document audiovisuel · Daarul Hadeethis Salafiyyah · 17 mars 2013 Citer
Ziyarar Shugaban Malamai na Izalah
- Type
- Enregistrement vidéo
- Créateur
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Editeur
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- Date
- 17 mars 2013
- Importance matérielle
- 119 minutes
- Support
- DVD
- Sujet
-
Yan Izala
Annotations de valeur
- AI Model - NER
- Claude Haiku 5.5
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000030
- contenu
-
[Segment 1/6 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yan uwa na kusa da na nesa da wadanda suke sauraran mu da kallon mu kai tsaye da kuma wadanda zasu saurare mu kuma su kalle mu ta kafofin yada bayanai na zamani kuna kallon mu da sauraran mu ne daga makarantar mu mai suna dake nan number four Madarkaci road gaskiya layout Zaria jihar Kaduna a nan Najeriya Yanzu da muke magana safiyar ranar lahadi ce wadda tayi daidai da biyar ga watan Jumada al Ula Hijira na da shekara dubu daya da dari hudu da talatin da hudu daidai da sha bakwai ga watan March shekara ta dubu biyu da sha uku Allahu Akbar
[Speaker seg1-spk:1]
Allahu Akbar
[Speaker seg1-spk:0]
Wannan rana tana da girman tarihi ga tarihin ahlus sunna a Najeriya Wannan rana tana da girman tarihi a tarihin makarantar mu ta Darul Hadith Wannan rana ce babban ta farin ciki Malamai dake nan zamu ce to yau kakarku ta yanke saka Domin ga shugaban malamai yazo
[Speaker seg1-spk:1]
Allahu Akbar
[Speaker seg1-spk:0]
Allahu Akbar Don haka yau kowanne malami ya shiga ya fita Ga shugaban malamai gaba daya ya kawo ziyara zuwa ga ayar ta matattara ta kananan dalibai Allah madaukakin sarki ya saka da alheri
[Speaker seg1-spk:1]
Amin
[Speaker seg1-spk:0]Lire le texte intégral — 12 521 mots restants Réduire le texte intégral
Ga tsarin yadda muka tsara taron jama'a Tsarin gudanar da taron shine bude taro da karatun al Qur'ani Daga malam ainihin Umar daya daga cikin malamai a wannan makaranta Sannan sai kuma makasudin wannan taro Sannan sai gabatar da ainihin manufa ko kuma jaddada manufa ta wannan makaranta Da kuma bayanin alakar wadannan manufofi wadanda su suka kai ga wannan taro Sannan daga karshe zan mika abin gabatarwa a hannun as sheikh Abbas Isa Lawaya Wanda zai gabatar mana da malam Ya kuma gabatar mana da ainihin sauran malamai da suka rufo mishi baya Muna fatan jama'a a dan samu natsuwa kadan Domin ainihin malam Umar ya matso kusa ya karanta mana abunda ya saukaka na ainihin al Qur'ani mai girma Na'am Tsaya daga nan kawai ko a tsaye ne malam insha Allahu bismillah Bangare na biyu a makasudin taro Makasudin taron nan Shine ziyara Da muka kai Jos daga makarantar nan tamu gurin as sheikh al Allama Yahya Shugaban majalisar malamai Ta ainihin kungiyar jama'atu izalatil bidi'a wai kamatus sunna Allah ya saka da alheri
[Speaker seg1-spk:1]
Amin
[Speaker seg1-spk:0]
Malam da shi da sauran malamai da almajiransu suka mana tarba hannu biyu biyu Kunji dadi mun gode kuma munzo duk mun zayyanawa daliban makarantar nan Malam muna kara godiya mun gode Allah ya saka da alheri Malam yayi mana jawabi Masu karfafa gwiwa kwarai da gaske Malam ya bada shawarwari malam ya mana addu'o'i Mun gabatar da bukatar cewa muna rokon A cikin kuncin lokaci da malam yake dashi A sa mana wata rana da wani lokaci da za'a ziyarce mu Malam ya fada kuma malam ya cika malam muna kara godiya Allah ya saka da alheri Babu shakka Ga duk wanda ya saurari Wasu jeran giyar kasusuwa da nayi guda hudu wadanda na sa musu Take da farin sako na fatan alheri Zuwa ga ainihin Kungiyar jama'atu izalatil bidi'a wai kamatus sunna Na kawo takaitaccen tarihin kungiyar da kuma shi shehin malamin da ya kafa ta as sheikh al Imam Isma'il Idris Zakariya Allah ya gafarta mishi
[Speaker seg1-spk:1]
Amin
[Speaker seg1-spk:0]
Babu shakka Hakika Tarihin ya nuna cewa manufar itace gyara Wannan maudu'in na ajiye shi zamu gayyato wani dattijon malami wanda malam ya fini sanin shi Daga garin Bauchi Muna fatan insha Allahu ta'ala zai zo wataran zai mana Ziyara gurin nan kuma zai takaita mana tarihoki irin wannan to in yaso malam a lokacin zai kare mu da wasu wadanda kuma zasu Kara rufa mishi baya insha Allahu ta'ala Allah madaukakin sarki ya saka da alheri Bayani na gaba shine Ita wannan makaranta tamu mai suna makarantar Darul Hadith Salafiyya Mun kafa ta a cikin watan Satumba Shekara ta dubu daya da dari tara da casa'in da idai Yau kusan shekara ashirin da biyu Manufar wannan makarantar Itace kokarin dawo da al'ummar musulmi zuwa ga al Qur'ani da sunna annabi ingantacciya Da kuma fassara su da fahimtar su a bisa fahimtar malaman farko as salafus salih Kokarin tace abubuwan da suka makalkale wa musulmi na shirka Da bidi'a Da monanen tunani Wadanda ainihin sunzo ne sakamakon son zuciya da kuma hadisai na karya da masu rauni Wadanda wadannan shirka da bidi'o'i Sune suka kashe haske da kyalle Na ainihin addinin musulunci Tarbiyyar musulmi akan addinin su na gaske da kuma kiran musulmi zuwa ga aiki da manufofin addini da kuma dabi'antuwa da dabi'u na addini wannan da wannan ne kadai zai sa musulmi su samu yardan Allah Rayayye kyakkyawan tunani na musulunci a bisa fahimtan malaman farko Na daga ainihin wadanda suka gabace mu cikin sahabbai da tabi'ai Da kuma tabbatar da cewa musulunci addini ne mai yanci Musulunci ba bautar can addini bane wanda za'a makala tunanin ka Da wani shehi ko kuma wani imami a hana ka ainihin ka zarka zarka dangane da abunda ya dace kai To sa'annan matsaloli da suke damun musulmi na yau da gobe Kokarin basu shawarwari Da kuma warware wadannan matsaloli ta hanyar gayyato malamai Da kuma ainihin malaman nan su karantar su kuma ainihin wa'azantar da mu domin su taimaka mana wajen abubuwan da suka dame mu Domin aga abunda suke su Domin kokarin cinma wannan manufa Makarantar Darul Hadith tana da tsarin kafa makarantu Da bangarorin a lafiya Da bangarorin sana'a Da bangarorin abunda ya shafi Wato tarbiya Bangaren makarantu makarantar tana da manufar samar da makaranta ta nazri da primary Da makarantar secondary da cibiyar karantar da ilimin computer da fasahar zamani Da kuma jami'a wadda jami'ar muke fatan ta kasance tana da bangarori guda biyu bangaren farko mun sanya mishi suna Ranka dade Abubakar Mahmoud Gumi University of Islamic Bangare na biyu Mun sanya mishi Albani University of Information and Communications Technology Zaria Makarantar tana fatan ta ringa gabatar da harkoki na ainihin wato sadarwa kamar ICT consultancy da internet services Samar da asibiti pharmacy da kuma ayyuka na ainihin gurin gwaje gwaje wato laboratory Sannan cibiya ta gabatar da bincike dangane da harkokin magunguna da abubuwan da suke da alaka da haka buga takardu littattafai da yarurrukan turanci larabci Da Hausa da yaren platanci da yarabanci da yaren iyamiranci da makamantan haka samar da tashar talabijin Da tashar radio da kuma buga kasusuwa da sidina da kuma yada su samar da cibiya ta koyar da sana'o'i A harkar gyaran computer da harkar saka da dinki da kuma harkar unguwar zoma da kuma kula da lafiya Horar da malamai na musulunci ta hanya harda Qur'ani da hadisai Da kuma kwarewa dangane da littattafan mu na fiqihu wadanda muka ainihin san su a kasan nan da kuma wadanda ainihin yan uwan mu ahlus sunna suke ainihin ta'amuli dasu a sauran bangarori na duniya Gabatar da bincike da gabatar da lacoci da taron karawa jula ilimi dangane da harkokin addini siyasa tattali da kuma harkokin rayuwa Na cikin gida da waje samar da Gurin ainihin rainan yara marayu Da kuma wadanda ainihin ake zubar da su da sauran su sai kuma bangarorin da suka shafi harkokin kasuwanci Wadanda wadannan sune ainihin manufofin makaranta a dunkule a karkashin wannan manufar Muka ga cewa Hakikanin al'amari Duk inda yan uwa suke ahlus sunna yan uwan mu ne
[Speaker seg1-spk:1]
Na'am
[Speaker seg1-spk:0]
A lokacin da muka ji labarin cewa Malam Muhammad Sani Hayya Ya kai ainihin ziyara ta ta'aziya lokacin da malam mai Ganduje ya rasu Allah ya gafarta mishi Ya gabatar da su jawabi babu shakka munji dadin wadannan jawabi kwarai da gaske Wadannan jawabi sun nuna karin ilimi da dattaku Hakan cewa azo a hade Malam ya kara mana sharhin wadannan maganganun wadanda muyiwa malam ko zai kara mana yanzu amma dai mu malam yayi mana an dauka a cassette kuma malam ya aiko mana da cassette Ayi kokari a cire gaba dake tsakani abiyi juna sallah abai wa juna uzuri Wadannan kalmomi ne takaitattu guda uku amma suna bukatar mujalladai ne wajen shirkin su malam Allah ya saka da alheri Malam bai fadi wannan maganar a baki ba kawai a aikace sai muka ji kungiyar izala ta hade Muka ji duk inda ake sanarwa sai ace hadaddiyar kungiyar izala sai mu ce alhamdulillahi Duk masoyin musulmi yayi murna duk masoyin sunna yayi murna Muka kai ziyara malam ya kara jaddada mana cewa kungiya ta riga ta hade don haka an wuce wannan ajanda yanzu sai aiki To muka ce to malam kuna da yaya Kuna da jikoki da tattaba kunne basu taba ganin ku ba Labarin ku suke ji Akwai wadanda wasu ma in mun sanya musu murya as sheikh Isma'il Idris Wallahi sai sun tambaya waye wannan Sai mu dan yi dariya To Yau dai wanda bai taba ganin Isma'il Idris ba insha Allahu ga kaban copy Insha Allahu Malam Muhammad Sani Hayya Babban malami ne wanda a wani cassette da wani dattijo ya aiko mini bayan as sheikh Isma'il Idris ya gama kawo tarihin kafa kungiyar kap Sai da malam yayi wa'azi na wajen minti arba'in da biyar Malam Allah ya saka da alheri Malam ya ziyarce mu Nayi zarbabin sanarwar cewa as sheikh Abbas Isa Lawaya zai gabatar da malamai sai dai anyi mini gyara cewa as sheikh Nasir Abdul Muhyi Ko Shine zai ainihin gabatar da malamai Allah madaukakin sarki ya saka da alheri Allah ya gafarta malam as sheikh malam Nasir Yahya malam Nasir Muhyi
[Segment 2/6 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
Ibrahim Duguri kuma sarkin malaman Duguri har yanzu. Kuma ba Duguri ne. Ah sannan kuma cikin waɗanda suke nan har ila yau akwai Malam Shu'aibu wato Idris Kaduna imamu na masallacin na Gwamutse kuma ɗayan wato waɗanda suke suna tare da Malam Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi a tsawon lokaci har ya koma ga Allah Allah ya ji ƴan Malam. Ah kuma yana tare da Malam Sheikh Ismaila Idris ko har lokaci da Allah ya karɓi ransa shima. Akwai har yanzu cikin birnin Zaria dai akwai Malam Abubakar Salisu shima yana nan Malam Abubakar Saleh ko? Saurayi ne gashi nan matashi kun san shi shima a nan garin. Akwai kuma koma chairman na ƙaramar hukumar Anchau wani mutum mai sauƙin hali gashi nan a nan ƙasa yana zaune. Allah ya saka da alheri. Akwai ɗaya daga cikin limaman mu na cikin garin Jos wato Malam Muhammad Musa ah Malam Musa Alburhan wanda yake shi daga Makka yake Malam ya tura shi wani aiki kuma ya biyo ta nan shine gashi Malam Musa Alburhan. Limami ne na Juma'a. To sannan kuma akwai ƴan agaji waɗanda muka taho da su da sauran jama'a sannan ni kuma da nake magana an riga an faɗi sunana Muhammad Nasir Abdulmuhyi sakataren gasa karatun Alƙur'ani ta ƙasa baki ɗaya kuma akaramakallahu kafin zamu roƙi Malam Abdulrahman Ahmad ya karanta ayoyin Allah girma kafin a cigaba Malam Abdulrahman.
[Speaker unknown]
Alhamdulillahi Ah Allah ya saka da alheri. Jama'ar Zaria mutanen Zaria muna muku fatan alheri wannan kaɗan daga cikin wato guzuri da Malam ya taho da shi muna roƙo Allah ya taimake mu Malam bismillah. Akaramakallahu to jama'a zamu miƙa abun magana kai tsaye ga Sheikh Imam Muhammad Sani Hayya Malam Allah ya saka da alheri. To bismillah akaramakallahu. To jama'a na buɗe wannan tsayuwa dan gabatar da jawabi da Allah yasa shugaban wannan makaranta ta Darul Hadith wadda take karantar da hadisai na Annabi sallallahu alaihi wasallama masu fassarar ta Alƙur'ani mai girma kuma bisa ga fahimta na na wannan al'umma ta musulunci kamar yadda shi shugaban wannan guri Malam Muhammad Al-Awwal Al-Sheikh yayi mana bayani. Na buɗe da yi wa Allah mai girma da ɗaukaka yabo da godiya da salati ga shugaban halittar Allah gaba ɗaya Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam shiran Allah da amincin Allah su tabbata ga wannan manzo mai girman daraja shi da alayensa da sahabbansa da masu koyi da su da kyakkyawan aiki bii da bii har zuwa ranar tashi alƙiyama Allah ya sa da mu cikin su. To alhamdulilllah duk da ban sani ba ko minti biyar ne ko goma ko sha biyar jawaban da zanyi Malam a haife na ka dai. To gaskiya ni inga na zo naga zunzurutun matasa musulmi a halin sunna akan wannan kyakkyawar manufa da na ambata dalilin kafa makaranta kamar yadda muka ji daga bakin babban malamin mu na wannan makaranta da yayi bayani da irin kuma ni manufar da ta kawo ni gari ya gari tun daga cibiyar gudanar da jagorancin ƙungiyar sannan niyyar ƙungiyar wa'azi na musulunci da Allah ya nufi da kafawa shekaru talatin da biyar da suka gabata a wannan ƙasa ta Najeriya a mazauninsa cikin wannan lokaci babban birnin jihar Fulato Jos inda cibiyar wannan ƙungiyar take. To na taho da manufar ziyara ta ƴan uwantaka ta musulunci. Tun muna da jajayen sawo da mahaifansu suka kama hannun mu zuwa makaranta muka yi kidayar baki muka yi farfaro muka yi hajjatu kuma muna ɗaukan karatu na ilimi na fassara ta Alƙur'ani da hadisai tun daga in ka karantar da yaro shi mai ƙananan shekaru yana koyan karatu mai risala ya dubi hadisin Annabi sallallahu alaihi wasallama yace kamar rubutu ne ko zane akan duwutse ba zaka hure da hannu kace ai ya ba iska ta bi ta kai ya canza ba. To sai ina tuna a an karantar da mu duk wani abun da zaka so to ka so shi dan Allah. Da aka soyayya tsakanin wato iyaye da ƴaƴa ayi ta dan Allah. Idan soyayyar ta zama ba dan Allah ba sai mu ga ga waƴansu ƴaƴan da iyaye an raba gari kamar Annabi Nuhu da Kan'an ka ga saɓawa tafiya akan hanyar Allah shi ya kawo rabuwa. Kamar Annabi da Azara su ma suna da dangantakar ta iyayen amma an saɓa saboda Allah. To idan aka ɗauko uwa da uba aka ce su ma dan Allah za'a yi zama tare da su to ka ga in tsaya ina ce haka ma uwa ƙani miji mata ka ga na iyayen ma ai a wannan zamantakewa ta ƴan adam min babi aula. Kuma na zo wannan guri dan Allah na so shi Malam Muhammad Al-Awwal dan Allah saboda nayi la'akari da in aikin Allah za'a yi to ba dama fa ayi daka. Da ana aikin Allah daka da Allah bai saukar da Alƙur'ani ya aiko da annabawa tun kafin zuwan shugabansu gaba ɗaya su karantar da dalilin halittar bayi ba kuma ka buɗe buɗe Alƙur'anin da ya yi karatu da sunan ubangijinka wanda ya halitta Allah wanda ya halitta mutum daga dalaki na gudan jini mai rataya a jikin mahaifa. Kai karatu shugaban halitta Allah yake gayawa kuma Allah ya nuna duk abun da muka samu kaɗan ko mai yawa kyauta ce daga Allah to amma duk irin kyautar da aka ba mutum in aka rega ciki ba ilimi to ta gina ne bata shiga ba. Kai karatu warabbuka kuma ubangijinka Allah shine mafi karamci mai baiwa babbar baiwa da ba kamanta bayan halittawa to sai ilimi. Dan sai da shi imani zai inganta sai da shi aikin bautar Allah zata inganta. To sai na leƙa naga wannan guri fa makaranta ce ta karantar da addinin musulunci ba daka ba akan hujja Alkitabu wassunna. Alƙur'ani littafin nan na Allah wanda ɓarna bata zuwa gare shi gabansa da bayansa. Ba magana ta ka ba Allah da ya nuna Alƙur'ani sai yace Ɓarna bata zuwa ga Alƙur'ani babu wani wahayi da aka yi ya nuno Alƙur'ani kafin zuwansa ya soke shi. Haka bayan Alƙur'ani ya sauka ba za'a zo da wani kuma wahayi daga Allah kuma ya shafe hukuncinsa ba. Saboda haka da gabansa da bayansa ɓarna bata zuwa masa wannan littafi mai girman daraja zancen Allah ne dokokinsa ne a ƙunshe da aka yace saukar wace da ta zo daga Allah gwani mai ajiye komai a inda nan ya dace ya ajiye wato godar dai shine yace To sai naga kuna karatu kuma ana aiki ga makarantu ga niyyar buɗe asibiti gidan rediyo talabijin sa a ikace a ikace kusa da nesa. To ka ga Islam kenan za'a karantar shi ake yi wanda Allah ya hana cewa duk abun da zamu yi kar mu yi na ka Kar ka kuskura ka ba abun da baka da ilimi a kai. Domin hanyoyin nan na gane ilimi ji da gani da tunani mahasusa Inna sam'a lallai ji wal basara da gani wal fu'ada da tunani shi ɗan adam mutum ne ko aljani akan wannan ji da gani da tunani za'a yi mata tambaya a kai. To kun ga wato dole in zaka so mutum ka tarayya damu da bin Allah a ilamance yana gudun abun da Allah ya hana a ilamance wanda wannan shine Allah ya mana baiwa da manyan malaman sunna a wannan nahiya ta Sudan niyya su Sheikh Usman bin Fodi suka zo suka yi jihadi suka yi wa'azin musulunci a ilamance waɗanda suka biyo baya lokacin da suka samu rauni suka ƙi karatu Allah ya jeho turawan mulkin mallaka suka tarwatsa su suka kwace gwamnati aka dinga karya ƙa'ida ta rayuwar musulunci ɗaya bayan ɗaya da yake Allah baya barin al'umma cikin ɓata sai kuma ya kawo mana masu jaddada shari'ar musulunci su yi faɗa da turawan mulkin mallakan a ilamance Allah ya kawo mana Sheikh Alhaji Abubakar Mahmoud Gumi ya fara karantarwa yana yi yana sanɗa ya jefa darasi ya shekara biyar kafin yayi ɗori. Duk inda aka tsaya za'a yi magana to akwai maganar da ita ce cancanta ayi wannan a wannan gurin kuma duk zamanin da ka sani to yana da waƴansu mazaje da Allah ya musu baiwa da zasu jagoranci addinin musulunci a ƙa'idarsa. Ya zo yana wannan karantarwa Allah ya haɗo masa waɗanda ya buɗe kirjinsu da gane tauhidi da bin sunnar manzon Allah sallallahu alaihi wasallama har muka yi wannan tsuntuwa ta Sheikh Ismaila Idris bin Zakariya ya tashi tun daga gidan uwa da uba a farfajiya ilimi wasu karatuttukansa a gurin gyatumar sa yayi ya gaya mana da bakin sa waƴansu a gurin mahaifinsa karatu ya bunƙasa har ya zo cikin birnin Bauchi ya ɗora darasi a gurin Malam Ahmad na kan Kusurwa daga nan ya zo gurin limamin Bauchi Malam Mahmoud ta gamma da karshe bayan ya zama malami ya zo nan Zaria babban birnin ilimi wanda ya daɗe yana riƙe da tuta ta yaɗa ilimi a wannan nahiya wanda sakamakon haka sa Ahmad Bello da sardaunan Sokoto da ya zo zai kafa jami'a sai ya zaɓi Zaria birnin ilimi aka kafa jami'ar Ahmad Bello wanda take riƙe da tuta ta rayar da ilimi sai dai kuma ilimi yana da wani abun mamaki ba ruwansa da launin fata ba ruwansa da gado ba ruwansa da gurin zama har irin ɓarnar da jahilci ya jefa a ƙasannan in an tashi neman karatu aje ayi rubuce-rubucen sha a sha wai za'a haɗa ce Alƙur'ani a kamo alhuda huda wanda Hausa suke kiransa kahu hu a yanka a ƙone tokar ayi rubutun sha a wanke a sha gardawa suka buga aka sha hadda bata zauna ba aka sha hadda bata zauna ba sai suka fito da wa wani kirari a Hausance suna cewa kahu hu kuka sha sai kayi. To ka ga wato ashe tarihin nan da na kawo na kafi wa jami'ar Ahmad Bello gaban zage zage ƴan uwana na addini na harshe wanda wani lokacin suke cin gyaran mu wani lokacin mu cin nasu to ba dama wani kenan daga cikin samari ko maza ko matace mun yi sa'a tun da jami'ar Ahmad na nan a wajen mu mu ba sai mun je makaranta ba to ko ka sha sai kayi. Kun ga ni wannan ziyara da Allah ya bamu mu zo don sanku kuna aikin Allah kun yi amfani da jinku da gani da kuma lokacin da Allah ya bamu da
[Segment 3/6 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
ayi karatu. Da lokacin in baku adadin makarantun da sanadin sheikh Isma'ila Idris. Ya karantar muka bita a tsari. Da jituwa da juna. Da hadin kai. To wallahi sai an dada takawa da karfi. Abin da yasa kuka ji a cikin jawabin malam Muhammad al-awwal. Ya bayyana soyayyar na kira ahalin sunnah. Mu taho mu hadu. A kan hanyar Allah madaidaiciya. Yaji farin ciki ya kama shi. Ya debi sashin dalibai. Yaje mazaunin mu. Muka ini. Domin awa daya. Ta karantar da addini da son juna. In na kira ta ini ni ban ga laifin da nayi ba. Domin in an tashi ranar tashi alkiyama ma gaba daya. Da wanda yazo ya shekara. Dubu da wani abu kafin ya bar duniya. Irin zamanin su annabi Nuhu alaihis salam wanda samari matasa yan shekara dari bakwai bakwai ne. Da wannan zamanin da annabi sallallahu alaihi wa sallama ya nuna cewa tsawon ran mutane lokacin girbi. Tsakanin shekara sittin ne saba'in. Kadan ne wasu suke wucewa. To kaga in an tashi ranar tashi alkiyama ba dama yan shekara dubu su rika cewa mu ai mun dade a duniya mun girme muku mun sha yau kaza kaza kaza. Sai annabi sallallahu alaihi wa sallama da. Allah yayi magana da shi ta hadisul kudusi ya isar. Sai ya nuna mana wannan zaman duniya kar wani yaje ya dauki wata hanyar da ba wannan ba. Kar kayi maganar na girme maka na fika kudi na fika tara karatu na kaza um um. Iyakarka da wannan zaman duniya shine ayyukanku da kuka yi mai kyau. Ko a fili kuka yi ko a boye ina kiyaye ku ba abin da zaku yi ya bata a rububbe. Kuma Allah mai tausayin bayi Allah latif. Mu taku ka kadan a aikin shari'a ce a ninka lada goma. In na daga addini ne a ninka gida dari bakwai in mukayi dace mukayi aiki na gari a daren lailatul kadari. Sai mun shekarar tamanin da hudu muna yi in ba a daren lailatul kadarin ba bamu samu ladan da muka samu a daren lailatul kadari ba. Kai wani aikin ma idan mukayi a ninka a ninka sai Allah yace kuma duk laifin da sukai kuma a kankare. To kaga. Aiki mai kyau da ya dace da shari'a shi ake nema a guri na a gurinka a gurinki a gurinku a gurin mu. Saboda haka. Gaskiya na kwalla rai da inzo in sadu daku kuma nazo na ga farin gani. Allah ya kara mana albarka.
[Speaker seg3-spk:1]
Amin.
[Speaker seg3-spk:0]
To. Manzon Allah a gabansa a sahabbansa. Sai yace. Addini nasiha ce. Kaga da munji wannan. Abin da zai zo cikin kwakwalwan mu shine eh to za'a bada kyawawan shawara kenan anyi nasiha. Inda muka bar wannan. Muka ajiye muka ga addinu an nasiha na da ma'ana mai fadi fiye da haka. Sai da sahabbai suka tambayi annabi. Addini nasiha ce gawa. Sai yace addini nasiha ce ga Allah. To kaga nan lallai kowa yasan ba'a bada shawara bace. Domin Allah gajiya wa bata shafarsa. Ba taba lokacin da ba Allah ba dama yana nan. Allah bazai kare ba. Har abada. Kuma mai cikakken iko ne mai cikakken ilimi mai cikakken ji mai cikakken gani. Da abin da muka samu da wanda ya same mu daga Allah ne. To kaga shi yaushe zai nema a bashi nasiha. To gashi kuma annabi ya fada shi kuma. To meye ma'anar nasihar kenan a nan. Shine kada yita Allah da ibada. Kada musuffan tashi da wata sifa da bata cancance shi ba. Shi daya yake a zatonsa Allah tabaraka wa ta'ala shi kadai yake aikinsa ba mai taya Allah aiki. Shi kadai yake a cikin sunayensa da suffofinsa shi kadai ya cancanci bauta ga talikai duka. Wanda wannan ya kafi a zuciyarsa da bakin sa da aikinsa yayi nasiha ga Allah. Ashe nasiha ga Allah. Ta banbanta da yadda muke tsammanin nasiha ta bada shawara. Addini nasiha ce ga littafin Allah. Gaskata. Al'kur'ani zancen Allah ne. Dokokin da suke cikin sa ba kure a ciki. Umarninsa wajibi ne mu bi bisa ga yadda annabi sallallahu alaihi wa sallama ya fassarta mana sahabbai suka fahimce shi. Wani gurin yazo a wajibi ko farilla wani yazo a sunnah wani yazo a mustahabbi wani yazo a kan. Wato wani yazo a kan makaruhi wani yazo. A kan haram wani ma ya kai ga kafirci Allah ya tsare mu. To kaga wannan al'amari. Ko ba'ayi dogon bayani ba dole sai da karatu. To kuma in da Allah yana so. Rana daya lokaci daya kankace mai nayi wannan aiki. Sai ya halitta mu tun daga na farko har na karshe. In shekara triliyon yake so muyi a duniya. Ya karbi ran mu ayi tashi alkiyama in yaso yayi haka ashe yi. To mashi kuma Allah ba haka yayi ba. Sai yasa. Zamuyi zuwa ne na duniya biyu da biyu. Don biyayya dole ce. Don haka wani. Mahaifin wani. Wani. Dan wani. Wani jikan wani wani mahaifin wata. Wata mahaifiyar wani haka akayi mu daki daki ana zuwa. Jama'a da Allah yace. Yaku mutane. A gaya mun wanda wannan kiran ya ware. A cikin mutane. Ni dai nasan da ni. Sai Muhammad al-awwal kana jin abin da na fada. Ya ayyuhan nasu ta hada da kai. To kuma majalisan malamai fa. Maza da mata yara da manya wanene ya ayyuhan nasu bata hadu da shi ba. Sai ace sai Allah yace. Kuji tsoron ubangijinku. Ku sanya garkuwa tsakaninku da azabar Allah. Shine abin da Allah yace muyi muyi iya karfin mu abin da ya hana mu ne ya sance shi. To kaga mun sanya garkuwa kenan yadda Allah zai rufa mana asiri ya yafe mana bazai mana azaba ba. Jama'a dukkan talikai waye mahaliccin mu Allah Allah ne. To muji tsoron Allah wanda shi ya halitta mu. Sai Allah ya nuna duk da ya halitta munnann bai ajiye mu. Tsarin kai da kai kunnen doki ba na gaba ba na baya ba. Sai yace. Ya halitta mu daga wata rai guda daya baban mu na farko. Bari ma in huta in fadi wa sunan sa. Annabi Adamu alaihis salam kowa ya sani don haka ma ake kiran mu yan Adam. Don haka uban mu na farko. Annabi Adamu. Ko a cikin mutane. Akwai wanda shi babansa na farko ba annabi Adamu bane. To saboda haka farko tukun Allah ya hada kan mu. Bai yarda mu tarwatsa ba sai ya bamu uban mu na farko annabi Adamu shi daya. Wato daga wannan uban namu na farko. Sai Allah ya halicci abokin gwami na zaman tare na wannan rai na annabi Adamu matarsa. Hawa'u an samu gidan aure. Ya kuma matasa. Ya mu dattijawa ya na kusa ya na nesa. Wallahi da mu maza da mata. Mai son kansa da lafiya yayi aure. Idan kuma kayi aure. To ka zama half cat. Domin. In mutum yayi aure. Bari in gaya maka wani ma'auni duk namijin da yake yaba laga. Kar ma ka bata lokacinka tambayarsa yana son mata. Duk mata da ta ba laga ita ma tana son maza. Duk wani guzuri ne da Allah ya kawo mu kowa ba wata makarantar da ka shiga ka koya cewa in na kai inyi aure in ina ma da ina da mata. Kowa na da wannan. Ita mata na da shi. Namiji na da shi. Allah bai bar mu mu lalace ba. Sai ya hukunta tsarin aure. Ya bamu misali uban mu na farko annabi Adamu ya halitta masa matarsa. Wato itace nanu hawwa. Hadin kai. Ko yadda mu cewa kai dan Adam namiji yi aure. Ke yar Adam mace yi aure. Don haka annabi sallallahu alaihi wa sallama da yazo yana fassarta mana rayuwa sai ya nuna mana cewa wato. Duk wanda yayi aure ya shawo kan rabin matsalolinsa na rayuwa sai kuma ya gwagwarmaya garabi. A samu Allah ya yafe mu ya rufa mana asiri ya ciccika mana mu haye mu tsira. Waye hayar da mu Allah waye tserar da mu Allah. Saboda haka kar wana hure mar kunne. Yaki aure yazo yana. Waige waige duk wata mai koriyar a tanfan ta wuce sai ka waiga. To yi aure mana. Ga hanya ta gaskiya mai kyau. To albarkar aure haihuwa. Kar kayi auren kuma kai an haife ka. Kar ka zullumin kar ka haihu. Sai Allah yace. Sai Allah ya watsa irin albarka na samun haihuwar. Yaya maza da yawa. Da yaya mata da yawa tab duniya ta cika. Yaya za'ayi mu zauna lafiya wani yafi wani tsawo. Wani yafi wani. Gwabi. Wani yafi wani farapata. Wani yafi wani karatu. Wani na gabar wani na yamma wani na kudu wani na arewa wani mai dukiya wani talaka wani mai mulki wani wanda ake mulka. To gashi duniya ta cika ya za'ayi mu zauna lafiya sai ya sake dauko hanyar zaman lafiya yace. Kuji tsoron Allah ku tsare dokokin Allah ba abin da zai zaunar da duniya lafiya sai shari'ar musulunci sai tsare dokokin Allah inda duk aka shirya wani wayo wallahi ayi ma aje. A addaka kai da dutse ba'a samu hanyar fita ba. Hanyar nan ta Allah ta addinin musulunci ita kenan tilo. Za'a iya tafiya a samu zaman lafiya. Saboda tsoron Allah jama'a wai shi ruwan sama ne aka daina mana a Najeriya ake fama da yunwa wayansu sun dade a cikin mu duk sun karace. Ah ah rashin tsoron Allah ne yasa wayansu suka cinye kudi. Ana watina ne. Shin. Wai. Karfin da mutane suke da shi suke tare hanya. Suke yi wa wasu duka wasu ma su kashe su su ibe musu dukiya. In da tsoron Allah za'ayi haka. Kaga da da tsoron Allah da ba barawo. Da da tsoron Allah da ba yan siyasa azalumai. Da da tsoron Allah da ba maza maza na ta da ba mata maza na ta. Da da tsoron Allah da akwai tausayin na baya. Da da tsoron Allah da akwai ganin girman na gaba. To sai Allah ya nuna mana. Tunda ya halitta. Yadda za'ayi mu zauna lafiya. Kuji tsoron Allah ba kuma wanda bai san Allah ba. Wanda da shi sunan sa ma kuke magiya don Allah abun kaza don Allah a yafe ni da sunan wa akayi magiya. Wanda zaka wa din yasan Allah din. Kai da kayin ma kasan Allah. Saboda haka Allah nan da kuka san shi kuke magiya da sunan sa kuji tsoron sa kuji tsoron yanke zumunci. Kar ace babanka ya haife ku ko kaza. Amma baida dara ba ja baida girma. Ko kuma malam Muhammad al-awwal ya tashi furfuran nan tasa tayi sammako. Ba dan dawainiyar karantarwa da wahalhalu na tsayawa ya karantar daku ba wata kila da gashin sa bai fari kamar haka ba. To dan Allah ace duk karantarwar wannan yanda yayi muku baida girma baida daraja a gurin ku wannan daukan alhaki har ina. Duk mutumin da yace ubansa banza ne. To in kai kana cewa mai ake kira banza to wannan din kaga banza ganin idonka. Wanda yace malaminsa banza ne shine banza. Matar da tace mijinta banza ne itace banza. Talakan da yace shugabansa mai adalci banza ne shine banza. Da menene da Allah baya son mai biyayya sai halitta mu rana guda ba'a riga kowa ba. A gurin Allah mai sauki ne. Iyakal amarin ubangiji halitta da gabaye ba wata ta taburza bace a wajensa in yayi nufin halitta wani abu. Ba neman suna dare ba neman masu taimakawa. Shine da yace da wannan abin da yake so ya halitta kun kasance sai abin yayi ta kasancewa yadda Allah yake so. To kaga tunda yayi mu uban mu na farko annabi Adamu to biyayya yake so muyi tsakanin daya da uwa. Aka riga halitta miji kafin mata. Nanu hawwa'u biyayya aka koyar da mu. Iyayeyye. Kafin yaya yaya yaya kafin jikoki biyu da biyu biyu da biyu biyu da biyu. Saboda haka yaya akayi gashi. Bayan musulunci hijirarsa na shekara dubu daya da dari biyu da shekara talatin da hudu bana. Da da dari hudu ko da talatin da. Hudu bana. Amma muna cewa makaranta da za'a karanta al'kur'ani hadisi. Karantarwa a kan yadda salafus sali suka tafi to salafus salihin ina daya yanzu sun wuce. Amma. Ba su sukai almajirci a gurin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ba. To in ka cici kai ba ruwanka da su. To kaima ba kowa ba. Idan kace fahimtar su baka damu da ita ba. To kaima baka da wata fahimta. Yanzu kaga misali. Yana da kyau. Idan malam Muhammad al-awwal zai zai binciki a kan sheikh Isma'ila Idris daga cikin wanda zai yi wa tambaya yamin. Da menene na rayu da shi. Mun yawan wa'azi tare. Mun kwana tare. Na dauki karatu a gurinsa. To ina da banbanci da wanda. Shi labarinsa yaji. Ko babu. To. Muna university. Sai wani. Yazo yana bada lacca sai yace su sun fi sahabbai ilimi. Kai subhanallahi naji yar jikina ba dadi. Sai wani abokin karatu na sai yace eh sai yace naga hankalinku ya tashi yace yace to ai lokacin sahabbai. Babu Bukhari ba Muslim ba kaza ba kaza ba kaza ba kaza saboda haka su sahabbai basu ga wannan ba. Don haka ya ya ya ya yayi taddaga na tadda na gaba wuce ya fofi sahabbai. Ah. Wato ilimi inji shi. Can a bakin sa. To sai. Wani aboki na malam Abdullahi bazan karasa sunan ba don kar. Addreshi yayi yawa. To sai. Yace mun to ai kaji ya bada hujja. Nace ta me yace ai wai su sun karanta kaza kaza. Sai nace to sai nace malam Abdullahi yace nace ka gane nan. Yawa nace to ni nasan sar dauna. Dashir nasan sa dauna naji maganarsa da komai da komai. Sai nace to. Bayan mu cewa sa. An rubuta. Littafi dangane da sar dauna. Mai laifi. To sai kazo ka karanta mai laifi
[Segment 4/6 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker unknown]
Ni ko da shi mukai ta hira. Don haka saninka da Kafi ni sanin sardauna. Yace a nan gaskiya ban fika ba. Nace to su sahabbai wani rashin gata suke da shi a gurinku? Da za'a ce sun zauna da annabi sallallahu alaihi wasallama sun yi yaki, sun ci abinci tare, ya aike su, sun ji maganarsa, sun ga ranar da yake cikin fara'a sosai, sun ga ranar da wani ya tabar gaza fuskarsa bata amsa ba domin shi baya goyon bayan abin da ba daidai ba, a ce wanda yazo ya gani an rubuta wai shi yafi wanda aka yi da shi. Nace kai kaga wannan tayi? Yace wallahi Allah ya taimake ni na gane. Kun gani rubutu yana neman malami. Wannan yace malamin sa banza ne shi kan ya gama asara. Domin Iziya aka tasam rubutawa. Sai aka zo wani kawai sai yace shi tafi da malamin tafi da malaminka, tafi da malaminka. Wai shi zai iya gane abu ta komputa ko ta kaza ba sai ya abin nan ba. Sai ya dauko ya iya karatun Hausa yazo mai Iziya yayi bayanin yadda wato najasa idan mutum na salla ta zuba a kansa sallarsa ta baci sai ya kaza. Kawai da yazo yace ya jama'a yace sai yace don mutumin da aka hadu a masallaci ana salla sai ingulu ko wani abu mai najasa ya yayi kashi akan kwanan masallaci sallan mamu duk da liman babu. Aka ce a ah kai mutane suka je duk da dai suka ce kai ko bamu yi karatu ba mu mun dade mana anya? Sai aka zo aka ce to a ina a yace da hujja ta ina yake? Ya kawo Iziya. Aka bude to a gurin boko ba banbanci tsakanin rubutun masallaci da masallaci. A boko ko da banbanci? Ku ne malami. Da in an zo an rubuta masallaci da masallaci a a haka da banbanci? Sai ka duba gaba ka duba baya sannan ka ga to ka fi da ma'ana ko? To shi da yaga wato ance idan najasa ta zuba akan masallaci ta bata masallacin sai yace in najasa ta zuba akan masallaci sai yaje shi bai fahimta ba yaje zai kashe mutane da ka. Rashin malami. Da da malami yayi haka ya jama'a wanda ya karantar da kai karatu tsakanin daraja da koma bayanci me Allah ya bashi? Kai ga yanda maza muyi mu gane. Karantarwa Allah ya aiko manzon Allah sallallahu alaihi wasallama da annabawa gaba daya zuwa ga duniya. Ko ba haka bane? To ya kaga daraja da girma irin ta annabawa? Ya kaga daraja da girma irin ta shugaban annabawa da manzanni gaba daya annabi sallallahu wasallama babban aikin su shine karantarwa to sai mutum yace malamin sa banza ne. To sai mai adua mu fita gurin mu barshi kai ya shafa mana. Bayan haka ya jama'a akwai wajabcin biyayya tsakanin na gaba da baya a tsarin musulunci ko babu? To kuma ka'idar shi na gaban gaba fa da gabanta. Duk yadda ka kai da daraja da girma to baza'a maka biyayya a hada kai da kai don a saba wa Allah mahalicci ba. Sannan kuma a haifi yaya maza da yaya mata a watsar da su watsa a dakin duniya ko a ce za'a dora su akan gargajiya Allah bai yarda da wannan ba. Da mun taba ganin abun mamaki wani mutum wai dansa ya zama dan izala sai aka zo aka ce yadda suka yi makwabtaka suka zo aka ce wane eh dannan naka ina gani yana so ya zama dan izala. Yace menene? Yace baka jin yadda yake yin kiran salla irin na Larabawa? Wai yana fitar da Wai a bakin su chan wai zai lalace. To da Allah ya taimaki wannan dattijo sai yace kai amma ko kun bani mamaki yaron nan kiriniya da ya taso da ita har gidan yan chache yayi ta zuwa baku taba zuwa kun yi mun kun ce mun ga yaro yana chache ko yana karta ba su zauna da karu wai suna yi a sawa wata ganye baku kawo kararsa ba sai yau da ya kiran salla abun da aka ce mai yin sa ranar tashi alkiyama zai tashi da wani kyakkyawan wuya dogo yace to ku tashi ku bani guri. In dai wannan shi da izala nima uban sa ma dan izala ne. To kaga za'a yi biyayya ne akan yadda shari'ar Allah ta ce. To ni ba tsawaita jawabi zanyi ba don naga lokaci yasa kai ainihin to amma abun da nake so da mu gaba daya ko matasa kun ga hadin kan nan ba ra'ayi bane. Allah tabaraka wa ta'ala ne yace Ku yi riko da igiyar Allah gaba daya. To ka san da yake al'qur'ani littafin Allah ne mai bayani. Wannan ance ma gaba daya sai ya sake tambaya kamar yaya kenan gaba daya? Allah yace Ko yanzu ma baka gane ba. Kar ku rarraba. Mu hadu akan igiyar Allah a daina musulunci, al'qur'ani, hadisan annabi sallallahu wasallama al'qur'anin da hadisin an aiko ne zuwa ga mutane manzon Allah sallallahu alaihi wasallama sannan Allah ya zaba masa bayin sa managarta sune suka zama diban fari suka amsa. To fahimtar da su na farkon suka yi baka isa ba yanzu kaga daga baya kace zaka rushe ta da gida dancinka. Saboda haka akwai bayani na fiqihun musulunci. Duk muna da wannan abu a zamanin nan wai sunan sa mai tatsine ne ko menene ko boko haram kawai. Sai mutum yazo yace maka qur'ani kawai ba ruwansa da sunna shi ba ruwansa da fasara. Ah ah qur'ani kawai ba ruwanka da fasara eh. To gaya mun ran nawa ga watan nawa da za'a saukar da al'qur'ani aka yi yekuwa cikin duniya a zo a taru a wani fili ga al'qur'ani nan daga sama kowa ya daka wawa ya dauka yaje gidan su. Babu akwai wanda aka aiko da shi wanene? Annabi Muhammadun ne sallallahu alaihi wasallama. Kuma Allah yace yayi bayanin al'qur'ani Daya daga cikin sunayen al'qur'ani akwai don kayi bayanin shi dinnan ka bayyana abun da aka sassaukar zuwa gare su su mutane cikin shekaru ashirin da biyu da wata biyu da kwana ashirin da biyu ko kuma wani kaulin a hade kawai a huta a ce cikin shekara ashirin da uku. Ka bayyana musu abun da aka sassaukar zuwa gare su. Shin ai bayanin da annabi sallallahu alaihi wasallama zai wa mutane shine a wannan ayar ko ba shi bane? Ayar tana cikin ayoyin al'qur'ani ko babu? Idan mutum ya karyata bayanin da annabi sallallahu alaihi wasallama zai yi na hadisi wanda wani yayi da bakin sa mai tsarki mai daraja wani yayi da aikin sa wanda yake na daidai wani yayi shi da tabbatarwar da yayi wa sahabbai wani yayi shi da irin kyawawan halayen sa na hakuri na fara'a na kaza aka dunkule gaba daya ya zama bayanin al'qur'ani yake mana. To sai wani yazo yace shi bayanin ne baya so. Shi dai gundarin al'qur'ani kawai zai dauka yaje yayi gaban kansa saboda haka in in in in kai wasa sai yace maka kai sallar juma'a karfe tara. In kai wasa sai yace maka mata tana haila zata kewaye ka'aba tayi dawafi in kai wasa tunda shi ba ruwansa da fasara ta hadisi shin za'a iya dauka al'qur'ani ba fasara hadisi a iya tafiya da al'qur'anin a gane akwai wanda aka aiko da al'qur'anin ya isar ko babu? Shine manzon Allah annabi sallallahu alaihi wasallama sannan kuma dole sai da fiqihu. Me misali? Yanzu kaga idan kace ya kaci qur'ani kawai baka yi daidai ba da sauran magana akwai hadisi qur'anin kuma shi ya tabbatar da al'qur'anin ya tabbatar da hadisin in ka dawo kace qur'ani hadisi kawai ba fiqihu nan ma baka yi daidai ba don qur'anin shi ya tabbatar da qur'anin ya tabbatar da hadisin ya tabbatar da fiqihu din. Kuma ga yadda zaka dada ganewa mun gane wanda suka ce al'qur'ani ba hadisi sun bata an gane wannan? To wanda suka ce al'qur'ani hadisi ba fiqihu suma sun bata. Ta yaya gashi jama'a in mun zo zamu yi salla cikin hadisan annabi sallallahu wasallama akwai wanda yayi magana akan kabbarar harama ko babu? Cikin hadisan annabi sallallahu wasallama akwai wanda yayi magana akan karatun fatiha ko babu? Cikin hadisan annabi sallallahu wasallama akwai wanda yayi magana akan amin bayan fatiha ko babu? Cikin hadisan annabi sallallahu wasallama akwai wanda yayi magana akan tahiya ko babu? Akwai to da kabbarar haramar da fatihar da fa dan amin bayan fatihar da tahiya din a hukuncin salla karfin su daya ko wani yana gaba da wani. Wani in ka karya shi sai an sake sallar wani in ka karya shi za'a iya yin qabliya a dora wani in kayi zarbabbia kai a ce kai ba'a diya ka dora wani in kayi sai a ce ah ah ba komai. Sallar ka tayi sai dai ranar tashi alkiyama in an tashi bada lada wayanda suka hada da hadda mustahabbin nan zasu fika samun gwagwaban lada a masallan tayi ko ba haka bane? To kaga a ina ake sanin farilla sunna mustahabbi kaza sai a fiqihu. To kace ba ruwanka da fiqihu to ba ruwanka da addini. Saboda haka kana iya yin sujada ba'a diya kenan in ka manta baka ce amin ba ko qabliya salla ka taba ce in kaga dama in ma baka ga dama ba don addinin ba naka bane. To saboda haka kafin in tsaya jama'a gaba daya mu mace tsoron Allah. Duk wanda tsoron Allah ya kubuce masa to yayi asara. Mubi sunnar manzon Allah sallallahu alaihi wasallama a ilmarce duk wanda yayi addini yace al'qur'ani kawai ba sunna baya da addini. Mu karanci fiqihun musulunci a gun malamai kar kayi malantar kanka da kanka. Allah zai tausaya mana ya sa muga irin hasken nan dayar wata irin ta musulunci muyi ta tafiya akan haske. Sannan daga karshe na baya yaga girman na gaba da matar da tace mijinta banza ne zata yi ta yawa a duniya don mutum ya gwada ya gwada yazo shine miji ta shake mar wuya in wani ya hakura wani fa ba hakura zai yi ba. Tunda yake akwai kofar aure akwai ta saki duk da cewa halaliya ce da Allah baya so wallahi wani in ya fusata sai ya latsa ido ya sauta. In ta koma ta sake marin wani sai ma sai a sake haka sai a dinga lissafin ta zauna gidan kaza ta dan ta wane yana gidan wance wata yana gida ina mata? Wallahi in dai ba kaddara ba a cikin yabo da suka to daya tafi karfi a jikin ta. Saboda haka mata su bi aure mu kuma mu rike su da amana. Maluma a daure wahala ayi karatu kar ayi karatun yan duniya. Karatun yan duniya shine karatu da ban aiki da ba shi wai wai wai malantar sa gyaran nahawu kawai. Sai Allah To lallai bai kamata a sa wannan yayi daidai amma ina amfanin mutum yazo yace waya ya fasalta ras baki ya jawo fasara ta jawo amma da ya kwanche kwanche sai ya ya rarraka karya sai da mutum suka rika ce waya fadi magana kace wane aka ce kai wannan mutum akwai mutumin banza. To ina karatun? Jama'a daga cikin abubuwan nan misali guda biyar da aka ce sai sun tabbata sun a ce wanda ya ruwaito hadisin yana da su ai akwai adalci. Makaryaci ma adali ne? To yanzu in kazo kace ka haddace hadisi dubu to karanta sai ka karanta a cikin ka'ida makaryaci ba'a cewa hadisin da ya karbo shi ingantacce ne ko ana fada a Yauwa to sai kace ka haddace hadisi kaza amma karya kai kai makaryacin garinku ne. Kai mayaudarin garinku ne, kai makwadaicin garinku ne, kai ragon garinku ne, kai mai ha'incin garinku ne to haddan nan taka sai fa a zauna muga irin su imamun malik sai yaje malami ya bashi hadisi yaki karba wani malamin in ya bashi kuma wannan hadisin sai ya karba a gurin wannan in ance menene ya ce wannan yayi da yaudara. Tunda mayaudari ne bazan karbi nasa ba wannan tunda ba mayaudari bane zan karbi nasa. Jama'a in muna son bin addini don Allah mu rike tauhidi da kyau duk abun da ya shafi shirka kar mu yarda da shi. Mu girma ma manzon Allah sallallahu wasallama da sahabban sa kuyi hankali da shi'a da duk wanda yayi kwanche kwanche ya kira sunan sa sayyidina Abubakar Siddiki ya zage shi. To ni ban ga ta inda za'a yi Allah ya ba bayin sa shaida wani yaje ya tinga ya rika zagin su yace kuma yaji ya gani ya ja ya ceke shi ma mai addini ne a ce wani addini yace na musulunci jama'a wani littafi Allah ya saukar wa manzon Allah annabi Muhammad sallallahu wasallama al'qur'anin kareem a ciki ne fa Allah yake cewa zuwa karshen aya. Marigaya wanda suka gabata diban fari na farko Allah ya ya yaba musu zai wuka kasa gane wa ya ce Sayyidina Abubakar yana cikin muhajirun ko ba wa yace? Shine na farko Sayyidina Umar fa Nana Aisha fa To Allah ya yaba musu mahaliccin kowa da komai wanda ya san komai ya san kowa hatta abun da muke sakawa a zo ciyar mu Allah ya sani A ce wanda yayi halitta bai san halittar ba waye mahaliccin? Allah ne ya san saka zuci sai ya ce to shi ya yarda da sahabbai yaddar Allah ta tabbata a gare su In ji wa? In ji Allah a ina? A al'qur'ani. Shin da wani zai ce shi wannan gurin ne ya karyata al'qur'ani to ai ya karyata duka. Ko ba haka ba? Saboda haka kun ga zagin sahabbai ba addini bane, zagin sahabbai ba musulunci bane, zagin sahabbai ba hanyar tsira bace duk farfagandar da dan shi'a zai zo ya maka in zai kwanta ko ya kwana a tsaye zubur yana salla to wannan soke abun da Allah ya yaba ya kassara shi. Saboda haka ko matasa Allah ya kara mana albarka gaba daya. Kashejin mu gaba daya kar wani ya zagi sahabi kar ya ma Hakanan da wanda suka biyo baya bi ihsanin da kyautata aiki aka bi sallan wayancan din insha Allahu hanni har malam har ku har mu. Allah ya nifa Saboda haka idan wayancan suna tsalle tsalle gefe ance ga kwazazzabo chan wanda ya zindima sai yayi tafiyar shekara saba'in yaje yaddara akan mashi. To kaga mutum yana ce shi yayi tsallan a bishi. Saboda haka muyi hankali da su hatsari ne. Kuma zaka iya ganewa wallahi daga cikin abun da in na tuna yana mun dadi. Wai iya kai ma in ka tuna yana maka dadi shine kowa an san mahaifi na. Kasan yafi wuyan sani mahaifi na. Yauwa ma'ana ina da uba na kara da mahaifin ka muna da mahaifan mu ko? Wato mahaifi kai darajar da Allah yasa yake daita dangane da da wallahi ta kai ta kawo Allah ya kiyaye Allah ya kiyaye Allah ya kiyaye Allah ya kiyaye da za'a ce ga mahaifin wane chan a juji yana tsince tsince yafi sauki da a ce baya da mahaifi. Ko bai fi ba? To kaga sai shi'a su zo su fito da mutane maza da mata kawai a layi. Kaga doki wawa yaro wawa
[Segment 5/6 | 01:20:00–01:40:00]
[Speaker seg5-spk:0]
ga mata, ga namiji. Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace Aka ce kai maulidi jama'a a haɗe. Aka ji aka aro aramba badujala a coci coci aka ce a buga kai hankalin kowa ma ya ya ya firgita mai ƙwaya ya ɗan yafa. Sannan goro ne ba ya da mata ko tuzuru ne aka ɗauko ƴan mata aka ce su hau tsinas su yawo. Wallahi akwai abun da ake nufi a koya musu na karya tarbiyya. Idan aka je aka sadu aka haife wani a wancan layi to waye baban sa? Wani yace a shi shine baban sa aka ce mai yace ai wa matar ya aure ta da safe ya saki ta sha biyu, wannan shine ya aure ta da magariba, wannan ya aure ta da asuba su uku ne suka kwana da ita ranar. To ɗan waye a cikin su? Ina tarbiyya? To mutum yanzu yana so ya kawo maka wata falsafa ya faɗɗa kai ya ku mata sa wallahi ku yi hankali. Kuma mu haɗa kai akan gaskiya mu haƙura da junan mu. Amma duk haƙurin da zamu yi fa ba abun mu shirki sallah. Domin shi da Allah ya riga ya saba. Abun da yasa kaji ina ce ahali suna da mu zo mu haɗa kai. Meye damuwa ta dan na zo makarantar ah malam Shehu Muhammadu Awwal ga sunan ta eh Darul Hadis. Ni kuma ga makaranta da jama'ar wai ƙamatus sunna ta kakkafa dukan muka koyi tauhidi, muka koyi sallah, muka koyi azumi, muka koyi zakka, shi a Zaria, ni a Jos eh wannan malam a Kano, meye zai cuce mu? Da fari da baƙi meye zai cuce mu? To amma sai wani mutum ya zo yace shi shehun sa fa To malam in shi ya haife ka kar ka bishi sallah. Dan baka da ita. Ya kafurta a tsakanin sarari kuma sun yi ta zagin mu wai dan me za'a daina bin ƴan ɗariƙu sallah. Aka ce kun zagi alƙur'ani kuma inji malamin su. Aka ce menene? Yace wai sun ce wai wai dan an ba daraja da tafi alƙur'ani can bakin sa wai shine aka ce ko kuma dan mutum yace shehun sa ma Allah ne. suka ce wai wai jahilci ne yasa. Allah mai hana kunya ran gaskiya. Sai ga malam Ɗahir Bauchi ƴan jarida sun sun tare shi suka ce ga wani yace ɗan ɗariƙa ɗan onku yace ya zagi Allah yace eh Inyass shi malam sai yace ai wannan kafiri ne. To kaga ya fara zama cikin almajirai. Sai sai ya sa ya sa aka rabi'u ƴan jarida suka je suka ce ga wani fa ya yi wa Allah jafa'i yace shehu Inyass yace ai wannan kafiri ne. To kaga ya zo shi ma ya cigaba cikin wanda ya kafirci ace kafiri shi ma ya faɗa. Sai ga malam Abdul Jabar yace kai yace su fa sun san abun da zurfi zurfi zurfi. Yace wannan da kaji ina ka toɓar nan a layi akwai masu sa shi a ɓoye. Yace to ya san yanda zai ce ya ku ƴan izala yace kuyi shiru abun ku. Yace shi zai fita ya bar ɗariƙa ya sai ta hujjoji ya ɗauki ɗariƙa da hujjoji da alƙur'ani da hadisi ya dalkake ɗariƙu yace tunda wannan ita ce ɗariƙa Allah ya tsine mata albarka. Abdul Jabbar ko ni na faɗa? Mu mun riga shi faɗa da daɗewa. Aka ce duk wanda ya zagi Allah ba ya da addini kafiri ne. Duk wanda yace gashin sa yafi na sa abban manzon Allah sallallahu alaihi wasallam aka ce rashin musulunci ne yasa shi faɗa. Duk wanda ya taro ƴa'yan mu musulmi ya kassara su irin abun da aka yi a jahar Kaduna a wani gari saboda sun mammana hoton shehi ne an hana su jin wa'azi an hana su koyan karatu da sauran su. An na guda basu kai 100 ba suka je suka tare babban gari sai da suka kori mutum 60 a mako. Sannan kuma samari majiya ƙarfi sai a zo a ce kwanta sai kwanta wa'annan sai a yanka sai a ce Sai wani ya sake kwanta kowanne shine maganin mutuwar uku. Jama'a shirka tana sa mutum shakka da tsoro da kokwanto da rashin gaskiya Allah ka nesanta mu da ga shirka kar ta shafe mu.
[Speaker seg5-spk:1]
Amin.
[Speaker seg5-spk:0]
Ka ƙarfafemu da tauhidi
[Speaker seg5-spk:1]
Amin.
[Speaker seg5-spk:0]
ba inda za'a je a samo tsaro ɗahir tun daga duniya har ƙabari har ranar tashi alƙiyama sai a tauhidi. Wanda suka yi imani basu gauraya imanin nasu da shirka ba. To wayancan sune suke da tsaro. Zaman aminci a duniya da cikin ƙabari da ranar tashi alƙiyama daraja da girma ta ɗore mana har gidan aljanna firdausi darhamar ubangijin mu. Kuma sune shirye yyo Allah ka samu na daga shirye yyo. To jama'a ina ganin nan ya kamata in duk duga aya da karanta wannan aya Ya ayyuhallazina amanu ya ku wanda suka bada gaskiya ya ku tsare dokokin Allah ya Allah dan Allah samari a kula da tauhidi dan Allah kuyi karatu. Dan Allah abu Allah abu manzon Allah sallallahu alaihi wasallam a ilmance ilimin shari'a. A girmama wa'yanda Allah ya girmama na daga sahaban annabi da tabi'ai da a daraja uwa da uba da wa da ƙani.
[Speaker seg5-spk:1]
Allah ya biya.
[Speaker seg5-spk:0]
Ayi adalci da tausayin maƙwabta mai wani abu na alheri dan Allah a taimaka wa mutane jama'ar mana wahala. An samu mukuwar gwamnati an cuce mu ƴan ƙwadayi sun ƙwashi kuɗi an jingada su za'a yanka uban su sun karɓi kuɗin haka. Za'a yanka uwar su sun karɓi kuɗin haka. Yau gashi nan kowa na cikin masifa. Allah ka bamu kyakkyawar mafita. Kai kowa yayi nazari ya duba me ya gabatar ne dan gobe ƙiyama in an zo awun aiki Allah ya ɗora a mizani mu haye kana da tauhidi kana sallah guda biyar cikin dare da yini akan ilimi kana zakka ga dukiyar da Allah ya baka kana aikin hajji kana kyauta kana sadaka kana kyautatawa mahaifin ka wanda zamu zo ranar tashi alƙiyama a ɗora a mizanin lada kana karatun al'ƙur'ani hadisi kana darajan maluman ka. Ashe ma duniyar nan ba a daɗewa ake ba ku ji duk shekarun duniyar nan ranar tashi alƙiyama sunan ta gobe ashe nan yini ne kawai. Ashe duniyar gaba ɗaya yini ce ba a kwana ba a duniya in an kwanan miliyan triliyan to Allah ya kira ta gaba ɗaya gobe ranar ƙiyama Ina hanyar fita Allah yace Ku ji tsoron Allah kuma kar ku kuskura ku bi ta ƴan duniya wanda suka manta da Allah ana ce ku zo mu haɗa akan aikin Allah suna ce sai sun ga dama ko kuma ana ce ku zo mu haɗu mu haɗe ƙwadayi mu gina ƙasar mu mu gina ilimi suna ce su ko kafiri ko wanene in ya basu kuɗi za su ci in an so a mutu to mugun fatan ku ya koma kanku ya koma sharrin ta. Saboda haka kar ku zamanto kaman wanda suka manta da kansu. Sai Allah ya mantar da su kawunan su yanzu fisabilillahi in ba wanda ya manta da kansa ba ace wai kai me maka darasi a university kafiri me maka allura a asibiti kafiri me siyar maka da buro da a gari kafiri me siyar muku da kayan tayar mota kafiri wanda za su yi muku aikin nasu kafiri sannan ƴan tsiraru mu gamu da yawa ga kyan hali ga ƙarfi bamu karace da giya ko shan kayan maye ba wai ma wa'yansu sun ɗaure wa mutane ƙwaƙwalwa wai sai zai a zuba wa kafirai ido wai su zo su yi kai samari kowa ya je ya shiga makaranta ku je kuyi aiki. Kar kuyi sata kar kuyi caca kar kuyi zina kar kuyi damfara kar ku bi ƴan duniya mu tare mu ba Allah Allah zai rufa mana asiri zai fitar da mu daga wannan mugun muguwar matsayi. Allah ka tausaya mana wa'yancan sune marasa ɗa a fasikai. Wallahi tallahi rashin ɗa'a ya kassara wasu. Da na gari da mugu dai daban. In kaine sarkin mahaukata dai da na gari da mugu daban. Da ɓarawo da liman daban. Ko in maka bayani wani mahaukaci a kwan fan ya fito yana fasa mutane sai wani malam Muhammadu Kwako eh malam Muhammadu Dakwal yana tafiya da mashin ɗin sa sai ga malam Muhammadu Dakwal yayi shiga irin ta musulunci da riga wando sa da yana fasa mutane ana gudu da ya zo wajen malam Muhammadu sai yace Allah ya gafarta malam. To kaga da na gari da mugu da banbanci to wallahi da mai tauhidi da mushirki daban. Wallahi da fasiki da salihin bawa daban. Wallahi da mata aure da karuwa daban. Ko ba banbanci? To gurin kyau ɗin nan na imani na tauhidi na aikin yi na halaliya na biyayya na gaskiya na riƙon amana aikin aljanna ne Allah ka tabbatar mana da shi Allah ka shigar da mu aljanna ka ta firdausi da rahama. To kun ga shirka shakka sata zina liwaɗi shiga ƙungiyoyin kultuzim na asiri tsafun turawa da suka kawo to ya kassara wa'yan su wanda ya bi hanyar su ya zama ɗan wuta Allah ya tsare mu. Amma ƙofa tuba fa fa tana nan a buɗe da ba ta buɗe fa fa roma ya tuba. Jama'a ba fa roma ya tuba wai tunda an riga an an faɗa sai naga kuma ni in yadda da ya tuba ya musulmin tan yafi wahatta fa fa roma amfani. Da wanda yace a a ina nan ina kafirci da ni da nace na ji wai ya tuba ya tuba to magana ta tafi wa fa fa roma amfani da mai cewa har yanzu yana kafirci ko ko duk ɗaya ne Allah ya sa ya tuba. Kuma manya manyan kiristoci da suke tuba saboda rashin gaskiyar da yake ciki wanda a ƙasashen Turai sai da aka yi ta yi wa coci coci tara har shekarar jiya waccan ma an fita a labarai an ɗaga wa'yansu coci coci an an an yi musu tara dala miliyan kaza za su biya dan sun yi fiyaɗe sun yi liwaɗi to kar wani ya shiga liwaɗi in za'a tara maka jifa jifan ƙasar nan a baka kar ka kwanta wani yayi liwaɗi da kai wo. Kuna ji? Da na gari da mugu daban. Da ɗan wuta da ɗan aljanna daban. Inda alheri yake a wajen ƴan aljanna Allah ya sa da mu a cikin su. Ƴan aljanna sune masu samun babban rabo Allah ka bamu.
[Speaker seg5-spk:2]
Ashe Muhammadu Sani Hayan Allah ya saka da alkhairi. To jama'a kamar yadda malam ya faɗi babu shakka malam yayi mana nasiha. Mun ji ma'anar nasiha ga Allah nasiha ga shugabannin musulmi nasiha ga littafin Allah nasiha ga manzon Allah mun ji malam ya fassara mana wannan abu malam Allah ya saka da alkhairi. Ba shakka al'amarin ya wuce yadda malam yace jawabi mu nan daru sa muka ɗauka masu ɗin bin yawa ƙwarai da gaske. Kuma karatu ne wanda yake ba yanzu ba zai zama guzuri har zuwa numfashin mu na ƙarshe. Muna fatan ya amfanar da mu har zuwa ranar da zamu tashi gaban mahalli cii. Saboda mun san malam akwai harƙoki da yawa ƙwarai da gaske a cikin ido aka yi tsawuriya wato a yanayin wancin lokaci aka ɗauri aka bamu wannan awanni. Domin su malam sun taso tun ƙarfe shida kuma yanzu ɗin na da ƙi ne mun an tafi fa ba za'a tafi ne a kwanta ba akwai wasu harƙokin. Muna roƙon su malam a cikin wannan a ɗan yi mana uzuri akwai wani babban baƙon da muka yi daga Zafara ya ɗan yi mana ta'aliƙi minti biyar zuwa minti goma. Shine Malam mun bada minti biyar zuwa minti goma ayi haƙuri malam. Insha Allahu
[Speaker seg5-spk:0]
Gaban malam
[Segment 6/6 | 01:40:00–end]
[Speaker seg6-spk:0]
Kuma sahabban da dama sun ga sabani. Har shi maruwayi ce wannan hadisi Domin ya rayu Har hijirar annabi ta kai 70 ko a 56 Sannan ya rasu. Hijirar annabi na 57 Haddasuwar ko wa'innan sabani wannan sabani da annabi ya fadi da wa'innan bambance bambance a cikin musulmi ya fara faruwa ne tun hijira na 31 Ba hijirar annabi Daga nan aka fara samun sabani nan da annabi ya fada. Sai ga khawarij Sun bayyana kadariyya murji'a jabriyya har zuwa sauran kungiyoyi na bata Har ka dinga dai da dari kun sufaye Duk suka zo suka bayyana sabon nan daidai kunsu kamar shi da irin irin duk sun shaidi bayyanar wa'innan kungiyoyi na bata da annabi yace duk wanda ya rayu a cikin ku zai gansu. Kaga annabi ya riga ya yi hukunci yace wa'innan kungiyoyin gaba daya na bata ne. Kuma dukansu fa suna karbar sunan musulunci Amma yace na bata ne. Sai ya fadi wa'inda suke kan shari'a Sai yace Wannan shine dalilin na farko da ke nuna ku ke kan gaskiya. Dalilin na biyu shima hadisi ne mashahuri Mai ruwayoyi daban daban hadisin mu'awiya Ibn abi sufyan Kawun muminai Allah ya kara masa yadda Da manzon Allah ke cewa Wannan ishara ce ga Annabi yace duk yadda zamani ya kai ya kawo za'a samu wasu jama'a kan gaskiya Wanda sune Sai kuma hadisin Shima mashahuri ne Hadisin da manzon Allah yace Yahuda sun kasu su kashe 73 Da daya Nasara sun kasu su kashe 72 Sai kuma ya dawo yace Kuma ummati yace Al'ummar su suka karba suka karbi da'awarsa Amma yace dukansu 'yan wuta ne. Yace sai daya A cikin ruwaya ingantatta Wadda zo ta hanyoyi daban daban Ta kuma inganta akan zuwanta ta wa'innan hanyoyi. Annabi da sahabbai suka tambaye shi Su wanene zasu tsira? Sai yace Wa'inda suke kan abinda nike kai yau ni da sahabbai na. Don haka Wa'innan dalilai ne a takaice da ke tabbatar da cewa ku kadai ne akan gaskiya. Domin zaka ga Akidarsu Ibadarsu Sulukinsu Manhajinsu na da'awa Duk yana dugaro ne da al'kur'ani da sunna akan fahimtar magabata. Duk kungiyoyin bata ba wanda ke kan wannan Al'ummar sunna kadai suke kan kur'ani sunna kan fahimtar magabata. In ba al'ummar sunna ba duk firaku ba wanda ke kan wannan. Don haka albishirin ku Ku kadai ne akan gaskiya. Abu na biyu Soyayya ta hakika a cikin ku take. Taron yau babban misali. Soyayya ta hakika a cikin al'ummar sunna take. Misali taron yau. Naji dadi nayi farin ciki Da Allah ramma Ya bude wannan taro Da aya Daga cikin suratul maryam inda Allah ke cewa Sai na girgiza ma Allah ramma nace Allah maka albarka. Ka bude taro Da aya da ta hada taro. Allah yace hakika wanda suka yi imani suka aikata aiki na gari Allah zai sanya soyayya A tsakanin su. Babu soyayya tsakanin yahudawa Ba soyayya ta hakika tsakanin kiristoci Babu soyayya ta hakika a wajen 'yan shi'a Babu ta a cikin dukkan dari kun sufaye. Soyayya ta hakika Tana cikin al'ummar sunna. Sune zaka ga Ko da an ware Anyi dambe Ko an share fili anyi kokuwa An nuni juna An shammaci juna An jima kadan zaka kuma zaka samu wasu rungume juna suna son juna suna kaunar juna. Domin abu daya ne ya hada su. Na kasan nan ne ko na waje ne. Don haka soyayya ta hakika tana cikin al'ummar sunna. Wanda Allah ya tabbatar da wannan a cikin al'kur'ani mai girma inda Allah ke cewa Toh wannan yace soyayya ta hakika wanda ga alama ta kun gani. Malam ya tashi daga zaria Yaji ya kai gaisuwar barin girma Da girmamawa Da malamin mu Kuma lokaci daya ga yau malamin mu shima yazo ya mai da buki. Allah ya saka masa da alkhairi. Abu na karshe Al'ummar sunna An fa yi taron dangi a kanku. Duk wani abu da ake fadi kan musulmi A ce 'yan ta'adda ne 'yan ta da zaune tsaye ne 'yan zafin addini ne 'yan kaza ne gida dawa ne wanene wallahi wallahi ba'a nufin kowa a duniya sai al'ummar sunna. Mu kadai ake nufi da wa'innan sunayen. Yahudawa sun sa ido akan mu Sun dauki matakin karya mu kiristoci haka shi'a haka dari kun sufaye duka haka. To kada ku manta da wannan 'yan uwa al'ummar sunna. Kuyi hakuri da junanku. Kada ku sanya kiyayya da adawa akan matsalolin da basu kai a sa kiyayya da adawa akan su ba. Ku tausayawa wa junanku. Al'ummar sunna Toh wannan yace sai ku faku. Kunsan gaskiya kuma kuna da tausayi. Tausayin al'ummar sunna bai tsaya ga kansu kadai ba. Tausayinsu ya hada kowa. Don muna kiran yahudawa zuwa ga addinin musulunci Muna kiran kiristoci zuwa ga addinin musulunci muna kiran shi'a zuwa ga sunna muna kiran dari kun sufaye zuwa ga sunna don haka muna tausayinsu. Malam ya bada wani misali kamar da papa roma Wanda ke nuna hakikanin wannan maganar da na fada. Magana yaji amma yace yana batar Abinda yake zato ya zama shine domin shi zai amfani papa roma. To wannan shine na al'ummar sunna. Sun san gaskiya kuma suna da tausayi. Sannan a karshe malam yayi maganganu masu tarin yawa Wanda ke nuna ilimi Da hikima Da kwarewa A cikin wannan fanni a cikin wannan kuma addini. Yayi ishara akan ladabi da biyayya Ga dalibai zuwa ga malamai Wanda wannan wani abu ne mai muhimmancin gaske. Kuma ya kamata a ce an kula da shi. Wajibin mu mu tuntu malaman mu Ko ba dam komai ba Don sunna da suka dora mu akan ta. Wannan kadai ya isa mu mutunta su mu girma ma su. Jiya jiya Ina jiya su gidan malam Bayan sallar La'asar malam yayi taro Da mutane kusan awa biyu ko uku Yana sallar la'asar sai ya koma ya ya kwanta. Na samu wa'innan 'yan uwa Suka karbe mu suka karbi sakon mu da muka zo da shi Daga jahar zamfara zuwa ga malam. To abinda ya ban mamaki Sai nace musu don Allah kuyi hakuri zamu tafi. Suka ce abu zaku tafi fa Sai mun karrama ku. Suka dubi hadisin da annabi ke cewa Sai zaka ce mun baku wani abun sha Ko wani abinci ko da a hannu ne ku rike ku tafi da shi. Abu na biyu malam bazai ji dadi ba ace ba'a kinsu sun zo gidansu basu ci komai basu sha komai ba. To sai naga abinda da malam ya fadi Na dalibai su girma malamai malam ya tarbiyyar dalibai shi akan wannan. Kuma da'awar izala tun farkonta har zuwa yau wannan wani abu ne sannan ne a ciki. Umarni da girma ma na sama. To ina fata Allah madaukakin sarki ya sanya ma malam albarka ya kuma sanya wa al'ummar sunna albarka. A karshe Allah gafarta malam zanyi amfani da wannan dama Muyi hakuri da junan mu Wannan haduwar Muyi hakuri da ita ta dore domin dama ita siffar mu ce. Dama siffar haduwa siffar mu ce. Abinda 'yan uwa brothers muslim brothers suke magana ikhwanul muslimun hadin kai hadin kai duk karya ce. Ya za'ayi hadin kai da dan shi'a Kuma ace kar ace masa shi'a ba kyau. Ya za'a hada kai da dari kun sufaye kuma ace ayi shiru kar ace dari kun sufaye ba kyau. Kuma a ce wannan tafiyar kuma al'ummar sunna ya taho a cikin ta kuma a ce wai sunan tafiyar hadin kan musulmi. Ai kaga wannan yaudara ce. Da Allah yace ayi hadin kai ai sai da ya fadi akan me za'a hada kan. Aya da malam ya ja Allah bai cika hada kai ba sai yace Da yazo kuma wata aya yace sai yace Kaga kenan bai bar abun a bude ba don haka nike shawarar kalmar da ke fito a bakin malam ko ina a wajen wa'azi yana cewa a hada kai akan gaskiya. Toh wannan hadin kai a cikin al'ummar sunna kawai yake. Don haka kungiyoyin bata kap Muna kiran su zuwa ga wannan tafarki na sunna. 'Yan suka zo akan wannan tafarki toh lokaci ne muka hada kai da su. Muna kuma kiran yahudawa da kiristoci kap zo shiga musulunci. Dari kun bata dinnan kap muna kiran su dawo Akan wannan tafarki domin shine tafarkin gaskiya.
[Speaker seg6-spk:1]
Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu. A sheikh sa'idu mai kwano daga gusau Allah ya saka da alkhairi jama'a taro yayi taro. Malam daga cikin kwazon da 'ya'yan ku Almajiranku dalibanku suke a wannan makaranta Domin tabbatar da wadancan abubuwa Babu shakka ranku ya kara fari. Da'awarsu ta kafi kwarai da gaske. Matasa suna kwazo kwarai da gaske akan duk wa'innan abubuwa. Akwai matasa wadanda suka zage har da kur'ani suke zalla a makarantar nan Maza akwai mata. Akwai wadanda suke 'yan haya islam mai zalla wato 'yan arabiyya da dirasa islamiyya. Akwai wadanda suke zallansu 'yan boko ne amma kuma suna ta fita tare da karatun al'kur'ani da hadisi wa'innan scientist ne cikin su ake fatan a samu da kuma da sauran Sannan a makarantar nan Babu shakka kamar yadda muke cewa Kamar yadda malam ya fadi yayi tafassara maganganun nan na haka. Babu mujamala dangane da duk wani mai yin shirka Ko bidi'a Ko kuma wani wanda ya bayyana kiyayya shiga sahabban annabi Kowa ya san mu akan haka. Kasantuwar irin nasihohin nan da malam yayi muka lura ba shakka matasan al'ummar sunna Kar a barsu a baya a duniyar mutunta wadanda suka gabata wajen yi wa wannan addini hidima. Makarantar nan akwai wani project akwai wata harka wata gudunmawa wadda muke wa da'awar da dan fodiyo yayi. Littafin da dan fodiyo ya ainihin rubuta da shi da ainihin da yawa daga 'ya'yan shi su muhammadu bello da 'yan uwanshi su malam abdullahi da nana asma'u da makamantansu. A makarantar nan muna nan muna aikin Tace su da rubuce su a bisa tsari na computer wanda zamu dora su akan internet kuma a buga su a irin bugu yadda ainihin suke tare da wasulun su. A makarantar nan muna nan muna wannan aiki wanda zuwa yanzu mun kai kusan littafi na 120 Wadanda za'a iya buga su ko yaushe daga yanzu dinnan amma saboda ana ci gaba da aikin muka ga a kara hakuri insha Allahu. Sannan akwai karatun da ta san fikihu wadanda da dama muna ganin matasa da basu yi karatun suru a irin yadda karatun da'a aikin nan ba. Aka samu kuma dayawa ana kya maryam zuwa a shiga suran saboda gaskiya wasu surayen 'yan bidi'a ne. Kaje garin akwai a maka kawa'idi su dora maka ka'ida ta shirka. To alhamdullilahi sai muka zo muka karar da karatun wa'innan littattafai a wannan wuri matasan nan wallahi sun bada goyon baya malam. Da safe ake karatun askari a makarantar nan malam sai ayi awa biyu tashi sannan a zo a sake karatun risala haka sannan karatun dukkan ahaliri ishmawi su kuma ayi su da daddare. Matasan nan sun bada kwazo kwarai da gaske akan haka. Saboda haka gaskiya malam biyayyar nan da malam yake ta magana To matasan nan gaskiya sun bada goyon baya kwarai da gaske kuma suna yin ta don haka muna rokon a cikin addu'i da malam zai mana na rufe wannan majlisi ayi wa matasan nan addu'a Allah ya saka musu da alkhairi. Domin wa'azo zin da kuke ta yi na biyayyar nan muna gani a aikace a wurin su kuma Allah ya kara rike mana wannan yanayi. Kuma kamar yadda nake fadi Wallahi na fadi wannan magana ina jin kusan shekaru 20 da su gaba ta kuma nayi ta fadin ta. Ba'a kafa wata kungiya Wanda ainihin ta yi wa addini hidima ko aka samu wani mutum guda da yayi wa addinin nan hidima tun daga gushewar su dan fodiyo har zuwa wannan zamanin kamar kungiyar Kuma dukkanin wani matashi ko ya yadda yana cikin kungiya ko bai yadda yana cikin kungiya ba matukar ya yadda da shi ahalin sunna ne ya san wannan gaskiya ce baya ja a Kuma kuna da girma a idanun matasan nan malam. Kuma yadda ku kuka tashi su malam abubakar gumis sune malaman ku da kuka zauna gaban su Su a sheikh ismaila idris sune malaman ku da kuka zauna gaban su matasan nan haka suke kallon ku malam. Haka suke mutunta ku haka suke daraja ku don haka muna fatan malam kamar yadda wa'innan malaman suka rike mana amana muka tashi muka gansu a hade Tare da cewa bazai yu a rasa wasu abubuwa a tsakanin su ba amma dai suka hakura. Kowa ya san cewa in za'a ce Wato dalibi mai biyayya takat to za'a sa malam ismaila idris a ciki. To amma duk da haka dai mun tashi munga a hade suke har suka rasu bamu taba jin wani abu tsakanin su ba in ma akwai mu bamu sani ba. Malam kuma ku kara hakuri haka wa'innan matasan Allah ya sa su zo su shigo sahu su samu tsintsiya madaurin ki daya. Malam Allah ya saka muku da alkhairi. Za mu takaita a nan kuma malam muna fatan a kara mana addu'a. Malaman nan namu na zaria Malam a kara musu addu'a. Duk abinda ake sunyi Kuma suna yi kuma muna da yakinin zasu cigaba da yi. Basubar ahalin sunna sun tagayyara game da wani fanni na ilimi ba. Basuyi wa ahalin sunna rowar wani abu da suke bukata na ilimi ko tarbiyya ba. Don haka gaskiya malam ayi wa daliban addu'a sannan ayi wa malaman mu addu'a Allah ya saka da alkhairi. Jama'ar musulmi gaba daya muna fatan Allah ya saka muku da alkhairi. Zamu mika abun magana karshe a hannun malam malam ya cike mana da addu'a. Allah madaukakin sarki ya saka da alkhairi Ya ubangiji mahaliccin Allah mai tsarkakan sarauta da daukaka mahaliccin mu mai cikekken iko ya madogaran masu imani abun bauta mu da gaskiya. Allah tabaraka wa ta'ala muna ta walo da Allah madaukakin sarki muna rokon ka Allah ka raya mu akan imani da musulunci Allah ka karbi rayuwar mu muna muminai musulmi Allah ka shigar da mu gidan aljanna ka tafir dausi da rahamar ka. Allah ka rinja da mu akan kafirai da fasikai da munafukai Allah ka dawo mana da lafiya da zaman lafiya da amana cikin wannan daula ta nigeria da kuma dauloli na musulunci. Allah ka tsare mana maka da madina ka taimake su wajen abubuwa da suke na daga addini. Kuma da mu da su duk wani abunda ya shafi kuskure na dan adam Allah ka yafe mana. Ubangiji yadda muka zo muka samu wannan makaranta da alkhairi da albarka da kuma hadin kai da son juna kamar yadda wannan babban malamin mu da yayi mana jawabi ya dauko mana manyan na kudodi ya dada faranta mana rai da shi. Ubangiji Allah ya saka wa maluman da alkhairi ya saka wa daliban da alkhairi ya saka wa masu sauraran mu kusan ko nesa da alkhairi. Wannan makaranta Allah ya kara mata albarka ya kara mata karfi da hadin kai akan gaskiya. Alkhairin duniya da alkhairin lahira Allah ka sa damu da shi. Duk Na biyu ranar lahadi mai zuwa ranar ce Akwai wa'azi wanda malam sa'idu zai zo zai mana anan karfe goma na safe don haka don Allah muna amfani da wannan a musanyin hanyar sallawa don Allah malam don Allah jama'a kowa ya saurara sannan don Allah kayi yadda ake ta tarbiyyar kar wani yace sai ya shafi rigar malam a sheikh Gaskiya gaskiya Allah Allah ya saka maka da alkhairi. Allah Allah ya saka da alkhairi. Eh nagode Allah ya saka.Annotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Ziyarar Shugaban Malamai na Izalah. Daarul Hadeethis Salafiyyah, 17 mars 2013. DVD. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15879.
Zaria, M. A. A. (2013, 17 mars). Ziyarar Shugaban Malamai na Izalah [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15879
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Ziyarar Shugaban Malamai na Izalah. Daarul Hadeethis Salafiyyah, 17 mars 2013. DVD. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15879.
Télécharger
Visualisations
Chargement des visualisations…


