audio-visual document · Daarul Hadeethis Salafiyyah Cite
Goron Gaiyyata
- Type
- Enregistrement vidéo
- Creator
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Publisher
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- Description
- en Sheikh M.A.A. Albani warned politicians and the rich to stop taking everything into their homes.
- ha Sheikh M.A.A. Albani ya yi gargadi da janhankali ga yan siyasa da mai kudi kan su daina kai masa komai gidansa don baya bukata amma shi yana da shi.
- Extent
- 82 minutes
- Medium
- DVD
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifier
- iwac-video-0000045
- content
-
============================================================
[Part 1]
============================================================
[Segment 1/4 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker unknown]
Za ka gan ka je Sokoto sai ka je an ce dan Dan To saboda haka wasu suka sha alwashin in sarkin musulmi ya ce 29 ga Shaban za su ce karya ne 30 ne, in ya ce 30 za su ce karya ne 29. Wasu sun riga sun gama yanke shawara musamman a Sokoto kuma suka ce Don haka sarkin musulmi da ya ce ba a ga wata ba wasu karya ne An gani. Ita kanta wannan fatawar dimokuradiyya ce da tasu din da da ta abin na A musulunci Hakika abin da sarkin musulmi ya mana mu musulmin arewacin Najeriya ya goyi bayan Bai kyauta mana ba. Ya ci amanar mu ya kamata yayi kabbara ne mu ma mu mu amsa. To amma sai aka yi wata irin sallah a arewacin Najeriya ma mu ne ke kabbara sarkin musulmin kuma liman ya ki amsawa. To wannan ya kawo sabani sai dai kuma wannan fa Bai kai a ce sarkin musulmi Ya bada shaidar an ga wata a ce ba za a karba ba gaskiya. Tsakani da Allah Amma abin da ya san bai kyauta ba Ko karamin musulmi ba sarkin musulmi ba bai halatta ya goyi bayan Balle sarkin musulmi to ka ga inda kuskure ya faru. Don haka akwai bambanci tsakanin abin da yayi da Idan mas'alar ganin wata musulmin Najeriya suna ganin akwai son zuciya To kuma wannan wani abu ne daban. To amma ni Abin da na gamsu da shi tsakani da Allah Wata magana ce da naRead the full text — 12 614 more words Collapse the full text
dade ina fadi fiye da shekara 15 a cikin wasu kasusuwa da nayi ta magana akan mas'alar ganin wata Cewa in ma A Najeriya a kafa wata hukuma mai karfi dangane da abin da ya shafi ganin wata To wannan hukuma in tana aikin ta to ba ruwan mu da ko ina a duniya. Saudiya sun gani basu gani ba ba ruwan mu da su. Amma na ce in har zamu ci gaba da zama a karazibe Kamar yadda ake To babu alherin mu ci gaba da dogaro da ganin watan mu sai mu koma in Saudiya sun ce sun gani mu ce mun gani, in basu gani ba mu ma ba a gani ba. Indai zamu ci gaba na sha fadin wannan maganar. To hakikanin al'amari abin ni da na fahimta Sarkin musulmi da kanshi ya fahimci cewa Muslimin Najeriya a karkashin shugabancin shi Sun gagara su iya samar da irin wannan tsari. Domin na san wani lokaci da muka yi wani kasaitaccen bincike dangane da mas'alar ganin wata Muka bi kewayan arewacin Najeriyan nan muka yi sampling muka dibo wurare da aka ce an ga wata Wasu wuraren mu gane karya ne, na sha fada muku wannan je mu an ga wata a kauye kaza sai mu je kauyen su kuma sai su ce karya ne su ma a rediyo suka je an ce an gani a kauyen su. Don haka su ma basu dauka a ranar da aka ce an gani a garin su ba don su ma karya ne rediyo ne suka je ya fadi. Na biyu muka tafi fadar sarkin musulmi tun a wancan lokaci Muka bincika nan ma sai muka samu su wadanda aka ajiye a wancan lokacin don wannan bahasin namu ya wuce shekara goma. Basau dauki abin da muhimmanci ba Kawai sun bar al'amarin karazibe ne. Idan aka ce an gani kawai shikenan har ma wani muna magana da shi yake cewa za ku wahalar da kan ku ne Ba abin da za mu canza mu Ku yanzu saboda ganin watan ne har kun je Gombe Kun je Maiduguri kun je kaza mu muna nan ba wani abun an bugo wata an ga wata mu fada mai martaba an gani in ba a gani ba kawai ba a gani ba. Ma'ana basu kimanta wannan aikin namu da muke ba a lokacin. Muka sake dawowa A fadar garin nan muka yi binciken ita kuma sai muka gane Galibin wadanda ake ajiyewa a matsayin su ne za su zauna a gindin wayar tarho tun ana landline A matsayin in an bugo an ce an ga wata su rubuta su je su gayawa sarkin garin nan Su din wannan aikin da aka sa su Sai su kauce sai su samu irin samarin nan masu yawon banza kawai a fada wanda neman abin yi yake sai a zaunar da shi gindin wayar tarho. In an bugo waya daga ina Daga Madarkaci to mun ga wata sai ya ce to shikenan Madarkaci ko sai ya rubuta kawai. Ba wata tambaya ba wani abu kawai ya dan gama secondary ne ko ma bai gama ba dai ba yayi da aikin yana zaman a fada. To kun ga irin wannan karaziban Na fadi a wancan lokaci na ce in ba majalissar sarkin Kano ba a wancan lokacin na fadi na ce babu majalissar da muka je muka samu suna tsaurarawa Game da mas'alar ganin wata. To sai na ce indai har haka za a ci gaba da zama karazibe To gaskiya babu ma'ana mu dogara da mas'alar ganin watan mu domin abin ya zama karazibe ne kawai. Da mu ci gaba da yi karaziben gwam mu gyara in gyaran ba zai yiwu ba to kawai sai mu watsar da al'amarin mu kawai mu koma in Saudiyan sun ce sun gani Kawai mu ma mu dauka in basu gani ba shikenan. To a gaskiya abin da na fahimta a yanzu shine shi sarkin musulmi Muhammadu Sa'ada Ya fahimci cewa samar da structure wato samar da wata hukuma mai cin gashin kanta wanda zata karfafa akan wannan aikin Gaskiya yana da wahala. Amma kuma ba abu ne mai sauki ya fito ya fadi ba. Tunda in ya fadi haka kamar shine ya nuna gazawar kenan. Don haka a pakaice daga bara sai ni na fara fahimtar haka. Shi yasa kuka ga bara azumi 30 muka yi. Wanda a karkashin gaskiya saboda Allah rabon da ayi azumi 30 a Najeriya rasmiyan wa hukumiyan a hukumance An fi shekara 30 in ba bara ba. Don haka wasu dayawa suka yi tawaye. Wasu ma tunda aka haife su a kasar nan wadanda basu wuce shekara 25 30 din ba basu taba yin azumi Guda 30 ba. To wannan ya samar da matsala sosai. To bana ma gashi Shaban ya cika 30 Sannan aka fara azumi yau. To hakika ni kaina an bugo mun waya daga kasar Jega Ta jihar Kebbi Su kuma suka bamu tabbacin wasu 'yan uwa Daga ainihin karamar hukumar Kalgo sun bugo musu cewa Da idanuwan su sun ga wata. Yanzu to mutumin da da idon shi ya ga wata Amma yazo ya fadi Al'umma suka ki amtuwa. Ko shi da wasu 'yan tsiraru suka amtu ko ya halatta musu su dauki Azumi ko kuma suyi sallar idi ko suyi layya ko suyi Arafah To gaskiyan lamari a fatawa ingantacciya ta musulunci bai halatta ba. Saboda wadannan ibadoji guda hudu azumi daukar azumi Da sauke azumi shine karamar sallah Da yin babban sallah wato layya Da hawan Arafah ibadoji ne wadanda hadisi sahihi cikin Abu Dauda da Tirmizi da Ibn Maja suka bayyana cewa Ibadoji ne na gaba daya. In ba gaba daya ba to na al'umma mafi yawa hadisin shine Annabi ya ce azumi shine ranar da kuke yin azumi. Karamar sallah itace ranar da kuke karamar sallah Babban sallah itace ranar da kuke layya Arafah itace ranar da kuke hawan Arafah. Babban malamin da ya fara sharhin sunan a Abu Dauda a duniya shine A cikin littafin shi Yace Wannan hadisin Yana nufin inda mafi yawancin jama'a suka taru game da yadda da daukar azumi to nan kaima ake neman ka kayi. To idan kuka duba a jiya Ranar Lahadi ba shakka akwai musulmi dayawa Wadanda suka ga wata shekaran jiya kuma suka dauki azumi a jiya. Amma fa yawan su Bai kai ko rabin yawan wadanda basu yi ba. To a tsari na sunna To abin da ya fi shine yanzu kai kar ka dauki azumin Sai ka bari ka dauka tare da Mafi yawancin mutane. Ina fata an gane. Saboda haka gaskiya 'yan uwa da suka dauki azumi a jiya Ba zamu ce musu ko sunyi bidi'a ko sunyi son zuciya ba don ba mai musu wannan mugun zaton. Amma kuskure ne. Malamai suka ce koda kai da kanka ka gani amma ka fada sai aka ki amtuwa da a dauki azumin ba dan an karyata ka ba. Don ba ce musu aka yi kunyi karya ba cewa aka yi to mun yadda kun gani Amma mu dai mun gamsu cewa sai gobe ne za a fara azumi. To matukar ita kuma wannan cewar mun gamsu sai gobe za mu fara azumi ba magana ce da tazo daga son zuciya ba. Ita ma magana ce wadda natsuwa ce ta kawo haka. To gaskiya abin da ya dace shine a hadu tare da mafi yawancin jama'a don haka Ni kaina wallahi Na amintu da wadanda suka bugo mun waya suka ce sun ga wata da idon su Matan su sun gani da idon su. Ko kadan kuma bani karyata su Amma kuma saboda gamsuwar da aiki da wannan hadisi da fassara da malamai suka yi mai cewa azumi shine ranar da mafi yawancin jama'a suke daukar azumi. To gaskiya sai na gamsu akan a bari sai yau ne ya zama ranar daya ga azumi. Abin da yasa jama'a sun ta yin waya jama'a sun ta turo da sakonni suna neman Hakika me ya dace To jama'a tunda gashi wadannan maganganun da nake fadi ana daukan su a kalla a cassette Sai a yada su a matsayin ni dai maukifi na kenan Akan hakikanin abin da ni na gamsu Al'ummar musulmi su bari Har zuwa litinin din nan su dauki azumi shine ya fi dacewa. Wannan shine abin da na gamsu. Amma abin da nake fata idan akwai kuskure a cikin wannan abin Allah madaukakin sarki Ya fadakar da wani dan uwa yazo ya gamsar da mu amma madogaran mu kenan wannan hadisi. Shi yasa za ku ga Kasar Saudi Arabia Za ka ga su da kansu fa sun taho da lissafi kaza kaza kaza amma in aka zo Arafah Sai su ce ranar kaza ce Arafah Shikenan sai mu hakura. Domin ba za ka je da kai da almajiran ka ko da kai da mutanen kungiyar ka ko da kai da mutanen darikar ka ku tsaya a filin Arafah ba. Mutanen da suka fi kowa sabani da dukkan musulmi a duniya game da Arafah su ne 'yan Shi'a. Amma basu taba yadda sun hau Arafah wata rana musulmi sun hau Arafah rana Amma fa in sun je Arafar ka ga dai na daya ba za su yi sallah tare da musulmi ba. Ba kuma za su bar musulmi su yi sallar su lafiya ba don za su hada lasifi ko kine ma su karfin tsiya Su yi ta wakoki su yi ta ihu su yi ta Allah ya isa Sai sun rikita kowa a Arafan kai kadai kana sallah wani lokacin sai ka rasa wace sura kake saboda suna ta hayaniya za su sa katon katun lasifi koki Wanda bara har inaiwa wasu bayani basu fahimta ba. Suna son su bi wannan hayaniya ta 'yan Shi'a ina ce musu wadancan 'yan siyasa ba addini suka zo yi ba. Ba a fara sallah Arafah ba. Wasu suka kauce suka je suka yi sai can kuma sai suka ji an tada sallah Arafah wannan nan sun gama koramniyar da hayaniya sun gaji don ranar Arafah dole ka gaji. Fili ne dajin Allah kawai ba bishiya ba wani abu tsandauri ne sai 'yan tsirarin bishiyoyi da aka shuka ga rana sai ka ji kamar rana ake zubar da rana a wurin. Don haka duk hayaniyar da kayi Sai ka ga cikin 'yan mintuna sai ka ji mutum yayi lip sai ka same shi yana bacci a cikin yashi. Ina fata an gane. To saboda abu ne na wuni guda ba za ka iya wuni guda kana hayaniya ba dole in kai zuwa 12 rana karfe daya ka gaji sai ka yi shiru. Ina fata an gane. Saboda haka da suka yi shiru aka zo aka fara sallah Arafah sai na ce wa mutane to kun ga ga inda ake sallah Arafah nan yanzu. Sai kuma sadadan wasu suna sakewa tare da mu. Amma 'yan Shi'a basu taba hawan Arafah yau a ce kuma gashi a duk da haka za su yadda ran da aka tafi Arafar Rannan za su je sai dai kuma komi nasu za su yi daban ne. To A kashin gaskiya Arafah rana daya ce Ah idi rana daya ce babba. Shi yasa mun taba yin wani taro ina jin 1995 ko 96 a nan masallacin Juma'a na Mariga Alhaji Haruna Danja Allah ya gafarta mishi Muka kwana akan cewa hakikanin al'amari ga abin da mutane suka gamsu da shi saboda mas'alar yin karamar sallah yin babban sallah kaza kaza kaza. Aka nada wasu wakilai suka je suka samu sarkin Zazzau suka gayawa mishi to amma Gaskiya daga baya ni sai na ga to ai mu da muka taru muka hadu akan wannan ra'ayin Bamu kai ko daya bisa 100 mutanen Zariya ba. Don haka sai na sauka daga waccan fatawar tamu sai na dawo wannan ta cewa Ranar babban sallah itace ranar da mafi yawancin mutane suke yin Ainihin Abin nan suke yin a babban sallah. Wadannan maganganun duk da na fadi ba sai ka tafi da nisa ba suna nan Musamman tare da Da sauran littattafai irin su Fathul Bari da sauran su. Don haka jama'a muyi hakuri Idan sarkin musulmi ya sake dawowa ya ce azumi din ba a ga wata ba ko kuma ba a yi recommending ranar kaza ita ce kaza ba. To za ka ga yanzu mutane sun riga sun karkatu Akan me akan maganar sarkin musulmin kuma da ne ba a yadda ba. Yanzu kuma an riga an ginu Saboda haka 'yan tsirarin da za su ce basu yadda ba sai ka ga kadan ne. Wadanda suka yadda kuma su suke da yawa to saboda mu kiyaye alfarmar wannan sunna abin da ya fi dacewa shine mu tafi tare da mafi yawancin jama'a. Wannan kamar yadda na ce shine abin da na gamsu da shi kuma kaji wasu 'yan kadan cikin littattafai da na fadi. Magana ta biyu Rigiji gabji Jama'a akwai wani kasaitaccen wa'azi Wanda in sha Allahu ta'ala za mu gayyata kuma a wannan masallaci Ta yiu za mu iya yin shi a dare daya Ta yiu za mu iya yin shi a dare biyu Ko dare uku ko makamantan haka da gwargwadon yadda muka ga dacewar abu. Sanannan abu ne ga kowa A Najeriya Gara sai ka ji an ce 'yan sanda sun kama Albani To wannan masalar ba matsala ce yanzu koyayya ba matsala ce sananniya ga kowa ba wai a Najeriya ba Ba ga musulmi ba Matsala ce sananniya a dukkanin duniya. To abin da kuma mutane suke tsammani Shine daga fitowar Albani Zai yi jawabi akan me ya faru. Albani yana da technicality yana da ka'idoji na gabatar da wa'azi ko lacca. Albani na duba lokaci Yanayi ba dan komai ba saboda yau Shekara 31 kenan Albani na karantar da addinin musulunci har yau ba wani karatu da Albani ya taba ya dawo ya ce ya janye shi. To wannan ko ya faru ne saboda kafin shi Albanin ya gabatar sai ya gama gamsuwa Da hujjoji da maganganun da zai fadi don haka duk abin da ya fadi duk ja yadda za ayi Ba dai ya dawo ya Janye wannan wa'azin ba sai in an kawo dalilan da Suka rusa wadanda ya gabatar to kuma a cikin shekaru 31 nan Alhamdulillah Ni Albani Babu wani wa'azi da nayi na kammala shi Wani yazo ya same ni ya kawo munu wasu hujjoji wadanda Har suka sa ni din nan in gamsu in ce bari in janye wa'azin. Kamar yadda na ce Idan abin ya shafi mas'ala ce wadda sai an je wuri kaza sai anyi kaza sai anyi kaza Da kaina nake zuwa bana aikawa Don inje in gane wa ido na In tattauna da wadanda zan tattauna don ya zama duk abin da zan fadi komai tsawon shekaru ba zan janye abin ba don sai da na tabbatar da cewa haka abin yake. Ma'ana A karkashin wannan Wadanda suke tunanin daga fitowar ta ne zan yi wa'azi Ba wannan tsarin ne nake bi ba saboda dalili biyu dalilin farko shine Mutumin da aka kama shi aka tsare shi kwanaki 43 zuwa 45. Idan har yana da fasaha basira bai kamata daga fitowar ya fara magana ba domin An yanke ga daga duniya gaba daya Ba ka san me ake ba Kamar yadda fiye da shekara 1000 wani dan kurkuku yake waka yake cewa Wani dan kurkuku Wato wani dan kurkuku ne yake cewa mun fita daga duniya Amma fa muna cikin duniyar kuma. Mu dai muna cikin duniya mu ba matattu ba Mu kuma ba masu rai ba. Cewa idan Ma'aikatan kurkuku suka Shiga gari suka dawo sai suka zowurin mu da wata bukata wata rana A jibna sai mu rinka mamaki mu ce wannan daga duniya yazo. Amma mu ma kuma a duniyar muke amma a wuri don haka Dukkan mutumin da yake da basira Idan ya samu kanshi bari ka ji ba wai nan ba Idan na tafi kasar Saudi Arabia na dawo aikin hajji daga dawowa duk abin da ake ciki a Najeriya bana sa baki duk yadda ya zafi Saboda mutumin da ke Saudi Arabia Baya samun bayanai irin wanda yake Najeriya. Saboda ka ga dai a Saudi Arabia Mafi yawancin mutanen Saudi Arabia basa sauraron rediyo. In kuma za su saurari rediyon za ka ga baya wuce FM. Saboda haka mafi yawancin mutumin kasar Saudi Arabia Baya sanin menene ke faruwa a duniya sai a kasar shi kawai. Na biyu Mutumin da ke Saudi Arabia Wata tasha ta talabijin ta tsallako zuwa kasar shi Gwamnatin kasar tana kayyadewa don haka hatta receiver Kullum za ka ga suna zuwa shagunan da ake sayar da receiver. Don akwai receiver da ba a yadda a sayar da ita ba don kar a kalli wasu tashoshi. Tashoshin internet kuma
[Segment 2/4 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
ba ko ina ne zaka buga ka iya kama ko ina a duniya ba suna da wata wato wata katangar karfe wanda da kazo zaka shiga wani fage sai ka ga ance maka sunan sunan katangar kenan ce maka birnin sarki Abdulaziz bai bari ka shiga ba to saboda haka ko aikin hajji naje in na dawo na samu wannan wata hayaniya sai kuji nayi shuru tukunna saboda yanzu ne na dawo duniya irin ta duniya can duniya ce irin ta Saudi Arabia to balle irin wannan rayuwar wadda gaba daya baka san me yake faruwa ba saboda haka irin yadda mutane sukai tunani hatta yan jaridu shine daga fitowa a zo a same ni inyi magana sai nace a'a ai nima dan jarida ne me zan fadi to zan fadi maganar da gobe zan zo kuma in ce jama'a abunda na fada ba haka bane ban taba yin haka ba ba ina cewa ina da girman kan da in na gane nayi kuskure bazan abun nan ba a'a amma tun farko bazan yadda inyi magana ba sai na tabbatar ina da kyakkyawar masaniya a kanta ku duba duk hayaniyar da akai ta boko haram har yau babu kalma kwaya daya a cikin maganganun da na fadi wadda har yau na janye ta me yasa saboda abu ne sai da na taka naje sai da na zauna da wane sai da nayi kaza sai da nayi kaza sai da nayi kaza abunda na fada a wurin nan shekara biyu da ta gata a kansu sai mako biyu da ya wuce wani ne guda na addinin musulunci ya gano haka duk inda ya zauna hira sai ya fada har nima yana bani labari sai nace amma wannan ai mun fada tun mu shekara biyu da ya wuce wannan abun nace mishi kwarai da gaske tuni mun riga mun wuce wannan daya kenan ma'ana dalili na farko kenan shine a wannan yanayin ku dinnan kun fini sanin keke da keken wasu abubuwan da suke faruwa dan ni sai dan abunda naji a rediyo wanda bai kai ya kawo ba ko abunda na samu na karanta a jarida dalili na farko kenan dalili na biyu idan har zanyi magana sai ka tsaya kayi tunani ni dinnan albani da in na tashi zanyi magana akan wani zanci awa uku awa hudu ina magana to kana tunanin a kaina ne kuma zanci awa nawa kenan ai ya kamata kai nazari ko ba haka bane saboda Allah lacar da nayi a nan waye kashe malam Jafar awa nawa ce awa hudu da rabi lacar da nayi a demokradiyya nan awa tara lacar da nayi a nan Karambana awa hudu da rabi to anya sai a kaina ne ni din kuma kake tunanin za'a yi minti kaza a sai ya zama a lokacin din yanayin da bai dace ba saboda akwai akwai dokar ta baci duk inda muka zo muka fara wa'azi daga karfe takwas ne zamu iya fara wa'azi idan muka kai karfe goma da rabi to sha daya ce dokar kafin rabin awa wani ya tafi gida za'a kama shi to kaga bai dace ba to amma yanzu doka ta dage kanta ko kuma an dage ta wannan ma akwai fassara da in jawabi ya kama zamu yi insha Allahu ta'ala so hakika ne al'amari ba wata matsala ce ta boyo ba kuma mai dauke da kwandon gishiri tace a shiga wasa ayi kurme a kogi balle mai kwandon yalo saboda haka hakika ne abunda yake faruwa zanyi wa'azi insha Allahu ta'ala wanda mataki na farko na wa'azin yana dauke da cikkakkiyar godiya ga Allah madaukakin sarki akan baiwar da yayi mana gaba dayan mu mu al'ummar musulmi shine da Allah ya saka mana wannan abu a matsayin jarabawa sai bai wulakanta mu yasa mun manta da Allah ba sai bamu tafi neman taimako wurin kowa ba sai muka sake komawa wurin Allah shine ka karanta sharhin wannan ayar a cikin littafin bana tunanin akwai wani littafin tafsiri da zaka ga sharhin wannan ayar irin babu bani tunanin wani littafin tafsiri yayi mata wannan fassarar a karkashin wannan mu isar da godiyar mu ga Allah kamar yadda kuma muka isar a baya sa'annan kuma mu isar da godiyar mu ga jama'ar al'ummar musulmi baki dayansu da dukkanin kungiyoyin su da darikun su da dukkanin nau'in su mazan su da mata da jinsun su malamai limamai malaman islamiya malaman allo makarantun soro da kowa labarai na alkhairi sun zo mana game da irin addu'o'i da mutane suka rinka yin na alkhairi gaba daya muna yi musu kuma zamu ci gaba da musu addu'a Allah ya saka musu da alkhairi domin ita matsalar da ta faru madadin yadda su wadanda sukai engineering dinta suka tsara ta a yadda suka so ta bayyana sai bata bayyana hakan ba sai kowane musulmi yaji cewa matsalar ta shafe shi domin ta shafe addinin musulunci ne to saboda haka sai kowa yake ganin cewa wannan matsalar fa ba da albani ake ba wannan matsalar fa ba wai da yan salafiyya ake ba wannan matsalar da addinin musulunci ake kai kuma kowaye kai kana ganin kai musulmi ne kai kuma kowane ne kai kana jin kai mabiyin addinin musulunci ne to in ko an taba shi to dalili ne akan cewa ka fahimci cewa ba wane bane to wannan ma wata baiwa ce da Allah yayi mana mu al'ummar musulmi dan haka wajibi ne muna isar da godiyar mu ga al'ummar musulmi Allah ya saka muku da alkhairi kuma wannan yasa da izinin Allah ya zama wata ta cewa musulmi su dawo cikin tunanin su kamar yadda muke fadi akan cewa mata wahida abun duk da ya samu guda daya to kowa ya gane cewa ya samu kowa ne anan ne na zauna nake maida martani ga wasu da suke murna a lokacin ance an kama shehu Dahiru Bauchi a Mecca suna ta munna nace ba abun ayi munna bane ana nan su wadannan masu munna sai kuma suma aka kama nasu shehun Dr Abubakar eh Dr abun nan Ahmad Abubakar Gumi sai nace kun gani duk wanda aka fahimci cewa wannan wani icon ne wannan wani alama ne wannan wani abu ne na musulunci dan haka kenan yanzu in kai dan izala ka fahimci yan darika akewa kai dan darika ka fahimci yan izala akewa to kowa an kama shehun su to yanzu sai aka taho kan mu mu kuma da bamu ce darikar ba bamu ce izalar ba to kenan kaga koma wane iri ne kai inma kai darikar ne inma izalar ne inma ba ruwanka da ko dayan ne dai koma yaya ne dai to ashe daga nan zaka gane cewa kawai duk wanda ya jingina da addinin musulunci da shi akewa kenan musulunci akewa to mun gode Allah da al'umma suka fahimci haka dan haka mukayi wa jama'a kuma godiya da addu'ar alkhairi sannan na biyu da jama'a suka fahimci cewa wata dama ce aka shirya domin a tsogali jama'a suyi kayar baya azo a hallaka musulmi a karkashe su a rusa musu wuraren ibada su wadannan da za'a turo su samu wannan fa'ida shine tunda dai da kuri'ar mu mun kayar da wane da wance da su wane da su wane to sai kuma a turo azo a karkashe na kashewa su kuma can na sama sai su ce to ba lafiya a turo kudi in aka turo sai su kasabta a tsakanin su ba wani kudin security da aka taba turowa kasa don ga simple tambaya wanda yake kowa zai iya gane wa ko baka taba karatun boko ba tunda kake ka taba ganin an turo yan patrol da abincin su suna ci ko kuma lokacin cin abinci yayi su tafi hotel su ci abinci to amma duk sanda aka turo yan patrol za'a ware miliyoyin kudi sojan dubu arba'in aka tura mai duguri kaje ka tambaya ina ne ake dafa musu abinci an turo su ne an watso su gari kawai dubu arba'in su ci a jikin mutanen mai duguri amma can sama kuma fa mai duguri ance ba lafiya an danno kudi wadannan kudin da aka danno a sama ake kasabta su to haka suka so zariya sai kuma ace an danno sojoji dubu ashirin saboda haka sai an kawo biliyan biyu can suna ci nan kuma suna kashe ku sai aka mayar musu da anniyar su ba wanda yace musu ta tafa a sauke dan haka sai suka koma da bakin ciki akan bakin cikin su na uku duk wanda yayi zalunci baya so a fada ba kuma yaso a sirrin shi ya tono sai yan jaridu su kuma suka zage suna ta fadin abunda ake idan kai mai karatu ne ka karanta a jarida idan kai ba mai karatu bane mai saurare ne to gashi nan ance kace a fada haka ne ko ba haka ba dan haka sai ya zama gaba dayan abunda ake ciki kowa ya sani kafin kace wani abu marubuta akan internet su kuma suna ta rubutu duk sun fada wa duniya dan haka sai ya zama matsalar ta tashi daga ta zariya ko ta jihar Kaduna ko ta Nigeria ta koma matsalar duniya to dan haka duk wani azzalumin ta sai kuma ya fara nokewa haka Allah yace kisan kai ne Bani Isra'ila suka yi da suka ga asiri zai tono sai kuma wannan yace a wannan ne wannan yace a wannan ne a wannan yace haka haka suka rinka cewa wannan ya fito yace a wallahi wannan ne wannan ya fito yace wallahi ba ni bane wannan yace a wannan ne har sai da ya zama ni da su yan sandan wannan yace to wallahi mu ba laifin mu bane manyan mu ne su kuma manyan su ce to wallahi daga sama ne ce to saman bakwai tana can tana kallon ku kuma haka mukayi ta yi shine har wani wanda babu haushe bane yace to matsala ance kai dan jarida ne in ka fita zaka yi surutu nace a'a ai fadan ma za'a yi surutu wannan sabo ne ai dama duk wanda zai hada shirgi da ni to ya tabbatar da cewa wallahi tallahi wallahi tallahi ko mala'ika ka ajiye gaba na sai nayi magana abunda nasan ba karya zan fadi ba saboda haka duk abunda ya faru da in ance kace ne to yanzu ni ne zan fada da baki na saboda haka yanzu ba ance kace a'a ni ne gani to wannan lacar har ta tayar da hankalin wasu abunda ya bani mamaki ranar Lahadi sai ga gungun wasu mutane nasun su kuma nasan ko abokan su waye kuma nasan ko waye ya turo su sunzo suna son su tara mun kasa su nuna ni ai babban ne ni ai kaza ne ni ai kaza ne to zaka bai kamata in kula su wane ba yan iska ma da zasu gama abunda zasu gama shekara hudu suzo su lalace da su wane ma da zasu cire kakin ma suzo su abun nan sai musu to haka ne amma daga cikin hujjar da sukai shine ai nan gaba ni ake sa rai irin mu zamu zama irin su Abubakar Gumi kaza kaza kaza kaza an cin su to su kan irin su Abubakar Mamudu Gumi da wahala Allah ya sake maimaita muku irin su a Nigeria i Allah yana aiko mutane annabawa da malamai ne daidai da irin su ina san ku gana haka Bani Isra'ila da suka zama masu kekasasshiyar zuciya sai Allah ya aiko da annabi Musa dan haka ba wai Bani Isra'ila ba har wan shi Haruna annabi Musa duka yake in yayi kuskure shine haka yadda kuke haka Allah yake abun nan lokacin da kuke masu taushin zuciya sai Allah ya baku irin su Abubakar Gumi in kuka yi musu kuskure kuyi kuka suyi kuka suce sun yafe muku to da Allah yasa ko masu busasshiyar zuciya sai ya hada ku da malamai yan zamani wanda ko tabarau mu bazamu sa ba balle mu rage jin kunyar ka idano mu kamar yar baby zamu kalle ka mu gaya maka magana bama shakkar ka ko kadan saboda haka maganar ana sa ran irin mu ne zamu zama irin su Abubakar Gumi irin su Abubakar Gumi in kun zama irin mutanen zamanin su Abubakar Gumi masu mutunta malamai baku dauki malamai a matsayin yan iska da zaku iya musu sharri kowane iri ba Allah zai baku irin su Abubakar Gumi amma in kun zama mutanen da malami bashi da wata daraja sai Allah ya hada ku da malamai yan zamani wadanda ba abunda zaku yi ku gaya musu Allah ko ku ce musu kaddara ko ku ce musu imani a'a irin abunda kuka kama su da shi a karkashin dokar a irin karkashin wannan dokar zasu kama ku da ita saboda haka maganar cewa bai kamata ni abunda akai mini in kai kotu ba saboda ni babban ne banga girman ba inda ni babban ne a lokacin da su wadannan da suka turo ku dan da sun zo suna wani kwana kwana ne nace musu look ni yanzu na wuce yaro ba wata kwana kwana wane da wane ne suka turo ku saboda haka babu wata kwana kwana a lokacin da su da suka turo ku lokacin da kuka ji suna abunda suke yi mini a lokacin me yasa baku ce musu wannan fa babban ne kar kuyi mai haka sai yanzu ne da aka juyo nace kwarya daya muka sha Yahudu ne ya karantar da su karatun boko nima Yahudu ne ya karantar da ni saboda haka irin dokar da suka bi a kanta suka yi min abunda suka yi mini irin ta ce nima na sake dauka na tafi kotu ni ne yanzu bai dace in kai su kotu ba sun zalunce ni amma su sanda zasu kai ni kotu kun gaya musu ko baku gaya musu ba suka ce sun gaya musu basu ji ba eh to nima bazan ji ba yo ni ne wawa baka jin abunda Kalarawi yace ne yana tarihin annabi Nuhu yace a kama annabi Nuhu ayi mishi duka ya suma a jefar da shi a bola da asuba in ya farfado sai yace Kalarawi yace annabi Nuhu kenan yace amma ni kawai wani kato ya jibge ni wai in zo ina kuka ance Allah ya shiryar da yace ni shirye-shiryen ne tuni kana duka na nima dukan ka zanyi yace nima shirya nake nema to gaskiyar lamari wannan itace jama'a lokaci ya wuce da zaku samu malamai irin su Abubakar Gumi gaskiya eh kunyi kuskure dama Bahaushe yace ba rabo da gwani ba to an rabu da gwani to yanzu duk sai yan a chaba ku chaba mana muma mu chaba muku iyakar ta kenan ku kai mu kotu mu kai ku kotu ace muku bai kamata ba ku ki ji muma ace mana bai kamata ba mu ki ji iyakar ta kenan kawai karambana ne kawai maganar Zoman bana iyakar cin ta kenan saboda haka wadannan group na farko sun zo ne suna roko na akan ni na kai kara wadanda sukai min abunda sukai mini kuma kara ta shiga sun rasa yadda zasu yi shine suka fara neman azo ayi sulhu har ta kai wai to yanzu inda mutanen nan zasu fito gidan rediyo da jaridu suce sun tuba nace ina ruwa na tuban banza ba abunda ya shafe ni da tuban su ba abunda ya shafe ni da tuban su ni nayi imani ayi aiki da doka nace ai ba fada ake ba fada ne na masu hankali sun zarge ni sun kai ni kotu nima na zarge su na kai su kotu kun ce musu su janye a'a sai ni ne zan janye to wannan sune gayya ta farko dama sai da na gaya musu nace zaku ji ku a cassette duk wanda yayi magana da ni wallahi ko a ban daki ne wata rana sai kaji a cassette lokaci ne kawai bai ba ba wani abu rufin asiri yau me za'a rufe ba abunda za'a rufe yo ba sharrin rufe wane ba in yau ka rufe ran da suka zo suka bankado wani abu sai ya zama kai ka zama wawa me ban fada wa mutane anan ba ba shine ya taimaka asirin su ya ta tonuwa ba ace dama yace kaza dama yace kaza har kamun ni ina sanin da kamun ina takardar kamun sati biyu kafin ma a kama mu ko sati uku har na farfada duk daliban darul hadisi sun sani har list din ina nan da shi ba abunda bamu sani ba mu saboda haka wannan sune kashi na farko kashi na biyu su kuma wannan wa'azin ne suka ji labari zo da haka akai marmaza aka kira wasu suka je Abuja aka zauna da su dan Allah azo a roki malam zai yi wani wa'azi don girman Allah ya saurara nace kowa ta ta fito daga kabari tace kada inyi wannan wa'azin wallahi sai nayi dan shi wa'azin biyayya ce ga Allah tana sama da biyayya ga uwa a duk duniya ko ba wanda yake da girman hakki a kaina bayan Allah da manzon shi sai ita amma wannan abun ba an taba ni bane an taba addinin Allah ne shiyasa yin shuru game da wannan matsalar cin amanar addinin Allah ce kuma zanyi wa'azi abun duk da insha Allahu ta'ala in nayi wa'azin abun duk da zai biyo baya ya dade bai biyo baya ba me kuma ya rage ne ba abunda ya rage ba abunda ya rage ba abunda ya rage kuma taken wa'azin nan na sanya musu na sanya mishi fashin kwai sunan wa'azin kenan kawai fashin kwai kar kace fasa kwai ba fasa kwai ba baka san Hausa ba sai nazo zanyi larabun Hausan fashin kwai haka zaka ce fashin kwai ba fasa kwai ba fashin kwai Hausa ce sai nazo zanyi bayanin me ake nufi da fashin kwai me banbancin fashin kwai da fasa kwai fashin kwai ne sai nazo za'a yi wa'azi insha Allahu to dan haka wannan wa'azin da zamu yi shi zamu yi shi akan wannan kadiyyar ne kuma zamu buga takarda a aika da goron gayyata ko ina ko gidan rediyo zasu sanar ko gidan rediyo bazasu sanar ba mu wannan ba matsalar mu bace ba babban abu
[Segment 3/4 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
shine. Takardan muna so in Allah ya so, daga jibi zata fara bayyana. Ko ina a yada ta, a manna ta a ko ina, kuma ba boyayyen abu bane kada wani yazo yana neman takardan wai ana jin tsoron a bashi. Ko mala'ika ne na mutuwa yazo ku bashi takardan. Yo meye kuma? Ba wani abu kuma. Ba wani abu. Inna ma rana ce a zuwa yanzu bamu san wacce rana za'ayi ba, sai mun zauna tukunna. To shiyasa wadannan hikimomin guda biyu su suka sa muka saurara. Na farko dole ne kasan menene ake ciki tukunna. Kayi kayi Ka bincika ka shiga ka fita, ka hada da wasu abubuwa ka fitar. Sannan na biyu shine mun dubi lokaci. In muka ce zamu yi wa'azin a makonni biyu da suka wuce, babu lokaci. Domin in mun sa wa'azin kamar yadda nace karfe takwas, dole karfe goma a tashi awa biyu, to awa biyu tayi mana kadan. A kalla mu samu awa uku. To kuma kar kaji shakkar sanar da wannan wa'azin ko ina, kuma kowa yazo mutane da aljanu da mala'iku na sama da na kasa da na ko na ina ne ka gayyato su. Ba wani abu. Kadai zamu bayyana wa mutane meye ya faru. Yaya ya faru? Kuma su wanene? Shine matsalar kawai. To sa'annan kuma sai mu amsa wasu shubuhohi da suka taso dasu wanda ko yau na kira wasu 'yan jaridu mun yi magana. Za'a saka a gidan radiyon Najeriya Kaduna don suma abun ya taba su. Meye abun ya taba su? Suma a kan wannan matsalar hadda daga cikin su shima sai da aka kama shi. Wato wai zalunci mutanen nan suke yi. Suke son wai a rufe baki ayi shiru. Na'am. Zaku iya sa ma'aikatan gidan radiyon ku da jaridun ku suyi shiru don suna cin albashin ku. Amma ni ban taba cin albashin uban kowa ba tunda uwa ta ta haife ni har yanzu ban taba aikin gwamnati ba. Ban taba aikin kamfani ba. Ni me zanyi da kai na ne? To irin shubuhohin da kuma suka zo suna yadawa wai sai suka zo suna cewa wai sun bani kudi ne. To wannan matsalar itace zamu zo kuma mu tinkari kowa da wannan kalubalen. Wanda duk yasan ya bada kudi yana duniyan nan ne ko ya tafi lahira ya dawo duniya yazo yayi jawabi. Ya dawo fada. Wa aka ba kudin? Waye ya bada kudin? A ina aka bada kudin? Nawa ne aka bayar? In hannu da hannu ne a gaban wa? Da wa da wa? Wa aka aiko in aiko wa akayi? In account ne a wani account ne aka sa? Duk bankin dake Najeriya kap za'a iya fitar da statement of account din shi. Sai a fadi bankin ana fadi kawai shikenan sai a je a fito da statement of account din. Wanda yasa kudin randa yasa kudin nawa yasa kudin? In hannu da hannu ne ba dai sarkin aljanu ya ba ba. Dole wani mutum ne ya ba wani mutum koda guda daya ne, to wanene wannan mutumin daya? To duk wadannan sai mun fito dasu. To a kan wannan wa'azin ne fa kuma shekaranjiya sai gasu wadannan wakilai su kuma namiji da mace. Anzo ana roko na don girman Allah kada ayi wa'azin nan nace a'a duk duniya ba wanda ya isa ya hana ayi wa'azin nan don ni ba yaron uban kowa bane. Ni ba kungiyar uwar kowa nake ba. Zaman kaina nake yi. Wannan kuma yana daga cikin fa'idar zaman kaina din. Don haka ba wanda ya isa ya hana kamar wa'azin wa ya kashe Malam Ja'afar. Wani irin kutukutu ne basu yi ba kar ayi. To menene yasa kake jin tsoron a bayyana? Ni yanzu bana tsoron inzo in bayyana in fadi wane in fadi wane in bada lambar wayar wane in kawo takardu kaza in nuna in kawo kalubale in jefa a kan kaza. Ina shiryar da duk abun da wannan zai dawo ya fadi. Meye yasa kai kake jin tsoro in kana da gaskiya? Ni yanzu ba zuciya ta hawa kes take bani da tsoron kaumi a kan abun. Meye yasa kai kake jin tsoron a zo ayi wa'azin? Kuma tunda kuna ba malaman kudi, malaman da kuke ba kudi ba sai ku shirya su suzo suyi muku yakin maimai suyi raddin abun da zan fada ba tunda ni kadai ne. Su kuma suyo gayya. Ni ni kadai ne ba karkashin kungiyar kowa nake ba ina tsaye da kafa ta ne. Duk wani wanda za'a ce kaza yana da security na kungiyar shi. Da ka taba shi kungiyar shi zata tashi ta yi masifa. Duk wani wanda za'a ce kaza yana da security na darikar shi ko yana da security na fadar shi. Ni ko ni kadai ne bana karkashin wata kungiya bana karkashin wata darika, bana karkashin wata fada, ba wani alhajin birni, ba wani office. In ka ganni ni kadai a motan nan tawa ni kadai ne. Ya kake take ne? To ni abun da ya bani mamaki jama'a wallahi wadannan da suka zo sai suka bani mamaki. Nace yanzu ku wance da wane su suka turo ku akan sunji labarin za'ayi wa'azi eh. Nace to ku kwantar da hankalin ku wa'azi sai anyi. Duk maganar da zamu yi a nan da ita da maganar banza daya ce. Ku cigaba da maganar bazata sa a fasa yin wa'azin ba. Inda ina da wani mai gida a duniya kap da za'a iya zuwa a same shi yayi mun magana bana karkashin wani shege. Ko dan siyasa ne ko sarkin gargajiya ko shugaban kungiya ko shehi ko malami, yadda ka ganni haka nake. Ba abun da ya shafe ni da kai. In kudi kake dasu bani bukata, in mulki kake dashi bani bukata, in mukami kake dashi bani bukata, in karatu kake dashi bani bukata. Abun da Allah ya bani nawa da tu dashi dan kadan din. Kuma na tsaya a kan kafa ta. Amma abun da nayi imani dashi shine kullum ina fade na sha fada wa mutanen kungiyoyi da dariku da 'yan shi'a da sarakunan gargajiya haka. Duk wanda zai harkan shi yaje harkan shi. Nima zanje inyi harka ta ba ruwa na da kai. Amma duk randa ka shiga harka ta to kar kayi tunanin duk duniya kana da wani wanda zai zo ya roke ni cewa kada in magana a kan ka. Domin yadda sallah take ibada a wuri na to fada ma ibada ne.
[Speaker seg3-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg3-spk:0]
Idan na fara ba dai nawa. Su wa yanzu nace har abun ya ishe su nace to billahillazi ni ba'a fara ba ma. Tunda me ba'a fara ba har yanzu shari'o'in ni da suka kai ni har yanzu ba'a yi saboda tsoron su ba'a kai basu kai kotun da ya kamata ta hukunta maganar ba. Sai suka kai kotun da suka san cewa bata da 'yancin ta saurari maganar, sai dai kawai tace aje a kai shi a ajiye shi gidan yari. Amma in sun shirya da dalili me yasa bazasu kai kotun da zata hukunta abun ba? Ni da na tashi kai tawa karar kai tsaye sai na tafi kotun da kai tsaye zata hukunta ta saurara kuma. Aka caje ni sai na biya naira dubu dari biyu da saba'in da biyar. Na kawo kuma cib na biya don a saurare ni. Su kuma me yasa basu kai ba? Su ba gwamnati bane? To kuma yanzu ne zasu taho ta karkashin daki su turo wani ustazu mai dagaggen wando da wata mai hijabi wai kuma a zo wai don Allah wai malam kada yayi wannan wa'azi saboda dama wa'azin ya taba su wane dama abun ya taba su wane da su wane. To kuma yanzu in akayi wa'azin zai kara sa rusa su. Nace Allah yasa in na gama wa'azin su shiga jahannama su tabbata sai nayi wa'azin.
[Speaker seg3-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg3-spk:0]
Gobe ma wani shege ya sake taba Albani.
[Speaker seg3-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg3-spk:0]
Baka ga sarakuna ba tun suka yi shiru, baka ga 'yan shi'a ba tun suka yi shiru, baka ga 'yan darika ba. Duk wanda ya tabo ni sai nayi buji buji dashi don bani da alhakin kowa. Ni ban tashi nayi maka irin yadda kungiya kaza zata ce kaza kaza ba abun da ya shafe ni da kai. Haja ta nake yadawa itace kayan mai gida na. Kur'ani da hadisi kawai. Yauwa in ka shiga harka ta to shikenan. To ka dawo kuma yanzu ai ba'a fara komai ba. Amma wai su har abun ya ishe su. Saboda haka ana ta turowa wai ana son za'ayi sulhu. Nace ai ba'a fara ba tukunna. Duk wannan hayaniya a radiyo akayi. Tunda ake hayaniya kai baka taba jin murya ta ko daya a radiyon ba. Ashe kaga ba dani ake ba ba'a fara dani ba. Yanzu yau 'yan jaridan nan da suka zo zuwa a sabar lahadi sun ce zasu sa, to yanzu ne aka fara tukunna. To amma a kotu kan ba'a fara ba. Tunda har yanzu su basu kai kotun da zata iya sauraran meye suka zo dashi ba. Kaga ashe ba'a fara ba. To amma su fa yanzu har abun ya ishe su. Suna neman za'ayi sulhu don Allah kar ayi wa'azi kar ayi kaza. Nace a'a wa'azi dai masallacin mu ne. Baki kuma baki na ne. Ni kuma ni nawa ne, ni da kaina nawa ne. Ba na kowa bane shikenan. Shikenan matsala ta kare. Matsala ta kare. Saboda haka jama'a kuje tunda ga yau ku fara yada labarin nan za'ayi wa'azin nan ma ba'a sa rana ba. Ba'a sa lokaci ba. Insha Allahu ta'ala za'a sa rana da lokaci amma a cikin ramadan din nan zamu sa rana zamu sa lokaci. Kuma zamu fadi duk abun da ya faru bazamu rage ba bazamu kara ba. Kuma zamu fada wa jama'ar musulmi a yanzu a ina ake? Me ake ciki? Sannan yaushe ne za'a fara abun da za'a fara? Don kamar yadda nace ba'a fa fara ba. To sa'annan kuma duk wadannan maganganun suma zan kawo su in fade su. Meye yasa aka turo wane da wane suna neman sulhu? Ma'ana har an abun ne? Meye yasa har an fara gayyatar to ya kamata malam yazo taro kaza wai ana neman hada kan Arewa. Yo in ba sardauna ne yanzu ya dawo duniya ba zai kira ni taron hada kan Arewa ba? Arewa kada Allah yasa ta hadu. Uwa tace Arewa ban leka ce in ta hadu na zauna lafiya? Ai yanzu sardauna ne kawai ni zai dawo duniya in ya kira ni taron Arewa in ce to to ranka ya dade zan zo. Amma waye Arewa ne? Meye Arewa? Ba irin Arewa kenan ba da sarakunan da malaman da suka suka ci amanar ku suka je suka watsar daku. Su kuma suna can sun zauna lafiya da dangin su. Ko kuma kune 'yan ta'adda in za'ayi passing bill akan terrorism a kan ku za'ayi. Sune 'yan Niger Delta. Amma su a freedom fighters suke. Amma ku kuma fa a 'yan ta'adda kuke. In za'ayi passing bill akan terrorism a kan ku ne su wa zasu yi supporting mutanen ku ne? Saboda haka jama'ar musulmi gaskiya mun gode muku. Da limaman juma'a da malamai da masallatan ko ina munji addu'o'in da akayi. Kuma Allah ya nuna mana karfin addu'ar musulmi. Saboda ko kwana bakwai ba'ayi ba sai ga mutanen da suna ganin sun shirya makirci da sharri sai gasu suna boye kan su. Kowa yana cewa shi ba shi bane. Nace ai ba'ayi komai ba. Karfin addu'a kawai ta rikita su kawai sun rasa yadda zasu yi. Saboda haka wallahi jama'a wannan babban kalubale ne a kan cewa ya koya mana darasi cewa lallai ne al'ummar musulmi duk abun da ya same ku ku fito ku ce zaku yi hayaniya duk ba itace taku ba. Amma kuyi ta gayawa Allah. Al kunutin nan kuyi ta yi da yara da manya da matan aure da limamai da ladanai kowa. Wallahi tallahi na tabbatar har ga Allah a irin yadda na gama ujiza da karama ta addu'ar musulmi a karan nan wallahi da musulmin kasan nan zasu sake haduwa suyi a kan duk wani azzalumi. Wallahi baza'a kai ko ina ba. Duk Allah zai kawar dasu. Saboda mutanen da suka shirya sharri ne sai gashi kowanne yana tona asirin kowanne. Har nuna mana suke a waya ka gani wallahi wane ne. Wallahi ka gani wallahi wallahi kuwa. To ba wani abu bane fa karfin addu'a ne kawai. Karfin addu'a ne. Saboda haka al'ummar musulmi a cikin wannan ramadan nan da muka shiga wallahi mu zage game da karfin addu'a da tawassuli da karatun al'kur'ani ku ga yadda Allah zai mutsu mutsu da duk wani azzalumi. So da haka jama'a mun gode kuma in Allah ya so wadannan jawaban a yau zasu tsaya a matsayin budewar karatun mu na bana duk da bazasu shiga cikin layin kasusuwa ba sai dai su zama masu zaman kan su. A gobe ne zamu cigaba da tafsirin mu insha Allahu ta'ala a wannan wuri. Kamar yadda muka ce kuma muna gayyatar al'ummar musulmi muna yin karatun sira a ainihin makarantar mu Darul Hadis karfe tara na safe zuwa sha daya, hudu da rabi zuwa karfe shida kuma muna yin ainihin a tafsiri na al'kur'ani mai girma insha Allahu ta'ala. Allah madaukakin sarki ya taimaki musulunci da musulmai. Allah ya rusa kafirci da kafirai. Allah ya tabbatar da diga digan mu a kan gaskiya da addinin musulunci. Muna rokon Allah madaukakin sarki Allah ya bamu dukkan alkhairi dake cikin wannan wata na ramadan. Allah ya taimaka. Malam zamu baka dama a tambaya kai kadai don lokacin mu.
[Speaker seg3-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg3-spk:0]
Na'am. Na'am.
[Speaker seg3-spk:1]
Wannan ganin wata yanzu da aka maida shi kaman siyasa. Ya matsayin shi wanda ya san ka da kirki kirki to menene matsayin wannan guda daya?
[Speaker seg3-spk:0]
Na'am. Shine wato eh kamar yadda kake cewa an maida abun ya zama kamar siyasa. Shine in ya tabbata muna ganin sun maida abun ya zama kamar siyasa to shine son zuciya ta shigo. To sai mu zawo mu duba menene amma mafi yawancin al'umma suka dauka. Mafi yawancin al'umma sunyi ta waye ga wannan sanarwar ta wadanda suka saka son zuciya da siyasa eh misali. To shikenan sai mu zama tare da mafi yawancin jama'a. To amma in ya zama mafi yawancin jama'ar nan kan su bai waye game da abun da ni da kai da wane da wane kan su ya waye ba. Ya zama in zamu dauki azumin bazamu wuce mu goma ko talatin ko mu dari ba. To sai ya zama kuma hakika mun saba waccen sunna din. Don haka yanzu ba muna bin son zuciyar wadannan bane. A muna tare da wadannan Wannan shi ne.
[Speaker seg3-spk:1]
Wanda zai ya san game ma da abun kaman siyasa abun da ke rike kenan.
[Speaker seg3-spk:0]
A'a shi wanda ya maida abu ya zan ya maida shi siyasa yana da laifi mana. Ba shine hadisin Bukhari yake cewa Annabi yace nan gaba zaku samu wasu shugabanni wasu limamai su nayi muku limanci. In sunyi daidai to tasu sallar tayi taku ma tayi. Idan sun sanya son zuciya shine son zuciya son zuciya In kun in sun sa son zuciya ku ibadar ku tayi zunubin wannan son zuciyar yana kan su. Saboda haka kun ga a irin wannan halin idan wannan abun da ya faru misali a tsakanin jiya da yau da sauran su ya zama akwai son zuciya to mu dai munyi abun da shari'a tace mana. Don haka ibadar mu tayi insha Allahu. Son zuciyar su kuma da alhakin da muka dauka in akwai alhakin duk yana kan su. Amma a a tsarin sunna shine ana son wajen wadannan ibadoji ku tafi tare da mafi yawancin mutane. Wannan shine jama'a. Idan da yau sallah ce ta azahar misali kaga mutane talatin sunzo zasu yi sallah a azahar ka tabbatar da lokaci bai ba. Bai halatta ka bi su ba. Bai halatta ka bi su ba. Don ita sallah a azahar kowanne masallaci da tasu daban. Amma ibadar azumi an Allah ka ta a kan lokaci guda. Saukewa haka haka nan babban sallah haka a rafa. Saboda haka in akwai son zuciya alhakin son zuciya yana kan su insha Allahu ta'ala. Ni
[Speaker seg3-spk:1]
Wanda ya maida wata fa
[Speaker seg3-spk:0]
Na'am. Eh shin ka maida baki zai yi ko ko shima
[Speaker seg3-spk:1]
A'a shima zai sha ruwa tare da jama'a ayi.
[Speaker seg3-spk:0]
Na'am. Zai sha ruwa tare da jama'a. Wannan itace fatawa al imamu Sufyanu Thawri kamar yadda in an karanta cikin littafin Za'a ganta insha Allah. Ni abun da nake cewa wadannan abubuwan da suke faruwa a kasan nan ko kadan matasa kar ku kar ku kar ku damu. Kuma da ta da hankalin ku ya tashi. Wato alamomi ne na gyara yazo. Alamomi ne na gyara. Baku ji wani tsohon shugaban kasa wanda yayi head of state yazo yayi president yayi kaza yayi kaza yace alamomi ne na juyin juye hali suke faruwa a kasar. Kuma yana fatan in zasu faru shi zai jagorancin yin wannan gwagwarmayar. Wadannan alamomin kar kace a Najeriya kawai duk duniya ne. Je kaga masar me ya faru? Je kaga me yake faruwa a Libya? Me yake faruwa a Syria? Zalunci ne idan yayi yawa. To sai Allah madaukakin sarki sai yayi amfani da wasu sai su tashi sai su karya kashin bayan zalunci. Haka Allah yace Saboda haka ko kadan kar ku damu wallahi. Wallahi izza ce karfi ne musulunci yake samu. Malam Abubakar Gumi Allah ya ji kanshi da daddewa ya dade yana fadin cewa in aka kwashe riki ce aka tafi sai a ga shi yana dariya. Mu nan an an sha yaji ana tashi hankali sai yace a'a ai kuna karatu ne da adda'a kifa kuke da da baza'a yi wannan rikicin ba. Shine da ka fara jin wannan kayan bayan kan mutane ne ya waye akwai jawabi da mukayi hira da BBC tun lokacin da ake wannan hayaniya yana nan na dauka. Abun da nake ce musu a lokacin da muke hira da tashar BBC nace yanzu ba irin da bane. Mutane suna bin labarai suna sanar da duk me ake ciki. Saboda haka ba irin wannan zamanin ne yanzu za'a cigaba da kama karya kuma a ce mutane su zauna lafiya ba. Ba irin wannan zamanin bane. Ta hansar yanzu mutane suna samun su a kwanni. Mutane suna jin labarai suna jin abubuwa. To ba irin wannan zamanin ne kawai zaka je ka kame a office a Kaduna ko a Abuja ko a local government kawai shikenan ka fadi kaza. Kana tunanin kawai da ka fada mutane shikenan zasu yiwu ba irin wannan lokacin bane. Ina karami jama'a a a a a a a a titin NTC Tabako a daidai kofar gidan da ake kira wasu akwai wani ana ce mishi baban Habi. Duk 'yan muciya sun san su. A daidai wannan wurin ina tsaye bana mantawa. Sarki ne yazo zai wuce na lokacin na garin nan. Iyayen mu duk sun fito sunyi kneel down sunyi haka. Duka sun gurfana sun daddaga hannun su har sai da sarki ya wuce. Sannan suka tashi suka abun nan. Mu muna ta dariya me ya faru? Wallahi ikon Allah wata ran na taho daga nan wajen NTC Tabako kuma ina gangarowa muciya sai ga sarkin wannan lokaci shi kuma yazo zai wuce. Dake wannan wurin yara suna cewa karya ne. Nace Allahu Akbar. Ka gama ujiza. A wannan wurin ne kakannin su suka kneel down. Kowa yayi haka sarki zai wuce ana jinjinawa. A wannan wurin kuma wani sarki irin haka yazo zai wuce aka ce karya ne. Shekaranjiya ba'a yi hannu da yawa ba? Ai an dan shiga wani fage. Ina ta buga waya zanyi jiwa
[Segment 4/4 | 01:00:00–end]
[Speaker seg4-spk:0]
sai wani bakano ya bugo shikenan daga karaye me yasa ne yanzu ake raina malamai me yasa ake raina sarakuna me yasa ba'a mutunta su irin yadda ake da sai yace a'a malaman ne ba irin nada ba sarakunan ne ba irin nada ba iyaka amsa kenan iyaka amsa kenan kaji yadda na fadi a farko dinnan kaji yanzu sokoto kaji me yake yawo a sokoto akwai wadanda tun kafin azumi ya tsaya sun sha alwashin duk fatawar da sarkin musulmi yace bazasu bi ba in yace anga wata zasuce karya ne in yace ba'a gani ba zasuce karya ne an gani aina ka taba jin wannan karatun babu shi a fikihu amma mutane sun dauka wa kansu ne kawai ka gani to haka akewa sarakuna haka akewa malaman haka akewa masu mulkin to wadannan abubuwan ko kadan kada wani ranshi ya baci gobe ma in kaji an kama wani malamin ko kadan addu'a zakuyi amma kadai abunda muke nuna wa malaman shine su malaman su san me suke yi kar ya zama an kama ka din kuma aje a same ka baka da gaskiya ka bamu kunya ya zama duk inda za'a kada a raya a kada a raya a kada a raya din sai kuma a dawo ana neman maganar ta lalace sai kuma a dawo ana neman sulhu din haka ya kamata bazaku yi mamaki ba shekara talatin da daya mutum yana wa'azi har kasusuwa da sidina da menene ba abunda basu dibo sun sa ba su da kansu fa sunce sun kama ni ne babu lafi ko kwaya daya kuma basa tuhumar lafi ko kwaya daya ma'ana amma bari aje a tsare ni a tafi neman laifin exactly abunda ya faru kenan inspector general of police hafiz ringim abunda yace kenan Allah ramma bama tuhumar ka da laifin komai da hausa fadi ba da turanci ba bakano ne to wanda ba'a tuhuma da laifin komai kuma an kama shi an tsare shi to kuma an tafi ana ta sauraren kasusuwa an tafi ana ta neman website wai ana neman sai an gano laifin to abunda nake so ka gane mutumin da ya shekarar talatin da daya ranar da aka kaini freezing itace ranar da na cika shekara talatin da daya cub da fara wa'azi a duniya itace ranar sha uku ga watan june 1980 daidai wannan ranar sha uku ga watan june litinin kuma itace ranar da aka kaini freezing din akan an yarda mutumin nan bai da laifi amma aje a tsare shi in yaso aje a nemo laifin aka je a sa kaset a sa cd a sa dvd a sa kaza to abunda muke so kenan kowane malami ya shirya ya zama an neme ka din da laifin baza'a same ka ba amma kaico da an taga step one two shikenan an same ka kuma shikenan dole yanzu kazo kaine zaka tuba kaine zaka bada hakuri daga ran nan kuma sun karya maka da'awa to dan haka kowa ya zama ya shirya kowa ya zama ya shirya shiyasa hatta maganar kudi da suke zamu zo mu fadi wadanda suka ba kudin ai mun fara fade a nan a karatuttukan da mukayi muka ce wadanda aka ba kudin muna jiran su suzo suyi aikin kudin ai mun fadi wannan muka ce muna jiran su suzo suyi aikin kudin muna nan to duk wanda yasan ya bada kudin ya fito shi da kanshi yazo yace mu muka bada kudin kaza kaza kaza kaza kaza in ku baku fada ba muma fadi wadanda kuka ba kudin dan haka sukai shiru baku a mamaki a garin ni kadai ne nayi ta magana ku kawo mana malamai nawa ne sukai wa'azi akan abunda suke kukan anyi musu wa'azin je karka duna ka bincika mutum nawa ne je ka sokoto ka bincika mutum nawa ne to in su bazasu fito da wadanda suka ba kudin ba da wadanda suka bada kudin muma fito da wadanda aka bada kudin kuma mu kawo dalili in su suna jin tsoro ma'ana ku ashe abunda kuka tsara wa kan kuma baku da gaskiya a kanshi shiyasa kuke jin tsoro ni yanzu nan na fito ne na fara maganar kuma har yanzu ma fa banyi taron da nace zanyi ba dan akwai taron yan jaridun duniya ma da nace zanyi har yanzu ba'a fara ba zamu kira cnn bbc aljazeera faransa germany duka suzo ayi da turanci da hausa da larabci da kowane yare da muke ji a fada yo muna tsoron su din zamuyi haka kuma munsan bamu da gaskiyar zamuyi haka to suma sai su fito amma me yasa zaku zo kuna boyewa kowane yanzu yazo yana cewa a'a ni bani bane wannan yazo yana cewa a'a ni bani bane wannan yazo yana cewa wallahi ba ruwana wannan yace billahillazi wannan ya rantse yace ba ruwan shi fa a'a to yanzu ba wanda yayi kenan kuma ga laifi anyi kuma kowa yace ba shi bane to in ku kuna jin tsoro wallahi mu bamu jin tsoro gobe ma
============================================================
[Part 2]
============================================================
[Speaker spk:0]
da irin waɗannan bayanan da nayi a farko farkon karatunmu, shi yasa ire ire wannan lokacin. Gaskiya saboda Allah jama'a, musamman da irin abubuwan da jama'a ku da kanku ne kuka rinka jin ire ire wannan jita jitar. Gaskiya nake so zanyi amfani da wannan cibiya tamu da ake kira In yi wannan sanarwa ta shiga cikin kasusuwa na rediyo da na bidiyo gaba ɗaya. Gaskiya kada wani ɗan siyasa ko ba ɗan siyasa ba ya sake aika mun da wani abu gida, musamman cikin azumin nan. Tunda azumi ya kama, wannan yace zai aika da buhun shinkafa, wannan yace zai aika da buhun gero. Gaskiya na gode. Kuma bani bukata. Amma aje a kai wa masu bukata. Abinda yasa ku kuma jama'a na fasa wannan magana a jama'a bayan duk waɗanda suka aiko nasa a mayar musu. Domin mas'alar yanzu nace na daina rufe ta. Da dama ana kuka dani bani da sirri. To ni kuma a da ne nake gan ina da sirri domin mai yiwa na kan rage. To yanzu gaba ɗaya zan rinka bincikawa saboda duk wani abu da ya faru jama'a su rinka sanin ga ma'anar shi ga fassarar shi. Ba'a bani ba ance an bani, ina kuma ga an bani na karba. To kuma dan Allah menene kamar albashi ace za'a kawo mishi gero buhu guda. Gero buhu guda. In naga dama azumi ya tsaya, zan sha gero a gida na buhu 100 zan kawo. Saboda haka bani bukatar kowa ya sake kawo mini gero ko sukari ko wani abu daban. Bani bukata ku daina. In ma kunene don tsogala to gashi na fito na faɗi. In ma dan Allah ne to Allah ya saka muku da alkhairi. Amma kada wani ɗan siyasa ya sake aiko mini da wani abu, bani bukata. Shi yasa wannan kaset da mukayi gashi nan ana siyarwa jama'a, ni na raɗa mai suna nace goron gayyata. Ma'ana abinda ke cikin kaset ɗin in kaji shi to ya motsa ka ka yo shirin jin abubuwan da zasu biyo baya. Shine shi kaset ɗin wannan goron gayyata ne kawai. Ina fata an gane. Ma'ana so mun taɓi ne. Samfoti ne irin ta yara masu kallon film. Akwai lokaci da za'a zo za'ayi magana. Amma ni na sha faɗa muku, iyaye na kanawa ne. Don haka akwai jinin kananci a jiki na. Ni ba malam zalla bane, yadda kaji ina karatun nan haka nake neman kudi gurjanjan. Gurjanjan haka nake neman kudi. Amma ba inje neman su ta sadaka ko ta zakka ba. Ni ɗan kasuwa ne. Duk wanda yake son haɗa harkar kasuwanci dani sai yazo. Kasuwanci ne irin na gargajiya ina yi. Kasuwanci ne irin na zamani ina yi. To wannan in zakayi ka taimaka mini. Ba wai duniya ba, Allah ya kaimu lahira. Ka hau minbarin Annabi Muhammadu kace ka taimake ni. Na yarda. Kuma akan haka nake. Shi yasa wallahi daga randa nayi wannan maganar har ofis ɗina nasa akaje Abuja aka ɗakko mini wasu takardu. Daga ciki harda takardar rijistar kamfani na na Safwa Technologies. Zan zo dashi a wurin wannan lacca ince duk duniya gashi kamfanin da ni nake dashi kenan kwaya ɗaya dashi nake kasuwanci. Duk wani ɗan siyasa da yasan ya taɓa bani aiki da wannan kamfanin yazo ya faɗi. Gashi in faɗi registration ɗin. Aje a duba CAC ko ko ta kan internet zaka iya dubawa. To ba wani wanda ya bani ko taro. Sunzo sunce waɗannan sunce sun bani miliyan goma. Miliyan goma banza. Billahillazi in na karɓo miliyan goma daga account ɗina ban taɓa kirga ta ba. Idan ne aiki turawa suka biya ni in dollars. Ban taɓa zuwa an canza mini ba. Nazo na kirga ta dan wallahi miliyan goma bata kan kirgar shegiya ba. Ban taɓa kirga ta ba. Miliyan goma me? Wasu kuma sunce miliyan ashirin. Duk waɗannan kudi ne na canji. Na ustazai da suke jin yunwa. Da ka gani nasa riga irin ta shehunnan darika. Ba ustazu bane ni, ɗan kasuwa ne ni. Miliyan goma me? Me akai me akai miliyan goma? Yo ba dan ma kuka ji toro ba, ku da muka jefa muku karan bara ba na muka ce duk ɗan siyasan da zai zo nan yazo amma sai ya ajiye miliyan hamsin a can. Har aka gama akwai wanda yazo? Ba wanda yazo. Ba wanda yazo. So duk wani wanda yake tunanin ya samu mukami ko gwamna ne shi ko minister ne shi ko director ko Pamsec ko MD ko shugaban kasa ko wanene shi in yana son ya samu alfahari na ya taimaka mini yazo sai in faɗa mishi. Shine ya bani aiki da sunan kamfani na. Inyi aiki na ya biya ni to zai iya zuwa ko ina yace ni na taimaka mishi na bashi aiki ya samu yayi kaza. To ina alfahari da wannan wato ina da aikin yi kamar yadda Annabi Dauda ma Annabi Dauda ma yana ci daga aikin hannun shi. Amma kawai in zauna don kaji ina ta karatun hayoyi da hadisai kazo ka kawo mini buhun gero. Gaskiya saboda Allah na gode in dan Allah ne. In kuma dan shegan taka ce to shikenan kayi izgilanci Allah ya mayar maka da izgilancin ka. Amma akwai malamai suna nan suna karantar da karatun al'kur'ani dare da rana. Suna bukata a kawo musu buhun gero. Ba'a kai musu ba. Bara baran nan ko shekara ɗaya da rabi da ta wuce haka wasu masu mukami suma suna gwamnati. Suka ce wai za'a bani trailer guda ta taki. Nace me zanyi da ita? Ni ban taɓa noma ba jama'a, ni a bariki aka haife ni. In ka ganni a gona wani tsautsayi ne Allah kada ya sake nuna mini shi amma ni bana noma, ban taɓa noma ba. Ba cewa nake noma ba kyau ba. Amma akwai malamai da ni nasan ma noma ne. Su ya kamata a ba taki amma ni in ka bani taki baka da lada. Saboda me zanyi dashi? Yanzu haka in naga taki iri kaza da iri kaza bansan wanda ake sawa masara ba, bansan wanda ake sawa kubewa ba. Ban sani ba ba abinda ya haɗa ni da taki. To na kasa gane irin wannan fitina jama'a. Annabi yake cewa Mafi sharrin abinci shine abincin walima wanda za'a ba wanda baya so ko wanda yafi karfin shi a kuma hana wanda yake so. So maganar cewa a ɗauki gero a bani wallahi bazai burge ni ba. Bazai bani sha'awa ba. Zuciya ta da kanta bazata iya godiya ba balle baki na. Domin ba abu ne da nake bukatar shi ba. Amma akwai wasu suna can suna bukata sai a basu. To tsakani da Allah jama'a ba'a bani ba, anyi karya ance an bani shi yasa na jefa wannan kalubale ɗin. Kuma madalla da rediyo Najeriya Kaduna duk da sun ɗan rarrage maganganun da mukayi amma sun ɗan sa a cikin barka da yau wannan kalubalen kuma har yanzu ina jiran wani ya iya fitowa ya duba tsabar idon nan na wanni yace ya bani kudi. Kuma na jefa wannan kalubale ban rage kowa ba a duniya. Ban rage ba. So dan haka dan girman Allah kada wani ɗan siyasa ko dan munyi campaign a nan munce a zaɓe shi a'a ba wanda muka ce a zaɓa muna ra'ayin mu ne kawai muskilanci irin namu ne. In ta juya in tazo sai kuji mun ɗakko Sai mu ɗakko Ba abinda ya shafe mu, abinda muka gamsu akai kawai shi zamuyi shine ma'anar 'yanci ɗin ai. So ya kamata gaskiya saboda Allah in ma abinnan shegan taka ne to don Allah ku daina mini. Ni ma abokin shegan takar kowa bane. Barni inyi harka ta kaima kayi harkar ka. Amma abinci da sauran sadaka da kyauta kuje ku kai wa akwai masu bukata amma kar wanda ya sake zuwa gida na ya kawo mini wani abu. Kar wanda ya sake aiko da wani abu. Idan dan Allah ne in muku addu'a Allah ya saka da alkhairi in kuma shegan taka ce Allah ya mayar muku da shegan takar Iyakarta kenan. Wannan sanarwar naga dacewar inyi ta domin in kara tsare mutunci na. Sannan kuma in kara kwankwasar bakin tsanya. Ya zama ba wanda ya isa ya ce wani abu sai ace a'a yace kaza. In kuma ba ga toro ba tafi kaje ka same shi. Yaka cin magana kenan. Saboda haka nayi amfani da wannan dama ne a bisa ni kaina ban so ace sai na matsu na tursasu zuwa ga in ta irin waɗannan maganganun ba. To amma daga lokacin da mukayi wancan kaset ɗin jama'a kuma shikenan sai gashi wannan ya abinnan wannan ya abinnan wannan ya abinnan. Haka na sake samun labari. Wasu sun sake ɗakko kujerun hajji an kawo wa su malam Musa sahabi nan suma suka ki karɓe. Wato 'yan siyasa kun kuskura fahimtar mu mu da kuke cewa 'yan salafiya. Mu fa ku daina saka mu layin 'yan darika ko 'yan izala ko 'yan tsubbu ku rinka saka mu layin wato mutane ne waɗanda yake kawai waɗanda suka san 'yancin kansu. Shine mu kadai muna goyon bayan mutane ne su kai ga mulki don muna fatan kasar mu zata gyaru ta hanyar su. Kuma su wane muna kin goyon bayan su ne in muka tabbatar cewa an gwada an gwada an gwada ta ki ci ta hanyar su. Saboda haka ku dinnan fa da aka ce a zaɓe ku dama cewa mukayi a zaɓe ku dan a gwada halin ku. So maganar ku sai kujerar hajji ku ba malam Musa sahabi ko buhun gero a ba albani wallahi tallahi kun kuskure mun fi karfin kujerun hajji. Mun fi karfin buhun gero, mun fi karfin duk waɗannan abubuwan kuma ba sune makasudi ba. Mu makasudi abinda muke so ɗinnan shine a samar da wutar lantarki ta wadata. A samar da ruwan pamfo ya wadata. Hanyoyi su wadata. Matasa su samu aikin yi. Abinda ya shafi harkar tsaro a samar da ita. Da ire ire waɗannan harkoki da suka shafi makarantu da harkokin lafiya. In kuka samar da waɗannan abubuwan guda bakwai bakwa bukatar sai kunzo wurin mu neman addu'a. Bakwa bukatar sai kunzo wurin mu neman albarka. Bakwa bukatar sai kunzo wurin mu neman goyon baya. Kar Allah ya sa ma mu sanku za kawai kuji mu nemi muku campaign. Sai mu ce saboda kunyi kunyi. Saboda haka shawarar da nake bayarwa ga waɗanda suka samu mulki ɗinnan kar ku shagaltu da siyan gero kuna ta rabawa mutane. Ku shagaltu da matsalolin da suka dame mu. Ku shagaltu da matsalolin da suka dame mu. Matsalar rashin wuta rashin ruwa rashin aikin yi rashin tsaro harkar ilimi lafiya tituna da makamantansu. Waɗannan abubuwan in kuka shagaltu da su shikenan kana ɗan majalisar dokoki na jiha, kana ɗan majalisar dokoki na tarayya, kana sanata, kana gwamna, kana shugaban kasa waɗannan abubuwan su zama sune zaka zaka damu da su. Bakwa ganin su mutanen South South 'yan Niger Delta yanzu sun daina jin haushin wannan kaboyin nasu. Me yasa? Saboda duk abubuwan da suke matsalolin su yana ta biya ne musu maganin su. Yana ta biya ne musu maganin su. To saboda haka gaskiya saboda Allah ku sani da cewa idan kuka shagaltu da wannan shirman kuna ganin kun ba 'yan darika kujerar hajji kun ba 'yan izala kujerar hajji kun ba 'yan fitiyanu mota kun ba 'yan izala mota a gaji idan zaɓe yazo wannan abun aikin banza ne a wurin mu kamar ka ɓata lokaci ne ka kwana sallar ta tahajjud. Lokacin sallar asuba bazaka tashi kayi sallar asuba ba sai karfe goma na safe. Saboda haka gaskiya saboda Allah ku bada muhimmanci game da yiwa jama'a aiki. Amma ku manta da tunanin cewa zakuyi mana kaza zakuyi mana kaza wannan ba shi bane. Shi yasa idan muka zo wannan lacar jama'a har wasu zama da muka rinka yi da su waɗancan ɗin tunda suka fito takara da sharadin da mukayi musu da kuma cewa basu cika ko kwaya ɗaya ba duk sai mun gaya wa jama'a. Shi yasa fa hankalin su ya tashi fa ɗan wannan kaset ɗin bai wuce awa ɗaya da minti biyar ba fa. Amma sai bugo waya ake ana taro kwon arziki dan girman Allah kada in sake yin wata magana nace ni ɗin nace ai bance komai ba wannan ma goron gayyata ne kawai invitation letter ne. Invitation card ne ma kawai an faɗi ne me yasa za'ayi magana akai. Ni bansan me yasa suka damu ba. Allah yasa ko kun fahimci irin yadda ni na fahimta. Ni banga me abun damuwa ba. Menene abun damuwa albani yazo ya bayyana abinda akai mishi yazo ya bayyana kaza yazo ya bayyana kaza yazo ya bayyana kaza me abun damuwa. Ni banga abun damuwa ba. Yadda kuke kokarin ku bayyana nine mara gaskiya da nine zan ta kokarin magana a rufe ta a rufe ta amma ni ina da kin interest a cikin maganar ina son maganar ina sha'awar ta ina jin daɗin ta. Don ta fito karara kowa yasan menene ake ciki. To amma me yasa ku kuke so azo ayi magana a cikin jama'a a'a wai so ake azo a same ni ni da mutum uku kawai wai don Allah wai sai aji nayi shuru a'a. So da haka gaskiyar lamari wannan shine sako na. Ina kuma fatan ya isa daidai ga jama'a kuma ina fatan wannan kaset ɗin in mai yuwuwa ce a buga shi duk a raba wa waɗannan 'yan siyasan da suke aikawa da gero da sukari da kujerun aikin hajji ace to wallahi ga sakon mutanen nan. Mutanen nan sunce ba sun goyi bayan ku bane don ku mutanen kirki ne ko don kuna da quality. Kadai sun goyi bayan ku ne don suna fatan zaku iya abinda waɗancan suka kasa. Idan kuka kasa suma zasu ɗakko wasu suzo su sake dasawa. Iyakarta kenan. So ni abinda na ɗauka a baiwa malami irin wannan kujerar hajji ko wannan gero saboda yace a zaɓuwa ne to gaskiya wannan bashi da banbanci da cin hanci. Don haka abinda nake fahimta haramun ne a ba wani malami ya karɓi irin wannan. Amma in za'a ba malamai to ga malamai can waɗanda su ba abinda suke cewa game da harkokin yau da gobe balle suyi maganar siyasa. To sai aje a saɓe su ga can suna karantar da allo suna karantar da kur'abi a suworo. Don akaje aka basu waɗannan sune zasu zauna suce salati goma ga Annabi. Amma gaskiya mu dan anyi mana wallahi tallahi aikin banza ne a wurin mu bashi da wata kima. Wallahi yanzu ni gaskiya kwakwalwa ta bata bugawa akwai abinda zaka iya bani da zuciya ta zata gamsu. Ni dai kaga bazaka bani wata mota mota da zanyi sha'awa ba. Bazaka bani gida da zanyi sha'awa ba. Bazaka sai littafi ko kujerar hajji ko ka ɗau 'ya ka bani wanda zaka burge ni ba babu. Kawai ni abinda zaka burge ni yadda zuciya ta ta jarabtu da son zariya ta gyaru to kawai sai in ga development a Zaria. To duk wanda naga ni irin haka to wannan shine nawa. Kawai shine abinda zakayi kawai kayi winning zuciya ta. Inga an barƙe titi kaza ana kwalta, inga an barƙe wuri kaza asibiti, talakawa kaza ana samun musu da wurin sana'a to madalla shikenan. Amma bayan wannan wallahi ba abinda zakayi bazaka burge ni babu. Wannan na faɗa maka shine sirri na. Don haka duk wahalar da zaka je kanayi kai a wurin ka kana tunanin cewa in kayi wannan a'a ni gaskiya ba wannan bane sai kayi asalin waɗannan abubuwan nan sune kuma waɗannan abubuwan sun fi komai sauki. Tunda gwamnati ke ɗiban kudi ta baka dan kayi.Value Annotations
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
How to cite this item
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Goron Gaiyyata. Daarul Hadeethis Salafiyyah. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/westafrica/item/15894.
Zaria, M. A. A. (n.d.). Goron Gaiyyata [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/westafrica/item/15894
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Goron Gaiyyata. Daarul Hadeethis Salafiyyah. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/westafrica/item/15894.
Download
Visualisations
Loading visualisations…


