document audiovisuel · Daarul Hadeethis Salafiyyah · 29 août 2008 Citer
Azumi Ibadar Zumunci
- Type
- Enregistrement vidéo
- Créateur
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Editeur
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- Description
- en Sheikh M.A.A. ALBANIY gives the guideline on fasting and the importance of fasting worship in Islam with reference to the Prophet Muhammad, Hadith his lecture title.
- ha SHEIK M.A.A. ALBANI, ya karantar damu yadda musulmin, matsayin ibadar azumi da hukunce hukunce akan azumi bisa hadith Annabi Muhammad a lakcarsa.
- fr Sheikh M.A.A. ALBANIY donne les lignes directrices sur le jeûne et l'importance de l'adoration du jeûne dans l'Islam en se référant au Prophète Muhammad, au Hadith et au titre de sa conférence.
- Date
- 29 août 2008
- Importance matérielle
- PT278M
- Support
- DVD
- Sujet
- Ramadan
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000036
- contenu
-
============================================================
[Part 1]
============================================================
[Segment 1/5 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yanzu da muke magana ranar lahadi ce wadda ta daidai da ashirin da biyar ga watan sha'aban hijira annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallam na da shekara dubu daya da dari hudu da talatin. Daidai da sha shida ga watan ogost shekara ta dubu biyu da tara. Yau itace ranar karshe in Allah ya so da zamu gabatar da lacoci da muke gabatarwa tsakanin sallolin azahar da la'asar a wannan masallaci namu na Majaror tudun wada zaria jahar kaduna nigeria. Asali kamata yayi yau ya zama kaset na hudu daga cikin jerin giyar lacoci da muke akan kadiya ta mantuwa illolin mantuwa maganin mantuwa da karkasuwa da kuma sabubban da ke haddasa da mantuwa. Sai dai gaskiya na so in yi amfani da wannan dama domin in gabatar mana da ainihin wato fadakarwa dangane da wasu hukunce hukunce na wannan wata na azumi wanda ainihin muke fuskanta. Kuma da yake ba wata lacca ce tsayayya ba zan so ne a dan saurare ni in ya so daga karshen dan bada yan mintina kadan insha Allahu ta'ala domin in haskaka mana akan wasu ayoyi guda uku zuwa guda hudu a cikin alkur'ani wadanda suke magana dangane da azumi sai kuma wasu hadisai na annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama sannan sai wasu mas'aloli da zan so dan haskaka a kansu inshaLire le texte intégral — 40 973 mots restants Réduire le texte intégral
Allahu. Azumi ibada ce daga cikin rukunai na musulunci kamar yadda yazo a cikin hadisin da bukhari da muslim suka ruwaito daga sahabi abdullahi dan umar da kuma sahabi abu huraira Allah madaukakin sarki ya kara musu yarda. Wadannan manya manya daga cikin ainihin sahabbai suka bada labarin cewa annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama ya ce an gina musulunci ne akan ainihin wato abubuwa guda biyar. Musulunci an gina shi ne akan dirkoki guda biyar. Dirkar farko itace shaidawa da cewa babu wanda ya cancanta a bauta mishi sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya kuma da shaidawa lallai muhammad sallallahu alaihi wa alihi wasallama bawan Allah ne ko manzon Allah ne. Sannan sai tsayar da sallah da bayar da zakka da kuma azumin watan ramadan sannan da ziyarar dakin Allah mai girma wanda yake makkah mai girma. Wannan hadisi ya bayyana mana tabbacin cewa azumi yana daya daga cikin rukunai guda biyar wadanda Allah madaukakin sarki ya gina addini a kansu. Ayar alkur'ani ta tabbatar da wannan magana tun kafin wannan hadisi ya tabbatar da haka idan Allah madaukakin sarki yake cewa Wannan aya tazo da abubuwa gimshikai guda uku abu na farko ayar tana bayyana mana cewa azumi dole ne. Abu na biyu ayar tana allaka zumuncin da ke tsakanin mu da al'umomin da suka gabace mu ishara akan cewa azumi na daga cikin ibadojin zumunci dan haka wannan kaset din takin shi shine azumi ibadar zumunci. Wato ina so in jawo hankali a cikin wannan kaset dangane da allaka zumunci da Allah madaukakin sarki yayi tsakanin mu musulmin yau da musulmin da suka gabace mu kafin zuwan annabin mu muhammad sallallahu alaihi wa alihi wasallama. Wannan zumuncin shine ke tsakanin annabin mu annabi muhammad sallallahu alaihi wa alihi wasallama da annabawa wanda suka ainihin gabace shi. Sa'annan wannan ayar tana nuna mana daga cikin kyawawan sakamako da ake samu dangane da watan azumi shine takawa da tsoron Allah. Wato ya kamata azumin ramadan ya gyara ka da gyaruwar yanayin da kuma gyaruwar ibadoji da suke faruwa a cikin shi. Allah madaukakin sarki yace An dora muku azumi an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi azumi din ga wadanda suka gabace ku. Allah yayi haka ne domin ainihin ku samu tsoron Allah a cikin ainihin rayuwar ku. Wannan itace aya ta dari da talatin da uku a cikin suratul bakara. Wannan ayar farkonta ya kiraye mu da siffa ta imani dan mu gane sirrin zumuncin ba kabilanci bane. Dan haka Allah bai kira mu da hausawa ko ya rabawa ko nufawa ko in ya mu rai ba domin in haka ta faru to zumunci ya yanke kenan tsakanin wata kabila daga wata kabila. Amma sai Allah madaukakin sarki ya hada zumuncin da zai iya yiwuwa ko wace kabila ta shiga domin da Allah ya ce ya ku hausawa to wannan yana nuna zumunci ya yanke tsakanin duk wanda baba haushe ba da wadanda za'a allakanta a baya. Amma da yace Za'a iya samun hausawa su shiga ciki don zasu iya imani. Yaraba zasu shiga ciki inyamurai zasu shiga ciki mutanen kasar rasha da japan zasu shiga ciki. Larabawa da turawa zasu shiga ciki. A karkashin wannan ne abdullahi dan mas'udin Allah madaukakin sarki ya yarda da shi kamar yadda al-imamu ibnu jaririn al-tabari ya ruwaito cikin tafsiri da isnadi sahihi yace Duk sanda kaji Allah madaukakin sarki ya kira wannan suna to ka kasa kunne da kyau alheri ne zai kiraka kabi ko kuma wani sharri ne zai kwabe ka. Kaga nan Allah yana kwabar mu mine ne game da wani sharri kar su dinga fadin wata kalma wadda ma'anar kalmar tana daukar rashin ladabi ga annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama. Na'am Idan jama'a kun fahimci wannan da kyau zanyi muku ishara a gurguje zuwa ga littafin babban malamin mu Mallam abubakar jabir al-jaza'iri inda yasa wa littafin Nida'atun rahman Ya bibii alkur'ani tun daga farkon shi har karshen shi idan Allah yake cewa gaba daya tafsirin su da kawo ma'anonin su. Na'am lallai wannan suna daraja ce domin Allah da muke wa imani mukayi imani da shi. Allah da muke fatan ya karbe mu a matsayin mu'minai shine har ya komo kuma yana kira da cewa ya ku mu'minai ashe wanda ya karbo wannan kalma ta imani ya samu shiga kenan Allah ya yarda da shi. Allah madaukakin sarki yake cewa Allah ya farlanta muku azumi kamar yadda ya farlanta shi ga wadanda suka gabace ku. Anan ana kamanta farlantawan ne namu da farlantawa gare su ba lallai azumin ya zama iri daya ba. Amma yadda dai azumi ya zama farilla akan mu haka azumi ya zama farilla akan su. Me yiwuwa ya zama suma Allah ya farlanta musu ramadan ne kamar yadda ya farlanta mana ramadan. Me yiwuwa ramadan din nasu da aka farlanta musu ya zama cikakkun kwanakin ne kamar yadda muma cikakkun kwanakin ne. Me yiwuwa ya zama ramadan aka farlanta musu amma kwanakin wasu ne aka diba musu. Me yiwuwa kuma ya zama wani watan ne ko wasu kwanaki ne ko wasu makwanni ne aka farlanta musu. Wannan dai Allah madaukakin sarki ya barwa ainihin kanshi sani amma abu mafi muhimmanci shine da mu da su muna tarayya akan wajabcin wannan ainihin azumi. To sa'annan sai Allah madaukakin sarki ya kawo samara itace me itace domin ku samu tsoron Allah. Anan wannan tsoron Allah zai fara samuwa a yanda zaka koma baya kana karanta tarihi a cikin suratul hud da suratul yunus da makamantan surorin da suka bada labarin annabawa da al'umomi da gwagwarmayar da suka yi da irin hallaka wadanda suka bijirewa wadannan dokoki. Dan ka gane ashe daga cikin rabt daga cikin hada zumuncin shine ka koma ka ga yaya karshe kyakkyawa na mu'minai na farko ya kasance yaya mummunan karshe ya kasance na wadanda suka ki bin wannan doka dan ka wa'azantu da su ainihin wadancan kafiran sannan kuma ka zaburu ya zama Allah madaukakin sarki ya duma maka da ainihin wato irin daraja da wadancan magabata suka samu. Idan ya zama azumi ya tabbata ibada ce ta zumunci tsakanin mu da magabatan mu. Me yasa azumi bazai zama ibada ta zumunci tsakanin mu da wadanda muke rayuwa ba mu'minai. Yanzu jama'a tsakani da Allah sukari da ke shigowa nigeria mafi yawancin shi musulmi ne ke shigowa da shi. Sukarin da akeyi a nigeria mafi yawancin shi musulmi ne suke yi. Raken da ake noma sukarin mafi yawancin shi musulmi ne suke nomawa. Amma me yasa buhun suga yana naira dubu biyar dubu biyar da dari biyu da dari uku ana cewa azumi ya kusantu yanzu har ya kai dubu bakwai da dari takwas yana neman ya kife ya cike. Ma'ana mu musulmi bamu da rahma ga junan mu bamu da tausayi ga junan mu bama neman mu kyautata domin Allah ya kyautata mana. Shin azumin nan da zamuyi laifi ne zamuyi wa Allah wanda ya cancanta yan uwan mu su azabtar da mu laifi ne zamuyi wa yan uwan mu yan kasuwa masu sayar da sukari wanda ya cancanta su azabtar da mu. Abinda ake sa rai ka diba ka bayar kyauta eh yaushe zaka kara musu kudi akan haka ko kuwa zaka ainihin karbi kudin da hannun dama ka mika ta wani wurin da hannun hagun a yabe ka misali buhun sugar da kake siyarwa naira dubu biyar yau ya koma naira dubu bakwai. Ita wannan naira dubu biyun zaka je kayi sadaka a cikin ta zaka yi zakka cikin ta zaka yi aikin alheri a cikin ta amsar itace na'am idan zaka yi me yasa tun farko bazaka kyautata tun daga wajen siyarwa ba. Addu'ar manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallama da tazo cikin hadisin abu dauda da yace Allah yaji kan mutumin da yadda ya siyo da sauki haka yake siyarwa da sauki. Abinda zaka duba jama'a tsadar sukari da tsadar abinci kadai tana tasowa ne a tsakanin musulmi daidai lokacin da aka taya yamma yin azumi ko yin karamar sallah ko yin babban sallah. Kashi casa'in da tara na ragunan nigeria da akeyi layya da su musulmi ne suke kiwon su. Kuma a yanzu da muke magana sun fara kiwon su amma abun mamaki har raguna sun fara tsada a yanzu saboda tattalin su da musulmi suka fara yi domin suyi layya da su. Jama'a wannan laifi ne bai kamata haka ta kasance a tsakanin mu ba. Ya kamata a kira wani taron karawa juna ilimi da taron kara wayar da kan yan kasuwa akan su gane wadannan abubuwan jama'a. Ku tafi kana shiga jidda yanzu ko ina jidda ta cika da manna manne yan kasuwa suna tamanna komai sun ruguza farashin shi komai har abunda bashi da alaka da sallah shine me littafi. Littafi bai da alaka kai tsaye da yin sallah idi ko karama amma bulugul maram idan yana real ashirin zaka ga ainihin an sa wato Ramadan bonanza ga rabasar watan azumi bulugul maram din nan sai a ruso shi daga real ashirin sai ya dawo real bakwai. Kuma wallahi mai siyar da bulugul maram din ba wata gara basa ya samu ba. Abinda yake fata wannan ramadan da yazo bayi da yadda zai saukaka wa musulmi bari ya saukaka a cikin harkar shi. Dan haka akwai daliban da zasu shekara suna tara kudi duk wani littafi da ya gagare su zasu je su siye shi cikin ramadan din nan. Akwai malamai wadanda su suka sunnan ta wannan dabi'u a jami'ar islamiyya dake madina malami ne duk cikin albashin shi zai wara dubu kaza ya aika madaba'a ya sai dibga dibgan littattafan da ya san dalibai na ki shiruwar su amma sun kasa siye. Sai ya sari littafi real dari bakwai sai ya zo ya siyar da shi dari biyu da hamsin ya fadi real dari hudu da hamsin saboda albarkan ramadan. Wannan kyakkyawar dabi'ar ta malamai da suka fito da ita a jami'ar islamiyya aka fara fito da ita tadarsu su ta komawa su jami'o'i yanzu har tayi tasiri akan yan kasuwa. Mutum bai da alaka da ilimi ba malami bane ba dalibin ilimi bane amma in ya samu labarin irin wannan maganar a wurin wa'azi sai yace zai fitar da miliyan kaza aje ayi ta siyan littattafan da suka dace a tara su azo a fitar da Akwai dan kasuwan da zai yi haka jama'a abun mamaki sai yaga littattafan an siya an siya kawai in yazo ya samu dalibai a tsaye sai yace kowa ya dauki littafin da yake so. Ku ce kai bai ce kowa ya tsuguna ya dauki wanda yake so a gani. Ya rage in ka diba a tsorace ya rabon ka kenan. In ka diba ka dora wani aka karata wani nan karata wani nan karata wani nan sai yace kowa ya dibi wanda yake so sai yace sai yace billah hayya da zai an baku saboda Allah kowa ya tafi gida. Me yasa Allah bazai wadata mutanen nan ba yaya Allah bazai haskaka kira zan su ba yaya bazasu zama masu rahma ba. Gaskiya musulmin nigeria kalubale ne wannan gare mu na'am tun muna matasa muke zuwa shagon siyar da ta kalma a nan zaria da aka fi sani da hamani daidai lokacin Duk wani takalmi mai tsada a lokacin zaka iya zuwa da naira ashirin da biyar ko naira talatin da biyar ka siya wanda kafin wannan lokacin naira dari da talatin ne ko dari da hamsin amma saboda tazo sai su yanke farashin sai su dawo da shi kasa. Tsakani da Allah yadda muke ganin ko mun taba ganin wani allo a nigeria ko wani kyalle dake cewa sallah bonanza to muna fatan a fara ganin wadannan abubuwan jama'a. Mu zama mu dauki siffa irin ta sahabban manzon Allah da yake cewa Ya zama tsananin mu ga wadanda suke makiyan mu ne amma masoyan mu masu imani irin namu fa mu zama muna da tausayi gare su. Na'am sadar da zumunci tsakanin masu wadata da wadanda basu da wadata Allah ya rufa maka asiri kai babban mutum ne kai mai kudi ne ko kana da wadata in aka zo aka yi sallah magariba na rantse da Allah wani talakan zaka ga yana zazzare ido ne bai san inda zai je ba bai san ina zai je ya bude baki ba. Wannan koko da aka kawo masallaci kwarya guda ko koko guda ya dan sha shine abunda ya mallaka kawai. Kuma da zaka bincika tafiyar minti nawa yayi kafin yazo masallacin dan ya samu wannan kokon da wannan kosan tafiya ce mai tsawo. To yanzu ya sha anyi sallah magariba yayin da zaka je gidan ka an cika table soyayyun kaji daban soyayyun tsuntsaye daban farfesun kifi daban kaza daban gasashen kaza daban cincin iri kaza daban da kai da iyalanka ku ci abunda kuka ci ragowa a tattara a zuba a bola. Me yasa sanda akayi sallah magariba bazaka tashi kace mutum biyar su biyo ni. Abinda sahabbai suke kenan yana nan cikin sahihul bukhari idan aka idar da sallar isha sai ainihin kowanne sahabi da ya san yau akwai abinci a gidan shi sai ya mike sai ya dubi ahlus suffa mutanen dake kwana masallacin annabi sallallahu alaihi wasallam basu da gida basu da abinci basu da mata basu da yadda zasu yi. Wani ma zanin shi kwaya daya ne sai yace mutum kaza su biyo ni. Abubakar ya taba kwasan gayya irin wannan yaje da su gidan shi suna cin abincin abincin na maye wayar da yake. Wannan hadisin ya fassara mana karama ce zahira ta bayyana ga abubakar wa yace maka bazata bayyana gare ka ba koda a fakaice ne ba lallai kana ci yana komawa ba. Kai kuma zaka iya ciyar da su gobe sai ka ga Allah an tayo maka fiye da abunda ka tsamata. Dan haka jama'a in yi mana nasiha akan irin wadannan abubuwan ya kamata a samu gyara a kasar mu sannan na biyu Zaku shiga masallatai musamman masallatai da muntada ta gina a nigeria da wasu masallatai wadanda wasu bayin Allah suka aiko da kudade aka gina daga kasashen saudi arabia ko misra. Ana ciyar da masu azumi. Wadannan dake ciyarwa karka dauka asali kungiyar muntada ce. Karka dauka asali gwamnatin saudiya ce karka dauka asali gwamnatin masar ce. Abun mamaki ita muntada tana shiga tsakanin talakawan kasar da take ne da kuma talakawan inda ta gina masallaci kawai aikin da take kenan. Ma'ana za'a tafi kasar saudi arabia ayi ta kwadaitar da talakawan saudi arabia da general public al'ummar kasa gaba daya akan muhimmancin ciyar da miskini. Wadannan kudin suka karba shine suna da limami ko wakili a nigeria sai su turo mishi shi kuma ya ringa dafa abinci yana baiwa talakawan nigeria. Karka taba daukan cewa gwamnati ce a can take turowa
[Segment 2/5 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
kar ka taba daukan cewa wasu masu kudi ne su ke turowa. Wallahi in kaje ka zauna kofar ofishin da suke ayyuka, a kasashen da suke, zaka ga wani yazo ya tsaya da tsohuwar tasi. Kafashi duk faso. Yazo da real hamsin. Domin ya bayar da tashi sadakar ta wannan shekara. Wannan real hamsin din ita kuma mun tada ba zuwa take tana aiko da ita. A dafa kokon nan a shanye babbadi kuma a koma ana lalube a'a sai dai cigaba. Wadannan real hamsin aka tattara su aka tattara su sai su waye gari domin za'a shekara ne ana tattara su. Sai su zama wajen naira miliyan ashirin na Najeriya ko talatin. Sai a zuba su a wani kasuwanci wanda wata guda. Sai wannan miliyan ashirin da biyar sai ta jawo miliyan uku ko miliyan biyar an ci riba misali nake muku. Sai a dibo wadannan kudi. Sai a zo a fara iftarus sa'im da su. Sai a dibi wani yanki na wadannan kudi a cigaba da juya su. Ana kawowa ana juyawa kenan ya zama. Da aka zo aka samu matsalar sa ido da gwamnatocin duniya suka yi wa ainihin kungiyar. Muntada da sauran kungiyoyi da ke ayyukan musulunci aka hana su samar da kudi tsakanin mutane. To yaya suke cigaba da gudanar da harkokinsu? Shine sun riga wadannan kudi sun kafa su a matsayin jali. Don haka ko an cigaba da bayarwa yanzu ko an hana. Wadancan mutanen da suka bayar shekara goma da ta wuce an maida kudin su ya zama jali. Ana cigaba da ciyar musu da talakawa da shayar da su suna cigaba da samun lada. Ma'ana yanzu ace. Watan al muharram ya shiga. Ko watan shawwal wato watan sallah karama. Sai mu fara siyar da wannan rasit. Sai mu tara kudi dubu dari biyar. Daga masallacin nan wadannan kudin sai mu yi ta juya su. Kafin watan shaban kusan wata takwas ko wata tara ko goma. Wadannan kudi miliyan nawa rabin miliyan dubu dari biyar sun waye gari sun zama dubu dari takwas. In muka zo sai mu dubi nawa ne zai ishe iftarus sa'im din sai mu gan naira dubu dari biyar zata isa sai mu yi iftarus sa'im bana. Dubu dari shida da muke da ita sai mu sake saka ta a kasuwanci ta cigaba da juyawa. Domin ku sani daga cikin hanyoyi mafi samun kudi a wannan zamanin sune kasuwanci. Ya rage kawai. Sannin sirrin ina za'a saka kudin. Me za'a siyo. Ina za'a kai. Waye ya iya kasuwancin. Wannan na gaya muku baya bukatar sai kun saka hannun jali ga wani kamfani da za'a je ana sabani ya halatta ko bai halatta ba a'a. Kuna bukatar ne ku hasasa gabashin Najeriya. Masu arewa, gombe, adamawa, taraba. Me yiwuwa akwai wasu abubuwa a can wadanda abubuwan nan arha suke yi. In kazo da sunan fa. Tsada suke yi. Dauki misali dabbobi, raguna, shanu. Sai kaje ka samu tirke kyan rago. A kasuwan guroro sai a siyar maka naira dubu bakwai. Naira dubu bakwan nan naira dubu uku zata kawo shi zariya tana kawo shi zariya sai kaje ya zama dubu ashirin a cikin murna kuma za'a siye shi a zariya. Wannan kasuwanci ne wanda ba ruwan ku da wani rikici ya halatta ko bai halatta ba wani ustazu zaku samu ya tafi ya je. Sannan mota daga can zuwa fitowa nan arha take saboda motoci ne sun kai kaya babu kayan da zasu dibo. Don haka madadin za'a biya mai mota naira dubu dari in aka bashi dubu talatin sai ya dibo kayan don bai dibo ba haka zai dawo. Yanzu wannan kasuwanci ne ko ba kasuwanci ba? Kasuwanci ne ku je ku ga yadda shanu suke arha ku je ku ga yadda yan marika suke arha a kasar adamawa da taraba da gombe da sauran su. Ku buga kuyi kasar mai duguri. Kuje ku ga yadda rakumi yake sauki da arha a mai duguri. Rakumin nan ana yanka shi a kano. Rakumin nan ana yanka shi a kaduna. Ka kawo ku ga nawa zai baku. Kuje ku ga kifi yadda yake arha a doron baga. Wannan nan kasuwanci ne musulmi duk zasu iya shiga suyi su. To sannan. Tafi jihar kogi. Ka ga yadda azara. Ka tako. Lemo. Ayaba. Suke arha kaje ka samu kauye sun rasa yadda zasu yi da su. Abun da ake bukata kawai ka shiga ka daure ka siya ka fito da shi. Kana fitowa da shi ka kai kano. Ko ka kai wata jihar sai ka kasa mu kudi. Irin wadannan kasuwancin sai kuyi. Su ustazan da zaku dibi kudi ku basu dama mutanen kirki ne amintattu sai dai basu da sani akan kasuwancin sai ku samu wani dan kasuwa ku hada su. Su sun samu aikin yi. Masallaci ya samu hanyar shigowa sannan iftarus sa'im duk shekara za'a dinga ana samun lada. Sai ku tafi gidan radio. Sai a je ayi wani shiri na musamman don ku samar wa da al'umma wayewar kai akan haka. Wannan fikrar taku sai kuji mutanen gombe sun dauka, mutanen sokoto sun dauka, mutanen katsina sun dauka, karshe sai zama alheri sai ya game mutanen mu. Kuna nan sai ku ga masu kudin da kuke tsoron su shigo sai ku ga sun shigo cikin izza. Ba tare da kun wulakanta ba don baku je neman su ba. Sun ji a talauci da naira hamsin hamsin. Kunyi karfin da har kunje gidan radio kuna fadin irin ayyukan ku. To da al'umman mu zasu bi haka jama'a. Wallahil azimi ba karamin alheri bane. A kudancin kasar nan. Akwai wanda zaka je kaga manja. Har lalace musu yake a wasu kauyukan. Saboda babu wanda zai zo ya siya ya fusar da shi su kuma wani kuma ba inda ya sani duk duk duniya sai wannan kauyen. Ga manjan yayi ya dura amma ya rasa ina zai daši. Tafi kudancin jihar kaduna. Kaje kaga yadda alabo. Daga roro go, daga rin menene wajen sanga da makamantan su kaje kaga inda wannan abun in kazo da shi nan zai zama wani abu da mutane ke marmari suke so ka samu alherai masu dimbin yawa. Tafi garin mubi. Ka ga hula irin wannan yadda zaka saro ta cikin sauki da arha. Duk wadannan haska ka mana ne akan ya zamu yi a taimaka wa wannan addini namu da wannan al'umma tamu. Ina aka samar da haka jama'a sai ku ga mun zo mun samar da wani yanayi na kauna. Wadannan kudin a cikin su. Sai ya zama har shanu zamu dinga siya yi. Muna yankawa. Idan sallah tayi. Ana duban gidaje da ke fama da talauci ana aika musu. Malamin nan assaf mai sab'una hadisa al mi'an nabawiya wanene wanene aikin da yake yi kenan. Sai ya dubi marayu yaran da yasan marayu ne a makarantar shi sai ya rubuta sunan su. Sai suzo suna karban abinci. Wanda zasu ciyar da iyalan su. Da azumi. Abincin da za'a yi sallah, abincin da za'a yi kaza, abincin da za'a yi kaza wadannan kofofi ne na alheri jama'a. Wadanda ya kamata muzo mu bude su a kasashen mu. Kamar yadda nake cewa kullum. Wallahi ba nace babu kyau bane. Amma ina ganin akwai hadari idan al'umman mu suka cigaba da dogaron taimakon da za'a zo musu da shi daga kasashen waje. Ba dan komai ba saboda wannan na jan son ido da sa ido daga cikin hukumomin mu na cikin gida. Karshen ta dubu dari za'a aiko muku da su. Amma aka tashi zero zero za'a kara a kara kamar guda biyar sai ya zama miliyan kaza. Nawa aka aiko muku naira dubu dari. Don haka duk wani abu sai ace ai daga waje ake aiko muku da kudi. Amma yanzu wannan dakan daka ne shikan daka bakwa kunyar kowa ya ji ya ga ina kuke samun kudin ku ya kuke samun kudin ku. Domin hanya ce da kowa ya same ta ma zai bi. Sannan. Daga karshe abun da nake bada shawara jama'a. A kashin gaskiya saboda Allah. Akwai bukatar malamai suji tsoron Allah. Su gane da cewa ba karantarwa ce kawai aikin su ba. Wannan taron karawa wa juna sani. Ya kamata ace kamar nan markazus salafiya muna da hole a sama. Sai mu kira yan kasuwar tudun wada. Idan muka ji azumi ya rage da wata uku. Mu kira yan kasuwar sabon gari in muka ce yan kasuwa ba wanda yake kulla sukari ba shima wannan irin mu ne talaka. Wanene ke shigo da sukari daga nan. Sannan daga can kano wanene ke shigowa. A gayyato su a je a za'una da su. A fadakar da su. Wallahil azimi akwai mutanen kirki da yawa amma kirkin baya bayyana. Sai an motsa su. Sai an fadakar da su. Sai an kuma nuna musu illar abubuwan da ke faruwa sakamakon. Mas'alolin da suke saka jama'a a ciki. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Don haka jama'a. Azumi ya kamata ya zama lokaci ne na tausayawa al'umma. Dazu nake gani a wasu tashoshi na kasashen larabawa fa jama'a. Hatta plate din da za'a ci abinci da wanda za'a shafa fesun azumi an karya farashin shi a kasar masar. Plate din da za'a shafa fesun bawai naman farfesun ba shi kanshi an karya farashin shi. Yana cewa gashi albarkan ramadan ya zama kaza da kuwa kaza ne. Plate din da za'a ci abinci chokali. Duk an karya farashin su saboda me saboda ramadan yazo. Wannan dabi'ar musulmin kasar masar ke yin ta ko to har kiristocin kasar masar yanzu suna yin ta. Kirista ne yake da shago yake da ma'aikata yake da wurin sai da kaza amma shima sai ace ramadan bananza. Kana azumi ne sai ya ace a yan uwa na suna yi. Yan uwan shi musulmi suna yi shi ba musulmi bane ma'ana yan uwan shi da ke zaunar da shi kasa guda ko yaran shi ko makamantan haka ko kuma kalma ce irin ta yan kasuwa koma dai yaya. Ya ta'asirantu da wata kyakkyawar dabi'a ta musulmi. Allah madaukakin sarki ya taimake mu.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
Idan muka dawo muka dubi falalar wannan wata. Falalar wannan wata tana bayyana. A wurare da yawa daga cikin hadisan manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallama. Daga ciki akwai. Ainihin wato. Hadis a wato dangane da ainihin wato falalar wannan wata akwai hadisin abu huraira wanda yazo cikin bukhari wanda manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yake cewa. Wanda ya azimci ramadan. Za'a ainihin wato. Yafi mishi. Zunuban shi. Baki dayan su. Amma ya zama yana mai imani da Allah kuma yayi ne don Allah da neman lada haka wanda ya samu lailatul kadri za'a gafarta mishi zunuban shi da su gabata. Bukhari da muslim suka ruwaito wannan hadisi. Har yau bukhari da muslim suka sake ruwaito wani hadisi da ke bayyana falalar wannan ainihin wata na ramadan. Idan ramadan yazo sai a bude kofofin aljanna sai a rufe kofofin wuta sai a kama shedanu sai a saka su a cikin kukumi shine sai a daure su. Shedanu su suke lalata mutane game da addinin Allah. Da su da ainihin marada duk sai a bi a kukumce su. To wadannan abubuwan me suke nuna mana suna nuna mana yadda sarkin wannan wata. Da kuma sarkin yanayin yake. Yadda in ba Allah ya lala Allah yasa mutum ya lala ce. Lalacewar da ya kai mustawa ko matsayin na shedanin kanshi ba. To ya kamata wannan wata ya chanza shi. Saboda mutane sun gyaru suna ibada. Ko ina karatun al kur'ani ake shedanu da ke kangarwa an daure su. Ta wace waya bata zata zo wa mutum sai dai in ya tabbata shi kanshi ya lala ce. Allah madaukakin sarki ya tsare. Jama'ar musulmi wadannan na daya daga cikin ko na kadan daga cikin abubuwan da naso ainihin in zayyana mana a wannan lokaci. Sannan wannan wata yana daga cikin ainihin watannin al kur'ani. Kuji abun da Allah yace a kur'ani. Watar ramadan shine watan da aka saukar da al kur'ani hadisi ya fassara wannan wanda yazo cikin littafin Annabi yace an saukar da al kur'ani daga sama ta bakwai zuwa sama ta daya. A cikin daren lailatul kadri. A cikin watan ramadan shine wannan saukar wanda ake magana. Wannan saukar wa Allah ya bada labarin ta a wurare da yawa a cikin al kur'ani. Mun saukar da al kur'ani a dare mai albarka. Lallai saukar da al kur'ani sai mu. A wani wuri yace. Mun saukar da al kur'ani a daren lailatul kadri. Wadannan dalilai ne da ke nuna mana cewa. Watar ramadan watan al kur'ani ne. A wannan wata aka saukar da shi. Daga sama ta daya a daga sama ta bakwai zuwa sama ta daya. A wannan wata aka fara saukar wa da annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama da shi kamar yadda malamai suka bayyana. Sannan kuma duk shekara idan watan yayi. To sai a saurara daga cigaba da saukan mishi da ayoyi. Sai mala'ika jibrilu ya dinga ziyartar shi ko wane dare. Yana zaunar da shi. Ya nemi mishi tilawar abubuwan da ya koya mishi ma'ana shi annabi sallallahu alaihi wasallama yana karanta abubuwan da malamin shi ya koyar da shi a wannan shekara. Idan gari ya waye. Annabi sai waye gari cikin murna. Da fara'a. Da kyauta. Da alheri saboda daren jiya ya samu ziyarar babban bako mala'ika jibril kuma sun zauna sunyi tilawa al'kur'ani. Me wannan yake nuna mana? Ashe wannan wata ne da ya kamata ko wane musulmi ya dage wajen dayan abubuwa biyu game da al'kur'ani. Karanta shi. Ko kuma me ko karantar da shi. Karanta shi. Ko sauraran shi. Karanta shi ko koyan shi. Ka gwada idan baka iya karatun al'kur'ani ba samu dama a wannan lokacin daga sallah azahar zuwa sallar la'asar kullum ka samu ka dinga zuwa kana dakkowa. Zaka ga albarkar da zata sauka gare ka saboda albarkacin watan watan al'kur'ani ne. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Sannan in muka koma wani wuri. Zamu ga cewa shari'ar musulunci. Tana da nata tsarin dangane da abun da ya shafi azumi. Na daya dai daga cikin tsarin shine ba'a daukan azumi sai anga wata. Idan ba'a ga wata ba sai ya cika kwanaki talatin. Wannan wata na shaban da muke ciki. Ana kirgen shi misali kwana ashirin da biyar yau gobe da shida da bakwai da takwas da tara idan magariba tayi a sunna sai a taso a fuskanci ainihin yamma. Ana neman ina ne watan nan ya fadi wannan shine abun da sunna ta tabbatar da shi daga ainihin annabi sallallahu alaihi wasallama daga kuma sahaban annabi sallallahu alaihi wasallama kamar yadda al dullahi dan umar yake cewa. Mutane sunyi kokarin neman ganin wata abdullahi dan umar ne sahabi ne yake cewa mutane sunyi kokarin ganin wata su wa yake nufi sahabbai. Don haka. Kokarin neman ganin wata sunna ne. Kuma. Da suka gani. Sai shi yaje ya bada labari ga annabi sallallahu alaihi wasallama. Idan mas'ala ta taso shin ana iya amfani da wata na'ura. Domin a ga wata. Ko ayi amfani da wata na'ura domin ta taimaka zuwa ga ganin wata. Malamai sunyi maganganu ga suka man haka. Dukkan na'urar da za'a sa. Wanda kai tsaye itace zata hasaso mana wata. Malamai sun tsoratar game da amfani da wannan ita ake kira da turanci Na'ura ce za'a sa ta a ido haka. Sai ta jawo kusa ai sai ta jawo nesa kusa. Sai ta washe duk wani abu da ake gani hazo hazo ne. Domin a ga abun da ake son gani a bisa yadda ya kamata a ganshi. Wannan na'ura. Malamai basu amince ta zama madogara. A wajen ganin wata ba a musulunci. Yo amma. Akwai wata na'ura wadda ba da jima wannan ba. Hukumar tsaro ta kasar america suka zauna suka kirkire ta. Wannan na'ura bata gama yaduwa a duniya ba. Kasantuwar jama'a da yawa basu san ta ba. Shi yasa lokacin da bayani yazo a bara a kasar saudi arabia. Akan za'a fara amfani da ita. Wasu kai tsaye sai suka dauka waccan ce. Wanda an dade ana inkarin amfani da ita. Kai tsaye. Sai suka ainihin bada fatawar bai halatta ya amfani da ita ba. Sai aka samu wani malami guda daya. Shi ya ga na'urar. Ya ga amfanin ta. Amma da yake ya manyan ta ya tsufa. Bai san yadda zai iya wa jama'a bayanin yaya take ba. Shine malam ibnul mani'a har yanzu wannan rikicin yana nan akan internet a bara aka yi shi uwar haka. Shi sai yace ya gamsu za'a yi amfani da wannan na'ura. Don haka yan jaridu suka diba. Suka fara bada labari. Malam ibnul mani'a ya bada fatawa akan ya halatta ayi amfani da na'urar ganin wata. Tasha al'arabiya, tasha al'jazeera sai rikici ya rude a kasar saudi arabia da waje. Aka yi ta raddo di a kai. Matsalar shi kuma ya kasa bayanin yadda na'urar take aiki. To zanyi amfani da wannan dama in dan dauki mintuna biyu zuwa uku inyi mana bayani domin wadannan bayanan sun zo mana Najeriya. An sake kwata yar gidan jiya. Suma malaman da suka je suka dauko labarin ta a Najeriya. Munyi taro da jiya da shekaran jiya da su a kaduna a ofishin jama'atu nasirul islam. Dayancin su da suka amintu da amfani da wannan na'urar. Sai dai kaicho basu san ta ba basu san yadda take amfani ba. Don haka wadanda basu yarda ba sunyi musu su kuma wadancan da suka yarda sun kasa bayyana yadda na'ura take amma Ina nan a wurin na samu damar gabatar da bayani akan yadda take.
[Segment 3/5 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker unknown]
Wato na'ura ce wadda aka yota a saka ta a waje a saman ɗaki. Ba kaine zakayi amfani da ita ba, sai dai zaka dawo nan cikin ɗaki zaka haɗa ta da computer ka. Haɗa ta da computer ta hanya biyu kamar yadda aka sani ko da waya ko kuma ta hanyar iska wato wireless. Wannan na'ura yadda kaga camera da ake amfani da ita wajen internet da ake ce mata webcam to kusan irin su ɗaya. Ido ne take da shi irin ido ainihin na abin da yake hassaso abin da yake nesa. Su kansu hukumar tsaron lokacin da suka yota sun yota ne ta hanyar ta riƙa amfani da digital signal. Wato irin hanyar da na'urar da ke sararin samaniya ta tauraron ɗan adam take haɗa kanta da ainihin wato wannan da kake ajewa a ƙofar ɗakin ka ko ƙofar gidan ka domin ya riƙa kamo maka tashar satellite. Zaka ga ana fara ruwa ruwa yayi ƙarfi sai ka ga abin ya ɗauke. Saboda wannan digital signal ɗin ko ɗan yaya aka samu motsi sai hoton ya motsa. Ba ainihin wave bace, ba iska ce irin ta rediyo wadda ko ina take iya harbawa ba. To sai suka haɗu da wata matsala itace a daidai lokacin da wata take zuwa rana tafi ƙarfin shi sai ya zama ta mamaye shi gaba ɗaya ido bazai iya ganin shi ba daga ƙasa. Wata na'ura da duk ƙarfin signal da aka bata daga ƙasa nan bazata iya ganin shi ba. Ita kuma na'ura an yota ne yadda idan gari ya waye sai a sa ta sai ta kalli rana. Daidai sanda rana zata fito idan ta kalli rana sai kaga ta ɗan gyara kanta haka. Domin Qur'ani ya bayyana mana Ita rana take gaba wata na binta. To amma zaka ga da safe galibi bazaka iya ganin inda wata yake ba, bazaka ga ina wata yake daga rana ba. To sai aka yota da farko sai kayi setting ta sai ta kalli rana sanda ta fito. Ita na'urar tana kallon rana sai ta hassaso inda wata yake. Sai kaji ta ɗan gyada kanta haka to tayi setting kanta da shikenan. Sai kaji ta ɗan yi irin yadda in ya shigar maka cikin handset tayi ɗililin haka to ta zauna daidai shikenan. Sai ka barta sai ka ci gaba da harkar ka. Idan yamma tayi wata kafin ya kai ga idda zai bayyana yana ɓoyewa zai ɓoye da minti biyar zuwa minti goma in har zai bayyana a wannan ranar to za a ganshi bayan minti goma. To daidai lokacin da zai tafi rana tana dab da ta faɗi. A daidai wannan lokaci shi kuma wata yake ɓuya to wannan ɓuyan da zai yi sai wannan na'urar sai kaji ta sake ƙara. To ta ƙaran nan tana ce maka sun rabu da wata kenan. Yanzu wata ya ɓuya ɓuyan da daga nan sai ya fito idan ranar fitowar shi tayi. Idan ranar fitowar shi bata yi ba fa bazai fito ba. To a daidai wannan lokacin taimakon da ita na'urar zata yi maka kai musulmi shine zata kai ka ne ta nuna maka daidai inda ya kamata ka sa ido da basira kaga wata. Don haka ba itace take ganin wata ba. Kamar zata kama hannun ka ne tace lalube shi daidai nan sai ta baka wuri to sai ka ci gaba da dubawa. Domin duk wanda ya karanta alƙur'ani cikin Sura scientifically tayi bayanin cewa rana takan fito dama takan faɗi dama takan fito tsakiya takan faɗi tsakiya takan kuma fito hagu ta faɗa hagu. Dr. Abubakar Imam a cikin littafin shi mai suna ikon Allah ya bayyana wannan haƙiƙar fiye da shekara hamsin da ta gabata. Cewa rana wani lokacin takan fito ta ɓarin dama wato takan shi bada ƙarfi gabas amma maso dama. Wani lokacin gabas maso hagu wani lokacin kuma tsakiya. To tunda wata binta yake yi idan yau ta fito dama ne kaga yana binta ta ina kenan ta dama kaga ta nan zai faɗi ta nan zai bayyana. In kaje kana nema a hagu fa zaka ganshi bazaka ganshi ba to shine wannan na'urar zata kai ka ne tace maka dubi ɓangaren hagu. Kawai amfanin na'urar kenan. Su kan ba sunyi ta bane don ta taimake ka wajen ganin wata. Sunyi ta ne domin ta taimake su wajen gano tafiyar wata kawai. Da rana in wata na tafiya ba a ganin shi. Da daddaren yana tafiya fa in ya bayyana ana ganin shi sai suka ce to suna son su san da rana yaya yake tafiya. Shine suka yi na'ura wadda shi wata yana bin rana ita kuma wannan na'urar tana binta haka haka suke tafiya haka suke tafiya. To akwai inda in yamma tayi sai ya ɓace. Idan ya ɓace ibba rana fitowar shi bace to baza a ganshi ba sai kuma gobe ya sake fitowa ta gabas. Yana bin rana. Idan wannan rana itace ranar da zai bayyana idan ya ɓata suka ce daga sanda kaji na'urar nan tayi wannan bippin tayi ɗililin ɗin nan to daga lokacin nan zuwa minti goma ka matsa suka ce in baka ganshi ba to bazaka ganshi ba. Ba rana fitowar shi bace. Don haka kunga ashe ita wannan na'urar kaɗai zata taimaka ne. Don haka babu laifi musulmi suyi amfani da wannan na'urar wajen neman ganin wata musamman ƙasar China ta rusa kasuwar wannan na'ura. Shine da na'ura ce wadda take da tsadar tsiya. Amma yanzu in ka shiga Jeddah ka shiga Dubai zaka ganta ana sayarwa real ashirin real hamsin real talatin ma'ana naira dubu ɗaya da ɗari shida na Najeriya naira dubu biyu kawai abin da kake buƙata kamar ƙala zaka haɗa ta da na'urar ka ta computer. Ina fatan an gane. Allah maɗaukakin sarki ya taimake mu. To in ya tabbata an ga wata to wajibi ne dukkan al'umma su ɗauki azumi. A nan bama so mu shiga saɓani mai yawa wanda ya faru tsakanin malikiya da shafi'iya akan malikiya na cewa ganin watan mutum ɗaya ko gari ɗaya ya wajabta wa dukkan mutane ko dukkan garuruwan duniya. Wannan magana itace fatawar malikiya. Fatawar shafi'iya su kuma itace ganin watan mutum 1 ya lazimta mishi shi kaɗai yayi abin shi. Ko kuma ganin watan gari ɗaya ya lazimta musu su kaɗai suyi abin su. Haƙiƙanin al'amari abin da yake daidai a cikin wannan maganar itace maganar da malikiya suka faɗi. Itace idan har aka ga wata a gari kaza to wajibi ne kowane gari ya ɗauki ainihin wannan azumi. Sai dai ya kamata mu gane a daidai lokacin da ƙarfe bakwai na almuru tayi wadda wannan rana itace rana ashirin da tara. Sai almuru tayi sai muka duba wata sai muka gani sai mu ce to yanzu daren Ramadan ya shiga kenan ɗaya ga wata. A daidai wannan lokaci a America da England suna nan da rana pau bata faɗi ba. To da yaya zaka iya wajabta wa mutanen America da England da Holland da makamantansu waɗanda ke yamancin duniya azumi da watan da ya riga ya faɗi kafin ranar su ta faɗi abu ne mai sauƙi. Shine in rana ta faɗi a garin su in sun ganshi suma shikenan suyi. Idan basu gani ba fa wajibi ne su dawo suyi amfani da naku ganin. Wannan itace haƙiƙar da mai wannan littafi ya tabbatar mai suna Jawo hankalin musulmi gameda haɗuwar kan duniyar musulunci wajen ɗaukar azumi da kuma wajen shan ruwa. Wannan littafi ya kamata al'umman mu su same shi musamman malamai su karanta. Mutumin da yayi shi bayan kasancewar shi malamin hadisi mutumin mutumin ƙasar ainihin yamancin duniyar mu ne nan wato irin ƙasashen Tunisia Maghrib da sauransu. Ya rubuta wannan littafi ya kawo hadisai ayoyi fatoyin malamai sannan ya tabbatar da wannan fatawa itace daidai. Babu shakka wannan fatawa itace daidai kuma babu ainihin tantama akan haka. Allah maɗaukakin sarki ya taimake mu. Amma in ya kasance labari bai zo muku garin ku ba gameda ganin watan mutanen wasu gari har kukayi hukunci da abin da yake daidai gare ku bakuyin laifi ba a nan kuma. Allah maɗaukakin sarki ya taimaka. To sa'annan lokacin azumi ɗin shine daga fitowar alfijir zuwa ainihin faɗuwar rana. Ita faɗuwar rana ana gane ta ne da gwargwadan mutanen da ke nahiyar da kuke ganin sararin yamma suka ga rana ta faɗi. Amma mutanen da ke ƙasa waɗanda dai sun mamaye su da mutanen da ke ƙasa waɗanda gidajen sama sun shallake su bazasu yi amfani da cewa da sun ga rana ta ɓata ba. Domin ɓacewar rana a nan tana iya faruwa ƙarfe uku na rana gare su. Daga ƙarfe uku na rana ya zama sun daina ganin rana saboda mai saboda duk gidajen sama ne a yamancin garin saboda don haka mutanen da ke da sarari yamma da su waɗanda za su ga rana su ga ɗan ƙwayar rana guda haƙiƙatan ga ta sannan sai su ga ta ɓace wannan da shi ake hukunci. Haske da tarsatsin rana da ke kewaye da sasannin yamma baya ainihin hana a sha ruwa. Allah maɗaukakin sarki ya taimake mu. To idan lokacin shan ruwa yayi abin da yake ainihin aka fi so shine mutum ya sha ruwa da dabino idan bai samu dabino ba sai ya ainihin samu ruwa ko kuma wani ɗanyen abu sai ya sha ruwa da shi. Sannan sai sahur lallai annabi ya ainihin yabi sahur da cewa sahur abinci ne mai albarka. Wani na cewa in yaci sahur cikin shi na kumbura. Likitoci sun tabbatar da sirrin kumburar ciki da wanda yake cin sahur shine kwanciya da mutum keyi da zaran yaci sahur ɗin. Shine da zaran kaci sahur sai ka koma ka kwanta lallai cikin ka zai kumbura. Amma kaci sahur kaɗan kai ka komo sannan ka kwanta insha Allahu ta'ala cikin ka bazai kumbura ba. Ƙaddara zai kumbura ɗin malamai suka ce samu wani abu ko da ruwa ne ko da dabino ne wanda ana da yaƙinin shi ba da faffe bane da zai kumbura ainihin ciki ɗin. Daga cikin abubuwan da suka halatta mai azumi yayi akwai aswaki. Aswakin nan ko da ice ne ɗan yi kuma mai ɗaci ko bauri kuma ko da ɗacin shi ko baurin shi zai tafi zuwa ga maƙaƙi a wiya bai karya azumi ba ya halatta ayi amfani da shi. A ƙarƙashin wannan ya halatta ayi amfani da brush da ko da brush ɗin nan yana kai ga fitar da jini ga ainihin dasashin ka azumi bai karya ba ko da ɗan ɗanan ɗin nan yana bayyana a maƙoshi babu komai. Sannan ya halatta mai ainihin wato azumi yayi alwala a wurin alwalar kuma ya kurkura baki ya shaki ruwa wannan babu komai. Kaɗai ba a so ya kai matuka wajen shakar ruwa ɗin. Ya halatta mai azumi ya rungumi matar shi ya kuma sunbance ta sai dai malamai sunce wanda yake dattijo to ana so yayi taka tsantsan dangane da ainihin wannan irin magana. A in matashi matashi ana son yayi taka tsantsan dangane da rungumar matar shi ko kuma ainihin sunbantar ta. Saboda akwai hadisi wanda ainihin wato yazo yake ishara dangane da wannan magana ɗin. Sannan sai allura ya halatta ayi wa mutum allura ko wace iri ce. Na'am in muka ce kowace iri ce maganar tana da faɗi. Akwai allura mai ɗaci wanda za a yi maka allura a ɗuwawu ko a hannu amma sai kaji ɗacin maganin allurar ko maƙaƙin shi a wiya. Malamai suka ce ya halatta za a iya wa mutum idan suka yi saɓani allurar da zata zama ta tsaya a matsayin abinci gamara lafiya. Na'am idan mara lafiya ne da ke kwance ya galabaita ai dama ba a maganar azumi gare shi. Amma akwai nau'in rashin lafiyar da za a ce za a yi maka allura sai dai ita wannan allura zata tsaya matsayin abinci gare ka. Wasu malamai sun dubi cewa zata tsaya matsayin abinci sai suka ce don haka bata halatta ba. Amma da yawa malamai sun dubi ai abincin da ke karya azumi shine wanda ya shiga ta baka ko ta makamantan wurare irin waɗannan. Don haka wannan irin allura da ainihin wato ake yin ta don ta zama ta baiwa mutum ƙarfi kamar yaci abinci. Kawai nazarin da malamai suka yi shine idan har mai azumi lafiyar shi ƙalau zai je ayi mishi wannan allura dan yaji ƙarfi irin ƙarfin abinci a cikin shi to wannan bata halatta ba. Amma bai da lafiya ne amma rashin lafiyar bata kai ga hana shi azumi ba. To wannan gaskiya ya ainihin halatta ayi mishi wannan allura kuma bata karya mishi azumi ba. Sai ƙaho ƙaho ma baya karya ainihin azumi. Wannan itace ingantacciyar magana. Sannan sai ɗanɗana abinci ko ɗanɗana wani abu ko sanya tozali ko kuma ɗiga maganin ciwon kunne a kunne da ɗiga maganin ciwon ido a ido wanda ɗacin su galibi takan bayyana a maƙoshi. Suma malamai duk sun tabbatar da cewa basa ainihin karya azumi. Don zaka sanya tozali sai kazo kana jin ɗacin shi a cikin wuyan ka a cikin maƙoshin ka ko ka ɗiga maganin kunne sai ka riƙa jin ɗacin shi a wiya ko ka ɗiga maganin ciwon ido duk waɗannan ga ingantacciyar magana basa karya ainihin azumi ko kaɗan. Sai kuma wata mas'ala itace ta matafi. Matafi yana da yancin da zai yi azumi. Amma kuma idan har yaga azumin zai wahalar da shi babu lafiya sai ainihin ci abinci amma bayan sallah ya rama. Ba dan komi ba saboda cikin hadisi annabi yana cewa Yin azumi a halin tafiya ba biyayyar Allah bane. Wannan hadisi Bukhari da Muslims ka ruwaito shi kuma yana tabbatar da cewa yin azumi a halin tafiya bashi daga cikin biyayyar Allah. Sababin hadisin sai ya bayyana mana ba kai tsaye hadisin yake magana ba. Yana magana ga matafin da zai ɗauki azumi azumi ya galabaita shi. To yin azumi gare shi ba ainihin biyayyar Allah bane. Saboda sahabi da ya ruwaito wannan hadisin ya bayyana cewa kuma sunyi tafiya tare da annabi da sahabbai annabi da kanshi ya ɗauki azumi a halin tafiya sai dai da aka bashi labarin wasu sun galabaita sai ya karya. Na ɗaya na biyu wannan sahabi da ya Anas ya sake bada labari cewa suna tafiya tare da annabi da sahabbai wasu na azumi wasu basa yin azumi. Masu azumi basa ai ban ta marasa yin azumi da cewa ku malalata ne. Marasa yin azumi basa ai ban ta waɗancan da cewa kun fa yi zafin addini. Ashe kenan al'amarin yana komawa zuwa ga ikon yi ne. Zaka iya yin azumi a halin tafiya sai ka ɗauka bazaka iya ba sai ka sauke. A'a kaji zaka iya ka ɗauka ka tafi sai kaji ka galabaita sai ka karya. Duk wannan ya tabbata a cikin sunnan annabi Haka mara lafiya mara lafiya idan rashin lafiya ta kai bazai iya yin azumi ba an ɗauke mishi bayan sallah sai ya rama. Idan ko zai iya ga rashin lafiya ga azumi to wannan kuma babu lafiya in yayi haka. Sannan sai mace mai haila da matar da ta haihu jinin haihuwa yake zuba daga farjin ta. Su waɗannan an haramta musu yin azumi wajibi ne su rama yin azumin bayan sallah. Sai tsoho da tsohuwa waɗanda su kuma bazasu iya yin azumi ba saboda tsofa. To in aka ce musu suyi azumin bazasu iya a yanzu ba to balle ace bayan sallah su rama ai sun ƙara tsofa bayan sallah. In aka ce to zuwa faɗi su rama sun ƙara tsofa malamai suka tabbatar da cewa an yafe musu azumin sai dai su riƙa ciyar da abinci na mutum guda a madadin kowane azumi. Suna da hanya biyu ko su tara abincin bayan sallah su bayar gaba ɗaya ko kuma kowane yini su bayar da abincin mutum guda. Sai matar da take mai ciki ce nauyin ciki yasa bazata iya azumi ba. Sai matar da take shayar da ɗa wanda tsoṣonta da ɗa yake yi yasa bazata iya haɗa ga azumi ga tsoṣonta a ne ba. Ko kuma ita zata iya yin azumin amma fa da ta fara azumin nono zai ɗauke ɗan zai galabaita to an ɗauke mata azumi gaba ɗaya ita sai dai ta ciyar da ainihin abinci kenan. Allah maɗaukakin sarki ya taimake mu. Na daga cikin abubuwan da aka so mai azumi ya kula da su sune gaggauta buɗe baki da kuma jin kirta ainihin yin sahur. Sannan da shan ruwa kafin yin sallah ta Maghrib. Bashi daga cikin gwaninta ko kaɗan mutum ya ainihin wato ce bazai sha ruwa ba gaba ɗaya sai bayan yayi sallah. Allah ya kiyaye. Abubuwan da ke ɓata azumi su kuma sun ka su kashe uku. Akwai abin da ke ɓata azumi ya wajabta rama wannan ranar. Akwai abin da ke ɓata azumi ya wajabta rama wannan ranar da kaffara. Akwai abin da ke ɓata azumi shi kuma bazai wajabta ramuwa ba bazai wajabta kaffara ba sai dai zai wajabta zama a gidan wuta ga wanda bai tuba ba ko Allah bai gafarta mishi ba. Abu na farko shine abin da ke karya azumi kuma ya wajabta a rama wannan rana guda ɗaya shine amai. Idan mutum amai yazo mishi ba tare da ya ƙakaro shi ba babu komai. Amma mutum yana azumi ya ƙakaro amai kuma yayi aman to azumin ya karya. Zai rama wannan azumi guda ɗaya sannan zai istigifari ga Allah gameda wannan ganganci da yayi. Kuma bashi da damar yace tunda azumin ya karya bari ya ci gaba da cin abinci. A cikin hadisi annabi Wanda amai ya rinjaye shi ba komai a kanshi. Wanda ya ƙakaro amai lallai ne ya ainihin rama wannan rana. Wannan hadisi al'imamu Abu Dauda da Tirmizi da Ibn Maja da imamu Ahmad sune suka ruwaito wannan hadisi sahihi ne. Mas'ala ta farko kenan mas'ala ta biyu. Amai ya karya ya wajabta ramuwa da kaffara shine mutumin da yana
[Segment 4/5 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
azumi sai ya sadu da matar shi. Na'am, ya sadu da ita. Kun ga da shi da ita sukai jima'in. Amma shari'ar musulunci shi ta wajabta wa rama wannan ranar. Da kuma yin kaffara ta azumin wata biyu. Ko ciyar da miskinai sittin. Ko kuma 'yantar da bawa. Matar fa babu komai a kanta. Wannan ita ce ingantacciyar magana. Ramuwa da kaffara. Da muslim da al imam al baihaqi eh ad dara qutni su suka ruwaito wannan hadisin. Ramuwa da kaffara. Sai azumin da zai lalace. Amma babu ramuwa. Babu kaffara sai dai azabar wuta. Shine mutumin da ya ci abinci ko ya sha wani abu. Duk mutumin da ya ci ko ya sha da gangan azumin ya karye. Babu shakka akan azumin ya karye. Sai dai a cikin shari'ar musulunci babu wani nassi dalili na qur'ani ko hadisi ko haduwar malamai wanda ya wajabta mishi ramuwa balle kaffara. Duk maganganun da malamai sukai kiyase kiyase ne akan wasu kullallun nassoshi wadanda suna komawa zuwa ga wadancan nassosi ne na jima'i. A karkashin haka abinda hadisi ya tabbatar shine azaba ta gidan wuta ga mutumin da ya ci ko ya sha da rana tsaka. Azabar ta hanyar daukar mai wannan karya azumi. A juya kanshi kasa. Kafafuwan a rataye su a cikin wutar jahannama. A nemi mishi azaba. Jini na zuba daga jikin shi. Ta kowace kafa daga cikin kafafun idanuwan shi da hancin shi da bakin shi. Wannan ita ce azabar masu cin abinci ko shan abin sha da rana. Amma babin ramuwa babu ramuwa kuma babu ainihin kaffara akan su. Sai dai su tuba. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Idan jama'ar musulmi sun fahimci wadannan abubuwa. Mun tattauna mas'aloli dayawa a gurguje. Yanzu ya rage fidiya ina so in mana bayani dangane da fidiya. Da aka ce tsoho ya ciyar aka ce tsohuwa ta ciyar mai sha yauwa ya ciyar ko makamantan haka. Shin mai zai ciyar? Mai sauki ne abincin da yake ci kawai shi zai ciyar. Tuwo da miya ne zai iya ciyar da shi. Da bino ne zai diba ya bayar zai iya diba. A'a alkama ce zai diba ya bayar zai iya bayarwa. A'a ya kasance gurasa da miya ce koko wani abinci ne wanda ya shahara a wurin su. Duk zai ainihin iya diban wadannan ya bayar. Mara lafiya da yake sa rai ya warke har ya zo yayi ramuwar azumi babu ciyarwa akan shi. Sai ya bari kawai bayan sallah sai ya ainihin rama wannan azumi. Wadannan sune mas'alolin da na so in tattauna mana su a gurguje. Kamar yadda nace wannan ayi hakuri a karba da hakuri. Ba lacca ce mai zaman kanta ba. Na so ne in dan tunasace mu. Sai wasu abubuwa wadanda ya kamata in kara fadakarwa kamar guda hudu zuwa guda biyar. Mas'alar farko ita ce azumin nafila. Sunna ta soka da yin azumi so uku a wata. Ka samu ranar sha uku da sha hudu da sha biyar ga kowanne wata na kiyasin na kirgen musulunci. In ba haka ba ka rinka yin azumin duk ranar litinin da ranar alhamis. In ba haka ba ana son ka yau kayi azumi gobe ka ainihin ci. To wannan yana daga cikin abubuwa ko kuma azmomi wadanda shari'a ta so. Sannan shari'a ta kwadaitar kwarai da gaske game da yin azumin sha'aban wato shine wannan wata na sha'aban. Sai dai zaka iya azumtar watan gaba dayan shi. Zaka iya azumtar mafi yawancin shi. Abinda aka kyamata shine ka ki fara azumin tun a sha biyar din farko. Sai a sha biyar din karshe. To an kyamaci wannan saboda wasu hadisi wadanda wasu hadisai wadanda sukai ishara akan haka. Sai azumin ranar arafa. In aka ce yau musulmi na can suna hawa arafa a hajji to ana so lallai ka samu kayi wannan azumi in kana da iko mustahabbi ne. Sai dai dukkan wadannan azumin muka idan sunyi karo da ranar asabar to shari'ar musulunci ta hana. Ba'a yin azumin nafila a ranar asabar. Wannan hadisi ya hana dan haka da ace za'a zama yau tara ga wata na dhu hijja wato arafa kenan kuma ta zama asabar ce. A wannan shekarar ba za'a yi azumin arafa ba kenan. Idan da za'a ce kana yin azumi yau gobe ka sha sai kayi azumi yau gobe ka sha. Goben nan da kasha ita ce juma'a. Randa zaka tashi da azumi sai ta zama ita ce asabar bai halatta ba. Ba za'a yi ba. Wannan hadisi ya tabbata akan haka ba tare da ainihin tsawaita magana ba sai a kiyaye. Sannan sai abinda ya shafi azumi na kwanaki shida na shawwal. Wannan azumi sunna ce hadisi ya zo cikin sahihu muslim. Zaka iya yi bayan kayi azumin ramadan. Kuma koda ana binka bashi ko ana binki bashi ma'ana kinyi haila kinyi al'ada cikin watan ramadan ana binki kwana uku. Wannan kwana ukun kina iya jinkirtata. Amma wannan na kwanaki shida zaki iya yi tare da cewa ga wannan bashi da ake binki. Hikimar haka ita ce wancan bashi akwai dama a jinkirtashi a shari'ance. Shi ko wannan azumi na shawwal babu dama a jinkirtashi har wannan wata ya fita. Dan haka sai al'umma sai su kiyaye. To sai wata mas'ala. Wannan mas'ala a hakikanin al'amari a dayawancin jama'a sun san matsayi na akan ta. Ita ce mas'alar haduwar arafa da ainihin sallah. Babu shakka arafa tana haduwa a kasar mu da sallah tun yau wajen shekaru goma sha biyar ko fiye da haka da suka wuce. Amma in kazo zaka iya cewa tunda aka fara musulunci haka na haduwa a duniya. Inna ma ba'a sani bane a wancan lokacin. Kasa kaza a lissafin su yau laraba ce arafa. Dan haka sai suyi azumin arafa. Gobe alhamis sai su fita sai suyi sallar idi. A can makka kuma sai ya zama a daidai wannan ranar da suka dauka cewa ita ce arafa. Ashe jaji barin arafa ce. A ranar da suka dauka ita ce ranar sallah a nan kasar su sai ta zama a wannan rana ake hawa arafa. To a nan babu komai a kansu tunda basu sani ba. Babu kafofin yada labarai. Amma yanzu da ya zama kafofin yada labarai sun tabbata. Babu wani uzuri babu wani dalili da zai sa mun san cewa yau ake hawa arafa. Kuma muyi karfin hali wajen yin sallar idi a yau. Wannan ya saba ma sunna.
[Speaker seg4-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:0]
Hakika na al'amari na dade ina fadin wannan magana domin in kara samun yakinin wannan maganar. Shine kuka ga sanda na shigo nan ina yin waya. Wato na bugawa wani malami ne daga cikin malaman mu dake saudi arabia waya shine samir ibn amin az zuhairi wanda yayi tahakikin littafin bulugul maram. Sai na bijiro mishi da mas'alar wadda mun taba tattaunawa amma dan in kara tabbatar da abinda na sani din da kuma abinda naji daga gare shi shine na kara mishi tambayar. Nassi shai a yanzun ma abinda ya tabbatar min kenan cewa indai ya tabbata yau ne arafa ake hawan arafa mu musulmin nigeria mun sani. To bai halatta muyi sallah ba. Kuma bai halatta muyi yanka ba. Kuma in har akai sallah ko akai yanka bata yi ba. Kai tsaye kalmar da ya fadi kenan. Sai ya ce abin tambaya shine shi sarkin musulmi da yake bada wannan sanarwa yana sane da cewa yau ake hawan arafa nace kwarai da gaske. Sai na tunawa shi samir wani episode ma da ya faru akwai shekarar da haka ta faru. Shi sarkin musulmin muna can tare da shi. Sai samir ya ce kai fiyaya nace eh a lokacin shi sarkin musulmin ma yana makka. Amma kuma ya bada fatawar a nan a hau idi a rana arafa ma'ana ranar da shi kanshi yake hawa arafa a can. A ranar nan kuma ya sa musulmi su fito su hau idi a nan. To gaskiya saboda Allah wannan ko a wuraren tarurruka in anje nakan bayyana wannan shine matsayi na kuma shine abinda na gamsu da shi. Amma inda ba'a da masaniyar yau arafa ko rana kaza ce arafa da in haka ta faru babu komai. Dan haka bara muna tare a ranar sallah a makka. Wato bayan sallar nigeria da kwana daya. Muna makka a nan darul tauhid muna taro da su ali hassan da su ainihin mashhur. Sai na bijiro da wannan masalah. Sai ya ce wani ma yanzu ya bugo mishi waya ya ce daga wani gari lagos a nigeria. Sai nace ina jin wani abdul ra'uf sai ya ce shi ya ce yanzu ya bugo mishi. Amma yaji tsoron ma ya bashi amsa saboda yana tunanin yaya haka za'a tayu ba'a da labarin an hau arafa ne nace akwai labarin. Ya ce to yaya haka za'a tayu. To a nan dai hakikanin al'amari dukkan maganganun da suka karkata a kansu shine bai halatta musulmi yana sane da cewa yau arafa kuma ya hau idi ba. Domin wani abun sha'awa shine yau arafa ce a can. Ni in nasan haka zan iya jinkirta idi na koda a lissafi na ina ganin haka ne daidai. Zan iya jinkirta idin. Kuma in na jinkirta idin idin yayi. Inna ma mai samir ya ce mini ko a yanzu ya fadan wata kalma wadda ya fadan a wancan zaman da mukai da shi cewa sai dai wannan matsala ce da bai kamata a dauki zafi har ta kai ta haifar da fitina kamar yyadda nake fahimtar wasu mu suke neman su maida ita ba. Dan haka ga duk shekara in tazo koda bana kasar bana yin wata magana. In kuma ina kasar fa shine sai na ba samir labari cewa to ya kuke sai nace akwai wasu daga cikin jama'a ta ahlus sunna. Sukan ware su ki yin sallah a wannan rana arafa. Sai ya ce sai kuje kuyi sallah tare da su. Wannan shine abinda na gamsu da shi. Yan uwan mu mutanen kungiyar izala bangaren jos su kam sun riga sun tabbatar wa da kansu wannan karar din. Matukar arafa to baza su hau idi a wannan rana ba. Dan haka zaku ga ko a nan zaria sai in dauki iyalai na in tafi muyi sallar idi a wannan rana wadda ita ce suka ajiye za'a su hau sallar idi ba dan komai ba saboda an shallake an wuce rana arafa. Koda kuwa rasmiyan a hukumance ga abinda hukuma ainihin ta sanar. Na biyu ina bada shawara akan cewar mataki da hukuma za'a ta ce za'a ta dauka na karfi akan hana wannan. Babu shakka har wasu jami'an tsaro ba rana neme su mukai taro da wasu lauyoyi shin a dokar nigeria a ina ne doka an rubuce ta tabbatar da cewa mutumin da ya saba daga ranar da sarkin musulmi ya sanar a kama shi a daure shi. Babu amma bara anje an kamo mutane daga nan wajen ainihin soba da wasu kauyuka da wasu limamai anje an kai su har CID office. Dan haka shi kanshi shugaban CID da yake cewa babu fa wata doka da ta tabbatar da haka. Kadai abinda ya kamata shi yake cewa. Abinda ya kamata mutanen nan a zaunar da su a ji hujjojin su. In hujjojin su fa hujoji bane to anan ne za'a iya zama an kure su a ilmance. Sai a ta nuna wa mutane basu da wata gaskiya shikenan sai mutane su watse musu. Amma in ka kama mutum ka daure shi baka nemi dalilan shi ba gobe ya zama gwarzo a wurin mutane. Musamman yadda mutane ke son suji yanzu wanene zai fito yace baya yi da hukuma sai a ce to wannan shine shahidin zamani. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Na'am to jama'a kunji wannan. Sai wasu tambayoyi wadanda daga cikin su shine fitar da maniyi ko maziyi a halin mutum yana azumi. Gaskiya bai halatta ba. Kana azumi ka shafa azzakarinka ko ki goga farjin ki har maniyi ya fito dan kiji dadi ko saukin al'amari. Wannan bai halatta ba. Sai dai kuma in anyi haka baya karya azumi balle ya ainihin sanyawa azumi ramuwa ko kaffara. Ina fata an gane. Ko wancan yake magana ya ce kamar an dai na fahimci abinnan. Wannan na'urar da muka ce ana hadawa ce ana hada ta da computer ne koko sai da internet ba ruwanka da internet ai abun bai da alaka da internet. Ba da internet bane computer ce da na'urar kawai. Allah ya taimake mu. Bazan so wannan cassette ya kare ba sai nayi ishara zuwa ga mafi yawancin littattafan da na dogara da su a wannan lacca musamman na fadi wasu maganganu da dama wadanda mai yi wa ba'a saba jin su ba. Daga cikin littattafan ga wasu a gaba na akwai wanda salim da ali hassan suka zauna sukai. Gashi Wannan littafin ma yana daya daga cikin littattafan da Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi. Na'am wadannan sune takaitattun abubuwan da zan iya ainihin tinawa daga cikin littattafan da na duba insha Allahu. Wa alaikumus salam wa rahmatullahi. Na'am. Na'am na'am. Eh a hata wannan littafin ma haka ya tabbatar. Ai nabi hanya ne ta ilmi shine na ce littattafan da na duba. Gashi na a gaba na littattafan da na duba shi malam jalo yana daga cikin malaman da sun goyi bayan ayi sallar idi a ranar arafa. Kuma da raddi akan 'yan kungiyar izala bangaren jos. Shine ko a wannan din ma haka ne sai dai ban wafa ka da shi akan wannan mas'alar ba. Sai dai na bashi uzuri tunda malami ne akan babban abinda ya dogara da shi abubuwa ne banda na so shi tukuna. Ya dubi na farko haduwar kan mu a nan kasar wajen ibada. Na biyu ya dubi wadancan dake sabawa 'yan son zuciya ne da neman su yi suna kawai. Bane wa mutanen izala jos wannan zargin akan wannan matsalar. Ni ina fahimtar wani abu ne da suka ga a fahimtar su abinda ya dace kenan. Nima kuma sai wannan ya daidai da fahimta ta. Sai dai kuma abinda zan bada amsa game da mas'alar farko ita ce mai? Kokarin kan mu ya hadu a nan kasar wajen ibada. Kaddarar kan mu ya hadu a nan kasar wajen ibada. Amma kuma ya bayyana duk duniya mun saba wa sauran 'yan uwan mu na duniya. Abinda yake wajibi shine mu mi kokarin mu bi mafi yawancin mutanen duniya. Yaushe ne suke sallah? Wato matsalar ita ce duk nassoshin da za'a amfani da su za'a amfani da nassoshi ne duk kullallun nassoshi amma ya kamata a gane. Muna da masaniyar kasar saudi arabia alhazi har da 'yan nigeria. Za'a hau arafa laraba eh muna da wannan masaniyar eh to ai bai halatta ba. Domin kamar yadda nace abinda ke bani mamaki wani lokacin shuwagabannin namu da za'a ce sun ce za'a yi sallar rana kaza. Su fa suna can da su za'a hau arafa a can. Amma kuma sai su bugo waya cewa a nan mu mi idi. To gaskiya anan ne nake ganin akwai wajha ta nazar dangane da wannan. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Tambayoyin ne wasu eh gaskiya saboda Allah wasu tambayoyin suna abinnan. Wannan yana tambayar sunan na'ura wallahi nima na manta sunan na'urar jama'a. Bara kuma kamar zan siya fa na shiga jidda kamar zan siya kawai ban ma san me ya dauke ni ba. 'Yan dan device ne zaka ga kamar kamar 'yan kwallon 'yan kemaran nan da suke sawa ta ta internet webcam. In Allah ya so nan da kwanaki ashirin zan tafi saudi arabia ko ashirin da biyar in Allah ya so ina fatan zan siyo ta. Allah ya so. Wannan yana cewa to idan matar ce ta jawo jima'i fa tunda ance ita baza tayi kaffara ba. Imamul shafi'i shi ya zama lauyan ta akan haka imamul shafi'i shi ya tsaya wurin janjan akan cewa tunda nassi bai ce tayi ba ai annabi ya san namiji baya jima'i shi kadai. Amma duk da haka shi ya cewa shikenan Sai sallar tarawih banyi magana dangane da sallah tarawih ba.
[Segment 5/5 | 01:20:00–end]
[Speaker seg5-spk:0]
sunna ce ta annabi ba bidi'a bace. ayi ta a masallaci bayan an idar da sallar isha ko a dan jinkirta kadan ko tsakiyar dare ko karshen dare sunna ce daga annabi ta tabbata cikin hadisan bukhari da muslim babu shakka dangane da ya kamata mutane su gane a bace wadda take sallar nafila ce. Idan kazo masallaci kayi ta daidai ne in kuma ka tsaya a gida kayi daidai ne in kazo da iyalanka daidai ne. Amma dai abinda ake so limamai su tsaya suyi nazari shine dangane da sallar tarawihi ana duba yar jejeniya ko kuma dacewa da mutane ne. Raka'a nawa ce zamuyi bazamu takura mutane ba. Adadin kira'a nawa ne zamuyi bazamu takura mutane ba. Yadda za'ayi a cikin nashaɗi Sahabbai sukan yi raka'a goma sha ɗaya Kuma ayoyi ɗari biyu A cikin nashaɗi haka imam malik ya ruwaito da a cikin littafin shi Za'a iya ragewa daga adadin waɗannan ayoyin za'a iya rage adadin raka'o'in za'a iya yin raka'a ɗaya ma. In sallama raka'a ɗaya gyal kuma a tashi a tafi ba wanda zai mukabalance shi. Sai in ya maida abun irin salla ce ta wasa kamar yadda wasu ke cewa ai bari inje wurin limami kaza shi fijo ne yafi gudu. To wannan kuma shine abinda ba daidai ba amma lallai sallar tarawihi za'a iya raka'a sha ɗaya za'a iya yin raka'a eh goma eh tara za'a iya yin raka'a eh eh bakwai za'a iya yin biyar za'a iya yin uku za'a iya yin ɗaya mafi karancinta ɗaya mafi yawancinta sha ɗaya in anyi haka daidai ne babu laifi insha Allahu ta'ala. Wa'alaikumussalam Na'am to ku ku dan bari mu karasa waɗannan ɗin ina jin. Masu ciwon asma da ulser da waɗanda bazasu iya yin azumi ba saboda cutar yunwa gyambon ciki Ah waɗannan suna daga cikin cututtukan da malamai suka kira su cututtuka muzminai wato cuta wadda take daukar lokaci kafin ta warke. A karkashinta sai malamai suka ce azumi ya sauka akan me irin wannan cuta sai dai ciyarwa babu laifi sai ya ciyar insha Allahu. Yarinyar da bata fara al'ada ba wato jinin haila bai fara zuba ba sai dai gashi ta girma meye hukuncin wajabcin azumi akan ta ah ai dama alamomin balaga suna da yawa. Daga cikin alamar balaga akwai jinin haila akwai fitowar nono akwai fashewar murya. Alamomin balaga sukan bayyana ta hanyoyi da yawa dukkan ɗaya cikin alama in aka same ta ko sauran basu bayyana ba ya tabbata ya balaga yaro ne karami sai kuji muryar shi ta fashe ta zama irin ta manya nono ne ya tsiro mata jini ne yazo mata duk irin waɗannan alamomi ne da ke nuna ainahin wato azumi ya wajaba akan ta ko akan shi ko makamantan haka. Wai fidyar da tsoho zai bayar wajibi ne ko mustahabbi wajibi ne ai madadin azumin take. Sannan in kana da hali ya ya halatta ka taimaka wa tsoho zaka iya taimaka mishi ko babanka ne ko dan uwanka ko makaucinka ko ka haka siddan a dinga bashi yana ciyarwa ɗin babu laifi insha Allahu. Wasu tambayoyin sunyi kanana ƙwarai da gaske yadda Allah ya taimaka sai takaitattun bayani dangane da abinda ya shafi layya jama'a layya anayi ne da dabba mafi zaki wannan shine abinda malamai suka bayyana anfi fifitawa dan haka aka fifitawa rago fiye da hadaya hadaya ita kuma itace a wurin aikin hajji ita kuma malamai suka ce anfi so ayi da nama mai yawa shine me shine rakumi ko saniya. To ragon nan ba lallai ka yanka ɗaya ba zaka iya yanka ɗaya zaka iya yanka biyar zaka iya yanka ko guda nawa ne amma kada almu bazaranci da kuma wato neman suna ya bayyana a ciki dabba ɗaya ta ishi mutanen gida idan mutanen gidanka ka tashi yanka layya sai ka nufi sai ka yanka da nufin layyar gidan nan ce akace kowanne ɗayansu zai samu lada da gwargwadan kamar shi ya layya guda amma idan haɗa kuɗi ne za'ayi to sai dai a haɗa kuɗi mutum bakwai ko kasa da bakwai su sai saniya ko kuma su sai ainahin rakumi amma wannan kakkawa da mutane suke yi wato irin wannan haɗawa da akeyi wannan naman salla ne. Amma in in layya ce za'a haɗa to saniya kar a wuce mutum bakwai amma za'a iya yin mutum shida mutum biyar mutum hudu mutum uku mutum biyu amma kar a wuce mutum bakwai haka ɗin rakumi ne amma rago ko tinkiya ko a kuya baza'a hada mutum biyu ko mutum uku ba a halin sa ainahin haɗa kuɗi idan akayi wannan kar ta zama tana da karyayyan ƙaho kar kuma ta zama tana da mataccen ƙaho wanda yake duk ya lime mata saboda ta samu matsala tana karama ko makamantan haka. Sannan ana so ta zama mai lafiya wato wajibi ne ta zama mai lafiyayyin gaɓoɗi dukkan gaɓoɗin ta sun fita zara zara kar ya zama akwai watana kasar shiyar gaɓa kar ya zama akwai karaya a jikin ta ko watana kasa ta rashin ido ɗaya ko watana kasa ta kasancewar bata gani gaba ɗaya ko makamantan haka. Sannan ta zama tana da alamomi na lafiya a jika wato kar a ganta da alama ta tsumburewa ko alamar rashin lafiya ko rashin maiko ko ramewa ko makamantan haka to waɗannan in suka samu dangane da ainahin layya shikenan ana ana yanka layya ne bayan limanya yanka tashi. Daga nan Har zuwa bayan salla da kwana uku in ka samu hali zaka yanka ku kiyaye zaka iya yanka da daddare dan mutane suna ganin wai ba'a yanka da daddare a kasar hausa ba'a daurin aure da daddare babu wani dalili. Zaku iya tashi sallar isha ku ɗaurawa yarinya aure ko azo ayi karatun sahihul bukhari ko muslim da daddare karfe goma ace jama'a ku tsaya a ɗaura aure ya halatta saboda haka za'a iya yin yanka ma da daddare ina fata an gane matukar baka samu halin yi daga lokacin ba duk sanda aka samu sai aje ainahin sai a yanka sannan ba'a ɗiban nama a ba mahauci da nufin an biya shi kuɗin fiɗa ko makamantan haka sai dai a bashi kuɗin fiɗa daban sannan kuma sai a ɗibe abinda za'a bashi sadaka ko kyauta. Ah mutum yana iya ainahin cin layyar shi ya bada sadaka wata kuma ya bayar da ainahin kyauta a ita. Idan mutum yazo yanka zai iya share kanta iyalin shi ma'ana Ya Allah wannan a madadi na da mutan gida na iya abinda za'a faɗin kenan ya isa babu alaka akan sai mai gidan yazo ya dafa limamin da zai yanka uwar gida ta dafa mai gida babban ɗaya dafa uwar gida kaga mutane sun jeru haka an rirrike juna an dafa juna kamar tarago na jirgin kasa sannan limami ya yanka babu alaka akan haka. Allah madaukakin sarki ya taimake mu lokaci ya taho zamu dan amshi tambaya ɗaya biyu wadda zasu ainahin kara samu mana lokacin insha Allahu ta'ala na'am.
[Speaker seg5-spk:1]
Assalamu alaikum.
[Speaker seg5-spk:0]
Wa'alaikumussalam.
[Speaker seg5-spk:1]
Malam a karkashin wannan Na'am.
[Speaker seg5-spk:0]
Haka hakikanin suna an siyo ragon sai ya zama an iso da daddare sai a yanka shi tunda har lokacin ya riga ya yi za'a iya yankawa na'am wa'alaikumussalam na'am na'am. To Allah na'am mutum ne iyaye ko yan uwa suna azumi za'a iya rama musu bayan sun rasu a cikin watan azumi basu samu damar yin wasu kwanaki ba a'a ai shi sharaɗin wannan ramuwar ga wanda ya mutu shine ya warke ya rama dan haka daga randa ya warke to lokacin ne abun ya zama wajibi akan shi to sai bai warke ba kaga bai kai lokacin wajabci ba kamar mai bacci ne yana bacci har karfe biyar na yamma tayi baiyi salla a zahar da la'asar ba har yanzu salla a zahar da la'asar basu wajaba a kanshi ba sai ya farka ko sai kuma ya mutu daga baccin baza'a ce ai ana binshi salla ba saboda haka uwa ko uba sun fara azumi sai suka kwanta rashin lafiya cikin ramadan basu samu damar yin azumi biyar ko goma ba misali sai suka rasu ko za'a rama musu a'a azumin da ake ramawa mutum shine azumin bakance shima ramuwar ba dole bace shine yace zai yi azumi in bukata kaza ta biya kuma bukatar ta biya sai ya mutu bai samu damar yin ainahin azumin ba da bai samu damar yin azumin ba abinda yake wajibi akan shi ai abinda yake afwan mustahabbi akan magadan shi shine su rama mishi azumin mustahabbi ba dole ba. Wa'alaikumussalam wa rahmatullahi na'am na'am banga a ho ciyarwa zai iya ciyarwa almajirai kun gane almajirai masu ko dan kan zo ko dan da gwa da gwa zaka iya ciyar da su dan dama ciyar da miskini guda aka sa na'am na'am itikafi bamu yi magana a kai ba itikafi ibada ce wadda an samo ta daga annabawa da salihai tun na daɗin kuma zama ne a masallaci mafi karancin shi ya zama wuni guda shine daga salla asuba zuwa sallar magariba ko daga sallar magariba zuwa ainahin wato sallar asuba mafi karancin itikafi kenan mafi yawancin itikafi kuma bashi da iyaka itikafin nan ibada ce wadda ba'a yin ta sai a masallaci sai dai hadisi ya fassara masallaci da yace masallacin annabi da ka'aba da kuma masallacin birnin kudus mutane suna cewa to yanzu mutumin da yaso ya yi itikafi a masallacin sultan bello ko a masallaci kaza dake gari kaza yanzu bazai ba kenan eh bazai ba tunda hadisi yace ga inda akeyi to yanzu an hana itikafi kenan ba'a hana ba an faɗi mahallin shi ne wanda yazo a nassi da babu wannan nassi to za'a iya yin itikafi a dukkan masallatai kamar yadda bukhari ya faɗi amma nassi yazo to akal hankali da fatawa dole su hakura wannan shine ainihin abinda ya tabbata insha Allahu wa'alaikumussalam wa rahmatullahi wace na'am eh wajen yille yan baka iya da larabci ba sai kayi da hausa kwarai da gaske wa'alaikumussalam na'am ah in yan kala kato ne kam dan me zaka ciyar da shi ba annabi yace kada wanda yaci abincin ka sai mai tsoron Allah ai kaga a nan bazaka ciyar da su ba na'am wa'alaikumussalam na'am na'am kawai dai abinda na sani shine umumin cewa sallar nafila ana iya yin ta a zaune in anyi ta a zaune shikenan an samu rabin lada in nama an samu wani lokaci annabi sallallahu alaihi wa sallama ya sunnan ta zama a karshen ta amma cewa umumin ko akwai wani khususin nassi akan ayi ta ya abinda na sani kenan Allah ya taimaka lokaci na'am wa'alaikumussalam na'am shima kunga tunda muna da ilimi sabiki gama da cewa jiya ance sai karfe bakwai kenan yau in rana muka ga tayi dilim dilim karfe shida ai mu da kanmu munsan cewa yanzu muna da mi'yar muna da abun gwaji wanda mutanen da basu da shi kenan yanzu in muka sha ruwa karfe shida a yau munyi son zuciya tunda munsan tsakanin jiya da yau bazai yiwu ya zama awa ɗaya ba musamman ga yanayi ya canza anyi ruwa anyi jido da sauransu saboda haka kenan abinda ya dace a jiya sanda mukayi amfani
============================================================
[Part 2]
============================================================
[Segment 1/5 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
'Yan uwa masu sauraran mu da kallon mu. Kai tsaye da wadanda zasu saurare mu su kalle mu ta hanyoyin yada bayanai na fasahar zamani. Kuna jin mu ne kai tsaye daga kofar gidan Alhaji Tata mai kaji, Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi. Shahararren gidan da aka fi sani da number seven Zobe road, muciya sabon garin Zaria, jihar Kaduna, Nigeria. Dandalin da aka fi sanin shi da nadin salafiyya ko kuma ofishin albani. Yanzu da muke magana jama'a mun shiga daren asabar wanda daidai da daren ashirin da tara ga watan Sha'aban, hijirar annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallam na da shekara dubu daya da dari hudu da ashirin da tara. Daidai da ashirin da tara ga watan August, shekara ta dubu biyu da takwas. A hakikanin al'amari muna da taken wa'azi ne kamar guda biyu ko guda uku wadanda ya kamata mu gabatar da su a wurin nan a cikin wannan wata na Sha'aban. To amma Allah madaukakin sarki cikin rahamar shi ya ta saukar da ainihin rahama tashi ta ruwan sama. Yau kusan kwana goma da suka wuce duk sa'ar da aka sa wa'azi sai ya zama daidai da lokacin wa'azin yayi daidai da Allah yana saukar da rahama ta ruwan sama. Allah mun gode. Allah ya albarkace mu a cikin abubuwan da yake saukar mana na ruwan sama din. Abu na biyu kamar yadda na fadi yanzu gashi ana ainihin danyin yayyafi a daddafe a daddafe zamu samu mu ga cewa ko zamu gabatar da daya daga cikin wa'azozin a yau. Idan haka ta faru babu laifi. Gobe sai mu gabatar da ainihin topic na biyu wato wa'azin mu na biyu. Idan gobe anyi ruwan sama to jibi sai a zo. To amma in jibi ma anyi ruwan sama to kuma sai ku saurari sanarwar da zata biyo baya a karshen wannan ainihin wa'azin. Ma'ana dai muna da dar muna da wa'azi a nan a yau da gobe da jibi insha Allah. Idan har ba'ayi ruwan sama ba to wadannan wa'azozin kazo zaka ji su. Amma a yau zamu dauki daya daga cikin mas'alolin ne wanda zamu ainihin wa'azantar da al'ummar musulmi akai. Sannan nan abu ne cewa Allah madaukakin sarki ya aiko annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallama da musulunci wanda yake da rukuni guda biyar. Sannan Allah madaukakin sarki ya aiko annabi da imani wanda yake da rukunai guda shida. Sai kuma ihsani wanda yake da rukuni guda daya tak. Wadannan rukunai guda biyar wadanda in aka hada su su ake kira musulunci. Al-imam al-bukhari da muslim da Ahmad sun ruwaito daga sahabi Abdullahi dan Umar da sahabi Abu Huraira Allah ya kara musu yarda cewa musulunci an gina shi ne akan diraku ko genshikai guda biyar. Daga cikin wadannan guda biyar manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallama ya ambaci saumu Ramadan azumin Ramadan. Shi azumin Ramadan azumi ne wanda Allah madaukakin sarki ya farlanta shi da nasoshi na al-kur'ani da sunna. Sannan malaman musulunci tun daga nada har zuwa yanzu suka hadu akan cewa azumin Ramadan farilla ne. Azumin ya kusanto bai wuce nan da sauran kwana daya ko kwana biyu ba za'a fara yin azumi insha Allahu ta'ala. Tafiyar mu da muke yi ta kiran al'umma zuwa ga al-kur'ani da sunna ingantacciya tasa zamu ainihin tattauna dangane da bayani akan ainihin azumi. Taken wannan ainihin wa'azi namu insha Allahu ta'ala ya kamata ya zama azumi ibadar zumunci. Mun kira azumi ibadar zumunci ne saboda wata aya wanda Allah madaukakin sarki ya fade ta a cikin al-kur'ani a cikin suratul Baqara a inda Allah yake cewa An wajabta muku yin azumi na watan Ramadan wato an wajabta muku yin azumi. A nan ayar tana magana akan wajabcin azumi ne. An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta shi ga al'umomin da suka zo kafin ku. Wannan ayar ta hada zumunci tsakanin mu al'ummar annabi Muhammad sallallahu alaihi wa alihi wa sallama da sauran al'umomin baki daya wadanda suka gabata. Tun daga kan al'ummar annabi Nuhu har zuwa kan al'ummar annabi Isa Baki dayan mu Allah ya kulla wannan zumunci a tsakanin mu cewa azumi shari'a ce kuma azumi farilla ne. Akan mu kamar yadda ya farlanta shi a ga 'yan uwan mu wadanda suka gabata. Zumuncin farko dake cikin ayar kenan. Zumunci na biyu sai Allah madaukakin sarki ya fade shi a pakaice Daga cikin hikimomin da suka sa Allah ya shar'anta azumi din shine dan a samu tsoron Allah. Shi wannan tsoron Allah yana samuwa a cikin zukatan masu wadata da zukatan wadanda suke da kuncin yalwata. Ba dan komai ba saboda daidai lokacin da mai wadata yake cika cikin shi ya koshi yaci abin da yake so na marmari ya kuma sha abin da yake so na marmari. Yayi jima'i da kyakkyawar matar shi a cikin tsalelen gidan shi a sanda yake so. A daidai wannan lokacin Allah ya hada shi da shi da talaka da wanda bai da abinci da wanda bai da abin sha da wanda bai da matar da zai jima'i da ita ya hada su baki daya yace ya shar'anta musu azumi din. Yanzu an samu zumunci anan wajan ibada imu imu din kenan. Ma'ana tsakanin yalwa dai wane da talaka wane tsakanin mai sarautawa ne da bafade wane tsakanin talaka wane da alhajin birni wane. Allah ya hada zumuncin su baki daya yadda yunwa take karkarar cikin talaka haka take karkarar cikin alhajin birni. Anan zumunci ya samu wannan zumuncin Allah sai yi ishara akan sakamakon da zai haifar shine ta kawa da tsoron Allah. Yayin da masu wadata basu san irin yunwar da talakawa suke sha ba saboda suna da wadata, saboda suna da abinci, saboda suna da abin sha, suna da kayan marmari. Talaka yunwa ke karkarar shi da ainihin rana tsaka. A daidai wannan lokacin sai aka shar'anta azumi din ga dukkan musulmi balagagge. Wannan zai sa masu wadata da masu hali su dandani irin yunwar da talakawa ainihin suke sha. Wannan zai haifar musu da ciyarwa fisabilillahi a cikin watan Ramadan. Wannan ciyarwa fisabilillahi a cikin watan Ramadan na tsawon wata guda dindi zai sabar musu da dabi'ar ciyarwa wanda ake fatan su koye ta koda bayan azumi ya wuce su dore akanta. Sannan wannan zai sabar musu da tunanin wace hanya ta kamata a samar wa da talakawa wanda yake zata rayar da su wanda zata fitar da su daga kangin da su suke samun kan su. Domin so da dama talaka bai shan wahalar azumi dan musamman a Nigeria idda ake halin hau. Dama rabi azumin ake rabi tokarawa. Kadai dai babu lada ne domin babu niyya. To yayin da ya zama mai kudi ko mai wadata ko mai wadatuwar abinci ya zama yana jin irin wannan yunwar. Wannan zai haifar mishi da wani tunani wanda ake fatan ya dauki ainihin mataki a cikin rayuwar shi insha Allahu ta'ala. Wadannan bayanai jama'a nayi su ne a matsayin shimfida dangane da tabbatar da dalilin da yasa na kira wannan wa'azi na yau da cewa azumi wato ibadar zumunci. Dan haka kaji azumi ibada ce da Allah madaukakin sarki ya shar'anta ta dan mu bauta mishi. Sannan mu kuma ta haifar da zumunci tsakanin mu imu imu sannan kuma ta tabbatar da zumuncin dake tsakanin mu da al'umomin da suka gabata. Tsarki da daukaka sun tabbata gare ka ya Allah. Asalin kalmar as-siyamu a larabci abin da ake nufi da ita kamewa ma'ana rike baki ko rikewa kamar fi kaulihi ta'ala kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fadi a cikin al-kur'ani Allah yace Maryamu take cewa nayi bakancen azumi ga Allah mai rahama. Me take nufi da saumu anan shine kamewa ba zata yi magana ba. Dan haka koda kamewa kayi alkaurin yau ba zaka yi magana ba sai kace yau ina azumi. Me kake nufi da azumi yau ba zaka yi magana ba. Akan ce akan ce ainihin wato doki mai azumi. Me ake nufi da doki mai azumi? Ana nufin a harshen larabci dokin da ya kame baya tafiya. Dan haka asalin ma'anar kalmar azumi a cikin harshen larabci itace kamewa. Amma a cikin shari'ar musulunci ma'anar ta kamar yadda malaman fikihi suka fadi suka ce kamewa daga ci da sha da kuma saduwa da matar aure ko kuma kuyanga da niyya wdd take anyi ta saboda Allah fi jami'in nahari a cikin dukkan yini wato tun daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana. Abin da yasa muka fadi haka Allah ne da kanshi yace Idan kuka dauki azumi tun lokacin da alfijir ya fito to ku cika azumin naku har zuwa dare. Me ake nufi da dare? Shine sanda ainihin rana ta fadi. Hadisi yazo sahihi a cikin littafin sunanin Tirmizi annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallama yake cewa idan dare ya taho daga ainihin nan haka yayi ishara zuwa ga ainihin gabas. Ya ainihin wato taho zuwa ga yamma ya fadi wato duhu ya taho ya taho tun daga ma'ana rana ta dinga taowa tun tana haske har tazo ta fadi. Duhu yazo ya hadu rana ta fadi sai annabi sallallahu alaihi wa sallama yace mai azumi azumin shi ya kare. Dan haka matuƙar rana ta fadi ka sha ruwa ko baka sha ruwa ba azumin ya kare. Dan haka ba gwaninta bace wai kace kai bazaka sa koda dabino a bakin ka ba har sai anyi sallan magariba. A'a gwaninta itace bin sunnar fiyayyen halitta sallallahu alaihi wa alihi wa sallama. Al-imam Malik ya ruwaito a cikin annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallama ya bayyana cewa na daga cikin abubuwan da aka samu a wurin annabawa tun na farko shine gaggauta buda baki. Da zaran rana ta fadi ladan ya kira sallah ko bai kira sallah ba. Da zaran rana ta fadi hasken rana yana nan ko kuwa domin rana gudan ta ake nufi. In gudan ya fadi sai kaga jajaja jajaja a yamma. Wannan jajaja jajaj baya hana ka sha ruwa matuƙar an tabbatar da ta fadi. To shikenan azumi ya kare. Koda kaci gaba da yin azumi ba azumi kake ba. Nan kuma wata shari'a ce ka dora akanka. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Dangane da falalar azumi kuwa al-imam Muslim ya ruwaito hadisi sahihi daga sahabi Abu Huraira Allah ya kara mishi yarda Abu Huraira yace Allah da kanshi ne ya fadi wannan hadisin jama'a shi ake kira Allah yake cewa duk aikin da dan adam yake nashi ne sai dai azumi anan sallah da kake yi ta waye ta Allah ce. Zakka da kake ta waye ta Allah ce. Amma Allah ya ware azumi a cikin wannan hadisi yace azumi nashi ne. Amma sauran ibadoji kuma naka ne. Ba wai yana nufin cewa naka ne amma yana nuna darajar da azumi yake da ita akan sauran ibadojin. Sai yace shi kam azumi nawa ne dan haka ni zan bada sakamakon shi. Manzon tsira sallallahu alaihi wa alihi wa sallama sai ya tsai da wannan hadisi al-qudusi sai kuma ya cigaba da bayani da sharhi da ta'aliki. Annabi yake ta'aliki yake sharhi akan wancan magana ta Allah madaukakin sarki. Annabi yace na rantse da Allah wanda ran Muhammadu yake a hannun shi bashin bakin mai azumi yafi kanshi a wurin Allah fiye da tiraren Me ake nufi da bashi? Shine abin da ba wari ba ba doyi ba ba karni ba ba kanshi ba ba hamami ba sai ace bashi. Asalin wannan tiriri ne yake fitowa daga cikin uwar hanji saboda ta jima bata ci abinci ba. Sai irin wannan tiriri sai yazo sai ya bushe baki sai ya zama bakin ba wari yake ba dan ba'a ci abinci ba. Abinci ne ke jawo ainihin warin baki to ba'a ci abinci ba. Ba karni yake ba ba doyi ba amma me yake yi bashi yake saboda sirka kincen dake fitowa daga uwar hanji wadda babu komai a cikin ta. To irin wannan bashi da zaka ji baki yake yi. Allah yafi son irin wannan fiye da tirare mafi daraja a aljanna. Shine tiraren Tirare mafi daraja a aljanna shine Saboda haka kaji Allah yake cewa 'Yan aljanna in suka sha ruwa ko suka sha wani juice ko wani fruit ko wani drink ko furar aljanna ko menene na aljanna in suka sha irin takwa takwan nan da in kaga ma shan fura zaka ga yafi kowanne zaki na karshe sai dai kuma wani lokacin kayi karo da tsakuwa to na 'yan aljanna aka ce shi kam tiraren al-misk ne kuma. Tiraren al-misk shine tirare mafi daraja. Alfaza zai yake cewa Alfaza zai a cikin ishiriniya cewa ike ya manzon Allah Inma kafi halittu baki daya ai wannan ba abin mamaki bane. Ba abin mamaki bane halittu baki daya manzon Allah yafi su ba abin mamaki bane. Sai yace domin ai al-misk asalin tiraren al-misk wani bangare ne na jinin barewa. Domin tiraren al-misk iri biyu ne. Akwai wanda yake asalin tiraren al-misk shine baushi yake kira tiraren Juda, kashin magen Juda. Shine al-misk. Sannan akwai kuma wanda zaka gani gashi na masu saida man habbatussauda suna siyarwa a kwalba su ririya. Ka ganshi jawur kamar jini. To wannan irin tiraren da kake ga masu habbatussauda suke siyarwa shine alfaza zai yake buga misali da shi cewa ai asalin shi jinin barewa ne. Jinin barewa aka diba akayi wannan Amma kuma daga baya sai ya waye gari yafi me yafi barewar da jinin ta daraja. Me ake nufi? Manzon Allah mutum ne daga cikin mu. Mutane ne suka haife shi suka rene shi amma kuma sai waye gari yafi su daraja saboda daraja din daga Allah take. Ina fatan mun gane? Abin da nake so inyi hujja da shi anan ka gane darajar tiraren al-misk ka gane muhimmancin tiraren al-misk amma duk da haka bashi da bakin mai azumi yake yana hamami. Wannan hamamin Allah yafi son shi fiye da me? Fiye da tiraren al-misk. Da wannan hadisi ne wasu malaman fikihi Allah ya gafarta musu suka ce makaruhi ne mai azumi yayi asuwaki ko ya goge bakin shi. Suka ce saboda yin asuwakin yana kawar da wannan bashi wanda Allah yake so. Sai imamu Shafi'i yace kunyi kuskure. Ai shi wannan bashi da bakin mai azumi yake ba yana fitowa daga asalin bakin bane. Tiriri ne daga uwar hanji dan haka ko anyi asuwaki wannan ainihin bashi yana nan zai dawwama. Dan haka ba makaruhi bane yin asuwaki da safe ko yin asuwaki da rana ko da hantsi ko da la'asar ko da azahar ko kusan magariba. Ba makaruhi bane yin amfani da brush da ma clean ko close up ko wanene wajan yin broshi ka tsaftace bakin ka koda rana tsaka koda almuru koda bayan sallah magariba ko azahar ko yaushe ne ba makaruhi bane. Koda kuwa kana cikin yin brush da ma clean din sai ta kai brush din naka ya zama ya dargaje mai yiwuwa ya fasa maka baki har jini ya zuba. Azumin ka bai lalace ba. Koda bayan ka gama yin brush din zaka je kana jin dandanar ma clean ko close up ko kuma wani abu makamancin haka daban kana jin dandanar shi a cikin makoshi makoshin ka ba makaruhi bane. Amma dai abin da ake so kayi taka tsantsan kayi kokarin tsaftace bakin ka ba tare da ka ainihin wato bashi ya wuce ba.
[Segment 2/5 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
amma dan kaji ainihin turrishe daga ciki babu komai insha Allahu ta'ala Jama'ar musulmi, wannan hadisi na Abu Huraira yana nuna mana darajar ainihin azumi ba dan komai ba saboda kunji wannan irin dan wari wari da bakin mai azumi yake Allah da kanshi ma yana son wannan warin kaga azumi yana da daraja a cikin wata riwaya ta wannan hadisi wadda itama al imamu Muslim ne yayota manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace mai azumi yana da halaye guda biyu wadanda zai shiga na farin ciki halin farko shine idan yayi sha ruwa da zaran mutum ya sha ruwa sai kaji ya samu wata kwanciyar hankali sai kaji ya ji wata natsuwa sai kaji yana samun wata ma'ana yana samun wani ruhi daga cikin shi yana hakan nan sai kaji yana murna yana farin ciki wannan yana daga cikin darajar azumi sannan na biyu ranar kiyama in ya hadu da Allah zai yi farin ciki domin abunda yasa ladan mai azumi to ladan mai hakuri ne kunsan babu abunda ya kai hakuri lada hakuri shi kadai ne ibadar da in har kayi shi ka samu ladan shi to ranar alkiyama tun kudo maka za'a rinka yi ba tare da hisabi ba Allah yace masu hakurin Allah ya tashi basu lada baya kirgawa to manzon Allah sallallahu alaihi wasallama a cikin hadisin shi ya kwatanta azumi da hakuri dan haka azumi ma ladan shi baya kirgawa tun kudo wa ake ai wannan na daga cikin sirrin da a baya kaji manzon Allah yake cewa Allah yace azumi nashi ne domin kowace ibada ana iya kwange a cikin ta banda azumi sallah kana iya kwange ko ka rige ta ko ka kara ta ko kayi ta wata saboda alhaji wane ko saboda malam wane ka kyautata ta darriya ana yi ko ba'a yi ana yin zakka da sadaka darriya ana yin hajji darriya ana yin umara darriya ana yin kaza darriya amma riya bata shiga cikin azumi in kaje ka shake cikin ka da tuwo ka fito kace kana azumi Allah yasan karya kake kaga ba azumi kake ba kaga ba'a riya eh in ma dai da gaske kake azumin kazo kana wata hamma ta karya kana wani yaushin baki eh saboda me saboda a gani waye ga yunwar dan zaka iya cika cikin ka kuma kazo kana yaushi kamar ashe wannan ke nuna kenan cewa da Allah yayi azumi nashi ne saboda babu wanda yasan sirrin azumi tsakanin mai azumin da azumin sai Allah dan haka dan uwa karka sake a barka a baya dangane da yawaita ibada ta azumi musamman ta nafila Allah ya taimake mu
[Speaker seg2-spk:1]
amin
[Speaker seg2-spk:0]
sahabi Huzaifatu dan Yaman Sahibus sirri Allah ya kara mishi yarda shi ko cewa yayi naji manzon Allah yana cewa fitintinu da dan adam zai rinka samu game da iyalin shi ace kana da mata sai ta zama fitinan niya ce sai Allah yasa maka hakuri da ita kana da mata sai Allah ya dora mata larurar rashin lafiya sai ka zama mai hakuri game da ita kana da mata sai zantana da wani uzuri sai ka zantana da hakuri game da ita wannan irin fitinar da ta same ka game da matar ka kai hakuri to zaka ji irin wadannan matsaloli da zasu rinka shiga suna fita wanda zasu rinka afkar da kai a wani hali wanda baka so ba zaka ji darajar azumi da zata bayyana game da wannan mutum yana da dukiya dukiyar sai ta saka shi a wata fitina wadda wannan fitina zata ja mishi yin wasu abubuwa wadanda ba daidai ba ko kuma shi da kanshi fitintinin da zasu rinka faruwa shi da kanshi a rinka samun na kasa game da ibada da fitintinin da zasu rinka samun shi game da 'ya'yan shi da matsalolin da zai rinka samu game da makwabcen shi yana cutar da makwabcen shi ko yana na kasa hakkin makwabcen shi wadannan irin zunubai wadannan da matar ka zata sa ka rinka yi zunuban da zai sa dukiyar ka ta sa ka rinka yi zunuban da ranka da kanka zai rinka saka ka a ciki zunuban da 'ya'yan ka da makwabcen ka zasu sa ka rinka shiga ciki azumi zai rinka kankare maka ire iren wadannan zunubai ma'ana wasu matsaloli da zaka rinka shiga game da matar ka ko matan ka har ya zama kana zalinta ta ko kana zalinta su lazimta azumi zai kankare maka lazimta sallah lazimta umarni da kyakyawa da hannun mu muna zai kankare maka sa'annan fitintinin da zaka rinka shiga game da dukiyar ka fitintinu da zaka rinka shiga game da 'ya'yan ka da makwabcen ka ya kai kana zalinta ko kana tauye hakkin su yin azumi da tsai da sallah da tsayawa akan yin umarni da kyakyawa da hannun mu muna yana sa ainihin Allah madaukakin sarki ya kankare maka wannan ainihin hadisi al imamu Bukhari da Muslim suka ruwaito shi to ko wannan hadisi zai zama hujja a shar'ance kenan tunda dai mutum yana kula da azumi yana kula da sallah ya rinka zalintar matar shi ko matan shi a'a ko wannan dalili ne akan cewa matsalolin da mutum yake shiga game da dukiyar shi ya kai ga ya ci haram ko ya jinkirta sallah ko ya wani abu na dukiyar shi wanda bai halatta ba yace to ai ba komai tunda yana yin sallah a'a abunda ake nufi abubuwan da suka zama kura kurai wadannan da suka fi karfin ka har ka aikata game da matar ka azumi zai kankare kura kuran da suka fi karfin ka game da dukiyar ka kura kuran da suka fi karfin ka game da 'ya'yan ka ko makwabcen makwabcen ka sune ake nufin yin azumi da tsai da sallah yana kankare maka su Allah madaukakin sarki ya taimake mu har wa yau sahabi Huzaifa Allah ya kara mishi yarda yace manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallama yace azumi garkuwa ce ita garkuwa itace abunda mai yaki yake tun kudawa sanda aka kawo mai sara ko suka ko duka wato wato abunda zai sa sanda aka kawo mishi sara sai ya mika wani kwano haka sai a daki kwana manzon Allah sallallahu alaihi wasallama sai ya kwatanta azumi ga musulmi a matsayin haka ma'ana azumi garkuwa ne game da zunubi azumi garkuwa ne game da sabawa Allah azumi garkuwa ne game da shiga wutan lahira ashe azumi yana da daraja jama'a duk abunda zai tsare ka daga sabon Allah a nan duniya ranar lahira ya tsare ka daga shiga wuta wannan abun jama'a bai kamata ayi sakaci game da shi ba manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace azumi garkuwa ce dan haka sai manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace to kaga wanda ya samu irin wannan garkuwa ta ibadar azumi to lallai kada ya sake ya saki bakin shi ya rinka batsa kana azumi kana batsa kana maganganu irin na banza na zinace zinace da makwabcen su manzon Allah yace karka yi haka sannan yace karka rinka yin wauta karka rinka shashanci karka rinka yin rashin kan gado ma'ana a same ka da natsuwa kaga natsuwar jiki da natsuwar baki in ta samu zata bayyana wa wanda ya gan ka cewa lallai wannan yana cikin wata ibada ne sai manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace da ace wani zai zo ya samu mai azumi na azumi ya ainihin neme shi da fada ko ya zage shi shi mai azumin kan ya tanka mai in ma har ya zama dole to ya bude baki yace ni azumi nake ni azumi nake ma'ana ina azumi ina cutar niya da ibada dan haka maganar fada babu maganar ashar babu maganar zagi babu idan kaga haka zata gagara fa sai ka tashi sai ka bar gurin ina fatan mun gane
[Speaker seg2-spk:1]
na'am
[Speaker seg2-spk:0]
jama'a wannan hadisi hadisi ne ainihin sahihi wanda al imamu Bukhari ya ruwaito shi to idan kun fahimci wadannan abubuwan da kyau sai kuga cewa to ashe babu shakka ibada ta azumi ibada ce mai girma wadda yake bai kamata ayi ainihin yin sakaci game da ita ba babu shakka akwai hadisai masu dinbin yawa wadanda ke bayani akan falalar azumi wadanda inda zamu ta karkare mu ce sai mun koro su a nan to babu shakka zamu ainihin samu falaloli masu dinbin yawa amma saboda falalolin nasu bari mu gani manzon Allah sallallahu alaihi wasallama ya cigaba da cewa ina rantsuwa da Allah da raina yake a hannun shi wadannan sune ake kira a hadisus sifat hadisan da manzon Allah yake fadin wata sifa ta Allah har ya sha alwashin rantsuwa da ita manzon Allah yace na rantse da Allah wanda raina yake a hannun shi wannan hadisi dalili ne akan Allah yana da hannu to malaman ahlus sunna baki daya tun daga na farko har na karshe sun yarda cewa Allah yana da hannu amma basu yarda ace Allah yana da hannu iri kaza ba basu yarda ace Allah bai da hannu ba basu yarda a fassara hannu din da karfi ba sai su ce tunda Allah yace yana da hannu to fassara a cewa hannun Allah yana saman hannun su in aka ce to yaya hannun Allah yake sai ka ce kwatanta mana sai ka ce ai ba abu ga misalin Allah babu abunda yake irin Allah dan haka yaya hannun yake bamu sani ba to tunda baka sani ba kace babu sai kace a'a akwai to akwai yaya yake sai kace baka sani ba to tunda haka ne fassara shi kace karfi sai kace a'a dan haka malaman ahlus sunna wannan itace ka'idar muna gayyatar ku darasi na musamman wanda wannan darasi zamu yi shi tsawon watan azumin ramadan dinnan sai dai darasin matan aure za'a yi wa da karfe goma na safe zuwa karfe sha biyu na rana kullun tun daga farko har ashirin da biyar ga azumi insha Allah sai dai bayane da zamu zo muyi a karshen wa'azin nan a wannan masallaci namu mai suna al jami'us salafi wato masallacin nan namu na juma'a na kasuwar muciya daga karfe goma na safe zuwa karfe sha biyu zamu karantar da matan ahlus sunna littafin Allah ya gafarta mishi da yake karatun za'a sa shi a ne maza zasu iya zuwa su zauna can gefe ma'ana can nesa inda yake sakon zai rinka kai musu amma dai koda basu samu halarta ba duk karatun da aka yi wa mata za'a dauka a kaset zasu ji to a mukaddimar karatun akwai wata doguwar shimfida wadda take zata kwakushe wajen kwana bakwai na azumi ko kuma ma goma ta farko in ma ba'a shiga goma ta wyia ba wanda wannan mukaddimar baki dayanta na shiryo ta ne don in bayyana menene akidar malaman ahlus sunna na farko game da ayoyi da hadisan sifofin Allah ma'ana ayar da Allah yake cewa jirgin ruwan annabi Nuhu na gudana akan idon mu ayar da Allah madaukakin sarki yake cewa hannun Allah yana kan hannun su ayar da Allah madaukakin sarki yake bayyana cewa irin wadannan ayoyi da ke bada labarin wata sifa ta Allah yaya malaman ahlus sunna suka yi musu yaya suke fassara su bincike ne nayo na musamman wanda yake kowa zai samu dan ka'idar da muka dauka itace duk abunda zamu rike muna karantawa kowa muna so shima ya samu dan haka ranar farko da kaji za'a fara karatun za'a zo za'a siyarwa da mata wannan ainihin muzakkira wato wannan za'a siyarwa da maza kuma kowa ma zai iya mallaka bahasi ne game da ta farkin malaman ahlus sunna na farko game da yadda suke mu'amalantar ayoyin da ke sifanta sifofin Allah madaukakin sarki da kuma irin wadannan hadisan a cikin hadisin Bukhari da Muslim manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace idan daya bisa uku na dare ya rage sai Allah ya sauko daga saman bakwai zuwa sama ta daya yace wa zai bauta min in karbi ibadar wanene zai roke ni in biya mishi bukata manzon Allah yace haka Allah zai yaya malaman ahlus sunna suka fassara wadannan hadisan to mu hadu da kai a wurin wannan darasi insha Allahu ta'ala zaka samu bayane akai mu dawo kan hadisin nan da muke magana da manzon Allah yace ina rantsuwa da Allah da raina yake a hannun shi wannan hadisin dalili ne akan Allah yana da hannu sai manzon Allah yace bashin da bakin mai azumi yake yafi kanshi a wurin Allah fiye da turaren manzon Allah yace mai azumi ya bar abincin shi wato Allah yace mai azumi ya bar abincin shi ya bar abun sha ya bar jima'i da matan shi ta aure da rana tsaka saboda wa saboda Allah sai manzon Allah yace sai Allah yace lallai azumi nawa ne ni kuma ni zan bada saka makwancin shi amma sai manzon Allah sallallahu alaihi wasallama sai na kalto Allah yake cewa duk ibada daya idan musulmi yayi in aka tashi za'a ninka ladan wannan ibada goma sai a bashi a madadin wannan guda daya ishara akan cewa idan kayi azumi kwaya daya ladan azumi goma za'a baka wannan lada ladan keke da keke kenan lada a matsayin na ibada sai irin ladan da muka fadi na dazu lada na maghfira shi kuma sai a danno maka ba tare da allissafa ba ina fatan an gane kamar yadda na fadi wannan hadisi al imamu Bukhari ya ruwaito shi Muslim ma ya ruwaito shi a cikin aljanna akwai wata kofa sunan ta kofar koshi masu kula da azumi kawai zasu shiga aljanna ta wannan kofar ranar alkiyama wato wannan kofa ce ta kasaita ba kofa ce ta kofa ce ta wasu mutane na musamman wadanda koda masu shiga aljanna da basu baiwa azumi muhimmanci baza su shiga aljanna ta wannan kofar ba to wannan dalili ne akan cewa kenan shiga aljanna ta wannan kofar to daraja ce daraja ta musamman misali yanzu idan ka baro gwagwalada ka tinkaro Abuja wato daidai iya na Abuja kenan inda manya manyan su wa gabanin kasan duniya in zasu shigo Najeriya ta nan suke shigowa akwai wata kofa guda daya itace ake shigo Najeriya ta ita idan kai Yakubu Bayi ne sai a kada ka yi dama ka zagaya amma in shugaban kasa ne yazo ko wani babban mutum sai a bude mai wannan kofar to shigo Najeriya ta wannan kofar mukami ne amma fa duk daya ne duk Najeriya zaku shigo amma kai sai a kada ka dama Yakubu Bayi yi can amma in shugaban kasa ne special sai a ce in shigo ta nan amma fa duk Najeriya zaku shigo haka wanda yake kula da sallah zai shiga aljanna mai kula da zakka zai shiga aljanna mai kula da biyayyar iyaye zai shiga aljanna mai kula da azumi zai shiga aljanna amma tashi kofar ta musamman ce kofar mukami ce ina fatan an gane to sai manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallama yace idan ba masu baiwa azumi muhimmanci ba ba wanda zai shiga aljanna ta wannan kofar in aka je aka taro a dandalin alkiyama za'a cewa 'yan aljanna su masu azumi sai a ce ina masu kula da azumi in ba su ba ba wanda zai shiga aljanna ta wannan kofa Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallama yace idan suka shiga aljanna ta wannan kofar ba wanda zai sake shiga aljanna ta wannan kofar tunda sun kare masu azumi wannan hadisi sahihin hadisi ne al imamu Bukhari da Muslim suka ruwaito shi sahabi Abu Sa'id al Khudri Allah ya kara mishi yarda yace wanda duk yayi azumi wuni guda saboda Allah Allah zai nesanta fuskar shi daga wuta tsawon shekara sabain ranar lahira wato duk sanda kake azumi indai ka ne dan Allah ne to ana kara nesanta ka daga wuta ana kara nesanta ka daga wuta amma sharadin sai in kayi saboda Allah in ba saboda Allah kayi ba to duk abunda kayi saboda shi to zai kusantar da kai wuta ne kuma amma in kana son ka kara nesa daga wuta to in kazo yin azumi kayi shi saboda Allah wannan hadisi sahihin hadisi ne shima al imamu Bukhari da Muslim suka ruwaito shi sahabi Abu Umama al Bahili Allah ya kara mishi yarda shi ko cewa yayi daga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace wanda yayi azumin wuni daya saboda Allah Allah zai sanya wani gwalalo wani wagegen rami tsakanin shi da wutan jahannama wannan ramin fadin shi kamar ainihin tsakanin sama da kasa ne duk sanda kayi azumi saboda Allah wancan hadisin yana cewa za'a kara challara ka ka kara nesa da wuta tsawon shekara sabain amma fa azumin wuni guda to yanzu in kayi azumi guda talatin saboda Allah ku buga talatin su sabain tsawon wadannan shekarun za'a kara challara ka nesa daga wuta to kuma kazo kayi kazo kuma kana yin azumin litinin da Alhamis kazo kana yin azumin Abu Zarri azumin kwanaki uku a cikin wata rana kun sha
[Segment 3/5 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
uku, sha hudu, sha biyar. Kullun kake kara yin azumi dan Allah, kana kara nisa ne daga wuta. Haka wancan hadisin ya fadi. Wannan kuma sai manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya ce sai a rinka sa tsakanin mutum da wuta wani wagegen rami ne, fadin shi kamar fadin sama da kasa. Duk sanda ka yi azumi saboda Allah. Shi yasa jama'a a musulunci ba'a yin ibada kace bari in yi dan in batawa wane rai. Wuta zaka tafi. Bari in yi dan in farantawa wane rai. Wuta zaka. Ana yi ne dan Allah. Ya abun yayi wa jama'a dadi oho, abun ya bata wa jama'a dadi ya bata musu oho. Kai dai wa kayi wa Allah. Kuma me kake nema a wurin Allah. Yarda Allah kake nema wanda yarda Allah tafi aljanna girma. Saboda yazo a cikin hadisi sahihi wanda al imam al bukhari da muslim suka ruwaito. Manzon Allah ya ce sai 'yan aljanna sun gama shiga cikin gidan aljanna. Sai Allah madaukakin sarki sai yazo ya bude musu fuskar shi sai su gani. Sarki ya tabbata ga Allah. Malam mai badu'ul amali ya ce mumine zasu ga Allah a ranar alkiyama insha Allahu. Idan suka ga Allah sai su manta da duk ni'imar da suke ciki. Yaku 'yan shi'a da kuka ce baza'a ga Allah ba sai ya ce ku kukayi asara kune baza ku ga Allah ba ranar kiyama. Amma mumine zasu ga Allah. Saboda Allah ya ce Wasu fuskoki suna cikin saboda zasu ga Allah a ranar alkiyama. Akidar musulmi baki daya itace baya yiwuwa a ga Allah a nan duniya. Wanda duk yace ya ga Allah a nan duniya kafiri ne. Karya ne ba'a gani. Hadisi sahihi cikin Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya ce Ku saurara. Baza ku ga ubangiji ba har sai kun mutu. Duk wani shaidani ko wata shaidaniya da yazo yace yana ganin Allah to zindiki ne arne ne. Ba'a ganin Allah a nan duniya jama'a. Ba'a ganin Allah. Amma a ranar lahira mumine zasu ga Allah. To idan suka ga Allah kamar yadda hadisi ya bayyana yaya fuskar shi. Sai su manta da duk ni'imar da suke ciki kuma. Saboda ni'ima idan babba tazo takan share karama. Haka ne ko ba haka ba?
[Speaker seg3-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg3-spk:0]
Kana cikin cin kuli kuli aka miko maka soyayyan nama. Eh? Kuli kuli ni'ima ce amma soyayyan nama fa? Ina fatan mun gane. Saboda haka yayin da dan aljanna ke cikin ni'imar aljanna. Idan yaga Allah sai kuma ya manta ma da aljannan yanzu yaga babban ni'ima. Sai kuma Allah ya ce yaku 'yan aljanna akwai abunda kuke so wanda ban muku ba sai suce a'a babu. Sai Allah ya ce akwai saura. Sarki ya tabbata ga Allah. Ma'ana ni'imar ma kai baka ma san ni'imar ba ma. Ina fatan an gane. Ni'imar ma akwai abunda na ni'ima one sai suce ai sun gama kure ni'ima sai Allah ya ce akwai ni'imar da tafi wanda kuke ciki. Sai suce mecece sai yace na yarda daku bazan sake fushi daku ba har abada. Shine wannan hadisi yana cikin bukhari da muslim manzon Allah ya fassara wannan aya da tace Yarda Allah tafi aljanna girma. Dan in Allah ya yarda da kai har abada baya fushi da kai. Dan haka duk sahabban manzon Allah nan da Allah ya ce Sahabban nan baki dayansu da ansarawansu da muhajiransu Allah ya ce ya yarda dasu sun yarda dashi. Shi yasa 'yan shi'a sun fi kowa asara a duniya. Mutanen da Allah ya ce ya yarda dasu sun yarda dashi. Allah baya Allah baya jawo abunda ya riga ya zartar. Duk wanda Allah ya ce ya yarda dashi to har abada Allah bazai sake fushi dashi ba. Allah ya hada wadannan sahabban baki daya da nassin al'kur'ani. Karantar suyuti a cikin littafin Aje mujalla ba mujalla ake magana ba dan shi'a littafi ake magana karatu. Kaje ka karanta kaga suyuti yace da zaka ce ka rantse da Allah duk sahabban manzon Allah na aljanna. Yace rantsuwar ka tayi daidai. Saboda Allah yace ya yarda dasu sun yarda dashi. Yayi musu tattalin aljannatai. Wadanda koramu iri iri ke gudana a karkashin su. Allah ya ce wannan shine babban rabo. Yace kuma in sun shiga zasu zauna dindindin har abadan abidina. Waye kai darajar sahabbai? Babu. Sai annabawa. Idan kun gane wannan jama'a. Yarda ta Allah madaukakin sarki ita bawa yake kokari ya nema. Dan haka ya kai mai saurare na. Duk abunda zakayi kace bari in yi in bata wane rai to ba sunan shi ibada ba sunan shi shirka. Duk abunda zakayi na ibada kace bari in yi dan in farantawa wane rai ba sunan shi ibada ba sunan shi shirka. Ibada ana yinta ne Ina fatan an gane. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. To sa'annan wannan hadisi da muka gama karantawa na abu umama al imam tirmizi ya ruwaito shi da isnadi sahihi. Sannan har wayau abu umamatul bahili Allah ya kara mishi yarda. Kaji wani hadisi wanda al imam nasa'i ya ruwaito shi da isnadi sahihi. Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam ya ce Ina umarnin ka da hijira. Me ake nufi da hijira? Mun karanta a cikin sharhin sahihul bukhari in baku manta ba tun a sharhin hadisin farko a fathul bari a wurin karatun mu a markazu salafiyya a tudun wada. Inda ibnu hajirin yace malamai suka ce hijira iri biyu ce. Ko dai hijira daga kasar kafirci ko kasar da aka hana ka addini zuwa ga kasar musulunci ko kuma kasar da aka barka kayi addini. Ko kuma hijira daga sabon Allah zuwa ga biyayyar Allah. Manzon Allah ya ce to lallai dai ina umarnin ka da yin hijira domin babu abunda ya kai darajar hijira. Idan suka kuntata maka baza kayi addini a gari kaza ba. Ko a unguwa kaza. Ko a kauye kaza. Ko a gida kaza. Ko a kasa kaza. Ko a kasuwa kaza. Ko a wuri kaza. Sai ka hada ina ka ina ka sai ka bar gurin. Manzon Allah ya ce to irin wannan hijirar babu abunda ya kai ta lada. Sanda abubakar ni siddiku ya gina masallaci a kofar gidan shi. Sallah yake yana karatun kur'ani. Matan kuraishawa suzo su kewaye gasu kafirai mazajensu kafirai kuma suna sauraren kur'ani. Suna jin gaskiya. Sai mazansu suka ce haka bazata sabu ba. Aka zo abubakar ya kawo fitina, abubakar ya raba kan mutane, abubakar ya kade zukatan mata suna zuwa suna sauraren kur'ani. Ko dai abubakar ya rufa masallaci in ba haka ba za'ayi yaki za'a zubar da jini. Kafirai akwai cika baki. Abubakar yace to baza'ayi yaki ba, baza'a zubar da jini ba. Amma bazai daina sallah ba bazai daina karatun kur'ani ba. Sai ya dibi kayan shi ya zuba a jaka. Sai ya hada ina shi ina shi sai ya bar kasar makka. Mahallush shahid kenan. Duk inda aka hana ka addini rabu da wurin. Koma inda zakayi addinin ka ko a kasuwa ce. Ko a gidan haya ne. Ko a gidan ku ne. Ko a ina ne. Ko a kasa ne. Ko a unguwa. Domin lallai sai anyi addini jama'a. Tsantsar addini na Allah ne. To in har tsantsar addini na Allah ne dan me za'a ce ka zauna kana addini a takure. Sanda aka takura mutane a makka. Annabi cewa yayi kuyi hijira ku tafi kasar habasha. A kasar akwai wani sarki baya yarda ayi zalunci. Wane sarki ne wannan shine sarki najashi. Ba musulmi bane. Kirista ne. Reverend father ne koma bishop ne. Amma bai yarda ayi zalunci ba. Kowanne irin addini kake bi bazai bari a zalunce ka ba. Dan haka manzon Allah ya hada su su abu salama, su ummu salama aka dauki ja'afar dan abu talibin. Aka nada shi shine komandan tafiyar. Ja'afar kuma saurayi ne ya haddace al'kur'ani. Ya iya da'awa. Ya goge. Da aka je aka ainihin gabatar dasu. Ga wasu bakin kuraishawa ranka ya dade. Sun zo daga kasar makka. Garin da aka ce mutumin nan ya fito yace shi annabi ne Allah na magana dashi daga saman bakwai. Da suka shigo fada su basa sun kuyawa kowa sahabbai basa sun kuyawa. Basa gaisuwa irin wannan tamaguza da ake wa sarakuna basa yi. Gaisuwa ce irin ta musulunci ayi sallama a baka hannu. A samu falala. To da yake baza su iya zuwa suje suyi sujuda gaban shi ba ko suyi mai irin wannan gaisuwar. Balle shi sarki najashi yana da wata ka'idar ma. In ma kai gaisuwar sai dai ka koma da Shi ba'a juya mai baya saboda kasaita. To sahabbai sai yace bazasu iya ko daya cikin wannan ba sai da suka shigo fada sai suka koma gefe guda suka tsaya. Da suka tsaya sai hankali ya bayu zuwa gare su. Ga wasu samari can farare kar. Da gyamma. Da raunna. Da yankakkun wandina. Su wanene? Sai aka ce ai bakin kuraishawa wanda aka gaya maka ne sai yace to su matso. To yanzu kunga tunda su ance su zo ne. Ba su suka zo ba. To in suka zo zasu nuna tasu al'adan ne da suka zo sai suka yi mishi sallama irin tasu. Sukayi mishi gaisuwa. Kamar soja ne yanzu in ka gayyato shi yazo office dinka bazai cire takalmi ba. Bazai durkusa ba. Yana zuwa sarawa zai kibda haka Sannan yaga dama ya miko maka hannu. Gaisuwar shi zai fara bazai yi taka ba. Idan kun gane wannan da kyau jama'a. Wadannan sahabbai da suka zo. Sai sarki najashi yace menene ke wurin ku? Ku fadi bayani ku fadi sako. Wane sako kuke dauke dashi? Abun mamaki jama'a wannan itace ranar farko da aka fara fassara al'kur'ani da wani yare a duniya. Sarki najashi baya jin larabci. Su kuma basa jin yaren shi. Ja'afar ibn abi talibin ya zauna ya karanta suratu maryam gaba dayanta sai da ya sauke ta. Da ya sauke ta mai fassara yayi wa sarki najashi fassara baki dayanta. Sarki najashi yana rike da wani tsinke a hannun shi sai yace na rantse da Allah da ya aiko annabi isa da gaskiya. Yace baka kara ba baka rage ba game da abunda muka karanta a cikin injila ta gaskiya game da annabi isa. Duk abunda ka fadi a cikin karatun nan naka muma haka yake a littafin mu. Jama'a. Wannan kaiwa matuka ce wajen me? Wajen bayyana da'awa da kuma sakon musulunci. Amma me suka je yi? Hijira suka je yi. Dan haka jama'a musulmi yanzun aka hana shi yin addini a unguwar musulmi. Idan unguwar kristoci zasu barshi yayi addini sai ya koma unguwar shine abunda sahabbai suka yi. Makka kasa annabi ibrahim ce. Kasa annabi ismaila ce. Amma kafiran makka suka ce baza'ayi sallah ba. Amma sarki najashi yana krista yana bishop ko Yace azo kasar shi ayi sai sahabbai suka tafi can. Saboda haka ku kiyaye jama'a. Hijira tana da daraja. Amma hijira tana da matakai da ake bi kafin ayi ta. Sai in an hana ka addini ko an hana ka yada addinin na daya na biyu hijira nau'i ta biyu itace barin sabon Allah zuwa ga biyayyar Allah. Ko kuma barin wurin da yake akwai fasikanci a cikin shi. Suwa ga komawa ga wurin da babu fasikanci dan Allah yace Yanzu mutanen da ke zaune a marar raba hanyar jos nan in ka tafi kaduna kullun naje ina cewa nakan ce musulmi a wannan garin suna da hadari ko dai su bar garin. Ko kuma a koru karuwai da masu neman karuwan garin. Amma in ba haka ba bai halatta musulmi ya zauna a wannan garin ba. Ya haifi 'ya'ya. Ga gidan musulmi ga gidan liman ga gidan karuwa. Kaga motoci sunyi parking sun hana ku wucewa. Ba sun tsaya gyara bane ba sun tsaya shan mai bane sun tsaya zinace zinace ne neman karuwai kuma musulmi ne suma. Ka tafi zaka shiga abuja kaje tafa haka take. Ka tafi marar raban rido ko ka tafi marar raban ina duk gasu nan haka suke. Direbobin motocin galibin su musulmi ne. Kashi 90 da tarbi bisa dari. Me suka tsaya yi ba sallah a zara suka tsaya yi ba zina suka tsaya da karuwai. To irin wadannan garuruwan bai halatta musulmi ya zauna ba. Domin me? Domin fushin Allah sai ya sauka akan garin gaba daya sai ya shafe ka ba dan kayi laifi ba sai dan kama kwaftaci masu laifi. Manzon Allah cikin hadisin bukhari da aisha ta ruwaito. Yace nan gaba wasu mutane zasu dauro yaki zasu zo zasu yaki ka'aba. Kafin su iso kasar makka sai Allah yasa kasa ta hadiye su. Sai aisha tace kasa ta hadiye su manzon Allah yace kwarai. Tace to ai wasu kasuwanci suka taho. Wasu sun taho aikin hajji ne wasu umara suka taho. Manzon Allah yace kasa zata hadiye su tun daga na farkon su har na karshe. Da mai aikin hajjin da kowa me yasa sai Allah yace sai manzon Allah yace sai a tashe su kowa akan niyyar shi. Mai aikin hajji ya tashi yana labbaika Allahumma labbaika tayi kyau kenan. Mai cin kasuwa kuma da burgaman shi zai tafi cin kasuwa a lahira kenan ko? Tunda kowa zai tashi da niyyar shi ne. Wanda kuma yazo rusa ka'aba fa ya tashi shima gashi zai tafi lahira rusa ka'aba su hadu da Allah a daidai. Dan haka jama'a ba'a zama wurin da fasikanci yayi ka tutu akwai bacin tarbiyya. Akwai bacin tarbiyya. To sannan sai yace Karinka kula da azumi Babu ibadar da takai ladan azumi. Karinka yawaita sujuda ga Allah. Domin babu wata sujuda kwaya daya da zakayi wa Allah. Sai Allah ya daukaka darajar ka saboda wannan sujuda. Duk sanda ka fadi kayi sujuda ga Allah sai Allah ya daukaka darajar ka. Kuma jama'a ku kiyaye sujuda ba sai a sallah kawai ba. Akwai sujuda ta shukur. Godiya ga Allah in wani abun albishir ko albishir ko annashuwar yazo maka zaka iya faduwa kayi sujuda wannan sujuda ce. Akwai sujuda ta tilawa al'kur'ani tana nan wurare goma sha biyar a cikin al'kur'ani. In ka karanta zaka yi sai ka fadi kayi sujuda. Sannan akwai sujuda ta ga Allah in ka tuno kayi wani laifi. Sai ka fadi kayi sujuda kana kuka. To wannan ya tabbata ruku'u ko sujuda aya tana fadin ruku'u amma sujuda ta tabbata kuma. Saboda haka zaka iya yin wannan. Almajirin shi ibnu al kayim yace wani lokacin ibnu taimiya ya karanta wani abun ya kasa fahimta sai ya fadi ya yi sujuda yana kuka ga Allah. To jama'a kunji. Duk sanda kayi sujuda saboda Allah sai Allah ya share maka wani laifi. Wannan hadisi kamar yadda na fadi hadisi ne sahihi al imam nasa'i ya ruwaito shi. Sahabi abdullahi dan amru dan as Allah ya kara musu yarda ya ce Da kur'ani. Da azumi. Zasu ce ci bawa ranar alkiyama. Wannan hadisi yana tabbatar mana da cewa ce to gaskiya ne. Mu ahlussunna mun yarda akwai ceto sai dai bamu yi wa ceton yarda irin yaddar da kristoci 'yan mushen sukai mishi ba. Ko kuma irin yaddar da 'yan dariku sukai mishi. Su kam kristoci sun dogara ne cewa kawai suyi tashar holiyar su. Mai ceto na nan zuwa a karshen duniya shine annabi isa. Wannan ba daidai bane an kuskura fassara. Bakin ba'a jashi daidai ba. Kai tashe ganta ka ka mai ceto na zuwa. A'a ba haka nassin yake ba. Na daya kenan. Su kuma masu bin darikun sufaye kowa ya ayyana ma wanda zai cece shi. Wane ni shi zai cece ni. Har ma wani shaidani yace zai je da da babban riga. Zai rinka zuba ina shi ina shi a cikin aljihun babban riga. To wannan karya ne. Ceto a wurin musulmi shine ceto gaskiya ne. Amma ceto na Allah ne saboda Allah ya ce Kace ceto na Allah ne baki daya. To ceton na Allah ne. To shi zai ba wanda ya ga dama daga cikin bayin shi. Kuma ya ayyana wadanda ya ga dama a ce ta. Dan haka ku kiyaye abun babu dari kanci babu dimokuradiyya a ciki. Bawai wane zai tsaya bane ya rinka diban ina shi ina shi yana zuba a aljanna ba haka ake ba. Allah zai ce wane na baka izini. Ka cece suwa ne. Shi Allah shi zai ayyana wanda zai ce ta. Ya ayyana wadanda za'a ce ta. Dan haka ku kiyaye ku karanta littafin Ceto matsala ce wanda ya tabbata ahlussunna sunyi ijma'i akan ta. Amma ceton a nan duniya bazaka ce ni wane ne zai cece ni ba. Sai dai babu laifi kace Allah ka sa
[Segment 4/5 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker unknown]
Annabi Muhammad ya ce ya cece ni Don me? Don ya tabbata cewa Annabi zai yi ceto. Hasali ma manzon Allah shine yake da Manzon Allah zai cece kowa da nassin ainihin hadisin shi. Zai cece annabawa da manzanni da aljanu da mutane da kwari a ranar da Allah yayi fushi fushin da bai taba yi ba kuma ba zai sake irin shi ba. A ranar da ba wanda ya isa ya je wurin shi ya roki alfarma a ranar sai fiyayyen halitta dan Amina baban Zara Sallallahu alaihi wasallama. Shi kadai ne ya ce zai je ya fadi gaban Allah yayi yabo yayi kirari da wasu kalmomi na zikiri ya ce a yanzu ma ban san su ba sai mun je kiyama za'a koya muna. Rigijigabji in ba Annabi ba ba wanda za'a yi wa darasi a dandalin kiyama. Ya ce za'a koya mai kalmomin da zai ambaci Allah da su a ranar. Duk da shi na musamman ne fa sai Allah manzon Allah ya ce sai a bar shi sai Allah ya ya rabu da shi tsawon lokaci sannan sai ya ce ya Muhammad Daga kanka ya Muhammad in ba ran nan ba Allah bai taba fadin sunan shi da haka ba. Don ranar kiyama kowa an cire mai mukami ne. Manzon Allah ne aka bar shi da nashi mukaman amma wajen suna a ranar kiyama ba wanda za'a ce Annabi wane. Kowa tsuren sunan shi za'a kira. Da wane da wane kan waliyyi ba'a zo ba babu labarin su Annabawa ma Nuhu Nuhu Allah zai kira shi Nuhu Musa Musa ran nan kowa Annabi da kanshi ran nan Allah ba zai ce mishi ya Annabi ba amma karanta kur'ani ba inda Allah ya kira shi ya ce ya Muhammad amma sauran annabawa kur'ani ya kira su Waye kai manzon Allah? Babu dan haka in ka kama kafar wala ka rabu da shi ka kama manzon Allah shine Dahir Saboda haka manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama ya ce yana daga kanshi sai ya ce Ya Allah al'umma ta manzon Allah baya kungiyanci manzon Allah baya darikanci kaga su ka cewa su kayi shehin darika zai tsaya yan darikar shi kawai zai zuba. Amma manzon Allah shi cewa yake ya Allah al'umma ta dukkan mutumin da ba al'umma ce ta dame shi ba inashi inashi suka dame shi wannan mutumin bashi cikin sunnan manzon Allah Sai a ce me kake so sai ya ce a zo ayi hisabi to wannan shine matsayi mafi girma matsayi mafi daraja da Allah madaukakin sarki yake ce mishi da daddare ka tashi kayi sallah. Yin haka zai sa Allah ya sa ka a wani matsayi wanda babu irin shi matsayi abun yabo. Sai manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama a cikin hadisi sahihi da Imamul Muslim da Imam Ahmad suka ruwaito manzon Allah ya ce duk sanda aka kira sallah ka zo kayi salati ka zo ka ce Ya ce duk sanda kayi wannan addu'a bayan an kira sallah kayi salati manzon Allah ya ce ya tabbata zan cece ka. To yanzu ya tabbata ke dan manzon Allah zai yi ceto ya tabbata da wannan hadisin da muke karantawa kur'ani zai yi ceto azumi zai yi ceto wanene ya ayyana su Allah ne ya ayyana su a bisa harshen manzon Allah to mun yadda. To kada kai kuma ka ce to ai shehi na shima zai yi ina hadisin da ya ambaci shehin ka? Babu to tunda babu eh to ka ja baki kayi shuru kayi fatan da kai da shehin ka Allah ya sa ku haye. Ina fatan mun gane? Saboda haka jama'a kun ji wannan hadisi yake cewa azumi zai yi ceto al'kur'ani zai yi ceto za su cece bawa ranar kiyama. Ku ji abun da azumi zai ce wa Allah ranar alkiyama ya ubangiji ni na hana shi cin abinci ni na hana shi ya biya bukata da matar shi da rana saboda yana azumi. Allah ka bani izinin in cece shi. Jama'a kun ji al'kur'ani a ranar alkiyama zai yi magana. Kun ji azumi zai yi magana kur'ani sai ya ce na hana shi bacci da daddare ya zauna ya tashi yana karatun kur'ani yayi tarawihi yayi tahajjud yayi tafsiri ya ja baki ya saurari karatu ya saurari tafsiri duk wannan kur'ani kake saurare sakamakon haka baka yi bacci ba ko? To ranar alkiyama sai kur'ani ya ce Allah kayi mun arziki kayi mini taimako in cece shi. Manzon Allah ya ce sai a basu ceton wannan bawa. Saboda haka jama'a in azumi yazo zagewa ake idan goman karshe tazo sai ka kara zagewa manzon Allah a cikin hadisin Bukhari Aisha tace in goman karshe tazo sai ya tsuke wandon shi ba ma sauran ya kwana da iyali i'itikafi zai shiga karatun al'kur'ani sallar tahajjud zikirori babu wasa saboda wannan wata ne wanda yake babu watan da ya kai shi daraja. Jama'a wannan hadisi sahihi ne Imam Ahmad da Imam Tabarani suka ruwaito shi. Kun ji wannan kenan to azumi nau'i nau'i ne jama'a amma nau'i biyu sune nake so in bada karfi a nan. Nau'i na farko shine azimin farilla da azimin nafila azimin farilla da azimin nafila shi azimin farilla jama'a shi kuma iri uku ne azimin farko na farilla shine azimin ramadan azimi na biyu na farilla shine azimin kaffara wato kana azimi sai ka je ka sadu da matar ka to zaka rama wannan azimin kuma zaka yi azimi guda sittin na kaffara to yin wannan azimin dole ne ko kuma kai kisan kai da ganga da mantuwa da mantuwa ba da ganganci ba to zaka ainihin yi azimi guda sittin a jere ko kuma ka ce daga yau in ka sake saduwa da matar ka kamar ka sadu da uwar ka to Allah ya ce maganar banza kake kuma karya kake kuma baka yi ladabi ba don ba'a kwatance da uwa to ya zaka yi ka gyara wannan aure tsakanin kai da wannan mata da kai mata wannan wulakanci shine kayi azimi na wata biyu dindi to duk wannan azimin na kaffara to azimi ne na farilla a rantsuwa kai ka ce wallahi ba zaka sake zuwa gidan wane ba kuma sai uwar shi ta mutu wajibi ne a musulunci ka je kayi mishi ta'aziya to yanzu sai ka je to in ka je dole kayi azimi to irin wadannan azomomi na kaffara to wajibi ne suna daga cikin azomomin farillai sannan nau'i na uku na azimi shine azimin da ake kira azimin bakance wai bahaushe ya ce bakin ka ne ya ce kana zaune lafiya ka ce ya Allah in ka bani kudi na dinka rigar sallah sabuwa bana ni ko zan yi azimi sai Allah ya baka kudin to yanzu wannan azimin wajibi ne kayi shi amma yazo a cikin hadisi sahihi da Muslim ya ruwaito manzon Allah Sallallahu alaihi wasallama ya ce bakance baya sa Allah ya baka komai dan ka ce ya Allah in na samu kudi zanyi azimi wannan ba zai sa Allah ya baka kudin ba sai manzon Allah ya ce kawai Allah ne yake fitar da wani abu daga jikin marowaci mai wa da bakin ka ya tashi fadi cewa kai ya Allah in na samu kaza zan ciyar da miskinai goma da can baka ciyar da kowa kuma a cikin ilimin Allah Allah ya kaddara dama zaka samu ko baka yi wannan bakance ba kaga abincin miskinai ne Allah ya so ya fitar daga jikin ka shi yasa kai wannan bakance din bakin ka ya ce to wannan kenan na farko nau'in farko kenan na azimi nau'i na biyu kuma shine azimin nafila insha Allahu ta'ala zamu yi magana a kai azimin farilla wanda yake na ramadan shine mukayi ishara a dazu a inda Allah madaukakin sarki yake cewa an farlanta muku azimi kamar yadda aka farlanta azimin nan ga wadanda suka gabace ku anyi muku haka ne don ku ji tsoron Allah yanzu wannan azimi da aka ce an farlanta hadisi sahihi yazo kamar yadda nayi ishara a baya daga Abdullahi dan Umar ya ce an gina musulunci akan rukuni biyar tare da sheda wa sannan tsayar da sallah sannan bayar da zakka sannan hajji sai kuma yin azimin ramadan to jama'a azimin ramadan dinnan azimi ne wanda yake farilla shine watan da zai shiga nan da kwana daya ko kwana biyu masu zuwa insha Allahu ta'ala ma'ana kenan gobe ce zata zama ranar duban fari domin yanzu muna daren ashirin da tara to gobe zai zama ranar ashirin da tara to gobe idan almuru tayi rana ta fadi sai a fara laluben yadda za'a ga wata yadda kuma ake neman ga wata ba irin yadda kawai mutane suke fitowa ba bayan anyi magariba mutane su fito su yi ta duba rudo a yamma a'a kur'ani ya shiryar damu ce mana yayi Allah ya ce yana rantsuwa da rana da hasken ta da take Allah ya ce yana rantsuwa da wata da bibiyar da yake wa rana na'am wannan kur'ani ne yake bamu labarin cewa duk inda rana take wata yana nan yana bin ta duk wanda ya karanta science ya san haka wannan karara ne ma a science theory ne wanda yake yan science suka gano shi kwanan nan amma kun ga gashi wannan theory gashi kur'ani ya fade shi a cikin sanda rana ta fito to wata yana nan yana bin ta tana tafe yana tafe tana tafe yana tafe to yadda ake yin a bisa wannan tsarin in kana son gobe ka ga wata in dai ba hadari ko jido ko makamantan haka ba sanda rana ta fito sai ka samu wata bishiya ko wata falwaya sai ka duba ka ga yaya rana take fitowa daga wannan falwaya domin ita rana takan fito tsakiyar gabas takan fito ta karkata bangaren dama takan fito ta karkata bangaren hagu haka Allah ya bamu labari haka eh a ha idan kun fahimci wannan da kyau rana ba tana bullowa bane haka shi yasa kake ganin masallatai wannan ya dan muskuce nan wannan ya dan muskuce nan duk dai dai ne ba yadda za'a yi masallatai duka su fuskanci saiti guda saboda sanda aka zo gina wannan masallacin da aka duba rana sai aka ga ta fito ta nan sai aka sa fuskar shi nan da aka zo gina wannan kuma sai ya zama ranar ta fito ta nan sai suka sa haka in aka hada su wuri guda sai ka ga wannan masallacin yana kallon nan wannan yana kallon nan aka samu ustazu ya dan karanta ahalin shi bai gama fahimta ba sai ya ce ba daidai bane ya karɓa ilimi ina fatan an gane daidai ne duk inda ya anshi sunan gabas a yammacin Africa in aka kalla aka yi sallah sallah tayi saboda haka wannan masallaci kaga ya dan karkace wannan ya dan karkace babu laifi to sai mu dawo yayin da ka ga rana ta fito misali daidai saitun wannan falwaya daidai saitun wannan falwaya to idan yamma tayi sai ka sake juyawa ka kalli yamma sai ka ga ina zata fadi zaka ga zata fadi daidai saitun wannan falwaya ne amma ta yamma to daidai inda ka ga ta fadi din nan to daidai nan zaka kula ido zaka zaka ga wata a daidai wannan wurin in ba haka ba sai ka tafi watan yana can bangaren dama kai kuma kana ta balau balau bangaren hagu dalibin kuma mutane haka suke yi wannan ita ce ka'idar ganin wata a cikin musulunci jama'a sannan yana daga cikin sunna tara alhilal neman ganin watan jama'a ba wai ku ba tsofaffi tukub wadanda idanuwan su sun disashe ba sahabbai matasa daga cikin su da kansu suke fitowa suna neman ganin wata Abdullahi dan Umar ce waye mutane sunyi kokarin ganin wata shima Ibn Umar din yana daga ciki ya ce sai na gani na je na gayawa Annabi Sallallahu alaihi wasallama dan haka matasa gobe idan yamma tayi kune ma kuke da idon ganin wata tsofaffi kan ido ya fara dishi dishi wani sai ya sa tabaran hangen nesa wani sai ya je yayi tozali wani sai ya shafa man zaitun wani sai ya je an diga mishi kunfa in ba haka ba ba ma ya gani don haka kake jin kullum ake rikici don me kun bar abun hannun tsofaffi ne tsofaffin kuma galibi idon yayi dishi dishi matasa idan almuru tayi gobe sai ku fito sai ku sa fusa kun ku kuna duban daidai ina ne rana ta fadi to daidai nan za'a nemi wata wannan shine abun da sunna ta shiryar damu Allah madaukakin sarki ya taimake mu to jama'a kun ji wannan kenan menene ke tabbatar da ganin wata na daga cikin abubuwan da ke tabbatar da ganin wata akwai guda biyu wato abubuwan da ke tabbatar da watan ramadan ya shiga abu na farko shine idan muka nemi wata a gobe da take ranar ashirin da tara to in muka neme shi da daddare wato daren da ake sa rai ya zama daren talatin ga Sha'aban ko daren daya ga ramadan idan muka nema bamu gani ba to sai mu ce Sha'aban ya cika kenan don haka jibi sai mu ce ta zama talatin to gata baza mu ce talatin da daya ba sai mu ce daya ga ramadan in aka ce ya akai kuka tabbatar da cewa ramadan ya shiga sai mu ce saboda Sha'aban ya cika talatin kuma bamu samu ganin wata ba a daren ashirin da tara ko kuma a a cikin daren talatin din don haka muka tabbatar da ramadan ya shiga hanya ta biyu kuma ita ce a ga watan kuru kuru to wannan kenan to bayan wannan sai wani bayani mai matukar muhimmanci shine ana soratar da musulmi gama da hadarin da zai shiga idan ya karya azimi da rana tsaka ya karya da gangan ta hanyar yaci ko yasha ko kuma yayi jima'i jama'a yayi jima'i balle yayi zina yayi jima'i da matar shi a cikin watan ramadan ma haramun ne balle kuma yayi zina balle yayi ya je yana shafa azzakar in shi don ya fitar da maniyyi wannan duk haramun ne yazo a cikin hadisi sahihi wanda Imam Ibn Huzaima ya fitar manzon Allah Sallallahu alaihi wa alihi wasallama ya bada labari ya ce an dauke shi an kewaya da shi sai ya ga wasu mutane gasu nan an nuna mishi halin da za su kasance a ranar alkiyama wadannan mutane laifin me suka yi? Ah wadannan mutane suna karya azimi ne da rana tsaka to amma ya akai musu anyi musu rataya ne irin taragon layya in aka ran aka yanka ragon layya zaka bayan an fede shi sai a daga kan ya yo kasa kafafuwan a rike su sama ya dige ko duk mutumin da ya karya azimi da watan azimi da gangan manzon Allah ya ce ya ga haka za'a yi musu a ranar lahira a cikin wuta kuma kai ba fede ka za'a yi ba balle ka ce ai tunda ka mutu ma ka huta a'a da ran ka da lafiyar ka za'a makale ka sai manzon Allah ya ce sai bakunan su da idanuwan su su rinka diga jini azabar da za'a yi wa masu karya azimi da gangan cikin watan ramadan kenan ya ku matasa da baku damu da addini ba da kuke ganin wai kwaikwayon baturan yammaci gaba ne matasa da rana tsaka sai a hada kudi a je a sai kaji ko rago a je JRA ana gasa musu suna party da watan azimi shi bature dan iska ne bai da addini kai ko musulmi ne kana da addini me kai ka ka kwaikwaye shi duk mutumin da ya karya azimi da ramadan kun ji hukuncin shi Allah ya kiyaye to wannan kenan sannan ga wata ka'ida ita ce idan gari daya suka ga azimi to ya lazimci duk sauran garuruwan duniya idan suka ga wata idan gari daya suka ga wata azimin ramadan ya lazimci duk sauran garuruwan duniya wannan matsalar matsala ce wanda yake haka ta tabbata a musulunci inna ma wasu malamai ne da suka rayu daruruwan shekaru wadanda a lokacin babu hanyar sadarwa da zata bayyana musu ya duniya take sai suka fahimci cewa akwai bambanci tsakanin kasashe jama'a duk duniya babu bambancin da ake kira abun da ake nufi da a cikin geography ko a cikin malaman a samu tsakanin wani gari da wani gari akwai bambancin awa ashirin da hudu to duk duniya babu wannan misali yanzu karfe goma na dare a nan Nigeria daren asabar to babu inda duk duniya ake yanzu karfe goma na dare daren lahadi ko kuma daren juma'a babu sai dai a samu wani wurin yafi wani wurin da awa biyar kamar tsakanin Nigeria da America ko Nigeria da England ko a samu tsakanin wani wurin da wani wurin awa hudu kamar Nigeria da Iran ko Nigeria da Afghanistan ko Pakistan ko Turkistan ko awa biyu tsakanin wani wurin da wani wurin kamar Nigeria da Saudiya ko awa daya tsakanin wani wurin da wani wurin kamar Nigeria da Ghana ko Nigeria da Libya yanzu misali idan karfe bakwai a nan na Nigeria to karfe takwas kenan a Libya a daidai wannan lokacin da muke karfe bakwai a nan karfe takwas a Libya karfe shida kenan
[Segment 5/5 | 01:20:00–end]
[Speaker seg5-spk:0]
a gane. To awa 1 ne. Ko suke Ko kuma suke To babu inda ake awa 24 to da da akwai inda ake da banbancin awa 24 dindi. To shine ya nuna wadancan kasar azumin su daban namu daban. Shine ake nufi da Don haka wajibi ne in aka ce an ga wata. To lallai ne dukkan musulmin duniya su dauki ainihin azumi. To amma a nan bari muyi sauri muyi wani gyara. Wannan fatawar da muke bayarwa sarakunan gargajiya na Najeriya suna amfani da ita. Akan cewa a karbi labarin ganin wata da suke bayarwa. Na'am. Amma abun da muke cewa shine. Ko sarakunan nan na gargajiya sun bada muhimmanci game da harkar ganin wata? Ko ko sun maida ita harkar shashanci ce? To dayawa daga cikin su sun maida ita harkar shashanci misali. Yanzu gobe da take 29 sai kaji radio yazo yace. Jama'a ana umarnin mutane. Da umarnin mai martaba sarkin musulmi cewa yau ne duban fari. Don haka duk wanda yaga wata. Ya bugawa 'yar tsunnufe kaza, ya bugawa sarkin zazzau kaza, ya bugawa sarkin Kano kaza, wato matsalar ganin wata an maida ita matsalar telepon. Wannan yana nuna addinin musulunci bai damu wadannan sarakunan ba. Ina muka gane haka? Sai kawai mutum ya bugo waya yace naga wata a ina? a Samaru, shikenan sai an rubuta. An jima sai ku ji a radio ance an ga wata a Samaru. Wannan shirme ne, wannan shahada muzayyafa. Ba wanda yake karban irin wannan labarin duk duniya tun daga malaman hadisi har malaman shirme. Ba wanda yake karbe. Wannan shirmemiyar shahada ce.
[Speaker seg5-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg5-spk:0]
Sai a samu wani yaro yana yawo a fada bashi da aikin yi sai a zaunar da shi gindin telepon da takarda da biro sai ka buga waya naga wata a ina? a PZ sai a rubuta to Allah ya saka da alheri. Naga wata a ina? a dan magaji sai a rubuta Allah ya saka da alheri. Da haka wai kuma sai a tattara wa. Wannan a cikin harkar yada labarai ta yau. Muna kiran ta Wannan labarin bashi da tushe. Labarin kanzan kurege ne. Mai martaba sarkin Kano a kasar nan shine kawai ya bayyana in kazo kace kaga wata sai an taso kiyanka an kai ka gaban shi. A zaunar da kai gaban su Isa waziri tsoffin malaman gasu nan. Su dube ka tukunna su kada carbin su ya. Ace kai eh kaga wata? To sai kaji mutum yana cewa dama dai Allah gafarta malam. Ace a'a. To sai a sa sarkin fada ya baka kashi. Amma gaskiya jama'a. Yau fiye da shekara goma mukai bincike muka bincika kasashe da garuruwan da ake da'awar cewa an ga wata sai muka gane mafi yanci karya ne jama'a. Misali muka je wani gari a Bauchi muka ce mun gani a radio an fada a jaridu an fadi a radio. An ce an ga wata a garin ku gashi ko kuma baku dauki azumi ba. Sai suka ce suma haka suka ji radio yace an gani a garin su. To muma nan haka aka zo akai mana nan a PZ fa. Aka ce an ga wata a Zaria, a Zaria a ina? a PZ. Nan muka kafa komiti sai da akai wajen shekara uku ana bincike. Ashe kawai wai mutane ne sun tsaya suna neman ganin wata. 'Yan dako suna sauke sukari ko kuma siminti sai wani dan dako yazo wucewa sai yayi irin raha din nan yace naga wata ga wata sai ya shika da gudu irin shigantaka ta 'yan dako. Daga haka ne aka dauki wannan labarin wai aka je aka bayar aka saka a radio. Haba jama'a addinin mu na musulunci ku maida shi irin wannan? Saboda haka muna kira zuwa ga mai alfarma sarkin musulmi. Akan idan ana son musulmin Najeriya su daina shiga rudani game da matsalar ganin wata. To matsalar tafi karfin ace kawai a bada lambar waya. Bayar da lambar waya yana nuna ba'a dauki azumin da daraja ba kuma musulmin ba'a damu da ibadar su ba. Domin makiyin mu ma kenan zai iya bugowa yace yaga wata. Ko ba haka ba? Haka ne saboda haka indai ana son a daina samun sabani to ya kamata a dauki mataki mai nagarta. Yo ai wannan shine dalilin da yasa kasashe irin Saudi Arabia basa yadda da ganin watan Najeriya. Sai ace to ya Saudiya basu yadda da namu ba yo dan me zasu yadda da naku bayan sun san shirme kuke yi? A Saudiya Arabia su suna da hukumar ganin wata. Akwai komishinan ganin wata, akwai ministan da ma'aikatar hukumar ganin wata a karkashin shi take. Idan kazo kace kaga wata sai an tambaya tun daga anguwar ku har sama kai mutumin kirki ne? Amma yanzu nan ko kwaya kasha kawai zaka iya bugowa kace naga wata a ina? kace a Muciya shikenan sai kaji a radio ance an gani har da Muciya. Kum karya ne dan kwaya ne ma ya fadi. Ina fatan an gane?
[Speaker seg5-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg5-spk:0]
To Allah madaukakin sarki ya kiyaye amma indai ya tabbata an gani to wajibi ne musulmi lallai su dauki ainihin azumi. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. To wadannan kenan jama'a. Kamar yadda nace zamu takaita ainihin wannan lacca domin laccoci ne muke da su masu dinbin yawa amma sai Allah yayi ta saukar da rahmar shi ta ruwan sama bamu samu damar yin su ba. Azumi yana da rukunai jama'a shima kuma da kanshi. Daga cikin rukunai akwai niyya saboda Allah yana cewa Ba umarci mutane basu kawai sai suyi addini tsantsa su bautawa Allah suna masu tsarkake addinin gare shi. Azumi jama'a sai da niyya. Niyya nau'i biyu akan azumi nau'in farko itace tsarkin zuciya ya zama dan Allah. Nau'i na biyu shine ayyana irin azumin. Kasan wane irin azumi zaka yi azumin Ramadan ne ko azumin kaffara? Azumin nafila ne azumin litinin ne da Alhamis ko ko wane iri ne duk ana bukatan irin wannan. Kuma niyyan nan bada baki ake fadin ta ba. Ace wai Bakin dogola ba haka ba. A zuciyar ka zaka kudurta a shikenan wannan littafi da ke koya muku niyya Ga niyyar yanka kaza ga niyyar yanka zakara ga niyyar yanka sumamman zabo duk wannan karya ce jama'a wallahi duk karya ce ba karatun musulmin bane. Suna bata muku lokaci ne kawai eh. Allah ya taimaka.
[Speaker seg5-spk:1]
Amin.
[Speaker seg5-spk:0]
To. Sannan rukuni na biyu daga cikin rukunin azumi shine ka mewa ka daina ci da sha daga jima'i tun daga fitowar alfijir har faduwar rana. Sannan Daga cikin ainihin rukunin azumi ko kuma daga cikin ladubban azumi sune abubuwan da muka gabatar a baya. Mai azumi ana son a ganshi da natsuwar jiki ana son a ganshi da natsuwa a wajen ainihin magana. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. To yayin da azumi ya zama farilla amma sai Allah madaukakin sarki ya saukar da wata aya yake cewa Wadanda za su iya azumin sai dai azumin na basu wahala to sai su ainihin ciyar da abincin miskini guda. A farkon musulunci jama'a komai lafiyar ka da ranka da lafiyar ka in ya zama in kai azumi zai baka wahala sai ka bar azumin sai ka ciyar. Amma daga karshe an shafa wannan dokar sai ya zama wannan ayar kadai tana aiki ne akan tsoho. Da tsohuwa da mai cuta cuta wadda take Kamar cutar ulcer cutar da bata iya jurar yunwa. To duk masu larurori irin wadannan zasu iya azumin amma zasu sha wahala zasu galabaita. A'a mace ce tana da ciki idan tayi azumi zata sha wahala ko kuma dan dake cikin ta zai takura a'a mace ce tana shayar da nono idan tayi azumi nonon zai kafe dan zai galabaita ko kuma ga tsotso ga azumi zata wahalar ita to duk wadannan sun shiga Azumi ya fadi a kan su sai su ciyar wannan itace ingantacciyar magana wadda sahabi Abdullahi dan Abbas da Abdullahi dan Umar suka ainihin bada fatawa a kan ta tana nan a cikin muwatta ta Imam Malik dan haka mata masu shayarwa da mata masu ciki da tsoffi da masu cuta irin ta ulcer cutar da take da wahala kuma bata iya jurar yunwa azumi ya fadi a kan kuwar was. Babu ramuwa sai dai ciyarwa ciyar wannan ta me? ta abincin miskini guda. Manan aka dafa tuwo da miya ko shinkafa da miya sai ka dauka sai ka bashi idan babu hali a yanzu sai ka bari bayan sallah sai ka tattara sai ka bayar daidai daidai ko kuma ka hada ka bayar. Da ace tsoho ne tukuf ko tsohuwa zata kasa ko zai kasa azumi. Kuma bashi da halin ciyarwa kuma ba wanda zai ciyar mai to yadda azumin ya fadi a kan shi ciyarwar mata fadi a kan ta. Ina fatan an gane? Allah madaukakin sarki ya taimake mu. To jama'a kunji wannan haka matafi mutumin da yake matafi ko mara lafiya rashin lafiyar da ba ta kai tsanani ba. Ina fatan wato rashin lafiyar da tayi tsanani ko kuma tafiyar da ta kai bazai iya yin azumi ba sai a ainihin sauke azumi ma'ana daga nan zuwa Kaduna in ba zaka iya yin azumi ba tafiyar nan a mota ne? Tafiyar nan a kasa ne? a jaki ne? a jirgin sama ne? matukar bazaka iya yin azumi ba saboda tafiyar. Saboda wadanda basa tafiye tafiye jama'a basu san me ake nufi da tafiya ba amma Annabi da yake tafiye tafiye wanda ya hau dabbar da tafi kowace sauri itace buraqa. Amma duk da haka yace Tafiya wani yanki ne na azaba. Wasu suna cewa ai yanzu ana tafiya ne a mota ana tafiya ne a jirgin sama tafiya a jirgin sama wahala ne da ita tafi wahala a mota. Baka taba shiga jirgin saman bane wani lokacin kafun a je a daidaito a sama dan cutuwan dake cikin ka ma ya zai zaye an kada cikin ka anyi kasa anyi sama anyi kwana anyi sai kaji gaba daya ka fara jin gudawa. Saboda haka tafiya a jirgin sama ko a mota basu dauke sassaucin da Allah yayi wa mutum ba. In kaga zaka je Lagos daga Kaduna zuwa Lagos minti nawa ne minti hamsin ne a jirgin sama. Amma kaga bazaka iya azumi ba sai ka sauke. Bayan sallah sai ka rama. A'a rashin lafiya ne ya zama bazaka iya yin azumi ba sai ka sauke a'a kana cikin azumin ma sai rashin lafiya ta fado maka bazaka iya ci gaba ba sai ka karya a'a ka dauki azumin zaka yi tafiya kana cikin tafiyar sai ya zama azumin zai galabaita da kai a halin tafiya sai ka karya shi. Haka kuma zaka ainihin yi tafiya bazaka yi azumi ba. Jama'a ba munafunci bane ba wai cewa za'a yi ka boye kaci abinci bazaka iya cin abinci a waje. In aka tambaye ka lafiya kace baka azumi saboda kai matafiyi ne. Wannan itace sunnar sahabbai. Abu Basratul Ghiffari hadisin shi yazo cikin littafin Sunan Abi Dawuda. Matar shi ta saka mishi abinci a cikin flask. An kada jirgin ruwa za'a bar garin kenan sai ya jawo flask din shi ya bude yace jama'a bismillah fa ko akwai iri na wanda baya azumi? Yace subhanallahi kai kuma babban azumi malami haka kuma baka azumi kaza kaza. Lafiya yace ai ni matafiyi ne akace amma kai matafiyi ne malam ai baka bayyana ba ai baka yi kaza kaza akai ta kawo irin tawili na jahilai. Sai da ya isa garin yana isa can garin sai ya tara daliban shi. Kalmar farko sai yace ya Allah ina rokon ka ka gaggauta daukar raina. Dalibai suka ce lafiya malam kake irin wannan addu'a yace naga wasu mutane ne suna kyamar sunna. Ma'ana nace musu manzon Allah ya halarta mai azumi ya fara cin abinci ko a Amma sun ta shine nake addu'a Allah ya dauki raina. Matafi
============================================================
[Part 3]
============================================================
[Segment 1/5 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
ainihin wato yin azumi din a watan ramadan, amma kuma akwai ainihin wato ramuwa akan su. Ma'anar wannan maganar ita ce, wance ba zata iya yin azumi ba, ba zata iya azumi ba saboda me? Saboda tana ainihin haila to zata rama bayan sallah. Wance ba zata iya yin azumi ba saboda ta haihu jini na zuba dalili saboda jini na zuba ba dalilin shayarwa irin na da zuba. To ba zata iya azumi ba amma zata rama amma ba zata rama sallah ba. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. To in muka dawo kuma muka dubi rana kwan da aka hana yin azumin su, an hana yin azumi ranar sallah karama ko babba. Yin azumin ranar sallah karama ko babba haramun ne. Haka azumi kwanaki uku na bayan babban sallah yin wannan ainihin wato azumin shima an hana yin shi. Ina fatan an gane. Sai dai ga wanda bai samu dabbar da zai hadaya da ita ba ma'ana ga wanda yake aikin hajji a can yake tamattu'i to zai iya yin wadannan azumi da ainihin aka dora mishi yayi. Sannan an hana yin azumin ranar juma'a ita kadai ka wara ranar juma'a ka rinka yin azumin ta. Haka kuma an hana yin azumin ranar asabar jama'a sai dai azumin farilla. In aka ce ranar asabar ta dace da ranar arafa jama'a ba'a yin azumi saboda yin azumi ranar arafa mustahabbi ne. To in ya fado daidai da ranar asabar to abubuwa biyu sun hadu. Abun da yake mustahabbi da abun da kuma aka hana. Annabi sallallahu alaihi wasallam a cikin hadisi sahihi da Abu Dauda ya wailato yana cewa Kar kuyi azumin asabar sai dai na farilla. Duk azumin da ba na farilla ba in ya fado asabar ba'a yin shi. Don haka azumi ranar asabar ita kadai ce ko za'a hada ta da wata bai halatta ba. To bayan wannan sai kuma ainihin mu duba ga wasu ranaku wadanda shari'ar musulunci ta sunnan ta ainihin wato wato daga ciki afwan in karasa wadancan bayanan. Akwai wasu ranaku wadanda har wayau suma shari'ar musulunci ta hana yin azumi. Ranar shakka ita ce jibi. Ranar da ake shakka shin yau talatin ga ramadan ko talatin ga sha'aban koko daya ga ramadan sai kace kai bari kayi azumi duk ma inda ta fadi sha ne. Idan anga wata aka ce anga wata dama kana azumin ramadan. In kuma ba'a ga wata ba ya zama nafila to an hana wannan azumin. Sannan sai yin azumi kullum ya zama kullum kana cikin yin azumi to an hana. Haka an hana matar aure tayi azumi a halin mijin ta yana gida bai yi tafiya ba. In ko har ta dauki azumi ba da izinin mijin ta ba azumin nafila in ya dawo yana son ya sadu da ita zai karya wannan azumi indai na nafila ne. Allah ya taimaka. To sa'annan har wayau daga cikin azumin da aka hana akwai Idan sha'aban ya kai ainihin wato karshe kamar yadda sha'aban ace ya kai sha biyar sha shida har zuwa ashirin da tara talatin to bai halatta kayi azumi ba sai dai dama in ka saba yin azumin litinin da alhamis ko ka saba yin azumin kwanaki uku na wata ko ka saba yin yau azumi gobe sha babu laifi. Amma ka kirkiri yin azumi a karshen sha'aban ba sidi ba sada da sai dan karshen sha'aban ne to bai halatta ba. Sannan an hana yin azumin sa bizarce shine ka kwana biyu ko uku babu sahur babu bude baki an hana wannan. To bayan wannan kuma sai azumin mukan da ake so musulmi yayi daga cikin su akwai azumin litinin da alhamis. Akwai azumin annabi Dauda yau kayi azumi gobe ka sha sannan akwai azumin kwanaki uku a wata shine ranar sha uku sha hudu da sha biyar ga wata na musulunci. Wadannan azumin muka duk suna da falala. Sannan yawaita azumi a cikin watan sha'aban wato kafaru tun daga farkon shi to ka yawaita yin azumi a cikin shi. Wannan ma an so shi. An so yin azumin sittashawwal bayan karamar sallah sai ka ainihin yin azumin kwanaki shidda a cikin wannan wata ko a hade ko a rarrabe. Duk wannan mustahabbi ne hadisai sunzo sahihai akan haka. Sannan a cikin kwanaki tara na farkon ainihin wato watan watan hajji watan zulhijja wadannan kwanaki kwanaki ne na yin azumi zaka iya diban wasu kwanaki daga ciki ka ainihin yin azumi suna da matukar falala kwarai da gaske. Sannan azumin yin ranar arafa ranar da alhazai suke can suke hawa arafa to ana so kai kuma kayi azumi a nan amma shi alhaji da ke can to bashi daga cikin sunna ya ainihin ya azumi. To sannan ana son yawaita yin azumi a cikin watan almuharram wato wata na farkon kalandar musulunci da kuma ainihin watan ashura musamman ainihin wato ranar ashura din da kuma rana ta tara ita ce ranar tasu'a duk wadannan sunna ainihin ta tabbatar da su. To sai dai tambaya ko abubuwan da ake yi a ranakun ashura da tasu'a daidai ne? Ba daidai bane abubuwan ko ahlussuna suna yin wannan barna kuma 'yan shi'a suna yin wannan barna. Ahlussuna sun kirkiro da wata barna wadda yake basu san cewa makiyansa habban manzon Allah sallallahu alaihi wasallama da makiya ahlul baiti su suka kawo ta. Wannan ainihin barna ita ce bidi'a ta cika ciki da bidi'ar takuta ha da bidi'ar shara ace wai wannan wata watan shara ne. Duk makiya ahlul baiti ne da makiya sahabbai suka kirkiro wadannan bidiyo'i. Ace wannan watan shara ne tunda sunan kakana ne da kai sai ka bani kudin shara wannan bidi'a ce. Sannan cika ciki. To wadannan bidiyo'i ne jama'a da kuma cewa ranar tasu'a da ashura ranaku ne da ake son wai a yalwata wa iyalai har kaji malamai suna karya musamman ranakun juma'a in suka zo hudubobi suce wai amma fiso a kyautata wa iyalai da abincin ashura fiye da abincin idi. Karya kuke yi limamai wannan bashi da asali a musulunci hadisan karya ne kuka kwaso. Ranar idi karama da babba babu ranar da ta kai ta daraja a musulunci. Sune ranakun da ake so ka yalwata wa iyali a canza girki a sauya to wannan shine daidai amma ranar tasu'a da ashura babu wani azumi na musamman babu wani ainihin wato abinci na musamman. Abun da aka shari'anta kadai shine mai shine azumin. Amma maganar abinci na musamman maganar sanya tozali na musamman maganar ayi ayi kwalliya ta musamman duk babu wannan a muslimci makiya sahabbai ne da ahlul baiti suka kawo. To su kuma 'yan shi'a sai suka bullo da bidi'a ta zanga zanga da zubar da jinin su wai saboda a wannan rana ce aka kashe sayyidina husaini to tunda wannan rana aka kashe sayyidina husaini wai indai da gaske kana son sayyidina husaini wai kaima jinin ka ya zuba. Wannan zindikanci ne kuma karya ce bata da asali. Duk da wadancan ahlussunnan da wadannan 'yan shi'a duk wadannan abubuwan da suka kawo karya ne ba musulunci bane. Abun da yake musulunci shine abun da Bukhari da Muslim da Ahmad suka ruwaito yin azumin tasu'a da ashura in baza ka samu yin biyun ba to kayi ashura tafi tasu'a. Karawa kuma da yin azumin hadiya ma'ana yin azumin sha daya ga wata fa hadisi bai tabbata akan haka ba. Don haka abun da ya tabbata tasu'a da ashura jama'a addinin nan fa sai an tsaya an tace shi Domin yanzu sallah ta kusa kana nan kana binciken wannan ya dine. Ba ko wane irin yadi kake zuwa ka siya ba. Wanne tela ne ya iya wanne mai surfani ne wanne mai guga wanne takalmi yafi amma addini ko wace kwama cala da akwamari sai a dibo a zubawa. Addinin musulunci a'a Addinin musuluncin sai an tsaya an tace shi a cire bidi'ar 'yan bidi'a hadisan karya a ware su a a bayyana wa musulmi abun da yake daidai don haka musulmi wannan hayaniya da 'yan shi'a suke gaba daya ma guzanci ne suka kawo. Na suruda addini su sabbabar da sababin a zagi sahabban manzon Allah su suka kashe husaini babu wani sahabi da ya kashe husaini. Ku je ku saurari kasusuwa guda goma da muka yi su yau kamar shekara biyar tasu'a da ashura lokaci ne na azumi ibadar Allah ba lokaci ne na zagin ainihin magabata ba. Cewa da ake wai mu'awiya ko yazidu shi ya kashe duk wannan karya ce hayaniya ce irin ta 'yan shi'a in kuka saurari wadannan kasusuwa duk mun kawo mun karanta muku. Saboda haka jama'a ku ahlussunna wannan bidi'a da kuka kawo ta watan shara karban shara karban kaza ku bari ku kuma 'yan shi'a ku tuba ku bari wannan bidi'a ta zagin sahabban manzon Allah. Saboda kaskanta Aisha da wulakanta ta ranar ashura sai kaga 'yan shi'a sun samo bakar karya sun sa mata bakin kaya suna dukan ta wai ita ce Aisha su samu bakin kare suna dukan shi wai shine mu'awiya da wane alhakin zaku ji da alhakin zagaro manzon Allah mata ko da alhakin wannan karya da kuke azabtar da ita. Wannan addini kafurci ne kuke 'yan shi'a ku karbi addinin musulunci ku bari. Allah ya taimaka. Wannan kenan sannan bayan ainihin wannan yana da kyau mu ainihin fadakar da musulmi game da cewa mai azumin nafila yana da 'yancin kan shi in ka dauki azumin nafila kaga dama haka siddan ba sidi ba sada da zaka iya karyawa. Cewa da hausawa suke wai in ka karya ka kashe mutum karya ne. Ba wannan aka karatu karya ne. Azumin nafila ka dauka kaji kana so ka karya sai ka karya. A'a ka dauka ne sai kaji wani dalili da zai sa ka ka karya misali sai akai maka tayin wani abinci sai ka karya. Ko kuma dama ka tashi ne kana zaton yau fa hantsiya dubu lu da yi. Ba komai a gidan can kuma sai aka kawo wani dambu. To kawai shikenan sai ka damba ce azumin ka fasa. Ina fatan an gane. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Yin sahur yana daga cikin ladubban azumi jama'a. Yin sahur yana daga cikin ainihin ladubban azumi to amma a wancan matsalar shin wajibi ne ga mutumin da ya karya azumin nafila ya rama ba wajibi bane. Domin shi kan shi azumin da ka karya ba wajibi bane to yaya biyan shi zai zama wajibi? In ka dau azumi nafila ka karya ba lallai bane ka rama in kaga dama kaje ka sake in baka ga dama ba ba maganar ramuwa. Ina me Eh Azumin goman zulhijja ai ba goman zulhijja ba shi yasa ayi babu goman zulhijja goman zulhijja an hada da ranar sallah munce ba azumi ranar sallah. Tara ga zulhijja ne aka ce tara din ba wai ka azumci taran ba ana nufin wadannan taran kwanaki ne na azumi zaka iya tsintar wasu kwanaki daga ciki kayi azumi. Na'am sahur jama'a yana daga cikin sunnar azumi ta ladabi. Ba gwanin ta bane kace kai baka sahur ko da bino ka tashi kace ko ruwa ka tashi ka hadiya makorwa guda. Ba gwanin ta bane. Sannan yana daga ainihin wato tabbatar da lokacin sahur jama'a shine lokacin da alfijir yake gab da ya fito. Ba'a so kace zaka yi sahur tun karfe goma na dare. An fison ka jinkirta sahur din ka yadda da ka gama sai alfijir ya fito. To ta yaya yiwuwa ka jinkirta kuma kana cikin yi baka koshi ba sai kaji ladan ya kwada kiran sallah. Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace ba komai sai ka cigaba da yin sahur din ka har sai ka gama ka sha ruwa ka wanke hannun ka wannan bai bata azumin ka ba. Amma kafin ka fara sahur sai ya zama an kira sallah to wannan kuma babu yadda za'a yi an riga an rufa kofa kafin ka sawo kafa. Ina fatan an gane. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. To wadannan suna daga cikin abubuwan da ainihin nake so in tattauna mana kuma na tattauna mana su insha Allahu ta'ala wadanda suka shafi ainihin azumi sai kuma gaggauta bude baki. Bude baki shima ana so a gaggauta shi. Bude baki na tabbata koda da makwarwar ruwa ce in ka sha. Amma an fiso ka ainihin yin bude baki da dabino. Sannan akwai addu'a wadda manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallama yakan yi yakan ce Manzon Allah yakan ce ki shirwa ta kare jijiyoyi sun mike lada ya tabbata in Allah ya so. Wannan hadisi ne sahihi al-imam Abu Dauda ya ruwaito shi. Amma addu'ar da ake cewa Wannan hadisin da yazo da ita bai inganta ba don haka bai halatta ayi ita ba sai a tsaya ga abun da yazo daga annabi sallallahu alaihi wasallama. Sannan ana so mai azumi sanda ya sha ruwa zai iya yin addu'a addu'ar mai azumi a sanda ya sha ruwa to karbabbiya ce bata da hijabi tsakanin ta da Allah. Sannan ana son yawaita ayyukan alheri da yawaita karatun alkur'ani ai shi yasa kaga yana daga cikin sirrin da ake karanta alkur'ani musamman mu da ba larabawa ba'a yi mana tafsiri. To manzon Allah sallallahu alaihi wasallama idan watan ramadan yazo malamin shi Jibril yakan zo sai su rinka yin musaffa suna ai wannan yayi ya bawa wannan wannan yayi ya bawa wannan ana gyarawa manzon Allah ana kara tabbatar mishi da karatun. To lallai a yawaita karatun alkur'ani jama'a sannan a yawaita alheri. Idan kaga zaka sha ruwa ga wani bai da inda zai sha ruwa sai ka kira shi sai ku sha ruwa tare. Sannan da dagewa wajen yin ibada musamman a goma ta karshe. To daga cikin ibadar jama'a akwai ibadar i'itikafi. Ibadar i'itikafi Allah ne yake cewa Kar ku sadu da matan ku kuna i'itikafi a masallaci. Wannan aya da tace a cikin masallatai wasu malamai suka ce wannan dalili ne akan ana iya yin i'itikafi a ko wane masallaci. Wasu kace sai a masallacin juma'a wasu kace sai a masallacin da ake Amma dai ya tabbata a cikin hadisin manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallama wanda al-imam Abubakar bin Abi Sheba ya fitar da shi annabi yace Babu i'itikafi sai a masallatai guda uku. Yace wa Wa Masallatai uku annabi yace nan ne kawai don haka wannan hadisin ya fassara wancan ayar. Ma'arifar can wacce iri ce Ba wanda ya san ta sai wanda ta shiga cikin kwakwalwar shi da wannan hadisin na manzon Allah sallallahu alaihi wasallam don haka jama'a ba'a i'itikafi. Har dai ake yanzu ana rikice da mutane a i'itikafi a masallacin Sultan Bello har abu ya zama sai anyi register har abu ya zama kaza babu wani masallaci da ya halatta ayi i'itikafi duk duniya sai masallacin ka'aba da masallacin Madina da masallacin baitul makdisi hadisi ne sahihi yana cikin littafin almusannaf na al-imam Abubakar bin Abi Sheba. Fatawar Aisha da Aisha tace ana iya a masallacin juma'a kuskure ce Domin manzon Allah mijin ta kuma malamin ta yace ga inda kadai ake yi don haka fatawar Aisha bata da kima in ance ga fatawar manzon Allah sallallahu alaihi wasallama. Ta yewa wani yace to yanzu bana baza ayi i'itikafi ba kenan a'a baza ayi ba sai a can inda aka ce ai hajji ma baka yi a garin ku. Baga tudu dai ana da su na fulato har sun fi nasafa da marwa tudu amma baza ka tafi fulato ko nasarawa ba baza ka je inugu ba baza ka je kayi aikin hajji ba akwai tudu dai akwai safa da marwa a can amma baza ka je kayi ba don mai a makka kadai aka ce ake yi. Saboda haka i'itikafi ma haka amma matsalar fatowoyin malamai ne suka zo suka ratsa mutane ga wannan littafi nazo muku da shi ga wadanda basu samu ba don mun ce anyi foto start kuma wannan littafi yana daga cikin littafin da za'a buga mana shi kwanan nan. Ka samu wannan littafin ka karance shi zaka ga dalilai gamsassu akan cewa bai halatta i'itikafi ko ina a duniya ba sai a masallatan nan guda uku. Allah ya taimaka. Sannan daga cikin abubuwan da suka halatta game da azumi ya halatta game da azumi yayi wanka don ibada kamar me yana azumi da rana sai mafarkin jima'i ya tashi ya gama niyya a jikin shi zai yi wanka azumin shi bai karya ba. Amma in bai gama niyya ba fa yayi mafarkin yana jima'i da rana gashi yana azumi amma ya tashi bai gama niyya ba azumin shi ba komai kuma ba wanka akan shi amma in ya gama niyya zai yi wanka. To wannan irin wankan ya halatta sannan kuma ya halatta yin wanka ko wanke kai saboda samar da jin sanyi a jika ko ka sa kanka a pamfoye dan yi sanyi ko ka kurkura bakin ka da ruwa ka guntsa ka zubar dan mai saboda bakin ka ya bushe duk ya halatta a musulunci. Ina fatan an gane. Ya halatta ga mace mai girki ta dandana girkin ta gishiri yayi ko bai ba sai ta tofar ya halatta ga matar da take da yaro wanda ba'a iya cin abinci ta tauna mishi sai ta bashi in yaso sai ta furzata wanke bakin ta ya halatta kamar ydd kaji ya halatta kuma sanya tozali ya halatta ayi asuwaki ya halatta ayi brush da makilin duk wadannan abubuwan sun halatta. Mai azumi ya halatta ayi mishi allura allurar nan kuma ga ingantacciyar magana koda ga allurar ciyarwa ce ta likitoci don allura akwai wanda yake allura ce magani ake sawa. Akwai allurar da ita wannan allurar ana yin ta ne saboda ba zai yiwu ya ci abinci ta baki ba sai a rinka dura mai abincin ta hanyar allura ta jijiya mara lafiya indai yana azumi kuma zai iya haka babu komai bata karya mishi ba domin inda kawai abinci zai shiga ya karya azumi shine ta baki. Amma wannan abinci ne ma ba hakikanin abinci ba abinci ne kawai a wurin likita. Don haka hakikanin al'amari allura bata karya azumi. Akwai allurar da za'a yi maka ita ko a duwawo ko a kafa ko a hannu amma sai ka dawo kana jin dacin ta a makoshin ka bata karya maka azumi ba. Abubuwa daewa da mutane zaka ji suna wa'azi a gidan radio kaza azumi ya karya kaza azumi ya karya basu da dalili akan haka jama'a kamar lokacin aikin hajji ne kaji ana ta cewa alhazai da kayi kaza zaka yanka rago don haka sai alhazai su dawo basu sidi ba sada da bai cin abinci ba bai yi tsare ba ba duk malamai sun sa shi yayi ta kaffara da babu dalili. Kuma in kaji ya musu kai ba komai akan ka hadisi bai wajabta maka ba sai yace ina malamai sunce yace to malaman dai har yanzu baku gaji da ibadar su basu yi ta wahalar da ku Saboda haka jama'a kunji wadannan abubuwan duk da ake kallafa mutane a azumi babu matsala akan su insha Allah. Allah ya taimaka. To bayan nan kuma sai karshe karshen bayanan mu wadanda wadannan bayanan zamu karkare su ne insha Allahu ta'ala dangane da abun da ya shafi abubuwan da ke karya azumi. Abubuwan da ke karya azumi akwai ci da sha da gangan
[Segment 2/5 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
ta hanyar baki da kuma ainihin wato kasantuwar mutum yayi jimai amma mutumin da yaci ko ya sha ko ya jimai da mantuwa babu komai a kan shi babu ramuwa babu kaffara jama'a yin amai da gangan yana karya azumi amma aman da yafi karfin mutum ne yazo wa mutum to babu komai wadannan sune bayanai insha Allahu sannan mutumin da ya sadu da matar shi jama'a da watan azumi to shine zai yi ramuwa da kaffara shi kadai ita bazata yi ramuwa ba bazata yi kaffara ba wannan shine abunda sunna ta tabbatar Allah madaukakin sarki ya taimake mu ita wannan kaffara lallai dai sai ayi ta a jere bazaka rarraba ta ba saboda kaffara ce ta laifi mai nauyi na karya azumi da gangan dangane da istimna'i fa akwai wasu gwagware ko tuzurai ko samari ko yan mata sun ki yin aure da wuri wasu sun ce auren yayi tsada ne wasu sun ce sai sun gama makaranta ala ayyi hal ko da uzuri ko ba uzuri wasu suna komawa zuwa ga yin istimna'i wanda bature yake kira masturbation wato mutum yaje ya talugwi gwita azzakarun shi har mani ya fita to wannan haramun ne a cikin musulunci jama'a kuma alkitance likitoci sun tabbatar da yana haifar da illoli kamar haka illar farko yana haifar da zubewa ko rugujewar hadda illa ta biyu yana haifar da randa kayi auren ya zama ka kasa haihuwa ma'ana yana kashe azzakarun mutum ko ya kashe yayan mani kwantitin su adadin su ya ragu yadda manin da zaka rinka zubarwa bazai haifar da da ba biologically yana haifar da kwarkwata sannan daga karshe yana haifar da tabuwa da motsuwar hankali ko abunda baushe ke cewa kwancewa ace wane fa ya zare to yana daga cikin abunda ke kawo zarewa ku karanta littafin malam Abdullahi Nasiru Ulwan mai suna dan haka samari ku daina yin wannan masturbation din yan mata ku daina yi me mafita kuyi aure babu dalilin da zai sa bazaku yi aure ba jama'a yanzu in gari ya waye ka zauna nan yan mata dari sai su wuce duk wadda ka tuntube ta the first and the last agenda tana son aure samari dari sai su wuce duk wanda ka tuntuba aure yake so to a zo ayi auren mana mu dai limamai mun shirya fatiha da qulhuwallahu kafa uku bazata kare ba a shirye muke ba sai anyi mana juye a baki ba ko yaushe a shirye muke ko bacci muka tashi to me ya rage shedu da shedu suna nan wakili yana nan da zai karbi auren waliyin da zai bayar yana nan amma me ya faru al'adu kuka kawo kuka sa al'adun da kuka sa sai samarin da yan matan suka halatta wa kan su zina sai kana da naira dubu daya bazaa baka aure ba ko zaa bada aure a dubu daya baza su baka ba dubu daya sai ace bazaa bayar ba ace sadaki dubu daya a ina bazaa bayar ba to bazaa bayar ba eh to yaje ya bata dari biyu kuma ya sadu da ita kunga kun buda kofar barna shi yanzu ba ruwan shi haram ko ba haram ba shi bukatan shi ta biya kuma ta biya kuma kuna da alhaki duk zunubin da yaran nan suke na zina iyayen su suna da alhakin wannan zinar ba dan komai ba saboda sun ki su aurar da su duk yarinya budurwar da kaje ka samu a university in ka tuntube ta zaka ji aure ne ajandar ta wata ma zata ce ta taho ne saboda baban ta yace bazai mata aure ba sai tayi graduation dan haka duk inda aka ce akwai party zata tafi a wannan daren ko sai an keta mutuncin ta saboda haka iyaye ku aurar da yayan ku ina yin wannan maganar ne a madadin yan matan da samarin ba kuma na a rubakin su na ci musu albasa bane wannan albasa sun yadda a ci musu ita ina fatan an gane Allah madaukakin sarki ya taimake mu wallahi zaka je ka samu yanzu galibi masturbation suke yi sai kaga yarinya da hijabi da nikabi tana son aure an ki a aurar da ita sai taje ta zauna sai ta samu kyandir sai ta rinka sokawa a farjin ta yana sosa mata to haramun ne bai halatta ba a musulunci kuma yana da side effect yana da illa kuma baban ki yana da zunubi a kai sannan kai kana son aure bazaa baka aure ba saboda me wai baka da kudi kudi basu daga cikin abubuwan da aka lissafa a cikin aure a musulunci abunda aka lissafa shine in kuka yadda yana da addini yana da dabi'a ku bashi ya kudi arziki na Allah ne sanda aka dauki ya aka baiwa annabi Musa baa san zai zama annabi Musa ba fa sai daga baya waye gari ashe wannan dattijo ya ga ashe yaron nan da na dauki ya na bashi ashe ma ya zama babban mutum ya zama amma wai yanzu in kai talaka ne bazaa baka ya ba saboda me saboda wai mutane sun leko gaibun Allah cewa wannan fa har abada talaka ne alhajin birni zaa ba shi kuma an leko gaibun Allah cewa har abada shi kuma zai zauna a mai kudi in Allah ya ga dama sai ya a kasanta iyaye kuji tsoron Allah wannan matsala ta aure ba karamar matsala bace tana rugurguza mu turawa da kuka dauko dabi'ar su jama'a su turawa suna zina mazan su da matan su zina suke a cikin ku kuma haramun ne zina dan ku musulmi ne dan haka sai mutum yace bazai aurar da yar shi ba sai tayi makaranta shi wannan yace bazai aure ba sai yayi makaranta me yake faruwa wai yana ganin system din da ake a kudancin Najeriya yana ganin system din da ake a Turai ai sai mutum ya gama makaranta amma kaje ka samu kafin ya gama makaranta yan mata nawa yayi zina da su guda nawa yayi wa ciki ke da kika ce bazaki aure ba sai kin gama makaranta ko kai da kace bazaka aurar da yar ka ba sai ta gama makaranta yan mata nawa ne suka yi ciki na Turai da kake cewa ai a ba Allah yace muyi koyi da su ba Allah ce mana yayi muyi koyi da al'qur'ani Allah ce waye ku bi abunda aka saukar muku daga ubangiji kar ku dauki wasu masoyan ku wai kuna son turawa kuyi koyi da su bature bashi da dabi'a yanzu rannan suka fitar da report jama'a sun fada gidajen rediyon su da tashoshin internet sun ce yanzu fitina mafi girma da suke fama da ita itace fitinar rashin aure da fitinar rashin haihuwa suka ce yanzu haihuwa ta ragu da a America sakamakon aure ya ragu da yanzu baa yin aure to me yasa zai yi aure yana da yana da guda tara a waje dan me zai yi aure yana hauka ne to irin wannan dabi'ar ce suke kawo mana saboda haka yan boko wallahi boko ba hauka bane kace wai kai saboda boko a'a ku je ku saurari dina da na sa mishi ainihin nace aure bautar ubangiji me nake nufi a wannan wurin nace lallai muna son yayan mu suyi karatu kuma lallai shari'ar musulunci tana son mu aurar da yayan mu to dole mu gabatar da shari'ar musulunci akan abunda muke so mu rinka aurar da yayan mu in ya so suyi karatu a gidan miji muna bukatan mu samu ta zama ta zama ta zama kaza ta zama kaza ta zama kaza to amma kuma abun zai ana ganin akayi aure sai a samu wanene dalibin ilimi sai ku samu wani shima dan makaranta sai ku hada su abunda suke kenan jama'a mune nan a arewa wai sai anga kana da kudi ake baka ya abunda suke duba wannan yana karatu eh wannan yana sana'a eh sai ace a bashi ya amma mu nan a'a sai wai yana da ruwan kudi ruwan kudi in ba haka ba bazaa bashi ya ba wannan kuskure ne jama'a wallahi wannan ta'adi ne sai kana da ruwan kudi sannan zaa baka ya amma a dan makaranta ne sai ace a dan makaranta sai da akuya ta dawo tana susar dannin mu to randa ya zama governor fa sai kuma ace kaga dana bashi ya ta dawo ta ni yanzu ni surikin governor ne oh ka gani ina fatan mun gane saboda haka a yana makaranta eh yana da abun yi zai iya rike ta eh to ku dauka ku bashi yana da kula da addini yana da mutunci sai ku dau ya ku bashi arziki na Allah ne babu ku saurara jama'a babu wanda Allah ya haifa cikin halittar Allah ba wanda Allah ya rubuta talaka ba matsiya ci duk halittar Allah da yayi hadisin ibn Mas'ud yace randa aka hura mai sai da aka ambaci arzikin shi kai abunda ka sani arziki shine kudi to kayi kuskure kudi ba shine arziki ba arziki daban auren Allah ku kuma matasa mugun kuskure ne ya zama kai kuma ka zauna sai karatu zalla baka da sana'a domin wannan irin tiyorin jama'a yanzu ko a American da kuke koyi da ita da Turai basu amfani da wannan ba wanda yake zuwa yayi degree yanzu dan ya samu aiki a America da Turai so ake kai kayi degree din da zaka samowa da kan ka aiki ka samowa da wasu amma kana makaranta dan ka samu aiki to wadanda ke rike da aikin suna nan da yaya irin ka sun tura su Ingila da Malaysia suna yo karatu wanda yafi naka kyau in yayan su suka dawo yayan su zasu matso da su kusa da su suna fita yayan su na mai yawa kai kuma sai dai ka zama me sai dai ka kare gantalin ka a kasuwan mitya kana karanta jarida kana tsaki boko ya buga kenan ka zama dan boko ko iyi mana iyi amma so ake in kai karatu kai ka kawo aiki ba wai aiki kake jiran kayi ba kowa yanzu ka taba wai yana makaranta ne dan yaje ya samu aiki shi yasa ya zama gaba daya su turawan sun ci gaba Bill Gates jama'a drop out ne mutumin da yafi kowa kudi a duniya yau yana makaranta aka kore shi amma bai koma ya zama dan iska ba sai yaje ci gaba da habbaka abunda ya karanta har yanzu bai wuce shekara bai kai shekara hamsin ba Bill Gates amma yana nan yanzu yafi kowa kudi a duniya me yasa zuwa yayi ya zauna dan abunda ya ko ya sai yaje ci gaba da rili tashi sai ya kirkiro kan shi abubuwa gashi nan shi ya kawo wannan abunda ta zama computer yau a duniya amma yau sai ga mutum wai yana makaranta ai shi fata yake alagawata malam naga wani shugaban custom yazo wurin ka naga makaranta ina so a dauke ni custom a dauke ka custom eh kaje ka kwace dukiyar jama'a bazaa dauke ka ba ai shi so yake a dauke shi immigration ai shi so yake a dauke shi kaza in kace mishi to shikenan zo gashi zaa dauke ka zaa kai ka police academy sai yace a'a shi bai san ya zama dan sanda ina fatan mun gane jama'a saboda haka jama'a ku samari kuskuren ku shine ku zauna baku da aikin yi ka zauna kana jiran a baka wallahil azimi ko karatun qur'ani ka zauna ka ne manzon Allah yace wanda yake baka yafi ka daraja ko karatun qur'ani kake kaga dai shine aiki mafi daraja amma wanda yake dauka ya baka ya ciyar da kai yafi ka daraja a cikin musulunci akwai productivity so ake kai kayi ba wai ayi maka ba yanzu ku duba jama'a kafintoci da teloli har yanzu basu ishi mutane ba idan baku fahimci haka ba yanzu da akayi ta aurar da yan mata din nan yanzu akwai kafintan da ya gudu ya bar garin saboda bai gama aiki ba ga daurin aure zaayi an jima da azahar dan haka dole ya gudu kafintocin sunyi kadan teloli yanzu wata yazo na azumi yanzu zasu fara kwanan dare amma sai wani yaron yayi wa uwashu kukan sallah to me yasa bazaku je ku koyi carpentry ba me yasa bazaku koyi saka ba ba inda aka ce namiji baya saka ku je just da Lagos ku gani ku gani gifta gifta din samari suna saka rigar sanyi amma a nan Zaria wai kun bar yan mata ne kawai suke saka ku shigo da saka ku gani ku samu shaguna ku fashe su ku zuba kekunan saka karti ku zauna kuna saka ku ga yadda ake samun kudi duk abunda ake samun kudi ya halatta kayi babu wata sana'a da zaa ce wannan sana'ar ta mata ce wannan ta maza ce ku je Lagos ku ga yadda samari suke yin saka ku je Jos ku ga yadda samari suke yin saka Allah madaukakin sarki ya taimake mu to wannan kenan jama'a dan haka istimna'i da ake jama'a haramun ne to in ku har akayi shi da watan azumi to haram cin ya kara muni Allah madaukakin sarki ya taimake mu to yana daga cikin ibadoji mafi girma jama'a daga cikin ibadojin ramadan shine ita sallar tarawihi jama'a an kira ta sallar tarawihi ne saboda da watan azumi sahabai in suka yi raka'a hudu sai su zauna su huta su sake yin hudu sai su huta sai su sake yin uku sannan sai su shakata su sha ruwan zamzam sai su tafi sai aka kira ta sallar tarawihi ma'ana sallar da ake ake hutawa a tsakan kanin ta itace sai dai ina son ka gane dan mutumin da yaje wurin tafsiri ya saurari tafsiri to yayi daga nan yaje ya kwanta yayi domin abunda ake nufi da shine samar da wata ibada a cikin dare daga cikin dare rakin ramadan dan haka ko da kayi a cikin dare guda ka samar da sai dai mafi falala itace sallah domin a cikin ta akwai karatun al'qur'ani akwai ruku'u akwai suju'u da akwai tahiya akwai kabbara akwai kaza akwai kaza dan haka wannan kenan yazo a cikin hadisin manzon Allah da ta ruwaito tace annabi baya wuce raka'a goma sha daya haka abun yake ku daina wuce raka'a goma sha daya raka'a sha uku din nan bata daukar ma'anar da kuka bata raka'a ashirin bata daukar wannan ma'anar kuma ita bata inganta ba imam Malik ya ruwaito da kan shi cewa sayyidina Umar raka'a goma sha daya yasa ana yi wa maza ana yi wa mata a zamanin shi dan haka raka'a sha daya shine mafi yawa mafi karanci fa itace raka'a daya wannan raka'a kwaya daya ma'ana zamu iya taruwa a masallaci zaayi ko liman yayi raka'a daya in akayi sallama ya tashi ya tafi kowa ya tafi kuma anyi yazo a cikin Bukhari daga manzon Allah zaa iya yin raka'a uku zaa iya yin raka'a biyar zaa iya yin raka'a bakwai zaa iya yin raka'a tara zaa iya yin raka'a goma sha daya jama'ar musulmi wadannan sune takaitattun bayanai da naso in gabatar sai dai akwai wani azumi da yan bidi'a suka kirkiro wa mutum ne shine azumin tsofaffi wannan azumi an kirkiro shi ne kawai dan a zaptar da tsofaffi dan haka nazo muku da wannan littafi da na dade ina baku labari mai suna abun mamaki gama da azumin tsofaffi wannan malami mai ku samu littafin nan ku karanta shi yace yin azumin tsofaffin nan bashi da kyau domin duk hadisan da sukazo hadisan karya ne yace wajen hadisai talatin da uku ne duk ba daidai bane wadannan hadisai sune ya kawo su ya kawo su amma gaskiya basu tabbata ba Allah madaukakin sarki ya taimake mu to wadannan sune bayanai da zan gabatar a yau insha Allahu ta'ala sai matashiya akan abubuwa guda biyu matashiyar farko itace dangane da abunda ya shafi matsalar da mukayi wa mutum ne bayani a ainihin tudun wada yau kusan wata daya da rabi koma an shiga wata biyu aka ainihin wato zo min da wata ziyara har nan yan jaridun duniya ne gaba daya suka zo ziyara ta muryar America, BBC, muryar Faransa, rediyon Najeriya ne, rediyon jaha ne, jarida duka dai suka zo nan wajen su takwas suka zo wuri na ko su tara da zo suka same ni a nan suka ce sun zo ne suna son muyi kira ga yace musu domin mu cewa ne to yaushe kuma kawai zaku zo kuna yan jarida kawai ku ce mana kun zo ku ce ayi ku ku ku bamu dictation kawai ku ce ga abunda kuke so nace a'a to dai munyi bayanai da su wajen awa biyu na kawo musu wai akan internet da littattafai duk na ba basu dai na su je su duba sai na gana ma ma bama yan jaridu bane kawai masu dai dauko labarai ne kawai domin dan jaridar ma da baya hawa internet bai san me ake ciki ba mu a yau ma bama kallon shi a matsayin dan jarida to dai muna kallon shi mai neman na tuwo ne ya gama makaranta bai samu aiki ba to duk dan abunda aka jefa mishi redio ta fuka kwaso labarai yasa sai kaji nan ya kwaso hatsin bara nan ya kwaso damai kwaso har gudu ya ta rikita mutane jama'a muna gaya muku rahoton da suka fitar suka ce Zaria ta samu saboda mutanen Zaria sun ki yadda babu shakka mutanen Zaria bazamu yadda da ba har sai anyi abu daya sarkin zazzau da su tara mana likitoci likitoci su iya amsa mana tambayoyin da zamuyi musu akan da muka binciko na amma ba maganar mu ba yara bane manya ne mun fi karfin kawai ace ga abunda ake so kuma mu ba bane mu malamai ne masu cin gashin kan mu ba mu ba yaran kowa bane kada wani sarki na gargajiya ko dagaci ko wani karamin alhaki yayi tunanin cewa eh yayi tunanin cewa kawai zai zo yace ne ga abunda yake so mu ba malaman gwamnati bane kuma ba malaman yahudawa bane kuma duk duniya ba wanda muke wa aiki sai Allah saboda haka duk abunda muka gani cewa ba daidai bane zamu gaya wa mutane dan haka jama'ar Zaria abubuwan nan da muka gaya muku ku sake zuwa ku saurari muna nan a kan su dindi bazamu taba yadda da ba saboda me an kirkiro wannan ce dan a share nau'in bakar fata a bayan kasa har ana haka ne ko ba haka ba haka ne to saboda haka tabbas nan da akayi shi sarki yana yi ne dan ya kara kujerar shi
[Segment 3/5 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker unknown]
kujerar shi ne. Saboda haka abun da muke cewa sarki ba da gaske yake ba, dan sarkin yau da za'a sauke shi daga kujerar, gobe bazai fito yana kare ta ba. Shugaban da za'a sauke shi ko ya sauka bazai kare ta ba, ina har muga haka makarfi. Gwamna makarfi da ya sauka daga kan fitowa yayi yana ƙaryata mu muna ƙaryata shi. Har muka yi nasara akan ƙaryata shi yazo yana nadama akan abubuwa. Yanzu makarfi ya fito da kuɗin shi mana ya kashe dan ya ƙara allurar riga kafi, amma tunda ya sauka daga gwamnatin yanzu yayi shiru ashe ba da gaske yake ba. Mu ko mu ne ne iya rayuwar mu muke don mu addini ne. Don haka wannan allurar riga kafi jama'ar Zaria ƙarya ce yaudara ce. Na ɗaya na biyu waɗannan makarantun yan mata da kwantattun zawarawa da suka yi kwante da ake basu wannan roba allurar riga kafi. Wallahi muna muku nasiha Ramadan yazo idan Ramadan yazo a ƙasar Hausa ana ƙoƙarin ana zawarawa ne da yan mata ko naira 250 aka kawo sai a karɓa liman a daura aure ai sauri. Kuyi ƙoƙari a aurar da ku wallahi yafi muku kuna yawo da buta saboda za'a baku naira dubu biyu kuna kwankwaɗawa yayan musulmi guba. Na rantse da Allah allurar riga kafi guba ce kuma ina muƙabalar ta duk wani likita da yake duniya yazo ya rantse mun da Allah cewa ba guba bace. Ai ai mun kawo muku dalilai daga yahudawan akan internet su da kansu suka ce gashi allurar guba ce ga damage da take kuje ku saurari kansu su da muka yi a tudun wada. Wai yanzu sunzo suna raba wa mutane sabulai. Wai sunje sun tara malaman allo wai malaman allo wai sunzo fadar sarki wai sunce wai malaman allo sunsan me ake ciki ne malaman allo ku daina waɗannan yan siyasa mayaudara ne fa zindikai ne wallahi. Wallahil azimi mayaudara ne wallahi yan siyasar nan namu na Najeriya mayaudara ne siyasar da kanta ba da gaske suke ba. Wallahi ba da gaske suke ba ba irin siyasar sardauna bace wadda suke ba da gaske suke ba suna siyasar ne kawai dan me dan su cimma burin su. Saboda yahudawan suna gargadin su in fa ba'ayi allurar riga kafi nan bazasu kawar da su daga kan mulki shiyasa akazo wai aka ƙirƙiro wai har doka aka ƙirƙiro a cikin constitution na Najeriya wai mutumin da ya hana ayi wa ɗanshi allurar riga kafi za'a ɗaure shi tsawon lokaci kaza za'a ci taran shi kaza kuma dole ayi wa ɗan allurar riga kafi wai kuma yanzu ana son ace wai bazaka je aikin hajji ko umara ba sai me wai sai anyi maka allurar riga kafi ko kuma sai ka bada shaida cewa anyi wa yayan ka allurar riga kafi. To ni dai ina da su sun fa 20 a gida na yayan kuma ba ɗayan da za'a yi wa kuma hajji sai naga dama ma zanje ta hukumar alhazzai sai naga dama in ba haka ba duk ku gama shirman kujerun ku sai inje in taka jirgi kawai a Kano kana da kuɗi baka da matsala. Ga jirgi nan kawai shikenan sai ka taka kawai kaje ka tafi. Ba randa su da su gama sai ba kujerun su ina buga mai duguri aka ce akwai jirgi na hau mota na tafi naje na na tafi nayi aikin hajji na ba ruwa na da su saboda haka abun da muke gaya muku yan siyasa bazaku iya wannan yaƙin ba yafi ƙarfin ku ku ja baki kuyi shiru. Allurar riga kafi ba taku bace sarakunan gargajiya kukan abun yafi ƙarfin ku kuyi ƙoƙari a yadda da kuma ayi muku albashi ayi wa gidajen ku fenti yafi muku mutunci fiye da ku ce kuna maganar allurar riga kafi wallahi karon ba ni ne da zangayi yake sa sarkin gargajiya ke maganar allurar riga kafi dan shi gwamnatin bata yadda da shi ba ba da mahalli a cikin ta ba wata ministry ko parastatal ko wata commission da ke ƙarƙashin shi. To amma kuma yazo yana ta haƙiƙan cewa don haka mu abun da muke cewa matsalar ta ilimi ce azo a abun da muka ce musu kenan a haɗa mu may dibet mana. A haɗa mu da su muyi dibet ba wai ace wai ran nan wai ance wai sarkin zazzau wai ya tara malamai wai ya aiko a kira mai shago wai dan Allah mai shago yazo a roƙi albani dan Allah aka ce a'a A iya ran mu fada da allurar riga kafi babu sai dai sarkin zazzau ya tara waɗannan yan bokon maƙaryata da waɗannan yan siyasar mayaudara a tara su sa amsa mana wannan zamu zo da computer fadar sarki mu kafa internet mu nuna musu ga haɗarin su kuma su nuna mana ba haka bane. Amma kawai sarki zai mana wahayi sarki Allah ne yace kawai ga abun da yake so Allah ne kawai yake wannan kuma wahayi ya ƙare akan Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam. Saboda haka jama'ar ƙasar zazzau kada ku sake ku yadda da allurar riga kafi. Duk wanda yake da magana in tayi gumurzu a taro a filin su kuwa ace a tara manya manyan likitoci da yahudawan duniyar da ake ji da su mu mun ce mun shirya zamu tattauna da su. A ƙure mu a kunyata mu mana in da gaske ne dan bakin mu mu ja muyi shiru. Amma wannan ne da aka kawo dan a cutar da mutane. Ina kira zuwa ga iyaye da ke barin ƴaƴayen su a nemi su allurar riga kafi an samu malaman gwamnati suna fitowa suna yaudara wai suna cewa wai ai a musulunci akwai riga kafi akwai bambanci tsakanin akwai riga kafi da kuma allurar riga kafi mu ba muna faɗa akan riga kafin bane ita allurar da aka zo ne kamar misali mutum ne ya zama Miranda ce aka ce ga Miranda amma sai ya zama Miranda an sanya maganin fiya fiya a ciki. Sai ka ce bai halatta a sha wannan Miranda ba sai ya ce ai ya halatta shan Miranda sai a ce shan Miranda ya halatta amma wannan bai halatta ba. Wannan guba ce aka sa muku guba ce aka sa muna kishin ku muna kishin addinin mu muna kishin ƙasar mu. Me yasa da aka je Kaduna aka yi taro Dr Ibrahim Ahmad Aliyu ya miƙe ya gabatar da bayanai me yasa ba'a sa bayanan shi ba sai aka sa bayanan irin waɗannan mayaudaran malaman gwamnati waɗanda kawai fa abun da suke sa rai lokacin hajji yazo za'a basu kujerar hajji. Za'a basu ainihin yanzu ba'a ba malamai kwangila sun isa a basu kwangila ne. Sanda suke da ɗan daraja ne ma ke basu kwangila yanzu akwai wani malami da suke gani da daraja ne ɗaura gwalliya ne za'a aiko mata da wani ɗan matun biri ace ku raba ku bakwai. Saboda ai raina ku abun da suke yi kenan jama'a sun raina malaman saboda mai malaman sun yadda sun karɓi raini da wulakanci a hannun su. Ai wallahi da ne ma suke ba malaman kwangila yanzu wani malami za'a ba kwangila dama sai in suna tsoron ka ne zasu ce zasu baka kwangila. Yanzu bayan sun riga sun gama da su saboda haka abun da muke cewa malaman gwamnati da kuke cewa al'umma su fito su yi allurar riga kafi wallahi ƙarya kuke yi mu munsan baku da dalili. In ba haka ba mu haɗu da ku jama'a abun duk kan ƙungiyar da take ja ta rubuto mana muzo ayi dibet cewa kuma dibet ɗin ba a ɗaki za'a yi ba ba'a duk a filin su kuwa za'a zo a sa a sa radio live talabijin live kowa ya gani muna son ka kawo mana dalilin wannan allurar riga kafi mu kuma duk inda za'a yi maganar allurar riga kafi indai da sama a wurin to zamu haɗa internet zamu jawo internet mu ajiye a wurin mu ce to gashi. Duk ƙaryar ɗan boko da yau iya ƙar ta kenan internet. Saboda haka jama'a wannan allurar riga kafi bamu yadda da ita ba kuma bazamu yadda da ita ba har abada ba dan komai ba saboda me makirci ne aka shiryo wanda kristoci wai suna ganin cewa wai mu musulmi muke ƙi kawai. Manufar shi shine a a a share baƙaƙen fata daga doron duniya ku karanta ku karanta wannan website ɗin ku karanta a nan Haruna kai tayi faɗa professor ne shi na pharmacy a nan yazo ya faɗa ya ce da da da da da da da hantar biri ake yi da ƙodar biri ake yi kuma sai da na lalubo muku ga document ɗin ga hoton biri akan internet gashi sun ce ga abubuwan da ake allurar riga kafi. Mu musulmi cim biri a wurin mu haramun ne. Sannan aka kawo irin poison guba wadda ainihin ake zubawa a ciki. To me ya kai baku kawo sabulu kun bamu ba muna fama da dauda sai yanzu dan kuna son ku yaudare mu. Duk wanda aka ba sabulu ya karɓi amma bazai yadda ya mishi allurar riga kafi ba dan cikin kuɗin ka ne aka fara kwasowa kafin aje lahira. Saboda haka karɓi sabulu karka ƙi karɓe. Eh saboda haka jama'a kada ku yadda da allurar riga kafi. Tanbihi na farko kenan tanbihi na biyu jama'a mun sanar cewa bana zamu fara tafsirai a wurare biyu wurin farko shine wannan masallaci namu na Juma'a zamu fara tafsiri ɗin daga ɗaya ga Ramadan wato daga jibi kenan ƙarfe hudu zuwa ƙarfe biyar da rabi na kowace ma har zuwa 25 ga Ramadan. Wuri na biyu shine a masallacin Markazus Salafiyya da ke tudun wada shi kuma za'a fara tafsirin 15 ga Sha'aban wato kwana 14 da suka wuce to amma gaskiyar lamari abun da ya faru jama'a injiniyoyin da suke jagorancin mana aikin masallacin sunce in aka zuba kankarar dakin irin wannan indai ana so ya zauna lafiya to sai ya kwana a ƙalla 21. Don haka baza'a cire kankarar nan ba suka ce sai goma ta cika ta azumi shine zai haɗa kwana 21 da zuba shi. To sai muka ga ina amfanin ba du ba rai saurin me muke yi dan haka muka ce su ci gaba su gama aikin su a goma ga Ramadan in aka cire to sai muzo sai a share mana masallaci sauran gyare gyare na masallaci a bari sai bayan sallah. Masallaci dai ya samu an rufe to sai a zo a ci gaba da karatu. In Allah ya kaimu sauran bayan sallah a zo ayi plaster ayi shafe ayi duk abun da za'a yi don haka jama'a sai goma ga watan Ramadan za'a fara wannan tafsiri Insha Allahu. To tafsirin nan mu ciya shi kuma ina makwanar shi shima wannan tafsirin sai wannan ranar za'a fara lokaci guda za'a fara su amma sirrin da ke haka shi littafin tafsirin da na sa muku shine na ɗaya babu wannan tafsirin a kasuwa don dama malam Mashhur shi ya buga shi bara bara iwar haka ina Saudiya ya bani copy. Wannan tafsiri yana tafsiri ne akan ayoyin tauhidi da hadisan tauhidi zalla ma'ana tauhidi tafsiri ne al maudu'i tafsiri ne wanda wato yana ware wani abune yana tafsiri akai akan tauhidi. To gaskiya saboda Allah yanzu haka da kuka gani jama'a na sai ticket na samu visa ranar Juma'ar nan zan tafi Saudi Arabia kwana uku zanyi rak ko kwana hudu ko kwana biyar Insha Allahu Ta'ala zanje siyo mana waɗannan tafsirar ne Malam Mashhur zai ainihin buga mana su. To kaɗai abun da muka ce shine wanda yake buƙata ya tattali naira dubu bii zuwa dubu biyu da 500 yayi tsada dubu uku shine tafsirin mujalladi hudu ne. Wannan tafsirin shine zamu karanta to akwai wasu littattafan da yawa waɗanda zamu je mu siyo azo a siyar wa da jama'a kunji abun da zai kaini Saudiyyar nan ranar litinin Insha Allahu Ta'ala amma kamar yadda na ce tafiyar dai ta kwana uku ce domin litinin zan tafi talata Insha Allahu muka yi alƙawari da shi zamu haɗu a Madina muna haɗuwa kuwa zan wuce Makkah da nayi umara in naga dama nan sai in yo kwana in ba haka ba to sai ainihin in zauna zuwa kwana bakwai amma dai bazan yadda wancan lokaci da aka yi alƙawari yayi ban dawo ba Insha Allahu don haka ku taya mu addu'a. Don haka jama'ar musulmi kunji tafsirran ba an fasa bane amma kunji abun da ake ciki. Insha Allahu Ta'ala ƙarfe hudu na ranar la'asar na la'asar na goma ga Ramadan to kazo za'a fara a nan mu ciya Insha Allahu to suma matan aure abun da zan gaya musu kenan da muka ce zamu yi musu karatun safe ɗin nan suma duk sai wannan ranar za'a fara musu Insha Allahu. To lokaci ne ya ƙure mana jama'a ayyuka sunyi mun yawa hatta in zauna in rubuta takarda da ne alƙawari cewa in an samu saɓanin abubuwan da muka rubuta za'a rubuta takarda to lokacin yayi ƙunci don haka sai ayi haƙuri kuma a yaɗa wannan sanarwar. Amma ba'a fasa duk abun da aka yi ba in Allah ya so za'a abin nan. Allah ya taimaka. To ga wata tace malam don Allah a a ƙara jaddadawa iyaye muna son aure wai sai munyi karatu. A saurara jama'a tace suna son aure amma wai iyayen sun ce wai sai sunyi karatu kuma shiga cikin matsala suke waɗannan wanene barace barace ne ko menene gashi nan tace to gashi nan dai eh ala ayyi halin dai wata buduruwar ce ta rubuto an sosa mata in da ke kai ƙayi to kunji fa to wannan fa ta zama vocal ne ita tayi magana da baki wata tana nan abun kamar zai kashe ta. Wallahi iyaye kuji tsoron Allah. Wannan yace maganar rantsuwa mutum yayi rantsuwa cewa bazai shiga gidan wane ba sai in nassa ta rasu. To ya kira shi ta waya domin yayi mishi gaisuwa to ya kenan shikenan yayi mishi ta'aziya sai dai kawai bai zo ya abun nan ba ba baka fara a kanshi. Wannan cewa fitan rana daga gabas ta ɓangarori uku shine Allah yake ishara akan a'a ba wannan bane wannan wani abune yake magana da ba. Wannan yana tambayar azumi ga mai ciki da shayarwa an riga an amsa wannan Insha Allahu. Wannan yace zai iya bayar da kuɗi ayi mishi addu'a akan wata matsala a'a dan in kace bayar da kuɗi wato zaka biya kenan to ai ita addu'a ibada ce. Sai dai ka samu alhajar ta malam ayi mana addu'a Allah ya biya mun buƙata ta in da ɗan abun sadaka sai ka kawo amma in kace zaka bayar wato kenan yanzu alhajar ta malam ga kuɗin nan ayi mun addu'a a'a addu'ar daban sadakar daban amma in aka ɗauka cewa za'a biya shi kuɗin addu'ar ne to kuma ta zama kwangila kenan ba lada. Allah ya kiyaye. Wannan yana cewa don Allah wani website ne littattafai suke kamar su Ɗibbun Nabawi to wato in ka tashi neman abu a internet hanya mafi sauƙi kawai ka tafi ɗaya daga cikin ka buga Google ko Yahoo ka buga Google ko Yahoo kawai sai ka sa abun da kake nema kawai in ya fito kawai ka dubi wannan in ka rubuta sai kace go zai tafi duk inda yake a duniya zai lalubo maka sai kaga website ɗin ina fata an gane. Allah ya taimaka. A faɗakar da matasa wannan yace a faɗakar da matasan sunna a kansu su rinƙa girmama malaman sunna haka ne wannan yana daga cikin albarka da kuma ladabin ilimi lallai ne a girmama malaman sunna jama'a. Wannan yace me yasa ake yin azumi 29 mai makon 30 haka yazo a cikin sunna jama'a dama azumi asalin shi 29 ne annabi tunda yake azumi 29 yake amma yace ne in ba'a ga wata ba sai ayi 30 ɗin don haka shima bai taɓa yin 30 ɗin ba ya taɓa ɗaukan na 30 ɗin sai aka ce mishi an ga wata a jiya sai ya ƙarya yace to tunda an riga lokacin idi ya wuce gobe sai aje a rama. Annabi bai taɓa yin azumi 30 ba jama'a duk azumin da yayi guda 29 ne wasu malamai da suke cewa wai sai ƙwaya ɗaya sai hadisi ne mun kar ku karanta Ibn Mas'ud ya fitar da shi yana nan a cikin sunan ne Tirmizi don haka annabi azumi 29 amma mu matsalar da muke cewa a rinƙa tantance cewa game da ganin wata ɗin. Wanda yake magana wannan yana magana ne don gane da azumin ƙofar Rayyanu da aka ce ƙofar Rayyanu to ita wannan ƙofar wai masu azumi ne kaɗai zasu shiga ko ko yaya azumin na nafila ko ko gaba ɗaya a'a asali ance waɗanda ke baiwa azumi muhimmanci da kuma masu kula da azumin nafila ai akwai waɗanda azumin na nafila ma basa bashi muhimmanci yawa to masu baiwa azumi muhimmanci jimilla ko farilla ko nafila da kuma masu lazimta azumin nafila ɗin. To wani yace wai masu bin aƙidar ƙala ƙato wato masu cewa wai su qur'ani kawai zasu bi. To wannan kan ai aƙida ce ta mu'uta zilawa wanda yake shi marwa mai tsini shine ya kawo ta nan in yana in yana wa'azi yana cewa Allah ta tsini shiyasa ake cewa mai ta tsini ko kuma in ance musu annabi yace sai suce ƙala ƙato wai su ƙato basu yadda ba ba annabi ne yace ba. Wannan muguwar aƙida ce jama'a wadda take ɓata ce kawai inna ma matsalar da aka samu an samu wani shaiɗani ne mai suna Usman Ɗan Gungun da ya samu matsala da ƙungiyar Izala wai sai yace sai ya rusa ƙungiyar Izala don haka bari ya ɗakko abubuwan da Izala take karantar wa ya rusa su don haka sai ya dubi hadisai gaba ɗaya sai ya ce ƙarya ne. To kullum ina faɗi cewa Usman Ɗan Gungun dai ɗan iska ne kuma fitsararre ne. Abun da yasa nake faɗin wannan kalmar wadda itace kaɗai kalmar da ta dace da shi. Ɗan Gungun yace zai rusa Izala don haka zai faɗa da hadisai to amma jeka ka duna kaga a ina Ɗan Gungun yasa ƴaƴan shi makaranta. Makarantun ma ba ma na Izalar ba na Salafiyya ma yasa ƴaƴan shi duk ƴaƴan shi gaba ɗaya mazan su da matan su makarantun Salafiyya yasa. Amma shi kaɗai ne yake wannan iskancin dan me in ya haɗu da mu irin mu da ya san ƙarta san ƙar sai ya dariya yace ai ku mutanen Zaria zafin kai ne da ku. Shaiɗanci ne kawai jama'a wato akwai abubuwan da wasu shaiɗanu wai bari in ɓata wa na rai to ka ɓata wa na rai kayi faɗa da Allah. Jama'a misali fa irin faɗan kenan ai da zuwa yayi samu waɗanda suka kore shi daga ƙungiyar ya tube suka yi dambe. Yafi sauƙi jama'a da kaje kaji hadisan manzon Allah ƙarya ne kuma kai kasan ƙarya kake kuma ƴaƴan ka su taso sai ka ɗibe su ka kai su in da ake karantar
[Segment 4/5 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
da hadisan. Babu yayan shi wadanda suke wadannan shaidanin makarantun. Allah madaukakin sarki ya kiyaye. Dan Allah jama'a ga wata sanarwa zan yi, kuma kowa yi na tsudo Allah domin mun yi sanarwar wasu basu fahimce ta ba. Idan baku manta ba jama'a a ranar rufe karatun mu na karshe na tudun wada nayi sanarwa game da wani committee da na kafa na sa mishi Ma'ana Kowa ya san taron dangin da yan siyasa da yan dariku da shi'a suka yi wajen kashe malam Ja'afar Mahmoud Adam a kasan nan. Kuma wai su suke zaton kenan ta faru ta wuce. Mu kuma muke cewa a'a su saurari sakamako da zai biyo baya, abinda muke cewa kenan. Domin jinin malam Ja'afar Mahmoud Adam bazai tafi a banza ba Haka suka ce ko? Toh akwai committee ne da ni na kafa in nace ni ni mai magana Muhammad Awwal Adam da aka fi sani da Albani Zaria wannan committee shine mutum goma ne na ware. Nace ya tabbata a cikin littafin cewa sahabban manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama da salaf baki dayan su wato hadda tabi'ai sukan sanya wa yayan su suna na shahidi na karshe da aka kashe a cikin su. Misali kamar Mus'ab ibn Umair da aka kashe shi a yakin Uhud. Da aka yi ta haihuwar yaya sai suka sahabbai suka yi ta sa musu Mus'ab Mus'ab toh wannan sunna ce ta sahabban manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Kashe malam Ja'afar Mahmoud Adam yasa dayawa mutane a Najeriya da wajen Najeriya sun tasa wa yayan su suna Ja'afar Ja'afar har ma daga karshe na samu bayanin cewa har ma da mata in aka haifi yarinya mace sai a ce mata Ja'afariya saboda dai son lallai a sa wannan sunnan. Toh wannan abu ne wanda ya tabbata a wurin salaf. Sai nace toh akwai makaranta wadda zan gina ita wannan makarantar wato daya daga cikin makarantu ce dake karkashin Amma ita tana nan daban inda kuka san ta. Amma wannan makarantar bai wuce yan kwanaki kadan da suka wuce ba na sai Cikakken fili ne a tsaye haka dogon fili na bayar anyi design anyi quantity survey anyi komai da komai yau da magariban nan an gama mana a number two a gaskiya wannan makarantar makaranta ce wato muka ce muna son ne muyi wani abu wanda yaya kanana da zasu taso bazasu fuskanci irin matsalolin da muka fuskanta musamman na koyan ba misali mu makarantar allo daban makarantar islamiyya daban makarantar boko daban makarantar koyan sana'a daban ma'ana inda muka koyi karatun allo daban inda muka koyi na islamiyya daban inda muka koyi dinkin keke da kafin ta da walda daban inda kuma muka koyi karatun boko daban toh wannan kuma bashi daga cikin tsarin ilimi abun yayi yawa ka gama nan ka tafi can ka gama nan ka tafi can shine kafin ka gama sai ka fara furfura. Amma in aka samu wani wani tsari wanda zai tasar da yaran tun suna kanana toh dan haka sai na tsara ta Ni na zauna ne din da hannu na wato tsarin da zata gudana da yadda in aka sa yaro a wurin da boko da Mohammadiya da karatun Allah wato hadda Kur'ani da sana'a duk a wurin zai koyo insha Allahu toh shiyasa sai na kira ta domin abu ne wanda bawai munga ane a wani wuri bane wato muna son mu gwada ne muna muna gyara kurakuran kuma malamai masu ilimi suna zuwa suna bamu shawaran gashi kaza gashi kaza gashi kaza. Toh ita wannan makarantar kowa zai iya kawo dan shi sai dai makaranta ce ta kudi kudi kuma tsababa domin kudi muke kashe wa jama'a kaje kaga din duk tsawona yanzu in na shiga bacewa zan yi Je kaga gani ba ba karamin aiki bane gobe zasu fara zuba kankara kaje kaga kudin da muke narkarwa a wurin so ba ba ba abu ne kawai kudi ne za'a kashe tsababa kuma makarantar hawa biyu zata kasance ko hawa uku. Toh sai muka ce a bangaren wannan makarantar dukkan dan da aka sa mai suna Ja'afar ko yar da aka sa mata Ja'afariya toh mun dauki nauyin tun daga farkon makarantar su har su gama har university ko ina suka dace su university ta dauki nauyin haka insha Allahu. Amma ga tsarin yadda abun yake shine idan kana da da da kasan an sa mishi Ja'afar abinda zakai kawai abu daya ne in kai mai takardar haihuwa toh kaje kayi photo stat ta takardar haihuwa. In bakai ba kuma gobe ma zaka iya zuwa kaje kayi mishi wanda za'a rubuta ranar haihuwar shi wanda za'a rubuta sunan shi a rubuta sunan ka kai mahaifi sunan uwar shi sunan kaza sunan kaza sunan kaza. Wannan takardar bata wuce naira dari ba zaka je nan court ayi maka ko ofishin iya ko ofishin gasi ko hakimi. Sai kaje ka adana ta ma in so samu ne kai mata A lullube ta da leda a dafa ta dan zaka ajiye ta sai kaje kayi in kayi a bayan sai ka rubuta mana cikakken sunan ka da cikakken da lambobin wayar ka ko lambar wayar ka sai kazo sai ka ba daya daga cikin yan committee nan mutum goma nima yanzu na manta sunan su sai dai ga malam Ahmad yana daya daga ciki akwai Alhaji Murtala yana daya daga ciki akwai malam akwai malam Musa Sahabi ga sunan dai wadannan sune na iya tunawa sai kaje in ka samu daya daga cikin su kawai sai ka bashi in ka bashi za'a sa a file ne. Idan yayan anan Zaria suke shi ginin ina fatan in Allah ya so nan da badi ma na gama amma asalin plan din ginin na shekara uku ne. Domin abinda yasa na dauki ginin ne daidai da lokacin da yaran su ma sun girma. Shekara uku itace mafi karancin shekarar da za'a sa yaro a Toh ginin na shekara uku ne amma tayi ma kar kai mamaki mai yawa kaje nan da kwana bakwai ma kaga an kai tsawon ginin Magina dai suna nan suna aiki. Toh daidai lokacin da yaran zasu kai shekara uku a lokacin wadanda kenan Zaria sai a kawo mana su. Zamu zamu muna da zamu samu mota dan kareriya safa wadda zata kewaye Zarian nan zata kwaso yaran duk inda suke Nazri ce a zo ayi musu nazri zuwa karfe tara zasu ringa fara karatu zuwa sha biyu awa uku ya ishe su toh dama wasa ne da yan tsalle tsalle da yan wake wake da kuka da cin bredi haka da makamantan su shine nazrin ai kawai reno ne goyo ne jego ne ina fatan an gane. Toh in suka kammala nazri din nan shekara uku sai kuma su fara Primary one two three din duk dai ne ka kashe shekara shida shekara uku nazri shekara uku Primary shekara ukun su da zasu yi toh nazri ne toh daga sanda zasu shiga ko Primary three toh zata koma wadannan yaran sai su zama zamu zo da zaran na gama wannan ginin kuma zan zo in fara ginin hostel insha Allahu ta'ala. Toh wannan ga wadanda kenan Zaria kenan toh da yake sanarwar muna yada ta ne duk Najeriya jama'a ina so zan sata a website ko in sa a jarida ko kuma ma inyi hira da yan jaridu domin sanarwar sanarwar ko ina ne ko daga Nijar ne ko daga ina ne indai kai zaka yi yadda ka kawo dan ka toh abinda muka ce shine a daidai lokacin da zai zama yaran dake nesa sanda za'a sa wadannan a nazri su ma sai a sasa a nazris a wasu makarantu saboda irin takardun da za'a aiko mana na yaran zai samu iya gane sai mu aika wa da iyayen su bayanan irin tarbiyyar da ya kamata a ba yaran a can inda suke dan sun zo sun shiga Primary three ko four da wadannan kada wadannan su tsere musu. Ina fatan kun gane tunda bazai yiwu ayi dai daga dama turu ba daga dama turu a je a kawo yaro yazo ya gama toh kuma kaga yaro dan karami kuma baza a kawo shi amma duk yaran da aka sa shi ya shekara uku yazo ya sake shekara ainihin uku ko kuma ya sake shekara hudu kaga ya shekara nawa kenan? ya shekara bakwai toh a daidai wannan lokacin za'a iya yi musu insha Allahu mun shirya. Toh idan kun fahimci wannan da kyau makarantar asali bawai ta wadannan yaran bace kawai a'a makarantar ta kowa da kowa ce amma duk wanda aka sa a suna Muhammad ko Abubakar ko Ishaq ko Aliyu ko wanene zai biya kudi. Amma wanda ya zama Ja'afar ne toh an dauke mishi kunji maganar kawai kuma wannan sanarwa ance ne daga sanda aka kashe malam Ja'afar zuwa karshen watan Muharram na wannan eh Zulhijja na wannan shekarar wato duk wadanda aka haifa daidai wannan lokacin in har wannan sunan aka sa musu toh suna da kunji daya kenan jama'a dan haka zasu yi nazri da a wannan wurin sana'a ko wani makeken fili kuma shima wanda shi ce za'a ita ma ce za'a cigaba da karantar da su tsari irin wannan ita kam dama ce anan zasu yi toh kuma zamu zo da kosa kosa wadanda zasu zama toh ko su yi anan ko kuma duk inda zasu je su yi karatu dai matukar sunan shi an sa mai ne zamu samu mishi zamu dauki nauyin wannan shine abinda ta daukar wa kanta. Kuma ba abu ne da zaka zo ka roke ni ko ka bani shawara ba a'a abu ne wanda kawai ba wani a ciki haka aka tsara kawai in dan ka yaci ka wannan sharadi ba zuwa zakai kace toh ai kai a'a ya cika ne kawai shikenan. Wannan shine abinda ta daukar wa kanta jama'a dan haka wannan gini yana nan yau din nan an gama an gama hakan gobe goben nan za'a fara zuba kankara zasu fara za'a fara ginin in Allah ya so amma kamar yadda nace ginin ta iya yiwuwa kaga ma na fara shi kuma a tsaye da shi saboda dama kawai dai muke so a kai sai muzo muna yin shi a hankali don cikin shekara uku muke so yaran na girma ginin su ma yana girma insha Allahu. So kunji abinda muka tsara amma kamar yadda nace ga wanda yake son dan shi ya shiga makarantar randa kaji anyi sanarwa zaka iya zuwa ka zaka iya cikewa zaka iya kaza zaka iya kaza makarantar kuma maza da mata ne sai dai da zamu yi itace baza a hada maza a ajiye daya ba baza a hada mata da maza a ajiye daya ba maza ajin su daban kuma malaman su mata ne maza ne mata ajin su daban malaman su mata ne haka muka tsara a makarantar tana nan insha Allahu in kaji kusa da gida na ne nan yanzu ana aiki insha Allahu ta'ala toh wannan shine da zaran mun kai wannan toh sai mu dawo dan dama ginin ne yanzu a gaban mu toh da yake da yake babban aiki ne wajen wata takwas su kansu injiniyoyin suka ce suna zana mana sai makon da ya wuce suka kawo mana toh dama jira muke su kawo mana sun kawo mana dama muna da matsalar ruwa kuma din mu ta kawo ruwa dan haka yanzu bamu da matsala nan da bayan sallah da ikon Allah cikin watan Shawwal zamu fara kuma ginin idan muka abin nan toh shine yafi muhimmanci dama a wurin mu. Toh muka gina insha Allahu sai ya zama kenan ga cikakken masallaci muna da shi a can tudun wada sannan makarantu kuma da yayan mu zasu yi karatu duk ga sunan muna da su sai dai duk mun tara su ne galibi anan gaskiya ina fatan mun gane. Jama'a wannan shine ina fatan kun fahimci sanarwar toh sai wasu da suka yi ta bugo waya suna wata magana wadda kadai dan muna wa'azin ne anan zan bada amsa itace sun nuna sunji dadin ayyukan alheri da suka ji na je inna tayi a wani wuri amma ina makwanan mu ciya amsa ce mai sauki mutanen muciya ne basu so ayi musu ba duk duniya ba inda naso inyi sai a muciya suka ki da suka ki kuma ina da kudi na mai kudi ko yau ba yadda matsala duk duniya har Makkah wallahi baka da matsala in kana da kudi kunga yanzu nan jibi zan tafi Saudiya yanzu banyi booking inda zan sauka ba sai na sauka Jeddah tunda ina da kudi kawai zance a nemo mun daki kafin in isa Makkah an samu in kana da kudi baka da matsala amma in baka da ko ko toh kuma sai kayi marmaza kayi marmaza ka kama fara da wuri. Matsalar yadda ta faru jama'a duk duniya babu inda nake so in zauna in rayu sai muciya duk duniya na shafa dan haka tun daga birnin Kabi wani yazo yaga muciyan nan yaji a kasa dai ce yana son yazo yaga muciyan nan da yake dan boko ne sai yace yace saboda nace ko Makkah aka bani gida zan siyar da shi in zo in zauna a muciya na shafa dan haka kuma haka yake a zuciya ta. Ina jin ina sauran makonni zan gama makaranta na bugo waya anguwan nan ga fili a siyar mun ne zan yi gida aka ce ba na siyarwa bane na gama makaranta nazo da kai na in bi wannan fili wane eh siyar mun da filin nan zan yi gida ba na siyarwa bane wane siyar mun da filin nan zan yi gida toh jama'a da ina dan makaranta na zauna a gidan haya yanzu na girma na zama mahaifi tsakani da Allah sai in cigaba da zama a gidan haya? Ina da hali tsakani da Allah? Dole ne in samu inda zan yi gida toh inda nace ina son in yi gida kowa yace wannan yace na gado ne bazai siyar ba wannan yace zai baro yayan shi wannan yace kaza wannan yace kaza toh ya za'a yi? Har sai da ta kai na sa wasu su taya ni bincike toh a bi ya gagara jama'a dan haka kawai shikenan na koma sai na kama gidan haya anan gaskiya din ana daga filin kofar gida na za'a siyar ko kawai sai nace ga kudi na siya shine na kewaye shi nace toh na darul hadis ne daya kenan wannan fili da kuka gani wanda nake maganar wannan shi mai gidan da nake zaune gidan haya shi yazo ya same ni saboda muna wasa da shi yace toh yaya na na samu maka wani fili fa gashi amma nawa kasan kaza ne nace toh Allah yasa zan yi mukayi wasa da dariya nan da nan ko ya kawo mai fili na dauki kudi na basu kunji yadda aka yi saboda haka kunji sai maganar makaranta maganar makaranta jama'a ita ma makaranta anan anguwan na so inyi hatta maganar masallaci anan anguwan na so inyi makaranta tun 1998 ko 97 jama'a yau shekara goma kenan na tafi Potiskum naje na samu kudi na na shigo da su garin nan tun kafin in shigo na bugo waya ga filaye can na Alhaji Lawan mai taba guda uku a jere nace a je a tuntubi Alhaji Lawan ya siyar mun da filayen nan makaranta zan yi. Aka je aka yi ta wasa da magana aka yi ta wasa da magana aka yi ta wasa da maganar karshe dai aka yi blocking kada in saya kuma ni na tabbatar menene ba ba bakin ciki suke da ni ba kawai sakarci ne kawai gaskiya ba bakin ciki bane wallahi ni na sani ba bakin ciki bane kawai yo da gida nace zan yi shine zasu yi tunanin zanyi competing da su amma makaranta za'a yi wa yayan su saboda haka lokacin suka je suka shiriritar da wannan maganar aka zo na tafi na je na juye kudi na nayi wata harkar sai aka zo aka siyar sanda nazo nace zan siyar filin jama'a naira dubu dari takwas nake da su a gane mazgo a daki na. Kuma filin da aka tashi jama'a filin bai wuce naira dubu dari biyar ba amma saboda nine aka ji zan siya sai aka ce miliyan biyu da rabi sai nace wa abokai na ni fa ban san kan fili ba in miliyan biyu da rabin yayi mu bada wadannan kudin zan tafi neman kudi sai a nemo sauran a siya don ban sani ba suka ce yayi tsada nace aka bari karshe nawa aka sai da filin dubu dari bakwai aka zo aka sai da filin sai da rikici ya taso wanda ya sai filin kuma aka zo ana roko na wai in zo in sai filin nace musu dan boko kar ka samu garanti game da kudin shi yanzu yana da kudi an jima bai da su naje na saka har kudi na a wata harkar bazan rike kudi ba ni ba Alhaji birni bane Allah dan birni ne suke tara kudi dan suyi kudi mu bama tara kudi dan muyi kudi muna da manufa ne akan kudi. So wannan matsalar kunji yadda ta faru dan haka tun ne wannan na biyu da aka taso jama'a ku saurara da kyau ku ji na biyu da aka taso gidan Alhaji Lawan direba inda muke karatu masallacin Alhaji Lawan direba Allah ya gafarta mishi har ya mutu yana kara mana dakuna ana rusawa ana yin ana kara masallaci wata ranni da shi yace da yana da hali da ya bar mana gidan nan sai a maida shi masallaci gaba daya nace Alhaji wallahi kayi duk abinda ake kayi nan din ya isa jama'a bara bara sai nace na samu hali har ina fadin maganar nace kada su fahimci isgilanci ne a'a shi yace da yana da hali a ce toh ni na samu hali su siyar mana da gidan zamu je sai mu rusa gidan sai ayi makaranta akwai dan shi Khamis yana karantar da yara a bar mishi makaranta ya cigaba da karantar da yara na daya kenan na biyu ga wani fili can shi kuma a je mai filin ya siyar mana a maida masallacin can shi mai wannan fili yace bazai siyar ba sai in yaji za'a siyar da wancan gida aka je sai da aka yi wata uku committee na kafa ana ta wasa da hankalin su daga karshe dai aka ce bazaa sai da gida ba shima yace bazai sai da filin shi ba shin jama'a na samu kudin zanyi abinda shine burin rayuwa ta sai in zauna ina jiran mutanen muciya sai randa suka ga dama jama'a zai yiwu? bazai yiwu ba jama'a ni a wuri na bazai yiwu ba koda wani zai ce shi zai hakura koda kudin zasu lalace ni bazan iya hakura ba saboda haka kawai sai na sa su mai shago nace ku bincika mana bazaa samu filaye ne anan zaka ce mafi yawancin filayen dake gaskiya kwatas ma za'a siyar za'a iya siyar maka ko ko mutum bai niyya ba in kace zaka siya kawai sai kaga zai siyar maka nace dan haka jama'a ina gaya muku bayan Allah toh ni kadai nasan filayen da suke wurin
[Segment 5/5 | 01:20:00–end]
[Speaker seg5-spk:0]
Ku wadanda na siya. Ku kawai kuna jin fili daya ne na darul hadisi, ni na san filayen da darul hadisi ta mallaka a wurin. Duk kuma ni na siya da kudi na. Kuma zan je can din in gyara, kuma sai nayi ta irin addu'ar da mai gidan mu manzon Allah yake yi. Cewa ya Allah kamar yadda ka sa mini son in zauna muciyan Allah ka sa mini son in bar ta. Addu'ar ni da na dinga yi kenan don haka gaskiya yanzu ma ko sha'awar zaman unguwar bana yi. Yanzu yau kwana uku da ta wuce ina gaya muku gaskiya ne don kusan me yake ciki ku saurara. Yau kwana uku da ta wuce aka zo aka yi mini tallan fili gashi na ministoci ne ke zasu yi gidaje a wurin. A jikin energy research center. Gashi nan za'a ga wani fili ne wani gyararran fili sai ka kai ka haka, ministoci ne da gwamnoni suke ta siyan shi. Kuma dan nan unguwar ne yazo ya mini talla yace ga fili nan gashi gashi. Naje na gani nace to a kira mai fili. Har ma mai filin saboda ana ta zuwa ba'a iya siya nazo nace a'a ni ina da kudi na a aljihu yanzu. Muyi ciniki ka siyar mini. Yazo da takardu kan nace to ga biri ga waina ga takardu na bashi kudi. Yanzu har na bayar yanzu da gobe ne ma zasu je su suyi mini katanga a wurin gida zan yi a can. Gobe goben nan zan je a yi katanga to amma saboda wancan aiki ya taso na foundation kuma ma'aikatan duk daya ne sai na kwashe su nace duk su bar wannan aiki su koma wancan aikin makaranta idan sun gama ko bani nan an biya kudin bulo da siminti da sauransu suje su katange mana daga baya sai muzo mu gina don haka mutanen muciya bamu muka ki ko kuma ba ni na kiku ba. Nima kuma na san ba kina kukai ba sai dai sakarci ne wato sakarcin shine. Jama'a ni talaka ne. Kuma dan talaka ne. Ina son kuyi marking wannan statement din kuma ku sa shi in court. Don haka tunanin su in aka ce zan sai ka ba sai suyi tunanin ba zai iya ba. Akwai uncompleted building gini ne ba'a gama ba. Sai nayi sha'awar in siya in karasa da aka je aka yi wa mai filin magana wane yana so sai irin izgilancin nan na alhazan birni yace to ya siya mana. Wai izgilanci ne yake yi yace to ya siya mana. Shine da yayi dariya. Karshe nawa aka ce wai dubu dari takwas. Wai dubu dari takwas aka siyar da filin wai gani yake da billahillazi zan iya siya miliyan takwas. Amma shi abun da yake gani. Wannan yaron da yake zuwa makaranta ake kyaushe ya samu haka wannan shine na ce muku sakarci in ba haka ba ya zaku yi tunanin wanda yake talaka ne ba zai samu ba a ina kuka karanta. Kun gano gaibi ne don kasan wanan talaka ko don kasan shi a dan makaranta. Does that mean har abada haka zai zauna kuma kasan wanan mai wadata. Does that mean haka zai zauna da wadata abu ne a hannun Allah fa kuma sirrin Allah ne. Saboda haka jama'a kunji don haka gaskiya saboda Allah. Yanzu abu daya kawai ya rage mana a muciya ko ya rage mana a muciya shine. Masallacin juma'a. Na kafa su Sani su zama committee suje su samu mai filin nan gashi dake gaban masallaci. In ya yarda zai siyar da fili nace kar suyi mini wani dogon turanci ya fadi kudin fili kawai suzo su karba. Yau shekara nawa ana yi yau shekara biyu. Har committee an kafa a masallacin nan kai har iya sai da aka je aka samu. Iya sai da ya kira shi yayi mai magana sai yace yana rokon iyaye cire bakin shi akan wannan maganar. Toh misali jama'a yanzu in aka ji naje na gina masallaci a wani wuri sai ace nayi laifi. Ga inda za'a yi ga dai filin billahillazi idan ya yarda zai siyar gobe karfe shida na asuba kuzo ku fada mini zan baku kudi. Karfe shida na asuba in ya yarda kuzo. Toh amma yace ba zai siyar ba to ya za'ayi jama'a. Toh in naje zan ga wani wurin da ya dace sai in ki jama'a. Ba zai yiwu ba amma mai abun ya neman zafi don abun da na so in developing unguwar da aka haife ni. Ba don fa ina da wani benefit ba don ina da wani amfani da zan samu ba sai lada da nake fata Allah ya bani to amma da ya zama sun gida dan jefa. Don haka gaskiya duk project dina yanzu kunga gaba daya suna can tsallaken. Kadai yanzu abun da na samu shi Alhaji na gaya mishi na samu Alhaji Ali nace to tunda mutanen nan sun sun taurare. Wannan masallaci da muke da shi ai jama'a ko daki kake da shi ciki daya. Kai aure bayan shekara ashirin ai ya kamata ka kara. Saboda me saboda yaya sun samu ko. Jama'a shekara nawa muna sallah a masallacin nan ai yayi mana kadan yanzu. Toh in da bamu da hali to yanzu ni limamin masallacin na samu hali. Ba kuma ina fadin haka ne na alfahari ko ji da kai ba a'a ina fadin hakikanin al'amari ne domin domin andanareting da mutane suke yi suna ainihin wato fassar a haba sun isa gaskiya ina gaya muku mu bamu isa ba amma shi Allah ya isar damu. Shikenan. Kamar yddda suke cewa annabi ne waye a unzila alaihi zikru min bainina. Su ce muna nan din. Haka zuma yan muciyan sai mutum yace muna nan din. Abun na Allah ne fa ba nawa ba don ina nawa ne wasu sun fi ni fasaha wasu sun fi ni waye wasu sun fi ni komai amma abu ne na Allah ya rage. Kamar yadda Allah yace wa uraishawa ne mun sau Darajar su ce sai su basu gane ba. Wato kawai abun da suke kallo suna kallo na ne kamar yadda nake yaro ina shekara biyar ko shekara bakwai. Toh ai ko makaho ya laluba fuskan nan tawa yasan an samu bambanci daga shekara biyar ko shekara bakwai misali to amma su abun da suke kallo kawai abun da suke kallo kenan na daya kenan don haka gaskiya bakin ku mukai ba. Kuma muma mun san bakin mu ne kukai ba sai dai kawai muna ganin kamar yadda muke cewa Mutanen kirki sukan yi sakarci. Toh sakarcin mutanen kirki ne ya kama ku kunsan malaman hadisi haka sukan ce sai ace wanan mutumin kirki ne sai dai yawa kanshi sakarci. Ina fata an gane.
[Speaker seg5-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg5-spk:0]
Saboda haka jama'a. Yanzu abun da ya rage mana kawai wannan masallaci namu shine na samu Alhaji Ali nace mishi to abun da za'ayi. Zamu dage saman shi mu dan kara mai tsawo sai a sa shi ya zama upstairs. In ya zama upstairs shikenan ga Zubairu yana karantar da yaran nan kowa yana jin dadi shikenan ya samar musu aji. Wanda zai cigaba da karantar da su to amma akwai wani fili da Alhaji Ali ya bamu yau shekara ashirin da daya. Wannan filin shima anyi watsi da shi. Wannan filin nasa engineers sunzo sun zana shi anyi mana makaranta wadda zata samar mana da azu zuwa koda guda goma. Da zaran na gama wadancan gine ginen to zamu zo mu gina amma abun da muke cewa a yadda naso jama'a. Wallahil azimi da sai an gama karantun da ba'a taba ganin su ba a nigerian nan wallahi a nan muciya to amma sai sai sukai tunanin haba eh wai sun gan ina yawo da tsohuwar mota ba su san kawai ne wallahi. Tsabar ne wallahi. Tsabar In naga dama gobe sai su gan ina yawo a keke. Wannan baya nuna ban da hali tsabar ne kawai. Toh wannan sai ya cutar da su don haka in aka ce wana zai siya kaza sai su daga kai suyi dariya sai na yawo da tsohuwar mota. Saboda haka jama'a. Kunji wannan. Don haka yanzu wancan masallaci shikan mun barshi iya nan. Wannan masallaci kuma shi zamu dan daga. Mu dan gyara shi da iya abun da zamu yi amma kar ku manta sai da takai na taba muyi kiya a cikin masallacin nan. Nace makobtan masallacin nan su siyar mana da gidajen su mana wasun ku zasu shaida sallah a zahar na miyake. Anyi magana shi wannan mai fili yace shi ba zai siyar ba shi kaza da ya karshe yace to shi ba yanzu zai siyar ba kaza kaza sai nace makobtan masallacin abun da nake sa rai dama da hagu gabas da yamma a samu gidaje kamar guda uku uku suce zasu siyar mana duk sai a siya a fada da masallacin. Don haka masallacin manzon Allah ya zama yadda ya zama jama'a da dan karami ne wannan yace ya bada gidan shi wannan yace ya siyar wannan yace ya sadaukar haka aka abun nan saboda nan ne da'awar ta tsoro. Amma tunda mutanen unguwar. Basu san baiwar da Allah yayi musu ba kamar yadda kuraisha Allah yake ce musu Manzon su ne ko dai basu san shi ba ne da yawa na kan ce basu san ni ba. Toh tunda basu san ni ba to shikenan sai a tafi a haka. Gaskiya amma development din mu duk mun tara shi a can jama'a. Kuma gaskiya babu abun da zai sa mu kar ka ta mu dawo nan. Domin ba ba shashashe bane mu munje can mun fara wani abu kuma ace a'a to ai yanzu mun gane kuskuren mu sai muce ku gyara kuskuren ku akan wani da Allah zai tayar muku nan gaba. Amma mu dai gaskiya yanzu kawai tsakanin mu zamu zo muciya in lokacin karatu ne. A wannan masallacin haka wasu na bakin kwata wasu na bakin rijiya a zauna ayi. Iyakar ta kenan jama'a. Can din kuma haka a zauna a kuntace a kuntacen amma wallahil azimi abun da muka so jama'a munso ne muciyar yadda ake jin ta a cassette. Toh in aka zo a gan muciyar hakikanin to amma sai basu fahimci haka ba amma gaskiya yanzu yanzu hatta addressing dina bana addressing kaina da na. Don ba a nan nake ba yanzu hatta wannan office din jama'a nan da wata uku zai tashi. Kawai zai zama shagon sai da cassette. A'a ba ai ba fushi bane. Wallahi ba fushi bane. Ba fushi bane. Nasa an fitar mini da offices har guda uku a can manya manya yaushe zan tsaya nan daki kamar kabari dama kawai saboda mun jarabtu da son muciyan ne wallahi. Amma yanzu tangantan ga offices ku je ku ga plan din ku gani. Offices ne manya manya ga su can to mun fitar jama'a wanda zamu yi ta aiki. Nan din kawai kwana biyu zaku dinga zuwa kuna siyan wadannan kasu suwa ya zama shagon cassette ba office din albani ba kuma yanzu haka kudin haya wallahi bani na shekara uku da rabi na basu. Na basu kudin haya daga daga september nan da zata shiga shekara uku da rabi na biya ma'ana ba zamu bar gurin ba amma cassette za'a zo a dinga a zo a dinga siyar wa. Amma can kuma shine can office ina me yasa saboda ai kamar yadda nace for how long dan adam zai cigaba da zama a gidan haya. Har zuwa yaushe dan adam zai cigaba ai misali. Tun tsawon da mutane sun ta cewa malam ka siya gida dariya nake musu ai a wannan lokacin bai kamata in siya gida ba don ni dan makaranta ne. Kudin sayan gidan sune nake tabar na tawwa a lokacin nake ta biyan kudin makaranta saboda nau'in irin karantun da nayi makaranta ne masu tsada. In nace a lokacin in bar makarantar inyi gidan zan yi. Toh amma kuma karatun ba zai yiwu ba to amma yanzu na kammala karatun. Fine don haka yanzu me zan sa a gaba sai in sa to yanzu ne zan yi gida shi yasa ma nake cewa irin wadannan masu cewa ya kamata ku ce wa malam yayi gida. Jiya musamman na tafi abuja naje na dauko plan din gida na na abuja kaje kaga irin gidan da zan dinga ba irin gidan ku na zaria nan ba irin gida na na abuja zan yi. Ai dama ayin zaka ci kwado kaci mai mai. Yau wato gidan ma jiya na tafi abuja wuni guda naje na dauko plan din irin plan din gida na abuja tsaf irin shi kawai za'a yi mini a nan saboda haka gaskiyar lamari kunji jama'a wallahi mun gode muku. Ku saurara jama'a ku saurara mun gode muku kun haife mu kunyi tarbiyar mu kunyi mana duk abun da ake wa iyaye sai dai kawai matsalar ita ce sai kuka fahimci cewa Irin wadannan ba zasu taba zama kaza ba. Toh kuma wannan kuskure ne shine abun da mutanen maka sukai wa annabi suke cewa yatimu abi talibin. Marayan gidan abu talib. Eh. Haka ne fa yanzu ni din nan gane a dan muciya jama'a jiya da naje abuja fa aka Tasa na cike form yanzu ni zan wakilci nigeria taro za'ayi a america za'ayi shi a sudan za'ayi shi a eh eh rabat ina ne morocco akan me masana computer na duniya amma sai aka dauko dan muciyan da suka raina. Ka kaga kuskuren su yanzu a nan suna ganin ka dan Allah ba kowa bane ga baban shi ne yana wucewa a keke talaka kawai saboda haka tunanin su haka to amma yanzu kuma ita duniya ta san waye to matsalar ta samu kansu kenan. Na fadi wannan ne wallahi ba don gori ba don ku iyaye na ne ba gori tsakanin mu ba.Annotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Azumi Ibadar Zumunci. Daarul Hadeethis Salafiyyah, 2008. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15885.
Zaria, M. A. A. (2008, 29 août). Azumi Ibadar Zumunci [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15885
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Azumi Ibadar Zumunci. Daarul Hadeethis Salafiyyah, 2008. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15885.
Télécharger
Visualisations
Chargement des visualisations…


