document audiovisuel · Daarul Hadeethis Salafiyyah Citer
Muslim #135-136
- Type
- Enregistrement vidéo
- Créateur
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Editeur
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- numéro
- 135
- 136
- Est une partie de
- Muslim
- Importance matérielle
- 175 minutes
- Support
- DVD
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000034
- contenu
-
============================================================
[Part 1]
============================================================
[Segment 1/5 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker unknown]
Yanzu da muke magana daren Alhamis ne da ya daidai da daren ashirin da biyu ga watan Jumada al-Akhira Hijirar Annabi na da shekara dubu daya da dari hudu da talatin da hudu daidai da daya ga watan Mayu shekara ta dubu biyu da sha uku wannan shine kasan na dari da talatin da biyar daga cikin jerin giyar karatuttukan littafin Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi karatun da mukayi watake da karatun hadisi da aiki da shi shine zama lafiya ga musulmi muna cikin matattarar da Imam Muslim yake taro mana hadisan Annabi dangane da imani yana da malaman farko daga cikin sahabbai da tabi'ai suka yi wa ainihin wadannan hadisai dan Allah kunna mana fankar nan a nan a yau zamu tashi inda Malam yace babin da ke bayani akan cewa mutumin da ke tsoron kar a taba lafiyar shi ko kar a taba rayuwar shi to zai iya ainihin wato dogewa akan imaninsa ma'ana kana tsoron in ka bayyana imaninka zasu hallaka ka to kuma sai kaga cewa kai ba zaka iya boye imaninka ba dan haka sai ka bayyana imaninka da ka bayyana imaninka kuma suka cutar da kai ta hanyar bugu, dauri, kisa ko dai wata cutar wa daban shin yin haka ya halatta ko bai halatta ba shine Malam yake cewa ya halatta mutum yaLire le texte intégral — 22 763 mots restants Réduire le texte intégral
ainihin wato doge akan imaninsa a halin yana jin tsoron cutar da shi da za'a ainihin yi ko kun fahimta jama'a ka doge akan imaninka amma kuma sai ka ainihin saka yi imaninka ka rinka yin abubuwan da zaka yi a boye din Muslim ya samo wannan hadisi daga manya manya malaman shi guda ainihin uku wadannan manyan malamai guda uku sune da kuma ainihin wato wadannan malaman nashi guda daya sai Muslim yace amma lafazin da ya zaba zai kawo shine lafazin kalu dukkanin su cewa suka yi malamin mu wato Malam shi ya ainihin bamu hadisin nan ya karbi wannan hadisi daga malamin shi wato Malam shi ko ya karbi wannan hadisi daga Abu Wa'il shi ko ainihin ya karbi wannan hadisi daga yace muna tare da manzon Allah wani lokaci sai yace ku ki duddiga mana mutum nawa ne suke furuci da kalmar musulunci mutum nawa ne musulmi ku kirga muni sai yake cewa sai muka ce ya manzon Allah da kake neman a kirga mu kana ji mana tsoron wani abu zai same ni ne kana ganin bamu da yawa ma'ana gamu muna tsakanin mu dari shida zuwa ainihin dari bakwai mun kai dari shida zuwa dari bakwai kana jin tsoron wani abu zai same mu ne kana ganin bamu da yawa ne sai manzon Allah yace baku sani ba mai yiwuwa nan gaba a jarabce ku sai kuwa aka jarabce mu har sai da aka waye gari daga cikin mu mutum baya iya yin sallah sai dai a boye to jama'a kun ji wannan hadisi yanzu wannan hadisi yana nuna ma'ana kana tsoron in ka bayyana imaninka za'a cutar da kai in ka bayyana wani abu na ibada kaza za'a cutar da kai sai Imam Muslim yake nuna maka ya halatta ka doge da imaninka amma kuma sai kayi shi a sirrance saboda tsoron cutarwar da ainihin kake ji za'a yi maka ina fatan mun gane to wadannan wasu al'amura ne wadanda suka faru a tarihi amma a zamanin manzon Allah basu faru ba manzon Allah yake musu ishara zuwa gare shi ko bahaushe da manyan shi ba wahayi ake musu ba yakan ce abin da babba ya hango a zaune yaro ko yana tsaye baya hango wa ko yana kan dutse baya hango wa balle manzon Allah da ake mishi wahayi to kuma wannan yana nuna maka irin salo da manzon Allah yake da shi na karantarwa manzon Allah yana nufin ya karantar da su wannan masala ne cewa nan gaba zasu shiga halin musiba wanda yake ibada ma sai dai su rinka yi a boye to amma sai manzon Allah ya fara share fage da cewa ku kirga munu musulmi nawa ne suke fadin kalmomin musulunci mutum nawa ne musulmi sai suka ce ah ya manzon Allah kana ganin mu 'yan kadan ne har kana ji mana tsoron wani abu zai same mu ne to amma dai mu dari shida ne zuwa dari bakwai sai manzon Allah yace mai yiwuwa nan gaba za'a jarabce ku ne to da yake wahayi ake mishi da ya tashi sai yace mai yiwuwa to cewar shiga mai yiwuwa da yake wahayi ake mishi duk daya take da yanke yace saboda za'a jarabce ku ne nan gaba shi yasa nake fada muku haka dan in kintsa zuciyarku ku tattali yadda zaku iya yi yace haka ko al'amari yazo ya faru aka ainihin jarabce mu har sai da muka koma sallah ma daya daga cikin mu a boye yake yi bari ku ji daga cikin maganganun da manyan malamai suka yi da yazo tattaunawa dangane da ma'anar wannan hadisi sai yake cewa a cikin yace a zahiri Annabi yana ishara ne zuwa ga abin da ya faru bayan shi a karshen khalifancin Usman an samu wasu sarakuna daga cikin wadanda ke rike da sarauta ainihin a kasar Kufa a lokacin da yake jinkirtar da sallah ko kuma yana yin sallah ba irin yadda ta dace ba sai aka samu wasu daga cikin malamai masu tsoron Allah in suka lokacin sallah yayi sai su je sai suyi sallar su a sirrance da yake sarkin shine limami a lokacin shi kuma in tashi tayi lokacin sai su je sai su bi wannan ainihin sarkin sun riga sun yi wa Allah tashi sallah amma yanzu kuma saboda suna tsoron imaninsu sai kuma ainihin sai su taho sai suyi tare da wannan ainihin mai sarauta saboda tsoron fitina kuma sai ya dawo sai ya bi wannan mai sarauta sallah ina fatan an gane shine ibn Hajrin yake cewa kace manzon Allah yana kwatanta wannan halin ne wasu kuma suka ce ah ah shi kanshi sayyidina Usman ai ya kasance shi a halin tafiya yana cika sallah to sai ya zama wasu daga cikin jama'a da ke biye da shi suna ainihin yin kasur sai mutum yaje kasurun shi shi kadai amma kuma sai yazo in lokacin da Usman yazo zai yi sallah zai cika sai ya bi shi saboda tsoron kar ainihin rikice ya faru tsakanin shi da Usman ina fatan an gane karshe Malam yace a takaitaccen takaitawa dai wannan jarabawa da sahabi Huzaifa yake nune zuwa gare ta ta faru ne bayan rayuwar Annabi kuma abin da yake a zahiri shine hakan din ya faru ne daga wasu masu sarauta 'yan gidan Banu Umayya ina fata an gane ko kun fahimta jama'a ma'ana an samu lokacin da shi al-Walidu dan baya yin sallar azahar akan lokaci la'asar baya yin ta akan lokaci gashi kuma shine yake gwamna sannan kuma shine liman to idan lokacin sallah yayi sai a samu wadannan bayin Allah sai su je daya daya daya daya sai mutum ya shiga cikin gidan shi sai ya sallah akan lokaci sannan kuma duk lokacin da aka kira sallah ta sarki to kuma sai ya fito sai ya tare da shi ko kun fahimta jama'a to kaga duk da a lokacin da wannan matsalar ta faru sun kara yawa fiye da yadda suke a zamanin manzon Allah amma kaga yawan su bai shallakar da su daga fitina ba ko kun fahimta to sai Imam Muslim yake hujja da wannan ainihin hadisi akan cewa idan mutum ya samu kanshi a cikin musiba wanda zata takura shi sai ya doge akan imaninsa amma kuma ya sanya ya ainihin zai iya tafiyar da yanayin a lokacin domin kun ga a wannan lokacin wadannan sahabban basu taba tunanin zasu samu kansu a irin wannan halin ba don suna daukan cewa ai musiba ta gama karewa tunda suka tsallako musibar kafiran Makka amma kuma sai ga musiba a cikin gidan musulunci a karkashin wadanda ke da'awar su shugabanni ne na musulunci da musulmai ina fata an gane to Malam yake cewa mas'alolin da zamu tattauna dangane da wannan hadisi wannan hadisin ba ma Muslim ne kadai ya ruwaito shi ba har da Imam Bukhari shima ainihin ya ruwaito wannan hadisi sa'annan kuma daga cikin malamai an samu Imam da Nasa'i dukkanin su sun fitar da ainihin wannan hadisi haka Imam a cikin littafin shi a cikin littafin shi shima ya fitar da wannan hadisi a cikin littafin wannan hadisi ko ba wanda ya lura daga cikin ku yayi mun tambihi ina ta karantawa da tun daga babin mu babin da ke bayani akan halaccin boye imani ga wanda yake jin tsoro kun ga yanzu ne abun ya kara fitowa sosai wannan hadisi yana nuna cewa duk mutumin da yake wa kanshi tsoron wata musiba zata same shi to babu laifi sai ya iya boye imaninsa idan kuma zaka iya dogewa to wannan kuma Allah madaukakin sarki ya baka dama amma dai ana nuna maka halaccin ka dauki ainihin mai sauki din amma in zaka dauka wa kanka din mai wahala to kuma wannan babu laifi amma dai asali addinin musulunci bai hana ka ba in kana tsoron in ka bayyana imaninka wani abu zai cutar da kai to sai ka boye imaninya to sa'annan wannan hadisi yana nuna mana halarcin a samu ainihin wani ko kuma wata roster ko wani list wanda za'a dauki sunayen ainihin wato sojoji wadanda za'a tura yaki wuri kaza da wadanda za'a tura yaki wuri kaza to Malam yace halacci sai yace kuma ta iya yiwuwa ma haka din ya zama dole ne idan bukata ta kama ta iya banbance su waye suka dace su je yaki su wanene basu dace su je yaki ba mai yiwuwa a iya kacin abin da muka karanta a nan na hadisin zaka ga baka ga haka ba ko an samu haka ne a cikin wasu daga cikin riwayoyi wadanda Malam yayi ishara kuma zai zo ya sake ishara su a nan gaba insha Allah wannan yana nuna duk mutanen da suke ganin cewa ai su suna da yawa yawan su yanzu ya kai suyi kaza suna ganin cewa sun dogara da yawan su sun manta da Allah to Allah yana iya yi musu ukuba duk da yawan nasu kaga dai sahabbai sun cewa Annabi kana ji mana tsoron wani abu zai same mu ne gamu da irin wannan yawa kuma duk da yawan nasu sai wannan jarabawa tazo ta samu wannan tayi iri daya da maganar Allah da yake cewa haka ranar yakin Hunain a lokacin da yawan ku ya burge ku sai ya zama yawan naku bai tsina na muku komai ba duniyan nan tayi muku kunci duk da fadin ta sa'annan kuma kuka juya a guje wannan Allah yana dakko mana tarihin abin da ya faru ne a daya daga cikin yakoki na musulunci suna ganin cewa yau kam ai ba wanda ya isa saboda gamu mun fito da yawa sai suka manta da kalmomin dogaro ga Allah koda zuciyarka na cike da dogaro ga Allah to bakin ka ya rinka furta wa koda zuciyarka na cike da alheri to bakin ka ya rinka furta wa na daga cikin ladabin da Allah ya ladabtar da musulmi akan haka to sai ya zama suna ganin cewa ai wannan yawan nasu waye zai yi musu to sai Allah madaukakin sarki ya maida yawan nasu ba a bakin komai ba duk da yadda duniyan nan take da fadi amma sai da tayi musu kunci ko duk da yadda wurin yakin yake da fadi amma sai da ya kuntata gare su har suka juya suka gudu wannan hadisi yana nuna mana ainihin wata alama wata mu'ujiza daga cikin mu'ujizoji na Annabi a inda Annabi ya fadi abin da zai faru kuma abin ya faru kamai yadda Annabi ya fade shi domin dai kaji Huzaifa Allah ya kara mishi yarda yace har sai da aka waye gari daga cikin mu akan samu mutanen da basa iya yin sallah sai a boye jama'a mun fahimta a lokacin da Annabi yake musu ishara a lokacin basu hangi abin da yake nufi ba ba amma abin da yayi ishara kuma sai gashi ya faru wannan shi yake tabbatar da manzanci na manzon Allah kamai yadda munji ire iren haka ta faru da dama Annabi zai fada abu karara ko yayi ishara zuwa gare shi kuma abin sai ya faru kamai yadda yayi fade shi wannan hadisi yana nuna mana irin tsananin tausayi da manzon Allah yake da shi da kuma tausasa wa sahabban shi a gamu musamman ma'ana Annabi yana da cikakken tausayi ga dukkan al'umma ga dukkan halitta Allah ya aiko shi ne dan ya zama rahma ga dukkanin halittu gaba daya to amma Annabi kuma yana da tausasa wa da tausayi na musamman ga sahabban shi sannan al'ummar shi baki daya musulmi da wadanda ba musulmi ba Annabi yana da tausaya musu dan haka Annabi yana tsoratar da ainihin musulmi gama da duk wani bala'i da zai same su ko manzon Allah yana basu labarin dukkanin wani bala'i da zai same su ta yadda yake za'a rinka ainihin kintsawa domin suyi tattalin shiri na hakuri wannan yana daga cikin na da'awa jama'a dukkan da'awa dukkan da'awa indai da'awa ce irin ta Annabawa dole a rinka tarbiyarku akan ainihin daure wa gama da duk halin da kuka samu kanku domin babu yadda za'a yi kuna imani har ka kuma kafirai ainihin su baku ku tafi haka zaku yi ta samun jarabawa daga kafirai da munafukai da zindikai zaku ji da fatan baki zaku gani a
[Segment 2/5 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
kace zaku gani a rubuce, zaku ji a kafofin yada bayanai ba inda ba zaku ji ba. Allah madaukakin sarki duk ya fada mana haka, kuma Allah bai lamunce mana cewa haka ba zata faru ba, amma abinda yace mana idan kukayi hakuri kuka sa tsoron Allah a cikin al'amarin ku duk wani ma kirci da kulle kulle da zasuyi muku bazai cutar daku ba amma Allah baice bazasu cutar ba so duk wanda yake yin ba musulunci kake ba indai musuluncin baka baka cewa ga abubuwan da zasu iya faruwa ga abubuwan da zasu iya faruwa. Saboda haka in sukazo suka faru sai kazo sai ka gigice, sai ka rude, sai kace yaya yaya ta yaya haka zata faru sai in ba musuluncin kuke yi ba toh wajibi ne kuma toh yana daga cikin alamomin da'awa ta gaskiya inma mai da'awar annabi ne toh ta hanyar wahayi da shiryarwa da Allah yake mishi ya rinka hasaso abubuwan da Allah ya fada mishi yana gaya muku idan ba haka ba kuma ya rinka amfani da torch light irin ta annabta yana haska gaba yana tsinkayo menene zai faru saboda ganin wadansu abubuwa da Allah ya fadi a Qur'ani da wasu abubuwa da annabi ya fadi a hadisi da kuma auna yanayi toh sai ya rinka gaya muku ga abubuwan yadda zasu kasance ga yadda zasu kasance dan ko kuma ku zama a bisa shiri da hakuri ina fata an gane
[Speaker seg2-spk:1]
na'am
[Speaker seg2-spk:0]
domin ku sani da'awa tazo ne dan ta canza halin da ake ciki mumuna ta maida al'umma zuwa ga nagartaccen hali da'awa ba kawai karatu ne ake ba saboda haka duk wadannan yan Arabiya masu digiri masu diploma masu suzo wurin karatu suyi ta wahalar daku a nahawu aikin banza ne lira biya aji ake yi abinda ake so menene ake so akai zuwa ga al'umma gare shi an fahimta jama'a kaje zakayi kashin kudi a wurin kashiya a banki ayi ta lissafi ana ta buga calculator ana ta buga takardu har lokaci ya aka rufe sai akace toh ka dawo gobe tun safe karfe takwas a a baka print out na takardu a lissafi zero zero zero zero nan shafi wajen tamanin ka tafi gobe ma ka dawo a sake ta lissafi duk aikin banza ne abar wannan lissafin a baka kudi so da haka ku fahimta jama'a domin da dama mutane kawai tunani suke wai da'awa wai karatu ne kawai ake tayi ayi ta karatu kawai shiyasa kullum nake gaya mana dukkanin da'awa indai ta gaskiya ce sai tayi inkari akan shirka da bid'a da zalunci da kuma fasikanci dukkan da'awa wadannan na daga cikin siffofin da'awar annabawa domin mutane da ake samun su ba akan shiriya suke ta annabawa ba inma a samu wani yana shirka inma a samu wani yana bid'a inma a samu wani yana zalunci inma a samu wani yana fasikanci duk wanda akayi magana akan abinda yake zai ce dashi ake zai ce fada aka zo neman shi dashi toh zai ainihin juyo kuwa toh in ya juyo toh shi ake kira ma kirci toh dole ne ku zama cikin shirin daure wannan ma kircin amma in kukace kawai zakuyi ta fadin wane yayi shirka wane kaza bid'a ne kaza ba daidai bane kaza ba, sannan kuma kuna tunanin wai abu zai kasance muku daidai toh gaskiya kuna yaudarar kanku ne don haka ina matasa wadanda zaka ga karatu kawai suke ta bata lokaci ai ta bata lokaci ana ta karatu ai ta bata lokaci ana karatu babu inkarin munkari babu amr bil ma'aruf wanda Allah madaukakin sarki ya siffanta wannan itace siffa mafi girma ta wannan al'umma Allah da kanshi ya yarda cewa ga wasu ma suma suna umarni da kyakyawa suna hana mumuna sai dai kuma basu da imani amma ku kuna umarni da kyakyawa kuna hana mumuna sannan kuma kuna da imani da Allah sai yace ahlul kitabi ma suna umarni da kyakyawa suna hana mumuna sai dai basu da imani da suna da imani da al'amarin ya zame musu alheri dan haka ku kiyaye wannan da kyau jama'a dole ne a rinka kintsa ku ana shirya ku zuwa ga in matsala ta faru me ya kamata ya ya kamata shiyasa kaga annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama yake fada musu ga irin yadda hali zai kasance domin su zama ainihin a cikin shiri da kuma yadda zasu dogara ga Allah da wannan sai gaskiyar maganar Allah ta bayyana da Allah yace hakika manzo yazo muku daga cikinku abin duk dake wahalishe ku yana batawa wannan rai yana batawa wannan manzo rai ya naimuku fatan alheri sannan yana jin tausayin momine kuma yana tausasa musu toh na daga cikin tausayi din ya fada wa al'umma abinda zai faru gaba dan su shirya wa al'amarin na daga cikin darsan da muke dauka a karkashin wannan karatu ka sani da cewa imamul Bukhari shi da kanshi ya kulla wani babi a cikin kitabul jihadi na littafin shi as sahih yace babin dake bayani akan shugaban jama'a ya rubuta ainihin wato mutane mutanen da za'a tafi jihadi dasu wato ya zama tafiya jihadi din ba kawai za'ayi ainihin rududu bane asan su waye zasu tafi rana kaza yaushe zasu dawo su wanene zasu tafi lokaci kaza toh sai imamul Bukhari kulla wannan babi al imamu ibnul munayyar darasin fikihu dake cikin wannan babi dan kada mutane suyi tunanin cewa rubuta sojoji da zasu je jihadi da kuma kididdige adadin su zai iya zama wata kafa ta rashin albarka bansan ko kun hasaso abinda malam yake nufi ba wato kawai a dibi wadanda zasu tafi ba tare da adadi ba abar wadanda zasu zauna ba tare da adadi ba karka dauka cewa haka din shine albarka a cikin tamanin in an kwashe sittin an tafi dasu ma'ana abin zai rashin albarka a'a imamul Bukhari ya kulla wannan babi ne dan ya nuna maka kididdiga a cikin gudanarwa bata kwashe albarka bari in muku da Hausa yadda zaku gane tunda Hausa ne suka haife mu so da dama idan ka ajiye buhun shinkafa a gidan ka ka zaunar da matar ka kace mata toh gwangwani nawa mike ci akace kaza toh kaza kaza idan labari ya shiga kasar Hausa sai ace ai yana da kididdiga ai abun ma zai yi albarka ai ko kun fahimci irin wannan irin wannan ne ibnul munayyar yake cewa annabi yana yin irin wannan kididdigar kuma imamul Bukhari ya kulla babi dan ya nuna maka cewa yin irin wannan kididdigar bata kwashe albarka abu a a gudanar da abu ne a bisa tsari shiyasa komai ku rinka yi a bisa tsari masallaci kunne mutemako kun tara dubu goma toh nawa ake bukata a lokaci kaza a rubuta a sanar da jama'a yanzu saura kaza a rinka yin irin wadannan ihsa'iyya din a gidan ka ya zama kana da kan gado game da me kake kashewa a wata guda idan ya karu ko ya ragu kasan ya zaka fuskanci abu galibi wadannan iyayen mu wadanda suke yan cira rani ne in suga ana haka sai suce ai wannan boko ne ai wannan rashin dogaro ga Allah ne ai wannan kaza ne amma a'a hakane abinda yake daidai rayuwar ka ta zama a bisa basira in ka siyo buhun shinkafa kasan a cikin wata kwana nawa zai yi a'a wata nawa zai muku katan din omo kwana nawa zai muku man shafawa yaya komai ya zama a bisa tsari ne an fahimta jama'a wannan shi zai gudanar maka da al'amari a bisa albarka din bawai kawai a rinka gudanarwa babu woba babu tsari ba jama'a Allah madaukakin sarki ya taimaka sai malam yake cewa shari'a da tayi umarni da a rinka rubuta adadin sojoji da za'a tura su yaki toh saboda wata bukata ce ta addini da kuma ainihin wato irin gano kuskuren da ya faru ainihin a Hunain kaga ai matsalar da ta faru da Allah ya kama mumine a yakin Hunain ko ya faru ne ta bangaren sun tafi ne kawai ba tare da ainihin adadi har suna ganin cewa su kaza ne su kaza ne su kaza ne toh sannan sai yace sai kuma yazo yana tattauna wasu masaloli na ainihin adadi mutanen Kufa sunce kaza in za'a kirga ma'ana wannan masaloli ne na nahawu Allah madaukakin sarki ya taimaka babin dake bayani akan lallashin zuciyar wanda ake tsoron imaninsa saboda raunin shi da kuma hani game da yanke hukunci cewa wane mumini ne in ba kana da wani dalili yanke ba wato wannan babi yana da manya manya bangarori guda biyu bangare na farko shine duk mutumin da ya zama musulmi ne mumini ne sai dai yana da raunin imani toh shari'ar musulunci tayi umarni da lallashin shi da kuma binshi sannu a hankali saboda raunin imaninsa bangare na biyu kuma shari'ar musulunci ta hana kai kuma kai tsaye kace wane mai imani ne ko wane dan aljanna ne sai in kana da dalilin da zaka iya dogara dashi yanke akan haka shine wato lallashin zuciyar wanda ake wa imaninsa tsoro saboda raunin shi da kuma hani da akayi game da yanke hukunci yanke wane yana da ainihin imani in ba kana da dalilin da zaka dogara dashi ba wannan hadisi al imamu Muslim ya ruwaito shi daga malamin shi mai suna malam Muhammad dan Yahaya dan Abi Umar Al Adni ina fata an gane shine malam Muhammad dan Yahaya dan Abi Umar ya bamu hadisi shiko yake cewa malamin mu Sufyanu dan Uyaina ya karantar da mu hadisi shi kuma ya karbo daga malamin shi al imamu Muhammad dan Muslim Al Zuhuri shi ko yace ya karbo wannan hadisi daga Amiru dan Sa'adi dan Abi Waqas shiko Amir ya karbo daga mahaifin shi Sa'adu dan Abi Waqas sahabi ne na annabi Sa'adu yace manzon Allah yayi kaso ya rarraba dukiya wane akai mai kaza wane a bashi kaza sai ni Sa'adu nace ya manzon Allah toh wane fa ai shima ya kamata ka bashi yana da imani da Allah mumini ne mutumin arziki ne sai manzon Allah yace kodai musulmi so uku ina cewa a'a ya manzon Allah wane mumini ne manzon Allah yana bani amsa har so uku yana cewa kodai musulmi sai nace eh sai manzon Allah yace nakan dibi dukiya ko kyauta in baiwa wani mutum amma na fi son wani shi fiye dashi nakan dauki dukiya in ba wane bayar wadda ne ga wane bata nuna na fi son shi na fi son mai yiwuwa wanda ban ba ba shi wane da nake diba nakan bashi nakan bashi ne saboda kada Allah ya kifa shi wuta ma'ana ana lallashin imanin nashi kenan saboda in an kawo an bashi za'a zauna lafiya dashi idan ba'a bashi ba fa toh zai je ya fada zai rubuta zai yi ma kirci zai yi munafinci toh kaga sai yaje ya saka kanshi akan abinda zai shiga wuta saboda me saboda bai samu yaci ba toh shine sai manzon Allah ya bashi toh da an bashi shikenan sai kaga ya zauna lafiya kuma ya bari kun zauna lafiya wannan yana daga cikin tsare tsare na gudanar da al'umma da manzon Allah yake yi ina fata an gane akwai ire iren wadannan a cikin kowace al'umma a cikin masallacin ku akwai a makarantar ku akwai a cikin kungiyar ku ko darikar ku akwai a cikin gwamnatin ku akwai a ko ina akwai wadanda in aka dauka aka basu toh bazasu yi sharri ba, bazasu yi makirci ba, bazasu yi ashar ba, bazasu yi ridda ba idan ku aka hana su toh zasuyi ashar, zasuyi bakan magana, zasuyi sharri, zasuyi ma kirci, zasu kulla abinda su da kansu ranar lahira zasu shiga wuta toh sai annabi yaji tausayin su sai ya diba ya basu toh bayar wannan kar ta fassara maka cewa saboda wane yana da cikakken imani ne shine Sa'adu ya fahimta sai manzon Allah yace mishi a'a shi yana fahimtar toh a ba wane indai ana ba masu imani ne a ba wane ai wane ma mumini ne toh sai sai tarjama ta biyu ta bangare na biyu na hadisin sai yazo a cikin babin shine wane mumini ne sai manzon Allah yace a'a kodai musulmi sai yace a'a mumini ne sai manzon Allah yace um um musulmi dai yace a'a ina ganin mumini ne manzon Allah yace a'a musulmi dai ko kun fahimta jama'a ma'ana indai mumine kake ba toh wane ma mumini ne sai manzon Allah yake nuna a'a bayar wadda nake ba wai imani ne nake dubawa so da dama nakan dubi wanene in an bashi za'a zauna lafiya dashi sai in bashi waye in ba'a bashi ba matsala zata biyo baya zayi kaza zayi kaza zayi kaza wannan yana daga cikin abubuwan da da dama wadanda suke shugabanci daga baya baya dinnan basu kware game da wannan ba shiyasa dan abinda zasu je suyi wa wane da su wane da su wane a dan zauna lafiya dasu sai su gaza sakamakon haka sai wadannan suje su ballo wa kansu su ballo wa kasa matsalar da sai anzo an kashe abinda yafi abinda ya kamata ace an basu tun ana zauna lafiya ko kun fahimta jama'a Allah madaukakin sarki ya kiyaye a cikin wannan riwaya ainihin Amiru dan Sa'adu dan Abi Waqasin yace mahaifin shi Sa'adu dan Abi Waqas ya dibi dukiya ya baiwa wasu jama'a ko ai manzon Allah ya dibi dukiya ya baiwa wasu jama'a Sa'adu yana zauna a cikin wadannan jama'a Sa'adu sai Sa'adu yace sai manzon Allah ya bar wasu daga cikin mutanen ba'a basu ba Sa'adu yace cikin jama'an nan da manzon Allah bai ba ba ai cikin jama'a da manzon Allah ya ba ina cikin su sai ya tsallake wani ni kuma shi wannan da manzon Allah ya tsallake yafi burge ni wajen imani da musulunci sai nace ya manzon Allah mai wane yayi maka ne ni fa ina ganin shi mumini ne toh sai manzon Allah sai bai bawa Sa'adu amsar maganar shi ba sai ya dubi kuskuren da yayi a cikin maganar sai yayi mai gyara me yasa baka ba wane ba kaga da sai ya fadi don ina ganin wane mumini ne toh sai annabi ya gyara mishi kalmar cewa wane mumini ne din sai yace kodai musulmi Sa'adu yace sai na dan yi shiru kadan toh sanin da nayi wa wannan mutum mumini ne mai sallolin daren mai karatun Qur'ani ga magogi ga tasbihi ga kula wannan mutum yana da imani sai nace ya manzon Allah wane da ka hana shi mai ya maka ne
[Segment 3/5 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
Sai manzon Allah yace Ko dai musulmi Yace sai na dan yi shiru kadan inji Sa'ad Sannan alheran wannan mutun da na sani sai suka rinjaye ni Sai nace ya manzon Allah Me yasa baka ba wane bane Ina ganin shi fa yana da imani Wannan yazo da Za mu tattauna wannan insha Allahu Ina ganin shi mu'mini ne ko ina tsammani shi mu'mini ne in ya gina shi akan Sai manzon Allah yace ko dai musulmi Kaga manzon Allah ya cije akan gyarawa Sa'ad wannan kuskuren ko To bayan da ya tabbatar mai da gyaran sannan sai Yace Nakan dauki dukiya in ba wani mutun Amma wanda na hana Nafi so fiye da wanda na ba Ina yiwa shi wanda nake ba haka din ne Domin tsoron kar a kifa shi akan fuskar shi a wuta Jama'a kun fahimci wannan da kyau Ma'ana saboda in ba'a bashi ba zai fadi magana zai yi kaza zai yi kaza zai yi kaza An fahimci wannan da kyau jama'a Wannan ana magana akan tafiya ne irin tafiya wadda take ta tsarin gwamnati na musulunci jama'a Tafiya irin ta tsari na gwamnati na musulunci wanda a yau yafi kama da tafiya irin ta kungiyoyi da mutanen ainihin dariku sune wadanda suke samun kudi da sunan gwamnati Wadanda suke samun kudi da sunan kungiya wadanda suke samun kudi da sunan darikar su ko da sunan wata Lallai ne dole a ringa duban wane da wane ana ba Amma idan tafiya ce ta cewa kowa mai zaman kanshi ne Wannan babu dalilin da wani zai ce in ba'a bashi ba zai fadi kaza don kowa yana ci da kanshi ne Wato ina yi mana misali ne na wake Yanzu misali Akwai kungiyoyi kamar kungiyar Akwai gwamnatoci da wasu masu kudi dake diban kudi suna basu saboda sun ga suna ayyuka na addini Akwai dariku irin tijjaniya ko kadiriya akwai wadanda ke diban sadaka ko bai ko ko zaka suna basu saboda suna ganin suna ayyuka na addini To irin wannan in aka tashi to a raba wane a raba wane a raba wane to sai a ringa duban su wanene wadanda suke da imani Da da raunin imani An fahimta ko sai a ringa diba sai ana basu shine ana dan tattausar su kenan Amma kunga tafiya irin tamu wannan jama'a Ba wanda zai samu kudi cikin mu kace dole sai ya baka kana jin haushin wane don bai je ya samo da sunan kungiyar ba don ba kungiya bace bai je ya samo da sunan tafiyar ba A ma'aikacin gwamnati ne dan kasuwa ne a wata harkar shi yaje yayi in ya ga dama ya baka in bai ga dama ba bazai baka ba bazaka ji haushin shi ba don ku ringa fassarar abubuwa yadda suke jama'a Idan an karbo kudi da sunan ku to a zo a raba muku Shiyasa a cikin In aka kawo dukiya in ba an same shi a gida ba baya yadda ta shigo gidan shi ba Yana masallaci aka kawo sai ya zaman shi sai a zube a gaban shi Wane eh Zodibi wane ungo wane dibi har ta kare shikenan ya tafi Wata ran yana gida aka kawo zinari a raba musulmi Da yayi ta sallar la'asar sai ya manta da zinarin yana sallar sai tashi a guje je dauko yazo ya ajiye musu yace gashi Ko kun fahimta jama'a Amma kaga a daidai wannan lokaci Abubakar yana da kudi Usman yana da kudi Abdurrahman Sa'ad duk suna da kudi Ba'a tursasasu fito da kudin su ba kowa ba don kudin su ne wannan da suka samo da kasuwancin su to ku ringa banbance abubuwa jama'a Ko kun fahimta jama'a Don mutane galibi a irin wadannan zamunan sai nake ganin basu da fahimta auna abubuwa idan kuka kafa kungiya kamar izala Ko kamar jama'atu nasirul islam ko ansaru wane ko ahbabu wane ko ushaku wane to akwai wadanda zasu ringa kawo muku kudi da sunan kungiyar ku To kada wani mutun daya ko wasu mutane su zama su kadai zasu ci Sai a ringa yayyafawa Kowa na samo to in ya zama al'amarin ya kai bazai yiwu kowa ya samo ba to sai a dubi su wanene wadanda in ba'a basu ba in suka shiga gari zasu ballo kungiya sharri Ko zasu fadi wata kalma da sai sunyi dalarar lahira Allah ya maka su a wuta To sai a ke shugaban yanki kaza zo eh rike kaza Kar maka Allah hadda mu ace a'a ai kun cancanta to shikenan sai ga an je an zauna lafiya da shi Saboda an bashi ne Inda ba'a bashi ba zai jawo bala'i Ko kun fahimta jama'a To haka tafiya ta dariku to amma kamar yadda nake gaya mana irin tafiyar da annabi sallallahu alaihi wa sallama yayi a farkon musulunci kafin a samar da gwamnatin musulunci annabi bai taba tursasawa Abubakar cewa ya fito da kudin shi a rabawa kowa ba A lokacin da Abubakar yake yafi kowa kudi Gasu Bilal su kuma sun fi kowa talauci Anzo Madina gasu Abdurrahman bin Auf sun fi kowa kudi gasu Abu Huraira su kuma sun fi kowa talauci To wannan irin tsarin ko shine yafi kama da irin tafiyar mu da muke musu albani dake manhaji na salaf Ba muna tafiya ne a kungiya ba Bama zuwa bamu taba ba kuma mun karbo kudi a wani wuri don mu zo muyi aikin da'awa ko muyiwa mutane kuma wani bai taba ganganci ko kuskure ko sadaka ya kawo mana ba Saboda haka duk inda kuka gan mu da kudi To namu ne duk wanda ka gani da kudi a cikin tafiyar nashi ne bamu da hakki a kai kar kaje kace yaya muna so mu gina makaranta ga wane yana da kazaman kudi a'a nashi ne ba dole bai bayar Don ba da sunan mu yaje ya samo kudin shi ba Ga annabi yana musuluncin ana fama da wadannan wahalalon amma Abubakar yana da su wane yana da su wane yana da su aka zo Madina gasu Abdurrahman bin Auf gashi kaza gashi kaza ga wasu kuma suna mutuwa basu da likafani So in ya ga dama ya kawo ya bayar shikenan in bai bayar ba shikenan to ku ringa tsayawa kuna auna irin wadannan in kuna fassara hadisan in ba haka ba sai ka samu matsala a cikin tafiyar ka Mu fara gini sai shekara guda bamu zuba shi ba sai kaga cikin mu ga wani yana da miliyan dari so dari Sai kaga kana fada a gefe a'a baka da hurumar da zakayi fada don ba da sunan mu yaje ya samo ba Ko kun fahimta jama'a to haka zaka je ka samu matasa nan in ka shiga gari sai kaji suna korafi gasu albani sun samu kudi ya bazasu yiwa ahlu sunna kaza ba a'a Su albani sun samu kudin su ne nasu na kansu ba da sunan tafiyar ahlu sunna ba amma sai ace gasu zazzaki sun samu kudi sune wayan shi a kaza anyi waya ra talatin aure anyi a'a anje an karbo ne da sunan tafiyar so ka ringa banbance wa Wando yaje ya karbo kudi da sunan ku yazo yayi muku aiki wanda ko yaje samo kudi da jibin kanshi in ya ga dama yayi in bai ga dama ba baku da hakki Ku banbance wannan yana da kyau kwarai da gaske Allah madaukakin sarki ya taimake mu Saboda dan Najeriya wallahi tuntuni yake fadi ana dariya yau wajen shekara arba'in Dan Najeriya wallahi in ba'a yi fassara kuru kuru ba Wallahi in ba irin wannan misalin ba dayawa ina son in gaya muku ko irin wannan ya haifar da rudani dayawa a wurare So da dama zanje wa'azi sai inje in samu suna rikici A to ai malam gashi wane ya abun nan sai ince a'a Ai ana tafiyar nan tare da shi yanzu ya zama komishina ba ruwan shi da mu a'a Dama an bashi komishina ne a mada dinku Sai ku tsaya ku duba in an bashi komishina ne a mada dinku to duk abun da ya samo zai kawo muku Amma a'a yana zuwa masallacin ku yana zuwa makarantar ku kuma dan jam'iya kaza ne Me wa anzo zabe ma zaku iya juya mai baya Sai je samu komishina To sai yaci kudin shi shi kadai in ya ga dama ya bayar in bai ga dama ba Ku ha ku rasa masallacin sallah ma ba ruwan shi ba hakkin ba hakkin shi bane So ku ringa auna wadannan abubuwan nakan tafi wurare gombe bauchi sokoto katsina sai inje in samu akwai irin wadannan ligingimu sai nake fahimtar akwai karancin suranta abubuwa a yadda suke A ringa tsayawa ana suranta abubuwa a yadda suke Ko kun fahimta jama'a Wanka ne yana da kudi kai kuma kana talaka sai kayi ta kunkuni dan mai bai azurta ka ba Ba akwai haka a cikin al'adun mu ba Da ya tashi ya tafi yaje ya karbo kudi ne a mada din gidan ku balle in aka zo a raba Yaje ya nemo ne to in yazo ya dan sai maka baburu yace gashi nan ka ringa a chaba Kar kace a'a kai kana hawa jip kana tafiya Abuja kana shiga jirgin sama ni ka bar ni ina a chaba a'a Ba shi ya barka ba Allah ne ya barka Amma da zuwa yayi ya karbo da sunan uban ku to in yazo sai ayi raba daidai To ku ringa fahimtar wadannan Yauwa Allah ya taimaka
[Speaker seg3-spk:1]
Amin
[Speaker seg3-spk:0]
To malam yake cewa Wannan hadisin da mu gama karanta jama'a Bukhari da Muslim sun fitar da shi gaba dayansu ba Muslim din kadai ba kamar yadda cikin malamai kuma an samu al imamu Abu Dauda da Nasa'i sun fitar da shi haka nan al imamu Abu Dauda ya fitar da wannan hadisi a cikin littafin Al imamu Humaili shima ya fitar da shi a cikin littafin Ibnu Abi Shaiba a cikin littafin Al imamu Ahmad a cikin littafin Haka nan Ibnu Hibban a cikin littafin shi Ibnu Manda a cikin Al imamu Abu Nu'aim a cikin Wannan hadisi yana nuna musulunci ta yadda Da alallashi zukatan wadanda ake tsoron imaninsu saboda raunin imani Idan baka da dalili kai tsaye kar kace wane mumini ne sai dai kace ina ganin wane musulmi ne In baka da dalili kai tsaye kar kace wane dan aljanna ne sai dai kace wane in mai fatan aljanna Wannan hadisi yana daga cikin hadisan dake tabbatar mana ashe akwai banbance tsakanin musulunci da imani kenan tunda kaji wannan yana cewa mumini annabi yana cewa musulmi dai To menene musulmi kuma menene musulunci menene imani kuma menene mumini Musulunci shine A mintuwa da wadannan rukunai guda biyar kalmar shahada sallah zaka azumi haji sai ace ka zama musulmi To akida da kuma yadda dasu shine yadda da Allah madaukakin sarki a bisa siffofin shi da sunayen shi da darajojin shi da martabobin shi da yadda da manzannin Allah gaba daya a bisa yadda Allah ya siffanta su da littattafan Allah da mala'ikun Allah da ranar lahira da da kaddara mai kyon ta da mara kyon ta wadannan kuma su ake kira imani To ba dukkanin musulmi ne ya kai martaba ta imani ba Wato ba duk musulmi ne yake da akida ta imani ba Akwai musulmin da bashi da akida ta imani To idan ya taka martabar imani to ya tsallake daga martaba ta musulunci yanzu za'a iya ce mishi musulmi Mu'mini ko kuma ace mishi mu'mini kai tsaye Don haka gaskiya akwai banbance tsakanin Musulmi Da mu'mini Musulmi Shine matakin farko Mumini kuma ya taka martaba ta akida akidar shi tayi daidai da yadda ake fatan ta kasance to sai ace ya zama mu'mini Jama'a kun fahimta wannan na daya daga cikin hadisan da malamai ke amfani dasu wajen tattauna wannan masalar mun taba dan tabota a can baya kadan Malamai kwararru suka ce Wannan hadisi dalili ne akan cewa dan ka fadi musulunci da baki Zuciyar ka bata yadda ba to wannan har yanzu da sauranka Ya sabanin wasu bangare na 'yan shi'a masu suna kirramawa Da kuma murji'awa wadanda suka zake a cikin akidar murji'anci murji'awa sune wadanda suke ganin cewa sabon Allah baya cutar da mutun matukar shi musulmi ne Kai musulmi ne eh to duk abun da kaje kayi sai ace a'a ai musulmi ne ba wani abu ai musulmi ne kawai Da suke cewa ai indai har mutun musulmi ne ya fadi da baki to shikenan wannan ya isar ko da zuciyar shi bata kudurce ba malam yace Wannan kuskure ne asarari ijma'in musulmi yana tunku da wannan kuskuren nasu sannan nasoshin dake tabbatar da kafircin munafukai kunga munafukai da baki ba sun fadi ba sun fadi imani amma a zuci fa Kafirai ne to kuma musulunci ya tabbatar da su kafirai ne To a karkashin wannan kenan cewa da baki ka fadi na yadda da Allah da baki amma zuciyar ka tana cike da kin Allah da rashin yadda da abun da bakin ka ya fadi bai isar ba Wannan hadisi ya nuna ceto a wurin masu shugabanci ga wanda ka kudurce cewa ya dace a cece shi Ina muna gane haka shine da Sa'a yake cewa ai manzon Allah wane ina ganin a bashi Wato manzon Allah shine shugaba an ba wane an ba wane an ba manzon Allah wane ma a bashi ashe babu laifi a matsayin ka da kasan kana da fuska a wurin shugaba Ka iya nemanwa wane wata alfarma ko wani abu amma sai malam yace Ga wanda ya halatta a nemawa alfarma din Admission ne ake na dalibai duk shekara sai aka ce wanda yake da credits biyar Amma wanda yazo da credits hudu da pass za'a iya bashi amma ya rubuta Cewa zai je kafin lokaci kaza yayi jarrabawa yazo da shi To amma shi wane bashi da fuska a wurin visi ko wurin wanene wanene da zai je sai kai ka dauke shi ka kai shi wannan ya halatta domin mai ya cancanta amma bai da hanyar da zai je bai da Haka ake fadi bai da bai da dogon kafa da zai tafi can Ko kun fahimta jama'a to kai sai kana da dogon kafa sai ka kai shi Ina fatan kun gane wannan jama'a wani ma'aikaci ne an murde mishi albashin shi wata biyar ba'a bashi ba bai san ma ina ne zai je yayi magana ba Sai ka nemo shi ya tattaro takardu sai kaga ya dace sai ka dauke sai ka kai shi wurin manaja kaza wurin chif kaza wurin oga kaza ya halatta Ko an fahimta jama'a amma ba ga abun da an san bai dace ba to wannan kuma musulunci bai dada irin wannan ba Allah madaukakin sarki ya taimake mu Sannan kuma wannan ya nuna Idan kazo kana tattaunawa a matsayin ka kai da kake neman ceto wane ko ayiwa wane alfarma ko To ya halatta wajen tattaunawar ka fada shi wanda kake neman alfarma a wurin shi shima ya fada indai wannan bazai kawo wata jayayya ba Yana ce maka a wannan ai yaron bai kamata a dauke shi ba kace a ranka ya dade wannan yaron ai naga an dauki wanda ma bai kai shi ba shiyasa ma nazo sannan kuma a kofar ofishin ka gashi can naga an rubuta wanda yayi kaza wanda yayi kaza Amma da sharadin in haka bazai kai ga wata barna ba na daga cikin barnan shine yace to zaka nuna min aiki na ne a'a to shikenan zo ka zauna kayi To in abun zai kai ga haka to kar ka kai ga haka amma indai har za'a iya tattaunawa ka fahimtar da shi yace eh to shikenan bari zamu duba An fahimta jama'a kenan wato muraji'a da wanda kake neman alfarma tattaunawa ko kamar dan yin jayayya dasu ya danganci yadda yake ne Ko a halin da ka same shi Ta yiwuwa ka same shi yana cikin wani bacin rai to dan abu bai kai ya kawo ba sai ya zama ya tunzura To sai kace ranka ya dade eh naga jama'a sun ma yawa na leko ne mu gaisa amma zan dawo zuwa gobe To kashe gari in kada ka same shi yana shakatawa yana wasa da dariya to sai ka kawo magana sai kasan yadda zaka abun nan wato kullum kamar da nake gaya mana jama'a sai ka zama mai kaifin basira wajen mu'amala da mutane wannan yana daga cikin afuwan ustazai yana daga abun da nake aiban ta ustazai kullum a kai galibi 'yan uwa na ustazai basu da auna Yaya ake mu'amala da mutane shi abun da yake dauka duk duniya mutane iri daya ne Don haka yaje Sokoto yayi mu'amala da wane sai ya taho gombe to haka zai mu'amala da wane a'a sai ka bincika kaga yaya ka samu wane ko kuma yaya yake sai ka mu'amalance shi a yadda ka same shi ko a yadda yake in ka tafi shi kuma wane ka mu'amalance shi a yadda yake to ka kware da mu'amala da mutane kenan Ko kun fahimta jama'a Kuna ga sahaban annabi sallallahu alaihi wa sallama da yake sun kware sun karantu sun dauki hannu a wurin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama In suna tare da manzon Allah sun fahimci abun da manzon Allah baya so sai su bari Anas yace na daga cikin mafi munin abun da manzon Allah baya so shine wani ya mike a tsaye a kanshi Saboda girmamawa ka mike tsaye Yace sun fahimci manzon Allah baya so kuma suna gane haka a fuskar shi don haka basu yi To da suka tafi wurin sarki na ja shi shi kuma abun da yake so kenan To amma kuma annabi da ya nuna musu baya son haka bawai dabi'a ce ba a'a
[Segment 4/5 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
Allah ne ya hana. To yanzu su kam da manzon Allah na so ayi kuma Allah ya yarda za su yi, to amma tunda an tarbiyantar da su ba kyau. Da suka tafi suka ga sarki na ja shi ga irin yadda ake mai. Sai suka ce to shikenan. Abin da za su yi su kuma ba za su shiga fadar ba. Su je su samu can gefe guda kofar fadar su taru kuma su ki aikawa kawai a hange su sun taru. Allah ya sa kun fahimta.
[Speaker seg4-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:0]
Yanzu idan kai kazo fadar mutum to yanzu dole kallon kwas zuwa ga ka'idojin shi dan kai kazo da bukata, amma sai suka samu wuri can nesa sai suka taru. Da yanayin shigar su ta fararen kaya da raunnan su da gyamman su da irin yadda tufafin su yake dagagge ya sabawa mutanen garin. Ana ganin su sai aka hangi wadannan baki ne. Sai aka ce a je a binciki su waye su. Suka ce su baki ne daga gari kaza daga gari kaza. Sai aka je aka gaya sarki na ja shi, da aka gaya sarki na ja shi sai sarki na ja shi sai ya ce su zo. To yanzu kun ga su zo an kira su ne ko? To da suka zo sai suka tsaya a tsaye sai suka gaishe shi. Amma ba a zuwa gaban shi a tsaye da rarrafe ake tahowa. Idan aka tashi tafiya kuma ba a tafiya da baya. Sai dai a juya gaba sai kayi ta rifas kana kallon shi haka kayi ta rifas.
[Speaker seg4-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:0]
Haka sarkin rumawa Bakillani al-imam Abubakar al-Bakillani shi kuma saboda girman kai in zaka shigo wurin shi komai tsiyar ka sai dai ka shigo da ruku'u. Sai yasa sai aka wani dan daki tsududu yadda duk tsiyar ka sai dai ka sai dai kayi haka ka taho. Bakillani da ya tashi shi kuma sai ya juya baya Eh ai in kasan wata baka san wata ba. Sai ya taho da baya a ruku'u an cin amma can yayi wa ruku'un amma kai da duwawu ya taho. Saboda haka ka kware wajen mu'amala da mutane ka san yaya in ka samu kanka a wuri kaza yaya in ka samu kanka a wuri kaza yaya. Ina fata an gane. Da can duk muna primary ana koya mana yanzu duk makarantu al'amura sun barkace. In ka shiga office ya zaka gaida su, ya zaka zauna, ya za kayi kaza, yanzu duk babu wadannan abubuwan gaba daya barkatai kawai ake rayuwa. Kowa ya kosa ne ya marmaza ya gama SSCE ya samu degree koma wanne iri ne yaje ya samu aiki ya ci kudin mutane. Don haka ko maganar da ake so ya fadi bai da yaron da zai fadi. Allah ya kiyaye. Wannan hadisi yana nuna cewa na kasa ya halatta ya fadakar da wanda yake babba ga abin da shi na kasan yake gani daidai ne. In yana ganin cewa shi babba din ya gafala. Ko kun fahimta? Sa'ad kasa yake da manzon Allah yana fadakar da shi a ba wane. Haka kaima ya halatta ka samu shugaban kungiya ko shehin darika ko sarkin gari ko gwamna ko shugaban makaranta ko wanene sai kace mishi ai ranka ya dade ina gani ya kamata ayi kaza. In kana ganin ya gafala ya shagaltu bai yi ba ina fata an gane. Sannan sai ya ke cewa Wannan hadisi yana nuna mana kamar yadda zamu zo mu ji a riwayar dake gaba da wannan. Ya ce lokacin da na manzon Allah yayi haka sai na mike sai nayi wa manzon Allah magana amma a sirrance. Wannan shine abin da yake da damuwa. To a matsayin ka na shugaba ko sarki ko wanene kai kuma ka rinka bada dama ana iya zuwa wa a gana da kai. Kai ya zama kofar ka a rufe take, kai ya zama ba a iya baka iya sauraren mutane. Wannan shine zai ja hanyar da ta kamata a bi ayi maka nasiha ba za a bi ta ba saboda baka bada damar ta ba. Amma in ya zama duk wanda ya ce yana son ganin ka zai iya zuwa ya samu ganin ka shikenan to sai kaga cewa a kai da shi zai maka nasiha amma yayi kokarin ya ganka ya rasa. To shikenan sai kaga yazo wurin dandalin hira ko yazo kaza yazo kaza wanda asalatan ba haka ya kamata ya kasance ba. An so in za kayi nasiha kayi ta a sirrance amma in ya zama komai yin ta a bayyane zai jawo ga wata barna to yanzu kuma yin ta a boye din ya zama wajibi. Ina fata an gane. Wannan karatu namu yau yana nuna mana shugaba ko babba baya karban duk abin da aka bashi shawara kai tsaye idan bai gane amfanin wannan shawara ba ba zai yi aiki da ita ba. Kada daga duk shawarar da aka baka kawai sai kace to ayi aiki da ita to zai zama baka da tsari kenan. Amma ga abu ka kawo sai wani ya ce ranka ya dade ko algafarta malam ko mai girma wane ni ina ganin kaza to sai ka tsaya kayi nazari wani lokacin ka rubuta abin, wani lokacin ma kana bukatar ka kira wasu jama'a masana su taimake ka wajen tattaunawa da fitan maka da mai ce ce mafita dangane da haka. Jama'a kuna fahimta yadda al'amari yake? Wannan shine musulunci fa. Ma'ana kai shugaba ka bada dama a zo a ganka ka bada damar a baka shawara ka bada damar kaza ka bada damar kaza to amma kuma ku kuma kar ku ce duk shawarar da kuka bayar dole a bi. Ko an fahimta jama'a? Domin nan Sa'ad ya bada shawara an karbi shawarar shi? Ba a karba ba. Wannan kada ya hana kuma gobe ka ki ba kace to ai mun bada shawara ba an sa'a bayar yau ba ansa ba muyi wa gobe za a ga ta dace a ansa. Ko an fahimta jama'a? Idan aka baka shawara sai ka lura shi mai baka shawarar saboda Allah yayi. To koda bata yi maka dadi ba kace kar kayi mishi fada. Jama'a kun fahimta? Sai dai ka bayyana mishi to menene daidai. Wannan hadisi yana nuna mana haka. Madadin manzon Allah ya wa Sa'adu fada sai ya nuna mishi a ga dai abin da ya fi dacewa. Saboda haka za a iya baka shawara amma baka ji dadin ta ba ko? To kayi wa ko baka karbe ta ba shi wanda ya baka shawara ka karfafi gwiwar shi kayi mishi bayanin dalilin da yasa wannan shawarar ba itace ta dace ba. Wannan hadisi ko wannan karatu yana nuna mana duk mutumin da yazo neman alfarma in ya zama ba za ayi mishi alfarmar ba jama'a to a bashi hamzari. Idan a rubuce rubuto a bashi a rubuce idan da baki ne ayi mishi jawabi ko kuma a rubuta mishi din. Ko? Idan har aka ga cewa ba za a karbi shawarar wane ba to sai a bashi uzurin dalilin da yasa ba za a karbi shawarar ba. Sannan shi kuma wanda ba a karbi shawarar shi ba ko ba a ba a ba ayi mishi alfarmar da ya nema ba to kar ya dauka an ci mutuncin shi ko an aiban tashi. Wato kullum kamar yadda na ce idan za kayi mu'amala da mutane ka rinka sakin zuciyar ka kar ka yanke shawarar abin da ka taho nema dole ka samu. Ka dauka cewa yanayin da ka samu wanda kazo wurin shi shi zai hukunta samuwa ko rashin samuwar abin ko kuma wata mafitar daban. To amma in ka yanke shawara dana ya ga 'yar wane yana so dan haka kawai sai kace wa danka ka kwantar da hankalin ka wannan yarinya ta zama matar ka, wane da yazo garin nan ba mu muka bashi daki ba. Ko an fahimta jama'a? Sai kaje ka same shi to yarinyar nan eh nayi mata miji da yaro na. Kaga yanzu wannan ba neman shawara ba neman aure kazo ba, kazo fadin doka ne. To in yace a a ai an karbi sadakin ta ma gashi kashi kaza kaza a to to amma dai ka san a garin nan mu ne iyayen gidan ka. To kaga duk kai ka haifa wa kanka matsala amma da karshe sai kace ya raina ka ya abin nan kai ka haifa wa kanka matsala. Duk sanda zaka tafi neman alfarma ko wata bukata ko zaka tafi wani taro ko wata tattaunawa ka dauka cewa yanayi shi zai hukunta menene zai biyo baya. Amma abin da ake so kai ka gaskatu a kan abin da zaka tafi nema. Kai ka amintu a kan abin kana da dalilan dan anyi maka zaka iya tattaunawa. To shikenan sai kaje sai ya ce maka ai wannan yarinya anyi mata miji kaza kaza ina ma da ga yarta ai yarta bata samu miji ba. Sai kace eh to abin da za ayi bari zan turo shi in ya gayyar tayi kaga baka taho da ajandar yar ba. Amma kaga sai kuma kaga sai ya ce ai ma yafi sanyar to ka gani. Haka ake yin al'amari jama'a amma kullum ka dauka cewa kai ka riga ka yanke kaza dan haka in ba haka ba zaka ce an raina ka, in ba haka ba zaka ce wane bai mutunta ka ba to sai kayi ta batawa da mutane kai ta samun kanka a cikin rigingimu wadanda babu ranar karewa su saboda baka mallaki tunanin mutane ba baka kuma mallaki rayuwar su ba. Duk wannan mai gida da kaji ana cewa duk siyasa ce. Zaka je kayi ta kulla abubuwan ka mai gidan ka bai sani ba. Ko kuwa? Allah ya kyauta. Malam yake cewa Wannan karatu na yau yana nuna mana duk al'amarin da za kayi ka rinka tantance wa da tabbatar wa abin duk abin da baka da yakini a kai ko to kar ka bada tabbacin shi. Shine Sa'ad yana bada tabbacin wane mumini ne to shi kuma imani a zuciya ke musulunci ne a baki. To kana bada shaida abin da ke zuci to kar ka rinka yin haka. Saboda haka ustazai irin kalmar nan taku da zaran wane ya dan gina muku masallaci kace ai wane ahlus sunna ne. Ai wane salafi ne. Ai wane tare muke da shi a kan da'awa. A'a. Kai wane dai alhamdulillahi wane musulmi ne kuma muna ganin mutumin kirki ne muna kyautata mishi zato. Amma cewa ahlus sunna ne cewa wane salafi ne kai. Wannan kalmar kaje in kana son kaga su waye salaf ka karanta suratul fatihi. Kaga Kaji wannan na daga cikin ayoyin da take bayyana su waye salaf fa. Sai ka duba kaga wannan da kake cewa salafi ne haka yake irin su ne? Saboda haka yafi sauki a ce wane musulmi ne alhamdulillahi kuma yana da kwazo kware da gaske to kaga in wani tusgaro ya faru dama an san musulmi tusgaro ya fara ya sa ba samun su. Amma ahlus sunna jama'a ahlus sunna bai taba rifas ba ahlus sunna bai taba fada ba a haskan sunna ahlus sunna bai taba kyamar sunna ba to duk sai ka gama ya ban shi ahlus sunna ne kaza kaza kwana biyu kuma sai yazo har masallacin da ya gina ma sai ya kwace. To kaga kai kuma ka bada shaida cewa ahlus sunna ne saboda haka ku rinka lura jama'a. Shine sai malam yake cewa Wannan hadisi yana nuna cewa shugaban musulmi zai iya sarrafa dukiyar musulmi a inda duk ya ga ta dace. Ya dubi dukiya kaza in tazo mai ya dace yayi da ita, dukiya kaza in tazo ya dubi menene ya dace da ita koda talakan basu gane wasu daga cikin al'amuran ba. Dan haka asali a musulunci jama'a in ana maganar musulunci babu demokradiyya a musulunci. Demokradiyya itace ta hanyar zabe na ainihin eh fidda gwani a fitar da wani daga nan ayi kaza a fitar da jam'iyya kaza ta fitar sannan a zo a buga ayi takara ayi kampin ayi gaba ayi yaki ayi kone kone wadannan duk sune lazimin demokradiyya koda wadanda suka tsara ta ba haka suke nufi ba amma sune abubuwan dake faruwa. A musulunci abin da ake ana samar da shugaba ne ta hanyar shugaban da zai wuce in ma in yazo rasuwa yace jama'a na nada muku wane. To kaga bature da yake kafiri ne bai yarda da wannan ba. Sai ya ce Sai ya ce bazan yi mishi mu'aaya ba domin ba a demokradiyance aka zabe shi ba. Ko kuma shugaban ya kafa wani committee na shura wanda su cikin su su fitar da mutum guda ko kuma su dubi wanene ya dace. An fahimta jama'a? Ko kuma shi shugaban ya rinka yin wasu isharori zuwa ga wane da wane da wane da wane. In ya rasu sai mutane suyi amfani da ilimin su da hankalin su da wadannan shawarwari sai su zabi shugaba. To idan aka zabi shugaba irin wannan jama'a to daula a hannun shi take. Kasa a hannun shi take dukiyar kasa a hannun shi take komai a hannun shi yake. Duk abin da yaso zai yi kai tsaye zai yi wannan abin. Sai abin da shi da kanshi ya ga ya kamata ya kafawa kaza committee dan haka babu wasu 'yan majalisa da za su ce basu yarda da kaza ba. Babu. Domin in ma 'yan majalisan ne shine zai dauko wane da wane da wane to ku zo ku bani shawara a kan kaza to rashin yarda ba rashin yarda ne irin na ta waye ba. Rashin yarda ne na cewa za su nuna mai kaza kaza kaza kaza kaza kaza shi yafi shiyasa za ka ga a cikin wannan na demokradiyya din in ya lura ba za su yarda ba shi kuma ya yanke shawara yana so sai a aika musu da wasu sakonni a gida. Ina fata an gane to shikenan sai ga abubuwan sun abin nan. Saboda haka ku kiyaye jama'a. Dukiya ta musulmi tana hannun shugaba ne zai sarrafa ta a inda yaso sai ya dubi menene ya fi dacewa sannan sai mai sannan sai mai. Koda wasu abubuwan talakawa ba za su iya fassara su ba. Domin an amintu shi kuma ba zai zalunci ba. To kun ga duk irin wadannan ko to a irin wannan tsarin rayuwar da muke ba irin su ne zaka dauko ka sa ba. Dan yanzu wani abu ne ake gudanar wa ba irin wannan shugabancin ba. Jama'a kun fahimci wannan da kyau? Wannan karatu ne yau yana nuna mana baka cewa wane dan aljanna ne kamar mutane goma nan da makamantan su da annabi ya tabbatar kamar su Abubakar da Umar da Usmana da Ali da sauran su kamar irin su Khadija da Fatima da Alhasan da Husaini da Ukasha wadannan duk na su ya tabbatar da cewa su 'yan aljanna ne. Ahlus sunna duk sun hadu a kan haka. Nawawi shi ya waccan magana sai Ibn Hajar ya ce a maganar ga yadda ya kamata ya ce wannan karatu yana nuna an hana ka ce wane yana da cikakken imani in ba da nasu a kai ba. Ya ce a cikin wannan nasin babu inda aka yi maganar aljanna balle a ce har wane ka a ce dan aljanna ne kai tsaye imani aka yi magana. Yara ne wai Ibn Hajar yake wa Nawawi. Wannan hadisin suna kawo matsalar aljanna a nan amma matsalar imani ce. To amma kuma da yake shi ma malami ne kwararre Ibn Hajar sai ya ce Ita matsalar haka take amma dai bata a cikin wannan nasin. Wato idan baka da nasin wane dan aljanna ne to kar ka ce dan aljanna ne. Haka matsalar take amma ba a wannan karatin ne ba. Dan haka kawo ta a cikin wannan karatin sai ya ce ba haka bane wannan karatin yana nuna kar ka shaida cikakken imani ga wanda baka da dalili a kan shi. Abin da yasa ba za a goyi bayan Nawawi a kan maganar da Ibn Hajar yayi mai gyaran ta ba saboda matsalar akida ce matsalar akida babu ijtihadi a cikin ta. Ba za ka dauko waccan kai kiyasun waccan da ita ba. Imam al-Bukhari da yazo wannan hadisin sai ya ce wannan hadisin yana nuna an hana na ci wajen roko ko bara. Na ci. Zamuzo mu ji wani lafazi na wannan hadisin ba da jimawa ba. Da manzon Allah ya ce a a ko dai musulmi sai Sa'ad ya ce a ina ganin mumini ne sai da ta kai manzon Allah ya sa hannun shi tsakanin wuyan Sa'ad da ka fada ainihin Sa'ad nan ya dafa haka ya ce kai Sa'ad haba. To shine sai malamai irin sun Imam al-Bukhari suka ce to wannan ya nuna in kana da bukatar wani abu a wurin wani mutum to an hana ka shine na ci. Ka na ci an ce maka a'a ka ce a'a an ce a'a ka ce An hana ka yin na ci in ji Imam al-Bukhari kenan. Za ka ji inda manzon Allah ya ce mishi Sa'ad fada menene abin? An ce maka a'a ka ce a'a ka ce a to fada ni. Kaga yana ishara zuwa ga an hana. Sai wannan magana ta kara nuni a kan cewa an hana na ci a wajen rokon arziki. Amma wannan tsakanin mutum da mutum amma tsakanin ka da Allah ko to kayi na ci. Eh malamai sun nuna wannan ne na ci in ka roki Allah ka fada sau uku. In ka dan yi shuru ka sake fadi sau uku ka sake fadi gobe ma ka sake da'a wajibi ma ka sake da'a har sai an maka. To wannan Allah kai mai amma mutani to akwai matsala saboda Imam al-Shafi'i yana cewa
[Segment 5/5 | 01:20:00–end]
[Speaker seg5-spk:0]
In Allah baka rokon shi jawo shin ka, dan Adam kuma in kana rokon shi, ya ji haushin ka. Tsarki ya tabbata ga Allah. To kayi wa Allah naci akan bukatan ka amma dan Adam in ka fada aka ce a'a to shikenan ka dan sake kiwa kaga ana hararar ka wuce. Ina fata an gane? Na'am. Na'am. Umm. A'a inda dai yake cewa kawai wane musulmi ne ai mumini ne annabi yana ce mishi a'a ko dai mumini eh ko dai musulmi wato da ya kamata ka tabbatar kafin kace mumini ne. To kuma ana ce maka a'a kaza dai kai kuma to ka tabbatar mana shine Ka dinga neman tabbatarwa kafin ka abun nan. Ina fata an gane? Yanzu kamar ka ga baka Ka ga baka nake ya wuce da tsohon mashin sai kaji suna cewa engineer. To kafin ka cigaba da kiran shi engineer bincika baka nake nene ko engineer. Kasan mutane ko lantarki wani ya gyara maka shikenan kasa mai engineer. In kaga kaga abun nan mai shari'a asibiti ta fito tasa irin korayen rigan nan mu duk doctor ake ce mata yace ai wancan doctor ce. Duka. To kaga to a kayi tasabbut tukunna in ba haka ba za'a yi likitan shata a madin gaya. Umm na ganin kurji sai ya jefa wuka na'am.
[Speaker seg5-spk:1]
Tambaya yake akan cewa me yasa ba'a bashi ba?
[Speaker seg5-spk:0]
Mene?
[Speaker seg5-spk:1]
Yace malaka an fulani.
[Speaker seg5-spk:0]
Umm tambaya ce ba tambaya ce ta abun nan kawai yana ne yana kamar jaddadawa takriri ya kamata a bawa ne. Eh Ba tasabbut tasabbut din shine kafin kace wane mumini ne kayi kokarin tabbatarwa tukunna. Ina fata an gane? Ai gashi yace Da kuma barin yanke hukunci ga abun da mutum bai da bai da masaniya akan yanke hukunci yana maganar wannan imanin ne. To sa'annan sai yace Yace wannan hadisi yana nuna halaccin rantsuwa idan zato yarin jaya. Idan zato yarin jaya cewa kana mabirin jayen zato ga wane can zaka iya cewa wallahi ga wane can. Saboda Sa'ad yana rantsewa eh yana cewa wallahi ko kaga yana rantsewa saboda zaton shi ne yarin jaya. Amma kuma manzon Allah bai hana shi ba. Sai ibn hajar yace Amma maganar tashi akwai gyara wanda gyaran ma ba'a boye yake ba. Saboda shi Sa'ad da ya rantse ai ya rantse ne saboda ya samu wannan zato. Kuma shi a wurin shi haka abun yake. Wani ne daga waje yake zato amma shi a wurin shi fa Shi da yakini yake ashe kaga kenan annabi ya dauki akan yakinin shi da yake rantsuwan ne akan haka aka rabu da shi. Ko kun fahimta jama'a? Wato ibn hajirin jama'a in ya tashi sharhin hadisin ba kawai ta kalidanci yake ba. Scholarly aiki yake yana aiki ne irin na masu ilimi. Ma'ana masu ilimi jama'a ba suna duban me wane ya fadi kawai suma su fadi ba. A'a sai sun dubi menene abun da ya fadi daidai ne ko ba daidai bane in ba daidai bane sai su gyara shi yasa zaka ji ana cewa ibn hajirin da wane ya fadi kaza sai ya ci gyara da wane ya fadi kaza sai ya ci gyara. Wannan aikin da ibn hajirin yayi a cikin Shekara ashirin da bakwai yayi yana yin shi. Tun yana yin shi yana da ido sai da ya makance karshe ya karasa littafin da imla'i ne da shifta mujalladi na sha uku na da ka yayi shi. In aka jawo nasin sai yayi sharhi sai an rubuta. Amma duk da haka bayan shekara ashirin da bakwai yana iya gane cewa a cikin mujalladi na daya ya fadi kaza sai kaji yana cewa a wuri kaza da nazo magana kaza na fadi kaza na fadi kaza sai yace a koma a gyara wannan wuri kaza kaza kaza kaza. Wato sunyi kansu da ilimi ne sun saka kansu a cikin ilimi ne su basa komai sai wannan harkan kawai. To amma kai kuma rabin kafar ka tana makaranta rabi tana kasuwa itama ta makaranta a shirye take zata fita a guje amma ta kasuwa a tsaye take ita a wurin to yasa sai ga abubuwan in ka shiga karatun karatun shima yana ce maka a'a saboda shima ya fahimci baka yarda da shi ba. Ina fata an gane? Al kadi yace wannan hadisi yana daga mafi ingancin dalilai da malamai suke hujja da shi wajen banbance tsakanin imani da musulunci. Allah madaukakin sarki ya taimaka. To barin mu karasa ainihin karatun babin yace Wancan hadisin ne dai amma muslim ya kawo shi da wata hanya daban. Yace ne ya bada labari cewa manzon Allah ya bada kyautar dukiya ga wasu mutane Ina zaune a cikin su sai kaga malam yayi dige dige haka sai yace Irin yadda kaji wannan hadisin yayi daya da hadisin da muka gama karantawa na dan uwan ibn shihab sai dai a cikin wannan riwayar an samu kari da ya kara da cewa sai na tashi naje wurin manzon Allah sai nayi mishi nasiha nayi magana da shi a sirrance kaga waccan maganar da ya fadi da muke ji a zahirin can riwaya kamar a sarari ne ko a wannan riwayan tana bayyana cewa a sirrance ne inaje nace mishi ya manzon Allah amma wane kuma ya kamata ka bashi dan ina ganin wane mumini ne mutumin arziki ne a sirrance ne yaje sai nace ya manzon Allah wane da baka bashi ba fa ya akai baka bashi ba a sirrance ne ya gaya mishi wannan magana. Ina fata an gane? A gusa tsarin wannan hadisin ne ake ta samo su ta wasu hanyoyin daban wannan yana daga cikin banbancin muslim akan Idan bukhari ne kunga hadisin duk daya ne sai ya rarraba maka shi ya jefa wannan can ya jefa wannan can ya jefa wannan can dan haka in baka samu malam yayi maka aikin hadawan ba sai kayi ta kallon su hadisai ne daban daban muslim ko yanzu kaga yana tattaro maka su a wuri guda kana taji yanzu riwayar da muka gama karantawa munji tazo da karin cewa maganar da Sa'ad ya gayawa annabi ba da shi da a jama'a bane a sirrance ne to yanzu kuma wannan riwayar kuma gatan muslim yana nuna mana cewa sai manzon Allah ya dafa ko ya bugi tsakanin wuya na da kafada ta sai yace Haba Sa'ad abun fada ne ka fada nace a'a ka fada nace ka fada to fada ne Sannan sai manzon Allah ya fadi wannan maganar kaji na daga cikin fa'idar wannan karin riwayar da al imamu muslim ya kawo Allah madaukakin sarki ya taimaka. Anan ne inda zamu kwana in sha Allahu ta'ala sai anzo karatu na gaba za'a tashi Babin da ke bayani akan karin natsuwan zuci saboda bayanan dalilai wato idan kana kara ganin dalilai akan abun da kake akai kullum sai kaga zuciyar ka tana karan natsuwa da wannan abun. To babbar hanya kamar yadda zaka zo kaji karatun zai bayyana in sha Allahu ko itace sauraron wa'azi zuwa makaranta idan kai malamini ne kuma cigaba da bincike akan abun da dama ka gamsu da shi. To duk lokacin da ka samu kanka akan ka yarda da kaza sai kuma kaga ga wani karan dalili sai kaga ka kara natsuwa kana da imani sai kuma ya zama kana zuwa wurin wa'azi sai kaga imani na karuwa a'a kai malamini ne ka gamsu akan kaza sai ka shiga ka kara bincike sai kaga ka kara ainihin natsuwa akan wadannan abubuwan shine karatun mu na gobe in sha Allahu ta'ala Allah madaukakin sarki ya taimaka anan ne zamu saurara in sha Allahu na'am malam.
[Speaker seg5-spk:2]
Na'am.
[Speaker seg5-spk:0]
Ya danganta Wani ne yake tambaya dangane da mutum ya boye imanin shi saboda tsoron wata fitina ko wata cutarwa. Sai yace yanzu kamar mutumin da yake yankin da in ya tafi saboda gemun shi saboda dagaggen wando da doguwar riga ga magoge a aljihu ga qur'ani mai zi In aka gani za'a ce mishi dan boko haram ne to yanzu ya dace ya aske gemun shi ya take wando ya sanya shat. Shine nake cewa amsa wannan tambayar ya danganci yadda yanayin gurin yake. Akwai yanayin da tsanani yayi tsanani ba'a tsayawa ana bincike ko banbance wa duk wanda aka gani da siffa kaza kawai za'a hallaka shi ne. To a irin wannan halin imma ka hakura da zuwa ziyaran iyayen naka ka takaitu ta hanyar gaishe su a waya da tattaunawa da duk wani abun makamancin haka. Kaga wannan akwai maslaha a ciki sunsan cewa ba ka bijire musu bane yanayi ne ya hukunta amma kuma kana magana da su a waya dan abun da ya kamata ka aika musu kana bi ta hanyar banki ko ta hanyar abokan arziki kana aika musu. Imma in ya zama akwai matsananciyar bukatan kaje to shine sai a dubi zaka iya tafiya yadda in kaje za'a tsaya a bincika a iya tantance ka sai ka tafi da wannan siffar domin wannan ya kara tabbatar musu da cewa ashe masu wannan siffar ba mu gaye bane. Idan ko ya zama babu wannan tantancewar ga iyayen naka sun matsu to a wannan halin babu laifi sai ka ainihin boye wannan siffa taka ta hanya aske gemu da kuma yin shiga irin wanda zata boye ka. A kashin gaskiya saboda Allah wadannan abubuwan sun faru a farkon al'amari. Amma daga karshen al'amari su kansu wadanda ake kira jami'an tsaro sunzo suna amfani da ba dan komi ba saboda wadannan da ake tunanin sune su wane da su wane da su wane sai suka daina yin wannan shigar sai suka koma suna yin wata shigar daban. To da wannan ne zaka gane asali shi a musulunci jama'a idan aka zo bincike dama ba wai mai siffa kaza kawai a'a kowa ake bincike. Yana daga inda kuskuren ya faru. A daidai lokacin da suka shagaltu da masu gemu da masu dagaggen wando suna ta kamawa sai wadanda suke so suyi musu abun da zasu yi su kuma sai su sauya shiga har sai kaga wani yayi kitso ya sanya ya kawo sarka ya sanya ya kawo dankunne guda daya ya sa. Me zai faru? In yazo sai a sai ace a'a obo ya dai ya ashe shine zai ce ya buga musu kaza a can. Baku ji abun da ya faru a jihar adama ba a garin ganye? Da suka je zasu yi mota suka je da jinia su kansu jami'an tsaron da suka zo sai suka sara musu suka wuce da mota da jinia kaga inda tsarin musulunci ne da mai jinia da mara jinia da gwamna da talaka sai an bincike shi kowa sai an bincika. To amma sai aka ci su ta hanyar tunanin su. Idan kazo da jinia in kazo da babban mota baza'a bincike ka ba haka abun yake har yanzu. In kaga an raina ka ance tsaya nan zo ka bude boot to anga motan ne kuna tafiya kuna rangaji kai da ita. Amma kazo da wata mota mai nishi sai kaga an sara maka a'a o gamu muna nan sai a kawo a basu. Ashe abun da za'a buga yana nan a boot an biya su an wuce. To saboda haka a musulunci kowa in yazo binciken shi ake yi. Allah madaukakin sarki ya taimaka Ina fatan kaji amsar jawabin ka malam. Na'am wa'alaikumussalam. Na'am. Eh. Na'am. Na'am. Wadanne ne su? A'a ai sai ka kaya dai malam kasan abun da yawa. Eh? Eh. Eh. To ai duk an karanta su anyi bayani ko baka nan ne? Da na shida Eh. Na sha biyar yana magana akan cewa karka rinka yin naci wajen neman bukatan ka na shida kuma yana magana akan Ilaihi fil amri Muraja'a daban ilha'a daban. Kazo da credit biyar na yaro kana neman vice chancellor ya taimaka maka sai ya kawo magana sai ka fahimci kamar bai gane ma abun da kai kake magana ba. Sai yace a'a ai baza'a dauki wannan ba sai kace a'a ai ranka ya dade ba medicine ne yake so ba accounting ne yake so misali kaga muraja'a kenan amma nan a'a abun da an yarda za'a taimaka maka to kasa naci. So muraja'a kamar istifsar ne kana neman ka fassara mishi kayi mishi bayani ne dan ya gane me kake nufi ku tattauna babu laifi amma ilha'a shine naci kan naci yana ture ka kana nacewa shine basu yi kama da juna ba ba. Ka fahimta? akwai banbanci tsakanin eh na'am. Jama'a anan zamu saurara in sha Allahu
============================================================
[Part 2]
============================================================
[Segment 1/4 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yanzu da muke magana daren litinin ne daidai da daren ashirin da shida ga watan juma'a hijra na da shekara dubu daya da dari hudu da talatin da hudu daidai da biyar ga watan mai shekara ta dubu biyu da sha uku wannan shine kaso na dari da talatin da shida daga cikin jerin giyar karatu ta littafin sahihu muslim wallafar al imamu abul husein muslim ibn al hajjaj Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi karatun da mukayi wa take da karatun hadisi da aiki da shi shine zama lafiya ga musulmi idan ba'a manta ba muna cikin kitabul iman wato matattarar da imam muslim imam muslim yake tattaro mana hadisan annabi dangane da imani yana fassara mana su da fassarar da ya samo daga manyan malaman farko daga cikin ainihin sahabbai da tabi'ai da wadanda suka zo bayan su da kyautatawa a yau zamu tashi babin da ke bayani akan karin natsuwar zuci saboda bayyanar karuwar ko kuma bayyanar dalilai ma'ana ka yarda Allah daya ne to amma in ka kara samun dalilai daga Allah na qur'ani daga manzon Allah na hadisi sai su kuma su kara wa zuciyar ka natsuwa wannan yake nuna da gwargwadon ilimin ka da gwargwadon tsoron Allah haka ake fata ilimi yana da alaka da tsoron Allah, tsoron Allah yana da alaka da ainihin ilimi saboda haka malam yake tabbatar mana da cewa zuciya tana kara samun natsuwa da gwargwadon yadda dalilai masu gamsarwa suka karu wannan na daga cikin dalilan da yake sa zaka ga cewa malaman hadisi sukan yi kokarin gabatar wa da mutane dalilai wadanda suka fi ko wanne bayyana na daga al qur'ani ko hadisi domin zuciyar ka ta gamsu kuma ta natsu akan ainihin abinda take akai insha Allahu wannan hadisi imam muslim ya samo shi daga babban malamin shi malam ainihin ne kuma malamin imam muslim Allahu akbar shi ko yake cewa babban malamin kasar masar ya karantar da mu hadisi kunji yadda al'amarin yake shi kuma sarki ya tabbata ga Allah yace malami na malam yusa ko kuma ya karantar da ni ainihin wato hadisi daga malamin shi mai suna muhammad dan muslim wato shi ko ya karbi wannan ainihin hadisi daga ainihin abu salama ta dan abdur rahman dan auf wasu malamai suka ce abu salama din shine sunan shi kuma shine alkunya shi wasu malamai suka ce sunan shi alkunya shi ce abu salama wasu kuma suka ce sunan shi ismail alkunya shi ce abu salama a karshen gaskiya saboda Allah kamar abu huraira ne ya shahara da alkunya shi ta abu huraira a musulunci shi yasa har hakikanin sunan shi ya bata shin sunan abu huraira abdullahi ne ko abdur rahman bayan malamai sun san cewa a jahiliyar sunan shi amma da yayi musulunta fa abdullahi ya zama ko abdur rahman wasu suka ce abdullahi wasu suka ce abdur rahman saboda alkunya ta danne suna to abu salama ta dan abdur rahman dan auf duk inda zaka ji riwayar shi a cikin hadisi ko daga ainihin su aisha ko daga su abu huraira ko daga su ibn abbas ko ina ne ba zaka taba jin an ambaci sunan shi ba sai dai kaji ance to wanene abu salama din shine wasu suka ce a'a ai sunan shi kenan abu salama to mecece alkunya shi aka ce alkunyar kenan kuma itace suna wasu kuma suka ce a'a sunan shi abdullahi alkunyar shi ce abu salama wasu suka ce sunan shi ismail alkunya shi ce abu salama ingantacciyar maganar da malamai suka fi yawo akanta sune maganganun farko guda biyu sunan shi abu salama ta dan abdur rahman dan auf alkunya shi kuma abu salama ta dan abdur rahman dan auf to magana ta biyu kuma itace sunan shi abdullahi alkunya shi kuma abu salama Allah madaukakin sarki ya gafarta musu baki daya zuhri ya karbi wannan hadisi daga abu salama ta dan abdur rahman dan auf wadannan manyan tabi'ai guda biyu sun karbi wannan hadisi daga abu huraira abu huraira yace lallai manzon Allah yace mu muka ficcencenta da ace munyi shakka fiye da annabi ibrahim ta iya yiwuwa kace ah menene ya kai ake zaton annabi ibrahim ya taba yin wata shakka wadda har annabi yake kora cewa ba shakka bace idan ma ko har shakka ce to mu muka ficcencenta da mai shakka to kowa kuma yasan annabi baida shakka game da Allah ko to in har ya zama annabi bashi da shakka game da Allah to annabi yana nuna maka to annabi ibrahim ma baida shakka anan sai annabi ya dawo da kanshi kasa ya maida annabi ibrahim sama tare da cewa a wajen daraja annabi muhammad shi yake sama annabi ibrahim yake kasa amma sai yake nuna inma shakka ce to mu muka ficcencenta da mai shakka ba manya manyan annabawa irin su ibrahim ba kaga anan ya girmama ibrahim akan kanshi duk zaka ji fassarar wannan ne wadanda manya manyan masana suka fadi to wannan dalili ne yasa har aka fahimci kamar ibrahim yayi shakka a wani wuri sai annabi yace a lokacin da annabi ibrahim yace wa Allah ya ubangiji ka nuna mini yadda kake rayar da matattu sai Allah yace bakayi imani bane to wannan maganar sai ta ja wasu suke fahimtar kamar annabi ibrahim yana da dan shakka ne bai gama yarda bane bai gama samun natsuwa bane bai gama hankalin shi bai natsu game da cewa Allah na rayar da matattu ba da Allah yace baka yarda bane ibrahim ina iya tayar da matattu har kake cewa in nuna maka annabi ibrahim yace a'a na yarda tabbas wannan kalma na daga cikin kalmomi dake wa bahaushe wahalar fassarawa bala saboda bahaushe bashi da irin ta a kalma sai dai a cikin ko a jawabi ko a jumla in kace na'am ba haka ne ma'anar ta ba in kace la ba haka ne ma'anar ta ba baka yarda bane a'a na yarda in kace a'a to me kenan ba yarda ba baka yarda bane in yace eh me kenan bai yarda ba bahaushe baida irin ta wannan na daga cikin mu'ujiza da karama da Allah ya karrama larabci da shi shine harshe ne wanda yake takaitacciyar kalma guda daya sai ta kunso abubuwan da har suna da yawa sai kaga basu da ainihin ire iren su ko an fahimta jama'a tare da cewa harshen hausa a cikin tarihi na daga cikin tsaffin harsuna wadanda suke iya muqawamantar tsaffin harsuna na duniya amma duk da haka ya gaza daga ya iya fassara larabci keke da keke sai dai da bayani ko da ma'ana annabi ibrahim yace a'a na yarda ya Allah zaka kana tayar da matattu na yarda sai dai na tambaye ka ne ka nuna min dan zuciya ta ta natsu ko ta kara natsuwa to kaji hujjar imam muslim duk lokacin da ka yarda to kana neman karin bayani dan zuciyar ka ta kara yarda ta kara natsuwa shi yasa yana daga cikin manhajin da muke bi mu idan muka fada maka magana sai mu ce maka ga inda muka dauko ta wannan bazai rage mana daraja ba sabanin 'yan bidi'a so yake shi ace shine da ilimin shi da kanshi kanshi bai karanta a ko ina ba mu kuma a wurin mu aibi ne ace ilimin ka bashi da tushe dan duk abinda kake da shi daga baya ya samu a sanda ka fito daga cikin uwar ka baka san komai ba to daga baya da kazo ka sani ta ina ka sani a ina ka karanta waya gaya maka fade shi shine sai kaji malaman mu salafiyun sai kaji muslim yace sai ya fada maka ina ya samo ba aibi bane daya kenan idan kuma zuwa kai ka karanto a wani littafi sai kace ga wurin ga wurin ga wurin shi yasa sai kaga a duk duniyar kafa hujja mu salafiyuna mu muka fi kowa dadin mu'amala mu ba sai muqabala ta kama muke cewa a duba wuri kaza ba muna fadin maganar sai mu ce a duba wuri kaza dan haka ko makiyin mu zai je ya duba sai dai in ya gani yayi wani ta'awili amma zai ce maganar da suka fadi gashi nan sun kawo hujja akai shi yasa kaga 'yan bidi'a basa son zama da mu me yasa saboda suna yanke wa kansu shawara ne akan abinda suke akai mu ko bama yanke wa kanmu shawara akan abinda muke akai in za'a zauna so muke da gwargwadon dalilan ka meye dalilan ka meye namu menene ka fadi yaya abun yake yaya ma'anar yaya kaza a tattauna sannan a karshe sai ace an kwana akan kaza a karkashin wannan jama'a duk wanda yake son ya bi manhaji as-salafi na farko in yayi karatu yayi kokari ya rike ina ya karanta wannan abun yau shekara goma sha takwas da ta wuce ko sha bakwai ne wani kaser da na sanya mishi suna plato tambaya ce aka aiko mini da ita a rubuce mai tambayar bai sa sunan shi ba bai sanya daga inda kawai dai yace daga plato shi yasa kawai kaser din da nazo zaka ji sai nace sunan kaser din plato jiya da daddare kusan sha daya na dare wani ya bugo min waya daga togo yace yaji wani kaser nawa plato yaji wata magana da na fadi kaza kaza kaza kaza kaza nace a duba daya littafin ne bai ji ba kuma ya nemi ai ya nemi kaser din ya rasa sai nace mishi sai yace kwarai da gaske shekara goma sha takwas alhamdulillah kan duk abinda idon ya karanta kan yana rikewa yau bayan shekaru ko nawa ne kusan sha daya na dare jiya daga togo ya bugo min maslaha ce ta yaji yace yaji nace a duba tamamul minna ya duba to daya littafin ne ya manta kuma be ga kaser din ba sai nace mishi nace maganganun ibn rislan ne a jiya jiyan nan da daddare ba alfahari ne muke ba haka manhajin yake sun tarbiyantar da mu ne malaman mu akan ka karanta kayi kokari ka fahimci abinda ka karanta sannan ka rike a ina ne ka karanta kuma ka sani da cewa ba dole ne sai wani ya yarda ba amma dai dole ne kai ka fadi meye dalilan ka in yaso in bai yarda ba amma dai bada son zuciya akai ba shi yasa babu wani abu da muke akai wanda yake da son zuciya ne duk inda ka taba min sai mu ce a gashi anan wurin ya rage kace wannan hadisi ne ku baku aiki da hadisi malikiya kuke aiki da ita baku aiki da hadisi ku dariqa kuke aiki da ita baku aiki da hadisi ku ga abinda kuke amma dai mu ga hujjar mu dan haka duk wanda zai bi wannan manhaji namu da muke kai manhaji salafi to ya tabbatar da cewa sai yayi karatu sannan sai ya mallaki littattafai kuma sai ya karanta littattafan shi yasa a cikin wannan manhajin namu baka da lokacin tsegumi baka da lokacin gulma baka da lokacin kinibibi baka da lokacin komai gaba dayan lokacin ka karatu ne zaka sadaukar da shi kuma kana karatun kana tawali'u ga Allah Allah ya rike maka karatu dan ba ba dabarar mu ce take rikeya babban mu isa ba in ba haka ba kana ji bacci ya fara dauka ta kusan sha daya da wani abu ya bugo waya ko fadin sunan shi kafin yayi kawai shikenan kaza kaza kaza kaza don ina iya ina iya har ina iya tuno tambayoyin da amsoshin da na bayar a cikin kaser din wannan daga Allah ne duk kaser din da ne indai ka rike sunan kaser din bakayi shirme ba don duk kaser din na kana canza sunan nima bazan gane ba sai in ce maka bashi bane banyi wani kaser haka ba misali wani ya bugo waya daga nijar yace a cikin kaser din ka waya kashe sheikh ja'afar nace banda wani kaser haka yace a'a gashi a gaba na nace a'a karya ne nace duba ka gani sai yace waya kashe malam ja'afar sai nace sunan kaser din kenan kana canza sunan kaser din na a'a ba ni ba ni ne nayi ba kai kasan inda kayi kayi Allah ya kiyaye maganar itace yazu anan annabi ibrahim yana cewa Allah ya nuna mishi yadda yake rayar da matattu me yasa to kaji hujjar imam muslim an gane idan dalilai suka karu suka kara bayyana to sai kaga zuciya ta kara natsuwa ko an fahimta jama'a saboda haka kai in zaka yi magana ka tattali dalilai dan zukatan wadanda kake fada wa su samu natsuwa tunda gashi har Allah madaukakin sarki an gaya wa haka to ba wani malami dan ance mishi to kara kawo mana dalili Allah ya gafarta malam dan mu kara natsuwa anan Allah madaukakin sarki bai yi wa annabi ibrahim in kari ba sai yace me dauki tsintsaye guda hudu ka yanka su ka hada naman su su anan ka kiraye su shine ya samu tsintsaye guda hudu kamar yadda Allah ya fadi kar kace gauraka cilukowa hankaka zakara karya ce ta masu tafsiri ba inda ta zuwa qur'ani ko hadisi ya yanka tsintsaye nan ya cuda naman su sai ya kira sunayen su sai suka taso ko wanne ya hadu to yanzu wannan aiki da annabi ibrahim alaihi salatu wassalam yayi yana tabbatar da tambayar da annabi ibrahim yayi yana nuna babu laifi ka tambayi malam Allah gafarta malam maganar nan da ka fada kara mana bayani kara mana hujjoji fada mana wasu littattafan dan mu kara dubawa dan mu kara samun natsuwa ba kura bane dan 'yan bidi'a suna da tambayoyin da sai suce wai wadannan tambayoyin kura ne wai wadannan tambayoyin ba daidai bane misali manzon Allah ya tambayi wata baiwa yace mata a ina Allah yake tace 'yan bidi'a yau sai suce a'a ba kyau ayi wannan tambayar manzon Allah yayi ba kyau a gaban manzon Allah an bada amsa ance har yau har yau ba kyau jama'a kun fahimta dan haka yanzu wannan irin tambayar da annabi ibrahim yayi ta halatta ko ta shar'anta ko ta sunnanta maka ka tambayi karin hujja da karin haskakawa dan ka kara samun natsuwa to kai kuma malami idan iyakar hujjojin da ka kawo da bayanan iya abinda kake da shi shikenan sai kace abinda nake da shi kenan amma akwai sauran karin bayanai to kuma sai ka kara cewa ai kaga ka kara duba aya kaza mana dubi misali kaza mana je kaga ka duba littafi kaza hada da littafi kaza zaka ga duk wadannan ka nemi mai ne dan me domin ainihin ya kara samun natsuwa amma kar ya zama kana jawo ayoyin kana jawo hadisan kana fadin littattafan kawai dan ka burge jahilai suyi kabbara dan wuta ne kai haka hadisi ya fadi sahihi cikin ibn maja duk wanda yayi ilimi domin ya jayayya da malamai domin ya burge jahilai manzon Allah yace ranar alkiyama za'a jefa mai linzami akai wuta wannan itace aya ta dari biyu da sittin cikin suratul baqara jama'a kunji a cikin wannan hadisi munji tarihin annabi ibrahim a karkashin wannan tarihin ne manzon Allah imam muslim yake kafa mana hujja da wannan babin to amma hadisin yana da tsawo sai kuma manzon Allah yace Allah yaji kan annabi luthu a lokacin da tsanani yayi tsanani tsakanin shi da mutanen shi sai yake fa kowa zuwa ga babban garkuwa shine Allah kawai da tsanani yayi tsanani duk wanda aka gani a garin nema ake ayi luwadi da shi to al'amari ya tsanani sai ga bakin mala'iku yayi amma sai
[Segment 2/4 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
suka riƙi ɗan suka zo asiffar samari. Sai ga mutanen garin sun zo gidan annabi Luɗu suna cewa mun samu labarin annyi baƙin samari gidan nan a fito mana da su. Shine manzon Allah yace da tsananin yayi tsanani ya kasance yana fakuwa zuwa ga rukuni mafi tsananin ƙarfi shine sai ya koma ga Allah ma'ana waɗannan mutane al'amarin ku sai dai kawai ace Baki na ne kar ku kunyata ni. Ga ƴaƴa na nan ku je ku aura ga mata a cikin gari waɗannan baki na ne kar ku kunyata ni. Suka ce amma dai kai kasan halin mu. Kun gani to shine sai ya maida al'amarin shi ga Allah manzon Allah ya jinjina mai akan haka yayi mai addu'a ta alheri to sai manzon Allah ya sake tsallakawa duk duniya ba inda zaka ji labarin annabawa na gaskiya sai ƙur'ani sai hadisi duk inda kaji labarin annabawa in ba ƙur'ani ko hadisi ba to ka fara bincikar wannan source ɗin. Wannan tushen akwai abun tambaya. Sai annabi yace Da ni ne na zauna a kurkuku tsawon zaman da Yusufu yayi da na amsa wa mai kira. Yusufu aka kai shi kurkuku babu alhakin tsaye ba na zaune. Bayan kwana biyu sai aka aiko aka ce sarki na kiran shi ya fito. Sai yace a'a aje a tambayi matan nan tsakani da Allah na neme su ko ko su suka neme ni annabi yace a'a ana cewa in fito wallahi fitowar zanyi in na fito ayi jawabi. Yace da ni ne wallahi fitowar zanyi in anzo waje ayi jawabi. Annabi yana nuna tawal'un shi duk zaka ji fassara daga malamai na waɗannan hadisai insha Allahu ta'ala. Allah maɗaukakin sarki ya taimaka. To kamar yadda na gaya mana wannan na ɗaya daga cikin hadisai waɗanda malamai sukai rubuce rubuce akai ma'ana littattafai ne malamai sukai rubuce rubuce akai jama'a. Mafi girman littafi kun ganshi. Moshkilul asar akwai waɗansu hadisai waɗanda su hadisan da kansu suna buƙatar ka gane me cece ma'anar su akwai waɗansu hadisai kuma in ka haɗa su da wasu suna karo da juna to wannan hadisin shi duka yaci biyu.
[Speaker seg2-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg2-spk:0]
Shi da kanshi in ka dube shi akwai matsaloli a ciki waɗanda kana buƙatar fassarar su. Idan ka haɗa shi da waɗansu hadisan a zahiri zaka ga yana karo. To shine Al-imam Tahawi ya rubuta wannan littafi gashi kusan mujalladi goma sha shida. Sannan yana da Ma'ana hadisi ne ka karanta kamar wannan sai kaga ire iren waɗannan maganganu waɗanda mu yanzu manyan malamai da sukai sharhin wannan Sahihul Muslim duk sun tsuntsunto mana waɗannan maganganu dan haka kai a matsayin ka na ɗalibin ilimi sai dai ka karanta waɗannan littattafai dan ka kaima ka ƙara samun natsuwa da hujjoji. To sai malam yace Malamai suka tattauna dangane da wai me cece ma'anar wannan magana da annabi yace mu muka fi cancanta ace munyi shakka ba annabi Ibrahim ba. Maganganu masu yawa malamai sukai ina karantowa daga shafi na 999 in akwai anaku in babu kuma sai ku saurara. Bayan da ya kawo wannan hadisi bari ku ji abun da yace. Mu muka fi cancanta da mu tambaye Allah Allah ya ƙara mana bayani. Yace yana cewa Annabi Ibrahim tun a zuciyar shi yasan cewa Allah ke rayar da matattu. Sai dai yaso a nuna mai ne a ido da ido zuciyar shi ta natsu Allah ke rayar da matattu amma kuma yana so ya gani ya aikace. Saboda haka kaga kenan ba shakka bace. To amma mai yiwuwa mai saurare zai iya sauraren maganar annabi Ibrahim sai ya ɗauka shakka ce ko sai annabi yake cewa ba shakka bace. Amma in ma shakka ce to mu ka ɗora ta a kan mu. To kai kana jin annabi yana shakka ne to in har yasan annabi baya shakka to annabi ya neme ka ishara to annabi Ibrahim ma baya shakka. Jama'a kun fahimta? Inta fassarar da Al-imam Abu Awana yayi kenan ka duba littafin shi Al-musnad lamba hadisi ta 232 daga mujalladi na ɗaya shafi na 78 zuwa 79. Ibnu Hibbana bayan da ya kawo wannan hadisi sai yace Abu Hatim yace Da annabi yace mu muka fi cancantar ace munyi shakka ba Ibrahim ba. Ba wai annabi Ibrahim yana nufin yana shakka ne gama da tayar da matattu ba. Abun da annabi Ibrahim yake tantama ko Allah zai amsa mishi wannan buƙatar da yake cewa a nuna mai. Ba wai shakkar rayar da matattun ba. Da nake roƙon Allah To wannan maganar ce ko Allah zai nuna min ko bazai nuna min ba kaji wata fassara kuma daga wannan malamin. Ina fatan kun gane ba tayar da matattun yake shakka ba amma za'a amsa mai a nuna mai yadda ake tayar da matattun ko baza'a nuna mai ba itace yake shakkar. Abun da ya faru Ibnu Hibbana yace shi annabi Ibrahim Bai tabbata za'a amsa mai addu'ar ba wato wajen roƙon shi addu'ar shi da yake da kuma tambaya da yake wa ubangijin shi. Sai annabi Muhammad yace In ma har annabi Ibrahim yana shakkar za'a karɓa baza'a karɓa ba to mu muka fi shi cancantar ace munyi shakka. Saboda mu in mun roƙi Allah ta iya yiwuwa a amsa mana ta iya yiwuwa a ƙi amsa mana. Kenan yanzu annabi Ibrahim kamar labari yake bayarwa. Amma me yake nufi kamar karantarwa. Annabi Ibrahim ya roƙi Allah ne to ko Allah zai amsa mai ko bazai amsa mai ba sai annabi ya nufi ya baka labarin wannan maganar ta annabi Ibrahim ya karantar da kai. Idan har kana ga annabi Ibrahim shakka yake a'a ba shakka bace in ma shakka ce to mune to mu kuma kana da yaƙinin bamu da shakka eh to shikenan dan haka kenan ba shakka ce ta hau annabi Ibrahim dangane da rayar da matattu ba. Amma karɓan addu'ar ce yake ga za'a karɓa baza'a karɓa ba ko kun fahimta jama'a? Nawawi a cikin nashi sharhin sai yace Malamai sun saɓa me wannan maganar take nufi maganganu ne masu yawa mafi kyawun su kuma mafi inganci maganar da almajirin Shafi'i ya faɗi da wasu tarin malamai suka ce bazai taɓa yiwuwa annabi Ibrahim yayi shakka ba domin kuwa shakka gama da tayar da matattu Sai annabi Muhammad ke nuna cewa da annabawa na shakkar ta da matattu to da ni na fi cancantar inyi ba Ibrahim ba. Ku kuwa sahabbai kun san ni bana shakka to Ibrahim ma ba shakka yayi ba. Abun da yasa annabi annabi Muhammad ya keɓe annabi Ibrahim cikin sauran annabawa saboda kun ga ayar tazo tana maganar shi ne. Akan shi ake maganar ayar ko shi yasa ya keɓe annabi Ibrahim. To me yasa annabi Muhammad ya nuna cewa annabi Ibrahim ya fi shi daraja. Domin wannan maganar tana nuna annabi Ibrahim ya fi annabi Muhammad daraja ko? Wasu malamai suka ce fassara biyu ce. Fassara farko itace tawal'u ce da ladabi. Zaka iya haɗuwa da almajirin ka sai kace mishi ba aibi bane ko ka ɗan wallahi. Amma a Najeriya nasan da wuya wallahi. Wallahi jama'a amma mafi yawancin malaman mu na duniya kana kiran shi sai kaji yace To sai ka rasa me zaka ce addu'ar da zaka yi mishi kai yayo maka. E mu kuwa nan in ka gaya malamin ka ma saboda faɗin rai yace ma amin sai dai ya amsa a zuciya yana huci kamar sanda za'a yanka gobe sallah. Malamai suka ce ko dai ya zama annabi ya faɗi kalmar nan dan ya nuna annabi Ibrahim ya fi shi Amma annabi Ibrahim bai fi shi ba. Yafi annabi Ibrahim amma sai yayi tawal'u ko kuma annabi ya faɗi wannan kalmar ne kafin Allah ya sanar da shi cewa cikin ƴaƴan annabi Adam yafi kowa. Amma fassarar farko itace daidai. Yana da ainihin tawal'u To sannan fa malamai sukai ta tambaya to wai ma menene ya kai annabi Ibrahim zuwa ga ainihin wannan tambaya duk dai ƙarshen abun da suka ƙarke shine abun da Imam Muslim ya Annabi Ibrahim ba wai bai yadda da tayar da matattu bane ba wai bai yadda Allah zai amsa mishi bane a'a dan ya ƙara samun natsuwa. Shikenan kawai baban ka ne ya biya maka kujerar hajj ga rasit ga komai ga komai. Kuna hira sai kace yanzu nan baba ka biya mni a To shakka kake a'a kawai dai ƙara samun natsuwa ce sai yace ai yau ma jami'in alhazai yace kaje ma za'a gwada ka za'a yi maka yi nufin ɗin alhazai kaji ma wannan tambayar sai ta ƙara fito da me dalilan tafiya gashi ma ance kaje a ɗinka maka riga. Ina fatan an gane. To wannan itace fassara ta farko da malamai sukai cewa yayi ne dan ya ƙara samun natsuwa fassara ta biyu itace Yaso ya gane ƙarin matsayin shi shin ubangiji na amsa buƙatar shi ko ko akwai buƙatun da ubangiji baya amsa mishi yana son ya ƙara ganin yaya matsayin shi yake. Fassara ta uku itace Yana da yaƙini dama amma sai ya roƙi Allah saboda ya ƙara samun natsuwa. Wasu kuma malamai sai suka ce lokacin da annabi Ibrahim yayi wa mushrikan zamanin shi wa'azi cewa Allah ke rayar da matattu sai suka ainihin saka shakka to sai annabi Ibrahim sai ya tambayi Allah da nufin shi yana da yaƙini amma su su gani. Ko kun fahimta jama'a? Shi yayi tambayar ba dan shi yana shakka ba amma su da suke shakka to su gani. Don anyi abun a jama'a ne ba wani watar duba ne akai ko kuma a ɗaki ne akai aka fito aka bayyana karama ba a idon jama'a ne akai wannan abun sai ya zama kenan ku dake cewa Allah bai iya tayar da matattu ga zakaru yanzu yanzun nan Allah yasa na yanka su tsintsaye ga kaza amma kuma gashi Allah maɗaukakin sarki ya tashe su a yanzu ina fatan an gane. To jama'a kun dai ji haka malamai sukai ta maganganu duk dan ka gane duk abun da ya shafi ɓangaren annabawa ko to tashi ake wur jan jan ana kare shi. Dan kar kayi wa wani annabi mummunan zatu. Ina fatan an gane. To sai kuma dangane da annabi Luɗu shi kuwa dangane da annabi Luɗu kun ga munji irin maganganun da manzon Allah ya faɗi yace Allah yaji ɗan annabi Luɗu ina fatan an gane. Malam yace Mutanen annabi Luɗu rana tsaka suka ƙirƙiro luwaɗi. Sai annabi Luɗu ya kira su zuwa ga tauhidi sannan kuma su bar wannan alfasha. Haka ake in kaje gidan karuwai zaka yi zina ai zaka yi abun nan Allah ya kiyaye zaka yi wa'azi ba wa'azi akan zina kaɗai zaka yi ba sai ka fara da tauhidi sannan sai kazo kayi wa'azi akan zina. Suna alfasha ne ta luwaɗi sai yaje zai musu wa'azi sai ya fara da me? Tauhidi. Abun da yau in anyi muku wa'azi kuke cewa zai raba kai. Ko kun fahimta jama'a a in kun kira su albani sunyi wa'azi zasu yi maganar aƙida aƙida zata raba kai ko kuma kaji wani yace ni dai kuna burge ni yadda kuke abubuwan ku amma maganar aƙida ɗin nan da kuke yi shine baya burge ni. Zai raba kai gashi aka ce sai da ya fara kiran su zuwa ga tauhidi sannan ya neme su daina wannan alfasha sai suka ƙi daina wannan alfasha Kap garin sai kowa ya juya mai baya. Ba wanda ya goyi bayan shi. Wannan gari nasu ana kiran shi Sadum haka sunan garin yake har yanzu. Garin yana nan yanzu a Sai munzo tafsiri daidai wurin kamar yadda na alƙawarta insha Allah a muƙaddimar tafsiri na zanyi muku shuting garin zaku ga hoton garin a projector da komi da komi live ba wai hoto ba a video yadda zaka gani in ma muna son mai ɗin shi a Google. Google Art daga makarantar nan sai ayi ɗin shi live a yanzu da muke magana ba wai a'a a yanzu camera dake sararin samaniyar yanzu sai ta ɗakko mana hoton sai mu harba shi ka gaya yaya garin yake yanzu. Kamar yadda Allah ya faɗi. Ina fatan an gane. Sai yake cewa A lokacin wannan garin yana ƙarƙashin ƙasar Sham ne amma yanzu yana ɓangaren ƙasashen Jordan ko Oman. Da Allah ya nufi zai hallaka sai aka turo manyan mala'iku Jibrilu da Mika'ilu da Isra'il sai suka taho wurin annabi Ibrahim suka sauka a wurin shi sai al'amari ya faru kamar yadda Allah ya bada labari a cikin Da suka gama baƙunci wurin annabi Ibrahim yaso ya musu ɗan marƙi suka ce akai hidima aka tashi suka tafi. Sai ainihin suka ce zamu je mu hallaka mutanen garin can ne. Sai yace Luɗu fa na ciki ɗan uwa na ne kaza kaza ɗan baffa na kaza kaza To ai mun fi ka sanin wanda ke ciki. Hankalin annabi Ibrahim ya tashi saboda za'a annabawa da malamai na sunna ba hallakawa suke so ayi ba so suke a bi. Ko kun fahimta jama'a? To yaya za'a yi Allah ya riga ya ƙaddara suka je suka sauka wurin annabi Luɗu. Annabi Luɗu yayi musu hidimar baƙunta Sai annabi Luɗu sai yaji tsoro. Mutanen shi sun ga waɗannan samari lafiyayyu Sai yayi ƙoƙarin ya ɓoye labarin zuwan su. Matar shi dama tana tare da su. Sai taje sai ta faɗi yau fa akwai baƙin samari a gidan mu suna nan lafiyayyu sai suka taho wurin Luɗu. Suka zarge shi to ka ɓoye mana ne to gashi nan mun sani kai baka san muna da ƴan jaridu a gidan ba. Suka zaci cewa zasu iya danne su suyi luwaɗi da su. Sai Jibrilu ya bi ya sa hannu ya mammake su. Aka juya garin haka garin sai da aka ɗaga shi sama da aka kai shi sama sai akai mai bama bama tukunna akai mai ruwan ƙwaran ƙwatsa aka raga raga da garin daga sama sannan sai aka ƙifo garin ƙasa. Da aka ƙifo garin shine wani baƙin ruwa ya tashi ya abun nan. Abun mamaki har kafiran duniya sun karanta wannan sun san tarihin garin. Kuma kowa har kafiran duniya da malaman tarihi da malaman gano garuruwa da abubuwan tarihi dukkan su sun yadda cewa mutanen garin suna sahuwa da ƴan uwan su ne. Haka ta faru. Duka ba wani wanda yake musu akan wannan duk turawa in zasu rubuta duk abun da zasu rubuta har ma su kansu kamar yadda annabi yake faɗi suma haka suke cewa wane yana aiki irin na mutanen Luɗu. Amma kuma duk da haka suna promoting ayi wannan. A yanzu a ƙasar Faransa har masallacin juma'a aka buɗe na ƴan luwaɗi. Mun nuna muku a nan akan internet. Masallacin juma'a
[Segment 3/4 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
a kasar Faransa ta bayar aka gina na yan luwadi wai don suna zuwa masallaci na marsala luwadi ana banbance su. To su kuma kasa ce mai yancin addini babu Kuna luwadi zaku je ana kya maku eh to kuzo ga masallaci ku gina kuma kuyi sallar ku in yaso daga nan ma Sannan kuma a tashi a taho la'asar in an jima a kasar Faransa yana nan akan internet na'am
[Speaker seg3-spk:1]
Cikin bayani kace Annabi Ibrahim ya soya musu su dan maraki sun ci
[Speaker seg3-spk:0]
eh
[Speaker seg3-spk:1]
Ina ce da ya soya musu wannan namu
[Speaker seg3-spk:0]
eh a'a na na na na wuce ne da Hausa kawai amma da ya soya musu ai eh menene Ya soya musu ya soya amma basu ci ba baki na ne ya ya wuce abin nan Hausa ce ta dibe ni Ina fatan an gane ya ga hannun su baya kaiwa su shi kanshi sai ya tsorata to wadannan baki yaya dai suka kalli juna suka kalli juna to shima sai ya gane to wadannan fa su mala'ika Jibrilu ne ashe sukai mana abin nan a sha ruwan tsintsaye shine suka riki da kenan sarki ya tabbata ga Allah Jama'a kun ji To Annabi Lut ya kwashe iyalan shi suka fita daga garin sai matar shi ita sai tayi zamanta tare da dangin ta don dama yar garin ce shi kadai ne bako yazo ya aure ta da ya fara wa'azi sai suka hade mishi kai harda ita ko kuma wasu suka ce ta fito ta biyo Lut amma saboda ita ma tana da hali irin nasu sai Allah madaukakin sarki yasa azaba ta jawo ta gefen fuka fukin shi mala'ika Jibril yasa kawai sai ya tunsurar da garin sama ya koma kasa kasa ta koma sama sai wurin ya zama wani dan dan tafki mai doyi yadda kaji mun fadin nan haka yanzu In kana da internet kana iya capturing Google Art Google Map shine to duka dai An gane Google Map ko Google Art in kana iya capturing cap zaka iya Duk inda kake yanzu a duniya inda muke din nan yanzu Zaka je kana sawa kawai shikenan zaka ga ka kamo har kankan titin nan har inda makarantar nan tamu take Inda ma mu ma kartasan kar ne ba'a iya ganin makaranta amma na lamunce maka kaje ka sa ba'a iya ba'a ganin ta Amma zaka ga wannan street din amma ba'a ganin makarantar Na lamunce maka kaje Kaje kasa makarantar bata ganuwa amma zaka ga gaskiya zaka ga ina zaka ga ina duk zaka gani amma nan fa zaka gani Insha Allahu ai abin namu ne dan kura da kallon bin kitse Ba zata gani ba Allah sai dai mala'iku su gano ta daga saman bakwai amma wallahi duk abinda zaka sa in dai a Google ne bazata gano kaje ka gani kuma zaka gani duk zaka ga street din nan zaka ga ko ina Amma bazata gano ba in yazo wurin sai ya ga bako Allah ya taimaka To to jama'a kunje ji dangane da abinda ya shafi wannan Annabi Lut aka ce Duk wannan fassarar da sukai din dai shine mai shine kawai Allahu ina fatan an gane da yake cewa Ina ma ina da karfin hana ku In ba haka ba sai dai in koma zuwa ga Allah To al'amarin sai ya zama bashi da karfin hanawa Me yasa saboda galibi in kana da'awa kana neman dangin ka su goyi bayan ka ko almajiran ka to shi da yazo garin sai sukai mai kabilar shi ba wanda yayi imani da shi kuma dama bai da dangi amma kunga Annabi Shu'aib shi an kasa taba shi an kasa mishi komai me yasa sai suka ce Ba dan dangin ka ba damun jefe ka yana da dangi dan dangi ne Baku ga Annabi meye dalilin musuluntar Hamza Wata baiwa ce tazo ta hadu da Hamza ya dawo farauta Tace Hamza wannan irin wulakanci ne zaku bari ana wa dan uwan ku Dan yazo yana karatu kowa baya so yo kowa baya kawo kalon ko shiga ba garin nan kai sai sai ku bari ana wulakanci yace ke me kike nufi Tace yaya yanzu yanzu ga Abu Jahal can Yaje ya zazzagi Muhammadu yace haka aka yi yace eh Hamza yana zuwa sai ya dauki ainihin kwari da bakashi yana samun a kaga jahiliyya dama ba neman istifsari ba neman gaskiya ne abinda ta fada yana zuwa sai ya same shi cikin jama'a sai ya rafka mishi Amma dalilin shine sun san basa karya Baza tayi karya ba basa karya ne a jahiliyya ai sun gaskiya ne shine sirrin Ya tabbatar tunda ta fada to gaskiya ne basa karya Dan haka yana zuwa da ya dauki kwari da baka sai ya rafka mishi Lafiyar Hamza sai ya ce na musulunta dan kaza kaza nima tunda kuna dukan musulmi to nima musulbi ne Haka sai a dube shi a ce dan Allah ga fara ai ba irin ku ake dukawa mahaukata Shiyasa duk kuna bukatan wadannan yan kauraye da sauran su duk ku jawo su su shigo addinin musulunci Eh duk wani dan iska bazai taba ku ba Kwarai da gaske tunda Hamza ya musulunta da Umar ya musulunta su manzon Allah aka daina dukan su da sai ayi ta dukan su suna Allah ya isa suna kuka shi da Abubakar Saboda bayin Allah ne bazasu daki kowa ba amma Hamza yayi duka mara dalili ma balle ya shigo musulunci Allah yace a dake ka Allah Hamza Ai shiyasa da aka kashe shi manzon Allah yace wallahi bazai yadda ba Sai ya kashe mutun sa bayin Allah yace a'a Ai Hamza kai kadai gayya ne tunda ya shiga musulunci da shi da Umar ba'a sake wulakanta musulmi ba amma da sai ayi ta dukan su Annabi da sa Abu Bakar suna kuka suna Allah ya isa Shikenan su kuma yan iska dama Allah ya isa suke so ayi To amma tunda garin da Hamza ya musulunta kaga da duka ya fara wa zuwa yadda ki Abu Jahal yace to na musulunta nima tunda kuna dukan musulmi to nima musulmi ne Umar kuma zuwa yayi yace to jama'a Ga Umar zai yi hijira ya musulunta idan mai magana akwai mu hadu bayan duwatsun nan Sai a kalle ya shace dan Allah sakaran banza sakaran tafi ka bamu yace eh a mu hadu a bayan dutsan nan Ko kun fahimta jama'a shiyasa duk wadannan yara da ake ce musu yan iska kar ku ce musu yan iska kuje ku jawo su cikin musulunci Ina fatan an gane yana yin kaza na tsafi eh to bar kaza Amma yana da wani barandami mai kaifi kace to a je shi akwai randa zai amfani A kar maka Allahu to a yace a'a a je shi akwai randa zai amfani Ai kwarai da gaske baka ga duk abinda ya faru sai Umar yace bari inje in datsa wuyan shi Yana nan da barandamin shi kenan Shine Ya kamata ku rinka fahimta jama'a musulunci kawai kar ku bari yan iska su rinka wulakanta ku eh ku bayan Allah ne sai suyi ta wulakanta ku dole ya zama kuna da wadanda zasu rinka sassa basu In suka sassabu zai ku ce to ku kyale su kaga an ja maka an ja maka hadisi baka ji ba to kaga irin ka sun maka irin naku karatin Masailu ta ta'allaku bi hazal hadis Ga mas'alolin dake da alaka da wannan hadisin sai dai kafin nan ina so in duba cikin hadisin ku dan dubi wasu al'amura daya biyu uku haka da Annabi ya fada Annabi Ibrahim sai ya ce Ya halattan ka fadi sunan wani Annabi kace Ba sai lallai Annabi Muhammad ba sai dai kalmar anfi shahara ta ga Annabi Muhammad ne Sannan ya halatta ashe kace wa wani Annabi Gashi nan Annabi ya ce Allah yaji kan Annabi Lut ina fatan an gane To sauran bayanai kuma duk zaku je a cikin hadisi na'am Na mene dangane da A'a to bansan inda akai wannan kaidin ba Ma'ana cewa sai kamar Ibrahim kamar Nuh kamar Musa kamar Isa kamar Muhammad su kadai za'a ce wa Bansan wannan dalilin kaidin ba Ina kai ka karanta To ni bansani ba insha Allahu Allah ya taimaka Wannan hadisin na Abu Huraira Bukhari da Muslim sun ainihin wato haduwar wajen fitar da shi ma'ana ba Muslim ba kadai sannan banda Bukhari da Muslim da Ahmad da Nasa'i dukkan su sun fitar da shi Abu Awana da Abu Nu'aimin da Ibnu Hibban da dukkan su sun fitar da ainihin wannan hadisi ko da da dukkan su sun fitar da shi sai dai a cikin Al-Imam al-Baihaqi kuma a cikin littafin Idan baku manta ba mun ce ya fitar da shi ko kun ga gashi nan a cikin shine hadisi na dari uku da ashirin da shida wannan da na nuna muku ya fitar da shine don ya fitar da wadannan mas'aloli wadanda ke karkashin hadisin Wannan hadisi yana nuna mana zuciya na kara natsuwa da gwargwadan yadda dalilai suka karu An fahimta jama'a Domin gani da ido Yana karawa mutun ilimi ilimin da kafa hujja kadai bata isar wa Allah yasa kun fahimti wannan maganar shine abinda ya faru ga Annabi Ibrahim Dama yadda Allah na iya rayar da matattu amma kuma nuna mishi abun a aikace fa Yana kara samon mai da ilimi ilimin da Mai wada bazai same shi ba Ina fatan an gane Sai malam yake cewa Ya nemi ya samu Yakini kamar yadda zamu zo muji martaba uku ne Akwai Akwai Akwai To Ibrahim Bayan da ya samu ainihin wato ah ilimin da yake tabbas ne tunda Allah yace yana rayar da matattu to yanzu wannan ya zama ilimi tabbas ba shakka To amma sai ya nemi ya samu mai Sai malam yace Domin ilimi wanda ke gamsar da kai to matakai uku ne A wajen na farko Ana kafa maka hujja akan kaza sai kaji ka yadda To yanzu ka samu abinda ake kira ilimi na yakini Idan ka gani Ka halarci gurin To nan kuma sai ya baka Idon ka yaga abinda da ake fada maka Sannan sai Idan ka kai ga taba abun Ka kai ga sanya abun ko cin abun ko shiga abun Misali tafiya aikin hajji An yi maka passport An yi visa An dinka maka uniform an yi maka allura duk an yi maka wadannan Yanzu da kana da cewa akwai wani gari Makkah To yanzu ka fara samu tunda gashi har An dauki hoton ka har za'a tafi Ana sauka a Makkah in ka ganka a Ka'aba To kuma yanzu ka samu mai kenan Ka samu Yanzu ba'a hoto bane Ko an fahimta jama'a Gashi nan sai ya kawo misali dangane da haka Wannan karatu namu ne yau yana nuna mana imani yana iya karuwa kuma yana iya raguwa Shari'ar musulunci ta yadda ka kare musulmi in kaji za'a taba mutuncin shi Kaga inda Annabi Ya kare cewar shakka zata kai ga Annabi Ibrahim Dan wasu suna cewa Ibrahim na shakka Amma Annabin mu bai taba yin shakka ba bisa wata fassarar da akai wasu da suka tashi sai suka ce kaga Annabin mu bai taba yin shakka ba amma Annabi Ibrahim ya taba yin shakka da aka ce da Annabi yaji haka sai ya ce a'a in ma da shakka ce to mu maka fa dacewa To wannan sai ya shar'anta kaji ana zagin wani musulmi kaji ana suka wani musulmi kaji ana aibanta wani musulmi Me ka sani game da shi Alheri to sai ka kare shi a bisa wannan alheri da ka sani game da shi Wannan itace ka'ida a wurin Ahli Sunna jama'a Mutumin da dama kasan mutumin kirki ne sai kaji daga baya an danganta shi zuwa ga wani mugun abu sai ka dawo kai gini zuwa ga wancan kirki har sai an iya kawo dalilan da zasu rusa maka wancan kirkin Ba kawai kayi irin al'ada hausawa daga ance kaji wane kaza yake sai a ah ai sai a iya Ai mutun ne kai dai kaga mutun yau kuma a'a mutun kuma mutumin yau ai sai dai gyaran Allah To wannan hausawa kenan irin iyayen mu yan geto mu ci ya ci kaji daurawa tudun wada duka Eh nan irin haka zaka ji duk irin wannan tunanin sai wanda Allah ya kiyaye Wannan karatu ne yau yana nuna mana duk mutumin da yake da falala To kai kada bakin ka yayi yaushi karinka bayyana falalar shi a mutane Annabi ne shi kaima Annabi ne fadi darajar shi Malami ne shi kaima malami ne fadi darajar shi bazai rage maka daraja ba Dan wani malamin yana ganin baraza na ce game da tashi darajar in ya cewa ne yana da daraja Wani malamin yana ganin barazanar ilimin shi ce in ya ce wane na da ilimi saboda haka akwai malamin da yake saboda irin wannan mummunan kuskuren tunanin bai taba yabawa wani malami a majalissin shi ba Amma gashi Wane yana da falala Ba aibi bane in kace wane ya iya kaza wane ya kware akan kaza ba aibi bane Wannan ya Annabi ya siffanta Annabi Yusuf da hakuri da kuma bin abubuwa sannu sannu Ka duba jama'a kana cikin kurkuku an kai ka dama bakayi laifi ba fa Kuma sai aka ce fito Sai kace bazan fito ba sai an fada mun me nayi Annabi yace a'a ni inda ni ne fitowar zan yi To kaga anan Annabi ya yabi Annabi Yusuf da hakuri da kuma bin abubuwa daya bayan daya Da biye gaggawa fitowar daga wannan zama mai tsawo da yayi a kurkuku ba Da dan aiken sarki yazo mai mai Yusuf yace cewa Koma wurin mai gidan ka Kace ina labarin matan nan da suka yanyanke hannun su saboda suna Yaya suna nan akan batun su ko kuwa Kuma yaya sun yadda cewa su suka neme ni ko ko ya abun yake Annabi yace in ni ne duk bazan tsaya wannan jawabin ba fito kawai fitowar zan yi Wannan ya nuna irin yadda manzon Allah yake da da irin yadda Annabi yake kambama wani akan kan shi Manzon Allah yace da na amsa wa mai kiran Domin cewa da na amsa wa mai kiran Wannan Ba wai yana son ya nuna yana da gaggawa bane a'a Misali Dan aiken yana zuwa Sarki yace ka fito daga kurkuku Bazai harari dan aiken ba bazai raina shi ba Sai kawai sai ya ce gani sai ya fito Kaga wannan yana nuna Sai ya ce domin Idan kai babban ne kai Bazaka kaskantu ba In kana da daukaka kai Baya rusa darajar ka Kana da daraja sai kai darajar ka bazata zube ba Sai dai yana karawa mai falala falala Sannan yana kara yana sanya wa mutun girma da kuma al'kadari Har wai yana daga cikin darasin da muka ji a cikin wannan karatu Wannan karatun yana nuna mana in aka Sannan sai tan musulmi ta bayyana daga wannan abu To wajibi ne ya bayyana wa mutane wannan Kama kamar yadda Annabi Yusuf ya nemi haka Ko kun fahimta ina muke fahimta haka An kai shi kurkuku ba'a tsaya an an yada mai yaya yaya To yanzu an tashi fitowar kawai ya fito sai ya ce a'a a koma sai a bayyana magana a fito da magana a jama'a Shine abinda yanzu akai nashi a cikin harkokin tafiya kotu da tafiya media da sauran su Ma'ana ka akan kaza bai yi ba To bazaka shiga daki kawai shikenan a ce an warware ba Sai a fito A zo a fasa magana a kotu a buga a jaridu kafofin yada labarai duk su dauka shikenan Haka ya kamata
[Speaker seg3-spk:1]
na'am
[Speaker seg3-spk:0]
Kuma kai bai kamata kai girman kai ba in kasan kayi abinda ba daidai ba Ko kun fahimta jama'a zaka ga galibi turawa da yake su suna kiyaye dokokin da suke yi Zaka ga ko gidan radio ko jarida ko ina ne sun fito suna neman wane da suka bata wa suna suka ci mutuncin su ya yafe musu Anan ko sai dai ayi nemi ayi wasan kura da maganar Wai a'a an bata maka an ci mutuncin ka an ci zarafin ka Wai so ake a pirgita ka dan ka guduma kawai Shiyasa ku tashi kuyi karatu yan zamani karan bana yayi maganin zoman bana Duk wanda ya bata maka suna Ku tafi kaje ka nemi gaskiyar abinda ya fada
[Segment 4/4 | 01:00:00–end]
[Speaker seg4-spk:0]
Idan bashi da gaskiya shikenan, ya tuba, in ma ka nemi wata diya ya biya ka ko ba ya biya ka ba, ya tuba amma ya yada a cikin kafofin labarai cewa karya yayi. Ko an fahimta jama'a?
[Speaker seg4-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:0]
Abinda yake wajibi kenan. Baku ji wanda yayi wa Almustapha sharri ba? Baku ji gidan rediyo ya fito na Amurka ya fadi ba? Muna nan da kaset din mun sauke mun ajiye. Yana cewa karya gwamnatin Obasanjo ta sa shi yayi wa Almustapha. Yace ya rantse da Allah karya yayi, sharri yayi, anyi mai alkawarin za a gina mai kaza, gida kaza, a kasa kaza, za a bashi kaza. Yace ko taro ba a bashi ba. Akan wannan karyar tashi akai yau shekara goma sha ana rike da bawan Allah. Ba ada hujja sai wannan karyar. Shi kuma da yayi karyar yanzu gashi nan ya tashi bawan bawan. Da wanne zaka ji? Kayi karya aje a daura mutum shekara goma sha. Jama'a ku duba wannan wannan itace Najeriya. Kuma ya fito ya karyata amma har bayan ya karyata din kuma ance ma an yanke mai hukuncin kisa. Ba dole kuyi fama da bala'i a kasarku ba. Ba dole wasu Wasu yan mutsi mutsi yan kanana su tashi su gallabe ku ba. Ma'ana duk wani mai gaskiya shine za a tashi ayi fada dashi ga Criminals anyi Lefi ya zama official an karbe shi. Ga masu gaskiya ana fada dasu an koma an daure wa makaryata gindi. Ba dole Allah ya dora muku jaraba ba kuna gan bara'an yara ne ba suce kwaya rakwai ba. Suka fitini birnin London. Aka je aka tattaro alkalai da pastoci da masu sarauta duka suka zo majalisa. Sai aka samu masu ilimi suka ce Akwai abinda yake faruwa a garin nan ba daidai ba a gyara. Bazai wu yara yan sakandare suna ta bin mu suna kashewa ba. Anan majalisan nan take aka gano ga abubuwa aka ce a gyara shikenan ba musulmi bane ba qur'ani suka sauke ba. Correction suka yi wa kansu. Shikenan sai Allah ya karkatar da zukatan yaran shikenan. Yara ne yan sakandare a keke suke yawo. In sa ga wannan bulelan darekta harbe shi, in sa ga wancan komishina sai sa harbe shi, wancan sai sa kowa suke kashewa kuma yan sakandare a keke a cikin Ingila kuma. Kuma yayan kasan ne ba yayan Larabawa ba, yayan su ne. Sai suka zauna a majalisa suka natsu. Pasto yayi addu'a. Allah ya saukar da ruhi mai tsarki ya bayyana mana yaya wannan abu yake wani yace to shi yana ganin akwai abinda aka gane anyi wata rashin gaskiya ne anyi kaza to a gyara. Live tashar BBC suka sanya wadannan abubuwan duk duniya ta gani shikenan a cikin makon sai matsalar ta kare. Kuna nan kuna munafunci a Najeriya. Kuna cewa kun kafa komiti kaza kun kafa komiti kaza kun kafa komiti kaza. Yara tun da ana ganin cewa yan shekara talatin ne yanzu yan shekara goma sha uku sha bakwai sun gallabe ku. Da tun ana daukan wani big deal ne. Rannan wani babban professor ne muka zauna dashi a wata tsohuwar jami'ar mu abinda yake gaya mana kenan yace naira dubu biyu yanzu ake ba yaran suna zuwa suna kashe mutum. Naira dubu biyu sai a ba yaro sai yaje ya dirka wa wani bindiga. Ba munafunci zaku yi ba zaku tsaya ne tsakaninku da Allah. Ba a yi wa Allah munafunci a irin delicate hali irin wannan. Ayi addu'a sannan a gyara. Amma a a kai baka yadda ka gyara ba amma shi wancan da yake nashi ta addancin kace ya gyara. Ina Allah zai karkata zukatan shi? Dukan zukatan bayi. Hadisi sahihi anan cikin sahihu Muslim da sahihul Bukhari. Manzon Allah yace a tsakanin yatsun Allah suke guda biyu yana juya su yadda yaso. To da zaran ku roki Allah shikenan sai ya kwantar da hankali shikenan sai ya ga abubuwa sun lafa. Saboda haka ku ji tsoron Allah. Duk wani munafunci da duk wani abu ba shine zai zaunar da al'umma lafiya ba. Allah madaukakin sarki ya kiyaye.
[Speaker seg4-spk:1]
Amin.
[Speaker seg4-spk:0]
Gashi nan sai yake cewa Saboda an yada tsakanin mutane an zarge shi akan abinda ya barranta daga gare shi. A yaya ta wannan labari tukunna kowa ya san cewa shi barrantacce ne. An lalata zukatan su sun yadda cewa annabi Yusuf ya nemi matar mai gidan shi. To hakanan ya kamata ga duk wani bawa Ko wani bawa yayi kokari ya kubutar da mutuncin shi. Kar ka sake wani ya bata maka mutunci kawai sai wasu suzo suce ah to ai shikenan wannan abu kuskure ne a'a sai ka duba menene implication na wannan abu. Me zai ja maka me zai ja wa yayan ka me zai ja wa zuriyar ka abinda zaka duba kenan. Shiyasa yan arewa ku tashi kuyi ilimi na addini da na zamani kanku ya waye. Har a cikin musulunci ba komai ake wa Allah a isa ba. Sai a cutar da mutum kawai shikenan sai a zo a ce to mukaddari ne. Mukaddari ne. Haka Allah ya kaddara i. Amma me? Shari'ar musulunci ta baka yanci ka nemi hakkin ka. Ko kun fahimta jama'a? Shiyasa yan arewa yan uwa musulmi musamman hausawa da fulani da barebari da wanene ku tashi kanku ya waye akan irin wannan. Haka sidden sai jarida kaza sai ta buga karya akan ka. Gidan rediyo kaza sai ya fadi kaza akan ka. Shikenan kuma sai ace ka bayan wani lokaci sai a je a dauko wannan maganar sai a ce ba gashi ba shekaru arba'in ance ka ba akan shi ba shiru yayi ba. Duniyar da ake rayuwa yanzu ba irin waccan duniyar bace ta da. Soboda haka ku rinka fahimtar haka. Gashi abinda malam yake cewa wajibi ne tun da annabi Yusuf yanzu ya gane in ya fito to za a ga kamar an mai alfarma ne an taimake shi ko? Sai yace a bayyana mai me laifin shi kuma me matsayin matan nan yanzu. Sannan a cire duk wata shakka da ta shiga cikin zukatan mutane. In kayi haka to kayi koyi ne da wannan babban annabi. Soboda haka jama'a kun ji. Duk wanda yayi maka yarfe ko ya bata maka suna na in kaga dama zaka yafe fa. Amma kuma babban abun shine Allah madaukakin sarki ya sanya kisasi ne domin samar da zaman lafiya. Idan kasan cewa in ka taba mutuncin wane za a je kotu za a yi maka kaza za a yi kaza za a yi kaza bazaka yi ba. Ko kun fahimta jama'a? To galibi kamar yadda nace muna bukatar ina lauyoyin mu ina yan boko wadanda suka yi karatu suka koshi na ilimin zamani. Ku rinka tara mutane ko masallaci ne sallah asuba ka mike a matsayin ka na dan boko ka dan rinka wayar musu da kai dan su rinka gane wadansu abubuwa. Ina fata an gane? Na rantse da Allah abinda ya kaimu ga wannan halin kenan a arewa yanzu. Lokacin da yaran nan suka yi kukan an zalince su da muka je muka ce musu ku je ku kai kotu da wannan tunanin irin namu na yan arewa ya hada da kuma ganin halin da kasar take ciki. Sai suka ga cewa su kai kotu dan me ma za su kai kotu su basu yi imani da kotu ba su kai kotu dan me? In an kai kotun za a yi musu adalci akan me? Kawai sai suka ga cewa bari su dauki doka a hannun su. Gashi yanzu anzo ana lallashin su yanzu abun har ya wuce duk wani wanda yace zai sulhu karya yake da su wa zaka yi sulhu? Da su wa zaka yi sulhu? Kowa boko haram ne yanzu. A cikin malamai kan tuni dama cikin su aka fara samun boko haram. Cikin yan siyasa boko haram. Cikin yan boko boko haram. Cikin sarakuna boko haram. Almajirai dan kanzo ko dan dagwadagwa kowa akwai boko haram a ciki. Yan sanda manya da kanana boko haram. Kowa duka boko haram. To da wa zaka yi sulhu yanzu? Ai da da farko ne zai yu ayi sulhu amma yanzu da su wa zaka yi sulhu? In kayi da wadannan wadancan basu ma zo ba tukunna. Akwai wadanda su basu ma fara nasu ba tukunna. Duka suna nan a kasar. Shi yasa malaman ahlussunna suka yi ta bada shawaran tun farko ga yadda za a dakile matsalar kada ta faru don ta faru bala'i ne. In ta faru bala'i ne. Yanzu wasu an bude musu suna ganin hanyar samun kudi ne wasu kuma suna ganin ashe ma haka ake yi. Shikenan. Allah madaukakin sarki ya kiyaye. A cikin wannan riwaya Muslim yazo da wata dabi'a da tun da muke karatun bamu taba samun ta ba sai yau. Yace In Allah yaso malami na mai suna Abdullahi dan Muhammad dan Asma Adh Dhuba'i in Allah yaso shi ya bani wannan hadisi. To. Malamai suka yi ta maganganu bari ku ji abinda manyan masana suka fadi. Duk wanda bai da ilimin hadisi sai ya zargi Muslim akan dan me Muslim zai ce insha Allahu anan. Haka duk wanda bai kware ba Saboda Muslim yace Domin cewa insha Allahu din zata fassara wa wanda bai iya karatu ba me Cewa Muslim yana shakka. Musamman hausawa Kun san akwai abubuwa na ilimi na sha fadi kana magana cikin hausawa saboda maganganun malaman hausawa sun saba yi da karfi. To in kazo ka fada kace To sai wani ya fara shakka ko kuma ka gama fade ka ce To Bahaushe zai ce Wallahu a'alam ashe shima bai san abun ba karyar banza kawai. Duk wanda ya zauna a kasar Hausa jama'a ya san irin wannan a cikin abun nan. Malam yake cewa duk wanda yake ganin cewa Muslim shakka ce ta sa ya fadi haka ko To ai mummunan tunani Na farko dai tukunna Muslim wannan isnadin ma ba kafa hujja yake dashi ba isnadin farko na malam Yunusa shine hujja. Ya fade shi a matsayin mutaba'a ya bi waccan isnadin. Sannan kuma ya kara kawo shedar waccan hanyar. Malam yace ba wuri daya ba munga batar a baya cewa malaman hadisi suna iya kwararo hadisai ko isnadoji a wajen mutaba'a da shawahid wadanda in wajen asalin kafa hujja ne basa kawo wa. Wato in ma hanyar tana da tangarda ne Yasa Muslim ke shakka ta ko To ai ba da ita yayi hujja ba ba itace aslu ba waccan isnadin na farko Shine aslu wannan mutabi'i ne kawai. Kun fahimta jama'a? Maganar Nawawi kenan sai malam Muhammad Ali Adam yace Wannan magana da Nawawi ya fadi magana ce wadda take mai kyau kwarai da gaske. Nan gaba kadan zaka zo kaji Bukhari ma ya ruwaito irin wannan hadisi daga malamin imamu Muslim din. Kuma ba tare da ya kawo wannan maganar da kake gani da shakka ba. Dan haka Wannan hadisin ya tabbata malamin Muslim ya fade shi. Fatanabaha yace ka fada ka da wannan. Allah madaukakin sarki ya taimaka. Malamin imamu Muslim din sunan shi malam Abdullahi dan Muhammad dan Asma Adh Dhuba'i shi ko ya karbo daga malamin shi mai suna Juwairiya. Malam Juwairiya malamin imamu Malik ne amma baban shi dai ya haife shi sai ya sa mai sunan mace. Shima kuma nashi baban da ya haife shi sunan mata ya sa mai. Sunan baban shi Asma'u. Shi kuma da ya haife da shima sai ya sa mai Juwairiya. Malam Juwairiya dan Asma'u Ya halatta. Tunda gashi Abinda yasa ake fadin haka don kar kaga Malam Juwairiya dan malam Asma'u Ba dan malama Asma'u ba. Ina fata an gane? Malaman hadisi kenan duk wannan yana daga cikin bangarori na ilimin hadisi. In ka karanta karshen littafin Yace daga cikin sunayen malaman akwai wanda ke fassarawa Sabanin abinda kake zato. Ranar farko da muka fara haduwa da malami na malam Ali Nasur Alfaqih professor ne yanzu yayi retire daga jami'ar Islamiyya. Sai na yi wa wani kakan shi daga Albaniyya ne nace ba Nace lakabi ne kawai. Sai yake daukar cewa ah yace to ga ka bakin fata kuma Cace mai wa wani kakan shi tun daga Albaniyya yake nace la Lakabi ne gare ni. Kaga kenan Me kake fahimta in aka ce zaka dauka dan Albaniyya ne. Uhm uhm lakabi ne kawai. Haka wasu zaka ji an danganta shi zuwa ga wata sana'a Ba sana'ar yake yi ba mai wa rikici suka taba yi ma da mai irin wannan sana'ar. Misali yanzu wani malami sunan shi wane wane wane Alfaqih me kake fahimta Alfaqih? Talaka to amma Gadon bayan shi yana cikin karatun hadisi dalibai sai ya tsaya baya na shikenan suka sa mishi Alfaqih. To ka gani mai ciwon baya. To amma kai in kaji Alfaqih me zaka ce? Shine haka. Haka al'amuran su ke. An fahimta ko? Shi yasa galibi in kaji suna musamman a wurin malaman hadisi sai ka tambaya yaya akai? In ba haka ba in ka fassara abun da ka kamar yadda zamu ji gashi nan a gidan rediyo mutane suna tayi suna shirme. Ina fata an gane? To sai kaga kuma al'amuran sai ace maka ba haka yake ba kuma kai kana ganin ka riga ka fadi to ba yadda aka iya. Amma wancan isnadin ban gama fassara muku shi ba ko? Muslim yace in Allah ya so malami na Abdullahi dan Muhammad dan Asma'u Adh Dhuba'i shi ya karantar da ni wannan hadisi. Shi ko yace Malam Juwairiya ya bamu hadisi da ya samo daga Malik nace malamin Malik ko Almajirin Malik jama'a. Daga Dhuba'i Dhuba'i yace lallai Sa'idu dan Musayyib da kuma ainihin Abu Ubaidin wadannan manyan malamai guda biyu wato Abu Ubaidin Sa'adu dan Ubaidin Zukhuri Ina fata an gane? Su wadannan malamai su biyu suka bada labari ga Zukhuri an Abi Huraira labarin da suka samo daga Abu Huraira daga manzon Allah Sai dai a cikin riwayar hadisin Malik Iyakannan ayar ta tsaya Sai ya karanta wannan aya har sai da ya kara sheta. Kun ga a cikin waccan riwaya munji an karashi ayar ko? Anan ko sai yace sai ya karanta ayar har ya karasa ta. Sai ya bada labarin karanta ayar amma bai karanto ayar ba. Ku banbance can ko sai ya karanci ayar duka ai kunji a farkon hadisin ko? A cikin wannan riwaya sannan ya karanta wannan aya har sai da ya karashe ayar gaba dayan ta ya kawo ta. Allah madaukakin sarki ya albarkace mu akan abinda muka karanta. Abinda muka kuskure Allah madaukakin sarki ya gafarta mana. Gobe wannan karatun shi za a yi tsakanin magariba da isha in munzo za a tashi babu bayani Allah madaukakin sarki ya taimaka. Anan zamu saurara yanzu insha Allahu.Annotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Muslim #135-136. Daarul Hadeethis Salafiyyah. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15883.
Zaria, M. A. A. (s. d.). Muslim #135-136 [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15883
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Muslim #135-136. Daarul Hadeethis Salafiyyah. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15883.
Télécharger
Visualisations
Chargement des visualisations…


