ba a tuhumar shi da laifi to shikenan sai a sake shi ya tafi gida. Aka ce gaskiya ba a tuhumar shi da laifin komai. Nace to shikenan sai a sake shi ya tafi gida shikenan magana ta mutu aka ce a'a shugaban hukumar 'yan sanda ya matsa na Kaduna sai an kai shi. Sai nace to indai har sai an kai shi to abun da za ayi ku kuyi marmar za ku dauki lauya yazu aje a samu a samu watta doka daga kotu wanda tunda ba a tuhumar shi da laifi to ba ada alfarmar kuma ace za a tsare shi har ace an kama shi a karkashin kamun kuma a kame za a kai shi har Kaduna wurin shugaban 'yan sanda na jihar. To karshe da al'amari yayi al'amari al'amari yayi kamari wanda wadannan maganganu jama'a suna da reshi dan haka zaku yi hakuri yadda zaku rinka jin suna shiga suna fita. A cikin makon da ya gabata tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma sanata Ahmad Muhammad Makarfi ya kawo muna ziyara har gida na kuma har makaranta ta To daga cikin abubuwan da yazo yace to yazo neman goyon baya ne saboda ya fito takara a wannan shekara ma ta muka ce to muna mishi mara ba ko muna mishi fatan alheri amma muna da maganganu wadanda zamu yi wadanda daga cikin wadannan maganganun sune munyi mamaki kwarai da gaske yayi gwamna shekara takwas bashi da alaka da mu ko kwaya daya. Yayi sanata shekara hudu bashi da wata alaka da mu ko kwaya daya. Sai muka ce to bana ko dan al'amari yayi al'amari ne. To wannan matsala ta daya kenan matsala ta biyu muka ce babu shakka a wannan ta zara da aka samu ta shekara kusan goma sha biyu ta haifar da ta haifar da wata ta zara wanda aka samu aka samu ainihin wato ta zara wanda ta rinka haifar da abubuwa saboda rashin saduwa. Sannan ya sani da cewa daga cikin matsalolin sune sunyi mulki wasu mutane da suka rinka saka mana a matsayin 'yan takara na ciyamomi na kananan hukumomi ko na ainihin ko na ko na a wannan lokaci babu shakka sun rinka kama karya da wulakanta mutane wadanda sun ja musu bakin jini gaba daya domin mu a wurin mu yaron su ne da yawun su da sanyewar su sakamakon haka babu shakka yaddda wadannan na kasa suka yi bakin jini suma na sama din. Yace to yana fatan a bashi cikakken goyon baya don girman Allah duk wadannan abubuwa da aka yi kuka za a samu gyara a kai. To ni nayi iya wadannan maganganu na bar masu maganganu irin su Malam Musa Sahabi da wasu suma duk suka kawo nasu maganganun da tattaunawar da tambayoyi da jeho kalubale da makamantan su bayan duk da ainihin aka tashi muka ainihin watse shikenan magana ta cigaba a haka to a wannan lokacin ne sai na buga mishi waya da rikicin Malam Yahaya ya taso sai nace to kaga daga cikin abun da nake gaya maka ya kai mai girma sanata ga irin kananan 'yan siyasar da nake maka ishara a tattaunawar mu wadanda suke wakilta kwa kananan hukumomin Zaria da sabon gari yanzu sun sa anje an kama daya daga cikin malaman da kake fatan su fito su goyi bayan ka domin ka sake haurawa zuwa ga kujerar da ainihin kake a kan ta. Gashi nan sun sa an kama nan take ce in aje waya yasan wadanda ya bi bugawa waya nan da nan kafin wani lokaci aka ce magana ta mutu wannan maganar ban fito da ita ba sai yanzu. Dan haka a babi na adalci sanata Makarfi shine ya buga waya ya kashe wannan magana amma kafin ya kai ga kashe maganar su wadancan kananan 'yan siyasa na kananan hukumomin sabon gari da Zaria dama suna da kuka akan shugaban hukumar 'yan sandan nan sun hada shi da kudi ya ki sun nemi mishi barazana ya ka gara barazanantuwa sun nuna mai duk abun da zasu nuna mai ya ki dan haka sai suka ce baya goyon bayan su wai yana goyon bayan CPC ne. Ni ina da yakini kuma Allah ne shaida baya goyon bayan jam'iyyar CPC sai dai man ne ma'ana kwararran 'yan sanda ne wanda a karkashin kwarewar shi dole ne ya tsaya ya nemi wa kasa aiki ne ba ya nemi wa wata jam'iyya ba ba ya nemi wa wata jiha ba ba wasu mutane na kabilu ko wasu addini ba dan haka gaskiya gaskiya ce anyi anyi yayi abubuwa in su wane da su wane ya ki sakamakon haka sai suka ce dama baya goyon bayan su. Dan haka abun da suke so nan take a cire shi. Dan haka jama'a kunji ina sake buga mishi waya dan inji me ya faru sai yace a yanzu haka dinnan bayan na aje waya bai wuce minti biyar ba har ance ya hada inashi inashi an tashe shi daga Zaria an koma da shi Abuja. Dan haka jama'a kunji dalilin da yasa aka cire shi kenan kuma dalilin kwaya daya ne anyi anyi a hada shi da kudi ya ki karbe anyi anyi ayi mishi barazana bai barazanantu ba anyi anyi ayi mishi duk abun da ake gani zai chanza mishi tunani na farko dai tukuna ya kamata duk wanda bai sani ba ya san Alhaji Kabiru Ibrahim musulmi ne Bahaushe ne dan nan tudun wadar Zaria to daga cikin abubuwan da yake bayyanawa cewa shi fa ya nemi daga karshe karshen aikin shi ne a dawo da shi gida dan ya samu sabawa da dangin shi mutanen Zaria. Dan a san shi sannan yaga wacce irin gudunmawa zai bayar wajen cigaban kasar shi ta Zaria. Wannan tun makon farko da aka dawo da shi garin nan ni bana garin a waya nayi mu lambar waya ta bana mantawa ina driving daga Abuja zan tafi birnin Kebbi yake buga munu muke wannan maganar akan shi manufar shi kenan ta dawowa Zaria ma'ana dan ya kawo cigaba garin shi ya kawo zaman lafiya ya san dangi dangi su san shi sannan su san wacce irin gudunmawa ya san wacce irin gudunmawa zasu hadu su ba kasa a gaba daya. Sai ya nuna cewa to a irin wannan hali idan yayi abubuwan da su suke neman yayi randa ya da wani ido zai kalli zage zagi da wani ido zage zagi zasu kalle shi. Tsakani da Allah jama'a dan haka yace bazai ba. Sannan kuma shi shugaban su na kasa baki daya shine Hafiz Ringim tunda za a fara zaben nan ya tara duk 'yan sanda ya nuna musu cewa wannan karan gaskiya da gaskiya za a tsaya babu son zuciya kuma duk 'yan sandan da aka tuhuma da wata rashin gaskiya ko yaci kudi ko yayi wani abu zai hadu da mummunan fishi na ainihin shugaban 'yan sanda Hafiz Ringim. A karkashin haka a sata izin da gaggawa Hafiz Ringim yayi musu wani irin transfer aka dauki shugaban 'yan sanda na jihar Kaduna aka jefa shi jihar kaza na jihar kaza aka kawo shi ma'ana inma ya gama karban kudin su wane da su wane zai musu aiki kafin ranar zabe an jefa shi Akwa Ibom. Wannan kuma an jefa shi mai diguri wancan an jefa shi Patakwal wannan kuma an jefa shi Sokoto haka ya bi ya chanza su. Jama'a kun fahimci wannan da kyau? A karkashin wannan jama'ar Zaria dake waye da wadanda wannan sako zai je gare su
[Segment 2/3 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
Dalilin da yasa aka canza shugaban hukumar 'yan sanda na Zaria da Kewayi Alhaji Kabiru Ibrahim shine dan ya tsayawa gaskiya. Kuma duk wanda yake Zaria nan daga mako uku zuwa yanzu kowa yasan cewa abubuwan da 'yan sanda suka saba yi na rashin gaskiya da magun magun da ake amfani da su babu shakka sun samu kyakkyawar shaida a wannan karan. Toh a karkashin wannan muna yi mishi addu'a na farko Allah ya saka mishi da alkhairi.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
Mu kuma da aka yi wa wannan asara da wannan jamhuri Allah madaukakin sarki yasa wanda aka aiko mana ya zama na garine koma yafi nagarta fiye da wanda aka dauke.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
Sannan ku kuma 'yan sanda abinda nake ce muku musamman na Zaria da Kewayi Kudus to the Nigerian Police Command Zaria Branch ma'ana alherin Allah ya kai muku. Kunyi kokari kuma ku tsaya akan wannan kokarin shugaban naku wancan yana nan ko kuwa wani ne aka kawo wanda koda aka sunshi ne. Ku tabbatar da cewa ita wannan kasar babu abinda zai gyara ta sai gaskiya da adalci a bisa aikin da kowa Allah ya makala mishi a wuya. Saboda yazo cikin hadisin sahabi Abdullahi dan Umar wanda Al-imam Bukhari da Muslim suka ruwaito shi annabin tsira Muhammad sallallahu alaihi wa sallama yana cewa Kowannen ku kiwo aka sa shi kuma kowa sai an tambaye shi game da kiwon da aka sa shi. A cikin gabar farko ta hadisin sai annabi sallallahu alaihi wa sallama yace Shugaba jagora shugaban kasa gwamna minister a ministry gwamna ko commissioner a ma'aikatar shi ko permanent secretary a parastatal ko wanene za'a mishi tambaya dangane da kiwon da aka bashi matar aure yaron gida malami limami mai wa'azi kowa sai Allah yayi mishi tambaya game da amanar da yayi bashi. Dan haka ku sani jami'an 'yan sanda mu al'ummar Zaria mun yaba muku kuma mun jinjina muku hatta wadanda ake tunanin sun gurbace a wannan lokacin da yawa daga cikin su wannan gurbata ba'a ga ta bayyana ba. Dan haka muna rokon ku don girman Allah ku tsaya akan wannan gaskiyar ku sani da cewa da mu talakawa da ku 'yan sanda idan gaskiya ta tsaya a kasar kowa zai ji dadi. Ba tare da wani yaji ainihin wato an zalunce shi ko ko makamantan haka ba. Sannan jama'ar Zaria muna fatan kowa ya kwantar da hankalin shi kasantuwar wannan shugaban hukumar 'yan sanda na Zaria baya nan mu muna tare da shi da zuciyar mu da ruhin mu da addu'ar mu da gabobin jikin mu sannan kuma muna cigaba da yi mishi addu'a cewa Mutumin da aka dauke shi daga Zaria karamar hukuma aka kai shi Abuja kaga ana sa rai al'amarin ya zama farin goshi kenan ma'ana in Allah yaso gaba dai gaba dai 'yan Arewa. Abinda ake fata shine Abujan nan bazaka dawo ta ba sai ka zama I.G. Dan haka Allah yana tare da mai gaskiya duk inda yake abinda muke cewa kenan dan haka jama'ar musulmi kunji wannan ainihin al'amari yadda ya faru kuma kunji dalilin faruwar shi. Toh menene ya faru a Jami'an hukumar 'yan sanda ta nan ainihin wato lardin Zazzau a A karkashin shugaban su na wannan lokacin ai rinka yin amfani da shi wajen kama matasan mu tare da hukumar jami'an tsaro ta farin kaya wato S.S.S a wannan lokacin ana diban su ainihin ana kai su cibiyar hukumar 'yan sanda ta jihar Kaduna da cibiyar hukumar 'yan sandan farin kaya ta jihar Kaduna. A wannan lokacin aka kama matasa guda goma sha six da ko sha bakwai daga yankin Miciya Cikaji Daurawa Dogon Bauchi ma'ana yankin unguwannin da ni anan aka haife ni. Aka ji a kama su aka dibe su aka zaba su cikin 'yan fashi da makami da muga yan barayi a cikin wani tsurkukn daki aka danna su aka jawo ainihin abinnan karfi aka kulle ma'ana bugla daga cikin su abin mamaki harda lauya Ni na dibi lauyoyi na tafi da muka je muka ce toh mu munzo ne akan yaran mu da 'yan uwan mu da jama'ar mu da aka ce an kama an kawo su office din S.S.S munzo mu binciki menene suka yi. Abinda shugaban hukumar S.S.S a lokacin wakilin shi yace wani Muhammadu Gushi asalin mutumin jihar Borno ne ko Yobe yarshe hakikanin al'amari yaran ku ba laifin komai suka yi ba. An bamu umarni ne mu tsare su saboda zaben da aka yi makon da ya wuce sun bada wahala sun hana ayi abubuwan da ake so toh shine aka ce a tsare su har sai an gama zabe na gaba gaskiyan lamari mu umarnin da aka bamu kenan. Nace toh amma ku kuna yi wa kasa aiki ne koko kuna yi wa jam'iyya kaza da wane da wane aiki yace kasa muke wa aiki amma kuma dole tunda su wane da su wane nan su suke kan mulki wani lokacin ba yadda muka iya muma umarni muke karbi. Muka ce toh shikenan yanzu nan gungun lauyoyi ne muka yo gayya muka taho da su daga nan mu zamu wuce kotu idan ku bazaku kai yaran mu kotu ba saboda kunce basu da laifi toh mu zamu kai maganar kotu kotu ta gayyace ku ta gayyaci yaran mu aje abinci ka menene dalili suka ce a'a kar ayi haka za'a sallame su nan take aka kai mu gansu aka ce za'a fito da su ba'a wuce awa daya ba kuwa aka ainihin fito da su bamu kashe ko taro ba bamu kashe kuma ko kwabo ba wannan shine hakikanin abinda ya faru a A wannan lokacin Dr. Ahmad Dogarawa Malam Ahmad Dogarawa layin gida na daya da shi. Naje nayi wa'azi a Miciya na dawo sha biyun dare ya gaji da jira na yana son gani na yaji labarin wai a lokacin an bada dokar cewa ni kaina azo a kama ni da daddare ayi Kaduna dani. Meyasa a lokacin fa nace ne a zabi Namadi Sambo shine gwamna nace baza'a zabi Sha'aban ba nace kuma Amina baza'a zabe ta ba Abinda muka fadi kenan kaje ka samu kasid din sunan shi Masuniya in baka taba jin shi ba iya abinda muka fadi kenan. Toh a wannan lokacin shi shugaban hukumar 'yan sanda ni da shi yake gaya min ga Malam Musa Minshawi muka je muka zauna a kofar gidan shi wata rana da wata munasaba ta kama yace a wannan lokacin nima an bada dokar akan a kama ni. Amma gani suka in an kama ni menene zai biyo baya. Dan haka suka hakura ni ko a wannan lokaci abinda na gaya wa dan aiken Malam Ahmad Dogarawa da ya zaunar da shi cewa da nazo ya gaya min kada in kwana a gida nace a'a ainihin za'a yi a duniya ba inda zan kwana sai a gida na amma fa matsalar in ka matso kusa da gida na duk kiamar da ta tashi akan ka kai ka ja. Iya katta kenan iya katta kenan zan shiga gida na in kulle da bismillah kamar yadda hadisin bai hakiyace tsaf in kulle in zama na lafiya duk abinda yayi motsi zan kau da shi. Kuma ka'ida ta kenan daddare ne da rana ne da safe ne mutum ne dabba aljani ko shaidani ne zan ja maka haka ne ko ba haka ba haka al'amarin yake saboda haka na shiga na kwana gida na lafiya kalau babu abinda ya faru ashe shi shugaban hukumar 'yan sandan ne lokacin ya gaya musu hadarin da ke tattare da wannan lokacin toh a wannan lokacin ma abinda ya gaya mana karara ita wannan 'yar majalisa Amina itace tace wai azo a kama ni. Shi ya fada da kan shi gashi dani da Malam Musa Minshawi sai Malam Musa ma lokacin da yake bai saba mu'amala da su ba har yana mamaki haka al'amarin mutanen nan yake nace wuca nan ma an wuca nan fiye da nan. Saboda haka jama'ar musulmi kunji abinda ya faru toh abinda suka yi wadannan mutanen a 'yan jam'iyyar PDP su Amina Talhatu abinda suka yi a wannan lokacin na asa a kama mutane shine wannan shugaban hukumar 'yan sanda Alhaji Kabiru Ibrahim yace bazai ba. Shine suka yi mai sharri cewa a cire shi oho dai ta Allah ba taku ba ta Allah ba taku ba ta Allah ba taku ba duk allon ka daga was ta Allah ba taku ba Allah ya fiku ba'a kama kowa ba kuma baza'a kama kowa ba tare da cewa a irin wannan boye boyen da ake boye min magana sai yau naji an kama wani ya rokanin mata ta sai da ya kwana goma sha bakwai a Kaduna. Kuskure ne ku boye mini lokacin da mu muke matasa mu sharbo ta game da siyasa da wa'azi duk abinda ya faru muna zuwa mu gaya wa Malam Abubakar Gumi. Ku kuma yanzu wai kuna ganin kun nuna dan kun haddace Tabara ko kun haddace Bakara ko kun haddace Anan wannan ba wannan bane wannan siyasa ce ta duniya ba a littafi take ba ba karatu bane wannan wannan tsabar gogewa ce da yawan mu'amala yake sa in an bullo ka zaka yi ma kasan ta inda zaka bullo saboda haka boye mini da suka yi sai da yaron nan ya kwana goma sha bakwai a Kaduna yana tsare. Kuma duk su wadannan din ne toh jama'a ranar talata da ta gabata ko Laraba mataimakin shugaban kasa Akitag na ma Disambo yazo Kaduna kuma ya aiko naje mun zauna. Matsalar itace Zaria da sabon gari sun rikice wacce irin gudun mawa ni zan iya bayarwa nace lokaci ya kure domin wancan lokacin da muka yi mishi campaign nawa ya bamu ba ko kwabo zuwa ya roke mu babu hasali bamu san shi ba hasali bamu taba ganin shi ba sai sau daya amma muka ce shine namu ashe ba kiyayya ce tsakanin mu da shi ba ashe mu 'yan sabon gari da 'yan Zaria ma'ana zage zage bakin shi muke ba amma mai ya faru hakikanin abinda ya faru lokaci ya kure. A yanzu ya zama ranar Laraba ko ranar talata kwana biyu ko kwana uku za'a fara zabe ace wacce irin gudun mawa zamu yi. Yayi kuka da cewa malaman Izala na sabon gari da na ainihin Zaria da marigayi Malam Abubakar Gumi su suka je suka zauna da shi amma sun zo sun juya baya sun zo sun yi kaza sun yi kaza sun yi kaza oho dai mutuwar sarki a baki na ba amma wata magana ce ta kai nake so in kawo zuwa gaban nan daga ciki nace ranka ya dade abubuwan da ke goga muku bakin jini idan nace ku ina nufin ku 'yan siyasa baki dayan ku sannan kuma mu baki daya da muka yarda cewa a jam'iyyar PDP muke toh sai fa kuyi hakuri mu sai munyi halin namu ina fata an gane abinda ke goga mana bakin jini mu PDP shine mai na daya rashin cika alkawari in munyi alkawari bama cikawa wannan siffar mu ce duk PDP yasan haka ko ya fadi gaskiya ko ba ya fadi gaskiya ba na biyu tsayar da 'yan takarar da jama'a basa so sakamakon haka akai abinda ba'a taba yi ba a tarihin siyasar Nigeria a sabon garin Zaria gida daya gado daya matashin kai daya aka zabi miji da mata sune 'yan takara. Aina muka taba jin haka miji shike takarar majalisan Abuja mata ita take takarar majalisan Kaduna a ina aka taba yin haka sannan wacce nagarta da siffofi ne na nagarta har ya kai ya zama su kadai ne suka cancanta a gida daya a daki daya tsakani da Allah dole ne mutanen sabon garin Zaria su kar ku manta ina bada wannan amsa gare shi ne amsan cewa me yasa Zaria da sabon gari suka rikice meyasa baza su rikice ba tsakani da Allah kowa da kani aka ce kowa da kanwa ace su za'a fitar 'yan takara meyasa baza'a samu matsala ba anyi wa mutanen sabon garin Zaria adalci ba'a yi musu adalci ba ni dan sabon garin Zaria ne dan menene duk sabon garin Zaria baza'a nemo wadanda suka cancanta azo ayi taro a nemi menene mutanen sabon garin zai dace da su yadda in anzo an ajiye akwati baza'a samu adawa ba amma duk shekara sai a tsaya da wanda basa so kuma sai ace dan mai suke adawa mutanen sabon garin ba ja kuna bane mutane ne masu ra'ayi da 'yancin kan su in anyi abinda ya dace suyi in ba'a yi ba suyi abinda ya dace iya katta kenan dan haka dalili na biyu dake janyo wa jam'iyyar bakin jini shine tsayar da 'yan takarar da ba sune jama'a suke so ba. Na rantse da Allah hatta a kololuwar a PDP bana inda an tsayar wa da jama'a dan takarar da suke so da Buhari da C.P sun shi bakin jini zasu yi saboda pasto ne na dama da Buhari amma tun daga kololuwar sai ba'a yi abinda ya dace ba aka zuwa ka dauko tsarin mulki na jam'iyya aka ce tsarin mulki ya hukunta ga abinda za'a yi a lokacin da ake so Obasanjo ya hau aka ce mai aka ce akwai dan haka akwai bin bangare dan haka bangaren South West ne toh in sun gama fa sai North zasu yi toh shikenan North sun karba North suna cikin yi sun mutu sai a bar su su karasa sai aka ki sai aka ce wannan dokar yanzu ba doka bace da aka zo za'a yi aiki sai aka ce ba doka bace saboda an raina hankalin mu mu bamu da lauyoyi mu bamu yi karatun low ba bamu san constitutional low ba bamu da shikenan sai aka watsar da maganar sai aka dauko wanda hatta a yankin shi bashi da karbuwa bashi da farin jini aka zo aka sa shi. Wannan ina sharhi ne kar ku manta akan dalili na biyu dake ja wa jam'iyyar bakin jini shine mai shine dasawa mutane 'yan takarar da basa so kowa zai yarda dani in nace a yanzu jam'iyyar da tafi kowace karfi da nagarta a jihar Kano itace PDP ashe ba PDP ce tayi bakin jini ba asali 'yan takara ne yanzu mutanen Kano sunfi sha'awar su zabi Kwankwaso fiye da kowa tsakani da Allah haka ne ko ba haka ba ashe da idon mutane ya rufe ba'a san PDP ba yadda za'a zabi PDP a Kano amma yanzu 'yan majalisan tarayya nawa ta samu 'yan majalisan senat nawa ta samu ta samu tayi riba har tafi kowace a karkashin wannan yana tabbatar da kenan duk wani dan PDP member ne shi ko shugaba dan takara ne shi ko mai ku je kuyi nazari daga cikin dalilan gogawa jam'iyyar bakin jini shine dibo 'yan takarar da ba su jama'a suke so ba a dasa musu dan haka sai jama'a su karkata ga wata jam'iyyar a bana da ace tun daga zabe na kasa na kololuwa har na gwamnoni har na ko ina anbi ra'ayin jama'ar gari shine meyasa baza'a dawo ana jama'ar gari ne zasu fitar da dan takara tun daga karkashin kasa ba meyasa ya zama jam'iyya kaza jama'ar gari ke son shi jam'iyya kaza ma jama'ar gari ke son shi jam'iyya kaza sai kazo kaga kuri'u nan dari bakwai nan dari bakwai da biyu saboda kowanne jama'a na so kuma kowanne ta fadi ga jama'a daidai ne amma ka duba irin wannan rata ace kuri'u hudu nan kuma suna da dari shida da sabain haba jama'a ko a lahira wuta za'a je wallahi Allah ko a lahira ne in wannan ya faru wuta za'a ina fata an gane a karkashin wannan dalili na biyu kenan da na kawo dalili na uku shine amfani da masu ainihin mulki a karkashin wasu jam'iyyu suke yi ta hanyar muzgunawa talakawa da sauran 'yan takara da jama'ar gari ta hanyar amfani da wasu lalatattun jami'an tsaro wadannan abubuwan guda uku sune dalilan da suka janyo wa jama'a suka ainihin daukin mun munan bakin jini tsakanin sabon garin Zaria da kuma ita Zaria local government din dangane da jam'iyyar PDP shine rashin cika alkawura rashin cika alkawura tsayar da 'yan takarar da ba'a so amfani da gwamnati wajen muzgunawa duk wanda baya ainihin tare da su anan ne sai na gaya wa nace a wannan lokacin da kazo mana muka zauna da kai a maganar takarar munce zamu zabe ka kuma zamu ce a zabe ka amma 'yar majalisa da aka saka mace bazamu zabe ta ba ka roke mu arziki muka ce a'a muna da tsaurin ra'ayi ga duk abinda ya saba addinin mu da dan haka mace ta fito takara gwamna ne shugaban kasa ne majalisa ne kai mace koda takarar zama shugabar gidan mijin ta tayi sama da mijin ta bai halatta a zabe ta ba. Duk su daina muku wani tawili na cewa in ya kasanche mace wakilci ne zata iya zuwa tayi duk wanda yayi wannan fatawar zindiki ne. Mace ba inda ya halatta a dora ta shugabanci koda shugabanci na commissioner na ko ministry ta bai halatta ba haramun ne a dauki mace a bata kuma haramun ne in an bata ta karba kuma haramun ne ayi mata mu baya'a akan haka bai
[Segment 3/3 | 00:40:00–end]
[Speaker seg3-spk:0]
bai halatta ba. bai halatta ba, komin affairs baza a bata ba. ya ya wajaba duk wani mai imani da hankali ya san wannan saboda hadisin annabi sahihin hadisi garandan gangariya daga sahabi Abu Bakrata a cikin duk mutanen da suka sa mace itace ke shugabancin al'amarin su pau pau pau har abada baza su kai ga nasara ba. idan kun kafa makarantar yan mata WTC kusa ta ta zama principal bakuyi laifi ba, idan kun kafa aji na yan mata kusa ta ta karantar bakuyi laifi ba, amma a dauko mace ace itace commissioner kaza bai halatta ba balle ta zama yan majalisa balle chairman dan haka jam'iyyar PDP tayi zalunci kuma ya saba ma addinin mu da al'adar mu cewa wai dole ne a baiwa mata kaso wai hujjar su da suke kawowa wai South Africa su 50% ake ba mata, South Africa ma guzawa ne. mu musulmi ne yaushe zaku dauko dokar da ta zama ga kuzo ku dora ta ga wannan akwai rashin tunani da rashin amfani da diplomasiya ta duniya da kuma rashin lura da yanayi al'adu tunanin mutane duk abinda yayi yiwu a Inugu zai yiwu a cikin Kano? kaje kayi kwatar jakai a cikin Kano ka rinka yanka jaki saboda akwai inyamurai masu cin jakai kaga yadda zaku kare da kanawa. amma ba da kwata a abakaleke ba ta jakai saboda haka babu shakka wadannan sune dalilan a karkashin haka mun taso da zimmar cewa babu shakka mu dai baza mu iya yin komai game da wannan ba. iya katta kenan dan haka jama'a sun riga sun daukarwa kansu shawara mu kuma muna tare da jama'ar mu dari bisa dari abinda muka ga cewa kuskure ne ko da gyara to zamu cewa jama'a kaza kuskure ne ko kuma da gyara, na biyu muna wannan tafiyar mune muna cewa jama'a to ba girin girin ba tayi mai yan takarar da kuka koma kuna zaba a CPC kun san su kun san irin dabi'un su sun zasu rike muku amana din to kada fa kuzo kuna cewa wannan wata salan magana ce ta Larabawa yayin da wani balarabe kullum akai mutuwa sai ya bi dare sai ya zare ainihin likafani daga ainihin cikin kabarin sai ya mayar da gawar sai ya rufe ta. ana nan wannan mai sata likafani sai ya mutu da ya mutu sai wani ya gaje shi shi wannan da ya gaje shi in ya kwakulo gawa ya cire likafanin sai ya bar gawar a nan waje idan gari ya waye aka ga ainihin gawa a waje sai ace oh mai sata kabarin nan na farko Allah ya ji kanshi shi in ya sata zai maida gawar wannan ko kaga shi yanzu sabon yayi bama ya maida gawar to muna ji muku tsoro ku talakawa kar kuzo kuna cewa gwamma wane da wane haka kanawa suka yi suka ce basa san kwankwaso kwankwaso kwassalin alin ya fita ya bar su sai kuma suka dawo suna cewa gwamma kwankwasa da shekarau muka ce kwaji dai da shi kanawa yanzu kuma suka dawo suka ce shekaran zasu za ayi kwankwasan zasu zaba haka ne ko ba haka ba dan haka mu bama goyon bayan kowa sai wanda gaskiya ta tabbata ta tare da shi cewa da muke mu PDP ne wannan raha ce da bakano ne ya samu zage zagi yayi wasa da su, Bahadeje ya samu Bakatsine yayi wasa da su, Bayarabe ne ya samu ainihin Bazan fare ko Basakkwace suyi wasa haka ne ko ba haka ba iya katta kenan ba wata jam'iyya da muke ciki muna fada muku gaskiyar lamari duk inda gaskiya ta kenan muke goyon baya to jama'ar musulmi mu dai kunji ainihin matsawar mu wannan kuma shine bayani dangane da ziyarar yan siyasa wasu sukai mana wasu mukai musu muna nan a haka sai gashi ma mataimaki ko dan takarar gwamna na ainihin jam'iyyar CPC shi ma ya kawo ziyara makarantar tamu fa ta cika da masu ziyarar yan siyasa sai dai kuma bakin mu bai yi yauki ba ko menene ya cancanta mu fada sai da muka fada muka ce to shi kanshi dan takarar jam'iyyar na CPC din tsakanin shi da Allah me yasa bai zo ziyarar mu ba tun tuni sai da lokaci ya kure dan yaga cewa bana ruwan alkausara ya sauka a kansu mu kuma dayar al'abiyabi ne ya sauka akan mu na PDP maana ko yazo ko bai zo ba ko ance ko ba'ace ba talakawa idon su ya rufe nan zasu yi nace mishi to ba girin girin ba dan mu dai bamu sanka ba bamu san dabi'un ka ba bamu san kaza ba Allah yasa kada ka ba jama'ar da suka tsaya maka kunya mun fadi wannan mun nanata mun shiga mun fita mun shiga mun fita kuma ya alkawari yace bazai baku kunya ba ku talakawan jahar Kaduna indai shi kuka kadawa ainihin kuri'a yana tafiya suma namu da suka ji labari sai suka bugo waya suka ce shima malam ya kowo yana nan zuwa nace Albani mai jama'a kenan ina fata an gane Albani mai jama'a Albani na kowa eh ina fata an gane Allah madaukakin sarki ya taimaka jama'ar musulmi kunji wannan daga karshe babu shakka muna addu'a ta musamman ga dukkan jami'an tsaro na kasa musamman wadanda ke yankin Zaria din nan amma sama da su zamu fara addu'a ta musamman ga shi ainihin IGI wato shugaban yan sanda na kasa gaba daya shi Hafiz Ringim babu shakka ya fadi zai rike amana kuma ga dukkanin alamu yana kokartawa to al'amarin sai an taya da addu'a dan haka Hafiz Ringim mune maka addu'a kamar sunan naka Allah madaukakin sarki ya tsare ka daga dukkan rigingimun marasa gaskiya daga karshe addu'a ta musamman ga ainihin shi wannan shugaban yan sanda na yankin lardin nan namu na Zazzau Alhaji Kabiru Ibrahim wanda akai wa transfer dan ya tsaya akan gaskiya muna ce mishi ranka ya dade kayi hakuri mai gaskiya na tare da Allah a duk inda yake muna fatan tafiyar nan ta zama itace alkhairi mu kuma Allah madaukakin sarki ya sauya mana da wanda zai tsaya ya kula da amanar da Allah madaukakin sarki ya danka a hannun shi sannan kananan jami'an yan sanda na ainihin wato kasa wadanda suke nan Zaria baki daya mune muku addu'a Allah madaukakin sarki ya saka muku da alkhairi amma fa sai kun kara jurewa domin yanzu za'a shiga yakin Badar sannan a taho yakin Uhudu sannan a taho saboda haka lallai akwai aiki babu shakka sai kun dage za'a raba kudi za'ayi muku muzurai za'ayi kaza za'ayi muku kaza amma duk ku daure kasar mu ta gyaru in kasar ta gyaru shine abinda ainihin zai sa kowa ya samu abinda yake bukata a bisa halaliyar shi dan haka jami'an hukumar yan sanda mune muku ainihin addu'a ta musamman hakanan sojoji sojoji ma wannan kifawa sunyi bazata su ake amfani da su suna yawo da bulalai suna tapkar jama'a amma a karan nan ya zama sam sojoji sunyi bada hadin kai to lallai jami'an tsaro na hukumar sojoji koma mun jinjina muku ko mune muku fatan alheri da fatan Allah madaukakin sarki ya karfafe ku akan ku tsaya da gaskiya dan kasa ta gyaru hakanan jami'an tsaro na ainihin farin kaya SSS suma mune musu addu'a ta musamman domin su kansu sai sun bada hadin kai akeyin da dama daga cikin rashin gaskiyar to gaskiya saboda Allah suma sun jajirce babu shakka har ta kaima jami'an hukumar tsaro na SSS jama'a yanzu sun bada wasu layoyin waya maana layuka na waya wadanda in ta rikice ko daga ina ne zaka buga musu waya kace musu ga abinda yake faruwa wuri kaza wuri kaza kuma zakayi magana da Abuja ne can gaba daya din guringum kuma da ka buga wayar wayoyi suka bayar wajan guda bakwai da zaran ka buga zaka ji wani ya dauka kuma duk abinda ka fada za'a rubuta nan take zaka ga sun fara kokarin daukar mataki a kai in ko haka bata yiwu ba daga baya zaka ga anzo an dauki mataki a kai tare da cewa al'amuran su a boye suke yi wasu abubuwan ko sun dauki matakin baza ka sani ba Allah madaukakin sarki ya taimaka dan haka mune muku addu'o'i na musamman baki daya muna cewa Allah madaukakin sarki ya taimake mu gaba daya Allah madaukakin sarki ya gyara Najeriya duk wanda yake nufin zaluntar Najeriya ko wanene shi kada Allah madaukakin sarki ya taimake shi wanda duk ke nufin ya gyara kasan nan da al'ummar kasan nan Allah ya taimaka mishi sannan ku kuma jama'a ku dangwala kuri'a da sunan Allah da lura ba dan komai ba domin wannan kuri'ar ta kai da itace yanzu ake so ayi amfani da ikon Allah wajan makomar addinin ka da siyasar ka ta gaba da rayuwar ka da karatun ka da na yayan ka da zuwan ka sallar juma'a da ta idi da sallar jama'a da zuwan ka aikin hajji ta hanyar ake so ayi amfani dangane da matar ka a asibiti ko kuma duk abinda ya shafi ainihin wato al'amuran rayuwa na saukin ta ko kuma tsananin ta a karkashin wannan muna addu'a ta musamman Allah madaukakin sarki ya taimaki al'ummar kasar mu yadda aka shiga al'amarin nan lafiya Allah madaukakin sarki yasa a fita lafiya addu'a ta musamman ga professor Attahiru Jega Basakkwacen gaskiya Allah madaukakin sarki ya taimake shi akan tsaye da gaskiyar da dukkan wanda ya zauna jami'ar Bayero daga shekara ashirin zuwa kusan shekara biyu da ta gabata yasan wannan bawan Allah da kokari da kuma kwazo akan ya za'ayi a tsayawa gaskiya yayi shugaban ainihin malamai na jami'a yazo yayi shugaban hukumar ma'aikata yazo kuma karshe yayi shugabanci na ita jami'ar ainihin wato Bayero din da ke Kano muna rokon Allah madaukakin sarki Allah ya taimake shi sai dai abinda muke cewa ya kalli dama da hagun shi su wanene a dama da hagun shi sannan ya tsaya yayi nazari menene ake kaiwa menene ake komowa sannan yayi nazari wacce hanya ya tattali baiwa yan Najeriya amsa game da table guda da aka kama ta da ballot paper an riga an danna kuri'ar zaben da za'ayi nan da jibi muna fatan Allah madaukakin sarki ya taimake ka ya kai Jega Allah madaukakin sarki ya iya maka game da wannan harka daga karshe talakawa kar ku gaji kar ku gaza ma'aikatan gwamnati wadanda ke nesa duk mako ka dawo saka kuri'a kar ka damu ana son ayi amfani da wannan kuri'a ne a fiye da yadda kake tunanin ta a baya ba taba yin siyasa irin ta ba na ba siyasa ce wadda wasu sun dauke ta maana in bayin haka ba sai dai a mutu ko su su mutu ko su kashe amma basu yarda a rayu gaba daya ba sai dai in za'a rayu su suna aluja a karkashin wannan talakawa dan girman Allah a daure ranar asabar mai zuwa kowa ya fito ka kada kuri'ar ka inda ka gamsu da cewa nan ne ka yadda nan ne kuma za'ayi maka adalci duk wanda ya kawo kudi ya baka ka karba annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama ya hana ka kallafa ranka amma duk wanda ya kawo kudi ya baka ko ba musulmi bane ka karba dan haka dayawa kafirai sunyi wa annabi kyauta ta matan bayi an bashi mariya da kanwar ta sirina an kawo jaki Ufair an bashi an kawo taguwa kasuwa an bashi an kawo tsabar kudi an bashi an kawo suturu an bashi wanene ya bashi shine sarkin kasar Masar wanda yake Kristana mai suna Muqauqis kuma ya karba hadisi ya tabbata annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama ya hana ka ka kallafa ranka akan abinda ba'a baka ba amma abinda aka baka kuma in yazo maka ka karba hadisi ne sahihi Muslim ya ruwaito shi dan haka in sun kawo kudi sun baka ka karba kar ka ki karbe amma su kudin kar su chanza maka ra'ayi kar su chanza maka alkibla dodoru do da zasu yi maka da Qur'ani mai gafaka izu sittin sai ka fara tunanin su da suka rantse da Qur'ani izu sittin suka ci biliyoyi rantsuwar ta kama su balle kai da akai maka rantsuwa ta ikrahi wannan rantsuwa a wurin Imam Malik yace ta banza ce bata yi ba haka Imam na Malik ya bayar malikiya yace rantsuwar duk da akai maka ka rantse da Allah ko ka rantse da alkur'ani akan a sauya maka wani ra'ayi ko da ka fada ka rantse na rantse da na rantse da alkur'anin nan izu sittin ko saka sukai kayi alwala duk wannan sunan ta ainihin wato rantsuwa ta tilas idan kazo danna kuri'a dama ina kayi wa azama zaka danna danna inda kayi wa azama dan haka jama'a kamar yadda muka bada shawara kuje ku saka kuri'a in kun saka kuri'a lallai ne ku tsare wadanda suke cewa kar a tsare din nan dan me za'a ce ko baza a tsare ba da an tabbatar da cewa kuri'ar nan yadda littattafan ayyukan mu na lahira suke lafiya lau zasu je ba tare da ba tare da an gurba ta su ba da haka kuri'un nan zasu je in kowa ya saka sai ya koma ya kwanta dan haka sam baza a yadda ba ko a nan Zaria karfe biyu na dare bayan an gama tattara dukkanin akwatinan zabe sai ga wata mota tazo da cike da wasu akwatina mutane suka ce basu yarda ta shigo ba me ya kawo ta karfe biyu na dare bayan sha daya na dare an gama hada duk akwatinan an gama rubuta duk abinda za'a rubuta an kwanta ana bacci ana jiran gari ya waye a sanar da yan jaridu da samarin gari karfe biyu na dare sai ga wata mota kenan ashe wannan a kasa a tsare a saka a raka a kirga a jira a fada wajibi ne mutane suyi dan haka ku bi in aka tafi ba fada ba zage ba ashar ba ihu in aka je ku bar su su shiga kuyi zaman ku amma duk wata magun magun jama'ar su nuna cewa basu yarda ba wannan kuri'ar tafi kudin ka da ke banki mutunci saboda haka jama'a mu abinda muke cewa kenan daga karshe ko muna cewa Allah madaukakin sarki ya zaba wa Najeriya abinda yafi game da addinin ta game da siyasar ta game da tattalin ta sannan mu musulmi Allah ya tsare mu daga abinda muke jin tsoro kuma Allah ya zaba mana abinda zai kwantar mana da hankali amma fa ba girin girin ba ta mai kuma mu sani da cewa da sassafe ake kama fara al'ummar musulmi bayan wannan zabe ya wuce wajibi ne ku tashi ku fara tsara menene agenda ku ta kar ku jira wadannan tsofafi kuna jiran menene zasu yi ina zasu dosa yaya akayi wadannan gaba daya suna barin abun sai ya rage saura wata uku sannan suzo su ce ayanzu babu sauran irin wannan a tashi sata izin daga gawa dan haka dole ne ku tashi ku shirya ma al'amarin daga karshe abinda muke cewa duk wanda yayi imani da Allah da ranar lahira dan girman Allah ya tsaya akan abinda jama'a sukai dangane da zabe matukar kai musulmi ne dan sanda ne kai ko soja ne jami'i ne na hukumar AINEC mai mulki ne ko wanda ke kokarin ya shigo mulki ne wajibi ne kowa ya tsaya yayi nazari sannan ga nasiha ta ta musamman ga dangi na yan sabon gari yan muciya da cikaji da babban titi da dogon Bauchi da daurawa kudin nan da ake siyan wiwi ana zuwa ana baku tsakani da Allah wadanda ke baku wiwi a cikin ku akwai kannan su a cikin su akwai yayan ku a cikin ku akwai yayan su babu kunsan ina yayan su suke karatu yanzu yayan wasu suna Ingila wasu suna Australia wasu suna Dubai wasu kuma sun tura yayayen su yanzu haka suje suyi umara saboda ko da zata rikice me yasa ake amfani da ku dan haka duk wani wanda za'a bashi kudi akan yaje ya tada zaune tsaye ko a bashi makami ace yaje duk wanda ya gaya mai bakan magana ya datse shi shi wanda ya baka makamin ka fara datsa mishi domin shi ya fara gaya maka bakan magana bakan magana ta kai matuka yace maka kaje ka datsuwan nan saboda shi ina yaran da aka sa suka je suka daddatsuwan su a sabon gari suna can yanzu alkali ya kulle su wata kaza taran nawa ce naira dubu goma sha biyar amma wadanda suka sa su sun i zuwa su karbo su dan haka kai da ake tattalan wiwi ana baka akan kaje kayi rashin gaskiya kasha kan ka ya bugu ka shigo cikin muciya ka zagi yayayen ka ka zagi kakannin ka ka tsine wa limaman ka da malaman ka saboda an baka nawa an baka naira dubu biyu amma da yake kwaya ta buga idon ka sai kana ganin dubu biyun nan zata share maka hawayen duniya da lahira abinda za'a ce daga waccen kwayar da suka baka ta tunda ta sake ka sun sake dawowa sun baka wani abu basu sake dawowa ba saboda haka matasa kuyi a hankali kar wanda ya sake akai amfani da shi wajan a cimma wata mummunar bukata kuyi fito na fito wajan tsayar da gaskiya bawai fito na fito akan a murde gaskiya ba jama'ar musulmi da wannan nake cewa wannan ainihin wato cassette nawa mai suna rigiji gabji ya kare kuma ina fatan a dan farashi da wadancan jeren giyar kasu suwa guda biyu da suka gabata ba dan komai ba dan su fita akan MP3 guda daya da kuma DVD guda daya da al'amuran da mai yiwuwar suka iya yiwuwar su biyo baya da wannan nake cewaAnnotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani. In an bugi jaki... Habaa shehi!!!? Rigiji gabji. Daarul Hadeethis Salafiyyah, 2011. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15861.
Zaria, M. A. A. (2011, 3 avril). In an bugi jaki... Habaa shehi!!!? Rigiji gabji [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15861
Zaria, Muhammad Auwal Albani. In an bugi jaki... Habaa shehi!!!? Rigiji gabji. Daarul Hadeethis Salafiyyah, 2011. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15861.
Télécharger
Visualisations
Chargement des visualisations…


