document audiovisuel · Daarul Hadeethis Salafiyyah Citer
Karatuttukan Karshe a Ranar da Aka Kashe Shaykh Albaniy Zaria (Dariqus-salihin 1, Muslim 172, Bukhaariy 308)
- Type
- Enregistrement vidéo
- Créateur
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Editeur
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- numéro
- 1
- 2
- 3
- Est une partie de
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Importance matérielle
- 198 minutes
- Support
- DVD
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000022
- contenu
-
============================================================
[Part 1]
============================================================
[Segment 1/6 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yanzu da muke magana Yammacin ranar asabar ce da ta daidai da Daya ga watan Rabi'un Thani hijra na da shekara dubu daya da dari hudu da talatin da biyar. Daidai da daya ga watan February shekara ta dubu biyu da sha hudu. Wannan shine kasan na dari da sabain da biyu daga cikin jerin giyar karatuttukan littafin Sahih Muslim. Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi. Karatun da mukai wata ke da karatun hadisi da aiki da shi shine zama lafiya ga musulmi. Idan jama'a basu manta ba muna cikin Kitabul Iman. Wato matattarar da Al Imamu Muslim yake taro mana hadisan Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama dangane da imani. Yana fassara mana shi. Yana fada mana nau'uka da rassan imani. Abubuwan da ke warware imani da kuma abubuwan da ke kara imani da abubuwan da suke raunata shi ko su rage shi. To sa'annan Yana kawo mana hadisai har wayo wadanda suke bayyana falala daga cikin falalolin imani. A inda muke karkashin babu bayani Babin da ke bayanin Daga cikin yan aljanna Wanene yafi kowa karamar daraja A cikin aljanna. Al Imam Muslim ya kawo mana hadisai wadanda daga cikin wadannan hadisan Munji wani hadisi wanda yana tabbatar da Wanda daga cikin yan aljanna yafi kowa kasan matsayi. Sannan kumaLire le texte intégral — 25 905 mots restants Réduire le texte intégral
hadisin ya tabbatar mana da cewa za'a samu wasu muminai da suka rasu da zunubai. Basu tuba ba kuma Allah bai nufe su da rahma ba. In suka shiga cikin wuta Allah madaukakin sarki zai cece su saboda imaninsu Shi da kanshi. Ko yasa mala'iku ko salihai ko annabawa su cece su. Hadisin karshe da muka kwana akai hadisi ne wanda yake dauke da mas'aloli masu yawa wadanda suka shafi akida Da manhajin karantar da akida da kuma manhajin yada ta. Da kuma bayani akan wasu bidi'o'i da irin tafarkin da ake bi wajen raddin wadannan bidi'o'in. Wannan hadisin shine hadisin Al Imamu Hajjaju Ibnu Sha'ir wanda Muslim ya rawaito shi a lamba Ta ainihin wato dari hudu Da talatin. Haka yake a naku? A naku dari hudu da sabain Da biyu. Dama mun tattauna tun a muqaddimar littafin game da lambobi na fa'adu Abdul Baqi wanda malam Muhammad Ali Adam ya tattauna a kansu. Wannan hadisin ya samo shi ta hanyar malamin shi shi Al Imam Muslim Al Imamu Hajjaju Ibnu Yusuf wanda yafi shahara da Hajjaju Ibnu Sha'ir. Shi ko ya karbo hadisi ne daga Al Imamu Fadlu Ibnu Dukaini. Fadlu Ibnu Dukaini shi ko ya karbo hadisin daga Al Imamu Abi Asim. Wato Muhammad Ibnu Ayyub. Shi ko yake cewa malamin shi mai suna Yazidu Al Fatiir daya daga cikin tabi'ai. Ya bashi labarin cewa Wani ra'ayi daga cikin ra'ayin khawarijawa ya burge shi. Mun bayyana Khawarijawa Wasu mutane ne wadanda suka fara bayyana tun Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama yana da rai. Sai dai karfin bayyanar su Yafi daga lokacin karshen Sayyidina Usman zuwa har zamanin Sayyidina Ali Allah ya kara musu yarda baki daya. A inda su suka je suka azazzalo wuta Da fitina wadda aka kashe Sayyidina Usman a karkashin ta. Suka zo suka cigaba da azazzala wuta Wadda a karkashin ta ta ci Sayyidina Ali Da sauran wasu manyan malaman sahabbai. Babbar akidar su shine suna ganin duk mutumin da ya sabawa Allah To wannan mutum ya halatta iya kafirta shi ko da sabon Allah bai kai ga kafirci ba. To ba kafir tashi kadai ba Har da hukunta lazimta kafir tashi din cewa wato tunda ya kafirta To ya yarda. Don haka ya halatta a kashe shi. Sannan ya halatta a halatta dukiyar shi da duk wani abu nashi a matsayin kafiri. Wadannan sune khawarijawa tauni bangaren. Tauni bangaren suna halatta tawa ye ga khulafa'u shugabanni na ainihin musulmi. An kira su khawarijawa saboda wannan. Ko kuma Al Umman musulmi suna zaune khawarijawa suna iya kafir ta su. So afka musu suyi ta halatta jinanan su. Wadannan sune khawarijawa. Idan aka dube su a irin wadannan zamunan Khawarijawa akidar su ta yaya du kuma ta bazu a fannoni da dama Daga cikin nau'ukan kungiyoyin matasa a wannan zamanin. To a wannan zamanin Wannan mutum mai suna Yazidu Al Faqiri yace a matsayin shi na matashi Ustazu mai neman ilimi Sai wasu ra'ayoyi na khawarijawa suka burge shi. Sai ya je ya shiga cikin su Suka kudurce cewa Zasu kai hari cikin wasu garuruwa Su je su karkashe mutane Su kona kasuwanni Su je faffama bamai ga wasu wurare. Suka tafi cikin taron jama'a wadanda yake Daga goma zuwa arba'in. Amma sai suka ce bara abunda zasu je bara su je suyi aikin hajji tukunna. In suka gama aikin hajji to sai suzo sai su afka wa mutane. Da suka taso sai suka biyo ta Madina. Sai sukai ka cibis da wani babban malamin hadisi cikin malaman hadisi na sahaban Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam Sahabi Jabiru dan Abdullahi Allah ya kara mishi yarda. Ya tara mutane a masallacin manzon Allah yana karantar da su yana jingine da wata dirka daga cikin dirkokin masallacin. Da wa'azi yayi wa'azi Har wa'azi ya kawo bayanin wasu musulmi wadanda zasu samu kansu a wutar jahannama saboda wasu sabon Allah. A cikin wa'azin shi kuma ya bayyana cewa wadannan musulmin Daga baya Allah madaukakin sarki zai cire su Bayan ya azabtar da su da gwargwadon zunuban su saboda zunuban basu kai shirka ba. Wannan mutum mai suna Yazid yace ya zauna Yana cikin sauraren wa'azin nan sai yaji to wannan yayi karo da irin ra'ayoyin da su aka gina su akai na khawarijawa cewa mai zunubi In ya shiga wuta Zai zauna a cikin ta dindin dindin ya zama kafiri. To sai kuma yaji wannan sahabi yana cewa za'a cire irin wadannan muminai daga wuta Da gwargwadon azabar da akai musu. Sai yace haba Malam ka lura da irin wadannan hadisai da kake jawowa. Wadannan hadisan sun sabawa Qur'ani. Domin Qur'ani cewa yake Ya Allah duk wanda ka shigar da shi wuta Ka kaskantar da shi. To kuma ka'ida Qur'anituna cewa Wanda duk Allah ya wulakanta shi babu wani wanda zai karrama shi. To yanzu malam mutumin da Allah ya kai shi wuta kuma kace Allah ya wulakanta shi ya kaskantar da shi kuma kace wai zai fito Wannan hadisi na haka ya sabawa ayar Qur'ani don haka baza'a dauki hadisin ka ba Aya za'a dauka. Ya cigaba da cewa kuma malam Jabiru ka tsaya fa kaji Allah yana cewa Yan wuta duk sanda suka yi yunkurin fita daga wuta sai a sake komar da su. To yanzu malam wadanne irin hadisai ne wadannan zaka rinka wa mutane wa'azi da su bayan sun sabawa aya Al Qur'ani. Jabiru yace kai ya natsu Ka iya karatun Qur'ani yace kwarai. Ka kuma sauke Qur'ani gaba daya yace kwarai. Ka kai inda Allah yake bayanin cewa Annabi yana da wani matsayi abun yabawa Da Allah madaukakin sarki yake cewa zai tashe shi akan wannan matsayi a ranar alkiyama Karatun ka ya kai wannan wuri? Da Allah yace wa Annabi da daddare ya tashi ya rinka yin nafilfili ya rinka yin salloli. Allah zai tashe shi wani matsayi abun yabo wanda sai kowa ya yaba mishi. Ka kai wannan wurin yace kwarai. Yace to wannan matsayin abun yabawa Shine matsayin da Allah zai baiwa Annabi ya shiga gidan wuta ya je ya rinka fito da musulmi wadanda tsautsayin zunubai suka kai su. To me zaka ce? Ai wannan ma aya ce ta Al Qur'ani. Jabiru wannan irin tattaunawa tai tattaunawa ya tsaya ya fayyace wa wadannan wannan matashi a tsanaki Har wannan matashi ya fahimci ashe wadannan ayoyin Ayoyi ne da suka sauka akan kafirai. Kafirai ne Allah madaukakin sarki yake cewa Wanda duk Allah madaukakin sarki Ka shigar da shi wuta to ka gama kaskantar shi don haka da kafirai Allah yake. Sannan duk lokacin da sukai kokarin fitowa daga wuta Sai a mayar da su. Jabiru yace karanto kafin wannan ayar Sannan karanta ayoyin da suka zo bayan ta. Bayan da wannan matashi yaji wannan wa'azi da wannan jawabi sai hankalin shi ya kwanta. Shi yanzu ya fahimta ashe abunda suke akai kuskure ne. Musulmi baya kafirta sai in kafirci yayi. Kuma kafircin ma yana da sharuda da ka'idoji kafin a rarraba mishi shi don asali yanzu shi musulmi ne. To ba'a kafir tar da musulmi sai da dalili na kafir tashi balle ya halatta jinin shi da dukiyar shi. To amma ya zai yi da sauran abokan shi wadanda kungiyar su daya Sai je ya same su. Da ya same su yace to ni fa gaskiya na gamsu da wannan wa'azin. Suka ce ka gamsu yace ya gamsu. Ashe akan kuskure muke ba daidai muke ba. Sai yace kuna ganin wannan dattijon don a lokacin Jabiru ya zama dattijo ne. Wannan dattijon zai wa manzon Allah karya? Suka ce a'a. Yace to kunga wannan ra'ayin mu barshi. Domin wadannan sune almajiran manzon Allah. Abun duk da suke akai shine manzon Allah yake akai. Kuma sannan kunga wannan malamin ya nuna mana yadda ake fahimtar Qur'ani. Ashe ba'a ciro aya kwaya daya a tsakiya ayoyi. Sai an dibo ayoyin da ke kafin ta da ayoyin da ke bayan ta a hada a fassara. Saboda haka ni dai na tuba sai suka ce suma sun tuba. Sai rage saura kwaya daya shi ya taurin kai. Yace shi yana nan akan wannan akidar. Haka abu ya faru kuwa Ya zama cikin wadannan khawarijawa wadanda suka je suka fito Suka buga da sahaban Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama sahabbai suka kashe su. Munji irin wannan ainihin ya faru ga Sayyidina Jabiru Allah ya kara mishi yarda. Da wani matashin ma mai suna Talha dan Habib. Kamar yadda irin haka ma ta faru ga wani matashin mai suna Ainihin wato Amru dan Dinar. To duk irin wadannan abubuwan da na tattara su shine sai na tsaya in baku manta ba A karatun da ya gabata. Nace wadannan irin tunanin nukan suna tasowa matasa ne masu kishin addini. Su kuma sai su samu matasa wadanda asali ba kishin addini ne suke da shi ba. Sai dai suna cikin wasu damuwa na rayuwa Ko wasu matsaloli na wasu halaye da suka samu kansu. Sai suyi ta yada irin wadannan ra'ayoyin. Me cece mafita? Mafita itace abunda Annabi da sahabbai suke akai shine manhajin salaf wanda shi muke kira zuwa gare shi. Ai hakuri wadannan matasan a zaunar da su. Ayi musu nasiha A gabatar musu da dalilai. Sannan A basu lokaci su je suyi nazari. A dawo a zo a zauna da su. Domin wadannan matasan in muka nuna musu kuskuren su Muka nuna musu daidai Suka gane gaskiyar mu akan abunda muke fadi ba yan son zuciya bane zasu bi domin suna neman gaskiya ne. Sannan ya zama kai kanka malami kana da siqa da kanka kai kanka ka amintu da kanka cewa da gaske kake yi. Kai din ya zama ba mashirmanci bane. Na bayyana mana cewa Wannan irin da'awar Daga kasan Masar ta fara shigowa a wannan zamanin da muke ciki a wannan zamanin da muke ciki. Daga kasan Masar Ta kado ta yoo Sudan. Daga Sudan ta buga tai Algeria Somalia Mauritania Daga nan kuma ta sauka ainihin a wannan yammacin namu na Africa Kasashen Nigeria Da kasashen Senegal. In ka tafi bangaren Asia kuma da makamantansu Da Gabas ta tsakiya Kasashen Indonesia Da kasashen Pakistan Da kasashe irin su Saudi Arabia Da kasashen Yemen. Wadannan irin tunanin sun yi yawa a cikin su. Malaman Ahli Sunna Salafiyuna su suka fi kowa cin wahalar ita wannan matsalar a duk inda ta bayyana tun daga zamanin sahabbai. Don haka sahabbai su suka fi kowa cin wahalar ta. Saboda addinin da sahabbai suke akai Addini ne wanda yake tsakanin zakewa Da kuma gazawa. Zakewa itace daukar ra'ayi irin na wadannan khawarij Khawarij ko Boko Haram. Gazawa shine daukar ra'ayoyi irin na malaman da ake gani da yawa daga cikin su A yau a duniyar mu da kuma hukumomi Da kuma dattawa. Shine a matsayin ka na malami abunda ya kamata kayi bakayi ba. A matsayin ka na mai mulki abunda ya kamata kayi bakayi ba. A matsayin ku na dattawa abunda ya dace kuyi baku yi ba. Wannan ita ake kira gazawa. To manhaji na Ahli Sunna shine ba'a gazawa shi yasa kaga Jabiru ya tsayu da karantawwa. Sannan in kuskure ya faru ba'a yin shiru manhajur radd. Ya ake raddi? Raddin bada ashar ake ba Bada zagi ake ba Ayoyi ake kawowa Hadisai ake kawowa a fassara su a ilimi a zaunar da matasan nan a fahimtar da su. Saboda daliban mu ne Kannan mu ne Yayan mu ne Yan uwan mu ne. Idan muka bar su a cikin wannan kuskuren Ranar lahira Allah zai tuhumce mu. Sannan a nan duniya zamu dandani wannan sharrin wanda zai yada ta hanyar su. To amma abun takaici Kamar yadda na fadi Da su wadannan matasan Da muke tsaka tsakinsu Da kuma wadanda suke yaka kai tsaye sune gwamnatoci masu zalunci da malaman bidi'a da sauran su. Dukkan su sai suka tare suna zargin irin mu. Allahu Akbar. Yadda suke kafir tar da malaman sahabbai Suna zagin su Suna kashe su. Haka kuma a wannan lokaci gwamnatocin wadannan zamunan Suka rinka fama da Dora zargi Da tuhuma Akan wadannan malamai na sahabbai. Haka a wadannan zamunan Mu Ahli Sunna Salafiyuna Mune wadanda muka fi kowa fuskantar matsaloli tare da yan Boko Haram. Mu Ahli Sunna Salafiyuna Mune muka fi kowa tinkaran matsala da zargi da wulakanci tare da gwamnatoci na zalunci Da sarakunan gargajiya da malaman bidi'a. Tsarki ya tabbata ga Allah. Ka saurari karatu na da ya gabata a cikin wannan jerin giyar karatun Sahih Muslim. A lokacin da wannan fitina ta kunno kasan nan A sirrance babu irin kokari da kwazo wanda bamu yi ba domin danne ta. Har al'amari ya kai a bayyane Har muka fara fitowa muna yin Muna tara jama'a muna gabatar da lacco ci Tafiya tai tafiya har muka ainihin fito gidajen rediyoyi Da kafofin yada bayanai na zamanin da internet da makamantansu Muka cigaba Da ainihin ta bayanai ire-iren wadannan. Daga karshe Ba abunda wannan ya kare mu da shi Sai karin bakin jini Da karin zargi Da wulakanci Da kuma kashe da dama daga cikin mu da yan Boko Haram suka yi. Da daure da dama daga cikin mu da gwamnatocin Nigeria suka yi. Kamar yadda na kawo bayani a makon da ya gabata wallahi Ba gwamnatin Nigeria ba Har gwamnatin America Ba zata iya fada da yan Boko Haram ba balle yan Al-Qa'ida. Su da kansu masu ilimin su sun san haka. Wani rahoto wanda tashar America ta yada yana nan akan website din su a yau kwana uku da suka wuce yana nan Akan wani rahoton hari da aka kai wasu kauyuka kusa da garin Madagali a jihar Adamawa. An dakko wani kwararren masani akan harkar security Ya tabbatar da wannan maganar. Ba'a yakar ta'addanci da ta'addanci Amma ana yakar ta'addanci ne da hikima da ilimi. A karkashin wannan Har yanzu muna nan akan bakanan mu mu Ahli Sunna wadanda muke jin bin manhajin salaf.
[Segment 2/6 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
Kamar yadda daya daga cikin mu ya fadi shine marigayi. Dattijo malam Ja'afar Mahmud Adam, Allah ya haskaka mishi cikin kabarin shi.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
Cewa fitina ce wadda mu ba fata muke a barta sai ta ci ta cinye. Yadda yake baza a iya kashe ta daga ruwan ruwa guda ba sai an sa tankunan ruwa kuma basu yi maganin ta ba. Duk lokacin da aka buga bom zaka ga yan fire brigade sun zo ana ta amfani da tankunan ruwa kamar yadda marigayi malam Ja'afar ya fadi. Amma basa iya kashe wannan wutan balle ita fitinan. Hakika kamar yadda na kawo muku Tashar channel news Tashar channel TV news dake Lagos Tayi capturing tsohon shugaban jami'an tsaro na kasan nan Azazi Azazi ya ambata cewa Hakika Sojojin Najeriya da jami'an tsaron Najeriya baza su iya da wannan harkar ba. Domin suna tinkaran wasu mutane ne wadanda an horar da su a fagen daga. A daidai lokacin da da yawa daga cikin jami'an mu wadanda aka horar da su ma in a fagen daga ne wasu sun manta horon. Ba dan komai ba saboda an dade ana zaune lafiya a kasar. Don haka dole yanzu aka tayar da Kokarin rehearsals Ya za a motsa jinin jami'an tsaron. To amma Babban abu shine Da yawa daga cikin wadanda ake gani jami'an ne Sun rasa ethics Na yadda za a mu'amalanci talakawa wadanda innocently su suka fi yawa. Wadanda suke wadannan abubuwan a cikin talakawan yan kadan ne. To amma in aka zo Mafi saukin abun da za a yi wa innocent citizen shine ayi harafin din su A razana su A pirgita su A tayar musu da hankali in ba a ci mutuncin su ba haka saddan basu ji ba basu gani ba. Idan baku manta ba na bayyana lokacin da fitinan nan ta taso kasan Masar A irin yadda al'amarin ya zama. Gashi nan har yau kasan Masar Bata zauna lafiya ba sakamakon wannan fitinan. In muka koma kasashe irin su Somaliya da Aljeriya Har yau basu zauna lafiya ba. Amma kasashe irin kasashen Saudi Arabia Dake malamai masu bin manhajin salaf suna daawa a cikin kasar. Da suka bi irin wadannan techniques Wadannan intelligence strategies Sai Allah ya kwantar da fitinan. In ba haka ba wannan fitinan tayi yawa a cikin Saudi Arabia a garin Makka Da Madina Da kasar Riyad Ta yadu ta kewaye cikin matasa. Amma kamar yadda muka fadi Malamai suka yi ta rubuce rubuce in baku manta ba. Akwai wani littafi da nazo muku da shi Professor Khalid Al Ambari Ya rubuta shi dan karamin littafi nan muka kawo shi. Ka karanta mako Makka Tun kafin ka buga bom ka fashe din karanta tukunna. Wadannan laltafan suka yi ta rubutawa Suka yi ta tara daliban nan da matasan nan Aka yi ta musu nasihohi. Manyan malaman mu na duniya irin su malam Muhammad Nasiruddin al-Albani Da su bin Baz Da su Uthaymeen Da makamantansu suka rinka zama da matasan nan. Ana basu daman suyi tambaya Suyi kalubale Su fadi zargin da suke mana mu malaman su Su fadi zargin da suke hukumomi da talakawan gari. A basu amsa abun da ya kamata kenan. Saboda haka mu malaman Najeriya Mune kadai da ikon Allah na ahlussunna da muke bin ta farkin salaf. Mune kawai cikin lumana da nasiha Da ilimi da muka gada daga manzan mu Muhammad sallallahu alaihi wa sallam. Mune kadai zamu iya maganin wannan fitinan. Amma abun da jami'an tsaro da gwamnatocin nan zasu kara Sai dai su kara rikita mana al'amari Su ci amanan mu Su kara tunzura yaran nan Babu abun da zasu iya da ya wuce wannan shine abun da muke gani. Duk lokacin da kaji ance anyi maganin matsalar karya ne Na kawo muku abun mai sauki wanda yake kowa ya kamata yaje ya nazari da shi. Matar shugaban kasa ta fito tace tunda 2014 ta kama ita yanzu sunan ta Mama Peace Maman zaman lafiya Tace no more boko haram 2014 Amma wannan abun gaskiya ne? Ba gaskiya bane. Da kansu sai gashi sun fito suna tabbatar da cewa jiha irin ta Maiduguri Borno state Da jihar Yobe da jihar Adamawa Wadannan jihohin har yanzu suna nan karkashin dokar ta baci. Kuma zabe bazai iya yiwuwa a wadannan jihohin ba saboda babu zaman lafiya. Wannan Faduwa ce ga gwamnati Kuma yana tabbatar da gazawa ga gwamnati. Domin idan gwamnati ta cika Baza ta ce muku kar kuyi wannan taron ba saboda ana ganin akwai matsala sai gwamnati tace ku ci gaba da taron ku. An fahimta jama'a? Akwai shekarar da wadannan yaran muna wurin aikin hajji Suka zo suka ce zasu jefa bom a dutsen Arafat zasu jefa bom a kaza zasu jefa bom har gidan rediyon Saudi Arabia Ni na shiga nayi magana da larabci, nayi magana da turanci, nayi magana da Hausa. Mukayi musu nasihohi. Su kuma gwamnatoci aka basu shawara ya zasu yi. Ita kuma gwamnati tace ba abun da zai sa tayi alerting jama'a cewa bana akwai matsala Baza a yi aikin hajji ba baza a yi Arafat ba Gamnati ko kadan ma bata saki wannan sanarwar ba. Jama'a suka ci gaba Gwamnati ta san yaya ta iya managing abun Ta hanyar tsari na tsaro da ilimi. An fahimta? Ba wai bindiga ba bindiga tana kara ruda al'amari ne. Jama'a kuna fahimtar wannan? A yau Babu wannan matsala a kasar Saudi Arabia Allah yayi maganin ta amma ina son ka gane Idan da inda wannan matsalar Tafi dacewa tayi katutu Ta zama cikas to ba kasa irin kasar Saudi Arabia Saboda dalili guda daya Da zuzzuka da kungurmin duwatsu Da mafaka Tana daawa a Saudi Arabia wadda babu ita ko a kasan Nijar. Amma duk wanda yayi wani ta'addanci Karfe tara na safe kafin karfe biyu na azahar anje an samo shi. Saboda mai addua Daukar matakin da ya dace Gaskiya a cikin abun da ake fadawa talakawa Sannan kuma Da bibiyar shawarwarin malamai na sunna. Yanzu yana daga cikin barna wadda jami'an tsaron kasan nan suke yi. Ita ce duk wanda aka gani da dagaggen wando Da gemu To shi ake mai wa suspect. Wannan abun Ya kamata ace time yayi determining ma wannan tunanin is wrong. Amma sai ya zama har yanzu Wane yana tafe a cikin mota Yasa music yana rawa da kitso a kan shi In yazo check point sai a barshi ya wuce. Mai wa bindigogi ne a baya shine wanda ake nema. Wane ustazu yazo wucewa da gemu Da kiraa a motar shi shi kuma sai ace yayi parking Yayi parking sai ayi harafin din shi shi ake suspecting mai bindigar kuma ya wuce. Kun ga babu ilimi a cikin harkar Saboda haka Wadannan irin fitintunun jama'a Abun da muke rokon Allah Allah ya tsare mu daga gare su. Kuma kada Allah madaukakin sarki ya nuna wa musulmi su a karo na gaba. Amma Zan cike duk wadannan bayanan nawa Da tattauna wannan mas'alar Ta hanyar Bayyana menene ya kawo wannan fitina ta boko haram. Matsalar ta wayi gari Kowa da yana ganin bata shafe shi ba bata shafi jahar shi ba. Yanzu ta shafi kowa Ba wai a bangaren kasa kaza ba a duk kasar Ba a bangaren kasar ba a duk yankin Africa ta yamma Har zuwa African gaba daya har zuwa dukkan bangarori na duniya. Dan yanzu ba kasa America ba Ko kasar Saudi Arabia kai dan Najeriya kallon da ake maka jami'an tsaron Saudiya kallon da suke maka kallon tuhuma ne. Da zaran an ganka Tare da suna da irin ka wanda ya fika gemu mai tsawo Suna da irin ka wanda ya fika dage wando Wanda ya fika kama da ustazai Amma da an ganka tun daga airport sai ga an yi maka shigantaka. Wai ba boko haram de ko ba boko haram khalas shikenan khalas khushkiza Is gilanci To mai kawo wannan? Menene ya kara damalmala al'amarin da aka shiga Domin da matsalar ta taso ne a kwaryar wani wuri Amma menene ya maida ita Ta zama matsalar yanki Ta zama ta kasa gaba daya Ta zama matsala ta sashin Africa Sai ta wayi gari ta zama matsala ta duk duniya gaba daya. Allah madaukakin sarki ya kiyaye. Gaba na Littafin tarihin Sayyidina Ali ibn Abi Talib ne Wanda professor Muhammad Ali Muhammad Muhammad Sallah bi ya rubuta. Professor ne na Islamic Jurisprudence Daga ainihin garin Tripoli na kasar Libya. Yana nan da ran shi Ya rubuta wadannan littattafai sun kai su talatin Na tarihin musulunci Da kuma biographies tun daga na Annabi da Abubakar Da Umar da Usman da na Ali Da na Muawiya da Yazid da wasu sarakuna na musulunci da makamantansu. Har zuwa Umar Mukhtar wanda kake ganin Documentary na shi a video Wadannan laltafan ana kan fassara su yanzu Na farko dai an gama fassarar Tarihin Annabi sallallahu alaihi wa sallama da turanci da na Abubakar Da na Umar da na Uthman Dukkan su in kana son su Ka tafi ainihin daawa Kona ko daawa book shop ko Darul Tawhid Gashi can opposite Arewa house Akwai wasu bayin Allah sun bude book shop suna kawo wadannan littattafan Idan kai dan boko ne musamman Duk abun da zan yi wa bayani din nan Yana nan a cikin wannan littafin na tarihin Sayyidina Ali Da yazo bangaren maganar khawarijawa da yan shi'a Shi yasa shi ma sai ya ware wannan babin sai ya buga shi. Gashi akidoji Da dabi'u Na khawarij wato boko haram Da kuma ainihin Akidoji na yan shi'a. Ina son kuma duk wanda yake saurare na yaje ya samu jerangiyar kasusuwa na da nayi guda hudu Na daya demokradiyya kasusuwa ne guda tara suna nan akan CD guda daya. Na biyu in an kiji ba a yi ki gani ba. Na uku karshen alewa kasa Na hudu karamba na maganin zoman bana. Wadannan CD na Da kasusuwa dukkan su suna nan akan YouTube www.youtube.com In ka tafi search bar sai ka sa Albani Zaria Ko sheikh Albani Zaria Akan YouTube zai dauko maka su zaka gansu cikkakku insha Allahu suna nan akan internet. Duk inda kake zaka iya Accessing nasu insha Allahu ta'ala. Abu na farko Da ya haifarwa da duniya wannan ainihin wato musibar Shine Jahilta ilimomi na shari'ar musulunci. Wadannan makarantu da aka kakkafa na gwamnati Wadanda aka ce wai ana karantar da haya islam Da wadanda ake karantar da diploma shari'a Da wadanda aka ce ana karantar da Degree Islamic Studies Masters da PhD Hakika halartan su ba shine ya baka ilimi na addinin musulunci ba Wadannan alaranmomi da ake zuwa wurin su Ana ainihin haddace qurani Da wadannan malaman soro Da ake zuwa ana karatun littattafan hadisai da fiqhu da larabci da na zuhud. Gaskiya Hakika su ya kamata ace sun zama Galibi Su wadannan malaman mu na karatun qurani Da malaman mu wadanda suke na makarantun ta na zamani Da malaman mu wadanda suke na soro Da galibin malamai wadanda suke karantar watsakanin magariba da isha. Galibin su Wato sun komar da karatuttukan Sun juya su tunani irin nasu da al'ada irin ta su. Ilmomin sun zama ba a bisa tsari ne na riwaya ba. Ka koyi karatun Ka ruwaito fassarar An dora ka an wayar maka da kai ta hanyar raya maka Ilimi na ka kware da shi Da nufin cewa ana koya maka larabci ne wanda zai taimake ka ka fahimci alqurani da sunna. Ilimin hadisi haka ilimin alqurani haka Sai ya zama kawai babban abun da aka sa gaba aka bayar wa muhimmanci Shine kokarin ya za a yi kawai ka iya karatu Ka iya hadda Amma abun da zai baka ilimi ingantacce wanda zaka fahimci alakar ka da Annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam. Alakar ilimin da kake da ilimin da Annabi yazo da shi ya karantar da sahaba Galibin makarantun mu na hadda alqurani wadannan na zamani Da wadancan makarantun allo galibi ba akan haka suke ba. Dan haka Hatta karatun qurani yaya yazo daga Annabi wannan ba wanda yake damuwa a cikin mutun dari da wahala ka samu kwaya biyu. Abun da yake kokarin ya koya maka tajwidi Da hadda qurani a bisa ka'idojin da aka rubuta na tajwidi. Ko ka'idojin da aka rubuta na tajwidi Yayi daidai da irin yadda Annabi ya karantar da sahaba Ba a kokarin auna maka wannan a wajen karantar da kai hadda. Annabi da sahaba sun yi hadda qurani ya suka yi? Sai aka cire maka Tsarin su da ta farkin su da tunanin su Sai aka yi Methodologin duk da za a cire maka na Annabi a kawo maka wani cikas ne. Kun ji cikas na farko da aka samu. Makarantun mu wadanda muke cewa haya islam Dukkan su suna tafiya akan wani syllabus ne wanda aka yi designing na shi tun Syllabus Da Sune ake karantarwa. Kaje ka karantar Daya daga cikin ministocin ilimi na kasar Kuma daya daga cikin Na Shi ya rubuta wannan littafi Ya kawo yadda ya kamata a tsara haya islam. Kaje ka duba ka gani da turanci ya rubutin Amma haka aka tsara su ba haka aka tsara su ba. Su bawa mai shinkafa dukkan su haya islam suka yi. Basu yi degree ba. Amma da yake a lokacin akwai kokarin kwatantawa Sai kaji bawa mai shinkafa Certificate yake da shi kawai daga Arabiya ta Katsina. To suna nan da yawa. A yanzu mutun zaije ya karanta Arabiya Zaije ya karanta Bisan komai ba Babu komai haka Baya fahimtar komai shi za a dauka a sa principal gobe. Wancan yaje yayi law Wancan yaje yayi kaza Shi za a zo a sa alkali shi za a zo a sa komishina na shari'a. Shine za a sa shugaban kwamitin shari'a. Sannan Idan kuka dubi Syllabus din mu na Duk wadancan tsofaffin syllabus ne. Sai dai malami ko professor da ya fandare ko doctor ko wani Wanda yake Amma in dai zai bi abun da aka rubuta da abun da aka bashi gashi nan. Wasu abubuwan ana making references ana fadin wasu maganganun Kana ganin
[Segment 3/6 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker unknown]
Ya za'a a ci gaba. Mahir al-mu'akili, mahir da kuke jin shi sabon limamin nan wani yaro ne fa, shekarar shi talatin da biyu ne ko uku, mahir. Har da qur'ani fa ba fa gyen shi ba ce. Shari'a ya karanta. Expert ne a shari'a. Amma garin karatun shari'an ne har ya haddace qur'ani khirrijin abin nan ne. Daga diploma ya fara, ya first degree, ya masters, ya phd. Yana cikin limancin nan ne. A kai munakashar thesis din shi ko dissertation din shi na phd. Ya zama doctor. Amma har an nada shi limamin ka'aba. Ba phd yake da shi ba. Abin da nake so mu gane. Sai mun yarda an samu wannan matsalar a cikin educational system din mu na musulunci tukunna, sannan ranar farko ta gyara wanke nan. Shi yasa ku je ku samu jerangiyar kasusuwan farko da nayi a unguwar Magume na karatun littafin hiqba wanda nayi analysis game da ire-iren wadannan makarantu da kuma irin wannan har nake cewa gaskiya rashin inane ya cancanta ya sa muke goyon bayan yaran mu su je su karanta islamic studies da islamic law. Amma kai in ka karanta islamic studies a nan Najeriya kana haurawa Nijar wannan university ta sa yadda zaka raina kan ka. Nan Nijar idan kayi karatun soro a nan ka gama suna ce maka kai ne malami ko kai ne Allah ramma ko kai ne gangaran kana shiga nan kasar Chadi ko Sudan wallahi zaka raina kan ka. Ga su nan phd holders, lecturers, some of them if not all of them, professors zamu hadu da su a wurin aikin hajji. Su ne suke karantar da islamic studies a nan Najeriya. Su ne suke karantar da law da sauran su shari'a. Amma aka tafi taro da zaran sun ga yanayin wurin kawai sai mutum ya raina kan shi sai ya gane he is not up to date. Ka ce doctor ba za kayi magana ba, professor ba za kayi magana ba sai ya ce akaramakallahu tunda dai kunyi sai mu ce a'a ai mu Ku tashi ku ne za ku Me yasa Dan haka haka products din su ma suke zama. To kun ji matsala ta farko. To kenan a haka yaushe za'a yi wa addini kyakkyawar fahimta yadda za'a iya gamsar da matasan mu. Sakamakon wannan sai matasan mu suka raina malaman su saboda malaman gaba daya tunanin su ba tunanin da zai biya wa matasan bukata bane. Wannan sai tsallaka da mu zuwa ga matsala ta gaba ita ce mai Yaro ya ce duk malaman mu lalatattu ne. Na haka bari ya dauki littafi ya karanta. Shi kuma littafi in ka karanta shi baka samu jagorancin malami ba. Rather you miss interpret. Dan haka abubuwa sai suyi ta biyo baya. Sai ya zama babu ethics na ilimi a cikin abubuwan da zaka ringa gudanar wa. Dan haka jahilcin ilmomi na shari'a to kuma in har ana son a dawo ilmomi na shari'a na gaskiya ko wallahi sai an cire bidi'a. Sai an cire son zuciya. Sai an cire komai sai kowa ya yarda za'a yi gyara. Kowa sai ya yarda za'a yi gyara. Sannan kowa sai yayi Me yasa ake ilimi ne? Ana ilimi ne dan a samu certificate? Ana ilimi ne dan a samu abinci? Duk wadannan suna daga cikin matsalolin da suka ainihin tattaru suka tattare al'amari sai ya koma gaba daya ba ilmomin shari'a ake ba. Sai ka shiga cikin jami'a irin Ahmadu Bello ko BUK ko Danfodiyo ko University Ilorin ko Ibadan sai ka ga ka je ka ga professor a islamic studies. Sai ya shigo zai karantar da ku sai ya dube ku sai ya ce kartun banza kartun hofi. Ku duban ku wai kun zo karatun musulunci ku ku rasa abin da za'a karanta sai musulunci. Ku da wasu masu kokari ne ba engineering za kuyi ba da accounting da medicine da pharmacy yanzu kai duban ka gobjeje da kai matsa ka bamu wuri. Wanda wai zai graduating din ka ya sa maka albarka ya tsine maka tun ranar farko da ya shigo. Yaushe karatu zai yi albarka. Kenan shi kan shi yana bayyana maka a pakaice cewa nadama yayi game da karatun sakamakon haka sai ka samu kalmomi na zindikanci suna fitowa daga lecturerori na islamic studies daga lecturerori na arabiyya. Amma ba dukkan su bane fa. Amma abin takaici ne a samu koda mutum daya wanda yake professor ne a islamic jurisprudence ko islamic studies ko arabic language ko literature yana condemning arabiyya yana condemning din ka dan ka zo za'a karanta. Me yasa shi ya karanta? Kuskuren rayuwa yake so ya ce addinin musulunci yau akwai da yawa dalibai wadanda suke undergraduate suna islamic studies amma kullum za'a ganshi da littafin economics da handout na yan business admin saboda mai yana suturce kan shi cewa shi economics din ya karanta ko business admin. Jakar shi kuma fa ita ce take dauke da handout na arabiyya. Wannan ku saurare ni sai na zo cikin lecture ta wadda nayi muku alkawarin zan yi ta ba da jima wannan ba zan yi ta da na sanya mata in kun san wata ba ku san wata ba. Na daya daga cikin abubuwan da suka bullo mana suna yakar mu To lalacewa ta ilmomin shari'a da gurba cewa da lalacewar makarantun mu ka tafi kasashe irin nan nan libiyya din da nan kurkusa ka shiga nan Nijar din ka je wannan makarantar da nake fadi islamic university da ke Sayah ko Uganda malamin ka yana karantar da kai ne maka addu'a ya ne maka fatan alheri yana taimaka maka yana baka shawarwari yana alfahari da kai. Mahir da nake gaya muku ba da jima wannan ba aka tattauna game da thesis din shi aka bashi phd din. Da ya zo zai sai da ya fashe da kuka ya ce ya so a ce mahaifin shi yana wannan wurin a ranar amma mahaifin ya rasu. Amma sai ya ce supervisor din shi yayi mai abin duk da ya kamata mahaifin shi ya mishi kuma har yayi mai kari abin da ko mahaifin shi ba zai iya mai ba. Ya ce don mahaifin shi ba malami bane. Supervisor dattijo ne wani professor. Haka muke ji game da malaman mu da suke graduating din mu ko kuwa da Me kake tunani game da engineering Allah ya kiyaye. Wannan ya taimaka jama'a. Saboda haka wannan fitinan na daga cikin abin da ya taimaka mata rashin ingantaccen ilimi na addini. Mu mun zauna da matasan nan mun ga suna fama da haka na taba gaya wa wani babban mutum a Maiduguri tun wajen shekaru takwas da suka wuce na ce zan zo garin nan in kafa ration darul hadith salafiyya saboda matasan nan a karantar da su ilimi mai nagarta. Daidai irin wannan lokacin na ringa magana a Yola ga matasa amma ba'a karantar da su ilimi. Su kan su malaman basu ma gane wai menene ake nufi ba wai sai su dauka wai tara matasan nan da ake ana wa'azi ana takabbara wai shi ne karatu wai tafsiri da ake na magriba wai wa'azin kasa wa'azin mako wannan ne karatu. In ka ce kuna koyar wa matasan nan ilimin akida a cikin littattafai kuna koyar da su Islamic sciences ha'a sai malami ya ce akaramakallahu wannan ai sai irin ku. Saboda haka sai ya zama ga matasa tur amma babu karatu babu ilimi ingantacce. Sannan sai abin da zai biyo baya shi ne kamar yadda na fadi Matasa sai suke ta daukan littattafai suna karantawa ba malami wadanda ke fassara musu yanzu wannan matashin da kaji yana jawo Jabir ayoyi ba malamin da ya karantar da shi fassara ayar ya iya karatun ayar ne shi ya fassara ta da kanta da kan shi dai ya hadu da malami sai malamin ya ce a ba haka ake ba karanto farkon ta karanta ta bayan ta da ya karanta sai ya ce kaji ba akan musulmi take ba akan kafirai ne sai ya ce Allah gafarta malam na fa kaga da ya dauka ne kawai ya bude. Duk matashin da ka same shi a Najeriya tun daga kungiyar yan shi'a da kungiyar yan brothers da kungiyar yan boko haram zaka ji ya haddace maka ayoyi guda uku. Yana jijjiga wiya. In ka ce mai saurara budo min da take a qur'ani mai sani ba meye malaman suka ce game da ita mai sani bi sani ba ya haddace ne garin zafin kai da dimin kirji wanda bai yi hukunci da abin da Allah ya saukar ba kafiri ne azzalimi ne fasiki ne sai ga wani ya fadi ya suma wai imani ya shige shi. Ko kun fahimta jama'a? Wai ya mike matashi haka yana jawo saboda imani. Waye gaya ma haka ake fassara qur'ani rikita matasa ya buga kan su ba zai iya bude maka tafsiri ko kwade ya karanta ba bai san ilimin ba. Wannan sai ya ja daliban suka yi wa malaman ta waye sannan kuma suka zo suna mummunan zargi ga takalidanci na'am takalidanci ba wani malami da zaka makala kan ka cewa lallai sai shi ka rufa idon ka. Akwai ka'ida game da takalidanci akwai yadda ake bin malaman akwai yadda ba'a bin su akwai yadda ake abubuwan yana da ka'idoji. Amma sai ya zama waye ya koya musu ba wanda ya koya musu. Dan haka littafi irin littafin Muhammad Nasiruddin al-Albani Matasan nan basu je sun zauna an koya musu ba sai suka yi violating karatun da ke ciki ziya bai sai suka ja wa Muhammad Nasiruddin al-Albani mugun bakin jini. Sai ai littattafan Albani suke karantawa ai su Albani ne suke dora su. In kuma ka koma sai ka ga shi kuma Albani yana nuna musu kuskuren abin da suke a kai sun dauki littafin shi ne kawai sun karanta basu je an koya musu ba dan haka sun yi gaba daya basu fahimci me ake nufi da takalidancin ba balle zargin takalidancin. Dan haka jama'a kun ji na biyu. Abu na uku na daga cikin abin da ya haifar da wannan fitinar a duk duniya musamman a Najeriya kuma shi ne malaman da dama daga cikin malaman musulunci basu tsayu da yin abin da ya kamata ba na karantar wa da nasiha da wa'azan ta wa ga jama'a da masu mulki da kuma kokarin nuna wa jama'a yaya fuskar al'amura suke. Ina mai fadin haka. Amma ina fitar da malam Abubakar Mahamudu Gumi akan haka malam Abubakar Gumi uba ne. Ya karantar da mu ya fassara mana ya nuna mana munyi kuskure ya gyara mana zamu hallaka yayi kokarin jawo mu masu hankalin cikin mu sun bi maganar shi Allah ya kubutar da mu wawayen cikin mu kuma sun hallaka. Mutum nawa ne irin Abubakar Gumi wadanda suka tsayu tsakanin su da Allah suke kokarin a karantar da matasa a nuna musu kaza. Akwai lokacin da wannan matsayin na Abubakar Gumi ya fisatar da malaman Najeriya suka gayyace shi taro Kano. Dama kawai ashe sun gayyace shi ne dan su ci mutuncin shi. Suka ringa mike wa daya bayan daya su ne mai zagi na asharriya da maguzawa cewa ya je ya hada kai da yara yan iska suna cin mutuncin su suna kaza suna kaza. Duk suka gama aka ce mike jawabi yace ba abin da zai ce addini na Allah ne. In Allah ya nufi zai daukaka addinin zai daukaka addinin. Shikenan. Malam Abubakar Gumi da kan shi yayi wannan bayani me ya biyo baya kasantuwar malam Abubakar Gumi yana tsayuwa da yi wa matasan nasiha da yi musu addu'a da nuna musu abin da ya dace dan haka babu malamin da yake da kusanci da matasan da nuna musu me ya dace a kasar nan irin shi malam Abubakar Gumi din lokacin shagari ai shagari ya bada izinin fafaroma ya shigo Najeriya. Akwai wasu matasa da suka yi gungu suka ainihin tafi domin su je su tattauna da malam Abubakar Gumi. Suna so su dauki mataki na ta da rudani da hayaniya amma malam Abubakar Gumi ya zaunar da su ya nuna musu a'a da shi da shagari suka zauna domin ga kalmar matasan kasar din yana na a makarantan nan ta mu na taba fitar muku da kasar din na sanya wa kasar din Gumi suka ce yaya kai kana abokin shagari yana shugaban kasa zaka bar shagari ya shigo da fafaroma kasar mu ta musulmi. Sai ya ce gaskiya ne amma bari ku ji yadda aka yi taro muka yi da su. Suka zo suka samu ni suka ce suna so su goyi bayan mu mu musulmi shagari ya zama shugaban kasa. Amma suna da matsaloli guda biyu zuwa uku matsalar farko ita ce suna tsoron idan shagari ya zama shugaban kasa za'a tirsasa musu su zama musulmi. Matsala ta biyu ita ce suna ganin ba za'a basu damar suyi aiki da addinin su yadda suke so ba har ma takai ga su shigo da shugaban addinin su na duniya. Shagari ya ce a'a a zauna a rubuta ta yarjejeniya baza'a tirsasa musu su bi addinin su na krista ba kuma za'a basu yancin suyi addinin su kuma za'a yi musu izini su shigo da fafaroma. Malam Abubakar Gumi ya ce yana daga cikin wadanda ya halarci wannan yarjejeniya to karka manta Najeriya republic ce siyasa ce. Ba kai kadai ne ba hausa ya zauna a kasar ba ba kai kadai ne musulmi ba kana bukatan wasu abubuwa wurin shi shi ma yana bukatan wasu abubuwa wurin ka ba zai yiwu kai ka kai ka mai da shi bawa sai yadda kake so ba dole shi ma yana da yancin ya ce shi ma ga nashi tunanin. Ai akan haka aka yi wannan Saboda haka malam ya ce munyi kokarin cika musu alkawari ne ya ce me kuke tunani muka saba musu alkawari muka ce baza'a su shigo da fafaroma ba bayan anyi a rubuce. Sai wannan matasa hankalin su ya kwanta. Malamai nawa ne suka bai wa matasa dama irin wannan bamu san su ba a zamanin malam Abubakar Gumi. Sannan a fito ana karantar da mutane abin da zai amfani su shugabannin a fada musu gaskiya a sirrance in ta kai bukata ta kama a fito a bayyana ba wanda yake sai Abubakar Gumi. Je ka ka gani waye bai amfani da malam ta ya tara duniya ba shi kadai ne ba yi da gida sai wannan da yake ciki. Ba abin da ya mallaka sai gona kwaya daya bata dade aka raba wa yaran shi ita ba ga ta nan a rigaci ko. Ya abin da ya mallaka kenan. Shagari me basu tara ba da sunan malam ta sannan wadannan hidindimu suke wa jama'a na abin da ya shafi tsayuwa da abin da ya zama wajibi a kan su. Shagari da kan shi sai da ya fadi cewa mafi halin tashin hankali da yake samun kan shi shi ne in aka ce mai ga Abubakar Gumi ya zo office din shi. Amma fa Abubakar Gumi classmate din shi ne ka san ku classmate din ka ko me ya zama baka shakkan shi galibi ko me ya zama baka shakkan shi in kawai zaka iya tsikarin shi. Classmate dina ne wani professor ne yanzu a BUK wata ran na gani shi. Akwai wata shiganta ka da yake da zungure sai ya ce a na ce kai. Ka je gidan radio ka sanar da mu ne ka je yanzu ka zama professor ba ruwa na shi professor ne ni classmate dina ne. Ko kun fahimta jama'a? Saboda haka menene zai biyo Ya ce gaban shi na faduwa in ya je an ce Abubakar Gumi ya zo ya ce dan ya tabbatar to yayi wani abu ba daidai bane malam ya zo ya mai wa'azi ne. Ya ce amma duk wanda aka ce ya zo raini sai ya ce ku tsai da shi a nan wai tur mai ya zo nema takin zamani sai ya ce ku bashi buwushin kafa ku bashi motar shi ta tsofa ku bashi ana raba fila ya unguwar su ku bashi. Ya san ba sa wuce wadannan abubuwan ya ce amma aka ce Abubakar Gumi ya ce wani lokacin sai ya mike tsaye sai ya ce ku ce ya shigo. Da ya shigo sai ya ce Allah gafarta malam lafiya dai sai ya ce a to mun zauna mana. Saboda ya gane ba abin hannun shi yake so gyara ake so a yi.
[Segment 4/6 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
in cancanci. Je ka ga yana karrama shi ko bai karrama shi, ya gane ba kudin shi yake so ba. To malamai idan suka samu basu yi abun da ya dace su yi wa al'umma ba. Basuyi wa dalibai abun da ya kamata su yi ba. To dole za a samu birtsewa ta dalibai. Malam Abubakar Gumi. Lokacin da aka tattara wasu dalibai daga nan aka kore su da wasu ma'aikata. Ya kai gworo ya kai mari ya zauna da matasan ya zauna da hukumomi an gaya za ayi ya za ayi ya za ayi. A daidai lokacin da wasu malamai suke cewa wadannan matasa da ma'aikata 'yan iska ne ku rabu da su. 'Yan iska ne. Malam Abubakar Gumi yace a'a zai zauna da su. Ku ya akai kukai kaza? Ya akai kukai kaza? Ya akai kukai kaza? To ku bari ba haka bane ga yadda abun yake zamu je ayi magana da su gashi gashi gashi haka ya dinga kai gworo yana kai mari. Abun da ake so kenan malamai su yi. Wadannan matasan da suka zo abun da ya faru kenan. Malaman darika a kasar nan ce mana suka yi 'yan boko haram 'yan izala ne dan haka ba ruwan su da su. A ba ruwan su da su. Nasiha ba zasu iya musu nasiha ba dan su 'yan izala ne. Dattijo Malam Abba Aji Allah ya lullube shi da gafara. Zai aika musu su zo a to ku naji zaku yi kaza eh a'a kada kuyi haka. Ai wannan ya sabawa kaza ya sabawa kaza a gaba na anyi haka a kalla sau uku. A gaba na a kofar gidan Malam Abba Aji anyi haka. Sai yace Malam Albani tunda kazo naga yaran nan kaima suna saurara maka bari akwai wani abu da naji kai wane ije ka kace su wane su zo. Sai su taho du sai su zo. To naji labarin zaku yi kaza zaku yi kaza nasan kuna girmama ni ni baban ku ne na gode. To kuma kuna mutunta Malam Albani ma shine nake so zamu hadu mu tattauna muyi wani karatu na bai kai bane. Cikin lumana. Amma mahaukacin banza kace aje a kashe su. In an kashe su wasu zasu taso da suka fi su zafin ra'ayi akan wannan da suka fi su yawa. Zaka iya controlling wannan? Waye gaya maka danka bazai shiga ciki ba? Wani babban jami'in tsaro wanda yanzu da nake magana yana kurkuku. Yanzu yana kurkuku ni da shi yake gaya mani. Yace sunyi sharri kuma sharri ya ci su nace kamar yaya yace ranar farko da bomb zai tashi wuri kaza da dan shi ya tashi nace Allah ya ji kan shi. Daga bakin shi na tattara report din yana nan na watsa su a net. Abun da nake so ka fahimta ya kai dan uwa. Wallahi. Mu bama goyon bayan a kashe kowa. Ko waye zamu iya zama da kai shine kaji na kawo maka malaman mu malaman farko malaman sahabbai na kawo muku kadiya ta Ibn Abbas. Su dubu shida ne sun tare sun wara kansu a wani gida suna shirin zasu je su fara kashe mutane. Ibn Abbas yace zai je ya zauna da su. Yaje ya zauna da su kuma anyi nasara. Dayawa daga cikin su an dawo da su kan hanya. Da sahabbai. To malamai dole su tashi su yi abun da ya dace. Ku jawo matasa jika. Ku karantar da su. Ku gyara musu kura kuren su. Ku saurare su kuji me yayi tunani irin nasu yanzu Jabir. Bai bar matashin nan ya kawo aya ba. Sai da ya kawo aya ya gama fassara yayi kaza sannan sai ya fara bayyana mishi kura kuren. Kai yanzu da yazo zai magana ya kace jahilin banza uban ka ma mu muka karantar da shi malamin ka je ka tambayi limamin an kayi shuru bazaka yi magana ba tashi ka bamu guri ja'iri. Shikenan da kai zai fara. Ban shi bayani meye manufar shi meye fahimta. Dan haka dole ne malamai su yi abun da yake wajibi akan su. Wajibin malamai kuma nau'i biyu ne ta wajen karantarwa. Akwai karantarwa ta musamman ta wadannan matasan. Saboda matashi ne shekarar shi sha bakwai shekarar shi sha biyar shekarar shi sha takwas. Yana da lokaci yana da kwakwalwa yana da kaza danna musu karatun Sahih Bukhari. Sanya musu karatun Nailul Autar. Sanya musu Alfiya ta Ibn Malik. Dakko littafin ka sanya musu na Hakim. Ka jibga musu karatu kace su haddace. An tashi karfe goma na safe sai kace karfe biyu na azahar ku sake dawowa. An tashi sai kace bayan magariba ku dawo. An tashi sai kace to shikenan. Karfe biyu da rabi na dare. Ku zo muna da karatun Almuhalla ta Ibn Hazmin zuwa karfe biyar na asuba in aka yi sallah sannan kowa ya kwanta. Baya zai tunanin fitina. To ka basu shekara uku haka shikenan sun zama malamai shikenan anyi maganin fitina. Amma ba ruwan ku da su. Kun bar su. Sune ma malaman su suke karantar da 'yan islamiyya su kuma ba updating karatun su. To duk abun da ya fahimta sai ya fisawa matasa. Kafin ku nura sai gashi duk sunyi taking over. Na malaman izala da malaman Ahlussunna me yasa malaman suna can. Abuja neman AC mai sanyi da neman kudin da sake mota da kujerun hajji da umara. Sai gashi duk malaman izala gaba daya an juye da su ake wannan amfanin. So dole ne malamai su tashi su yi abun da ya dace na biyu. Karantar da mutane karantar da mutane nau'i biyu ne a sanya littattafai dubga dubga irin wannan. Yana daga cikin tafarkin malaman farko shine kaji abun da Jabir yake. Su su Jabir basu bukatar littattafai dan su sun zauna gaban annabi sun haddace da kansu. Mu kuma yanzu muna bukatar mu sanya musu littattafai. Sannan public lectures wadanda zasu yi Social. Da kuma educational aspect na rayuwa spiritual aspect na rayuwa da komai sannan a samar da Wadannan matasa da ke karkashin gadon ku banni ba tsinannu bane. Ba 'yan iska bane 'yan mu ne. Kanan mu ne 'yan uwan mu ne. Yanayi ne ya kai su karkashin gadon ku banni suna shaye shaye. Meye yawa kai kana da laifi me yawa ni ina da laifi me yawa dukkan mu muna da laifi. Muje mu dibo su. Mu zauna da su. Ya akai bama ganin ku a kaza kai ya akai kai ya akai kaza kai ya akai da kaza. Ba sai ga wani ta tasa ka ba kai malami ina fadin daga cikin ayyukan da ke kanka as malami abun da ya dace kenan. 1984 na gangara da babur dina cikin gadon ku banni dinnan a guda gangan naje da mashin da gangan kuma naje a guje. Na dira a guje daidai lokacin suna hawo saman gada sha dayan dare. A zo a kwace takalmin ka a kwace agogo a kwace hula. A ce Zara ta ci. Kana da magana sai kace a'a. Yace to wuce. To taka tayi kyau kenan ba haka ba a kwakkoda maka mari sannan a ce wuce. Da babur dina dira 1984 bani mantawa June. Pur na sauka da mashin dina sai suka taso wannan yana layi wannan ashe wani ya gane ni yace Alaga ta malam ya hadu. Malam kuma yau kai ne a nan nace sosai. Nace ana ta karatu ne baku zuwa shine nace bari in zo ayi muku naku a nan. Sai malam malam malam. Shikenan. Haka. Kaje ka gani akwai wannan taron yanzu a kasar ku banni babu. Tun daga wannan lokacin muka watsa su ba da duka ba ba da zagi ba. Amma sarkin garin nan ya taba zuwa da motar shi lokacin da fitina tayi fitina da haka da ya leka. Sai yace to wadannan sai addu'a. Su dawo koma. Haka ne musu a yola Jimeta. Naje na shiga cikin su muka saba da su nake mu'amala. Na kawo duk abun da yazo ko nayi tafiya sai su bugo min waya. Alaga ta malam kaji abun da aka ce me malam zai ce sai in ce eh to dama ina nan zuwa gode ku taru. Kafin kace wani lokaci. Munje wa'azin izala na kasa dinnan kwanaki da akai. Suna nan sun gyara sun zama mutanen kirki suna sana'a suna karatu suna ilimi. Shine kungiyar Suka zauna akai wannan tun Malam Abba Aji yana da rai muka kira shi daga Maiduguri aka dinga bin anguwa anguwa. Project din sunan shi kenan A hadu da matasan nan a tattauna da su a jawo su ya za a yi aiki da su. Ba 'yan iska bane yanayi ne ya kai su. Sayyidina Umar dan banga ne. Hamza dan daba ne. Su Aliyu 'yan club ne zuwa ake a sha giya a fito ana tambele a a mutane. Annabi bai yi musu Sai jawo su a jika. Ya gyara su daga karshe su suka zama Manzon Allah yace akwai kwayar su sune mutanen kirki. A jiya sun fi kowa lalacewa a duniya. A yau kuma sai ga Allah yana kiran su Saboda me? Manzon Allah yayi application a cikin su na me? Ba duka bane ba zagi bane. Kaji irin yadda ake karantar da su ake. Malamai ina 'yan mata? Ku dinga tattaro su. Magume tana cike da yara an turo su daga ko ina. Sun taho su Gaskiya layout tana cike da irin su. Sai ku zauna da su. Ku saurare su. Wani yana neman kaza ne wani yana neman kaza ne wata tana neman kaza ne ku saurare su as malamai. Ku saurare su. To amma da zakewa ya kai Kuna cewa wadannan yara 'yan iska mazinata. Wannan yarinya 'yan iska tana yawo tsirara. Magan sanda mala'ika zai zo ya gyara ta. Magan sanda Allah zai turo mishi annabi. Meye amfanin malam ta ka? Ka tafi yanzu nan ka darko nan na Inda ake sai da Tun karfe shida na asuba wata ran tun karfe biyar. Zaka same su suna tsaye tsaye wasu suna tsugune. Ba abun da zasu yi ne ba inda zasu je. Nan ne suka fito. In kazo ka basu naira biyar biyar ko naira ashirin ashirin ko dari biyu biyu. Kace to kun ga wadancan eh sun yi ridda. Duk wanda ya kashe su aljanna wadannan kafirai ne a je shikenan. Ka duba yana nan akan YouTube na internet sojoji sun kama wani yaro a Maiduguri yaro dan karami. An ce to kai eh. Me ka ke ce ya shiga boko haram me aka yi ya bayyana. Mutun nawa ka kashe yace eh shi mutun biyu ne ma kawai ya kashe fa ko yana fadi shi bai ma kashe da yawa ba. Dawa dawa yace akwai wani malamin makaranta. Da wani baba can. Ka san su yace bai san su ba. Me suka yi maka yace bai sani ba. An nuna ne ance kaga wancan eh to harbe shi. Kaga wancan baba eh harbe shi me yasa ma'aikatan gwamnati ne. Shi kuma fa shima ma'aikacin local government ne Eh. Yace shekaran jiya ma ya shiga kudi ya shiga an biya kudi. Ah to kana aikin gwamnati eh kuma aikin gwamnati yace to haka aka ce a yafe mishi kawai haka. Feliwa ne na malam ta. Malamai dole ku yadda. Ba kuyi abun da ya dace ba. Malaman mu ma basu ma san me yake faruwa ba akwai babban malami a kasan nan. Fitinar shi'a tayi kamari na same shi muna hira abun da yace min shi bai san ana shi'a a Najeriya ba. Bai san ana shi'a a Najeriya ba. Ko mun fahimta jama'a? Bai san ana yi ba. Lokacin da muka zauna a Radio Nigeria Kaduna muka yi Malamai ne ga su nan tattare da mu. Haka kawai suka yi suna kallo na a studio din. In anzo ance to Alaga ta malam me zaka ce sai yace to su bai ma san me yake ba yace ga ni najin ga su Malam Albani suna nace Da aka kira mu wani taro jama'atu nasrul islam sarkin musulmi sarkin wani duk aka kira sarakunan nan da malamai wannan malamin sai ya kira ni yace malam lawal nace mishi akaramakallahu yace wallahi. Duk wanda ke wurin nan bai san fitinar nan ba kar kayi shuru kayi magana. Yace ba wanda ya san fitinar nan yace wallahi ba wanda ya san ta so magan an tare a tattauna ya za a yi basu ma san ta ba. Basan ta ba. To dole ne malamai su yi abun da ya dace na uku na hudu Na daga abun da ya kara tunzura matasan nan suka zama yadda suka zama. Yaduwar zalunci. Wasu dayawa matasan nan sun shiga cikin tafiyan ne saboda An zalunce shi an wulakanta shi anyi mai kaza. Sannan da kuma hukunci da dagutanci hukunci da dokar da ba ta Allah ba ta kara taimaka wajen tunzura matasan nan. Mutane suka dinga fitowa suna kalmomi na kafirci. Shari'a da aka ce shari'a da Amma suka yi Suka iya Is unfortunate. It was indeed unfortunate. To zalunci a cikin mulki. Da hukunci da dokar da ba ta Allah ba ta taimaka wajen tunzurar matasan nan da kuma samun kansu a halin da suka samu kansu. Wani matashi ya fadi. Karara. Yace kudin da aka sace namu wanda za a gyara makarantu muje muyi makarantu. Aka koma aka gina manyan gidaje da wuraren sana'o'i. Mu kuma aka turo mu muna sai da bunburutu man fetur a bakin hanya. To zamu je mu bata wadannan kudin yadda mu bamu amfana ba to suma wadannan da suka sata bazasu amfana ba. An fahimta jama'a? To zalunci. Dole ne masu mulki su daina zalunci. Sarakuna daga tai hakimai ma'aikatan gwamnati. Sannan duk wanda aka zalinta. A tsayo a kwato mai hakkin shi. Ko kun fahimta jama'a? Yanzu abun da ya faru a nan jihar Kaduna Babban dalili ne da ke nuna maka wannan. An kwashi mutane basu goyi bayan jam'iyya kaza ba. Anyi musu sharri. An je an zuba su a daki dayawa wajen mutun dari biyar. Sai aka koma ma ana ce musu wai 'yan CPC. Ina kurkukun a lokacin. Nima anyi min sharri. Me yaran suke cewa? Su yaran sun gamsu ma suna cewa malam in mun fito zamu zo ka saka min a boko haram din dan Allah su wa suke wani dararrafe ma yake zuwa gaba na yana roko dan Allah shi yana so ne dan Allah in an fita za a zo a saka shi su yi kaza da kaza da kaza. Sai inna ce musu a'a. Ba haka za ayi ba. Da haka bane. Mu ba 'yan boko haram bane mu Ahlussunna ne. Sai dai muna gwagormaya mu ma bamu yadda da ayi zalunci ba. So manufar mu daya da ku sai dai mu muna wa'azi ne ku kuma ba wa'azi kuke ba. Amma ba shiga boko haram ne solution ba. Ya zaku yi kuyi sana'a ya zaku yi ku shiga makaranta suka ce ina sana'ar? Ina makarantar? Ina me ina me ina me? Muna ta yayyafa wa zuciyar su ruwa. Zuciyar su ta huce yanzu suna ganin basu da wanda zai gaya musu a wurin su yadda sai ni. Sannan Akwai wasu mutane da ba malamai bane a zamanin nan amma sun iya larabci. Suna da Sun iya magana. Sun iya kalmomi da suke jan hankalin matasa. Wadannan irin su. Sun taimaka wajen ruruwar wuta. Da kuma lalacewa al'amari. Wasu rubuce rubuce dayawa. Wadannan su Sayyidi Qutub suka yi da su Hassan al-Banna da makamantan su. Da makamantan wasu kalmomi da suka dinga fitowa daga bakin mutane a kasan nan tamu. Irin su Ibrahim Zazzaki da sauran su. Matasa ba a karantar da su ba. A sa su su fito layi suna rawar banjo. Ana sai mun dakko shi sai mun dakko shi sai mun dakko shi sai mun duk wanda daga cikin su yaje daukan karatu a wurin wani malami shikenan sai a ce anyi Ba a son shi saboda me? Yaje yana karatu wurin malaman yahudawa. Sai da aka waye gari duk matashin da yake tafiya tare da Zazzaki sai da Zazzaki ya ga ya kankare mishi ganin darajar wani malami. Sakamakon haka sai ya zama kawai shi kadai za a saurara shi kuma ba karatu yake ba. Ba karantarwa yake ba lacca ce wanda zai je ya saurari BBC da VOA da CNN yazo ya tara 'yan mutane ya sa da wani rawar ni na shaidan yazo kawai yana buga kan 'yan jama'a amma karatu fa juye bankwarya ta da muka fara jefa mishi shine wai sai a dibi matasa sai a tafi daji wai sai a ce za ayi karatun Muka ce ayi in aka je kuma sai a tara mutasa sai a zauna sai anyi tsu sai a ce
[Segment 5/6 | 01:20:00–01:40:00]
[Speaker unknown]
Muhammad sallallahu alaihi wasallama ya ce haka haka ake karatun fa da kalubale yawa wai shine yanzu ya fara tafsiri ku ji tafsirin me ake karantawa ana karanta tafsirin ga tafsirin su na shi'a ga su nan duka ana karantawa ba a karantawa matasan mu juwarin zuwa sai suka dauki zazzaki malami ne yaran mu suna suna suna da za su fita da aka ce musu karatun boko kafirci ne suka fita daga in Nigeria suka je suka taro a anan cikin masallaci suka zo suka zauna suka ce sun daina karatun boko kafirci ne akwai dan unguwar mu sabon garin Zaria ga gidan su nan da ka je gidan farko daga hannun hagu zaka ga yana karatun ya koma yana yankan farce a kasuwar sabon gari cewa karatun boko kafirci ne shi yanzu halal din shi zai ci shine yankan farce aka yi mana cikin da ba uba matasan mu shikenan aka ruguza mu to ire iren wadannan su ma sun taimaka ina son ku gane wannan dan haka ko dayan biyu ina cikin masallacin wannan lokacin ma ranar yana da karatun Bukhari da da safe zazzaki zai zo wadancan matasa yanzu sun dawo cikin taitayin su wani ya shekara 40 yanzu wani ya kai 45 wani yana 39 suka ce zazzaki da yasa suka yi daga makarantu shekarun baya shi zai zo suka ce suka ce yau sai su ko shi duk bishiyar da ke kewaye da masallacin sai da suka tsinke ta suka maida ita dorina da yazo ana cikin a cikin masallacin yana cikin wannan wani ya kukan kura ya ce karya kake ya fada tsakiya sai wuri ya hargitse a guje ruga da gudu ya hau ta masallaci a guje bayan an kwantar da ya sakko malam mai recording shi ya bashi koko ya fi tsari nan take saboda firgici Allah ne shaida a gaba na aka ji karka tambayi malam malam ilu shine zaka ji kana jin zaka je yana kabara yana shi je karka tambaye shi yana nan da ran shi wadannan matasan suka ce saboda ya cutar da su ya kware su ko kun fahimta to amma ya za a iya wannan kwarar wannan ya taimaka wajen samun wannan yaduwar barna tsakanin mutane ta taimaka a matasan mu da wajen wadannan abubuwan barna tana yaduwa a zo a bude gidajen karuwai gidajen giya sarakunan mu basa magana lami dan adamawa Muhammad Mustafa kakan barkin do wannan na yanzu kakan wannan baban wancan da ya rasu hanawa yayi idan tayi mace ta fito ko wace iri ce illa asar tayi shikenan babu fitowa sarkin zazzau Jafaru dan Isiyaku anan zazzau idan ya ga namiji da mace suna tafiya ko aka bashi labari da yake fitowa ran gadi zai kwantar da kai ya sa a maka bulala goma dan me kake jera tare da wannan matar kace mai hada ku sarkin Kano Usmanu a zamanin shi aka daina baiwar mata gida ko makamantansu saboda in aka bata gadon gida uban ta ya rasu sai ta koma in mijin ta ya bata mata sai ta dawo sai ta yi zaman ta a gidan daga nan aka fara samun magajiyar karuwai duk wadannan kyawawan misalai ne na sarakunan mu wadanda suka rinka fada da barna da masu mulkin mu yanzu ku duba unguwa irin wannan tamu sai mutum yazo ya saye fili sai ya gina gida sai ya dakuna goma sai ya dibi yan mata rida rida sai ya basu su yi ta karuwanci da fasadi babu wata majalisan sarki da zata yi wanene ya wannan babu hukumar jami'an tsaro babu kowa kuna zaune sai a kawo muku gangariyan karuwai tsakiyar ku dan haka wadannan yayan ku yan shekara 13 ko wace tana sha'awar ta rinka sanya mini skirt da mini jeans dan haka yanzu duk yarinyar da ka ganta da hijabi da nikabi da kaza daga kasa mai yuwa t-shirt ne da wando a ciki me yasa saboda an kawo musu wadanda za su bata tarbiyar su kafin ka lura yar ka tayi kawance da wata matar ka tayi kawance da wata daga cikin su yaduwar barna ya taimaka wa wadannan matasan sun dauki zafi suna ganin ba wanda kuma yake magana akan barnan nan mutane basa jin wa'azi basa gyaruwa shugabanni basa son su tuba basa son su bari malamai basa son su bar bidi'a basa son su maida addinin musulunci ya zama addini sai dai matsayin al'ada kowa baya shirin gyara duk wannan ya tunzurta matasa shine maganar da na gaya muku makon da ya wuce da na kawo muku littafin lokacin da barna tayi wa kasar Masar aka kama wani aka kashe wani aka kashe shugaban yan Ikhwan aka dauke shi aka jefa shi a prison matasan nan suka ga a to malamai kuna ji a nemi mana haka to kun zama kafirai mutanen gari kun zama alkalai kun zama malamin da yake masani ne sai ya ce wa daliban ya ce a'a ba wanda ya kafirta ba dai fahimci abun da ya dace bane kawai jama'a kun fahimci wannan to sakamakon wannan sai aka samu daawa daga cikin matasa sai suka kafa kungiyoyi ko wane irin suna ne suka sa amma dukkan su suna da manufofi irin wadannan wadanda na gabatar su suka kai su ga abun to yaya ne ake iya gane wadannan irin matasa ko ka kira su ko ka kira su yan boko haram ko ka kira su da ko wane irin suna ga wasu abubuwa wadanda zaka ga sune suke da tarayya a tsakanin kanin su zaka ga mutum ya dauki addini da zafi akan kan shi kuma ya dauka da zafi akan wasu na gaya muku ba daya ba biyu ba abun da ya faru a Maiduguri wani lokaci na tara su in yi musu nasiha sai aka nuna mun wani daga cikin su cewa gashi nan matar shi ta haihu sirikar shi ta zo tana kula da yarinyar saboda haihuwar farko ce tana nuna mata yadda ake yi sha dayan dare suka je suka kira shi a bokan shi mun ji cewa sirikar ka ta zo tana kwana da matar ka wai tana nuna mata yadda ake jego haka ne suka ce ya ce a'a ta baka hadisi akwai hadisi da ya ce tayi haka to ka je ka kore ta in ba haka ba ka zama kafiri zamu daina magana da kai daga daren nan ya shiga a baba a tashi baba tayi bacci ta wuni wanke wanke yara da baba kina da hadisi da ya ce ki zo ki zauna ta ce hadisi ai malamai ne suke kawo hadisi ita yarinya ta haihu na zo in ce a baki da hadisi a fita yar bidi'a a ce ki fita da daddare ya kore ta na ce to kai kana da hadisin da kai haka kai kuma akwai hadisin ya ce a na ce to kai ma kuma fa ya sunan ka shine haka muka yi ta gogarma da su amma tkuicin da gwamnatin Nigeria za tayi shine sai tayi back fairing akan mu ga America nan gudu take daga ina daga Afghanistan daga Iraq Russia gudu tayi daga ina daga Afghanistan amma abun da ya dace kenan wannan kuma sai an zo wurin ahlus sunna mu kadai ne muke da wannan techniques din domin ba wanda yake da tarihin yan boko haram shekaru 100 da ya ta wuce sai mu ahlus sunna gashi mun karanto a littafin nan farkon yadda suka fara bayyana kenan duk dunia babu wani historian wanda zai kawo maka wannan tarihi basu da shi ko professor wanene I challenge him bai san tarihin irin su ba mutum ya nada kan shi malami bai san komai ba ya hau kujeran manyan malamai shi yasa za ku ji a cikin lacoci na can da na fadi na rinka musu raddi na ce sai ka ga mutum ya nada kan shi kwana biyu ya shigo cikin mu ahlus sunna sai ya ture mu ya ce mu ba malamai bane shine malami ku je ku saurari lacca ta da nayi akan demokradiyya ka ga wani pigaggen mara kunya anan cikin garin Zaria ko diploma bai da ita a addinin musulunci bai san komai ba amma wai ya dubi mutum irin Abubakar Gumi wai ya dubi Abubakar Gumi ya ce wai malamin banza ne yayi mutuwar banza don wai har ya mutu bai yi jihadi ba sai ka tambaya shi yanzu tukunna ya ma san menene jihadi ya karanta littafin shi yasa na ce kowa ya sayo zamu zo mu sa muku karatun shi nan bayan mun gama duk wadannan littattafan a karantar da mutane ku ga bayan karantar da su za su cigaba da wannan haukan an rabu da su ne kawai faraga tayi musu yawa lokaci ya musu yawa ba abun da za su yi kuma ba a koyar dan haka dole ne sai su dibi wa kan su abun da suke gani shine kawai to sai ya ga dan pigagge da shi ya nada kan shi yana fatawa wadda fatawar idan aka kai ta wurin malaman sahabbai ko wallahi tsoron ta suke ji amma sai ka ga wani da an tambaya sai ya ce ah wannan ai kafiri ne na gaya muku irin wadannan da yawa sai mu zauna da su a Mecca ko a Medina ko a Mina ko a Arafah ko Muzdalifa ta yi magana sai ya ce kaza sai ya ce to jama'a ni dai wurin nan yafi karfin zama na sai me yasa in ce a na ji manya manyan fatawoyi sai ya nada kan shi kawai wallahi masala ce wadda in aka tambayi Sayyidina Abubakar ko sai ya girgiza amma sai ya ga wani pigagge sai a mishi tambayar kawai sai ya ce wannan ai kafiri ne wuta zai shiga me dalilin shi sai ya jawo aya sai ka ce mishi aya ba ma haka take ba tun daga karatun ta har ma anar ta tun daga karatun ta har ma anar ta ba ma haka take ba ko aya basa tsayawa su haddace daidai haka zamu zauna da su karfe uku na asuba karfe hudu wani lokacin sai an kira a salatu a Kaaba sun dibo yayan jama'a wai sun zo su yi musu mubaya a gindin Kaaba a kewaye Kaaba a ce to ka rantse da Allah a gaban Kaaba nan ka yi wa wani mubaya a in ya ce ka kashe mutan garin ku gaba daya zaka kashe su a sai ya ga ana mubaya a su din sai mu zauna me yake faruwa za a ce ina ruwan ka sai ya ce a da ruwa na sai mu fara tattaunawa sai mu wargaza wannan mubayar haka amma ita gwamnatin Saudi Arabia su sun yi amma mu nan da yake mutanen mu ba ilimi haka sai a ce to me ya hada ka da yaran kai dole sai ka yi musu nasiha yes duk abun da za su yi za su yi ne yanzu addinin mu aka bata sunan shi addinin mu aka bata sunan shi kabilar mu aka bata yankin mu aka bata abokai ne muke da su za su zo su yi investing anan kasar sai su ce suna tsoron boko haram sanna haka muka ji tsoron ka da ya faru wani wani kaza wani kaza director gidan radio mu ce ku zo ga wata musiba ta taho ya za a yi wayar da kan matasan nan kaza kaza wani wawa ma wai wai sai ya ce ku rabu da su yan iska in suka tayar sai mu karkashe su wani kuma sakarai sai ya ce muna ina ganin malam Albani kuna ganin wasu yara ne sun taso za su zama malamai kuke musu hassada haka muka yi ta haduwa da wallahi kuwa haka muka yi ta fama da mutum ya dauki sai ya ce ne kadai akan abu fa ba wai raayi na addini ba ah raayin addini ne yanzu raka'a hudu ce to duk wanda ya ce raka'a ta ko wane ne karya yake yi to wannan ba raayin ka bane raayin shari'a amma wani abu na raayi haka kana da yancin ka dauna ka ina da yancin dauki nawa to sai ka ce dole naka ne daidai kuma dole kowa ya barna shi ya dawo kan naka in ba haka ba fa ya zama kafiri wai kai ne Kaaban musulmi shine Kaaban musulmi ka san Kaaba duk wanda ya kauce mata ai bai da sallah ko to duk wanda ya kauce wa raayin shi gaba daya ko waye ba daidai bane kuma raayin fa ba dalili yake da shi Qurani ko hadisi ba ina jin dadin maganar nan amma ina tabbatar muku da cewa ga kasar ya kare zan tsai da ita anan ba dan ya kai in tsai da ita ba zan karasa ta a gobe insha Allahu amma zan rufe muku da misali kwai daya akan wannan wani lokaci na je Maiduguri na tara su akan maganar karatun boko da aikin gwamnati da siyasa na fada muku wannan a kasar amma ina so in cike wannan maganar dan ka gane raayin da kai kake gani kawai ka ce shine daidai wallahi lokacin ba ma san sun yi zurfi akan wannan ba sai na ce kuna cewa mu malaman ku ne amma mu yan boko ne na ce kun ga duk da karatu da kuke ganin na yanzu na dawo ina sake karatu ne kuma na boko wani amfani ku ke ci University Maiduguri FCI da sauran su sai aka nuna wannan guda daya aka ce ai sunan ba ruwan su da karatun boko aka ce wannan dan iskan ne ma anyi anyi ya daina haya Islam wai yana haya Islam na ce to amma menene dalili akan haka kuna da dalili shine abun da na fara gaya muku makon da ya wuce shine suka je suka dibo wasu photo start sai suka ga na kalla na watsar na ce wannan wannan photo start din littafin wanene sai kuma duk sai suka sai kowa a jikin shi ya sanyi wai ka san littafin na ce sosai kuwa su ashe ma basu samu asalin littafin ba photo start ne suke yawo da shi wannan littafin wanene aljaza'iri wannan kuma fatawa ce ta Usaimin wai suna mamaki to shikenan na je ina wa'azi a wajen menene wani NNC pump bana manta lecture ku je ku same ta amma ban sani ba ko mun zo da ita garin nan lokacin nan akan mantuwa nayi banda lacoci na na mantuwa da nayi a garin nan a Maiduguri na fara yi musu na ce Maiduguri nan ce cibiya ta hadda Qurani zan yi muku lacca akan mantuwa sai da na kwana biyu ina yin lecture kusan kasusuwa shida ne sai aka rubuto mun tambaya ga hadisi an ce aikin gwamnati an ce siyasa an ce kaza ga hadisi kai malamin hadisi ne ai sai na ce amma ba da ka muke malanta ba muna yi ne bincike muke mu gano kaza ba fada muke da ka ba sai mun bincika na ce saboda haka zan je in bincika na ce karatun boko nake yanzu ba littattafan Arabia wurin amma in na koma Zaria nan ne wurin aiki zamu shiga a bincika hadisin ya inganta shikenan fine an bincika hadisi bai inganta ba na hukunta hadisin munkar ne kuma na kawo malamai da littattafai wadanda suka gabatar da haka na rubuta musu da rubutun hannu ba da computer ba na yi type setting ba na aika ran da wasika zata zo ashe daya daga cikin su yana rike da daya daga cikin littattafan farko da nayi hujja da shi ana duba gani sai aka duba littafin sai aka ga magana ta ka ga littafi a hannun su basu yi bincike ba sun tafi suna neman wai su kura shi wannan da ya kare ta sai ya ce to kun ga abun da malam Albani ya fada wallahi gaskiya ne kawai abun da za a ce shi uban tafiya sai ya ce wannan malam Albani yayi yayi nufin ya rikita mun daawa ta ne kawai sai shi wannan ya ce a'a ai ga littafin da ya reference yayi reference da littattafai biyar na farko gashi a hannun mu kuma gashi mun duba mun ga haka ne yanzu ba raayin Albani bane gashi abu ne wanda mu ma muna da littafin ai sai aka ce to ya yayi ta waye jinin shi ya halatta shikenan har garin Difa Difa jihar Nijar eh kasar Nijar ya gudu yana buya za su kashe shi kawai yaro awwal ta kwara na ne sun sa shi har ya
[Segment 6/6 | 01:40:00–end]
[Speaker seg6-spk:0]
yana zagi na, zagin uwa ta, ban taba jin an zagi dan adam irin wannan ba. Rannan sai aka tara su kuma aka ce wai za'a tura su su da suka gama secondary suke da WAEC mai kyau, za'a tura su zasu je su yi karatun medicine da pharmacy. Sai shi yaro ne ba fulatanin Kano malam Ja'afar ya tura shi Maiduguri ya je ya karantar. Amma ya ci amanar malamin shi ya je ya shiga cikin wannan tafiyar Shikenan. To shi daga nan ne kwakwalwar shi ta buga ah to amma malam eh kace mana wannan abun kafirci ne. Yan zaka tura mu muyi kafirci sai ya ce ah ai ina da bukata ne sai ya ce ah malam kai baka yi boko ba. A cikin malaman mu duk ka raina saboda basu yi boko ba, Albani dan boko ne me yasa shi da yayi maganar boko tunda ya san ina na out? Me yasa baka yadda shi malami shi dan boko yayi magana kuma ka raina ka ce ah kuma yanzu kai zaka ce awwal ya zama kafiri. Wallahi a bishi a kashe shi Wannan jami'ar nan ya gudu daga baya suka bi shi. Shine Zarban ya dauke shi aka bashi admission yana jami'ar Islamiyya yanzu Madina. Jama'a wannan shine halin da aka samu kai. Kawai ra'ayin da ka kwana akai shine daidai. Duk wani ra'ayi kawai bashi da yancin ma a saurare shi kuma duk wanda ya saba kawai a kashe shi. Wallahi jama'a wannan shine asalin ra'ayin khawarij. Haka khawarij suka yi. Sayyidina Ali yace kaza kawai suka ce kafiri ne to suka ce jinin shi ya halatta. Mu'awiya suka ce kafiri ne jinin shi ya halatta. Sai wa Amru bunul as kafiri ne jinin shi ya halatta. Abu Musa al ash'ari kafiri ne jinin shi ya halatta haka. Ina za'a ci gaba da wannan? To dole ne malamai su tashi su yi aikin su kuma dole ne malamai su karbi gyara to sannan ta wani bangare wallahi yadda ake tunani ko wallahi gyara bazai samu haka ba. Kai ma'aikacin gwamnati, kai dan siyasa, kai mai mulki wallahi sai kun daina zaluncin da kuke don shi ma yana kara tunzura mutane. To sannan malamai ku kuma sai ku rinka regulating abun. To sa'annan zan zo zan yi magana akan galibi yanda awayan Saudiya dinnan yaran nan da in sun dawo daga Saudi Arabia su kuma an buga musu kai da tunani irin na Saudawa sai su zo su kawo mana tunani irin nasu. Su je su makalkale a jikin masu mulki saboda ana shafa musu zuma a baki. Ba abun da zasu yi sai dai su fito suna condemning yaran nan gaba daya basa tsaya suna luran menene complaint din yaran nan. Su dole sai anyi balancing. Malamai sai sun yi gyara. Wallahi masu mulki sai sun yi ma'aikatan gwamnati. To sannan sai a daga hannu sai a roki Allah sai kuga musiba ce dama. Sai kuga abun yana coming down. Wannan musibar ta faru a Ingila. CNN ko BBC World ko wacece Sky News live ta nuna zaman majalisa yara yan kanana suna bi suna harbin mutane da keke. Wannan ya taho sai wannan ya ce to tsaya nan kunnen hansa dinka sai ya kunna. Shi zai cameraman ne. Wancan ya tsaya sai ya ce harbe shi. Sai ya samu wani kawai sai ya harbe shi sai su tuntsire da dariya gashi kuma sai su je sai su yi uploading akan YouTube. Su su kashe wannan su su kashe wannan yayan suka fito suna harbin su kamar kwadangaru. Aka kai matsalar majalisa da aka kaita da yake masu ilimi ne. Makaho ne dan majalisa ya mike ya ce haka muka yi muna yara haka haka ake yi kwanaki ah ya ce to a gyara Dole a gyara. Amma ah ah kai baka shirin ka daina zalunci. Kai baka shirin ka daina bidi'a. Kai baka shirin ka karantar, baka shirin kayi wa addini hidima. Su yaran kun ce su daina wallahi baza su daina ba domin Allah ne yake rike da zukata. To in aka bi shi sai ya tankwara systematically sai ya ga komai ya lafa. Shikenan haka ake yi. Wannan fitina a gaban mu ta taso a Madina jama'a. Suna bi suna tattaral tafe malaman musulunci a makabartar Baki'a suna cinna musu wuta. Ana fitina da su. Malami yazo yayi musu tsawa yace gafara nan malamin gwamnati tsinanne kaza kaza kaza kaza. Amma da aka tsaya aka dubi abun yau babu labarin matsalar a Saudiya gaba daya an kashe ta. Jama'a da wannan zamu saurara muna da karatun Bukhari an jima insha Allahu karfe takwas a can markaz muke cewa
============================================================
[Part 2]
============================================================
[Segment 1/5 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker unknown]
Yanzu da muke magana daren Lahadi ne da ya daidai da daren biyu ga watan Rabi'in Sani Hijra na da shekara 1435 Daidai da daya ga watan Fabrairu shekara ta 2014 Wannan shine kasan na 308 daga cikin jerin giyar karatuttukan littafin Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi. Karatun da mukayi wa take da karatun hadisi da aiki da shi shine zama lafiya ga musulmi. Idan jama'a basu manta ba mun kammala karatun Wanda babin ko kuma yana daga cikin karatuttukan da yayi ta samun matsaloli Saboda ya hadu da damuna Watar azumi Da kuma matsalolin rashin samun dama halarta Shiyasa yana daga cikin Karatu mafi dadewa Da ya rike mana allo kwarai da gaske Toh amma Mun kammala shi lafiya Da sunan Allah mai rahama mai jin kai Wannan matattarar zai tattaro mana ayoyi da hadisai Da maganganun malaman farko daga cikin sahabbai da tabi'ai da wadanda suka zo bayan su da kyautatawa Domin ya bayyana mana hukunce hukuncen aikin hajji Kullum kamar yadda nake fadi Ma'ana Matattara tarawa Toh amma Abinda take nufi a galibin abinda mutane suka fi sani da Shine littafi wato Toh amma in kaji kalmar a cikin karatuttuka irin haka Toh tana komawa ne ta dauki ma'ana ta lugha Ba ma'ana ta Domin in ka dubi littafin Bukhari shi kanshi littafi ne Toh kuma a cikin shi sai kaji ance littafi toh sai kaga zafa fahimta toh yaya kuma littafi a cikin littafi Toh littafi Na A matsayin littafi ne da ma'anar da aka saba Amma da zai ce Abinda yake nufi Matattara wadda tayi bayani akan aiki hajji Bayan da ya kawo wadannan tattaunawa da aya da Bayan da ya kawo wannan ainihin ayar Sai yake cewa Daga cikin almajiran da suka ruwaito wannan littafi na Daga Haka yazo a cikin Rawi ne wanda ya ruwaito wannan littafi na Amma wadansu wadanda ba Daga cikin almajiran da suka ruwaito wannan littafi ta hanyar Bukhari Toh su ainihin Kuma babu wannan sai dai kawai Dan haka kawai abinda yake a cikin wadancan ruwayoyi Nasu shine Babu Yace a cikin ruwayar wadansu kuma da suka ruwaito wannan ruwaya ta littafin Bukhari Wato inda yake cewa ainihin An gane? An fahimta? Toh wajen Ma'ana Anan mun karanta ne Babu Toh a cikin wasu ruwayoyi kuma Sai ya zama wawun din na ne kenan sabuwar magana ce Zan zo zan dawo kan wannan mas'alar zan tattauna ta insha Allahu Amma a cikin Shi kuwa sai yazo Matattarar da ke bayani dangane da aikin hajji Ma'ana In ance kai tsaye matattara da ke bayanin hajji Wannan kuma ibadoji na aikin hajji kusan ma'ana daya ne Ya gabatar da bayani akan aikin hajji Sannan sai ya biyo baya da azumi Kun ga Daga zaka Sai ga ainihin hukuncin aikin hajji Toh sannan daga baya zai shiga azumi Wanda ya kamata da ya gabatar da azumi Sannan sai ya gabatar da aikin hajji Sai malam yace saboda wata Wanda yake ya ambace ta wato wata hikima ce wadda ya ambace ta a can muqaddimar Ayi min hakuri wallahi bazan iya tuna ta ba Ina fata an gane kuma ban koma in sake nazarin ta wannan hikimar da ya fadi ba Sai dai insha Allahu ta'ala in munzo karatu na gaba a gobe Zan tattauna mana wannan hikimar insha Allahu Toh sannan da ya tashi tsara wannan littafin na matattarar ta ta aikin hajji Sai ya biya shi a gwargwadon yadda ake yin aikin hajji din Ma'ana sai ya dubi a ibadojin hajji me ake farawa da shi Sannan sai me? Sannan sai me? A haka ya kwararo wadannan abubuwan daya bayan daya Sai Imam al-Bukhari sai ya fara magana dangane da mikatoci A ina ne ake tsayawa domin a dauki harama ta aikin hajji Mikati nau'i biyu ne a aikin hajji Akwai mikati wato wurin daukan harama akwai mikati lokaci Ba daga ko ina ake daukan harama aikin hajji ba akwai wasu wurare na musamman ga duk wanda yazo zai shiga Makkah Toh daga nahiyar da ka bullo zaka shige ta akwai inda ake fatan ka saurara a wannan wurin ka dauki harama Sannan ba ko yaushe ne ake daukan harama aikin hajji ba akwai watanni da ake daukan harama aikin hajji zamu zo muyi maganar su Sannan sai Imam al-Bukhari ya kawo Yaya la dubba Wadannan dokoki ake so ka cika su kafin ka shiga ainihin Makkah Da kuma abubuwan da zasu biyo baya na hukunce hukuncen shiga Makkah Sannan sai biyo baya da kwatanta yaya ake aikin hajji Sannan sai biyo baya da bayyana hukunce hukuncen umara Sannan mutumin da ya riga ya shiga harama ta aikin hajji Wadannan abubuwa ne suka haramta akan shi Sannan Imam al-Bukhari ya biyo baya da bayyana falalar Madina Ma'ana inda kana da basira Toh yadda ya jero dinnan ba abu ne wanda zai boyu gare ka ba wato yayi kokarin kwatanta maka aikin hajji ne a bisa gabobin da yake faruwa Kamar misali mutum ya tashi karantar da kai sallah Sai ya fara da kabbara harama Sannan dora hannu a kirji Sannan karanta Sannan ta'awuzi Basmala Fatiha sura Kabbara Daga hannu Dagowa misali kun ga abun ba a boye yake ba wato yana kwatanta maka sallan ne yadda take Ba wai yazo ya fara maka da bayani akan abinda ya shafi Sannan ya tafi bayani dangane da tahiya sannan ya dawo dangane da kabbara harama a'a sai ya biyo maka abun daya bayan daya toh ba abune wanda yake boyayye ba a sallali yake Menene hajji? Malam yace A larabcin akace hajji ana nufin nufi kawai nufi Ina fata an gane Ka nufi wani wuri kawai sai ace hajji ya nufi wani wuri Amma al-Imam Khalil babban malami kwararre a cikin harshen larabci Cewa yayi Yawan ainihin wato zuwa Wurin wani abu wanda ake girmamawa Wato duk wani abu wanda ya zama abun girmamawa ne Toh yawan nufin shi da ziyara shi ake nufi asalin hajji da larabci Amma a cikin shari'ar musulunci Mutum ya nufi Daki mai alfarma Da wasu ayyuka ke bantattu Malam yace kun ji aikin hajji ko? Kun ji abinda ake nufi da aikin hajji shine ka nufi dakin Allah Da nufin wasu ibadoji na musamman Toh sai a kira wannan ibadoji na musamman In anyi su da nufin hajji sun zama hajji in anyi su da nufin umara da gwargwado dai Ko kun fahimta? Toh amma da yake muna maganar Toh nufin dakin Allah Da nufin ibadoji na musamman wadanda sune ibadojin hajji din Kana iya cewa Kana kuma iya cewa Malam yace duk wadannan guda biyun daidai ne sun tabbata a harshen larabci Amma Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi Ya bada labarin cewa In kaji ance anyi kasara ha sabe din Toh lugan mutanen Najd ce Wato Najd Itace kamar kace Can gabashin Saudiya tun daga abinda ya kama wajajen sir da sauransu a yanzu An fahimta? Amma ba nan yake nufi ba abinda yake nufi da Najd gaskiya Shine Najd ta bangaren Iraki Kana sauka daga wannan gangara ta kasashen Yaman Toh shikenan wannan tudu da zaka hau sune har kasashen Iraki toh su ake kira Najd Wannan shine gaskiya Toh akace mutanen wannan yanki na bangaren Iraki da makamantansu sune suke cewa Hijju ina fata an gane Ita kuma Ga wasu wadanda su ba Jama'a kun fahimta? Kenan Malamin ya daidaita a dunkule cewa larabawa suna iya cewa hajji suna iya cewa Amma sai kuma ya dauko cewa amma larabawan nahiya kaza suke cewa Larabawan nahiya kaza kuma su suke cewa ainihin Sannan Ya bada labarin cewa wani malami mai suna malam Ya bada labarin cewa in akace Toh sunan kenan aikin hajji Masdarin kuma shi ake wa Hajja Ya zama Wani malamin shi kuma ya a kasanta haka Cewa Ismin kuma shi ake wa kasara ace Jama'a kun fahimci wannan? Wannan duk tattaunawa ce ta masu larabci a takaitaccen takaitawa Wanda duk ka fadi insha Allahu ta'ala daidai ne Zaka iya cewa Saboda al-Qur'ani yace Sannan kuma Qur'ani yace me? Dan haka duk daidai ne Wannan tattaunawa ce ta masana harshen larabci kawai Aikin hajji wajibi ne Shari'ar musulunci ta tabbatar da wajabcin shi kuma duk musulmi sun hadu akan cewa ba makawa Ba sabani aikin hajji wajibi ne Sannan malaman musulmi sun hadu Cewa aikin hajji Ba abinda zai sa mutum yayi Sannan ya sake maimaitawa ya sake maimaitawa A matsayin cewa dole Sai in ba kan ce ya dauka wa kanshi amma in dai kai so daya Toh shikenan sauransu duk abinda zai biyo baya kuma babu dole Amma in kai ba kan ce Bayan kayi aikin hajji na farilla Rannan sai wata larura ta same ka Haka siddan sai ka bude bakin ka kace Allah Idan kayi yaye min wannan larura ni kuma na daura wa kaina lallai ilalla zanje inyi aikin hajji Toh shikenan anan hajji ya zama dole akan ka saboda cika ba kan ce Sai dai kamar yadda zamu zo mu samu nan gaba a cikin Asali fa ba kan ce shari'ar musulunci bata son kayi Kya matar da kai ake kar kayi saboda Annabi a cikin hadisin Muslim Yace shi ba kan ce Ba abinda ainihin wato yake Kara maka na biyan bukata Sai dai kawai in kai marowaci ne toh dalilin a kwantalu wani abu ne a jikin ka Baka sadaka Baka kyauta Duk wadannan alhairai baka yin su Rannan sai kake da wata bukata a wurin Allah sai kwakwalwar ka kawai sai ta nuna maka cewa in kai wa alkawar in kai wa Allah alkawarin Idan an biya ka bashin dubu goma nan zaka yi sadaka da dubu uku Shikenan sai kuma wannan tunani da yazo maka sai ka gaskata shi Sai kace oh ya Allah Ni ko da zaka taimaka yau a biya ni bashin nan Allah ni kuma zanyi sadakar dubu uku Toh wannan alkawari da kai wa Allah ko bazai sa Allah ya gaggauta biya maka bukata muyi biyan bashi ya biya ka ba Amma in ya zama kayi magana daidai da Allah dama zai biya maka bukatan ka a yau Toh shikenan kana fadan haka ba dan ka fada ba Dama Allah ya riga ya tabbatar yau ne Toh sai Annabi yace dama marowaci ne kai kenan Allah ya kaddari almajirai su ci wani abu ne Dan haka nazar Baya gaggauta komai Amma in kayi shi kuma toh ya zama ibada Dole ne ka cika shi Sai dai in akwai sabon Allah a ciki Misali idan kace in bukatan ka ta biya ka samu kudi kaza Zaka sha giya kwalba uku Toh haramun ne ka cika wannan ba kancan Sannan akwai inda zaka yi bakancan wata ibada Toh baya zama dole sai kaje ka cika ta a wannan wurin Kamar kana Sokoto Sai kace kai kuwa in Allah ya biya maka bukata kaza Toh sai kazo zariya masallacin su Albani kayi sallah a zahar Sai Allah ya biya maka bukata Ko kuma sai kayi sallan nafila Toh duk masallacin da ka samu a Sokoto ko kuma duk inda kake kaje kayi wannan sallah ya isar ba sai ka taho masallacin su Albani ba Ina fata an gane Amma idan Zuwa masallacin Ka'aba ko masallacin Annabi ko masallacin Baitul Maqdisi kayi irin wannan alkawarin Toh malamai suka ce iya kacin shi mustahabbi shi ma kaje kayi a can din amma in ba nan kai ba Alkawarin Toh ko ina ne Halal ne ka tafi ko ina kayi Allah yasa kun bambance Idan kace in Allah ka biya min bukata kaza Zanje masallacin Annabi inyi nafila raka'a biyu Toh idan Allah ya biya maka wannan bukatan ba dole bane sai kaje masallacin Annabi zaka iya tsayawa a masallacin angon ku kayi wannan sallan ta isar Toh amma inda zaka tafi masallacin Annabi toh mustahabbi ne Amma ba dolen dole ne sai kaje ba toh amma duk wani masallaci in ba na Ka'aba ko na Annabi ko masallacin Kudus ba Idan kayi irin wannan alkawarin Toh zaka iya yin wannan ibada a duk inda ta samu Jama'a mun fahimti wannan da kyau? Idan kai alkawarin zaka yi wata sadaka ko zaka yanka wata dabba kayi sadaka da ita A wuri kaza sai kazo sai ka bincika sai ka gano cewa wannan alkawari naka ya cika Bukatan ka ta biya Amma sai ka gano cewa a wannan wuri matsafa suna yanke yanke Yan tsubbu suna sakin dabbobi a wurin suna sadaka da su ga aljanu Toh bai halatta kai kaje wannan wurin kayi ba sai kaje ko ina ne sai ka yanka dabbar ta isar Samar da abinda kayi alkawari shine yake da muhimmanci Ba inda kayi alkawarin ba Jama'a kuna fahimtar wannan? Annabi Yaqub Yayi tafiya Sai zuciyar shi ta riya mai cewa kamar bazai dawo ba A halin tafiyar sai yayi wa Allah
[Segment 2/5 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker unknown]
Allah in ka taimake ni ka dawo da ni cikin iyali na lafiya. Ba zan sake cin naman rakumi ba, na haramta wa kaina naman rakumi. A cikin dokar da su su annabi Yakubu suke aiki da ita. Ya halatta ka haramta wa kanka wani abu daga cikin abubuwan da Allah ya halatta maka. Domin ka nemi kusanci da Allah ta hanyar wannan haramtawa amma a dokar su ba tamu ba. Annabi Ibrahim ai annabi Yakubu. Allah ya warkar da shi ya dawo gida lafiya. To yanzu ya haramta wa kanshi cin naman rakumi. Shikenan sai dai na cin naman rakumi. Da 'yan shi suka taso sai suka ga baban su baya cin naman rakumi a matsayin naman rakumi ya haramtu gare shi. Da haramtawar da ya dau alkawari ba da haramtawa Allah ba. Har suka girma. Kunne ya girmi kaka cewa ai su haram ne su cin rakumi, haram ne su cin rakumi. Shine har zuwa zamanin annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallama. Jikoki da tattabakunnar annabi Yakubu sai suka yi da'awar cewa su haram ne cin naman rakumi gare su. Sai Allah ya saukar da aya cikin suratul Ali Imran. Yace. Duk wani abinci halal ne 'ya'yan annabi Yakubu su ci. Sai dai abin da shi Yakubu ya hana kanshi da kanshi shine ga kanshi yake haram amma su 'ya'yan shi halal ne su ci. Sai suka yi karyar cewa ai karatun ma yana cikin Attaura. Sai Allah yace a'a. To ai wannan abun ya faru ne tun kafin a saukar da Attaura. Me ya hada Attaura da wannan abun? Ina za'a samu wannan karatun a cikin Attaura? Ku zo da Attauran a ja baki a fasa. A karanta a ji ina ne karatun yake. Saboda haka ku kiyaye jama'a. Aikin hajji farilla ne. Sau daya akan musulmi. Ga aya zamu zo mu karanta wadda take farlantawa ga wanda ya samu iko. Wanda kuma ya samu hanyar tafiya lafiya kalau. Jama'a ku kiyaye wannan da kyau. Bayan nan babu wani dalili da zai sa hajji ya zama farilla a kanka. Sai in an gano wata matsala kamar ko kuma alkawari irin wannan. Kun ga in ka fahimci haka. Sai ka saukake wa kanka. Shekara ta zo ba na baka da hali shikenan. Ba dole bane. Musamman malamai. Da matasa wadanda suka fara tasowa. Ba daidai bane tunda hajji dinnan ba farilla bace ko a halin farko ba ka da hali ba farilla bace. Ka je kana zubar da ruwan mutuncin malanta ka saboda a baka kujerar aikin hajji. A yau wannan na daga cikin musibar da muka samu kanmu mu a ahlus sunna. Saboda haka matasa ku kiyaye. Zuwa aikin hajji ba biki bane ibada ce. Idan kana da hali Allah ya wajabta maka ka je baka taba zuwa ba sai ka je. Idan kana da hali bayan kayi ta farilla zaka iya zuwa a matsayin mustahabbi. Amma ba ka da hali kar ka tafi hukuma alhazzai ka je ka wulakanta kanka. Ku kiyaye jama'a. Don malaman ahlus sunna an wulakanta mana su a lokacin mulkin Yakowa a Jahannama. Za su tafi hukuma alhazzai. Suna dan raragefe. Karara. Aka sa wanda ya ci mutuncin su dama an sa shine don ya ci mutuncin su. Karara zai fito har tsakar filin ofishin hukuma alhazzai. Yace yauwa malaman izala an gama fada da mu. Yanzu ne mun samu mulkin hannu shine an zo mu bada kujera to ba za'a baku ba ku tafi ku bamu wuri shaku 'yan iska ku tafi ku bamu wuri. Ku ci mutuncin mutanen mu. Ba haka ba ma. Akwai malamin da da kudin shi ya je zai sai kujera aka wartake shi. Da kudin shi. Ya je zai sai aka wartake shi saboda shi malamin ahlus sunna ne. Me kake tunani in ya je roko? Umara. Umara ma ba dole bane sai in kana da hali in kayi sau daya. Ta sauka a kanka. Amma in kai baka da hali fa kar ka je ka roki wani. Saboda haka zamu zo mu tattauna wasu hukunce hukunce baka da halin zuwa aikin hajji sai wani ya baka kujera. Ba wani sharadi da zai maka. Cewa ga kujera amma dole ka je ba zaka siyar ba karya yake ya rike a bar shi. Ya kawo kujera hajji ya baka. Baka taba zuwa hajji ba ba dole ne ka je ba. Sai ka duba. Yanzu kai menene kake da bukata? Baka da masara. Baka biya kudin haya ba. Baka da sutura kai da iyalan ka. Sai ka same shi to ranka ya dade na gode Allah ya saka da alheri. A nemo mai siyan kujerar da ka bani. A siyar a bani kudin na gode Allah ya biya ka. Kai yi maka sharadi cewa dole sai ka je babu wannan sharadin ya rike a bar shi. Da yawa an biya wa mutane aikin hajji. Zamu hadu da su muna zaune da su a wurin aikin hajji sai ka ji mutum kuma ya zo yana wasiwasi toh. Yanzu in na koma gida ya zan yi gashi yanzu na zama alhaji. Duk masu bi na bashi yanzu da wadanda da suka dan saba taimaka mun su basu ma taba zuwa ba to ni kuma na zo ah. Wallahi ko haka zamu zauna da su ah me ya kawo ka to yace toh an bani ne a karamakallahu bayar da na iya a'a. Da sai ka zauna ana binka dubu talatin sai ka biya bashi. Ka je ka yi cefane. Ka samu jali. Ka samu babur. Uwar gida ayi mata suturu 'ya'ya a biya musu kudin makaranta kowa. Ya dawo cikin hayyacin shi. To ka ga duk gidan kun yi aikin hajji kenan kun je hajji mu kenan. Asirin ku ya ruku shine hajji mu. Wannan itace shari'ar Allah jama'a. Allah itace shari'ar Allah. Amma an dauki kujera an ba wani wallahi ya nemi ya zautu. Ya nemi ya zautu saboda da ya dawo ya shiga cikin rigingimu da dama. Ya sa ba ana dan taimaka mun shi da rayuwa ana dan yin abubuwa to yanzu a to yanzu ai kai alhaji ne to mu kuma a kasar mu an ce maka kai alhaji kawai abin da ake gani to akwai kudi. Kai alhaji ne to alhaji guda kuma ka zo neman masara wurin mu mu da bamu taba zuwa ba. Sai abin ya zama ma hajji ya fad da magana ake ah alhaji da kanka kuma zaka zo kofar gidan mu yanzu ku ba alhazzai bane. Ka gani. An saka ka a cikin rikici har ka mutu in ba Allah ya rufa maka asiri ba Allah ya kiyaye. To shine sai malam yake cewa. Aikin hajji a matsayin wajibi ba dole bane ba zai sake zama dole ba sai dai in ba kance kaiwa kanka ko kuma wani uzuri haka. Malamai suka ce toh. Shin wajibi ne in na samu dukiyar yin aikin hajji in mar maza in je ko kuwa zan iya jinkiri. Misali. Na je nayi wani kasuwanci na samu kudi. To amma sai kudin suka zo mana akwai wasu abubuwa sai na ga cewa to yanzu. In sai gida. In gyara iyali na wannan ba bani akai ba nawa ne. Kun ga hajji ta hau kaina. To shin dole ne in yi mar maza in yi hajji ko kuwa ina da 'yancin jinkiri. Malamai sun tattauna dangane da wannan. Malam yake cewa wannan sabani ne wanda yake. To bari mu tsaya mu tattauna wannan magana amma duk wanda yake da littafin. Ya je ya dauka ya baiwa mas'alar hakkin ta. Amma gaskiya saboda Allah wajabcin aikin hajji ko. Abin da wannan maganar take nufi da Hausa shine. Ba dole ne in na samu kudin aikin hajji a bana. A halin ban taba yi ba dole in tafi bana bana a'a. Ko da babu wata larura. In nayi jinkiri ba laifi bane. Ko da babu wata larura sai dai ana kwadaitar da kai. Idan babu wata larura din to kai gaggawa amma ba dole bace yin gaggawar. Saboda haka ka je ka sa kudin ka a hukuma alhazzai. Duk. An zo an yi maka. Ban kwana. Sai aka tafi sai aka ce matsala ta faru. Shikenan sai ka dawo. In ma hukuma alhazzai ta maimaita maka da kudin ka wanda haka ya dace. In ma kuma a ce za'a ajiye maka wadannan kudi yadda badi in tazo kai baka da sauran wata ta ta burza kana da tabbacin tafiya. Da gwargwadan yadda akai kuma ka amince. Ko an fahimta jama'a? Saboda haka aikin hajji wajibi ne. Amma wajabcin yin shi yana da yalwata gare ka na ka jinkirta a tsanaki sai ka je kayi. Sai dai ana kwadaitar da kai game da yin shi. Da gaggawa don na daga cikin matsalar da malamai suka ce in ka kwanta ka mutu. Baka yi ba a halin ya wajaba kanka kana da hali kuma akwai matsala. Yana daga cikin abin da malaman tafsiri suka fitar a karkashin. Malamai sun fitar da cewa zakka. Da aikin hajji suna daga cikin abubuwan da Allah zai tuhumce ka in ka zo mutuwa. Kana da hali da sararin ka yi kayi sakaci. Sakaci to sakaci ne za'a zarge ka akai amma in ba sakaci bane. Ka dauka abu ne wanda tunda akwai yalwatan lokaci to bari ka kinkin tsawon wasu abubuwa. Ko kun fahimta jama'a? Musamman irin halin da ake samun kai a ciki a yanzu. Zaka ga matashi ya taso yana kasuwanci ko yana aikin gwamnati. Yana gidan haya ko yana gidan gado ko yana gidan aro ko maka mantan haka. To baka tatan sai ka ga Allah ya rufa mai asiri cikin 'yan watanni kadan Allah ya kawo mai budi. To sai ya tsaya ya duba. Wadannan abubuwa ne yake da bukata tunda dai ya ga kudin sun fara shigowa sai ya marmaza sai ya yi wadannan abubuwa. In ya so daga baya sai ya kintsa sai ya tafi aikin hajji. Sannan malamai sun sake tattaunawa yaushe ne farilla aikin hajji ta sauka. Wasu malamai suka ce ai tun kafin ayi hijra tun ana Makka. Hajji ta wajaba malam yace wannan maganar ba daidai bace kawai. Wannan maganar yanke ba daidai bace annabi yana zaune a Makka. A lokacin ibada aikin hajji ba wajibi ba ce. Ina fata an gane wannan maganar ta sabawa maganar da malamai suke akai. Wasu kuma suka ce a'a bayan hijra ne aikin hajji ya zama wajibi wannan maganar itace daidai. Sai dai kuma. Sannan sai ko malamai suka saba to shikenan yanzu ya tabbata a Madina ne aka farlanta aikin hajji. To amma a wace shekara? Mafi yancin malamai suka ce shekara ta shida bayan hijra. Don a wannan lokacin ne maganar Allah ta sauka cikin suratul Bakara. Da Allah yace. Hajji da Umara. Ku yi su cikkakku cip cip. Ga Allah madaukakin sarki to wannan dokar ta sauka a shekara ta shida ne. Amma fa duk wannan fassarar za'a gina ta ne. Ko. Wato za'a gina wannan fassarar ne a bisa maganar cewa abin da Allah yake nufi da yace Ku cika hajji. Yana nufin farkon. Farlanta aikin hajji. Ku tsayar da hajji ka ga a nan ya zama me? Ya zama farkon farlantawa kenan umarni ne ake bayarwa ku tsayar da aikin hajji da Umara saboda Allah. Ko. Ai umarni ne. Shi ya fitar da wadannan kira'o'i. Daga wadannan malamai Alkama da Masruk da Ibrahim al-Nakha'i daga wadannan malaman da isnadi mai inganci. Duk wadannan bayanan suna nan a cikin tafsirin al-Imam ibn Jarir al-Tabari. A karkashin wadannan ayoyi na suratul hajji ai na suratul Bakara da kuma sura ta Ali Imran. Wasu kuma suka ce abin da ake nufi da Cikawa ko. Shine ainihin yin abun a cike. Bayan da ainihin aka fara. Ma'ana bayan da aka fara yi. To sai ya zama an karasa kar ka fara aikin hajji ka tsayar shine Allah yake cewa Ma'ana shin yana nufin ku cika aikin hajji ne ko ku yi aikin hajji. Amma ingantacciyar fassara itace wadda muka gabatar da farko gaskiya. Ku yi aikin hajji saboda Allah umarni ne to sannan sai kuma maganar cikawa din in za'a kuyi. To ka ga wannan yana nuna kenan dama hajji din ta farlanta yanzu aya ta zo ne don ta ce ayi a cike. In har wannan fassarar da itace daidai. In tana umarni ne da cika hajji. Ko kuwa yin aikin hajji in ka ce yin aikin hajji. To ya nuna aya ce ta farlanta aikin hajji. Idan kuma ka ce aya tazo ne tana umarni da a cika aikin hajji to dama ta bada Kur'ani ko kuma shari'a ta bada umarnin ayi tuntuni yanzu ana umarni ne da a cika abin da aka bada umarni tuntuni. Amma dai kar a manta. Akwai Wanda Ya zo wurin annabi ne a shekara ta biyar bayan hijra. Ya zo ya samu annabi sallallahu alaihi wa alihi sallama. Sai da ya shigo da rakumin shi har cikin masallaci ya samu wani wuri ya daure shi. Ya dirkusa da shi. Yana shigowa yace jama'a barkan ku da warhaka. Cikin ku waye Muhammadu ne? Suka ce wannan farin mutumin nan da ke kashin gida. Yace ibn Abdul Muttalib kai ne? Yace kwarai yace to nazo zan maka tambaya ne. Amma zan tsananta maka kuma kar ka ji haushi na. Annabi yace ina sauraron ka. Ya rinka wa annabi tambayoyi. Mai wa'azi ya zo yace mana ka ce Allah daya ne mai wa'azi ya zo yace ayi sallah mai wa'azin ka ya zo ina gaskiya ne annabi yana cewa kwarai da gaske. Da ya gama sai yace to ni suna na Daga cikin kabilar Banu Sa'ad ibn Bakar wato daga garin Sahali matu Sa'adiya ma'ana ni kawon ka ne. Ka sha nono a garin mu mu iyayen ka ne. To mai wa'azin ka ya je mana shine aka turo ni in zo in wakilci jama'ar garin mu. Ya ji wa'azi ya ratsa shi. Yayi wa annabi alkawarin musulunta. Ya kuma tafi da alkawarin zai je ya musulantar da mutanen kauyen su. Yana isa kauyeye ya kuwa aka taru. Sai yace Allah ya tsine wa Aka ce in in dimamu saurara yace Allah ya tsine musu albarka aka ce in in zaka haukace zaka tabu in in dimamu yace tur da ku. Kuma da baku fahimci wadannan gumaka bane ba abin da za'a su iya wallahi karya ne kawai mu kanmu waya waye mun je bariki mun samo wa akida. Ina fata an gane. Ya yi musu bayanai tsaf. Duk sai suka musulunta gap suka musulunta ba wanda ya rage kowa sai ya musulunta. To dimamu dan A cikin tambayoyin da yawa annabi kun ji dalilin da ya sa malam ya kawo hadisin. Akwai cewa mai wa'azin ka ya zo ya ce zamu yi aikin hajji. Haka ne annabi yace kwarai to kun ga wannan yana nuna tun kafin shekara ta shida. Tun kafin shekara ta shida wadda waccan aya ta sauka. Yana nuna akwai umarnin aikin hajji kenan. To wannan kuma yana karfaface wa kenan da ayan nan ta zo ta ce Cikawa take umarni. Kun je an yi kan kan kan. An fahimta? Gashi yace. Kamar yadda Dimamu dan ya je wurin annabi ne a shekara ta biyar. Idan ya tabbata cewa shekara ta biyar din ne. Me ya sa yace Saboda Akbari ne. Irin dan wa'azin Turmi ne irin masu wa'azin na batar dinnan da suke tsayawa a kwana. Amma yayi rubuce rubuce. Don kar ka je yana da littafi ka ce a'a to yaya kuma. Makaryaci ne. To shi yasa yace in ya tabbata a shekara ta biyar din ne. In ya tabbata cewa. Dimamu ya zo shekara ta biyar ne ga annabi sallallahu alaihi wa alihi sallam. Gaskiyar lamari. Aikin hajji. Ya tabbata a cikin bayanan nan na ainihin dimamu dan Sai dai tabbatar da zuwan dimamu a shekara ta biyar shine malamai basu yarda da tabbatar da zuwan cewa shekara ta biyar ba ne. Sun kai sun komo. Shi yasa ka ji ibn Hajar yace in ya tabbata. To malamai da yawa suna shakkar. Cewa shekara ta biyar ne dimamu dan Amma in Zamu samu hadisin a nan gaba a wannan lokaci zan kara tantance mana mas'alolin Don mun karanta hadisin dimamu a baya a wasu halaye a wasu dalilai can daban. Zamu zo mu sake karanta insha Allahu. Malam yake cewa to za dai a ta sake tattauna wannan mas'ala insha Allahu in an zo bayani dangane da Umara. Dangane da falalar aikin hajji fa. To falalar aikin hajji shahararren abu ne. Musamman dai irin yadda ka ji ayar tayi kwankwasa dangane da mutumin da yake da aikin halin ya je aikin hajji ya ki. Allah ya dora wa mutane su ziyarci.
[Segment 3/5 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
ya ci dakin shi amma cikin mutanen sai wanda ya samu iko da hali da yadda zai je zuwa ga aikin hajji. wanda ya ke mai mayaki ma'anar kafara kenan kana da hali sai kai keme maka ki Allah yana ce maka ya wadata ba kai ba duk duniya ma su ki zuwa aikin hajji ba abun da zai rage Allah duk duniya su je aikin hajji ba abun da zai kara Allah to kaga wannan a ciki akwai kwankwatsa ko? to wannan kwankwatsar tana nuna kenan aikin hajji yana da falala to za kuma mu zo mu je hadisai wadanda daga cikin wadannan hadisai za mu ji wanda duk ya aikin hajji bai yi kwankwasa ba bai yi jimai ba bai yi maganganun batsa ba bai yi duk wasu sakarce ba to zai dawo garin su kamar randa mahaifiyar shi ta haife shi an wanke shi daga zunuban shi subul ba shi da sauran zunubi ko kwa daya to kaga wannan yana nuna falala ta aikin hajji Allah ya taimaka
[Speaker seg3-spk:1]
amin
[Speaker seg3-spk:0]
malam ya ke cewa akan haka wanda shine lamba hadisi na dubu daya da dari biyar da sha tara insha Allahu ta'ala za mu zo mu karanta shi nan gaba kadan sai dai abun mamaki akwai hadisai da yawa da suka zo suna bayanin falalar aikin hajji amma Bukhari bai kawo ko kwa daya ba sai hadisin wata mata yar kabila Khath'amawaw wasu mutane ne cikin larabawa Annabi yana cikin tafiya a lokacin aikin hajji akan rakumin shi ya goya sahabyar shi Fadul dan Abbas wani saurayi ne kkyawa sai wannan mata sai ta tsai da Annabi ita ma matar budurwa ce kkyawa sai tana tambayar Annabi cewa gashi aikin hajji ya zama farilla ga baba na ya manyanta ba zai iya zama akan dabba ba balle ya dora shi a kai shi aikin hajji ko na iya mishi aikin hajji sai manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama sai ya ce kwarai da gaske to ta tsai da Annabi tana wannan tambaya sai Annabi ya lura wannan saurayi dake goye a bayan shi akan rakumi ya kwalla mata ido ita ma kuma hankalin ta yana kan shi sai Annabi ya juya kan shi daga inda take sai ya juyo kan shi daya bangaren to wannan hadisin Imam al-Bukhari shi kadai ya kawo dan ya bayyana falalar aikin hajji in haka dubi hadisin da kyau to a boye falalar aikin hajji take a ciki za mu zo mu tattauna zaka ga akwai falalar aikin hajji din amma sai an ci kwakwa za a iya ganowa a cikin hadis ina fata an gane kamar kace Imam al-Bukhari da ya kawo wannan hadisin na yana son ya fitar da falalar aikin hajji ne ta nuna gashi fa matan nan tace baban ta bai da hali bai da lafiya amma kuma Annabi yace lallai ilalla ya tsufa ba zai iya ba eh to wani ya mishi saboda dai falalar abun madadin Annabi ya ce to shikenan tunda ya manyanta Allah ya sauke mishi sai ya ce a'a dan dai uban ya samu wannan falalar sai Annabi ya ce ta tura ayi wa baban tayi wa baban ko makamantan haka to kun ji ta inda falalar ta fito ma'ana lallai kar ki sake baban ki ya mutu bai tafi da falalar aikin hajji ba ba zai iya zuwa ba eh to kiyi mishi ko kisa ayi mishi amma dai lallai kar ki sake tunda akwai hali to kaga yana nuna falalar a fa kai take ne malam ya ke civa malam ya ce zai tattauna insha Allahu ta'ala dangane da hadisin wannan mata da kuma irin hanyoyin da aka ruwaito wannan hadisi daga Zuhuri wannan hanyar ta sha bambam da wannan da sauran tattaunawa a karshen babin dake bayani akan abubuwan da suke haramun ne ga mutumin da yake haramun aikin hajji amma dai malam yace abinda ake so ka gane a nan Imam al-Bukhari da ya kawo wannan ayar itace ko? ya kawo wannan ayar ne a nan dan ya bayyana mai ake nufi da da Allah yace Allah ya farlantawa mutane su ziyarci dakin shi ga wanda yake da iko to mai ake nufi da iko? Imam al-Bukhari yana nufin yace iko ba yana nufin guzuri da abun hawa ba istita'a din iko na da alaka da dukiya kana da kudi jikin ka zai iya ko kun fahimta jama'a? banda guzurin abunda zaka ci banda abun hawa kana da kudin sauran wasu hidindimu kana da karfin da zaka iya zama duk wadannan Imam al-Bukhari ya tattaro su yana nufin suna daga cikin domin da ace an kebance cewa abinda ake nufi da iko shine guzuri da abun hawa ya zo a cikin wani hadisi ne da bai inganta ba zaku ji malam ya fadi ko? haka ne? haka ne? da mutumin da yake cikin wani tsanani to da sai ace shikenan a daure shi akan jakin a san yadda za a sa wani belt a daure shi ko da zai sha tsanani akan haka daidai sai anje da shi to amma da yake ana so a nuna idan ba zaka iya zama akan dabba ba to kamar yanzu idan ya zama tsoho yayi rauni raunin da ba zai iya hawa jirgin sama ba sai ku kama shi ku dora shi a zaunar da shi akan kujerar jirgin sama tsoho ya tuntsure haka to baza ace a daure shi da belt ba a'a baba ya hakura amma a biya kudin aikin hajji da sunan shi wani ya tafi ya je yayi mishi za mu zo mu tattauna wannan ya ake yin wakilci game da aikin hajji kaga kenan ashe ko akwai kudi akwai guzuri ana duban lafiya zai iya yi da wannan ne kun ga za a dubi masalan mata masu ciki mace mai tsohon ciki yaya masala zata kasance gare ta amma dai Annabi a zamanin shi ya bar mace da tsohon ciki ta tafi saboda zata iya to ashe ciki ba zai iya zama dalili kai tsaye da za a hana su zuwa aikin hajji ba ya danganci yadda cikin yake ina fatan mun gane Allah madaukakin sarki ya taimaka malam Abubakar malamin mai risala ne mai littafin ya ce wani hadisi wani hadisi da yake ambatan cewa indai kana da guzuri indai akwai abun hawa to dole ka tafi ya ce wannan hadisin bai tabbata ba ku karanta rashin ingancin hadisin ko da a cikin da cikin a cikin babin aikin hajji zaku gani hadisin bai tabbata ba cewa an tambayi Annabi game da me ce ce menene iko da Allah yake magana akan cewa aka ce sai Annabi yayi bayani cewa indai yana da guzuri yana da abun hawa to dole ne to zai zama ga guzurin ga abun hawa to amma bai da lafiya ko bai da karfi ko ya manyanta ko makamantan haka wallahi wani lokacin sai mu rinka lura jama'a mu da muke yawan zuwa aikin hajji alhamdulillahi wallahi muna fuskantar matsaloli da wasu mutane wadanda na taba baku labari wani dattijo dan shi ya biya mishi aikin hajji Umara kadai aka shiga aka yi yaje daidai irin wadanda aka kai a makarantar din nan to yaje a rintsi yaje ya shiga ya sha wahala da kyar ya fito yana dange shi yana ta fada baba lafiya ya ce Allah ya isa dama ya turo dani in sha wahala to Allah ya isa ban yafi ba nace to yanzu wanene ya ce da na nace me yayi ya ce shi ya kawo ni nan shi ya kawo ni kamar ya zauto to ina zaka ya ce yana tara mota ne motar ko wato sai ya fadi wajan kasar Katsina din nan motar wajan dan ja yake tarewa wai dan ja zai je abin nan a cikin hanyoyin kauyukan nan na dan ja wai yana tare motar dan ja ne zai sauka a wani gari haka kaga kamar ya zauto duk hawa jirgin da aka yi ya manta yanzu yana cewa yana basawa ne fa ko yana basawa ne ko yana nan cika ji ne yana sanya tara mota dan ja ne zai sauka garin su kawai da kyar na lallashe shi tukunna da kyar na lallashe shi aka samu mutanen garin su akan abun nan ina fata an gane to zaka yi ta ganin abubuwan dariya wasu tsofafi sun bata inna yaya ce sai da na ce mata yanzu mun ka wuce gwadaban Alhaji mai dankali kadan mu kadan mu ketare za mu bace kaga ita tana tunanin suna cikin Sokoto ne sun wuce gwadaban Alhaji mai dankali tana cewa kawar ta kada a wuce ga gwadaban to kaga irin wannan akwai matsaloli jama'a akwai matsaloli Allah ya kyauta yasa har nake sha'awar gaskiya wasu abubuwa da da nake karantawa na Ibn Jauzi Ibn Jauzi yana da tattara labarai irin haka wani abun sai in yi mamaki amma in kana mu'amala da alhazai duk abunda kake tunani ko wallahi tallahi malam wani zaka ji sunyi fiye da haka jirgi ne yana gudu da tsakar dare jama'a wajan karfe biyu na dare namu na nan kawai sai ga wani malami ya taso yana ta tsaki nace mishi akaramakallahu yaya yace gudu yayi yawa gudu yayi yawa shine zan je in gayawa direba ya rage gudu ko ya tsaya zan sauka to kaga yanzu kai kaga kaga akwai masala gudu ne yayi yawa wai gudu yayi yawa yazo zai wuce ne wai zai je ya gayawa direba gudu yayi yawa ya rage gudu ko kuma ya tsaya in sauka wallahi wadansu abubuwan in ba dan a gaba na akai ba sai in yaya wadannan abubuwan Allah ya kiyaye to jama'a kun dai ji irin wannan malam ya ke cewa ita wannan aya ta al'kur'ani ta zo baki daya ne tana magana dangane da duk wani abu wanda ainihin wato ya shafi idan hukumar alhazai tace baza ka ba shikenan istita'a bata tabbata ba baka da idan hukumar Saudiyya ta turo passport dinka aka ce kai an soke ka bana baza ka je ba shikenan istita'a bata samu ba saboda haka wannan aya ta shafi komai ila bayanin bata da bukatan wani bayani duk istita'a kawai ta shikenan kazo zaka wuce sai aka ce a'a koma ko kuma anje da kai Jidda sai a dawo da kai ace ka taba yin laifi tare da cewa nayi sensing wani abu wato basu shirya ma abun ba nayi haka ne lokacin da passport dina ya cika sai na koma a sake mun sabon passport da aka je aka sake sabon passport din sai na gan lambar sabon ta sha bambam da ta tsohon to shikenan duk wanda ya san yadda abubuwan computer suke shikenan anyi breaking security din don dama zasu sa wannan lambar passport din ne naka sai su gane ka taba zuwa ko ka taba yin wani laifi ko wani abu makamancin haka sai ya zama to passport dinka na da ya cika da abunda ya kamata ko shi wannan din za a sake gurza maka amma sai a sake baka ratan shekaru sai ya zama wannan lambar ta zama code dinka haka ya kamata haka ya kamata to sai ya zama lambar passport dina tsohon ta sha bambam da sabon da haka yanzu in na mika wannan passport din shikenan sai a dauka sabon Alhaji ne to sai magana dangane da dangwala hannu da sukan ce eh dangwala hannu suna iya suna iya ganowa amma wadannan abubuwan da dama kuma ba a aiki da su hatta a can Saudiyya din sai fuska da yan uwan mu yan Saudiyya basa gane mu ma gaba daya ko daya basa gane mu mace ko da namiji ko a shiga mu basa iya gane mu fa ko a shiga dan wani yana ce mun wannan wai namiji ne ko mace nace wannan mace ce baka ganta da kaya mata ba yace ki ya zai gane ya ganta ina ce ma gashi da atampa sai ya nuna mun wani yace ba ga wannan ma da atampa ba sai nace baka ganin wannan namiji ne baka ganin shi da gemu yace wallahi ba a gane basa iya gane wa ko kun fahimta jama'a da yake nan akwai alhazan da zasu je sai su ki dawowa sai su je sai su siyar da passport din su wani ya siyar real dari biyu dubu takwas shikenan ya soke kudin shi yaje ya gudu to akwai kuma wasu alhazai su kuma da daddun tafiya ne yanzu suna son dawowa sai kawai da ya dauki wannan passport din yana zuwa Jidda kawai bab bab sai su buga sai su ce ya wuce shikenan akwai passport din ba ya rabe ai babarbare muka doro ba ya rabe a kai yazo ya wuce kuma kowanne da tsaga wancan babarbaren yana da tsaga a hoton wannan bai raben kuma yana da tsaga a fuskar shi yazo ya wuce mun hadu da shi ne yace yana son tafiya gida ba ya da kudi nace mishi ba komai zaka tafi insha Allahu kaje ka hada kayan ka yace kayan shi a hade yake nace ba ya da ko masala ranar tafiya kawai na jefa shi a mota yana ta wani abun nan nace dan Allah ba wanda ya san kai wani abu ne kai ka ka ka ka ka ka ka rufa akan ka asiri ka saki jiki kawai muka tafi kawai shikenan na samu irin wadannan suna da yan abun nan mai ke da suna yan kamasho na samu wani dan kamasho nace dan Allah bani passport guda daya yace kai Alhaji kai tsohon Alhaji nace dan Allah bani indai bani ba ma asarar shi za ayi kawai shikenan na mika mai sai ya zama na babarbare ne da tsagan shi kwaya kwaya shi kuma da tashi ta ya raba kwaya kwaya to matsalar da ya samu ni na taso ta Kaduna shi kuma bai samu wannan jirgin ba sai muka da wasu za a je ho shi a jirgin Katsina hankalin shi ya tashi nace mishi ba abunda zai faru kawai za a kawo ka shikenan kuwa haka abun nan suna jirgi ya bugo mun waya ya ce ba gano ni ba nace ba gano ni ba baza su gano ka ba ko kun fahimta jama'a? mace da hijabi a hoto ko kai namiji sai ka dauko wannan passport din sai kazo a buga maka sai ka wuce da hijabi da hijabi a hoto sai to daga nan ne zaku gane istita'a muke magana idan kazo wani sanadi yasa suka tare ka ce ho duk tana cikin istita'a ina fata an gane a'a a ko? wato kenan kamar an kallafawa duk wanda yake da hali yake da iko na dukiya ko jikin shi lafiya kalau to indai yana da hali shikenan sai ya tasi malam ya ce za a zo a tattauna bayani dangane da wannan hadisin wanda malam ya ambata insha Allahu a can karkashin inda yake zai zo zai yi magana amma wannan cikin ina hukuncin mutumin da ana aikin hajji kunsan ana aikin hajji ance kar kayi farauta kar ka taimakawa wani in ya koro dabba a guje ko? in kai mai aikin hajji ne shi ba mai aikin hajji ba to kar ka taimaka mishi ba shi amma in ka taimaka mishi to doka biyu ta hau kanka in ya kashe dabba farauta baza ka ci ba sannan na biyu kuma zaka biya diyya ta ko an fahimta jama'a? to za mu zo mu tattauna wannan insha Allahu ta'ala ga kuma wasu bayanai jama'a sharar fage fa ake har yanzu game da karatun tukunna ba a ma shigo karatun ba sharar fage ce ake yi malam ya ce mutane sun kasu kashi biyu akwai wadanda hajji ya wajaba akan su akwai wadanda hajji bai wajaba akan su ba an fahimta? wadanda hajji bata wajaba akan su ba bawa bawa ko yana da hali ba ya da ikon zuwa aikin hajji domin halin shi da shi kan shi mallakar mai shine kun ji wannan na biyu sai wanda ike ba mukallafi ba yaro karami sai kuma wanda yake ba shi da iko
[Segment 4/5 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
ko bayani ga su nan da ya gutsutsura su gutsu gutsu. Ya ce kaga dai na farko. Akwai waɗanda hajji bai wajaba a kansu ba, amma kuma in suka yi yayi. Ma'ana wanda zai iya zuwa da ayyukan aikin hajji ko kuma ya zama ba zai iya zuwa da aikin hajji ba. Nan yana maganar yaro mumayyazi da kuma wanda ba mumayyazi ba. Akwai yaro wanda bai balaga ba. Amma kuma in ka ɗora shi a aikin hajji duk abin da ka ɗora shi akai zai yi mumayyazi kenan. To wannan idan yayi aikin hajji hajjin shi yayi. Sannan akwai wanda yake kuma shi hajji bata hau kanshi ba. Kuma wasa kawai zai ringa yi. Ka ga iyayen sun ɗora mishi duk kayan aikin hajji amma ba abin da ya shafe shi kamar yaro ne kazo da shi masallaci. Ka ajiye shi a sahu tsaf an jima sai yaji an kaɗa wata kararawa sai ya ruga a guje ya tafi wurin, yaje ya cigaba da wasa har sai ka fito ka neme shi. Sai kuma bawa da wanda yake shari'a bata hau kanshi ba. Bawa hajji bai hau kanshi ba. Wanda shari'a bata hau kanshi ba kamar mahaukaci ko yaro karami shi ma haka. Sai kuma akwai wanda yake da hali wanda zai iya yi da kanshi ko kuma ba zai iya yi da kanshi ba. Sannan sai kuma na biyu wanda yake ba mumayyazi ba yaro karami. Akwai kuma wanda shi kuma bai inganta mishi yaje yayi aikin hajji shi da kanshi ba. Ko dai wanin shi ya mishi ko kuma ba wanin shi ya mishi ba. Sai kuma kafiri. Kafiri na daya ko da ya so yayi yana da hali an ce kuma ba zai ba. Ba zai ce to wane je ka kai mun ba. Ko yayi ko anyi mai bata yi ba saboda shi kafiri ne. Kenan hajji baya inganta sai ga musulmi. Amma abin mamaki jama'a a shekarun nan mun ta ganowa akwai kafirai da yawa da suke zuwa aikin hajji. Da yawa har da karuwai mata kafirai. Sosai. Kuma musulmi ne zai je da ita. Akwai arna da makiyan mu waɗanda suke zuwa su kuma dan ance musu akwai kuɗi ana zuwa suna zuwa suna yin sata da sauransu duk akwai ana iya gano A guje jami'an tsaro suka biyo wani a gaba na. Ni sai da yazo ya wuce ne da karfi haka ashe in ya muryi ne. Da ya wuce da karfi ashe ya fusgi jakar wata ne Amina. Na nemi shi kururuwar barawo barawo wani tsoho wani tsoho yana dagara da kwagirin shi. Da ya hangi barawon ya taho sai ya natsu tukunna ya tabbata ya zauna akan kafafuwan shi sai ya daga kwagirin yana zuwa sai ya kwada mai sai suka zube tare. Amma sai da ya tabbata ya zauna tukunna da kafan shi. Sannan sai ya rankada mai sai suka zube tare aka zo aka kama shi. To da aka kama shi turanci da naji yana neman kuna Sai na fahimci wannan dan Najeriya ne. Sai naje nayi wa askarawa magana sai na fara magana dai sai na gane in ya muryi ne. Na ce shi musulmi ne yace shi ba musulmi bane. Me ya kawo shi yace wai yazo yayi nemi kuɗi ne kawai na ce to ai wannan wannan kasa ce mai sarki ba kowa kawai ya shigo da shi da wani suna ya shigo yace da ko Abdulaziz ne ko menene haka dai wani ya shigo da shi. Allah ya kiyaye.
[Speaker seg4-spk:1]
Amin.
[Speaker seg4-spk:0]
Sai musulmi shi yake zuwa aikin hajji. Yan kadiyaniyya yan ahmadiyya malaman wannan zamani sunyi ijma'i akan cewa kafirai ne. Don haka suna daga cikin waɗanda an hana su zuwa aikin hajji. Sai dai ya shiga wata rigar. Amma indai da sunan cewa shi musulmi ne to in har dan ahmadiyya ne ko dan kadiyaniyya ne in ya bayyana to baza a bashi visa ba. Saboda sun kafirce wan manzancin annabi a matsayin annabi shine cika makin annabawa. Sun ce sun yadda annabi annabi ne wai. Amma sun ce basu yadda shine cika maki ba wani annabi da yazo musu a kasar India mai suna Gulam Ahmad Miraza Mirza shine ainihin annabin karshen zamani. Suna nan da yawa a nan Najeriya amma dai lokacin da suka bayyana manyan masana irin su Alkali Abubakar Gumi sunyi rubuce rubuce a kansu kuma sun bayyana kafircin su. Har aka samar da wani littafi wanda aka yi hotan muki ji haka aka sa Kayi a hankali da yan kadiyaniyya. A nan Zaria suna nan da masallaci a can saman Yorroba street. Dab da tsohon masallacin juma'a na yan darika. Suna da masallaci a nan. Wuri na gaba da suka yi cibiya mai karfi shine Lagos a cikin jihar Kwara. Sannan sai a nan arewacin Najeriya inda suka fi samun karbuwa shine garin Bauchi. Har aka samu wata shaidaniya mai suna Aisha mai shanu. Tana rubuce rubuce tana fassarar litattafan su. Da can muna shiga cikin bookshop ne na ABUL nan muke siyo litattafan. Ban daɗe da shiga ba ma naga har da ɓurɓushin litattafan har yanzu. Aisha mai shanu yan kadiyaniyya ne. Yan ahmadiyya ku kiyaye. Su ba darika bace ma kungiya ce ko addini na musamman kamar yadda addinin musulunci yazo bayan addinin annabi Isa ko? To haka su kuma addinin ahmadiyya yazo bayan addinin annabi Muhammad sallallahu alaihi wa sallam. Sun fi karfi a Ghana don har suna rubuto litattafai suna da maɗaba'a suna da makarantu a kasar Ghana sosai. Allah maɗaukakin sarki ya kiyaye. To duk wanda ya tabbata kafiri ne ko yayi aikin hajji babu hajji a kanshi. Jama'a kunji sharar fage da al'imamu Ibn Hajarin Al-Askalani yayi da sunan Allah mai rahama mai jin kai matattara da ke bayani dangane da aikin hajji. Babin da ke bayani akan wajabcen aikin hajji da kuma falalar aikin hajji. Wannan kuma babin har yau zai fassarar maganar Allah da ya ce Allah dai ya farlantawa mutane ziyarar aikin hajji ziyarar ɗakin Allah. In ka ce Wato kamar yadda wannan babin zai bayyana wajabcen hajji da falalar hajji haka kuma babin zai bayyana wannan aya. Idan kuwa ka ce to wawun ɗin ya zama wawul isti'inaf ya zama sabuwar magana. Kenan wannan babi zai bayani dangane da wajabcen aikin hajji da falalar aikin hajji. Sai kuma ka ce maganar Allah maɗaukakin sarki kuwa da yake cewa kaza kaza sai kayi mata fassarar ta mai zaman kanta bata da alaka da babin. Amma a karkashin kasara da aka yi To sai ka ce wannan babi zai bayyana aikin hajji wajibi ne da kuma falalar aikin hajji da kuma bayanin wannan ayar. A karkashin haka ayar tana karkashin babin kenan. Idan kuwa ka ce to ayar tana cin gashin kanta ne babin kuma yana zaman kanshi. A cikin wannan aya Allah yana cewa ne To daga iya nan ake gane Allah maɗaukakin sarki yana da wajabci akan mutane. Allah yana da akan mutane. Tsakanin wannan lamun da wannan ki tabbatar da Allah maɗaukakin sarki yana da wajabci da ya ɗorawa mutane na su ziyarci wannan ɗaki ga duk wanda ya samu iko da hanyar zuwa ga wannan ɗaki. Wanda duk ya butulce wa Allah yayi ke meme ya ki ziyarar ɗakin Allah a halin yana da iko Allah ya waɗatu da dukkan halittu ma in basu je aikin hajji ba balle shi kaɗai dan bai je ba. Wannan itace aya ta 67 a cikin suratu Al-imran. Bayan nan imamu Bukhari sai ya biyo baya da hadisin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama domin wannan shine abin da aka san mu da shi mu ahlus sunna. Mu ahlus sunna dama kur'ani da hadisai sune hujjar mu. Don haka da ya kawo al'kur'ani sai kuma hadisan manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce Imamu Bukhari ya samu wannan hadisi da isnadin nan nashi da kaji ya koro har zuwa sahabi Abdullahi dan Abbas in Allah ya kara musu yarda Abdullahi ya ce Yaya ne ga Abdullahi dan Abbas fadulu dan Abbas. Shine Hausa ke cewa falalu falalu fadulu ne. Mai daraja mai ɗaukaka shine sai Hausa su ce falalu. Fadulu yana bayan manzon Allah akan abin hawa. Sai wata mace tazo daga cikin kabilar kunji hadisin da muke ishara akai. Sai fadulu ya ringa kallon ta ita ma tana kallon shi. Jama'a wannan zamanin sahabbai kenan. Balle yanzu a Hmm tayi jam baki da gazal tun karfe hudu na asuba suke tashi duk inda ruwa yake a jami'a sai ta ɗibo. Sai tayi Sai ta gyara ko ina sai ta duba a ɗaki sai ta juya kawayen ta sai sun duba ko ina yayi. Sannan ta fito ta zauna kusa da kai. Ko sarkin musulmi ne kai hmm kana jin wannan sahabi ne kuma wannan sahabiyya ce kuma a gaban wa a gaban annabi. Kuma a ina a Makka a Makka a ina Amina. Inda ma ake jifan shaidan ɗin ba shaidan ɗin amma ana jifan shi. Ka duba tana kallon shi yana kallon ta. Ko kun fahimta jama'a? Wayanzu sai a ce a'a ku kun ci kazafin addini ku bar su. Karya ne. Wannan irin secular system ɗin da aka kawo na karantar da yaya a makarantu wallahi buɗe hanyar ɓarna ce. Sai wanda Allah ya tsare kuma yan kaɗan ne daga ciki. Amma ko wacece ita kuma bata wuce wani ya latsa ta ba. Bata wuce wani ya harasin ɗin ta ya mata baraza na in bata yadda kaza ba baza ta ci jarabawa ba in bata yadda kaza ba baza ta yi graduating ba in ba in ba in ba in ba. Ko an fahimta jama'a? Saboda haka ku lura da waɗannan abubuwan jama'a mu musulmi ne. Su addinin musulunci shi yake jagorancin komi namu. Bai kamata kawai saboda munyi boko idon mu ya rufe ba. Kana ga gashi fadulu yana kallon ta fadulu sahabi ne. Matsayin kani yake ga annabi kuma a goye yake akan rakumi bayan annabi. Yana kallon ta tana kallon shi yana kallon ta tana kallon shi. Sai manzon Allah ya ringa juya fuskar fadulu zuwa ɗaya gefen ba sau ɗaya ba fa sai ya juya kanshi can kuma sai ya sake juya wa yana haka. Wannan a a wurin annabi kenan ake yin wannan abun. Amina inda shaidan jifan shi ma ake. Balle a cikin lecture theater din ko. Wanda sai ta dube kai mai imani ma sai ta ce kafi lafiya. Kusa da kai zata zauna baza ta zauna cikin waɗancan yan iskan da suka yi party jiya ba. Wallahi kuwa. Baraza na muke fuskanta iri iri game da addinin mu game da akidar mu game da tarbiyar mu da yayan mu da komi. Kayanin mu a yadda muke yana cikin haɗari akwai yiuwar mu tabbata haka ko akwai yiuwar mu lalace muna fuskanta haɗari da mu da yayan mu da zuriyar mu. Shine sakamakon duk tsarin da aka ce Ya ce ba ruwan Allah da mu. Kada Allah ya sa mana baki ba ruwan sallah yake so munje munyi to mun fito ba ruwan shi da mu. Allah ya kiyaye. Akwai mummunan haɗari. Yana ɗaya daga cikin abubuwan da nayi citing a cikin lecture da nake cewa zanyi muku. In kun san wata baku san wata ba. In kun san wata baku san wata ba kafirai sun shiryo hanyoyi suka ga sun bubbuge musulmi sun raunata musulmi amma sai suka ga musulmi sun sake farfaɗowa. Sai suka ce to gaskiya musulmin nan in sun san wata to basu san wata ba. To daga cikin hanyoyin da aka biyar da za'a ruguza musulmi ruguzawa ta din din din in ba Allah ne ya tsare mu ba shine amfani da mata. Amfani da mata ko ina a fagen siyasa a fagen ilimi a fagen talla kasuwanci a fagen ko ina amfani da mata. Ka duba yan dramar nan yanzu yadda ake yaudarar su. Shekarun baya suna cewa wayar da mutane kai suke yi. Yanzu su da kansu sun tabbatar da su kansu yan iska ne. Dan ba wanda zata zo ta ce tazo wayar da kai. Saboda irin iskancin da suke yi. Bayan shekaru kuma fa sai a jepar da ita gefe guda saboda ta tsufa don ba itace ƴar autan mata ba. Wata ta taso yanzu kuma itace ake yaudara. Ina director film? Ina producer? Da da kinyi sallama sai a ce a ki shigo mana ke a'a ya zaki yi sai kinyi sallama nan ki shigo mana. Yanzu bayan shekara takwas an gama da ke shikenan wasu sun taso. Sai a zo da Allah hajiya kin matsa mana muna cikin aiki a Alhaji baka gane ni ba nice wancan fa yace eh to kina ganin ana aiki kinsan aikin nan ba baki sani ba ki fita ki jira a can muna zuwa da Allah da Allah yi wa yaran nan magana su shigo. Haka yake faruwa. A lokacin zata ce zata yi nadama. A lokacin zata yi nadama. Wata tazo wuri na shekaru goma da suka wuce su ake yaudara da can an yi drama da su. Saboda zafin kai tunda take bata taɓa auren musulmi ba. Saboda lokacin suna zuga ta kanta ya waye tayi aure ta auri krista. Suka ɓata ai kwashe yayan. Yanzu basu cikin addinin christianity ya maida su suka zama suka dukufa a cikin addinin christianity. Baushe ya ce Ta sake auren wani shima krista. Saboda lokacin ita tana nuna kanta ya waye ita ba maganar bambancin addini ita kanta ya waye ba maganar bambancin kabila ita ba abin da ya dame ta. Don ma ta sake zuba wannan yayan. Shine tazo tana damuwa yanzu wai tayi nadama. Yanzu ita a rayuwar ta bata taɓa auren musulmi ba. A rayuwar ta bata taɓa haihuwar musulmi ba kenan wace irin rayuwa ta samu kanta. Yanzu kuma ba musulmin da zai aure ta. Sai ta zo neman shawara da tattaunawa yaya kaza kaza but abin da yake da ciwo shine a nan kasa Hausa dai jama'a ba ɗan da ya tashi ya lalace wanda manya basu zauna da shi sun nuna mai ba. A nan kasa Hausa duk wanda kuka ganshi ya lalace to an samu dattawa ko malamai ko iyaye sun zaunar da shi sun nuna mai amma a lokacin sai yana jin a'a shi yasan yasan yadda zai kakkauce duk haɗarin da ake hange. Rayuwa kamar kwaro ne jama'a da yake akan kwarya. Da yaga ka ganshi sai ya ɗauka da gudu sai ya nan gefen kwaryar da ka juya ta fa. Haka rayuwa take maka. Saboda haka matasa in aka ce kar kuyi kaza ku tsaya ku duba ku gani. Waye yace kar kayi mahaifin ka ne. Mahaifiyar ka ce malamin ka dattawan gari duk kare na su. To ya za'ayi da kai sai a barka. Shikenan. Ku je ku gani yan drama nawa ne suka yi aure suka iya zaman aure tun daga na kudanci har na arewaci. Guda nawa ne suka yi aure suka iya zaman aure. Duk wanda ka ganta ka aure ta saboda kaga tayi wata kisisi na tayi wani ado tayi wani kaza in tazo gidan ka irin wannan zata shirya ma bayan lokaci ta tarwasa gidan naka. Shikenan ya bugo ta shikenan. Wata sai ta ce ai dai ta ma taɓa yin auren shikenan wasu ma basu taɓa yi ba. In ta koma director ko producer na film ɗin ba ruwan shi da ita. Saboda yanzu in an sa ta a film ma film ɗin zai ɓaci. Sai dai a ce Hajiya eh zaki yadda a samu miki farin gashi saboda ki fito a mama. Sai ta ce a'a director eh ni ɗin kuma ya ce a'a to ai Hajiya yanzu ki duba yan shekara 16 da ke shekarar ki 30 kuma in muka sa ki a ke ce ai zamu yi asarar kuɗin mu baza a siya ba. Kuɗi ake nema da ke dama kawai. Wallahi kuyi a hankali. Don haka duk
[Segment 5/5 | 01:20:00–end]
[Speaker seg5-spk:0]
da ya tasha a arewa ko yar da ta tasha a arewa. Mu ya yan dattawa ne, kuma mu ya yan malamai ne, ba a ganin mutum ya lalace a anguwa wallahi a sa mishi ido. Saboda haka ke da kike ji na a yanzu. Kina wanka, kina kwalisa, kina fita. Wallahi ki rufa wa kan ki asiri zasu kai ki su baro ki ne. Bayan lokaci ba ki da amfani. Kowa ya san Dr. Chima Chikwe. Wannan tsohuwar ministan man fetur ta zamanin su wane da su wane. Ana ta bata Saboda ga ta yar boko, ga ta doguwa, ga ta fara, ga doguwar hanci, gashi ta iya turanci in ta sa tabarau kyau ta kara fitowa, abubuwa komi na ta goma da goma. Bayan lokaci shikenan. An taho an taho an taho an taho shikenan ta tsufa. Me take nema a bata? Magajiya take neman a bata a cikin jam'iyyar PDP, magajiya. Shine shugabar mata Aka ce a ina? Saboda yanzu hanci ya karkace. Majina tana zuba. Zani take daura an ta daura sai duwawun ya sukuce ya yayi Ba abun da ake so a jikin ta shikenan. Shikenan. Ku dubi Dora. Dora a kunye le. An yi amfani da ita an biya bukata kaza an biya bukata kaza. Ta rasa me zata yi, takaran ma zata yi ko Lecturing zata koma ko yaya. Duk abun da zata yi sun rikita ta. Haka. Dan haka ke ma kiyi a hankali. Da kike zuwa club ko kike zuwa kaza kuna zama ana tattaunawa ana shewa ana kaza. Wannan nonon naki ne ake kallo yana tsaye. Duk randa ya risina To za a warta ke ki. Wannan kazan kazan kazan kazan naki ne daga lokacin da duk wadannan abubuwan suka saki. To wasu sun taso. Dan namiji sai ya zamani da mace biyar. Da ya je ya dan yi kwalisa ya dan yi kwalisa shikenan sai ya sa t-shirt sai ki ga yana rawa shikenan. Ya sake dawowa kan layi. Ke kuma fa? Kin fita daga kan layi. Allah ya kiyaye. Dan haka Manzon Allah yana kau da fuskar zuwa daya barin Matar ta ce ya manzon Allah Farillan da Allah ya dora wa bayin shi ta yi aikin hajji. Ta riski mahaifi na ya tsufa kwarai da gaske. Ba zai iya zama akan abun hawa ba. Ko ya halatta in yi mishi hajji? Annabi yace kwarai ya halatta. Mai riwayar hadisi Abdullahi dan Abbas yace wannan fatawa ta faru ne a lokacin To kun ga Da wannan hadisi Imamul Bukhari yake bayani dangane da Wajabcin aikin hajji a ciki mun ji. Annabi bai ce tunda mahaifin ki ya tsufa an yafe mai ba. Wajabcin yana nan amma wani ya je ya mai. Sannan a nan ne bayanin falala da nayi magana zai fito karara. Wanda ke nuna cewa saboda falalar aikin hajji. Bayan wajabci to wani ya je ya mai domin dai wannan ladan ya tabbata tsohon nan ya samu. Sannan sai kuma babin da ke bayani akan maganar Allah da Allah madaukakin sarki yace Mutane su zo uhm? Mutane su zo wurin ka ya kai wannan daki mai alfarma. A tafe akan kafafuwan su. Haka nan su hawo duk wata dabba wadda take da dan kwararran kwankwaso. Ishara zuwa ga rakumi. Ka kalli rakumi zaka ga kwankwasan shi a matsayi ki ko? To shine Ma'ana wasu su tawo a kafa, wasu su tawo akan rakumi. Allah madaukakin sarki yace Zasu zo aikin hajji. Daga kowane kwararo. Amikin mai nisa, mai matsatsi, ma'ana duk surkukn duniya. Allah madaukakin sarki ya tabbatar wa da wannan daki mutane zasu zo su kawo mishi ziyara, komai nisa, komai surkuki, komai tsukin wuri, mutane wasu su tawo a kafa, wasu su tawo aikin hajji. Akan abeben hawa. Abeben hawan nan ko da ya kai ga rakumi ne wanda yake gashi nan ka dube shi mai dan kwararran kwankwaso duk zasu tawo gare shi. To shine ainihin Al-imamul Bukhari sai ya fara da dabi'ar shi. Yace ainihin Mutane su tawo aikin hajji domin su shaida amfanin da zasu samu ga kan su. Ma'ana a cikin aikin hajji jama'a akwai amfani mai dimbin yawa. Tsarki ya tabbata ga Allah. Wallahi jama'a na jaraba aikin hajji ban taba ganin haduwa mai albarka irin aikin hajji ba. Idan kai dan kasuwa ne. Zaka karu. Kan ka zai waye. Abun da nan kake sarar shi da kyar. Sai ka ga ga ka ga mai kamfanin da ke kera wannan abu a kasar India kun hadu. Zai kawo kati ya baka. Ba ka jin yaren shi baya jin yaren ka. Da alamomi na kurman ta kaza za kuyi magana. Amma so yake yi ya jawo ka ji ka. So yake yi ya turo maka takarda ya sai maka ticket, so yake ka zo kasar shi. Saboda me yanzu ya amince da kai ne saboda kun hadu a wurin aikin hajji. Idan kai dalibin ilimi ne nan ne zaka hadu da malamai masu tsoron Allah. Malamen da kake jin sunan su kake jin labarin su kake karanta littafen su kake sauraran wa'azozin su daga nesa. Zaka gan su zassauki, suna kaunar ka, suna yi maka fatan alheri, suna kokarin su kara bude maka hanyar samun ilimi. Hakan nan. Zaka hadu da wani a wurin aikin hajji. Sai ya ji ba abun da yake so irin kawai ka auri kanwar shi. Amfani iri iri. Mutumin da a nan kasar ku ya gagara ka gan shi. Sai ka gan shi zai shiga ban daki ya rasa ruwa. Saboda a chan an maida kowa daidai da kowa ne. Da ka dauki ruwa ka mika mai sai ya ji dadi sai ya ji sanyi. In ya fito sai ka ga jiran ka yake to ka shiga ban dakin ka fito. Amma shine director general auri kaza. Shine manager auri kaza. Shine oga auri kaza. Sai ya ce a ka san ni ne a'a yace a'a ni ne kaza a'a. To ga kati na. Muna dawowa ka zo ina neman ka. Sai ka tafi ofishin shi a Abuja ko a Sokoto ko a Katsina daidai lokacin da wasu suna layin zasu gan shi. Kai kuma ka zama wani bako na musamman kuma kai da wadancan duk iri daya ne mai yawa ma sun fi ka. Amma wai ina son ku gane albarkar aikin hajji. A wurin aikin hajji ake iya zama malamai da malamai wadanda ba a ga maciji a fahimci juna. A wurin aikin hajji ne ake zama a tattauna. Mas'alolin addini wadanda adawa ne yana tunanin shi fa ba wanda ya isa. A lokacin ne zai ga wanda ya fi shi. Yana hujja da littafin wane to sai ya ga ga wanan ya zo. Wadannan amfani kenan wadanda ke komowa zuwa ga duniya. Amfanin lahira ko wadanda dama aikin hajji dan haka aka shari'antashi. To wannan basu da iyaka jama'a. Lada ne ko ta ina? A wurin aikin hajji ne jama'a zaka je Arafat. Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallama yace Allah sai ya ce wa mala'iku Ku dubi wadannan bayin nawa. Gasu nan sun yi mutsu mutsu da kura. Sun yi busu busu da datti. Dan me suka tara a nan? Sai mala'iku su ce sun zo ne dan neman gafaran ka. Sai Allah ya ce ina kafa ku shaida duk na gafarta musu. Duk na karba aikin hajji su. Manzon Allah yace sai shaidan ya juya yana kuka. Saboda yana ganin an tara mishi musulmi zalla a wuri guda. Ya sa wannan yayi tsegumi, ya sa wannan yayi kaza. Dab da Arafat zata tashi sai Allah yace duk wanda ya halarci wurin Allah yafe mai. Shaidan kuma yayi asara duk barnar da yayi Allah ya cika shi ta da gafara. Wannan yana daga cikin Ko kun fahimta jama'a? Sannan kamar yadda Allah yace Kana karanta Alkur'ani, kana jin labarin Ka'aba. Kana jin labarin Zamzam. Kana jin labarin kaza. Yanzu sai ka ga ga ka a gaban rijiyar Zamzam kana shan ruwa. Ga ka a gaban Ka'aba. Duk wadannan suna daga cikin amfani. Sannan a nan ne in baka da hakuri za a koya maka hakuri. Ba a makaranta ba, ba a wurin wa'azi ba. Kai ka taka mutum. Amma shi zai fara lallashin ka ya fara baka hakuri ya ce maka Me nayi da laifi ya akhi? Sai ba komi ba komi, kai dan wace kasa ce? Haka zaka ga soyayya da kauna kai ka taka shi fa. Madadin ya ce malam baka gani ne baka da hankali ne? Za a ga ba haka. A nan ne zaka ga tarbiyya. Wani krista ne da yayi musulunta jama'a. Babban abun da yace ya lura da shi shine Idan har a ce yau wannan taro na kristoci ne Sai ya ce yace kusan duk matan da suka je zasu dawo da cikin shege. Kalmar da yayi mini kenan. Krista ne mutumin jihar Borno. Mun yi makaranta tare da shi. Har mukayi makaranta baya magana da ni, ni kuma ban hakura ba. Baya magana da ni. Department din mu daya. Zan dauki littafi ko wata makala ta turanci ta addinin musulunci in bashi sai ya karba. Amma baya magana da ni. Bai taba magana da ni ba, ni kuma ban hakura ba. Ashe in na bashi tarawa yake yi. Tsarki ya tabbata ga Allah. Ya riga mu kammala makaranta saboda su shekara hudu suke mu shekara biyar muke. Yana komawa sai wani babban mutum na jihar su. Ashe direban wannan babban mutum shi kuma yayan wancan ne, shi kuma direban musulmi ne. Aka kai shi ya gaida wannan babban mutum. Kawai sai wannan babban mutum yace to kai tunda ka gama makaranta Kai zamu sa takarar dan majalisan jihar na yankin ku. Ka san haka ake a Najeriya kai zamu sa kawai. Sai ya ji an fara ce mishi honorable nan take. Ya ga shi ya zo ya samu aiki inda zai dan ringa cin abinci dubu ashirin da biyar. Aka fara ce mishi honorable kuma babban mutum. Shine har sun fita da wani sai ya ce kai gaskiya zai musulunta ya ce a'a zaka musulunta yace akan me? Me a yace a'a kai yace soyayyar ta yi yawa ne zai musulunta. Shikenan ya musulunta. Ah to da yana wane wane wane ba musulmi ba ma za a je a murda kuri'a saboda shi. Balle kuma yanzu gashi gashi musulmi to ka gani za a iya yar gida kenan. Aka je dai aka sanyar da aka iya zama. Wallahi ni dai jama'a na gama sa'a yayi kenan kan safa zan juya marwa. Sai na ji an dafa kafada ta yace sheikh Na ce a'a waye barka da. Sai ya ce a baka gane ni ba na ce a'a ban gane ka ba yace kai hakuri ni ne mutumin kafa. Na ce a ina? Ya ce a Smith sunan department din mu kenan. School for Management and Information Technology. Na ce eh? Na ce okay ka gane ni ne ya ce eh to ya aiki ya ce baka gane ni ba na ce Ya ce ka tuna shegen yaro da baya magana da kai? Na ce Kana bashi takardun wa'azi baya na ce okay na tuna. Sai ya ce ainihin na ce Allahu Akbar. Shine yake bani labarin yadda aka yi. Yace shi honorable ne yanzu dan majalisa ne, gashi ya taho aikin hajji. Sai zumunci mai karfi ya kullu tsakanin mu. Fattaran wani shi ya dauko shi tun daga Maiduguri sai da ya zo da shi har gida nan. To amfanin aikin hajji yana da yawa jama'a. Amfanin baya kirgu.Annotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Karatuttukan Karshe a Ranar da Aka Kashe Shaykh Albaniy Zaria (Dariqus-salihin 1, Muslim 172, Bukhaariy 308). Daarul Hadeethis Salafiyyah. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15871.
Zaria, M. A. A. (s. d.). Karatuttukan Karshe a Ranar da Aka Kashe Shaykh Albaniy Zaria (Dariqus-salihin 1, Muslim 172, Bukhaariy 308) [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15871
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Karatuttukan Karshe a Ranar da Aka Kashe Shaykh Albaniy Zaria (Dariqus-salihin 1, Muslim 172, Bukhaariy 308). Daarul Hadeethis Salafiyyah. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15871.


