document audiovisuel · Daarul Hadeethis Salafiyyah · 2004 Citer
Jihadin dan Fodio...
- Type
- Enregistrement vidéo
- Créateur
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Editeur
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- Date
- 2004
- numéro
- 1
- 2
- 3
- Est une partie de
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Importance matérielle
- PT288M
- Support
- DVD
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000019
- contenu
-
============================================================
[Part 1]
============================================================
[Segment 1/4 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
muna fara da sunan Allah mai rahama mai jin kai godiya ta tabbata ga Allah muna gode mishi muna rokon Allah ya taimake wo Allah ya tsare mu daga sharrin kawo nan mu da miyagun ayyukan mu wanda Allah ya shiryar babu mai batar da shi kuma wanda ya bata babu mai shiryar da shi ina shaidawa babu abun bautawa da gaskiya sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya kuma lallai Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan shi Annabin Allah ne manzon Allah ne Allah ya aiko shi da gaskiya bayan haka yanzu da nake magana din nan kusan karfe takwas da mintuna ne kadan na daren Lahadi wanda ya daidai da daren tara ga watan al muharram daren tasu'a kenan daga Makka zuwa Madina na da shekara 1425 daidai da 27 ga watan Fabrairu shekara ta 2004 28 ga watan Fabrairu shekara ta 2004 muna tsaye ne a anguwar da aka fi sanin ta da yan awaki wanda ke yankin muciya sabon garin Zaria jihar Kaduna Nigeria a kofar gidan dan uwan mu aminin mu abokin mu Alhaji Jamilu Isa Dan Sukunde muna yi mishi addu'a Allah ya saka mishi da alkhairi Allah ya ji kan iyayen shi Allah ya yawaita dukiyar shi ya saka albarka a cikin zuriyar shi jama'ar musulmi ni mai wa'azi suna na Muhammad Awwal Adam an fi saniLire le texte intégral — 40 404 mots restants Réduire le texte intégral
na da Abu Abdurrahman Al Bani anan da nake tsaye anguwar mu ce wanda galibin wannan anguwar bama yin wa'azi sai dai karantarwa wato karatuttuka wadanda kuke ji a kasusuwa kamar karatuttukan da suka gabata da tsawon dadewa karatuttukan Sahibul Bukhari tafsirin Al Qur'ani da littattafai makamantan haka da kuke ji galibi a anguwar nan muke yi wa'azi irin wannan da bature ke kiran shi public lecture wanda za'a tara jama'a masu saurare da kabbara yau ne karo na biyu da zamu yi kadai a tarihin wa'azin mu a anguwar nan baza mu gushe ba muna masu godiya ga al'ummar musulmi musamman mutanen anguwar nan da suka haife mu suka yi tarbiyyar mu suka rene mu har zuwa wannan lokacin muna yi muku godiya muna yi muku addu'a Allah ya saka muku da alkhairi daga cikin mu iyayen mu sun rasu a anguwar nan muna yi musu addu'a ta musamman Allah ya gafarta musu kamar ni mai magana kusan shekara guda mahaifiya ta ta rasu a anguwar nan ina yi mata addu'a ta musamman Allah ya gafarta mata ba da dadewa wannan ba an yi mana mace mace da yawa a anguwar nan mutuwa ta kurkusa ta kurkusa da aka yi wanda take daga farko farko akwai babban malamin Al Qur'ani Alaramma Malam Habibu Yaro su muna yi mishi addu'a Allah ya yafe mishi ba da dadewa ba madakin iyaye ya rasu shima Allah ya gafarta mishi kusan kwanaki hudu ko biyar da suka wuce kuma wata dattijuwa uwar mu ita ma ta rasu Hajiya Bazanfara Allah ya gafarta mata da sauran wadanda bamu samu damar ambatar sunayen su ba kamar wani abokin mu ba da dadewa ba ya rasu lawa ayala Allah ya gafarta mishi wadannan mace mace duk a anguwar nan aka yi su a cikin yan watanni biyu da suka wuce to muna ta'aziya ta musamman ga mutanen anguwar nan muna yi muku ainihin addu'a ga wadannan mu mata Allah ya gafarta musu Allah ya dauki ran mu da imani a yau mu Baushe yace karshen cika cika tik yau ga Albani akan layin su an zo kusa to yau azifa til azifa ta kusa ta kusa toke wannan wa'azin gaskiya wa'azi ne mai tarihi domin wannan wa'azin asalin goron sallah ne da ya kamata shi kashi garin babban sallah da kwana daya kenan amma ba'a samu damar yin wannan wa'azin ba a wancan lokacin da ya kamata a yi shi ba dan komai ba saboda a daidai wannan lokacin na ta hudu ne kadai in sa a gida lokaci ya muna cikin jira ba wa a makaranta don haka a gurguje nayi kokari na koma a wancan lokacin da a ce wannan wa'azin ya samu taken wa'azin shine alamomin tashin alkiyama to amma abin duk da Allah ya zabar mana alkhairi bamu samu damar yin wannan wa'azi ba sai yanzu da na sake dawowa wani takaitaccen hudu wanda nan da yan kwanaki shima zan sake komawa to sai aka yi ta wani kasan namu ana wata ga wata waccan latta ba'a samu idi da ita ba sai kuma muka ji sarakunan kasar Hausa da yan bokoko sai suka hada kai muka ji suka ce suna bakin jihadin dan hudu yau ya cika shekara 200 saboda dan hudu yau ya ainihin da jihadi a 1804 a cikin watan October wannan tarihin da yan boko suka buga da sarakunan gargajiya sai ya basu shekara 200 da kaddamar da jihadin dan hudu yau sai suka yi ta sanarwa tun daga ainihin majalissar sarkin gargajiya ta Sokoto wanda aka fi sani da sarkin musulmi Muhammadu Maccido zuwa ga ainihin sarakuna har na nan kasar Zazzau suna sanar da cewa suna murna suna biki suna addu'a suna masu kai ziyara zuwa ga wasu makabartu saboda tuna yau shekara 200 da yin jihadin dan hudu yau ana ta hawa da wakai ana daba ana hawa da wakai ana yin hawan daushe da dai wasu abubuwa makamantan haka to tsoron kada yan bara bakwai matasa da wadanda basu san tarihin musulunci a kasar Hausa ba su dauki wannan danyen aikin sarakunan gargajiya da yan boko haka dan hudu yau yi wannan jihadin sai muka hada wannan lecture muka sa mata jihadin dan hudu yau ba hawan daushe bane domin kada a yi kuskuren fahimtar cewa sa'ar da dan hudu yau ya kaddamar da jihadi doki aka hau aka yi ta sukutun ana kewaye garuruwa shikenan yara su dauka to suma yanzu da aka yi haka sarakunan yanzu da yan boko sun yi jihadi kenan nan da wasu shekaru suma yara da za'a taso su hau doki suna kewaye gari suna sukuwa zuwa makabartu su dawo suna zuba su ma sun yi jimamin jihadin da kakannin su suka yi to wannan shi yasa muka ga idan muka yi shiru domin zalunci tarihi idan muka yi shiru mun zalunci aiki na gari wanda dan hudu yau yayi don haka muka tsayu domin ainihin mu yi wannan lecture wannan lecture doguwa ce ta yi ta kare a yau ta yi ba ta kare a yau ba zamu fadi sa'ar da za'a zo a ci gaba ko gobe ko wata rana daban amma dai abin da muke so ya shiga cikin tunanin ka a yanzu da muka fara wannan lecture har zuwa sa'ar da zamu kammala ta shine jihadin dan hudu yau ba hawan daushe bane mai yi wa'akai Bakano ne ko Bakatsine ne ko Basakkwace ne a garin ku ba'a hawan daushe to ya kamata mu zage zagen kasar Zazzau da fassara maka hawan daushe na daya daga cikin hawan sallah da sarakuna da masu mulki na kasar Zazzau da wasu ainihin kasashen Hausa suke yi to shari'ar musulunci kamar yadda muka sha fadi bata hana da sallah al'umma su zo su bayyana wasu wasanni nasu na gargajiya wadanda basu saba ba shari'ar musulunci wannan duk saboda sahihin hadisi dai yazo cikin Sahihul Bukhari da Muslim daga Sayyida Aisha Allah ya kara mata yarda ta ce mutanen kasar Habasha suka kwaso masu da kibiyoyi da takubba da kayan yaki suka shigo cikin masallacin Annabi suna wasan sallah Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da kanshi ya tsaya yana kallo Aisha tazo wucewa yaga ta ne tana leko wa Annabi yace da ita kina sha'awar ki kalla ne tace eh tace Annabi ya tsaya da ita a bayan shi ta sako ainihin kafar ta ta dora akan kafadar shi ta baya ta ne tana kallon ainihin wadannan mutanen kasar Habasha dangin mu ne bakaken fata suna wasa irin na gargajiya a cikin masallacin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ranar sallah Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai hana su ba saboda a cikin wani hadisi ne ya tabbata yana cewa ko wace al'umma tana da idi domin mu ma wannan idin mu ne ma'ana ranar shagalin mu ne da wannan Bazazzagi kake ko Bakano Bakatsine kake ko Bakobiri Bakawace ko Badauri idan Allah ya kai mu sallah karama ko babba in za'a yi hawan sallah zaka iya sawo rigar ka da jamfa da menene ka hau doki ka tafi ainihin hawan sallah ko ka je kallo ko makamantan haka sai dai muna cewa mu anan kasar Zaria akwai wata karya da ake sai a janye ta ance idan mace ta leko ta ga sarki ranar sallah Allah ya gafarta mata to wannan dangin mu zage zagi karya ne sai a janye amma hawan sallah dai in za'a hau baza ayi wani abu dai ya kece mutuncin shari'a ba to wannan shari'a ta yi sassauci akan haka to wannan na daya daga cikin saran hawan sallah da ake anan kasar Zazzau ana kiran shi hawan daushe a hau da wakai a yi ta gudu ana sukuwa ana nuna bajinta ana farin ciki to irin wannan hawan aka yi a mafi yawancin kasashen Hausa da umarnin sarkin musulmi Muhammadu Maccido cewa ko wane sarki ya fito yayi shagali ya ziyarci kaburbuka na kusa da shi ayi addu'o'i saboda murnar kaddamar da jihadin dan hudu yau ya cika shekara 200 to mu yanzu abin da muke musu shine wannan danyen aikin da shi sarkin musulmi yasa aka yi da kuma wannan danyen aikin da su sarakunan kasar Hausa suka mara mishi baya aka yi da danyen aikin da yan bokoko suka daura gindin aka yi wadannan abubuwan su muke musu domin wannan barna ce batanci ne ga jihadin Shehu sannan muna na tarihin jihadin Shehu ne sannan kuma lalata tarbiyyar yaya ce da kashe musu zuciya da kamata yayi ace a lokaci irin wannan in ma har za'a yi tunanin jihadin Shehu a zo a dubi wasu shawarwari wadanda zamu zo mu gabatar da su a karshen wannan wa'azi na daga ciki shine a kaddamar da jihadi irin yadda Shehu dan hudu yau yayi tare da cewa kai da kake saurare na bari in mara maza in ce maka jihadi fa da musulunci yake magana ba jihadi irin wanda iyayen gidan ka turawan mulkin mallaka da yan bokoko suka je a cikin Nigerian history suka rubuta maka akan cewa ma'anar jihadi shine yaki na takobi da takobi a kashe mutane a tursasa su shiga addini a kuma kwace musu dukiya da mata da yaya ba irin wannan ne muke nufi da jihadi ba zamu zo muyi bayanin irin jihadin da ya kamata sarakunan kasar Hausa su raya domin shine kakannin su Shehu Usmanu ya ainihin kaddamar Allah ya yarda da shi jama'ar musulmi wannan lecture tawa na tsara ta kamar haka nayi wa lecture ga'obi guda uku gafar farko ita ce jihadi a musulunci wannan jihadi a musulunci zai zama shin kudaden ga wannan taken wa'azi mai suna jihadin dan hudu yau ba hawan daushe bane to zamu yi shin fuda akan menene jihadi a musulunci ma'anar jihadi hukuncin jihadi a musulunci falalar jihadi da masu yin jihadi sannan nau'o'in jihadi a cikin addinin musulunci gaba ta biyu ta wannan lecture tawa zan yi magana akan takaitaccen tarihin kasar Hausa kafin zuwan Shehu dan hudu yau a karkashin wannan zan yi magana akan shigowar addinin musulunci kasar Hausa wanda wannan maganar ko ta yi rasa guda biyu ita ce ta ina addinin musulunci ya shigo kasar Hausa sannan kuma ta yaya ma'ana ya yaushe addinin musulunci ya shigo kasar Hausa sannan har waya a karkashin wannan zan yi magana akan gudanar da musulunci kafin dan hudu yau shin a kasar nan da aka fi sani da kasar Hausa a yau ana yin musulunci kafin dan hudu yau ko ko dan hudu yau ne ya kawo addinin musulunci a karkashin waccan gaba ne da zan yi magana akan kasar Hausa kafin dan hudu yau zan yi magana akan matsayin sarakuna da malamai a kasar Hausa game da addinin musulunci dan hudu yau ko akwai sarakuna sarakunan nan musulmi ne ko ko bakaken mahuza wa ne ko akwai musulunci a wannan lokaci in akwai musulunci shin akwai malamai malaman suna karantarwa suna da'awa shin daga cikin su an taba samun wadanda suka yi yunkurin su mike su yi gwagwarmaya domin tabbatar da addinin musulunci shi kadai a ainihin kasar Hausa ko ko babu zamu yi maganar wannan insha Allahu ta'ala gaba ta uku ta wannan ainihin wa'azi ne da ikon Allah zamu yi magana akan shi kanshi dan hudu yau su kutun da guda abin da nake nufi da wannan maganar ita ce zan yi magana akan tarihin dan hudu yau menene asalin Shehu dan hudu yau daga ina suke iyayen shi da kakannin shi katin katin mece ce nasabar shi abin hudu yau haihuwar dan hudu yau yaushe aka haife shi a ina aka haife shi abu na uku neman ilimin shi a ina ya nemi ilimi su waye malaman shi abu na hudu ya fara karantar war shi da da'awar shi yaushe ya fara karantarwa yaushe ya fara kiran mutane zuwa ga addinin musulunci abu na biyar shine tsarin da matakan da'awar dan hudu yau wane samo dan hudu yau ya daukar wa da'awar shi zuwa yayi rana tsaka ya kira wa'azi da aka ki amsa wa'azin kashi gari ya waye gari yana kashe jama'a dan hudu yau tashi yayi ya dubi sarakunan kasar Hausa da malaman kasar Hausa duk yace su kafirai ne shin wai ma dan hudu yau shi ya fara tayar da maganar jihadi ko ko tsogalar shi aka yi ya tashi domin ya kara kanshi zamu tattauna wannan insha Allahu ta'ala abu na gaba zamu yi magana akan rubutun rubutun dan hudu yau ko dan hudu yau ya rubuta littattafai ko ko wa'azi yayi ta da fatar baki kawai zamu yi magana dangane da yadda gidan dan hudu yau yake bayar da akan matan shi da kwarakwaran shi da yayan shi sannan shin dan hudu yau cima zaune ne yana jiran ta Annabi tazo ne maulana ta Sidi maulana ta Balarabe ko ko yana da sana'o'i dangane da magana akan sana'o'in dan hudu yau daga nan ne zaka auna kanka a matsayin ka na malami yanzu a kasar Hausa ko a kasar da aka fi sani da Nigeria a yau daga kana da sana'a ko ko sai tsabar malantar daga nan ne zaka gane abin da yasa dan hudu yau yake iya fadin gaskiya wanda kai kasan ta kana kasa fadin ta zamu yi magana insha Allahu ta'ala game da karshen rayuwar Shehu yadda ainihin wato Shehu Usmanu
[Segment 2/4 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
yau sheda tazo karshe ya fara tunanin yadda al'amura zasu faru bayan mutuwar shi. To a nan Dattijo in yazo rasuwa dole akwai wasu magana da yake gaya wa 'ya'yan shi. To wannan ba dattijo bane kadai, dattijon malami ne. Ba dattijon malami kadai ba, dattijon wali. Ba dattijon wali kadai ba, dattijon wali kuma mai jihadi. Irin wannan mutumin anya zai zo kwanciya ya kwanta kamar yadda inna mai saida rogo da gyada take basu ibasa rada bai cewa 'yan bayan shi komai ba? Kalla. Shehu dan fodiyo yana da wasiyya, to me ce ce wasiyyar shehu? Ga su waye wannan wasiyya. Insha Allahu ta'ala zamu tattauna wannan magana ta gaba gaba da manufofin shehu. Wacce manufa tasa shehu ya tashi yana karantar da jama'a? Ma'ana shehu ya tashi yana karantar da jama'a ne don yayi suna ace wannan yaro ya iya karatu, ya iya li'irabi, ya iya tafsiri. Shehu ya tashi ya kaddamar da jihadi ne akan sarakunan kasar Hausa don su Hausawa ne shi ba Fulani ma'ana yayi jihadi ne dan kabilanci ko ko shehu yayi ne saboda bakar fatara da bakin talauci wanda yake samun ba Fulani idan shanu sun kare mishi. Wannan magana ina fadin ta ne saboda nasan haka aka koya wa da yawancin daliban makarantun sakandare da suke karanta Nigerian history tarihin Najeriya cewa shehu ya tashi yayi jihadi ne jihadi na irin matalaucin ba Fulani da shanu suka kare mai. Ma'ana dai yayi jihadi ne dan tara dukiya. To zamu yi magana akan wannan insha Allahu ta'ala. A karshe zamu kawo rasuwar shehu dan fodiyo insha Allahu sannan sai mu buga wata alamar tambaya a yau da duk malamin da ya kwana kasar Hausa da duk wani sarki da ya kwana kasar Hausa ina makomar 'ya'ya da almajiran shehu a yau? Suna irin aikin shehu ko ko suna kwasar dawakai da gudu su yi ta kewaye gari su dawo suna zuba suna haki? Suna munnar irin wannan lokacin ne kakannin su yayi jihadi? Ina makomar da jikokin shehu a yau? Ko 'ya'yan shehu a yau suna karatu karatun addinin musulunci yadda zasu iya tashi suyi aikin kakannin su ko kuwa lalacewa ta kai lalacewa iyakar su boko boko kawai? Sannan ta yaya zamu yi a yau mu masu dawa masu neman juyin juye hali wadanda aka fi sani da Ta yaya zamu yi a wannan lokacin mu juya kasan nan ta zama ainihin wato ta koma tsarin shari'ar musulunci ba Shari'a ta musulunci wadda za'a yi al'kur'ani da hadisi ba da ra'ayin wani zindiki da ke Ingila ko wani da ke cikin wata jami'a ta kafirai ba. To wani hali zamu bi mu juya kasan nan ta koma irin wancan halin. In na samu damar lokaci insha Allahu ta'ala wadannan abubuwan duk zan gabatar da su a yau a wannan ainihin lacca. Sannan daga karshe wadannan abubuwan da yawanci sun shafi tarihi. Ni kuma daga kallo na kasan cewa ban yi zama a wancan zamani ba. In ma karantar da ni akai ko kuma karantawa akai to a ka'idar lacca irin wannan a ina na karanto? Wato dole in kawo mai littattafan da na duba. Wannan ita ce tsarin ainihin lacca ta ilimi. Ba ka gama magana ba ka ma nima ka wa'azi kuma ba wa'azi ake ba. Allah madaukakin sarki ya taimake ni.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
Kamar yadda muka ce jihadi a musulunci wannan shine shimfidar wannan wa'azin namu. Kalmar jihadi 'yan boko boko suna ainihin fassara ta da cewa To mu bamu yarda da wannan fassaran ba. Wai wani yaki ne mai tsarki. Yo sarkin Maguzawa ma ashe idan yayi yaki domin girma wa guma kan shi zai iya kiran shi jihadi kenan a karkashin wannan ma'anan. Kalmar jihadi kalma ce ta larabci wadda ta samo asali daga wanda ma'anan shine ainihin A larabci ana cewa Ana cewa yana jihadi ma'ana jihadi in mutum ya kai matuka wajen ainihin yin kokarin shi domin yin wani abu. Amma a cikin addinin musulunci jihadi yana daukar ma'ana mai fadi fiye da wannan. Amma in an so a takura ma'anan sai ace ita ce musulmi ya kai matuka yadda duk zai yi ya ga ainihin yabi Allah madaukakin sarki ya kuma kokarin yada addinin musulunci da gwargwadon ikon shi. To a karkashin wannan fassaran mai kudi zai iya zama mai jihadi mai ilimi zai iya zama mai jihadi mai bada shawara zai iya zama mai jihadi mai kudi zai iya zama mai jihadi domin zai diba ma kudin kudi ya bayar domin a saye kamai wajen yada ai wajen kare addinin musulunci. Zai iya diban malamai ya tura su su tafi suna wa'azi suna yada addinin musulunci. Wannan jihadi ne. Wanda ya gogu da duniyan nan yaga jiya yaga yau yayi nehu yayi 'yan PC, yayi 'yan PN, yayi PR P ake PDP da AMP P a zamanin shi a yansu. Tsohon zago kenan ya wuce a waza mai tsakowa a kama shi. Irin wannan ma za'a samu shawarwari daga gare shi. To haka samu tsohon komi irin wannan ya zo da ya bada shawara ga matasa wadda zata shiryar da su zuwa ga yadda zasu yi siyada ko su kawo ci gaban addinin musulunci wannan Dattijo ana iya kiran shi mai jihadi saboda shawaran shi. Kaman Salma Farisi wani Dattijo ne daga cikin Sahabbai wanda ya girmi kowa a cikin Sahabbai wajen shekaru domin sai da yayi shekarar 270 dindi a duniya sannan ya rasu. Wannan maganan haka Yace malaman musulunci suka ce sai da yayi shekarar 270 dindi sannan ya rasu. Amma kuma har a wannan lokaci in ka dube shi da tsabar idon ka sai ka ga bai wuce dan shekara 50 ba. Ma'ana kwage Kafiran duniya baki daya ba fa suka yi a wancan lokacin ba. International Alliance suka yi suka hade kai duk kafiran duniya da Kiristoci da Yahudu da bakaken Maguzawa da kai suka hadu akan cewa suje su rutsa Annabi a garin Madina su kashe shi domin su kawo karshen addinin musulunci kowa ya huta. Suka rutsa garin Madina aka shiga aka fita Sahabbai hankalin su ya tashi Annabi ya tara Sahabbai yace to yanzu fa ana neman shawara ce me ce ce mafita domin wannan yaki ne wanda yake makami ba zai yi shi ba. Amma muna neman shawaran yadda zamu fara tukunna. Ta yaya za'a diga dan badin wannan yakin? Salma Farisi ya daga hannu. To kaji abin da nake nufi. Kaga shi tsohon komi ne ya dade a duniya shekarar 270 duk wata shawara duk wata kifa daya kwala ya ganta ya haye ya zauna hannun Kiristoci ya zauna hannun Yahudawa iyayen shi bakaken Maguzawa ne masu bautar wuta. Saboda haka akwai shawarwari da yawa akan shi. Sai yace mu a kasar mu ta Farisa idan makiya suka rutsa mu sai mu guma hakan katon gwalalo. Wannan nayi muku Hausar kanawa kenan. Kataran Katan rami a jikin ganuwar gari sai mu dibo sojoji sai mu kewaye saman ganuwar gari yadda in makiya yazo zai hauro katangar ba zata yi dadin haurawa ba domin rami ne a kasan ta. In kuma yace zai mata bibango ya biyo ta dalla dalla ya kamo kafin yazo sojojin nan sun waso shi kasa. Annabi ya karbi wannan shawara. Haka zo ana haka ainihin wannan rami Sahabbai suna waka suna bayyana mubaya'a su ga Annabi sallallahu alaihi wa sallama sunayi wa Annabi kirari suna cewa Mu wuta wa Muhammadu mubaya'a akan jihadi matukar muna da rai har abada. Annabi ya fito da yazo ta yi waka sai yace Ya Allah ka taimaki ansarawa da mujahidi. Wannan abin da Annabi ya gani ya bashi sha'awa. Yana cikin kewaya su sai aka zo wani dutse ya kafe a kasa an kasa ciro shi. Sai Annabi yace ku kauce sai ya karbi diga ga ta ri. Da ya doka wa dutsan sai wuta ta kekyashe sai ta fito sai yace an nuna mana mun ci Farisa. Ya sake dukan dutse sai ainihin wuta ta sake tayi sai yace an nuna mana mun ci kasar Rum. Muna bugai sai suka ce kaji turi. Muna nan an rutsa mu mun kasa kwatan kan mu wai ace mun ci Amurka da Japan kaji karya. Kamar haka ne fa wadannan dauloli a lokacin kamar yadda Amurka ce take da kasar Japan da irin wadancan da wadannan kafirai ne a yanzu. Munafukai kenan. Suna fadin haka ne saboda rashin imaninsu da Annabi sallallahu alaihi wa sallama saboda su kashe zuciyar muminai. Allah madaukakin sarki yasa Annabi ya karfa fi zuciyar muminai an gama haka wannan rami Annabi sallallahu alaihi wa ali wa sallama ya ainihin daga hannu yayi addu'a. Da Allah ya tashi sai ya doko wata irin iska mai karfi. Kafiran nan suka kwashe da gudu malam. Abu Sufiyana a lokacin shine shugaban arnan Makka shine komandan su. Da gudu ya dafa rawanin shi ya gudu. Can da suka gudu mutanen Makka guguwa tayi fatali da tantunan su da 'yan runfunan su. Sai wata mace mai kamar maza sai ta rarrabo sai ta dauki tutar su sai ta kafa ta tashi tutar su sai sai sai mutanen Makka duk wanda ya gudu kuma da ya dangata tuta ta tsaya sai ya dawo da rarrabe ya dan tsuguna sai ya ga mace ce a gindin tutar take yi a gindin nan. To balarabe kuma shi dama yana son ya gane wani abu da ka taba yi ne don rana gori yayi maka. To Abu Sufiyana kamar bushi yanzu ace bushi ya rarrabo ya taho karkashin wata tuta da mace ta rike. Kaga in mu muka ga haka to ba shakka wannan zai shiga cikin waka. Lokacin da musulunci yayi karfi Annabi ya samu daga cikin wadanda ke kare shi akwai mawaƙa akwai Abdullahi bin Rawaha akwai Hassanu bin Sabiti. To shi Abdullahi dan Rawaha dan Makka ne saboda haka yasan uwar kowa yasan uban kowa. In ka taba Annabi in ya tashi mata waka ba sai ka binciki tarihin ka ba. Ya san da uban ka ya taba satan gonsu haka aka kawo ka yana kwarkwanci duk yasan wannan tarihin sai ya zuba a waka ba sai an wahalar da shi ba. Amma Hassanu bin Sabiti shi dan Madina ne bai san tarihin kowa a Makka ba. Don haka in yazo zai yi zambo sai ya rikice sai Annabi yace duk wanda zaka yi wa zambo kazo ka tambaye ni. Ni dan Makka ne gaba da baya wa walidun mu ma walida. Nasan tarihin kowa. To wannan labari sai yazo ga Annabi ai Abu Sufiyana ran nan da ya kwashe da gudu sai da yaji labarin tutar su ta tsaya sannan ya dawo da rarrabe yazo ya samu mace ce ma ke karkashin tutar. To ran da Hassanu ya tashi zai musu waka fa sai da aka saka wannan a cikin waka fa. Yace Yace jama'ar musulmi ga wasiyya akai wa Abu Sufiyana. Abu Sufiyana asirin ka ya tonu. Ta kubba musulmai da kai bawa bawan da mace ce shugaban ku. Wannan tarihi ne sai anyi fashin baki shine wacce magana. Tun daga ran da akai wa Abu Sufiyana wakan nan bai sake fitowa ba domin balarabe yana cewa Balarabe da yayi abun kunyar da za'a yi mishi waka gon mayan mutu. Saboda haka tun daga ran da akai mishi wannan waka ya tabbatar wani asiri ne na koyar ya fito to ni sake fitowa waje ba sai ran da ya musulunta. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? To saboda haka na kawo wannan ne kadai don waccen magana ta Salma Yanzu Salma nu da shawara ya bayar aka daga addinin musulunci to wannan shawaran jihadi ce iya abun da nake so ka gane kenan. Jama'a musulmi mun gane wannan da kyau ko? Shari'ar musulunci ba shari'a ce ta 'yan ta kife ba wdd zaka ce kuje ku cigaba da kashe arna in ba haka ba su musulunta ba haka ake ba. Sa'ad da Annabi yazo da wa'azi ya fara Allah madaukakin sarki da ya karantar da shi Wadannan ayoyi guda biyar da suka sauka aka karantar da Annabi ya tashi ya karatu ya nemi ilimi da ya dawo sai ya lilliba saboda jin tsoron mala'ikan da ya kawo mai wancan sakon. Yana kwance sai kuma yaji ana Wadannan ayoyin sai suka sauka yana kwance yana lillibe. Sai Allah yace mishi ya kai da ka lilliba tashi ba lilliba zaka yi ba. Ka tashi kayi wa'azi ka girmama ubangijin ka ka kaurace wa gumaka ka tsaftace tutafan ka kayi hakuri da umarnin da ubangijin ka zai cigaba da yi maka nan gaba. Wadannan ayoyi da suka sauka sai Annabi sallallahu alaihi wa sallama ya tashi ya tafi bayan garin Makka yaho kan dutse ya fara kiran Larabawa dangi dangi jama'a jama'a aka ce lafiya kai Muhammadu ne yake kiran al'umma. Sai da aka taru gaba daya yace ya ku mutanen Makka na taba muku karya? Suka ce a'a. Kun taba tuhuma ta da karya suka ce a'a. In na ce muku Allah ya aiko ni Annabi ne zaku yarda? To gashi dai bai taba musu karya ba balle su samu damar karyar ta shi karon farko. Amma kuma wannan gaskiyar da yazo da ita tayi nauyi. Domin wanda bai taba wa mutum karya ba zai fara karya rana farko ya fara da Allah? To sai maganan tayi musu nauyi sai suka yi shiru sai Abu Lahabi ya daga ya tsan shi yana tabban lanka ya Muhammadu Allah wanda ranka ya Muhammadu dan wannan ka tara mu? To Allah shi yake wa Annabin shi yakin mai mai da ka taba Annabi yanzu Allah zai kacce kacce da kai. Dan haka dan wuta na farko a musulunci shine Abu Lahabi sai Allah yace tabbata ya dawo Allah ya kacce kacce da tun daga hannu da yake nunawa har sauranci kenan shi. Matar shi ma da take yaho tana hadan maza da mata fada akan sun musulunta Allah bai rangwanta mata ba. To wannan tarihin dawowar musulunci kenan. Annabi ya fara ya cigaba da dawa yana wa'azi mutanen Makka wasu su ji su bi wasu su ji su karyata wasu su ji suyi shiru suce abun na Muhammadu ne akwai ban mamaki. Bai taba karya ba amma kuma in zai fara zai wuya fara da Allah to amma kuma wannan abu in gaskiya ne duk allolin nan kuma guda 360 da ke saman Ka'aba ace karya ne ace Allah daya hayi wannan abun mamaki ne. Kai wannan dai Muhammadu fa yana da wata manufa ayi a hankali. Haka sai abun ya faru wasu suka karyata wasu gaskata wasu ka shiga cikin shurha Annabi bai rage ba sai karawa yayi wa'azi yake. Kawun can nashi Abu Lahabi tun da Allah yace mai an farka sai yace to bari ya cigaba da barna. Annabi na wa'azi Abu Lahabi yana bin shi yana cewa kar ku yarda da shi dana ne uban mu daya da uban shi ni ban yarda ba ku zaku yarda? Haka ya rinka wa Annabi warwara Annabi na tikkawa. Jama'a mun gane wannan da kyau? Me ya biyo baya? Karshe da rikici yayi rikici Annabi in yana wa'azi sai ya zama har kashi ake ana dukan shi. Wata ran yana wa'azi a rurin Ka'aba suka tashi suna dukan shi sai da Abubakar ya mike yace
[Segment 3/4 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
Sai ku tashi zaku kashe mutumin da yazo muku da gaskiya daga ubangijinku. Ku barshi in makaryaci ne karya shi ta kai kanshi. Idan mai gaskiya ne abunda yake fadi zai same ku. Wata rana annabi yazo yana sallah a ka'aba. Tsoffin banza na makka suna zaune suna shan burkutu. Suka ainihin cewa wane irin wulakanci muke gani? A gaban mu muna shan burkutu ace kuma ana sallah? Yaya haka zata yiwu? Waye zaije ya kwaso kashi da mahaifara rakumar da aka yanka a unguwa kaza? Yazo ya bari sai muhammadu yayi sujjuda ya yaba mishi a ka'aba. Sai aka samu wani Wani matsiyacin cikin wannan al'ummar kamar yadda matsiyacin cikin al'ummar Ainihin annabi salihu ya yanka taguwa aka samu matsiyacin cikin wannan al'ummar shi kuma ya tashi. Yaje ya ainihin kama wannan ainihin kashin rakuma da mahaifa da aka yanka yazo ya dibo ya bari sai da annabi yayi sujjuda sai ya yaba mishi. Annabi yana jin wannan wulakanci yayi lip yayi shuru. Ibn mas'udun yake ruwaito wannan hadisi a cikin sahihul bukhari kitabul masadiji yace Ina ji ina gani ana wa gida na wulakanci bazan iya dama mishi Bazan iya magana ba. Yace sai na kwashe da gudu naje na gaya Nace kizo ga tsoffin banzan cecan sunayi wa annabi wulakanci ke mace ce in kika zo basu ta baki. Fatima tazo ta tsaya ta kwashe wannan kazanta ta zubar ta koma ta zazzage su. Ta cigaba da ainihin shan giya su suna dariya suna kaine shi kaine shi annabi ya tashi duk da kazanta a jikin shi. Annabi na haddago kai sai ya daga hannu Allah ka kama kuraishawa Allah ka kama wane da wane. To kuma sai suka daina dariya domin duk kafircin mutumin makka yasan addu'a a wurin dakin nan tana karbuwa. Don duk a jahiliyya in aka cuce ka sai ka kullo gane mazgudun ka ka taho nan. To wanda ya cuce ka yana jin ka'aba zaka tafi sai yace a'a yo kai kuma abunda Allah ya yaba maka zo ka karbi kudin ka. Tun a jahiliyya azzaluman jahiliyya basu yarda azo a zo kusa gaban Allah a nan ka'aba ayi musu addu'a amma yanzu azzalumai yanzu wallahi in akwai wanda ya wuce ka'aba daraja tun zaku tafi sai ma su ya kamu ku tikiti. Saboda gaba daya basa shakkar Allah. Saboda haka Wannan shine irin wulakancin da annabi ya rinka fuskanta. Sabon shi a kwace musu mata a kure su daga gidaje a kwace musu runfokasuwa a murde musu gonaki a kama su a hanya a dake su. Da wulakanci yayi wulakanci alimamu muslim ya ruwaito hadisi sai wani sahabi yazo yace ya manzon Allah Baka gan wulakancin da ake mana ba? A dake mu a kwace mana mata a kwace mana dukiya bazaka rokan mana Allah ba? Annabi yana kwance ya tada kai da wani bargo a ka'aba. Sai ya mike yace kun cika gaggawa yo me akai muku daga an dan mare ka ko an harare ka ko an zage ka? Mutanen da Da zasu musulunta a kama mutum a sa zarto a tsakiyar madugashi Ace ko ya radda ko a tsaga shi bi bazai radda ba sai a tsaga shi bi? Yo kuma me akai muku yanzu yace kuyi hakuri yace wannan addini sai Allah ya tsai da shi. Sai Allah ya zaunar da addinin lafiya mutum ya koro dabbobin shi tun daga hadar maut kasar oman ta yanzu Har ya kawo madina ba wanda yake tsoro daga Allah sai dai kura kar ta fado mishi. Amma baya tsoron wani kafiri yace kuyi hakuri kuna da gaggawa ne. To ayoyi sai suka fara sauka Allah yana cewa annabi Kayi hakuri da hukuncin ubangijin ka tsarin ubangijin ka ne sai an shawo yaya addinin yake zama? Allah yace muna ganin ka da idanuwan mu. Allah ya sake saukar da ayoyi Ka rinka yin hakuri ka rinka kau da kai Duk sa'ar da suka gaya maka bakar magana kai kace zaman lafiya. Allah yace amma ba da dadi ya ba zasu gasa maka wannan kakin su. Allah yace Ka rinka yafewa kyakkyawar yafewa. Allah yace Fada wa muminai Su rinka kau da kai cigaba da abubuwan da kafirai suke musu don kafirai Basu yi imani da Allah ba balle su sa rai da wata rana da zasu hadu da Allah. A wannan lokacin duk hakuri ake bayar wa. Allah bai ce a yakesu ba. Allah bai ce a tsai musu da jihadi na takobi da takobi ba. Sai dai jihadi na da'awa a kira su zuwa ga addinin musulunci. Da tafiya ta fara ainihin tafiya sai Allah madaukakin sarki ya fara ainihin dagawa. Sahabban annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama cuta. Allah yace Kayi sanarwa ga wannan sahabbai bayin Allah musulmi da ake cutar su Akan cewa lallai fa an zalunce su kuma Allah yana sanar da an zalunce su. Kuma lallai Allah mai iko ne akan ya ainihin basu nasara. Wannan sahabbai sune bayin Allah da aka fitar da su daga cikin gidajen su ba dan sun cancanta a kore su daga gidajen ba Sai kadai dan sunce Allah ne ubangijin mu. Allah madaukakin sarki yace ba dan wasu mazaje ba. Wadanda suka tsaya domin kare addinin Allah da duk wani wurin ibada an rugurguza shi tun daga cocina na ibadar kristoci tun daga cocina na ibadun yahudawa har masallatai da musulmai suke ambaton Allah ambato mai yawa. Ba dan an samu masu jihadi ba Ga ba wani wurin ibada da za'a samu duk duniya da ma. Barin muku kyakkyawan misali a wannan zamanin ku gane ma'anar ayan nan. Tsohuwar tarayyar sofiet Wadda kasar rasha ta mamaye kasashen musulmi masu dimbin yawa irin su kasashen kosovo Da kasashen bosnia da makamantan su cecnia da sauransu. Wannan nan kasashe ne da ke cike da musulmi wadanda sun musulunta tun zamanin khalifa usmanu Allah ya kara mishi yarda.
[Speaker seg3-spk:1]
Amin.
[Speaker seg3-spk:0]
Amma da kasar ta danne su Sai da aka waye gari a yau da nake maganan nan Masallacin al-imam bukhari ya zama disco center wurin kada disco ne gayu ne suke rawa. Duk wuraren ibada an rusa su domin su wadannan mutane masu akida ta kasar rasha basu yarda da Allah ba basu yarda da kristanci ba basu yarda da yahudanci ba basu yarda da musulunci ba su gaba daya basu yarda da akwai wani addini a bayan kasa ba balle akwai Allah. Anan ne aka samu wani malami ya shiga cikin primary aji shi ne yana karantarwa yana son ya juyar da hankalin yayan musulmi ya nuna musu babu Allah sai ya rinka nuna musu da misalai na kusa da su. Sai malami ya daga duster yace yara me cece wannan suka ce duster abun shara da allo. Ya nuna allo me wannan suka ce allo me wannan kujera duk abunda ya nuna sai yace ashe akwai wannan abu tun da kuna ganin shi. Yara suka ce haka ne. Malamin primary yace to ina Allah? Kuna ganin shi yara suka ce a'a sai yace to babu Allah. Shinfidar da yayi musu kenan. Sai aka samu wani dan musulmi wanda ya sha akida ya batse Yace su can kasashe ne na yanci ba irin kasashen mu nan malami yayi magana baka da damar ka yayi ainihin raddi ba. Sai ya mike yace nima ina da tambaya yara Ya nuna allo yace yara me wannan suka ce allo? Ashe akwai allo yara suka ce haka ne. Me wannan duster? Yo ashe akwai duster suka ce haka ne. Me wannan table? Yo ashe akwai table yara suka ce haka ne. Sai yace to yanzu jama'a Ina hankalin malam? Kuna gani suka ce a'a sai yace to malam bashi da hankali kenan kenan To ya tunda logic ne ko ai logic da bara bata wuce da bara. Wannan yaro da wannan hikimar tashi ya kwace yayan musulmi a wannan kasa. To haka suka rinka yi sai da suka rinka ganin suna rugurguza masallatai da makarantun islamiyya da cocin coci na yahuda da kristoci anan ne zaka gan musulmi sunje taro wurin kristoci a coci ranar lahadi da ranar asabar kristoci ranar juma'a suzo su tsaya a kofar masallacin juma'a a sauka sallar juma'a suzo taro saboda yanzu wata da'awa tazo wadda gaba daya zata rusa su. Don haka yanzu hadin kan musulmi da kafiri ake nema kristoci. Ku karanta littafin Jama'a mun gane wannan da kyau ko? To jama'ar musulmi kun ji Allah yace ba dan an samu wasu tsayayyun mazaje ba to da tuni an rugurguza cocina da masallatai wadanda ake ambaton Allah amma sai Allah yace Duk wanda yake taimakon Allah sai Allah ya taimake shi. Allah mai karfi ne gagararren karfi Bayin Allah na gari wadanda ke taimakon addini sune wadanda in muka basu mulki a bayan kasa Zasu tsai da sallah yadda ake yinta sa'ar da ake yinta idan ake yinta yadda ake yinta sa'ar da ake yinta su ba wadanda suka cancanta Sai umarni da kyakkyawan aiki Salaman munan aiki Karshen al'amura duk baki daya na Allah ne. Wannan aya itace ayar farko wadda ta sauka a qur'ani a garin madina wadda take dagawa musulmi tutar to lallai akwai wani abu nan nan zuwa Wanda nau'i ne na jihadin bugi in buga. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? A cikin wannan ayar akwai abubuwa guda uku abu na farko shine Allah ya nuna muminan nan yana sane da ana zaluntar su. Saboda an kore su daga gidajen su an kwace musu dukiya an kwace musu mata ba dan komai ba sai dan sunyi imani sun ce Allah ne ubangijin su. Abu na biyu Allah madaukakin sarki ya nuna ba dan wasu mazan kwarai ba to da tuni ma ba'a wata ibada a bayan kasa da sunan Allah. Abu na uku Allah madaukakin sarki yake nuna cewa Abunda ke kai muminai ga matukar nasara itace tsayar da sallah bada zakka da umarni da kyakkyawa da hana ainihin munmuna. Jama'ar musulmi Kuyi hakuri wannan shinfida ce nake a gurguje nake yinta domin matsalar jihadi mun taba yima ma'aji akan menene jihadi a musulunci? To ina dan yi mana wannan ne a matsayin tinasarwa. To a shekara ta biyu wadda malamai na usulul fikhi suka fi sanin ta da Shekarar kafa shari'o'in musulunci. A wannan shekara Allah madaukakin sarki ya farlanta jihadi Ayar farko da ta sauka itace Allah yace An farlanta muku jihadi yaki ko da yake kuna kyamar shi Amma so da dama kukan kyamaci abu shine alheri gare ku So da dama kukan kaunaci abu ya zama sharri ne gare ku Allah shike da ilimi ku baku da ilimi. Wannan itace ayar farko da ta fara sauka game da ainihin farlanta jihadi ta sauka a ainihin shekara ta biyu. To shi jihadi saboda yadda shari'ar musulunci take da nazari kyakkyawa bata farlanta shi akan kowa da kowa ba. Sai da ainihin ta kasarta abun tsari tsari. Daga cikin al'umma akwai wadanda jihadi ya zama wajibi akan su wajibi na wajabci shi ake kira Wane na irin jama'a ne wadannan? Sune al'ummar musulmin da makiya suka kwado suka rusa su to a wannan halin Hatta mace da ke cikin gida Zata futo da muciya ko tabarya ta tsaya a kofar gida. Ba'a rage wa kowa ba Ko balaratu kar albasa ka samu ka saka a aljihun wando in ta rusa maka wani wuri ka yanke wani. Duk yadda za'a yi a irin wannan halin kowa jihadi wajibi ne domin wannan Jihadi ne na tunku da makiya wadanda suka tayar ma rugurguza kasar addinin musulunci. Irin jihadin da yake wajibi akan musulmi musamman da ke kasar iraki a yau dole ne su tsaya su gwagwarmaya su ga sun kore arna kafirai yahudawa kristoci mutanen kasar amerika da su da yan tawagar su ba dan komai ba dan su sarkake kasar Allah daga kafirai makiya Allah. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Wannan kenan. To bayan wannan Allah madaukakin sarki a cikin hikimar shi Sai kuma ya sharlanta jihadi ga wasu ya zama farlu kifaya shine in wasu suka tafi ya fada akan wasu wannan shine jihadin fada da kasashen musulunci jihadi na da'awa jihadi na nunawa duniyar musulunci mai musulunci yake ciki. Wasu su tafi wasu kuma su tsaya a gida wannan shine ainihin isharar da Allah madaukakin sarki yake a cikin al'kur'ani a yadda yake cewa Bai dace ga muminai baki dayan su su fita ainihin jihadi ba. Ba daidai bane duk musulmi su yore su fita su tafi jihadi Sai dai a samu wasu su fita wasu kuma su tsaya koyon addini yadda in wadannan suka dawo wadannan sai su ainihin karantar da su addini din domin su ainihin bi dokar Allah baki daya. Jama'ar musulmi wannan shine tsarin musulunci game da ainihin wato sharlanta shari'a ta ainihin jihadi. Kamar yadda na fadi a dazu ba kowa aka farlanta wa jihadi ba To su wa kenan aka farlanta wa? Nau'i na farko na daga wadanda aka farlanta wa jihadi Musulmi ne su kadai suke jihadi. To musulmin dole sai an samu namiji sannan ya zama wajibi akan shi ma'ana jihadi anan ba wajibi bane akan mace. Namiji mai hankali Balagagge Lafiyayye wanda ba gurgu ba ba makaho ba Wanda kuma yake da wadataccen da zata ishe shi ya barwa iyalan shi sannan ya guzurin da zai tafi. Har ya dawo to wadannan irin nau'in sune jihadi yake wajibi akan su. Da muka ce jihadi farilla ne akan musulmi kafiri baya zuwa jihadi. Musulmi namiji mace tana iya zuwa jihadi amma ba dan tayi jihadi a aikace ba Sai dan suyi wasu hidindimu Kamar a samu wadanda zasu rinka dafawa musulmi abinci su rinka ainihin kula da wadanda ake jiwa rauni daga cikin sojojin musulunci. Aisha da ummu salama sunce suna yin haka idan an tafi jihadi. Mai hankali mahaukaci baya zuwa wurin jihadi. Baligi yaro ba farilla bane yaje wurin jihadi amma in yace zai je sai a barshi. Kamar yadda aka samu cikin sahabban annabi sallallahu alaihi wasallam abdullahi dan umar yana daga cikin yara kanana da suke zuwa jihadi tun basu balaga ba. Akwai kanin sa'ad bin abi wakkas yaje jihadi yana shekara goma sha shida aka kashe shi. Wani daga cikin ainihin sahabbai yaso yaje jihadi yana karami Sai annabi yace mishi kayi kankanta Sai ya cewa sai ya koma gida yana kuka sai yaje ya samu mijin mahaifiyar shi Yace yaya annabi zai hanani zuwa jihadi Bayan ga wane an kyale shi ya tafi Kuma in munyi fada da wane ina kayar da shi. Sai shi mijin koren yaje ya gaya wa annabi cewa dan gidan mata ta yace kaza kaza kaza annabi yace ka kawo shi. Da aka zo da shi Sai yace tun muna kanana in munyi dambe da abdullahi dan umar ina ka da shi. Ya za'a ce shi ya tafi ni kuma a kyale ni ai tsawon kafa ya fini kawai. Sai annabi yace to kuyi damben anan mu gani. So kama ko kowa Sai ya dauki abdullahi dan umar ya lika da kasa. Sai annabi yace to dukkan ku ku tafi kai kwage ne kwagantakar ka ka ka kai ka kai kuma tsawon kafa kai kai ka. Don haka ko yaro karami yace zai je jihadi za'a ainihin barshi yayi ainihin je jihadin nan. Amma ba a matsayin farilla ba a matsayin an kyale shi yaje domin zuciyar shi tayi karfi. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Allah yace Babu laifi ga makaho ko ga gurgu ko ga mara lafiya in basu je ainihin jihadi ba. Idan ka fahimci yadda muka kasarta jihadi a baya kai dan uwa na da kake saurare na cewa akwai jihadi na farlu ainihin akwai na farlu kifaya. To wannan shike lazimta wani kaso na jihadi. Game da harkar jihadi akwai neman izinin iyaye. Idan uwar ka da uban ka suna da rai Ko uwar ka na da rai ko uban ka na da rai in zaka tafi jihadi irin jihadin farlu kifaya jihadin fada da kasashen musulunci sai in baban ka yayi maka izini. In ba haka ba bazaka je ba sai in uwar ka tayi maka izini in ba haka ba bazaka je ba in daya daga cikin iyaye yayi maka izini daya yace bai yarda ba dole ka janye bazaka je ba. Domin izinin ba lallai bane kaje Amma barin lallai ne ka bari. Kana da uwa da uba suna da rai Sai aka ce zaka tafi jihadi jihadin fada da kasashen musulunci. To anan sai mahaifiyar ka tace ta yarda kaje sai baban ka yace bai yarda kaje ba to bazaka je ba. Ko akasin haka mahaifin ka yace ya yarda kaje babar ka tace baka yarda ba bata yarda ba bazaka je ba. Allahu malamai suka ce sai in limamin musulmi ne ya ayyana sunan ka Ya rubuta sunan ka cewa kana daga cikin sojojin da zasu je to anan kuma dole iyayen ka su kyale ka kaje ko da basu barka bazaka tafi. Karanta littafin Jama'a mun gane wannan da kyau ko? To jama'a wannan shine tsarin musulunci game da al'amarin da yake a ya shafi jihadi. Idan muka zo muka ce zamuyi magana akan falalar jihadi da masu jihadi kuwa To gaskiya masu jihadi sun kwashe kashe sun kwashe gyara. Basu barwa wanda baya jihadi komai ba. Don haka a cikin hadisin da al-imam ahmad da muslim suka ruwaito sahihin hadisi annabi sallallahu alaihi wasallama yace mutumin da ya mutu
[Segment 4/4 | 01:00:00–end]
[Speaker seg4-spk:0]
bai yi jihadi ba, zuciyar shi bata taba kyanƙesa mai tunanin yayi jihadi ba. To in har ya sake ya mutu a irin wannan hali, yayi mutuwa irin mutuwar maguzawa. Irin mutuwar baƙaƙen arna. Mutuwar jahiliyya, mutuwar da ba'a taba jin labarin musulunci a gidan ba. Abu na farko kenan. Abu na biyu imamu musulmi ya sake ruwaito hadisi annabi sallallahu alaihi wasallama yace mutumin da zuciyar shi take kaɗa mai, take riya mai game da jihadi sai ya mutu bai taba jihadi ba ko da a kan keson shi ya rasu. Annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama yace Allah zai kai shi matsayin masu mutuwar jihadi a ranar alƙiyama a aljanna. Kaga wannan daraja ce. Na daga cikin darajojin mai jihadi al imamu bukhari ya ruwaito hadisi sahihi. Annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama yace mutumin da aka yanke shi a wurin jihadi jinin nan da yake zuba ranar alƙiyama zai tashi jinin yana zuba da kalar jini jawurin amma ƙanshi kuma ƙanshin miski. Jama'a ku gane wannan da kyau, ƙanshin turaren miski, turaren da ko a aljanna babu ishi. Wannan hadisan annabi sallallahu alaihi wasallama kenan. Alƙur'ani ko Allah cewa yake Wannan aya ko da Allah bai taba saukar da wata aya game da falalar jihadi ba, Allah wannan kaɗai ta isa. Allah yace Allah yace ni kin rayuka da dukiyoyin muminai ciniki ne mai jihadi ake neman ya ƙulla da shi da Allah. Ciniki ne zaka ɗibi kuɗin ka ne ka bayar ka tafi jihadi ko ka bayar a tafi jihadi ka ɗauki ran ka ka tafi jihadi shine cinikin. Sannan kai kuma kuɗin da Allah zai biya ka Allah zai biya ka ne da aljanna. To amma a wacca kasuwar duniya za'a ainihin yi wannan ciniki da kai da Allah? Sai Allah yace a fagen jihadi a wurin yaƙin ta da addinin Allah. Muminai su je su kashe a kashe su. Wannan tabbataccen alƙawari ne Allah ya azawa kanshi. Yana nan rubutuce cikin attaura da injila tabbatacce ne a cikin alƙur'ani da Allah ya saukar da fiyayyen halitta. Sai Allah ya tsaya a nan ya ajiye alamar tambaya yace dan Allah ya ku jama'a, waye fa Allah ya cika alƙawari?
[Speaker seg4-spk:1]
Allah ya cika alƙawari.
[Speaker seg4-spk:0]
Wannan ciniki ne tabbas ranar ƙiyama ranar biyan ka kar ka taba tunanin alƙawari ne irin na ƴan siyasa. Alƙawari ne tabbataccen alƙawari gashi yake cewa dan Allah waye fa Allah ya cika alƙawari? Babu, sai Allah yace Albishirin ku ya ku masu jihadi Allah zai biya ku.
============================================================
[Part 2]
============================================================
[Speaker spk:0]
Ya koma su jihadi Allah zai biya Annabi san Annabi sallallahu alaihi wa sallama ke Alqur'ani ko Allah ce wa yake Wannan aya ko da Allah bai taba saukar da wata aya game da falalar jihadi ba Allah wannan kadai ta isa Allah ya ce Allah ya ce ni kin rayuka da dukiyoyin muminai Ciniki ne mai jihadi Ake neman ya kulla da shi da Allah Cinikin Zaka i duk kudin ka ne ka bayar Ka tafi jihadi ko ka bayar a tafi jihadi Ka dauki ranka ka tafi jihadi Shine cinikin Sannan kai kuma kudin da Allah zai biya ka Allah zai biya ka ne da aljanna To amma a wacce kasuwar duniya za'a ainihin yi wannan ciniki da kai da Allah Sai Allah ya ce A fagen jihadi A wurin yakinta da addinin Allah Muminai su je su kashe a kashe su Wannan tabbataccen alkawari ne Allah ya azawa kanshi Yana nan rubutacce cikin at-taura Da injila tabbatacce ne a cikin alqur'ani da Allah ya sauko da fiyayyen halitta Sai Allah ya tsaya a nan Ya ajiye alamar tambaya ya ce dan Allah ya ku jama'a Waya fa Allah ya cika alkawari Wannan ciniki ne tabbas Ranar kiyama ranar biyan ka Kar ka taba tunanin alkawari ne irin na yan siyasa Alkawari ne tabbataccen alkawari gashi yake cewa dan Allah waya fi Allah cika alkawari babu sai Allah ya ce Albishirin ku ya koma su jihadi Allah zai biya ku cinikin da kuka kulla da shi Wannan samun labura kiyama shine babban rabo Jama'a wannan aya Tana bayyana falalar jihadi Sai dai fa jihadin da kayi shi saboda Allah Jihadin da kayi shi ba dan a ce kayi sadauki ba Saboda sahihin hadisi da al-imamu Ahmad ya ruwaito a cikin kitabul musnad Da al-imamu Muslim a cikin kitabul jihadi Al-imamu Muslim da Ahmad suka ruwaito Annabi sallallahu alaihi wa sallama ya ce Ranar alkiyama Mutane guda uku zasu sha kunya Mutum na farko Shine mai jihadi A daga shi Tsakanin halittu tun daga na farko har na karshe A ce ya kai sadauki Ya kai kaura Da kai jihadi Kaine dan me Ya ce ya Allah nayi ne saboda kai sai Allah ya ce ka zarta kai ya kake Kaine dan a ce kai sadauki ne kuma an fada a duniya ta huta Don haka duk kana jihadi ne dan a ce kai sadauki ne Duk nau'o'in jihadi da zamu zo mu fada In ka nene don a ce kai sadauki ne da kudin ka da dukiyar ka da iyawar ka da shawara ka da menene kaine don a fada ranar kiyama ko binciken ka ba za'a yi ba bayan binciken sababin da yasa kai jihadi wuta zaka tafi kai tsaye Na biyu malam mai wa'azi ko mai karantarwa sai Allah ya kamo shi ya ce malam kayi wa'azi ka karantar Saboda wa'azi ya ce saboda kai sai Allah ya ce ka zarta kai ya kake Kaine dan a ce alimun malami Ya iya Ya sani Ya san hujjoji ya iya jan baki ya iya li'irabi ya iya kwamidu an fada Baka da sakamako wurin naka huta Na biyu mai kudi mai taimakon jama'a Ya taimaka wa talakawa Ya taimaka wa gajiyayyu da na kasassu Sai Allah ya kira shi ya ce kayi saboda waye ya ce saboda kai Sai Allah ya ce kai ya kake kayi ne dan a ce kai mai taimakon jama'a ne kuma an fada ta huta Wadannan irin mutane Sun gama shan kunya gaba daya domin sai da aka daga su a tsakanin halittu tun daga na farko har karshe Sannan Allah da kanshi ya tabbatar da cewa basu yi dan shi ba Sun yi dan a fada ne kuma an fada Allah kuma ba'a yi mai dan ayi wa wani ko kayi wa Allah shi kadai Ko kayi wa wane shi kadai amma ba'a raba kafa da Allah Jama'a mun gane wannan da kyau To matukar kayi dan Allah kaji sakamakon ka Aljanna itace makomar ka Mutumin da aka kashe shi a filin jihadi jama'a Ranar alkiyama Annabi sallallahu alaihi wa alhi wa sallama ya ce za'a bashi dangin shi mutum 70 ya cece su Dan Allah ka lissafa da kyau ka ji kana da dangi 70 Ranar alkiyama za'a baka dangi 70 ka cece ta in kayi mutuwar shahada a filin daga Yasa dan ku ya je an kashe shi saboda addinin Allah Ba cewa za'a yi to gashi nayi asarar ran shi ba a'a Allah ya ce a hir kar baku ce musu matattu Sai dai ku ce Suna can suna rayuwa Allah na ci she su a wurin shi Jama'a mun gane wannan da kyau ko Wannan na daga cikin ainihin falala ta ainihin jihadi Idan muka koma muna maganar falalar masu jihadi Al-imamu Bukhari da Muslim sun ruwaito hadisi daga sahabi Jabiru dan Abdullahi Allah ya kara mishi yarda Jabiru ya ce An kashe mahaifin shi a lokacin da aka je yakin Uhudu Da aka kashe mahaifin shi sai aka hada mahaifin shi da mijin Ainihin wato Kanwar mahaifin shi aka rufe su a kabari daya saboda an kashe sahabbai 70 a wannan rana Da yanzu sun yi wa sai Annabi ya rin a hada mutum biyu mutum uku a cikin kabari daya To da Abdullahi dan Hiram mazan Jabir Da ainihin mijin Kanwar shi Sai aka hada su a kabari daya Jabiru ya ce shi mahaifin shi Abun da ya faru an yanke shi ne a cinye da wuka Da ya dafe wurin jini ya ci gaba da zuba har jini ya dige mishi ya rasu Aka yi aka yi a bamfara hannun aka kasa haka aka saka shi a cikin likafani haka aka saka shi a cikin kabari Jabiru ya ce kullum sai Annabi ya ganni nayi tagumi Tagumi alamar damuwa ce dan haka yazo cikin hadisi Annabi ya hana tagumi Ya hana zaman dafe ya hana kwanciyar ruɗɗa ciki To tagumi alamar damuwa ce Sai Annabi sallallahu alaihi wa sallama ya ce ya Jabiru me yasa kullum nake ganin kana tagumi Sai ya ce ba wani abu bane ya manzon Allah Damuwa ce ta hadu ta har hade mini An kashe mahaifi na a wurin jihadi Uhudu Ina da takaicin mahaifi na ya mutu ya bar ni ina yaro karami Mahaifi na yayi mini wasiyyar kanne na yan mata guda tara Ya ce u kula da su in tarbiyar su in aurar da su nima kuma ban yi aure ba ta kai na nake Yanzu a ce yaro dan shekara 10 sha bakwai u bar shi ya mutu ya bar mai kanne yan mata guda tara ya ce ya ci da su ya sha da su ya tarbiyar su ya auratar da su Sannan kuma ba uwa daya suke ba uwa daya ne yan uwa da bahaushe ke cewa Wannan ba sai na miji ba Yanzu miji don a musulunci babu wani maganar yan uwa in kaji ana maganar yan uwa a musulunci wuri daya ne wurin raba gado Bayan wannan babin ba inda musulunci ya raba yan uwa da uwa daya uwa daya duk daya ne Domin daga kwankwaso na miji daya suka Jama'a mun gane wannan da kyau ko Saboda haka a cikin tsarin addinin musulunci babu bambanci ku daina bambance wa Kaine babban wa na gida Wancika sai mata kaza saboda dakin ku daya wancika ki sai mata wallahi wannan yanke zumunci ne kaji tsoron ran da Allah zai tuhumce ka akan haka Wanc dakin ku daya wanc ba dakin ku daya ba ya wai uban ku daya abin da zaka yi wanc shi zaka yi wanc duk daya ne wannan shi itace shari'ar musulunci Jama'a mun gane wannan da kyau Abu na farko dake damun Jabiru uban shi ya mutu abu na biyu an bar mai tarbiyya da kula da yan mata tara Jama'a yanzu Uhudu ruwa daya aka ban maka da ita A aiki Ya zaka yi kai tarbiyyar ta ka hana ta kai da koma wannan da yan mata suke Ya zaka yi kai tarbiyyar ta ta zama mutum mai kirki balle yan mata tara tarbiyyar mace ka fita na miji wahala Na miji in ka sai mishi dan falalar alawus na naira 10 sha biyu kadan ka manya sa hular shi ranar sallah a gaban ku shi ya hadu Amma mace sai an kashe wajen dubu biyu Sannan sai ta ce wai akwai sarka ba'a siya ba Akwai dan kunne ba'a siya ba akwai dagogorogo ba'a siya ba Zaka ga matsala ta faru tarbiyyar mace tana da wahala dan haka yazo cikin hadisin Muslim Sahihin hadisi Annabi ya fadi falalar tarbiyyar yaya mata Annabi ya ce wanda duk Allah ya bashi yaya mata a kalla kwaya biyu har yayi tarbiyyar su ya aurar da su Annabi sai ya ritsa yakin shi haka ya ce ranar kiyama haka zamu zauna da wannan mutum ka fada da ka fada Dan haka albishirin ka ya kai da ake haifan maka yaya mata baka so Ka tuba ka koma ga Allah yaya mace daraja ce Uwar Ha'a Maryamu Hannatu da na miji ta so ta haifa Sai ta haifi mace Ya fa tun na miji ne yake kamar wata macen ba yanzu duk taron nan an tara mu zamu kai kamar Maryamu uwa Annabi Isa To ka gani Jama'a mun gane wannan da kyau ko Duk abin da aka samar maka ka ce Allah ya sa albarka duk mutumin da ya ki a mace haihuwar ya mace ya dauko tunani na maguzawa ya marmar zai tuba A jahiliyya in aka zo aka ce wane matar ka ta haifu yana dandali yana cikin abokai ana hida ana nishaɗi In ya ce me aka haifa ana cewa mace ce sai ya jawo rigar shi ya rufe kan shi sai abokai su dinga dungure shi ana yi ho an haifan mishi mace yi ho sai ya gudu ya tafi yana shawara zai je ya haka rami ya binne ta ne ko ko shi zai gudu ya bar garin Allah ya ce Allah wane ran irin wannan hukunci nasu Jahiliyya maguzanci ce jama'a Sayyidina Umar ya taba kashe ƴar shi a jahiliyya Ya hada ta aka yi mata ado tsaf Ashe ya haka rijiya suna zuwa daji sai ya wurga ta ya ja kasa ya danne Sai da ta mutu haka suke a jahiliyya Jahiliyya kada Allah ya nuna mana jahiliyya jama'a Jahiliyya ko abin kar kayi fatan ka gan ta muguwa a bace Allah ya kiyaye Jama'ar musulmi Wannan shine kashin farko na shinkudar wannan wa'azin namu Amma abu guda da ya rage shine bayani dangane da nau'o'in jihadi Wannan shinkudar zata taimaka wajen ka gane aikin dan fodiyo Nau'o'in jihadin nan da muke magana a takaice malamai suka ce jihadi Daga an fade shi mutane sukan yi tunanin yakin takobi da takobi Amma fa yakin takobi da takobi shine matakala ta karshe daga cikin matakai guda hudu na jihadi wadanda matakan nan guda hudu ta farko itace jihadun nafsi Jihadun nafsi Na biyu shine jihadun shaitani na uku shine jihadun kuffari na hudu jihadun munafikina a takaice abin da ake nufi da jihadun nafsi shine mutum yayi iyakar iyawa ya yaki kanshi da kanshi a wajen ya je ya koyi ilimin addinin musulunci ya san addinin gaskiya domin ya bauta wa Allah da ilimi kada ya bauta wa Allah da ka wannan shine jihadin farko ya kai dan uwa na da kake saurare na Ko ka samu kan ka a irin wannan jihadi Kana zuwa makaranta Uku kana nan ka zauna kana jiran sai kaji matsalar musulunci ta taso kawai ka ci magogi kasa bakin ka to zaka shiga wuta Mutane sun waye gari a yau Sun daina zuwa karatu A yau an waye gari mata ne suke cika makarantu da yaran islamiyya Amma maza ba ruwan su Sai gari ya waye sai ka tura yaro ya tafi gabas islamiyya kai kuma sai kayi yamma Kana tafiya shima sai ya zarga hular hudu shi dan nan ya gan ta fa dala tunda da yanzu ka kasa da Domin ya lalata shi kai ya zaka kora shi ne nan gangare kai kuma kayi sama Ya dawo shima ya bika dan ya san can tafi falala dan haka ka bi shi Domin tarbiyya ba abun baka bace tarbiyya a aiki ne Sayyidina Abubakar da girman shi aka koya mai ilimi Sayyidina Umar da girman shi yana da mata yana da ƴaƴa yana da jikoki duk abin da kake kuka da shi kenan iyali sun maka nauyi Sayyidina Umar ya ce da ni da makamci na sai muka raba yau yaje makaranta ni in je kasuwa ni in dawo da ainihin cefane shi ya dawo da ilimi ni in ciyar da gidan mu da daddare shi kuma ya biya mun karatun da ya dauko Gobe ni in tafi makaranta shi ya tafi kasuwa shi yazo da cefane ni in zo da karatu ya ci mana da gida ni in biya mana karatu ya ce da haka na waye gari na samu ilimi Iya kacin abin da kake kuka da shi kenan da kake cewa ƴaƴa iyali sun maka yawa Masara ta danne ka To wallahi idan wannan masarar baka yi kokari ka danne ta ba kasa zata danne ka a cikin bakin jahilcin da baza ka iya bada amsar dalilin shi ba Yasa dan uwa na ka garika wa'ili ka tafi makaranta gobe da safe Da duk ahalin ka ka tafi makaranta Zari juzu'in an maka dai a koya maka amma wallahi in ka sake mutuwa tazo ta same ka da jahilci Allah Zaka ci bakin duka na wulakanci haka hadisi ya ce Nasun hadisin Bukhari Ya ce in aka tambayi kafiri Ko munafiki mar rabu ka waye uban gijin ka Bai san amsar da zai ce ba Sai dai yace ha'a yayi ihu ya dauki guduma a daki tsakanin kunnen shi da keyar shi Wata jijiya ce a wurin wadda take da gaggawar isar da sako ga dukkan jiki In baka gane ma'anar wannan hadisin baka je ka dauki karamar guduma yau da daddare ka dan kwankwasa ka Zaka ga muhimmancin Jihadi Da ran
============================================================
[Part 3]
============================================================
[Speaker spk:0]
jihadi da ran shi kai gugur maya duk yadda za kai ka yaƙi shaiɗan ka je ka koyi shirya To yanzu don Allah haka ake jama'a? Allah ya shiryar da mu. Nau'i na biyu mutum yayi jihadi akan aiki da ilimi wannan jihadin yafi na farko kuma kayi jihadi wajen ka koya kayi jihadi kuma in ka iya kayi aiki da sanin sannan sai kuma nau'i na uku shine jihadi wajen da'awa wajen yaɗa wannan ilimin da karantar da wannan ilimin idan ko ba haka ba to hukuncin waccan aya ta cikin suratul baƙara zai hau kan ka waɗanda suke ɓoye ilimi waɗanda suke ɓoye shirya da gaskiya da Allah ya saukar Allah yana la'anar wannan jihadin shine
============================================================
[Part 4]
============================================================
[Speaker spk:0]
wannan jihadin shine nau'i na hakuri akan da'awa. Da ka fara da'awa za a canza maka suna, domin da'i na farko sunan shi Muhammad. Saboda nagarta suka sa mishi Al'aminu. Yana fara da'awa sai suka sa mishi Azzalimu kuma. Dan suke ce mishi Muhammadun Al'amin, Muhammadu amin fect can Allah. Yau kuma sai suka dawo suna ce mishi Muhammadu Azzalim. Suka dawo suna zagin shi. Suna mishi sharri. Suna zuga kauyawa da wawaye akan shi. Har jita jita ta kai wani bakauye kauyen su boka cewa wani saurayi Muhammadu ya taba. Aljanu sun kada kai shi yana zagin alloli. Boka ya hado kayan aikin shi ya shigo birnin Makka. Yana zuwa ya ce jama'a ku nuna mana Muhammadu, na ji ance ya taba yana zagin alloli akan shi haka abun yake. Ina yake? Suka ce gashi nan suka nuna shi. Ya je ya samu Annabi cewa labari yazo gare ni. Aljanu sun tare ni kana zagin alloli. To ni kuma ina maganin shine na kwaso kayan aiki in zo in taimake ka ko kana bukata? Ka gani yake Annabi mai da'awa ne yanzu kai in kaine yanzu nan sai kayi kutu fo ka harbe shi, to kaga ya tafi da maugaci za a nemo jama'a a yi ka. Sai a fara aiki ba haka bane? To amma sai Annabi ya ce akwai dadi. Sai ya sake maimaita mishi ka sake maimaita mishi akwai dadi sai ya sake maimaita mishi. Sai ya ce ka miko hannun ka. Annabi ya miko hannun shi sai wannan mutum ya ce Ya ce naji wakokin mawa'aka, na tabbatar kai ba mawaki bane. Duk wani surkulle na masu surkulle ya ce naji. Bokanci kuma na tabbatar ba bokanci kake kamar yadda ake jita jita ba, na tabbatar Annabin Allah ne kai kuma musulmin ka ne ni. Ka sake miko hannun ka. In sake karban kalmar shahada in kai wa mutanen kauyen mu. musuluntar maka da su kafin ka zo. Annabi ya sake miko mai hannu ya sake bashi kalmar shahada ya dauka ya kai wa mutanen kauyen su. To Annabi mutum ne mai alheri. Hadisin Aisha cikin Bukhari Kitabul Ilmi ya ce Annabi yafi hatta iskar da ke yawo a gari alheri. Ka gani iskar da ke yawo a gari talaka na sha mai kudi na sha. Mai kudi ma wani lokacin ya kondishen shi in ya dimiya dagi sai ya fito waje yana shan ga talakawa. To Annabi yafi wannan iskar alheri. Haka Aisha da ce Annabi yafi iskar da take yawo alheri. Ka duba mutumin nan yazo da bakar magana ne. Yazo da zargi ne ya jita jita. Amma da Annabi ya gaya mai kalmomi masu dadi na musuluntar shi. Da Annabi ya dibi raguna guda dari ya bashi ya ce gashi kayi guzuri. Me ya faru? Bakauye yana zuwa kauye sai ya tsaya a bada lar kauyen su. Kofar kauye kenan baka sani ba kenan barin shi. Ya tsaya a bada lar kauyen su ya ihu. Aka ce lafiya aka taro? Ya ce ku je Madina ku musulunta wurin Muhammadu, ku je Makka ku musulunta wurin Muhammadu. Muhammadu na kyauta kyautar irin mutumin da baya jin tsoron talauci. Ya ce kunga kalmar shahada na fada kawai ku dubi tsaraba rabo dari. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? To alherin Annabi ya wuce da nan. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? To ya jama'ar musulmi da ka fara da'awa za a fara zagin ka. Za a canza maka suna. Za a yi maka sharri. Kar ka rama ka cigaba da da'awa. Allah ya ce ka doke ka cigaba da abin da aka umarce ka. Ka kauda kai gaba da wawaye. A kasar Larabawa akwai makarantu da ake karantar da yadda ake da'awa yadda ake wa'azi. Har digiri ake zuwa a yi a yi digirin digirgir a dingire ka zama doctor a ilimin da'awa Ga sunan jami'o'i ko ina kake sai ka ji Ya ake wa'azi? Ya ake mu'amala da jama'a? Duk abin da suka yi maka sai ka hakura. Duk abin da suka fada akan ka sai ka hakura kai mai wa'azi ne. Da da ka fara baka fara wa'azi ba baka farawa da kowa ba. Ba ruwan kowa da kai kowa yana son ka. Kana fara wa'azi shikenan ran nan wani kawai tun baka zo wa'azin kan shi ba yana sayar da shinkafa ne, yana sayar da wake ne, yana sayar da gero ne, yana sayar da dabbobi ne, yana sayar da kaza ne in ka fara wa'azi akan maroma sai ya fara yi maka haushi tun fa ba a fara akan na au ba. Saboda ka fara wa'azi. To sai ka hakura duk abin da za a fada kar ka rama. Domin kai Allah kake wa aiki. Da mutane kake wa yau dan me za ka fada musu a alheri? Baka ganin sarakuna basu son kowa ya gaje su sai 'ya'yan su? To amma malami sai ya fito ya tababatu yana fadi ana zagin shi. Me yasa? Saboda aikin Allah yake ba aikin uban shi yake ba. To wannan nau'i ne na jihadi jama'a. Sauran bangarorin jihadi da ya shafi jihadi da shedan jihadi da shedan shine ka ringa kokarin duk shubuha da shakka da shedan zai saka maka a zuci ka ringa kokarin kawar wa. Idan ta gagara ka kawar ka ringa ta'awwuzi. Jama'a mun gane?
[Speaker spk:1]
Na'am.
[Speaker spk:0]
Na daga cikin nau'in shedan a jihadin da za ka yi gaba da shedan tun kude ainihin irin barna da shedan zai ringa saka ka kana yi to kayi kokari ka ga ka yaki zuciyar ka, bakin ka, gabobin ka to in ka tabbata haka zuciyar ka duk wata shakka da ya sa maka ka kawar. Kar ka sake bakin ka ya fadi wata muguwa ko wata baka daga cikin kalmomi. Kar ka sake gabar ka ta aikata wani mugun aiki to ka gama da shedan in kayi haka. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Jihadin kafirai da munafukai shi kuwa wannan nau'i nau'i ne shima. Na daga cikin jihadin kafirai da zuci kake kafirci da zuciyar ka. Ka zo ka kira su zuwa ga addinin musulunci da bakin ka. Ka dibi dukiyar ka ka tashi kai da kan ka kuma ka je ka yada addini a inda kafirai suke. Jama'ar musulmi abin tambaya ko yanzu ana jihadin kafirai irin wannan? Daga idda shehu Danfodiyo ya bar musulunci ko an matsa da shi gaba ko ko sai bayan ma ya je? Ku je jihar Kogi, jihar Kogi tana daga cikin kasashen da ke karkashin mulkin Danfodiyo. Yanzu radda suke ta yin mutanen ainihin auci da wasu makamantun su. Me yasa? Ba je an karantar da su addinin musulunci ba. Christian Evangelist kuma suna can suna aiki. 'Yan mishan kristoci suna can suna ta yada bishara. Har ya kai mana daga aikin da kristoci suke yanzu a Najeriya ta Arewa suna tura 'yan Arewa kristoci wadanda suke jin Hausa kamar 'yan jahar Kaduna da 'yan jahar Plateau da 'yan jahar Bauchi da 'yan jahar Adamawa ana tura su kasar Masar da Iraki da Kuwait su je su koyo larabci a hannun kristoci Larabawa sai su zo su shiga kauyuka irin kauyukar da ke kewaye da kasashen Zariya da makamantun su. Irin garuruwa a kasashen Ekera da kewaye garuruwa da ke haka. Kristane, pasto ne sai ya sa babban riga da 'yar ciki da wando yayi rawanin. Sai ya riko carbi amma carbin idan kai ba natsuwa kake da ita ba ba za ka gane carbin kristoci ne ba. Madadin carbin ku da kuke sa ladan daliman da wacce tsiya ne su kuma kuros suke sawa. Sai ya riko in ya shiga kauye da Bible amma na larabci sai a shiga da majabaki. A ce to an saba a nemi ku wa'azi da Alkur'ani to Kur'ani gaskiya ne sai in ne mutanen kauye
============================================================
[Part 5]
============================================================
[Segment 1/4 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
To kur'ani gaskiya ne. Mene mutanen kauye? Annabi yace wanda duk ya zauna kauye zai yi jahilci. Kaje ka ga limamin kauyen da sallah take shan wahala a hannun shi balle mamu. Kauye. Shi yasa balaraben in yazo zakka in ka sai yace Allah ya maida kai kauye. Kauye akwai jahilci. Wani yana nan a kauye bai san kur'ani ba. To haka ja baibul da larabci sai a ce Wallahi daya daga cikin su da yayi musulunta muka dauko shi muka yi zaman hira da shi a Abuja, kasad din yana nan muka yi awa shida da shi na bidiyo. Da kanshi yake fada mana yace a nan kasar Zaria akwai inda suka je liman ne mai suna Abdullahi suka maida shi kirista ya zama Abdul Masihu. Idan kuma ku je kun yada addinin musulunci ba su zasu je su yada daga nan fitina zata faru. Yau wata biyu da suka wuce na je garin Goza. Garin Goza daga nan garin zai kai ka ma tafiyar awa goma sha biyar. Dan sai ka wuni dindinka ne ka shiga dare kuma sai ka bi wajen karfe tara na dare in ka tashi tun karfe shida. Daga nan garin in kace zaka je Goza sai ka kai kamar karfe tara ko goma na dare. Wannan kana gudu kenan ma ba tsayawa sallah ba cin abinci. Can Goza in ka bar Yola baka kai mai dugurba tsakiya, gari ne mai cike with duwatsu. Naje nayi musu wa'azi na kwana biyu a lokacin nan sarkin garin muke hira da shi yake cawa muna zuwa musuluntar da maguzawa yace duk sanda muka je akalla mutum dari su musulunta. Yace to amma matsalar muna da karancin malamai. Yace mu kuma ba malaman bane. Muna kuma da karanci yace kuma malaman basa zuwa garin. Yace tafiyar karshe da mukayi mun musuluntar da fiye da mutum dari da sabain. Yace da kiristoci suka ji labari da suka ji labari sai suka tura guda dubu uku, suka tura fastoci dubu uku su je wannan kan duwatsu su yi wa'azi. Yanzu kaje mutanen kan dutsen nan suka cewa mu musulmi muke hira suzo mu karba addinin su. Masu kudi ku fitar da kudi ayi wa musulunci ayi. Masu mulki kuyi amfani da mulkin ku ku yada addinin musulunci. Wallahi in ba haka ba kudin zasu kare, mulkin ya kare. Addinin Allah kuma Allah ya kawo wadanda zasu wanzar da shi kuma kuma baku ci falalar ba. Sardauna ya yada addinin musulunci a kasar nan me ya rage darajar shi? Ba abinda ya rage darajar shi. Sardauna ya kwanta ya mutu bai bar ko kwabo ba. Bayan ya kashe shi yace a je a bincika account din shi. Da aka bincika account din shi ca yake zai je ya samu Sardauna ya sachi makudan kudi irin yadda wadannan kansuloli da ciyamomi balle gwamnoni da ministoci da shuwagabannin kasa suke sata. Sardauna a lokacin nan matsayin shi firimiyan jihar Arewa duk jihar Arewa tana karkashin shi. Amma da aka duba account din shi aka ga ba ko kwabo sai da Aguiyi Ironsi ya yi nadama me yasa na kashe wannan mutumin. Shi ca yake ya sachi kudi ne da yake ganin shi da manya manya riguna. Sai da Aguiyi Ironsi yazo yayi nadama me yasa ya kashe Sardauna dan bai da ko kwabo account din sai ma ainihin bashi bankin take bin shi. Sardauna ya mutu da bashi. Gidajen Sardauna guda nawa ne? Yanzu kuka zabi yaro ya zama kansula wanda posta sai kun cika mai kudi an buga kafin shekara daya ya siya duk gidan da aka daga a unguwar. Duk wata budurwa da ta tashi tana kada kwakwasu sai ya aure ta. Wane irin abu ne wannan jama'a? Wane irin abu ne wannan jama'a? Bakuyi wa addinin musulunci aiki ba. Kun zama beraye a cikin ofisoshin ku. Jama'ar musulmi mun gane wannan da kyau ko? To a can kasar Adamawa jihar Adamawa akwai wani dutse da ake cewa dutsen Koma. Mutane suna so su karbi addinin musulunci a kan dutsen nan amma musulmi basa zuwa. Amma yanzu me yake faruwa? Koma kwande ya wuce ina Adamawa anyi program a ABC Adamawa Broadcasting Corporation gidan rediyon su. Suna ta karba addinin kiristoci evangelist kiristoci sun je sun cika garin yanzu ko ina cocin ce. Amma musulmi su suka fara zuwa amma sun daina zuwa. Ina kudin ku ina mulkin ku? Me zaku yi da kudi? Za a kulle maka kai kai kai abinnan kudi ne ka kai karuna kudi ne? Ko a nan Kurkusa ka kai a biola kudi ne? A nan Kurkusa an samu mai mulki irin na Abacha? Amma zuwa aka yi aka samu Gawarsha a daki bazaka ji tsoron Allah ba? Ku taimaki addinin Allah a yada addinin Allah. Mutane suna son addini. Amma ba'a kai musu ba ya zasu yi? A garin Wari a cikin jihar Delta idan aka je musuluntar da mutane da gudu suke fitowa suna musulunta suna tarbar musulmi da nau'i nau'i na abinci. Aka je aka musuluntar da wani kauye mutum fiye da dubu biyu a tsakanin kanin kauyukan suka musulunta. Sai aka samu wasu sun je NYSC sun je hidimar asacen jihar Delta sai suka ce su sun sadaukar da rayuwar su sun cire rigar bokon zasu yi musulunci aiki.
[Speaker seg1-spk:1]
Allahu Akbar.
[Speaker seg1-spk:0]
Amma a samu musulmi su dinga basa albashi da zasu ci su rayu. Me ya faru sai aka kasa biyan su albashi dole suka bar kauyen. Da suka bar kauyen me ya faru? Akwai daya daga cikin yan kauyukan ya ainihin zo Kano ya dan yi karatu. Da ya koma shima ya ga rayuwa ba yadda zai iya kawai shikenan dama kauyen me yasa suke bautawa? Sai ya dawo kawai sai ya samu katuwar mesa yana sa su suna bauta mata amma da sunan addinin musulunci ni sai da naje na gani. To yanzu ana jihadi kenan? Ko ko sai dai kawai a zo a ce yaku kiristoci yaku arna wuta a ce Allahu Akbar ba su kai cewa a tashi ba me aka ci gaba? Me aka ci gaba? An yi aiki kenan? An yi hidimu? Barna kuka yi. Barna kuka yi. Su dan fudiyo ba abinda suka yi ba kenan zamu zo mu je da suka yi aikin su. Da awa suka yi ba wai zuwa suka yi kawai suka hau kashe mutane ba. Ko kuma kawai su dubi tarin jama'a guda su ce wadannan duk dan wuta ne. Ba abinda suka yi kenan ba. Allah ya shiryar da mu.
[Speaker seg1-spk:1]
Amin.
[Speaker seg1-spk:0]
Bangaren jihadin munafukai kuwa wannan shine ayi ta musu nasiha. Munafukai ba yadda za'a yi a rabu da su, kullum ana tare da su, yanzu nan zaune muna zaune tare da su. Ya za'a yi ba'a iya rabuwa da munafukai sai dai ayi ta musu nasiha har su tuba. Da kyautatawa da nuna hali na gari abinda yasa wasu da yawa suka musulunta kenan. Abdullahi Ibn Uba Ibn Saluli shine shugaban munafukan zamanin shi. Dama munafunci ana yi ne don neman sarauta ko kudi shi sarauta za'a nada shi sai Annabi yazo Madina sai aka ce sarautar Garga jiya ta tashi. Yanzu sai mulkin musulunci. Sai yace to in ya tsaya a wajen musulunci bazai bazai ba ni ya shigo amma ya bata musulunci. Da ya shigo musulunci ya dinga barna. Ya dinga barna. Sa'ad da ya kwanta rashin lafiya danshi Abdullahi Salihi ne mutumin kirki yazo yace ya manzon Allah samu ruwa kayi min addu'an kawai baba na in sha ko Allah zai bashi sauki. In Allah bai bashi sauki ba me yawa in ya mutu ya samu saukin azabar Allah. Annabi ya samo ruwa ya mashi addu'a. Da aka mashi kun san abinda ya fada? Sai yace wa dan me wannan yace ruwa ne manzon Allah yayi addu'a ka sha ka dan samu sauki. Yace me yasa baka kawo fitarun uwar ka ba bai fi wannan ba? Wannan munafuki ne amma yana nan a samu farko da dangaje dangemu da nade. Ka gani? Ya za'a yi? Shi yawa manzon Allah cutar wanda ba wanda ya taba manzon Allah irin ta a musulunci. Shi ya dauki nauyin hada kazafin da aka yi wa Assali da Aisha yace an kama matar Annabi tana zina. Munafukai ne ba yadda za'a kai da su. Wadannan ba'a yakarsu yakin takobi. An zo an ce wa Annabi ka yake su mana, Annabi yace in na yake su wadanda ke wajen musulunci sai su ce Muhammad ya gama da na waje ya dawo yana kashe na ciki bazamu shiga ba. Domin yanzu kiristoci sun san waye munafuki a nan. Ba'a sani ba. Mu yanzu ko manzon shi in muna ganin shi yaci lafiya sai mu ci lafiya lafiya lafiya […]
[Speaker seg1-spk:1]
Ah.
[Speaker seg1-spk:0]
Sun cika gari yan bokon juna ne suna gaisawa lafiya amma kuma mun san gashi nan gashi nan. Kana mari shi sai a ce musulmi yana fada ya ji kunya. To ya za'a yi sai wa'azi sai nasiha in Allah ya nufi shi sai ya shiryar da shi. Amma kyautatawar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yayi da ita sai da ta dawo da mutum talatin da uku cikin kungiyar munafukai cikin musuluncin gaskiya bayan da Abdullahi dan Ubai ya rasu. Danshi yazo yace ya manzon Allah ka bada rigar ka ta ciki jampa da kake sawa wanda zufar jikin ka take diba. Ka bani in je in farke uwar uba na da kafani me yawa ya samu saukin azabar Allah don azaba ta tabbata da shi. Tunda kur'ani yace Wanda ya dauki nauyin shi ne wancan kazafi na Aisha azaba mai girma ta tabbata da shi. Allah ya fada ba yadda za'a yi. Ya tabbatar uba dan wuta ne amma ya za'a yi? A dan bada riga saboda tausayi dake gada. Ka bani in je in farke in mai da kafani ya dan samu sauki. Annabi ya dauka ya bashi saboda shima wannan munafukin ya taba Annabi wani alheri. Sa'ad da aka kashe Hamza kawon Annabi Annabi ya rasa kafani shi ya dauko da kafani ya ba Annabi. Shine yanzu danshi Annabi ya bayar da ramuwa dan kuma ya farantawa dan rai. Aka je aka mai da kafani. Yazo yace ya manzon Allah ka taimake ni. Baba na kazo ka tsaya kayi mashi sallah ko zai dan samu sauki. Annabi yazo zai sallah Sayyidina Umar ya tsaya gaban shi ya bangabanga yace a ina haba wanda yace kaza yace kaza dan Allah yace ka ja baya. Umar dake ya manzon Allah wannan sarkin munafukai ne fa kan za Allah yace ai Allah bai hana in yi musu ba sallah ko addu'a abinda yace in har zan roki Allah ko sau sabain in ne bazai karba ba. To shine nake so ko in yi fiye da sabain din Allah ya karba. Shi Annabi yana son ka kai ne kake kin shi. Saboda haka me ya faru? Annabi ya niki ya mai sallah. Dan nan bai gaji ba yace ya manzon Allah ka taimake ni kazo ka tsaya a kabarin uba na kayi mashi addu'a me yawa ya samu sauki. Annabi yazo ya tsaya yana dawowa gida daga jana'iza sai ayoyi suka sauka suratul tauba. Karka sake tsayawa kayi wa wani su sallah har abada. Karka sake tsaya kabarin wani cikin irin wadannan kayi musu ainihin addu'a. Sun kafirta wa Allah sun mutu suna fasikai mutanen banza ne karka sake kula su. Daga sannan ne Annabi ya ja baya. Jama'ar musulmi mun gane wannan da kyau? To munafukai ayi ta musu nasiha jama'a a tashi ayi ta wa'azi in sun gane sun bi shikenan. In basu gane ba kuma shikenan Sa'ad da sakon kwansul a a lahira. Sannan sai jihadi ga azzalumai da yan bidi'a. Shima wannan bayyana musu zalincin su gudun zalincin su kaurace wa zalincin su na daga cikin nau'ukan to duk wanda ya cika wadannan nau'uka na jihadi to lallai ya zama cikakken mai jihadi amma kuma jihadi baya yiwuwa sai da hijra. Jihadi baya yiwuwa sai da hijra. Hijra kuma bazata yiwuwa sai da imani. Wadannan abubuwan guda uku sune Allah ya hada a kur'ani yace Wadanda suka ainihin yi imani da Allah suka yi hijra suka yi jihadi wajen tada addinin Allah wadannan sune ke fatan su a suke sa ran samun rahamar Allah. Allah mai gafara ne Allah mai rahama ne. Mutumin da yafi kowa cika wadancan ainihin matakai na jihadi yafi kowa daraja a wurin Allah to babu wanda yafi kowa cika wadannan ainihin darajoji sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam dan haka Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam shine babban mai jihadi a duniya baki daya. Jama'ar musulmi kuyi mana afuwa in ce wannan shine muqaddimar wa'azin jihadin dan fudiyo baha wanda ya wuce bane wannan shi kudi ne. Gabar mutum biyu ta ainihin wannan wa'azi wanda itace zamu taho kasar Hausa kai tsaye. Itace wannan kasa da muke zaune cikin ta a yanzu. A nan da muke zaune yankin Zazzau ne. Da wanda bai sani ba bari mu fadi. Wannan suna na Zazzau na daga cikin sunayen da aka ainihin birkita shi kamar yadda turawan mulkin mallaka suka jirkita sunayen garuruwa da yawa. Zazzau ba Zazzau ake cema ta ba a da. Zak zak ake cema ta zak zak. Bature yazo ya cire wannan kak ya maida ita Zazzau. Kamar yadda Yola ba Yola ake cema ta ba Yolgace sai bature ya maida ita Yola. Ka ga matsala haka turawa suka rinka mana suna rikita mana sunayen abubuwa suka rikita sunayen malaman musulunci dan fudiyo suka ce dan fudiyo. In suka tashi ma da turanci suke rubuta basa sa waye su sa ko sai su sa ko din kauye da turanci kenan. In suka zo rubuta Zaria sai an rubuta da RIA madadin RYA in aka zo rubuta Mucia sai a sa CHIA wannan turanci ne. Dole ku tashi kuyi bokon ku yake arna in ba haka ba wallahi sai sun canza muku addinin gaba daya. Allah ya shiryar da mu.
[Speaker seg1-spk:1]
Amin.
[Speaker seg1-spk:0]
Kasan Hausa kafin zuwan dan fudiyo a yanzu da nake magana muna magana ne a yankin kasar Zaria ko in ce Zazzau wannan shine sunan da ya kamata a a fadi a zamanin can Zazzau. Da wadanda suke baki Galadima baki sai ka ji mutum yace sarkin Zaria in kace sarkin Zaria wani mafadi na kusa zai kilkwa maka duka ya rage wa sarki daraja sarkin Zazzau ake cewa. Dan Zaria itace can da kake gani da ganuwa Zazzau kuma itace yankin kasar gaba daya to itace kasa mafi fadi daga cikin yankin kasar Hausan baki daya. Jama'a mun gane wannan da kyau? To wannan kasa bazan tsauwata ba domin ba tsawon tarihi muka tsaya yi ba. Kafin zuwan dan fudiyo an raba kasar yanki biyu akwai Hausa bakwai akwai kuma banza bakwai. Hausa bakwai din nan daga cikin su kasar Zazzau na ciki Katsina da Kano da Daura da Gobir da makamantansu, banza bakwai kuma daga ciki akwai yankin Zamfara da Kebbi da Yauri da Nufi da Bargo da kasar Yawa ba bangaren Ilorin da makamantansu. Wadannan misalai ne na kawo. Kai a ya addinin musulunci ya shigo wannan kasar. Wannan kasa ta kasar Hausa kana cikin kasar da aka fi sani a yazo da Najeriya, Najeriya kuma tana yammacin Africa. Wannan kasa tana wani yanki ne wanda hanya ce ta yan kasuwa dake shigowa zuwa wannan kasa su wuce zuwa wasu kasashe domin isar da fata wuce su ko kuma su tsai da kasuwancin su zuwa wannan kasar. Hanyoyi uku a a a wato yan kasuwa daga kasashen larabawa suke shigowa wannan kasa amma duk wadannan hanyoyi suna shigowa ne ta Africa ta Arewa. Hanyar farko suna ainihin shigo wannan kasa ta ainihin wato kasar da aka fi sani da Libya a yau. Itace ainihin kasar Tripoli kenan da turanci. Yan kasuwa suna tasowa daga kasar shan larabawa su biyo ta wannan hanya tana tike musu zuwa ainihin Borno. Wannan hanya itace hanya da sahabin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yayi yayi ainihin biyo wanda bai tun karo ta sai da ya taho ya taba kasar Kairawan garin su mai risala a kasar Tunisiya ta yanzu inda kuka yi wasan kwallo a kwanakin baya. Sannan ya keto ta yazo ta kasar Libya sannan yazo har Borno. Sahabin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam. Hanya ta biyu itace hanya Tunisiya. Larabawa suna shigowa su taho kasar Tunisiya daga nan wannan hanya in suka yanko tana direwa da su har cikin birnin Kano Kano da aka sani ta yanzu. Hanya ta uku itace sukan taho su biyo ta kasar Moroko Maghreb. Wannan hanya tana biyo da su ta tun Buktu sannan sai ta shigo ainihin kasar Kano. Wadannan yan kasuwa dake shigowa suna tahowa kasuwancin zuwa Borno da Kano da wasu birane ko su wuce. Musulmi ne wasu su malamai ne. Wannan hanya na daya daga cikin hanyoyin da musulunci ya shigo kasar Hausa. Ina ma'anar wannan magana a takaitacce? Musulunci ya shigo kasar Hausa ta hanyar yan kasuwa. Kamar yadda a yau musulunci yake shiga wasu kasashe da dama saboda hanyar wasu da suka tafi kasuwanci kasashen ko kuma suka tafi wasu karatuttuka misali. Akwai samari da dama masu nishadin addinin musulunci a yau daga kasashen larabawa da wasu makamantansu. Da suka tafi kasashen turawa domin karatun boko ko dan kasuwanci. Amma kasancewar su ustazai ne a kasashen su wato malamai ne masana addini. In suka je suna karatun bokon su suna yada addinin musulunci. Suna kasuwancin su suna yada addinin musulunci amma bari in yi wani kyakkyawan misali mai barin shi awa. Akwai wadanda suke tafiyar kasashen turawa da nufin harkar tukin tasi ko kuma a caba. In suka je mutum malami ne dan kasuwa ne sai ya je ya siya tasi ya mata fenci ya bi duk doka da ake bi ta kasar America ko Faransa ko wata kasa daga kasashen turai. Madadin rigar shi babban riga da ya ciki da wando da nade irin na malam tasi ya kwabe sai ya koma yana sa tishat da hula hana sallah irin ta yan tasi ko?
[Speaker seg1-spk:1]
Na'am.
[Speaker unknown]
Ai da wahala ka ga dan tasi da babban riga da ya ciki da wando da nade da carbi da wahala ko? Amma kasan wata da ba'a da suke su suna wannan kasuwancin ne dan su yada musulunci. Malamai
[Segment 2/4 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
'yan boko ne suna jin turanci, faransanci, yaren Jamus, ko wasu yaran waje. Sai ya samu takarda, sticker, sai ya rubuta wata kalma, sai ya ya makala a bayan sit ɗin motar shi. Ko hakan dashboard akan kirjin motar shi daga ciki inda mazauni na kusa da driver zai gani. Kalmar da suke sawa ita ce Idan kana da wata tambaya game da musulunci zaka iya tambaya, iyakar kalmar kenan. Bature da ya shiga sai hankalin shi ya tafi ga rubutun. Da ya karanta sai ya waigo ya ce wa ɗan tasi Kan musulmi ne sai ya ce sai ya ce to mu je na kai shi gida. Idan ya kai shi gida Bature, shi Bature ba ruwan shi ba, shi yana neman hujja ne ba irin mu ne in na Shi Bature hujja yake nema ba ruwan shi. Don hakan aka in ya kai shi sai ya bashi number wayar shi su yi alkawari ka zo ranar Lahadi, ranar Hudu ko ranar Asabar, ranar Hudu. Suna da tambayoyi akan addinin musulunci. Shi dama abun da ya kai shi ba tasiri ba fa Amma yana aikin tasiri ne don ya yaɗa musulunci to ga dama ta samu. Don haka ranar Lahadi ba zai aikin tasiri ba. Sai ya shirya a nan sai ya taho da siffar shi ta malanta. Yanzu ya zauna gidan wannan Bature, Bature ya nemi tambayoyi yana bashi amsa game da addinin musulunci. Ta wannan hanyar an musulintar da da yawa daga cikin Amerikawa da Turawa. Na daga cikin su bari in muku misali Kwara dai Gyal. Akwai wani ɗan majalisa da ake faɗi shine ɗan majalisar da ta kwaya dai Gyal duk ƙasar Turai. Ba wani ɗan majalisa musulmi duk Turai sai shi. To ta wannan hanya ya musulinta. Daga driver tasi ne kawai ya riƙe mai hanya. Shin muna da auren addinin musulunci yanzu? Kun ji dai kasuwanci ne ya kai su. Amma sun yaɗa addini. Kamar yadda daga garin Azo mana da kasuwanci ne nan aka kawo mana addinin musulunci. Wasu malaman tarihi sun ce shi yasa Bahaushe galibi kasuwanci yake yin addinin a wurin shi. Don dama addini ya zo mai ta hanyar kasuwa ne. Allah ya kiyaye. To shin ko ana addinin musulunci kafin zuwan Ɗanfodiyo? Wannan amsar ko ban amsa ta ƙarara ba na amsa ta a taƙaice a ƙazo. Domin nayi ishara akan ana addinin musulunci ne tun ƙarnin Sahabbai. Ya tabbata musulunci ya zo ƙasar nan tun zamanin Sahabbai. Wasu malaman tarihi na ƙasar nan sun ce musulunci ya zo ƙasar nan tun Annabi na da sauran rayuwa da 'yan kwanaki kaɗan. An samu wani babarbare ya je wurin ainihin Sayyidina Abubakar. Wannan an samu wasu daga cikin malaman tarihi na ƙasar nan sun tabbatar da haka. Amma shahararriyar magana shine addinin musulunci ya shahara a wannan ƙasar a zamanin Khalifa na uku shine Sayyidina Usman Allah ya ƙara mishi yarda.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
Addinin musulunci ya shahara kenan tun zamanin Sahabbai. Tun ƙarnin farko tun musuluncin da ɗimi ɗimin shi bai huce ba. Akwai dauloli waɗanda cike suke da musulmi da malamai ana karatu duk irin karatun da ƙasar ake a yau. Na daga cikin daulolin nan akwai daular 'yan Doto wanda wannan daular shahararriya ce a tsahe a jihar Zamfara ta yanzu. Akwai daular Barno. Akwai kuma wata daula wanda ita ma an canza mata suna amma yanzu tana ƙasar Nijar. Ita ce Akdas Madinatu Akdas wanda aka fi sani da Agadas. Asalin garin sunan shi Akdas birni mai tsarki Kadasa Akdas Jama'a mun gane wannan da kyau? Akwai nan ƙasar Zazzau. Akwai ƙasar Katsina da ƙasar Kano duk ana musulunci a wannan yanki tun wancan zamanin. Ana karantar da ainihin tafsirai har Al-Imam Jalaluddini Suyuti ma ya zo ƙasar nan. Wanda kake karanta tafsirin shi ana cewa Tafsirin Jalalaini. Yau shekarar shi 500 da wasu mutsamutse da da su Bature ya zo Nijeriya. Ya zauna a Katsina, ya zauna a Kano. Anan ne Kanawa suka tara Suyuti suka ce ba zai bar garin ba har sai ya rubuta musu littafi akan Usulul Fikihi. Anan ne ya alfiya ta Usulul Fikihi. Abdullahi Gwandu ya zo ya rarraba wannan alfiya ya ainihin ƙara yira daga wasu abubuwa. Ma'ana abun da nake so in ce kar ka taɓa tunani ya kai ɗan bana bakwai Ɗan Fodiyo ne ya kawo addini. Ɗan Fodiyo ya samu ana addini a ƙasar nan. Tun kafin a san za a haife shi da ainihin fiye da shekarar 1000. Ya kamata ka gane wannan. Ina fatan an gane?
[Speaker seg2-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg2-spk:0]
A wannan lokacin ana karantar da tafsirin Jalalaini. Ana ainihin karantar da littafin hadisi irin Muwa ta Alfiya ta Suyuti ta hadisi a wajen Fikihi ana karantar da Ahlari da Ishmawi. Askari Risala Mukhtasar. Malaman anguwarmu Madaɓo ta birnin Kano har sun ƙware game da Mukhtasar har yara ake sawa suke haddace wa. Wanda har yau shahararriyar magana ce In dai yaro ɗan Madaɓo ne In dai ba ayi rashin sa'a ya zama ɗan taurin ba to ko ya iya Mukhtasar. In ko anyi rashin sa'a in taurin sun karɓe shi to ba shi ba Mukhtasar. Amma in dai bai zama ɗan taurin ba zaka ga ya haddace Mukhtasar. Malaman Madaɓo sun ƙware da ainihin karantar da littafin Mukhtasar. Suna karantar da littafin Usulul Fikihi wanda aka fi sani da Mukhtasar na Ibnul Hajim a cikin Usulul Fikihi. Ina fatan an gane? Da sauran littattafai da suke karantarwa na hau da Sarf akwai wani shahararren littafi ne shahara a ƙasar Hausa a lokacin sunan shi Mahuwa. Wannan akan nahau ne ake karantarwa. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Wannan nan kaɗan daga abubuwan da ke gudana kenan waɗanda ke nuna maka cewa akwai ainihin wato musulunci a wannan ƙasa tun kafin zuwan Ɗanfodiyo. Ina so ka riƙa wannan gaɓa ta tarihi tana da matuƙar muhimmanci game da alaƙar jihadin Ɗanfodiyo. Ana musulunci a Nijeriya tun kafin a haifi Ɗanfodiyo da fiye da shekara 200. Don kar ka zo ka ji Ɗanfodiyo ya tsai da jihadi ka ɗauka Ɗanfodiyo yayi jihadi da baƙaƙen arna ne maguza masha'a gurkutu. Ko ka ɗauka shi ya kawo addinin musulunci. Da shahararru malamai a wannan lokaci akwai wani malami da ya fi shahara da ainihin Malam Abdurrahman. Ana ce mishi Azzaiti. Wannan malami shahararren malami ne a birnin Kano. Yayi zamani da sarkin Kano da aka fi sani da ainihin wato sarki Yaji Ɗan Tsamiya. Akwai Malam Umar Kabara wanda har yayi shi ainihin sharhin wani littafi yana karantar da shi ya sa mishi Nazmul Kubawa. Da ainihin Malam Muhammadu Wali wanda yake karantar da littafin Ibnul Ward a cikin nahau da Sarf. Akwai Malam Ɗan Masani wannan wani ƙoƙaggen malami ne a birnin Kano sai da yayi wa 200 sharhi mujalladi biyu sunan sharhin 200 sharhi ne na 200 sharhi na 200 ni ina nan da wannan sharhin a Kano aka yi shi. Akwai wani malami da ya rubuta littafi a birnin Kano sunan littafin Waɗannan ne suna daga littattafan da aka yi ko da wannan na ƙarshe anyi shi ne bayan Shehu ya ya zo. Shahararru malamai da suka rayu a ƙasar nan tun zamanin Sahabbai akwai wani malami jikan Sayyidina Ali ne wanda ya zo ƙasar Hausa ya zauna. Sunan shi Malam Yahaya Abdullahi Ɗan Hassan Ɗan Hassan jikan Sayyidina Ali kenan. Allah ya ƙara musu yarda.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
Akwai Malam Magili wanda duk ya karanta tarihin musulunci a Nijeriya ya san shi ya zo ne a ƙarni na tara zuwa ainihin ƙarni na goma. Yayi zauna a garin birnin Kano ya rubuta littattafai shahararru guda biyu daga ciki akwai Ya rubuta waɗannan littattafai sai ya bar birnin Kano sai ya tafi sai ya je ƙasar Jazair ƙasar Aljeriya can ya rasu ƙabarin shi yana nan a yau. Akwai wani malami da aka fi sanin shi da Wali mai kargo. Kanawa sun san labarin wannan Wali mai kargo amma ɗaliban ilimi sun fi sanin shi da Waɗannan sun rayu a ƙarni na tara da ƙarni na goma ƙabarin shi yana nan a gefen goron dusa a yau a Kano. Akwai wani shahararren malami Bakatsine ne sunan shi Malam Muhammadu Alfullata Alkishnawi a ƙarni na goma sha ɗaya ya rayu. Dab da za a haifi Shehu Ɗanfodiyo kenan. Tafiya tayi tafiya sai aka samu wasu hamshaƙan malamai guda biyu waɗanda a lokacin su Shehu ya taso har sani ma almajirin su ne. Malamin farko daga ciki akwai Wannan Fulata Barno ne ba Fulata ni kuma babarbare. An fi sanin shi da Malam mai Fairama wanda duk ya karatu so ro a Kano yaji labarin Malam mai Fairama. Sannan akwai Wanda wannan shahararren malami ne mutumin garin Agadas. Malamin Shehu Ɗanfodiyo ne wanda Shehu yayi karatu Har Shehu in aka zo ana yabon shi kai Shehu ka iya ilimi sai Shehu yana raina wa yana cewa Ya ce in kuna ganin na kuna ganin wata tsiya ce ai ni ba komai ba ce. In aka dubi malami na Malam Jibrilla ainihin kamar ɗugon ruwa ne shi kuma kekuce. Malam Jibrilla bin Umar wani babban malami ne malamin hadisi ne. Sai dai an samu matsala a ƙarshen rayuwar shi ya koma a Don haka suka yi baran baran duniyar ilimi ta ji su da Shehu Shehu ya koma ya nemi sheren Ya ɗauki akidar nan da suke cewa ba ceto akidar nan da suke cewa Annabi Isa ba zai dawo ba da ainihin makamantansu shi yasa in zaka yi a hankali ka yi a hankali ahlussunna kar san cin hasada ya ƙwashe ka. Jama'ar musulmi kun ji wannan kenan. To ashe ana musulunci tun kafin a san za a haifi Ɗanfodiyo ko? To duk wannan lokacin ma fa da ake musulunci ba a haifi Ɗanfodiyo ba sai a cikin ƙarni na goma sha biyu jama'a. An daɗi ana musulunci a Nijeriya sannan aka haifi Ɗanfodiyo fiye da shekara 200. To tambayar farko yanzu me asalin Ɗanfodiyo? Wannan tambaya zamu amsa ta ne ba dan ƙabilanci ba domin sunnar malamai ce masu kawo tarihi duk wani malami sai an binciki salsalar shi. Shi dai Ɗanfodiyo ba Fulatani ne. Ɗan asalin ƙabilar Turankawa daga cikin Fulanin. Wannan da tarihi ya nuna sun taso ne daga garin Futa Toro da ke ƙasar Mali wanda ka sani ta yanzu. A cikin ƙarni na goma sha biyu suka zauna a ainihin wani gari Ɗagel da ke ƙarƙashin ainihin masarautar Gobir. Wanda ainihin shugaban su a lokacin kaka ne na shi daga Shehu sunan shi Musa Jakolo. Shine kwaso danyen shi suka zo suka zauna a garin Ɗagel suka yaɗa anan daular Gobir suna ainihin wa'azi suna malanta suna kiwo suna noma. Wannan dattijo Musa Jakolo shine kaka na shi da na Shehu zaka ji in ya zo faɗin nasabar Shehu. Cikakken suna da nasabar Shehu shine sunan shi Usmanu sunan mahaifin shi Muhammad sunan mahaifin mahaifin shi kakan shi kenan Usman ma'ana Shehu Usmanu ya ci sunan kakan shi ne. Sunan baban kakan shi Salihu. Salihu Ɗan Ayyuba, Ɗan Haruna, Ɗan Muhammadu Gaɓɗo Ɗan Muhammadu Jiɓo, Ɗan Muhammadu Sambu, Ɗan Ayyuba Ɗan Masirana, Ɗan Ayyuba, Ɗan Abubakar, Ɗan Musa Jakolo. Malaman tarihi da nasaba sun tiƙe da wannan nasaba suka ja ta har kan Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ma'ana suka tabbatar da cewa Shehu Ɗanfodiyo ta dama da hagu jikan Annabi ne ta hanyar uwa da ta hanyar uba. Jikan Annabi ne ta hanyar salsalar Assayyida Fatimatuz Zahra Radiyallahu Anha. Wannan shine cikakken sunan Shehu da kuma nasabar shi. Alkunyar shi ko ana ce mishi Baban Muhammad saboda sunan ɗan shi na fari kenan amma ba Muhammadu Galla ba kayi mana haƙuri kaɗan zan zo in gaya maka yayan shi kakan zaka ji akwai Muhammadu na farko ana ce mishi Baban Muhammad domin sunna gace ayi maka alkunya da ɗanka na farko ko ƴarka ta farko. Laƙabin shi ko na da yawa a ƙasar Hausa shahararren laƙabin shi shine Shehu wanda wannan kalma ce da ta samu asali daga sai Bahaushe ya murɗe ta ya maida ita Shehu. Har ta wayi gari a ƙasar Hausa saboda neman tabarruki da Ɗanfodiyo don haka a haifi ɗa aka sa mai Usmanu sai a koma ana ce mishi Shehu na Allah. Na daga cikin ainihin laƙabban Shehu ana ce mishi Mujaddadi da Hausa amma dai don abun da Larabci shine Mujaddadi mai gyaran addini. Ana ce mishi Nuruz Zamani hasken zamani. Ana ce mishi Ɗanfodiyo saboda baban shi malami ne na Fikihi. Da Larabci ai da Fillanci in aka ce Fodiyo to hamshaƙin malami wanda ya fi Modibbo. Modibbo malami kamar ka ce In malami ya zama za a ce mishi Babban malami hamshaƙi to da Fillanci sai a ce Fodiyo. Amma Malam Malam kawai kamar yadda Bahaushe ke cewa Malam sai ya bi Fulatani ya ce Modibbo. Amma in ya kai hamshaƙin malami irin su Gumi sai a ce Fodiyo misali jama'a mun gane wannan da kyau ko? Sannan ana ce mishi malami uban bayi. Wannan ana yi wa Shehu kirari da wannan. Ana ce mishi Gaigami uban tambari wannan kirari Kanawa suke mishi musamman a karatun Soro. Ta kai daɗɗen suna da tarihin ainihin salsalar Ɗanfodiyo kenan. Yau shi aka haife shi kuma a ina? Ana haifi Shehu Usmanu ranar Lahadi talatin da wata Safar hijrana da shekara 1168. Dai dai da 18 ga watan Oktoba Wato miladiyar Bature na da shekara 1000 da 754. Wato miladiyar Bature na da shekara 1000 da 754. Tun kafin a haifi Shehu an samu wasu salihan bayin Allah daga cikin manyan malaman ƙasar Hausa. Masu wa'azi sun yi iyakar ƙoƙari wajen su yi haƙurin su yi gyaran addini abun ya gagare su. Amma saboda bayin Allah ne waliyyai sun fara hasashen Allah zai zo da wani wanda zai gyara addini. Na daga cikin su an samu wani malami dattijo kafin ya rasu ga abun da yake faɗa a Hausawa. Yake cewa Ya ce ya ku Hausawa zamani ya riske ku wanda zamani ne na wani waliyi daga cikin waliyan Allah zai zo ya gyarawa halittun Allah addini zai rayar ilimi ilimi zai rayu. Wannan tun kafin a haifi Shehu an samu dattijo malami yana yawan faɗin haka. Akwai wata malama shahararriya ita ma ba Fulatana ce sunan ta Umma Hani. Ita ma waliyya ce ga abun da take wasiyya tun kafin Shehu ya zo cewa take Waliyyun min Auliya'illahi a wannan yanki na baƙaƙen fata wani waliyi daga cikin waliyan Allah zai bayyana. Zai jaddada addini zai samar ta addini. Kun gani? Su kansu sun san ba Ɗanfodiyo ya kawo addini amma waɗannan malaman me suke nuna addinin ya lalace a lokacin. Addinin ya saje da al'ada ni a gun malamai ni a gun saraƙuna da saraƙunan da malaman fa ba maguzawa bane malamai ne da suke amsa sunan musulunci. Amma sun rugurguje cikin al'ada. Saraƙunan ba baƙaƙen maguzawa bane suna da'awar sallah da hajji da sauran su amma addinin ya riƙe ce. Wannan bawan Allah ta ce wannan ɗa zai tashi ya gyara addini zai rayar sunna ya tsai da addinin musulunci. Amma ba waɗanda zasu iya bin shi sai waɗanda Allah ya datar. Ambatan shi zai shahara ko ina a duniya za a ji labarin shi. Mutane na kusa da na nesa na musamman da waɗanda daga magari duk zasu yi ko'i da shi. Wannan mata take cewa kuma wannan ɗa in an haife shi almajiran shi za a fi sanin su da cewa jama'a haka ake kiran almajiran Ɗanfodiyo kamar yadda yanzu duk inda aka almajiran Albani sai a ce salafiyya. To haka almajiran Ɗanfodiyo take cewa zasu yi shahara da wa? Wannan bawan Allah ta ce na daga cikin alamar almajiran Ɗanfodiyo su ba zasu damu da kiwon shanu ba kamar al'adar sauran Fulani. Ga wasiyyar wannan dattijo wa waliyi ya ce fa jama'a. Sai ta ce wanda dai da suke zamanin nan Wannan magana ba ni na ƙirƙire ta na faɗe ta ba. Ɗan Ɗanfodiyo shi ya faɗe ta Malam Muhammadu sarkin musulmi a cikin littafin shi mai suna a shafi na 133. Ƙanin Ɗanfodiyo shaƙiƙin shi uwa ɗaya uba ɗaya Malam Abdullahi Gwandu shi ma ya faɗi wannan magana a shafi na goma a cikin littafin shi mai suna An haifi Shehu Ɗanfodiyo ne a garin Ɗagel da ke ƙasar Gobir wanda ci biyar mulkin ta a lokacin ita ce wanda Bahaushe ya fi sani da Gari ne da ke cike da alƙane kamar yadda anguwar alƙane take a Zariya yanzu ko? To can kuma shine ci biyar mulkin Gobir. Daga garin da aka haifi Ɗanfodiyo zuwa
[Segment 3/4 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
na 160 ne. Sunan mahaifiyar dan hodiyo hawwau. Sunan kakarsa ruqayya, zaka ji dalilin da yasa na kwatanta wadannan sunayen baban zawa. Wannan maganar Muhammad Bello ya fada ta a cikin infakul maisur shafi na 33 da shafi na 66. Su waye malaman dan hodiyo? Ko ko dan hodiyo kawai kulle kanshi ya yi a daki ya yi karatu ya fito da rawanin ya fara wa'azi ya fara dukan jama'a. Sai da ya yi karatu tukunna don ka san abun ba hamasa bace. Ba zil bane in kana so ka yada addini sai ka je ka yi karatu. Sai ka dafu a cikin karatu sai ka zam baka tsoron karatu. Sannan zaka iya dawa. Amma ka zo kana jin tsoron karatu wai to ko ka baka kara shan dafin karatu tukunna baka sha rubutu ba fa ka je ka kara karatu nake. Amma ka zo kana karatu kana jin tsoron karatun baka halarta ka karantar ba baka halarta ka yi wa'azi ba. Ana so ne ka karantar da abun da kana da yakinin abun da kake fada. Shine Ya zan kafar ka ta dira. Baka shakka abun da kake fada sannan zaka yi karatu sannan zaka yi wa'azi. To wannan ba zai yiwu ba sai ka yi karatu a wurin malamai. Jama'a mun gane wannan da kyau? To shehu dan hodiyo su waye malaman shi? Malaman shi na farko shine malam muhammadu fodiyo. Dama mun ce baban shi malami ne. Baban shi yana wa'azi a lokacin a kasa hausa sai yana cewa ku ji tsoron Allah ku bi. In baku bi ba Allah zai tayar da wadanda in suka fada muku kuka ki bi zasu yake ku ashe ya'yan shi ne. Shi wa'azi yake ya zo wa'azi ya jawo mutanen shi ya shiga na gida ya yi zikir ya kwanta. Ba zai taba kowa ba amma yana cewa in baku bi da wuri ba da dimi dimi. To akwai wadanda in suka fada kuka ki bi ba zaku bata musu lokaci ba jibgar ku zasu yi su kaurar ku su kafa musulunci amma ba zasu dukan kowa ba. To baban shi shine malamin shi na farko shine malam muhammadu fodiyo. Sannan sai mahaifiyar shi hawwau ba jahila bace. Ita ma malamar shi ce. Sannan sai kakarsa ruqayya da bawan shi ya fi sani rakiya ita ma malama ce duk sun yayi karatu a wurin su. Wannan fa ana nufin malaman cikin gida tukunna kenan. Shehu dan hodiyo ya yi karatu a wurin baffan shi in aka ce baffa da fillanci ana nufin dan uwan mahaifi. Wannan baffan nashi sunan shi malam usmanu. An fi sanin shi a kasar hausa a karatun soro da uban dorin kabawa. Ban dorin kabawa. Baffan dan hodiyo ne. Dan hodiyo ya yi karatu har wurin kawin shi abun da ake nufi da kawu da fillanci shine dan uwan uwa. Wannan kawun nashi sunan shi muhammadu sambo dan abdullahi dan muhammadu dan sa'adi. Shine abdullahi gwando yake wa waka. Yake cewa muhammadu sambo zo ilmin wa khali. Tun muna sakandiri muka hadu da wannan wakar. Wannan muhammadu sambo kanin uwar dan hodiyo ne yayi karatu a wurin shi. Wadannan sune malaman cikin gida da dan hodiyo ya karatu da su a wurin su. Wannan gagarar sai zamu dauka a nan. Ya kai ustazu ba a auren jahila. Kan ganya yar talla. In ka aure ta kakari idan ka ya mutu. Dan hodiyo uban shi malami. Uwar shi malama. Kakarsa malama ta'adi. Sama dadi kasa dadi.
[Speaker seg3-spk:1]
Allah akbar.
[Speaker seg3-spk:0]
Dan haka sai da ya sha karatu a gida tukunna sannan ya fito waje shahararru malaman shi a waje a faye a sheikh abdurrahman ibn hamda wallahi na takaita tarihin nan ne don ba tarihi muka zo ba jama'a. Wannan lacca ta randa zan bude ta sai a kai kwana biyar ana yi ta tana da tsawo amma ni har yanzu ina so a kai ga makasudi ne shine jihadin dan hodiyo ba hawan daushe bane. Haka magana ta cikin lacca. Da sheikh ahmad dan muhammadu nil amin wannan malamin na biyu an fi sanin shi da malam bazan faye. An fi sanin wannan malamin da malam raji. Malaman shehu me na waje. Amma malam dan fodiyo an fi sanin shi da malamin shi da na fada a dazu shine a sheikh jibril ibn umar. Shine mutumin agadas ne. Kabarin shi yana nan a agadas zaka je ka ga yadda ake zuwa ziyarar dan hodiyo a sokoto kabarin shi haka ake zuwa ziyarar uban malam jibril ibn umar shine na ce dan hodiyo ne mai waka. Yana cewa Shine abdullahi gwando yake wa waka ya kamata ka dauki abun lura fa game da wakokin nan da muke kawowa. Dan hodiyo fa ba balarabe bane. In ka so ka yi da warin yanzu ka ce mai hausa balarabe. Amma ka ji da larabci suke hakokin su fa. To saurara abdullahi gwando shi kam wannan ce mishi ake balaraban mutanen yamma.
[Speaker seg3-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg3-spk:0]
Kanin abdullahi ai kanin dan hodiyo abdullahi gwando bari ku ji wakar da yake wa malam jibrilu cewa yake Waka ce mai tsauna takaita ne kawai saboda misali ake kawowa a nan. Ya wake shi ya ce malam jibrilu Allah ni kawo mana shi. Ya tsai mana da addini kyakkyawa ya gyara mana hanya. Rana ce ga ta nan ta kullo da hantsi. Ya ce tana zuwa yammaci garin mu sai ta haska mu. Kamar yyadda haske da ya sauka a gabas. Ya sau ya haska garin kuraishawa da kabilar khazraj muhajirai da ansarai annabi yake nufi. Jama'a an gane wannan da kyau ko? Jama'ar musulmi kun ji jami'ar da dan hodiyo ya fita. Wannan irin jibgar ku fa ya karanta. Dan hodiyo ya sauke al'kur'ani ya haddace shi hadda ba ta zuku ba yana shekara goma. Ba hadda zuku ba ya yi ratattattatta a kamo can a kamo can a kamo can a ce wannan yaro ya iya kyakkyawa ne uwar naina su. Dan dabba. Hadda gar da shekara goma ya hadda kur'ani chip. Yanzu me yi wa kai wannan maganar sai ta yi maka nauri don kai dan shekara goman ka yanzu fim din su ibro ya haddace. Duk wani gidan amarya da ake sa fim din ibro zai ji. To duk wata waka ya iya sai ya ga yaro ya makale a lungu wa si la To ina shekara goma ya haddace al'kur'ani. Amma fa kafin nan wai ma ya iya kira koki guda bakwai. Ruwayoyi goma sha hudu. Saboda ya sauke kuma ya haddace littafin malam shakubi. Ya haddace nazmin shakubi ya. Haka. Wannan shi littafin littafin ne ka ji na dan jawo maka ita. In kake wannan littafin da ikon Allah ka iya kira al'kur'ani bakwai ruwaya goma sha hudu. A shi nan dai haka. Yanzu dalibai irin mu ba san masu sunayen wadannan tukunna ba saboda ba sa karatun zauri. Kowa ya dinga lawannan shi ya sa rawanin ya zo ya zagi mu wai shi ustazu ne ya zo ya karantar da zauri. Karatun zauri shine karatu kuna cutar kan ku ne. Bama hana ku kayi haya islamiya ba ka ji haushin mu ko ka je kayi abu kayi digiri kayi digirgir kayi diploma. Amma karatun gaskiya yana nan a zauri nan ne za a fara Amma karatun haya islamiya ko abu ko arabi ko wanene biyu ke mai dubu ko ina ne syllabus ne za a bi wo sai a ce an sauke semester ta kare sai a ce ka sauka ka iya don haka sai zo kayi mana laccan duk sai ka rasa inda zaka kamu. Amma ka hada biyu ya kai mai sauri ne. Kai ka ce karatun zauri kadai zaka yi ba zaka yi na zamani ba in na ce karatun zamani a nan ina nufin karatun arabiya na zamani ka je kayi karatun soro. Ka daki karatu a nan nan ne gaskiya da gaskiya ne. Sannan ka je kayi karatun zamani shine karatun larabci wanda zaka iya mikewa a jama'a ka yi magana. Don in ka gama karatun ka a zauri ka kap randa aka tara maka jama'ar nan aka ce ka yi musu lacca. Kana zuwa aka kalle sai ta sadda kai ka ce salati goma ga Saboda ka saba zama cikin mutane. Amma in kai karatun aji idon ka tar matso tsabo baka shinkar kowa ko ya fika karatu zaka tsaya ka yi wa'azi a gaban shi ba ruwan ka da ya fika karatu zaka fada abun da ka sani. Saboda ka saba karatun aji. Don karatun aji shine zaka yi abokan ka kawayen ka da waye su yi maka dariya tun ana maka dariya har ka iya. Karatun zauri ko daga kai sai malamin ka shima baku hada ido in ka kifar da kan ka sai Jama'a mun gane wannan da kyau to ka hada biyu sai ka ci riba kayi na zamanin kayi na airihin zaure. Amma wallahi tsere wa karatun zaure da aka yi ba gidan sharri bane. Lallai a dawo a rayar karatun zaure shine asalin karatu ko karanta sahihul bukhari shine tsarin da malaman hadisi suke bi tunda ka zo ka zauna gaban malami tun daga farko har karshe ko malam ebiya ya fassara maka ko malam ka ja bakin ya fassara maka ko ka je ka ce haddasa na ko ka ce akhbarana ko kur'a alaihi ko anba'ana ko gashi nan. Jama'a mun gane wannan da kyau to haka a rayar karatun zaure jama'a. Allah ya shiryar da mu.
[Speaker seg3-spk:1]
Amin.
[Speaker seg3-spk:0]
Shehu usmanu ya yake karantar wa tukunna? Shehu usmanu ya fara karantar wa abun ma ba yana da shekara 20 raka duniya. Kun ji abun da ya kara hassada tsakanin shi da malaman fada. Dan shekara 20. Saboda mu a nan kasar hausa ba a saba ganin malami ba sai tsoho da furfura da sanda da malafa an kifa mishi wata alkyabba guda biyu. Yana ta zifa to in aka gan shi sannan za a ce malami. Amma ba a saba ganin saurayi ko yaro malami a kasar hausa ba. Shehu usmanu shekarar shi 20 zai zama malami. Kamar yadda ibnu taimiya yana shekara 17 ya zama malami. Uban shi ya rasu aka ce waye zai iya zama kujerar nan ya tafsiri irin na malam abdul halimi. Sai ahmad ya ce ni aka ce Ana ganin manyan malami masu rauni da furfura. Ya ce to a bani in gwada mana in ban iya ba sai a kore ni ba. Sai zo ya zauna sai aka ji ya fi uban karatu. Ilmi bai wace kamar yadda duk duniya an hadu a kan cewa dukiya bai wace ko. Yanzu kana da dan shekara 20 ya zo ya baka kujerar hajji ba zaka anshi ba? In ya baka riga baka kafan. Dan shekara 20 in Allah ya yarda ya iya risala. In ya baka fatawa ba zaka karba ba sai ka ce yaro ne. Ka zalunci kan ka. Shehu dan hodiyo yana shekara 20 ya zama malami. Dalibin shi na farko shine kanin shi. Abdullahi gwando ya fara karantar wa. Don haka abdullahi gwando yana da matukar biyayya da shehu usmanu. Matukar biyayya biyayya ta yadda ake bukatan biyayyan kanin yawa saboda wan shi ne kuma malamin shi ne. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Shehu usmanu yana karantar wa da harshen hausa da harshen fillanci. Wani lokacin sai a raba majalisin ayi da hausa sannan a zo ayi da fillanci. Saboda fulani ne da hausawa. Wannan kalubale ne ga masu kaurace wa harsunan su kenan kowa ya je ya iya harshen gidan su. Ka je ka yi wa mutanen garin ku wa'azi in kai babarbare ne. Ka je ka juya ka sa musu tafsiri wa hadisi fikihu da barbarci. A ja baki a fassara sai ka ji bari bari suna masha Allahu a a to ya shiga kenan. Ba haka bane? Haka ne. Kana iya fillanci ka je ka tara fulani a adamawa ko gombakani sai ka ja na alaraini modibbo alaraini modibbo to karatu ya shiga kenan. Tun da kana hausa basa je karin shadda. Ya sa in ka iya yaran gidan ku ka je ka raya shi kayi dawa da shi. In fa ba a na dangin ka tafi. Ka je kayi wa'azi da fillanci. Amma yadda mutane yanzu kowa ya kaurace wa yaran shi ya dawo ya tare a hausa ba kabilar muke so mu raya ba amma mun yi su dawa harshe abun dawa ne gare mu. Muna so kowa ya iya harshen su don ya je ya gaya mutanen garin su. Don dan adam wani lokaci yana da kabilanci duk maganar nan da nake fada in wani ya ji in ba bahaushe bane sai ya ce a duk da hausa ake fadi. Kana fada da yaran shi sai ya gane maganar kawai zaka fada sai ya ce sadaqallahu al'azim tunda ya gane abun da ka ce. To shehu dan hodiyo yana yin wa'azin shi in ya fito wa'azi a kofar gidan shi ake taruwa. A nan ainihin kasarsu ta dagel. Garin su na dagel. Yana da wata al'ada da dan shi ya fada mana in na ce ya fada mana nake nufi ya fada a cikin littafin shi. Littafin ainihin infakul maisur. Malam muhammadu Bello ya ce idan baba na. Ya fito karantar da dalibai sai in ga ya tsaya a wani lungu bakin shi yana mi mi mi mi mi mi mi mi ya ce na ga wannan ya fi a kirga ya ce rannan sai na yi karfin hali na ce me kake fade ne in ka fito karatu ya ce tsayawa nake ina rokon Allah Allah ya sa dalibai na su fahimci abun da zan karantar da su Allah ya karbi wannan aikin nawa ya sa mun sarkin zuciya a ciki ya ce abun da nake fada kenan. Wannan alma dan shi ya fassara mana wannan maganar. To jama'ar musulmi na daga cikin abun da shehu ya fi bada karfi. Shine karantar da tauhidi. Sannin Allah. Sarki. Sallah. Anwala taimama azumi zakka hajji aure. Ciniki da kuma yin abu don Allah sarkake wucewa tahzibi kenan. Wadannan sune manyan abubuwan da shehu ya fi bada karfi. Shi wa'azin shehu ya tsaya ga maza ne kadai ko ko wa'azin shehu ya kai har ga mata. Jama'a musulmi wannan matsala ce wanda nake so na dan tsaya kadai in tattauna mana ita. Saboda mafi yawancin masu dawa. Suna bada dawar su bangare daya da mai karfi. Wannan ya faru ga annabi da farko sai da mata suka yi mai tambihi. Malam suka zo suka ce wannan Allah duk ka tare wa maza. Guba naka bane Allah bai aiko ka gare mu bane? Annabi ya ce ba a Allah ya aiko ni wurin ku suka ce to a sa mana rana mana aka sa musu duk ranar alhamis. Aka tara su a je a yi musu wa'azi sai ta tambayoyi suna fatawa. Al-imam bukhari ya waito wannan hadisi ka karanta. Cikin littafin ainihin kitabul ilmi na sahihul bukhari ko ya fi salihina. Jama'ar musulmi shehu usmanu a majalisin shi akwai mata suna zuwa karatu. Amma wata matsala mai girma ta taba faruwa. Masu jita jita suka je suka ce shehu dan hodiyo yana hada maza da mata a majalisi daya ga kwankwasan namiji ga kwankwasan mace. To dama malamai sun kosa su ji kuskuren dan hodiyo. Ana nan dai a ji bai iya nahau ba. Bai iya nahau da irabi ba. To duk dai ya iya. To Ai dai abun ba ikhlasi ba to ba dai don Allah bane karatu ne ya duka dai. Ba a dai samu abun da za a zarge shi da shi ba sai aka yi ta cewa makarantar dan hodiyo ga kwankwasan namiji ga kwankwasan mace. Jita jita tayi karfi har ta kai kasar barno. Wani babarbare da ya ji kawai sai ya yi aiki da jita jita sai ya rubuto raddi. Bari ku ji abun da ya ce. Ya ce Wannan mutun sunan shi gwani mustafa. Gwani mustafa wani malami ne daga maiduguri. Abun da yake cewa a takaice labari ne ya zo gare shi shehu dan hodiyo yana cuda maza da mata a makaranta. Sai ya ce. Gaisuwanni masu albarka zuwa gare ka masu dauke dauke da kanshi irin na cilaran almiski. Ya ce ya kai dan hodiyo ka tashi kayi wa jahilai wa'azi. Me yi wa su fahimci addini su fahimci duniya. Amma fa ka hana mata zuwa makarantar ka. Domin hada maza da mata mumin ya kai matuka. Kar ka sake ka aikata abun da zai jawo mana masifa a kasar nan. Domin Allah bai taba umarni da wani aibi wanda zai cutar da mu ba. Ya ce baitocin shi baiti goma ne yayi a shekara ta kaza wannan ka'ida ce ta masu waka a takaice abun da nake so ka gane kai. Wannan mutun ya yi aiki da jita jita. Dan hodiyo na cuda maza da mata don haka shi kuma ya rubuto raddi. To wannan wasikar tayi wa dan hodiyo za.
[Segment 4/4 | 01:00:00–end]
[Speaker seg4-spk:0]
shi kuma Umar mutum ne mai sauƙin hali, bai son ɗaukar abubuwa da zafi. Amma shima yana da masu zafi a gaban shi ko? Tun daga Abdullahi bn Wandi.
[Speaker seg4-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:2]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:0]
Kamar yadda Annabi yake da masu zafi a gaban shi. Da Tariƙi ce sai a ce Umar mai ƙe. Aliyu tara can. A yanda ma suna da amfani kar ka taɓa cewa ba ruwan ka da 'yan daba, duk jawo su su cika makarantar ka suna kambara suna fahimtar ƙawa'idi da ahalari. Rabil da Rabil ana istigifari ko? A sauran wurare sun yi amfani, ƙwarai da gaske. Ai kuskure ne kana mai da'awa ka ce 'yan daba ba naka bane, duk 'yan daba ka jawo su ka ce mutanen ka ne. Kowa ya zo a biya ƙawa'idi. Suna nan za su gyara, duk Umar ɗin ba 'yan daba bane? Su Hamza duk 'yan kulab ne, su Aliyu duk mashahuran giya ne amma duk da suka tuba ba sune muke koyi da su ba? Jama'a mun gane wannan da kyau? Shehu ya ce wannan wasiƙa ta yi zafi ya ce Abdullahi ba shi amsa. Shi ya rubuto biyar Abdullahi ya goma. Ya ce Mun ji amsar Malam Abdullahi. Ma'anar ta kuma abun da ya ce a taƙaice ya kai wannan da ka zo ka ne shiryar da mu, ya kai wannan babarbare. Mun ji maganar ka. Allah ya saka maka da alheri amma ka saurari amsar mu. Ka yi mana nasiha. Kuma ka yi iyakar ƙoƙarin ka. Sai dai ya kamata ka karɓi hamsarun mu. Amma fa ka faɗi wata magana wadda tsarki ya tabbata ga Allah ƙarya ce. Ƙarya ce da ka ce muna cuɗan ya maza da mata. Ya ce domin shaiɗanin mutane in suka zo makarantun mu. In suka fita sai su yi ta yaɗa ƙarya a kan mu. Mun ce kaza mun ce kaza mun ce kaza muna cuɗan maza da mata garin haka jita-jita ta zo maka to ƙarya ce. Ya ce mu bama cuɗan maza da mata a majalisun mu a wurin karatun mu. Yau ta ya zamu yi haka? Mu da muke wa'azin ka a aikata gubin abu ai wannan gubin abu ne. Sai ya ce to kai ka ƙaddara ma haka ne. Ka ƙaddara muna haɗa maza da mata. Idan muna haɗa maza da mata ai ya fi sauƙi da a bar su da jahilci. Gwammu a karantar da su. Domin kuwa idan ɓarna biyu ta haɗu ana duban ƙaramin ne a taƙe ta in ba dama a bar su duka. A bar su da jahilci. Jahilci ya kai su ga kafirci ko a cuɗan ya maza da mata suna karatu an aikata saɓon Allah wanne ya fi sauƙi in ma har haka ne. Shine Abdullahi Wandi yake cewa haɗa maza da mata ya fi sauƙi. Ya ce wannan ƙasa ta Hausa mun same ta ne mutanen sun nutse cikin jahilci. Ya ce sai a hana su su fahimci addini da rayuwa. Ya ce kar ka manta malamai sun ce ana yanko wa mutane hukunci ne da ƙwar-gwadon yadda suke. Idan ka je ka samu mutane. Mutanen da basu fahimci addini ba in ka ƙarfa fa musu wani sharɗin jama'a. Sai su ƙi karɓan addinin ko kuma sai su ƙi fahimtar ka. Kun san me nake nufi jama'a? Yanzu kamar ƙasashe irin su Togo da makamantan su in ka shiga wa'azi za ka yi mamaki. Yadda ake faɗin nan haka suke za ka ga an zo wa'azi ƙwaƙwasan namiji nan ƙwaƙwasan mace. In ka zo kai da zafin kai. Cewa sai an ware. To wani fa da haza saboda mu duro shi ta zo wurin ne ya zo. Ko aka ce ta tashi ta koma wurin mata ya koma wurin maza sai ya fito ya fita. Kuma aka ci gaba da wa'azin in ya shiru ya gyara. Shine Shehu Abdullahi yake cewa ko da haka ne ma. Ka karɓi uzurin mu mana tunda mutanen nan jahilai ne. A karantar da su suna cuɗan ya maza da mata ya fi sauƙi a bar su da jahilci su je su saɓa ma Allah. Sai Shehu Abdullahi sai ya ce godiya ta tabbata ga Allah wanda ya shiryar da mu. An tsira da aminci su tabbata ga zaɓaɓɓe fifiyayyen halitta Allah manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Da mutanen gidan shi da sahabban shi ya ce ga wa'aka ta nan baiti goma. To jama'a wannan maganar amsa ce ta musamman da aka bai wa wannan babarbare. Amma maganar ta yaɗu a ƙasar Hausa. Har turawa da suke rubutu game da tarihin Shehu. Suna ɗaukar wannan gaɓar tana zama aibi. Su ce. Shehu ya zo yana hana ɓarna. Amma kuma ya haifar da wata ɓarnar yana cuɗan ya maza da mata. Ga ƙwaƙwasan namiji ga ƙwaƙwasan mace wannan maganar ƙarya ce. Gaba gare ni nan littattafai ne guda biyu Shehu ya rubuta su da hannun shi. Wanda ya tabbatar da haka ɗin ƙarya ce. Bayan ya tabbatar da haka ƙarya ce ya zo ya bayyana hukuncin mata su fita domin su nemi ilimi. Littafin farko gashi shine wasiƙatul jawadi. A na su'alin dalili a na su'alin dalili alaman i khurujin nisa'i. Wal muwalati ashirin. Wannan littafin akan hukuncin ainihin wato. Wani dalili ne yasa za ka hana. Ka ce mata kar su je suna su je biki kar su je biki amma kuma ka ce su fita makaranta wani dalili ne sai Shehu ya ce ga dalili sai ya rubuta wannan littafi. Na biyu Shehu ya ce tanbihi ikhwani. Ala jawazi tikhazi majlisi li ajli ta'alimin niswani ilmi furudi a'ayani. Mun dinillahi ta'ala rahmani gashi. Wannan littafin Shehu yayi shi ne akan a ware wa mata makaranta ta musamman. Anan ne ya fito ƙarare ya ce ƙarya aka yi mun sharri aka yi mun. Bana haɗa maza da mata a cuɗanye sai dai farkon ka makaranta ta maza na gaba mata na baya sannan na kawo labule na sa a tsakiyar Shehu da kan shi ya faɗi wannan. Ya ce da tafiya ta yi tafiya makaranta ta yi ƙarfi sai na ware wa mata rana daban na ware wa maza rana daban. Shehu ya faɗi haka a cikin wannan littafi. Wadan nan littattafan jama'a malaman ƙasar Hausa na wannan zamanin da yawanci basu san su ba. Shi yasa da muka tashi muna karantar da mata suka yi ta mana sharri. Suka yi ta mana ƙazafi. Da muka tashi muka yi ta bayyana su da suka san su yanzu ba wanda bai karantar da mata. Yadda 'yan izala ke da makarantar mata 'yan ƙarika na da 'yan shi'a na da ita 'yan ba ruwan mu na da ita yanzu kowa yana da makarantar mata.
[Speaker seg4-spk:1]
Allahu Akbar.
[Speaker seg4-spk:0]
Da zamu fara karantar da mata sai da muka je muka yi dukkan mu malaman izala na unguwan nan mu da su Malam Sani su Malam Umar su Malam Muhammad Awwal su duk sai da muka je muka yi ya ake karantar da mata mata kuma ba da ka muke ba anan sai da muka yi na shekara biyu. Kuma kun sani ba da muna wucewa lokacin kuna zagin mu muna tafiya neman ilimi. Sai da muka je muka yi na iya tuna ranar farko da ɗaya daga cikin malaman mu ya shigo yana yi mana shimfiɗa akan na duk ba karantar da mata. Ya ce ta'idi farko in kana da makarantar mata. Kai za ka zama na ƙarshen shiga aji kuma kai ka zama na farkon fita sai sun gama taruwa sannan kai ka zo ka shiga. Sannan kana addu'a ka fita. Kana fita kana wata ta ce tana da tambaya za ta gane da kai. Haka aka karantar da mu. A nan muka zo aka yi ta mana sharri aka yi ta mana sharri muna karantar da mata muna lalata da su muna kaza muna kaza muna nan muna yi musu addu'a muna cewa Allah ya shiryar da ku. Mu inda muke karantar da mata a makarantu ne a sarari kowa yana gani da rana. Maƙiyan namu da ke zagin mu da suka tashi buɗe makarantar farko a yankin sabon garin Zariya a cika ji aka buɗe ta da daddare. A rinfar kwano. To ka gane? Malaman ƙasar Hausa basu san littattafan nan ba shi yasa muke basu ƙazafi. Basan su ba. Saboda malaman biɗi'a sun danna littattafan nan sun ƙoye su Rabil kuma turawa sun kwashe su. Don haka aka waye gari a yau in ka tashi ka ce za ka jaddada addini irin na ɗan hudu. Malaman ƙasar Hausa da sarakunan ƙasar Hausa su za su yi faɗa da kai. Ba'a neman hujjar daga ɗan hudu ko ka ɗan an manta da wannan. Sannan Shehu alƙalamin shi bai ƙafe ba ya zo ya rubuta wani hamshakin littafi gashi irshadul ikhwan. Wannan littafin kowa ya kamata ya mallake shi ina hukuncin mace ta fita ta je asibiti ko ta je gidan suna ko gidan biki ko ta je aikin gwamnati ko ta je gona ko ta je ta'aziya ko ta je kamun amarya duka sai da Shehu ya tattauna ɗaya bayan ɗaya a ilmance da hujjoji. Wannan littafin akwai wani malami a kwalejin ƙarikeshen da ke can jahar Zamfara ya fassara shi Malam Muhammad Isa Talatan Mafara fassara Hausa wanda basu iya karatun larabci ba ku je ku nemi shi. Jama'a karatun ɗan hudu kun ji yadda ya fara matakin farko zama ake a karantar da mutane. Ashe idan kai an ce maka jihadin ɗan hudu. Kai kana tunanin ɗan hudu ya tashi ne ya ce ya ku mutanen ƙasar Hausa duk ɓarna ne ku to wannan kuskure ne ba haka ɗan hudu ya fara ba. Ka ji jihadin farko shine abun da yayi. Jihadin farko me muka ce a baya neman ilimi ko? Shehu ya nemi ilimi. Ɓangare na biyu karantar da ilimi yanzu akan haka muke zama da tarihin Shehu. Shehu yana cikin karantar wannan. Ka ji ga irin tsarin da yake yi. Wannan maganar ina faɗin ta ne saboda 'yan uwan mu matasa. Idan suka tayar ma da'awa a yau in suka shekara uku suna yi. To shikenan sai su kwaso kaulasan ƙwandor guda. Sai su watsa wa jama'a saboda wai sun gaji har yanzu ba'a zo alheri su ba. Shehu sai da yayi shekara arba'in. Sai da Shehu yayi shekara arba'in sannan aka buga. Kana ji ya fara karantarwa yana shekara nawa? Ashirin. Waka yake karantar wannan a hankali a hankali a hankali. Ana karantar da mutane. Qur'ani. Hadisi. Fiqhu in ya zo Khutbatul haja Khutbatul hajan shi yana farawa irin wannan da kake ji a biɗiyo Abubakar Gumi na farawa wanda take ƙarewa Sannan sai ya ce Sai ya fara karatun shi haka yake farawa wannan ɗan shi ya gaya mana haka a cikin littafin Jama'ar musulmi da makarantar Shehu ta ƙasaita. To yanzu ne za a fara matsalar jihadi. Sarkin wannan lokaci sunan shi ba wajan gwarzo. Ba kafiri bane. Ba arni bane ba bamaguje bane musulmi ne yana sallah yana salati. Yana can a alƙalawa sai ya ji labarin ga wani matashin malam ya an samo a garin Ɗagen. Yana wa'azi yana karantarwa. Wannan sarki da kan shi ya taso da ya taho gidan Shehu Ɗan Hodiya. Ya zo ya gaisuwa. Ya ce wa Ɗan Hodiya ni na yadda da wa'azin ka. Na yadda da karatun ka. Ina son ka zo gida na. A alƙalawa ka kafa makarantar ka a nan. Ƴa'ya na da mata na ka karantar da su kuma ka karantar da mutanen ƙasa ta a a babban birnin jiha babban birnin ƙasa alƙalawa. Shehu ya amsa wannan magana. Wannan magana ta faru ne daga Ta me da adiyar bature. Shehu ya yi shekara ta dubu ɗaya da ɗari bakwai da saba'in da. Shida zuwa da tasa'in da huɗu. Bayan da ya yi waba. Sai wannan sarkin ya rasu. Wannan sarki shine ba wajan gwarzo. Jama'ar musulmi ba wajan gwarzo bai yaƙi Ɗan Hodiya ba. Ba wajan gwarzo ya ƙarfafa da'awar Ɗan Hodiya ba. Don haka matasa da basu san tarihi basu bar la'antar ba wa wajan gwarzo. Ba wa wajan gwarzo Allah ya gafarta mishi.
[Speaker seg4-spk:1]
Amin.
[Speaker seg4-spk:0]
Bayan ya rasu sai ƙanin shi Yaƙubu ya karɓi mulki. Yaƙubu da ya karɓi mulki shima sai ya ci gaba da gudanar da da'awar Ɗan Hodiya kamar yadda yayan shi yake yi. Sai dai Yaƙubu bai daɗe akan mulki ba shekaru huɗu ya rak sai ya rasu. To daga nan sai ƙanin shi ya karɓa shine sarki na fata sannan ya mutu sai a ce tsautsayi ne Allah.
============================================================
[Part 6]
============================================================
[Speaker spk:0]
sarki na fata, da nan ya mutu sai a ce tsautsayi ne Allah ya kawo kamar yadda Hajjaju bin Yusuf ya kashe Abdullah dan Umar. Sahaban Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Imam Bukhari ya ruwaito hadisi a cikin Sahihul Bukhari Kitabul Hajji. An fito za a yi aikin hajji a shekarar da Amirul Hajji shine Hajjaju. Shi kuma Hajjaju mugun sarki ne ba a mai nasiha. To sai dan Abdullahi dan Umar mai suna Salimu ya je ya tsaya a babban dakin da Hajjaju yake wanka ya ce ranka ya dade sarki in dai sunna kake so kai marmaza ka fito a je a hau Arafa. Sai maganar sai ta fata mai rai shi za a ce in dai sunna yake so shi za a yi wa'azi da sunna. Shi ne mai wa'azi da sunna ne shi mugu? Sai ya fito yana fada sai ya ce a kira Abdullahi dan Umar uban wannan yaron da ya fadi maganar tun da uban malami ne. Ya ce abun da ranka ya fada gaskiya ne? Ya ce gaskiya ne. Sai maganar ta mai zafi dan me za a fadi maganara shi kuma ya gaskata. Shikenan sai ya ce a je a samu kibiyoyi a sa musu dafi a bakin su a soka su a kofar dakin Abdullahi dan Umar yadda yana fitowa da asuba zai sa takalmin shi sai ya taka su. Yana fitowa kuwa sai ya taka yana takawa guban nan ta bi jikin shi karshe ya rasu shikenan bayan ya dawo aikin hajji. Haka sarki Yunfa ya so ya kashe shehu ya hada rijiya in ya fada ya mutu ya ce tsautsayi ne Allah ya kawo. To amma sai Allah madaukakin sarki ya tsare shehu. Allah yana tunkuɗe wa mumini duk wani makirci da za a yi musu. Wannan da bata yiwu ba sai sarki Yunfa ya dauko wani mataki na ya kashe shehu amma ta hanyar almajiran shi. Sai sarki Yunfa ya hada rundunar yaki za a tafi yaki wata kasa sai a bi kauyukan da almajiran shehu suke sai a je a kama su a karkashe su a dibe dukiyar su a kwashe matan su da yayan su. Sai a ce sarki ya zo wucewa ne basu fito sun yi gaisuwa ba hasali ma sun jadde fa sarki. Aka rika bi ana kashe almajiran shehu ana kashe almajiran shehu. Wannan lokacin saura shekara biyu kenan shehu ya tsaya da jihadin nan da wadannan sarakunan gargajiya da 'yan bokoko suka yi biki makon da ya wuce. To wannan makircin duk na ya fada mana shi a cikin littafin Infaqu mai suna Shafi na 97. Ya ce to a shekara ta 1288 inji Bello kenan. Ya ce sai sarki Yunfa ya bullo da wani makirci yana son ya gwada shehu ya ga sai ya rubutawa shehu takarda cewa bayan gaisuwa ka tsince ina ka ina ka ka bar yankin mulki na gaba daya amma kada wani almajirin ka ya
============================================================
[Part 7]
============================================================
[Speaker spk:0]
Saboda da awarka komai ya daidaita. Dan in marmaze sai baba na shehu yayi amfani da kaifin hankali yace wannan makirci ne. Yace ba zai dawo ba sai in an cika sharadi biyu, sharadi na farko yauwa sarki yayi tuba ga Allah. Ya zama ba wai kawai zai gyara bane ya zama rikin shi zai watse ya tuba ga Allah. Sai ya tuba ya dawo ya tuba ga Allah. Sharadi na biyu shehu yace ya tsayar da adalci a kasar shi. Ya hana zalunci to anan ne shehu ya fadi da wallahi duk wani mai mulki ya saurare ni da kyau shehu yace. Ka sani da cewa gwamnati na rayuwa ta dore a karkashin kafirci. Amma bata rayuwa ta dore a karkashin musulunci koda ta musulmi ce, a karkashin zalunci koda ta musulmi ce. Gwamnati tana iya rayuwa a karkashin zalunci a karkashin kafirci ana kafirci a kasa. Sai Allah ya rabu da su su rayu Matukar ba zalunci tsabar kafirci ake. Sai ya rayu. Amma gwamnati ko ta musulunci ce ta saka zalunci shehu yace sai ta rushe. Jama'a ku duba Amerika. Duk duniya ba kasar da ke taimakawa wajen gajiyayyu. Ba kasar da ke taimako da duk wani alheri irin kasar Amerika duk duniya. Da mu makiyan Amerika da masoyanta mun yarda da haka. Amma saboda Amerika azzaluma ce duk alherin nata ba a gani. In kana zalunci duk alherin ka ba za a gani ba. Yanzu ana yin ambaliyar ruwa Amerika zata kawo gudunmawa, ana yin yaki Amerika zata kawo kaza ana amma saboda muguwa ce azzaluma ce sai Allah ya hana duniya su fahimci alherin can nata. Shehu yace gwamnati ta kafirci zata iya dorewa a karkashin kafircin ta in babu zalunci. Amma gwamnati ta musulmi ba zata rayu ba in ana zalunci a cikin ta, wannan maganar tayi daidai da hadisin annabi sallallahu alaihi wasallam. Sa'ad dan qusussu ke zaba. Zaku ce
============================================================
[Part 8]
============================================================
[Segment 1/6 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
kun soke zaba. Zaku ce kun soke zaba. Kuka soke zaban sai ya dawo gida. Sai kuzo ku sake fitar da dan takara a sake. Anyi a California. California itace jiha mafi girma a kasar America. Itace jiha mafi arziki a kasar America. Shekarar da ta wuce sukace gwamnan su sun janye zaba. Sai sukace sun janye sai ya dawo gida. Sai suka sake tsayar da dan takaran gwamna. Dan boxing suka dauko dan drama Ibro suka dauko suka tsayar suka ce ya wuce yanzu. Ya fi musu. Amma yanzu kuna ji kuna gani kun zabi mutum yana zalunci. Kuna zuwa ana raba zalunci. Duk wanda kaji ya fito yana magana to ba'a bashi bane. Amma in ya dinga aka yaya fa mun shikenan. In anzo ana magana sai kace Yayi naku yayi nashi. Zalunci dai kowa nayi. In na zo ana mai bayani ba na mai gidan ka ya bayyana. To kunji sharudan da shehu yayi wa wannan sarki. Da da da aka komawa da sarki Yunfa wannan takarda dauke da wadannan sharuda na shehu. Yunfa ya zindima a shar irin ta bakaken maguzawa. Yayi zagi ya kacaccala takardar. To sai zaluncin shi ya karu akan ainihin almajiran shehu. To anan ne sai shehu ya dauko wata ka'ida. Yanzu shehu ya dauki ka'idar farko itace mai karantarwa ko? Da'awa. Yana karantarwa yanzu shehu ya tsogali fada ko tsogalen shi aka yi?
[Speaker seg1-spk:1]
Tsogalen shi aka yi.
[Speaker seg1-spk:0]
Tsogalen shi aka yi. Da aka tsogale shi aka kuntata mai sai yayi mai sai abu na biyu hijra. Da yayi hijra. Da aka kuntata wa almajiran shi sai ya tafi mataki na uku shine Neman taimako sai ya fara aika sarakunan kasar Hausa. Ya aika wa sarkin Zazzau Jatau. Takarda cewa ku taimake ni. In tsai da addinin Allah Allah zai taimake ku. Alhamdulillah a lokacin sarkin Zazzau Jatau ya amsa dari bisa dari. Don haka bazaka taba jin a cikin tarihin shehu yana fada da Zazzau ba. Saboda sarkin lokacin bai jayi ya ba. Ya taimaka wa shehu dari bisa dari domin ba jahili bane. To sarkin Zazzau Jatau ya kokota daga wannan. Na biyu sai sarkin Katsina. Saboda yayi mugun abu bazan fadi sunan shi ba Katsina kuyi mun aikin gafara. Sarkin Katsina ana aikawa da takardar da ya zindima a shar sai yayi yaga ta. Shine mutumin farko da Allah ya fara kifar da mulkin shi a kasar Hausa. A karkashin addu'ar annabi da sarkin Kisra yaga takardar annabi. Annabi yace Allah ka yaga mulkin shi kamar yadda yayi yaga takarda ta. Haka Allah ya kace kace da mulkin sarkin Katsina na wannan lokaci. Dan Hodiyo ya turo wani sarkin yakin shi wani gwarzo sadauki mai suna Ummarun Dallaji. Shi aka turo ya rugu rugu da wannan gwamnatin ta Katsina aka kafa gwamnatin musulunci a wannan lokacin. Sarki na uku. Ya raba kafa shine sarkin Kano. Shima bazan fadi sunan shi ba kana kuyi mana aikin gafara don yayi mugun abu. Da aka ai ta mai da takarda dari bisa dari sai ya nuna goyon bayan shi. Amma sarki Yunfa yana ruguto mai takarda sai ya chanza ra'ayin shi daga goyon bayan dan Hodiyo sai ya goyi bayan sarki Yunfa. To shima nan aka ainihin turo mishi sarki Sulaimana. Ya zo da tutar musulunci wani matashi ne. Yayi rugu rugu da gwamnatin Kano ya kafa gwamnatin musulunci. To da wannan lokacin ne jama'a. Yanzu bari in dawo magana da 'yan boko. Ko kuma ince 'yan bokoko. Jama'a muga anan dan Allah ku kashe murya abun nan din. Daga wannan lokacin ne. 'Yan boko suka samu wannan tarihin jama'a. Kunga duk tarihin nan na baya na jihadin nan Hodiyo 'yan Hodiyo 'yan boko basu kawo shi ba fa. Abun da nake nufi. Da 'yan boko da sarakunan gargajiya basu raya wadancan matakan guda uku ba. Sai suka dauko abun da ya faru a 1804. Abun da ya faru shekara dari bisa dari chir yau shine suke bikin raya wa. Sun taba bikin san da shehu ya fara ainihin da'awar shi. Su ce to bari su yawo su yada musulunci. Sun taba yin bikin. Su ce a rinka diba gari gari ana zuwa ana musulintar da maguzawa ana kai taimakon addinin musulunci.
[Speaker seg1-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:0]
Wannan bai dame su ba. Allahumma sai Nadiran akwai wadanda suke Nadiran saboda da'awar musulunci da ake yanzu ta zama tsoman gier kan hanya. Akwai sarakunan da dole sun ga babu makawa sun sallama wasu kuma dama suna da imani ba abun da ya shafe su da gargajiya. To a daidai hijra na da dubu daya da dari biyu da sha tara wanda a daidai da miladiyar Bature 1804. Yau shekara dari biyu dundi kenan. Sai shehu ya kadaku gyan jihadi. To daga nan ne tarihin 'yan boko ya fara. Shehu ya kadaku gyan jihadi a hijra na da dubu daya da dari biyu da sha tara. Daidai da hijrar 'yan boko. 'Yan bokoko. 1804. Yau shekara dari biyu kenan. A wannan lokacin shehu ya kadaku gyan jihadi. Ya rinka aikawa da almajiran shi suna ainihin cin kasashe bayan yaci daular Gobir. Ya koru bawa ya koru wancan ainihin sarki Yunfa. Nan daga cikin almajiran shi da ya tura. Ya tura Yakubu a Bauchi. Yakubun Bauchi shi kadai ne ba Bafillatani ba. Yakubun Bauchi shine kakan wannan sarkin Sulaimana da ke kan mulki na yanzu. Wanda wannan sarkin baban shi malami ne Malam Adamu Jimba. To sarsarar wancan Yakubun Bauchi ne da shehu ya tura. Garin a kasar Adamawa an tura musu Modibbo Adama. Haka suka fi cewa amma sunan shi Adamu Modibbo Adama. Kano Sulaimana. Haka aka rinka rarraba wadannan almajirai na dan Hodiyo suna tafiya da tutar shehu. Me suka yi a da suka je wadannan kasashe? Ga yadda shehu ya basu aiki. Aikin farko shine su tsara gidan sarauta su dibi fada ta zama mai fadi gidan sarki ya zama mai fadi. Don haka zaka ga duk gidan sarakunan nan yafi na kowa fadi a gari. Wannan aikin shehu ne shehu ne ya ce musu su yi haka. Amma ba don su danna hakkin mutane ba. Domin sarki babban mutum ne. Yana da 'ya'ya yana da mata yana da bayi. In bala'i ya same ka ina zaka tafi? Gidan sarki in ba woi zo ina zai tafi? Gidan sarki in wane malami ya zo gidan sarki to sai shehu yace ku dibi gida mai fadi. Saboda babban mutum bai kamata ya zauna cikin kuntataccen gida ba. Sannan yace da masallaci a kofar gida. Kai sarkin da shehu ya tura. Kai ne malami kai ne limamin masallacin ka karantar kai limanci. Kai ne alkali. Sannan a jikin gidan kayi kotu kana alkalanci kuma kayi kurkuku. Ku kalli kofar kauyar da kake ga gidan kurkukun nan. Duk wata fada zaka ganta ga masallaci. Da. Kotu. Da kurkuku. Masallacin nan shine makaranta. Domin tsarin da suke bi karatu nau'i biyu suke suna karatun zaure suna karatu wa'am. Karatun zaure za'a zauna a fadar sarki sarki ya karantar. Karatu na gaba daya kuma ayi a masallaci a wadancan lokutan basu san tsarin su gina wasu makarantun Islamiyya ba. Malamai makarantun Islamiyya ba cewa mukayi ba kyau ba amma muna fadin tsarin da su shehu suke bi ne. To jama'ar musulmi daga wadannan bayanan nawa. Zaku gane to matakai guda hudu kenan shehu ya bi wajen gudanar da da'awar shi. Matakin farko shine. Ainihin wato karantarwa da wa'azi ga maza da mata. Da harshen Fillanci da harshen Hausa. Mataki na biyu da aka tsananta mishi sai ya gudun hijra. Mataki na uku sai ya nemi taimakon 'yan uwan shi musulmi wadanda suke kan sarauta. Mataki na hudu da abu yake tikikaka shine sai shehu ya tsai da jihadin ta Gobir da ta Gobir. Shehu yayi wannan matakai ne a karkashin wancan aya da muka karanta. Allah yake cewa Allah yace wadanda suka yi imani da Allah suka yi hijra. Suka yi jihadi wajen tada addinin Allah. Wadannan da ainihin suka tattaro kansu. Suka ainihin taimaka wa 'yan uwan su musulmi. Wadannan sune mumine na gaskiya. Gafara da arziki ya tabbata ainihin gare su. Allah mai gafara ne Allah mai rahama ne. Yanzu abun da nake so in tsaya anan. Yanzu mu malamai da muke da'awa anan kasar Hausa shin muna bin wannan matakin? Wannan wa'azin nawa da nace zanyi mutane hankalin su ya tashi. Albani yace zai yi wa'azi akan jihadin dan Hodiyo. Ba wanda ya woshi bane. Aka ce to in an kai gidan rediyo zasu sanar. Sarakunan gargajiya nace dan Allah me kuke tsoro wannan? Wannan wa'azin kan mai uwa da wabi. Sarakunan gargajiya da malaman ba sune magada shehu ba?
[Speaker seg1-spk:1]
Sune.
[Speaker seg1-spk:0]
To su wayen malaman da suke mikewa suna wa'azi a wannan zamanin ai ni din nan ina daga ciki ashe wannan wa'azin tsoman gier kan hanya ne har ni bai kyale ba. Dole in buga wa kaina alamar tambaya tsarin da'awa ta yayi daidai da tsarin da'awar shehu? Duk mai duk san da aka ce za'a yi wa'azi sai ku rude jama'a. Ace Albani zai zagi su wane. Yanzu wa aka zaga tunda aka fara wa'azi anan? Yanzu ba'a yi awa daya da rabi ana yi ba'a yi zagi ba yanzu sai nan da minti goma sha biyar shi za'a yi zagi. Me yasa kuke tsorata baku da gaskiya ne? Wallahi ba don tsoron ku ba ina yau na kunsan tunanin da nayi. Na rantse da Allah da ya halicce ni wannan wa'azin a kofar sarkin Zazzau nayi tunanin ayi shi. Amma kune masu tsorata amma wallahi ni za'a je a saka wa'azin kuma zanje in yi. Ba abun da ya shafe ni. Menene zagi ne nasiha ce malamai da sarakuna abun da kuke a yanzu haka shehu yayi? Yanzu ga tsarin da'awar shehu. Tsarin da'awar shehu itace a nemi ilimi tukuna. Shin yanzu malaman da suke da'awa a yanzu. Suna neman ilimin da za'a yi da'awa? Ko ko suna neman ilimi ne don su samu wasu bukatun nasu? Malami kawai zai tashi yayi karatu. Da zaran yaji gwamnati ta gano shi shi malami ne shikenan ba abun da ya shafe shi sai kaje ka samu littafin shi duk sunyi kura. In kace ina almajiran shi bai da almajirai baya karantar wa. Me ya dame shi a bashi kwangila yayi a bashi kujerar haji yayi yaje haji ya dawo ya ciku apartina yaga wata budurwa tana sheki a anguwa a nemo mishi izini ya aure ta. Aikin malaman kasar Hausa kenan yanzu haka shehu yayi? Wannan mas'uliya ce duk wani malami mai wa'azi ya tsaya ya duba. Matakin da shehu matakai hudu ne. Matakin farko matakin karantarwa da wa'azi. Wannan karantarwa da wa'azi shine a sa littafi ana karantar da mutane ilimi a hankali har su na kalta. Alhamdulillah ba yabon kan mu muke ba. Wannan matakin muka dauka. Muna karantar da mutane. Mutanen nan sun zo basu zo ba amma dai muna karantar wa. Nan kasa makaranta ce muke da ita yau shekarar makarantan nan goma sha hudu. Ko da mun ce makaranta sai a je ace Albani ya karya yace yana da makaranta. Me makaranta ne ba dalibi da malamai ba?
[Speaker seg1-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:0]
Dalibi dalibai da malami. To yau shekara goma sha hudu ana karatun masallaci ne mu bamu da makaranta bamu da kudi bamu gina ba tukuna. A masallaci muke karatu.
[Speaker seg1-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:0]
Ana karatun nan yau shekara goma sha hudu an fara shi tun wancan September 1990. Yau shekara goma sha hudu ana karatu. Wani yana nan anguwan nan bai taba lekawa aji ba. To sai kayi fushi kace kafiri ne? Zaka ci gaba da karantar wa ne. Matakin farko kenan na da'awa. Dole malamai su dawo. Yanzu muna da azuzuwa da muka sassaka a wasu wurare. Ina da aji a Yobe jahar Yobe. Ina da aji a jahar Kano. Ina da aji yanzu a Yola. Kasar Yaraba wa a Lagos na sa musu aji. Wannan karatun da turanci ne ma ake yi lokaci zuwa lokaci za'a je ayi sai san da na koma kuma sai a je a ci gaba dai haka ake. A Sokoto mun saka haka ake yi a hankali a hankali. Haka za'a yi ta karantar da mutane. Kana karantar wa wani bai taba zuwa ba amma yasan tarihin yadda ake karantar saboda tsabar iya rahoto. Zai je yace ance kaza ance kaza amma fa bai taba zuwa makarantan ku ba. Nan tun wada naje kotu yau shekara biyar da suka wuce 1999. Ina zaune wani yana bada labari na. Yace Albani nan wani kato ne dogo malami tauron tauron yace kwance yake a bayan marsan da ana jan shi. Kaga wani yake maganar fa. Sai na san da kai neman gushi zaka kama fito nace malam sai an ji na yi wa Allah. Yana ta bada labari ka gani haka mutane suke yi. To sai kace mai kafiri ko fasiki sai kace Allah ya shirye shi. Jahilci ne kai shi ga haka. In kayi fushi ka daina karantar wa yaushe zai ana karatun ma bai sani ba balle an daina. Malamai masu da'awa. Yanzu kafin a zo kan sarakuna ku auna kuna karantar da mutane? Kaduna nake zuwa duk ranar Asabar da Lahadi nake musu karatun Sahul Bukhari. Yau karatun an fara shi tun 1997. Yau karatun shekara bakwai ake yi. Da karatun ya habaka ya habaka masallacin yafi karfin eh muka yawan mu yayi yawa. Sai nace a je a nemo mana izinin masallacin Sultan Bello. Amma ba sabon ba saboda nasan sabo zai zai kashe wa malaman ido zasu yi hassada. Nace a bamu tsohon inda Gumi ya fara mu ma mu fara daga nan. Kunsan da muka je me aka ce? Zaka ce to zamu rinka biyan naira dari biyu da kullum. In zamu yi. Ai ina fadi ne yanzu kasan na dauka kuma nan akwai masu zuwa karatun ma. Sai na samu wani na danka mai dubu biyu nace duk ranar da Alhamis tayi ka basu kafin in zo ka yankira sai sai a baya a bada rasi ni zanje da generator ni zanje da rediyo ni zanje da camera ni zanje da komai ayi karatun sannan komai dare in taso in dawo nan haka ake ana yada addini. Amma wani anyi karatun anan Sultan Bello wani yana can anguwan nifa waya bada labarin abun da aka fada amma bai zo ba. Su ce an zagi Gumi wallahi Gumi aka zaga ance ku yi hakuri a yi. Amma in aka ce kaji sai yace kudu mu je ku a ugar mu. To ya zaka yi? Ba yadda za'a yi. Dole a karantar da mutane. Haka muka rinka mu biya mu fa zamu karantar kuma mu zamu biya yanzu mu ba ma muna sa ra'ayi a abun nan ba. Anana aka zo aka ce. Malamai ana gayyatar su su zo su yi program a gidan talabijin na Khalifa malamai sun ki zuwa. Sai wani ya bugo waya yace mu muna da malami indai yace zai zo zai zo. Yana ajiya sai ya bugo min waya yace malam naci bakin ka na ari bakin ka naci albasa. Nace ai bazaka ji kunya ba a sa program zan zo. Zaka sa aka ce sai mun biya fa tunda biya Albani me zai sai an biya da kar daga dubu goma aka yi da dubu shida. Sai da muka biya. Don haka da aka yi program din sai shi ya so ya daure ni. Yace to jama'a ga fa malam kun dai ji kun yaba suka ce eh. To malam ya alkawari kullum aka gayyato shi zai zo sai nace nayi alkawari amma fa zan fadi magana daya bazaka ji haushi ba. Nace me ce ce nace indai bazaka karbi kudi a hannu na ba to zan zo ina indai karatu ne zan zo in taimaka amma ni zan zo in yi karatu ni in bada kudi. Jama'a wannan da'awar gaskiya ban kai in yi ba. Ko ko jama'a ku tayi ni tufa. Yanzu fa ina maganar zan tafi Kaduna. A bani kudin mai ko a taimake ni a'a ni zan dau mota ta in tafi kuma in biya. Sannan in karantar sannan zanyi program a tashar talabijin kuma in biya amma ga wasu malaman ana neman su su zo su yi kyauta sun ki. Kunsan me ya faru ku je ku tambayi engineer Sardauna wanda ya gina masallacin Sultan Bello sai malaman Kaduna suka kwaso da gudu suka ce mun ji labarin ka ba Albani masallaci yace a'a. Kuyi hakuri na tsaya ne wannan duk ina sharhin wannan maganar ne tana da muhimmanci a wannan zamanin. Suka ce mun ji ka ba Albani masallacin Sultan Bello yace a'a. Ya zo yace a bashi masallaci amma tsohon muka ce to zai rinka biya dari biyu yace zai biya. Don haka in ya biya sai ya yi rasi in ya tashi kuma ma zai dauka sai ya bada. Suka ce to ai yace a'a san da malam Abubakar Gumi ya mutu na biyu ku daya daya daya daya. Har gida na same ku. Nace malam ya mutu kuzo ku saka karatu ku ci gaba da aikin shi me kuka ce? Cewa kuka ku bazaku karantar ba amma zaku rinka zuwa wa'azi ranar Juma'a. Ni kuma nace muku a'a har Gumi ya mutu shi ba wa'azin Juma'a yake ba. Karantarwa yake yi. Kuka ce a'a ku wa'azin Juma'a zaku yi nace muku to ba don Allah bane kuna zuwa wa'azi ne don ku yi wa gwamna da minister addu'a a baku sadaka. Nace to Albani ya kwaso jiki tun daga Zaria ya zo ya sa wa yara karatu. Suka zo suka ci ka masallaci ya biya kudi yace da wani dalili zan hana shi masallaci? Kunga duk baku san irin wadannan sirrorin ba don haka malaman ku ne in kuka ji mun sarkafe a wani kasari ku rinka ji a baki kuyi shiru baku san sirrorin ba kadan ne wannan. Duk guda ne wannan. Kun gani? Ana nan aka zo muka sanya karatu a can cikin tun din wada muka tun din wadar Kaduna nake magana muka sanya karatu muna karantar da littafin Mun yi karatu hudu na samu admission na tafi makaranta shine ba'a ce da ba har yanzu. To haka muke muna yawan mu karantar. Mu buga nan mu buga nan yanzu da naga na dan iya turanci zan dan bubbuga a fahimta yanzu kuma faransanci na fara koyo. To ya za'a yi? Dole ne mu fada. Muyi wa al'umma wa'azi da yaran da zasu iya mafi wancan kasashen da ke kewaye da mu. Faransanci suke yi. Duk wa'azin da muke da turanci in an kai musu basu ji ba. Kuma wasu basu jin Hausa. Hakkin mu ne muyi wa'azin kuma yadda za'a su ji. To ya za'a yi in mun tura ku ko kuma 'yan zamani muka ce ku je
[Segment 2/6 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker unknown]
ko faransanci, kuna koyar wa ko kuma sai ku kafirta wa Allah, ku ce ko ba ruwan ku da addini. To ya za'a yi? Dole mu malaman zamu je mu koya. Don haka yanzu nan faransanci nake koyo. Nan da yan shekaru kuma sai ka ji Dole ne a karantar da ma, ma gashi mun ce shehu yana karantar wa da Hausa fa? Yana karantar wa da Birtashi. Hausa yaren su ce? Ba yaren su ba ce. Haka ake yi jama'a. Matakin farko na da'awa karantar da mutane. To in ka tashi kana karantar wannan nau'i ne na jihadi, shine sai ka dauko nau'in karshe da muka fadi daga cikin mataki na hudu a dazu hakuri. Kana fara karantar wa sai a fara zagin ka. Yanzu nan galibin yara yan shekara goma sha biyar sha bakwai a unguwar nan duk an haife su ne sun ji ana zagin Albani. Shi ma wani yaron ya tashi sai dai ya ci gaba da zagin Albani, in aka ce mai dalili shima bai sani ba. Tunda dai an haife shi zikirin gidan su kenan, tasbihin gidan su kenan. Amin, to ya zaka yi? Sai kayi musu addu'a Allah ya shiryar da su. Haka shehu ya ta fama da su. Matakin nan a haka muke a yanzu. Bamu taba cewa a tashi a doki kowa ba. Bamu taba cewa a tashi a kona kowa ba, bamu taba cewa a tashi a yaki wani ba. To amma a yanzu wannan gwamnatin ta siyasar yanzu Tana tsananta mana kwatan kwacin tsananin da ake wa shehu Dan Fodio a lokacin Yunfa. Idan na ce wannan gwamnatin ina nufin gwamnatin gwamna Makera fi. Zaluntar mu ake yi. Ba'a sauraron mu. Da azumi ba na daya daga cikin malaman mu yana tafsirin yan shi'a suka je suka daba mishi wuka. Sarkin Zazzau ya mana alkawarin za'a dau mataki. Area Commander ya mana alkawarin za'a dau mataki. Gwamna yayi alkawarin ta hanyar daraktan shi na addini za'a dau mataki. Amma har yanzu shiru kake ji. To yanzu abin da muke cewa Kuna jin maganar zata wuce haka? Ba zata wuce ba. Shi yasa S S S State Security Service ku kara da S ko zuwa Z sai ku saurara da kyau ku ji. Munyi wata lecture da muka sa mata kunar bakin wake. Mun dauki rahoto a cikin lecture wannan duk mun ga rahoton da kukayi sai dai mun gode wa Allah rahoton ku da kuka rubuta baku yi mana karya ba. To yanzu ma ku rubuta da kyau. Wannan abin da aka yi wa malamin nan muna nan muna jira kamar yadda gwamnati ta ce zata yi shari'a ta gaskiya tayi. Idan tayi shari'a ta gaskiya shikenan. Mu mun san mutuncin shari'a. Mun san mutuncin doka. Idan anyi hukunci shikenan. In ko an ci gaba da wasa da hankali to kar ku manta mu din ne dai mu ne na Kano. Wanda aka kama wani arne ya ainihin dauki Alkur'ani izu 60 ya ajiye a ban daki. Kullum ya kashi sai ya zo ya shara kashi ya jefa cikin shadda. Haka ya ringa Alkur'ani. Da aka kamo shi aka kai shi gurin masu sarautar kasar Kano sai aka ce an kai maganar kotu sai aka kai shi kotu aka boye eh kurkuku. Aka yi ta yawo da hankalin musulmi. Mai matasa suka ce? Sai matasa suka ce ba zasu yafe ba. Suka bi dare karfe biyun dare suka fasa gidan kurkukun gwaran dutse ta baya. Suka je suka zaro wannan arne suka daza kanshi. A lokacin gwamna na mulkin farar koya na mulkin sojan wase gwamna wase. Me ya faru? Aka ringa kama matasan nan ana kashe su. Da muka mike muna karanta Alkur'ani muna gaya wa Allah. Muka tsine wa gwamna wase albarka. Muka ce Allah ya mai kisan wulakanci sai da jirgin sama yayi sama ya kulun kulufi ta. Sannan ya narke tun daga sama ya fado ya kashe matsiyaci. Abin da muke cewa a yanzu S S ku kai wannan rahoton zuwa ga mai gidan ku Area Commander. Shi kuma ya kawai mai gidan shi commissioner din sanda, shi kuma ya kawai mai gidan shi gwamna Makera fi Albani Albani da jama'ar shi an gama kore su. Wannan kam munyi rantsuwa da duk abin da mu mu nike rantsuwa da shi cewa Ba zamu yarda ba. Ba zamu yafe ba. Ba zamu hakura ba duk duniya ku ji wannan ba datti da ba malami da zai bamu hakuri mu ce. Sai ayi shari'a tunda an kama masu lefi. Malami ne dai yana tafsirin Alkur'ani su kuma yan shi'a mun jefa musu kalubale daya sun kasa, mun ce su kawo mana kasar din tafsirin malamin su to tunda malamin su ya kasa tafsirin shine namu malamin yana tafsirin to bara a zo a hana duka ai biyu babu. Aka zo aka daba mishi wuka. To an kama masu lefi Area Commander AC da kanshi ya kama mutum uku. Amma an je an karbi kudi an ce anyi belin su. To mu mun san su. Ko muna sane da duk inda suke. Amma mu ba yan iska bane. Mu na tsatson mutane ne kun ga tsarin da muke bi. Wannan tsarin muke bi yanzu karantar wa muke an zo an tsogale mu. Muna jiran yanzu gwamna Yunfa Yayi hukunci akai. In ba haka ba to mu zamu yi. To a lokacin da mukayi hukunci kuma in gwamna bata yi ba sai a ce mun dau doka a hannu ko? To wallahi S S ku kai wannan rahoton wallahi mun shirya zamu yake ku Allah. Amma in Allah ya kai mu lokacin Allah ya sa gwamna yayi adab Bara a koma yaren Hausa. Yau da gobe taki wasa ma'anar wakar kenan ko? Ka'idar ita ce mu da'awa muke jama'a. Bama tsogalar kowa da fada. Wa'azin mu in yayi maka zafi Ka ji abin da aka fada mana. Ka ji hujjar da aka fada mana. Iyakar cin ta kenan yadda muke wa'azi yayi daidai da yadda ya kamata ayi. An ce muna wa'azi muna habaici gaskiya ne. Taken wannan wa'azin ma nayi wa habaici ne don ni bahaushe ne. Jihadin Dan Fodio ba ha wani bahaushe bane wannan habaici ne in dai kai bahaushe ne. To Kur'ani ma akwai habaici. Zagi zagi takan kama ayi zagi Kur'ani ma akwai. Yauwa kamawa take yi. Amma habaici da zagi irin na yan iska Shine Kur'ani bai bar shi ne mu ma bama yi. Don Allah karanta inda Kur'ani yake cewa Akwai zagin da aka yi fi wannan ma a Kur'ani ne jibi fa wani takadarin mutum ne ya matsa wa annabi. Duk fitina annabi aka rasa yadda za'a yi da shi. Ashe matsiyacin ma shege ne bai da uba. Dan zina ne zina uwar shi ce ta haife shi. Yau kai kana shege ka fitina annabi sai Allah ya ce Duk wani shege mai yawan rantsuwa kar ka ji maganar shi. Dan ta'adda asi mai lefi Mai dan banza ko shege ko shashasha mazunaci yana jin wannan kalmar sai jikin shi ya sanyi sai ya zara takobi shi ya je ya tsaya a gaban uwar shi. Ya ce to kin san fa Muhammadu ba karya yake ba. Dama duk siyasa ce tun sa muke karya ta shi amma mun san ba karya yake ba ya ce ni dan zina ne. Ya akai sai ta ce wallahi gaskiya ne. Ta ce wani makewace ta je ta samo ya zina da ita ta haife shi ba dan uban shi bane. Tunda garin nan aka zauna lafiya. Yauwa to in bukata ta kama ai zagi ana yi. Ba ba irin yan iska ba. Ana yin zagi dan a irin wannan Wani dan iska ya fitine ka sai ka fadi dare ya ji kai kayi hankali ba. Yauwa mu muke zuwa ta bi gurin uwar ka. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Saboda haka Abin da muke cewa Domin ta iya yiuwa wannan maganar in ina fadin ta a nan ta iya yiuwa ta zama ita ce fitina ta farko da za'a turumce mu da ita a jihar nan. Kuma mai yiuwa jama'a ba za'a su san dalili ba. Sai dai a ga kawai mun tashi muna kashe wasu kisa. A lokacin dai sai a ce ah yaya a tsogalar mu akai kamar yadda Yunfa ya tsogali shehu. Ana tafsirin Alkur'ani da watan azumi Ku malamin ku ya fitar muku tafsirin mana. Kowa ya tafsirin mana ba shikenan ba kowa ya abin da yake so ba. Ba wani muna cikin tafsirin Kur'ani in wata guguwa ta juya sai mu ce to bana za'a yi wani irin tafsiri ne Tunda mun je mun ko yayi tafsirin zamu iya tafsiri na umumi ai ta tafiya Amma ana nan sai aka zo aka kai sai muka ce to a tsaya inda ake a bakara a dauko suratul anfal. Sai muka sa wa tafsirin jihadi ba tatsuniyar baka ba ce kasan goma. Jihadi ba tatsuniyar baka ba ce ka je ka nemi kasusuwan tafsirin suratul anfal. Jama'a mun fahimci wannan da kyau? To saboda haka Dan mai a ce malami yana tafsiri a je a ce a a farko sa gulab a dafa mishi wuka a yanke wani haba. Me yasa? Haka musulunci ya ce ayi? To mu ba yan iska bane ni na karanta civil law na san dokar Najeriya. Sannan kuma ni na karanta shari'ar musulunci na san dokar Allah. Ba zamu taba cewa a tashi ayi wani abu ba. Amma muna jiran doka ta yi aiki ni na yarda da gwamnati ni na yarda akwai gwamnati kuma na yarda akwai kotu. To amma idan gwamnatin take aiki idan kotu take aiki to shikenan sai ayi kamar yedd aka yi gwamnatin Yunfa kuma sai muyi lancing jihadi da Na dauki mataki shikenan? Na dauki mataki don haka mun ce muna jiran a kai maganar kotun shari'ar musulunci tunda sun ce su musulmi ne. Yan shi'a ne sun ce su musulmi ne. Mu ma kuma mun ce musulmi ne. Saboda haka abin da muke jira a kai kotun shari'ar musulunci ayi hukunci. Ka ji gwamna Makera fi ke kuma S S kunji ko wanene a kai wa wannan maganar tawa. Kuma wannan maganar tun ranar da Na koma makaranta kenan aka yi mun waya aka gaya mun na dawo. Na zo na samu AC abin da na gaya mai kenan tunda nayi waya kan AC na ce mishi to ga abin da ya faru. Ya ce har ya kamo mutum biyu. Na ce to abin da nake so abubuwa sun sha faruwa a baya. Don baku sani ba abubuwa sun sha faruwa. Sai a zaunar da mu sai a bamu hakuri. Sai a zaunar da mu a nuna mana Allah. Sarkin Zazzau ya lallashe mu Area Commander ya lallashe mu dattawa su lallashe mu to mu yayan mutunci ne yayan dattawa. To amma komai yana da iyaka. To yanzu hakurin ya tuke. Domin hakurin zai kai ga wulakanci. To don haka a yanzu muna jiran ayi hukunci in ba haka ba Zamu tashi duk wadanda suka yi mana wannan lefin zamu bi su dai dai dai dai zamu daddasa su In ya so daga nan kun ga zata rinca be kenan. Ana cewa Zaria ba'a taba rikici ba to kuma kun san irin wannan ran da aka tashi yi to abin ba zai yi kyau ba. Amma muna jiran kuyi hukunci na adalci hukunci ne rak mutum uku ne kadai za'a hukunta kuma an kama su. Me ya rage? An tabbatar musu da lefin su sun tabbatar da lefin su. Amma an ce ana jin tsoron su. Saboda me? Saboda gwamna nasu ne. To shikenan saboda haka ba za'a hukunta mutum uku ba? To akan a hukunta mutum uku to karshen ta dubu sa mutu. Wannan iyakacin maganata kenan mu ce jihadin Dan Fodio Jama'ar musulmi ko shehu Dan Fodio ya rubuta littattafai? Wannan magana tana da matukar muhimmanci. Malamar kasar Hausa basu cika rubuta rubuce ba wannan point wannan matsala ina so a dauke ta da muhimmanci. Malamar kasar Hausa basu cika rubuta rubuce ba shi yasa Da muka tayar ma binciken wadannan abubuwa wallahi muna shan wahala saboda malaman kasar Hausa basu cika rubuta rubuce ba. Amma shehu Dan Fodio yayi rubuce rubuce Babban malami a doctor Aminu Deeni Abubakar a cikin littafin shi mai suna da ya zo ta hakikan littafin littafin shehu ne. A cikin mukaddimar littafin shi Ya tabbatar da cewa shehu Uthman ya rubuta littattafai 110 Shehu Abdullahi Wandi ya rubuta littattafai 80 Muhammadu Bello sarkin musulmi ya rubuta 72 ko 76 ni ne na manta. A dan saurara jama'a. Yanzu tambayar tambayar ita ce wadannan littattafai ina suke? Abin takaici da yawa daga cikin littattafan nan sun samu kansu a halin maraici maraici guda biyu. Maraicin farko lokacin da turawan mulkin mallaka suka zo suka ci kasar nan da yaki kamar yadda yan boko suke cewa Yau shekara 102 kenan. A daidai wannan lokacin turawa sun kwashi wasu littattafai da yawa na shehu sun tafi da su. Amma da suka tafi da su sai suka sa kasa karanta su. Da suka kasa karanta su sai suka koma jami'o'i na kasashe irin su Jamus da wasu jami'o'i da ake karantar da Larabci suka je suka koyi Larabci suka zo suka fara karanta wadannan littattafai. Daga ciki sai suka ga akwai wasu littattafai masu hada rintsiya gare su. Sai suka dauki wadannan littattafan sai suka boye su a wani tsaran rami a cikin Oxford University dake Ingila. Wadannan littattafai guda biyu musamman su ne Littafi na biyu shine Littafin farko shekara daya kafin a kasha Sardauna. Sardauna ya je Ingila ya dauko wannan littafi sai ya biya kasar Masar ya samu wani babban malami a wannan lokaci mai suna Ya bashi ya ta hakikin wannan littafi aka buga shi littafin ya zo ya hadu a Najeriya. Yanzu akwai Littafi ne da ya kace kace da ya dassa sunna. Littafi na biyu jama'ar musulmi gashi gaba gare ni nan na zo da shi ne kadai don misali ba don wani abu ba. Wannan littafi mun taba saka karatun shi a nan unguwar duk sarakunan gargajiya hankalin su ya tashi. Kun ga littafin jama'a gashi nan Wannan littafin turawa basa kaunar shi arna basa son shi. Yan boko basa son littafin nan saboda wannan littafi in dai za'a karanta shi To insha Allahu za'a yi wa yan boko tawa yi. Insha Allahu za'a yi wa sarakunan gargajiya tawa yi. Muka saka karatun littafin nan yau kamar shekaru tara da suka wuce a masallacin cika ji da asuba sai an idar da sallah asuba tsap. Sai ka ji Albani ya fara Sarakunan gargajiya hankalin su ya tashi. Aka yi ta nemo dattawa to ina dattawa Albani yaya anyi ya ce to Albani ba kungiyar uban kowa yake ba sai a kira shi a Wannan littafi ne zai sa ya tayar wa da sarakunan gargajiya hankali. Sai dai shehu a ciki ya fadi illolin dake ga sarautun gargajiya da yadda ake kifar da sarakunan gargajiya a kafa sarautar musulunci. Da yadda ake kifar da tsarin mulki irin wannan shegiyar da demokradiya ta yan boko matuta a kafa shari'ar musulunci ta adilan musulunci. Wannan shi ya toshe musu to amma yaya akai na samu wannan littafin abin da zaka ce kenan domin dokar wannan littafin da aka sace shi aka gudu da shi can shine kar a sake wani dan Najeriya ya kai gurin. To ya akai yanzu gashi a hannun Albani Dan Najeriya a Allah ne kawai ya kawo shi Amma yadda tarihin abin ya faru shine Wani malami ne professor ne mutumin kasar Sudan ne sunan shi Al-Hassan Al-Masri professor ne ya karantar a jami'ar Ibadan. Jami'ar Ibadan din kuma a bangaren darussan musulunci da Larabci. A wannan lokacin da ya je
[Segment 3/6 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
asalin Ingila da yake shi ba yaje ne a ƙasar Najeriya ba sai aka barshi ya shiga. Da ya shiga sai ya je ya kwafi wannan littafi Da ya dawo da shi Najeriya sai yazo ya fassara shi da turanci, ya haƙƙaƙa larabcin shi sai aka haɗa aka buga yanzu nan gaba gare ni kwafin turancin ne da na Hausa gaba ɗaya. Da larabci da na turanci, da larabci da turanci gaba ɗaya. Toh wannan littafi ƴan bokoko basa son shi. Sarakunan gargajiya miyagu basa son shi. Jama'a mun gane wannan da kyau? Wannan na ɗaya daga cikin littafin ɗan fodiyo da Allah ya ƙwato da su. Toh amma yanzu dayanci ba'a san da littafin ɗan fodiyo ba yanzu kamar nan gaba gare ni ga waɗannan ƙwaya uku da na kawo a ɗazu. Kusan cin mutane basu san wannan ba. Ɗan fodiyo yana da littattafai da yawa jama'a. Kamar yadda nace Malam Aminuddeen kaɗai yace ɗan fodiyo ya rubuta littattafai waɗanda basu gaza guda 100 ba, dan Allah ina littattafan nan yanzu? Ina littafin Ina littafin Ina littafin Ina littafin Waɗannan littattafan na kushi kara goma sha bakwai ne ina tara su buhu guda nake da su a ɗaki na. Da nan warware su sune suka zama kanta guda. Toh sune a yanzu sai na tayar da wani aiki. Wannan aikin da na tayar shine kamar haka. A matsayi na alhamdulillahi na malamin musulunci wanda yake da manufar sabunta addini irin yadda ɗan fodiyo yayi. Shi yasa a lokacin muna karanta iya ussunna a nan masallacin mu. In muka karanta iya ussunna shehu yace sunna ne a daura baƙin rawani sai mu daura in mun wuce nan ana zage malam cewa ƴan shi'a, ni aka fara cewa ƴan shi'a fa wannan baku sani ba. Ni aka fara cewa ƴan shi'a kuma ƴan uwa na ahlussunna ƴan izala su suke fada mu har yau akwai waɗanda suke har aure naje nema anje ance musu ɗan izala ne. Ɗan shi'a ne. Ina cewa ɗan shi'a ne kar ku bashi kuma ƴan izala suka je suka fadi wannan. Kuma ita shi'a yau ance ke uwar albani ce zata ce ya ba abun da ya hada mu da shi. Ka gani? Shine har sana'a ce da jahilci. Lokacin da aka je a gaya ma Malam Abubakar Gumi ga wasu yara ana daura baƙin rawani suna da dagaggen wando. Gumi yace in kuna cewa musu ƴan shi'a zasu ce ku jahilai ne. Ga a iya ussunna baƙin rawani ga a iya ussunna a dage wando. Iya ussunna ba karatun ƙasar waje bane ba fa. Kuma waliyi ne ma ɗan fodiyo ya rubuta. Toh me ya faru jama'a? Waɗannan littattafan an ɓoye su. Turawa sun ɓoye, malaman bidi'ar sun ɓoye. Waɗannan littattafan a yanzu kamar yadda nace alhamdulillahi ba alfahari ba a matsayi na na malamin musulunci da nake da ƙudurar da zan iya zama in haƙƙaƙa su shine nake zaman rubuta su a kwamfuta ni da kaina. In zauna in wasalce su, in zauna inyi ta haƙƙiƙin su, inyi takhrijin hadisan su da ayoyin su. Wannan aiki na farko kenan ina so in tattara littattafan nan in buga su a wuri guda. Aikin farko ga yadda zai kasance. Waɗannan littattafai zamu tara su na ɗan fodiyo da na Abdullahi Gwandu da na Muhammadu Bello sarkin musulmi da na Nana Asma'u. Waɗannan sune na sa wa Ga misalin su kana gani ya kai ɗan uwa na. Tattaruwar ƙananan littattafai na shehu ɗan na gidan ɗan fodiyo. Wannan shine aikin da nake tattarawar littattafan. In aka kammala littattafan nan za'a buga su yadda kowa zai same su a yadda ka saba samun littafi. Aiki na farko kenan insha Allahu ku taya mu da addu'a Allah yasa muyi mu gama lafiya.
[Speaker seg3-spk:1]
Amin.
[Speaker seg3-spk:0]
Wannan aikin baya buƙatar ko kwabo. Baya buƙatar ko kwabo domin nine malamin da zanyi aiki na. Nine da kwamfuta ta da ƴan laptop ita duk ita nake a mota da na zauna naga ina jiran wani ina wani tausayi in ɗakko in ci gaba da abuna. Bana buƙatar komai a ciki ni zanyi abuna da komai da komai alhamdulillahi. Aiki na farko kenan, aiki na biyu na littattafan ɗan fodiyo sai muke sai mun yaɗa su kowa ya samu turawa sun shiga uku, malaman bidi'a sun kaɗe. Kowa sai yaji da awar ɗan godiyo. Waccan firasa da waliyyi suka yi akan ɗan fodiyo cewa za'a ji shi har duniya ta tashi sai ta tabbata insha Allahu. Wannan aiki farko kenan, aiki na biyu ga waɗanda suka iya sarrafa kwamfuta da larabci waɗannan littattafai gaba ɗaya in na gama su zan daura su akan CD ƙwaya ɗaya. Wannan aikin ma baya buƙatar ko kwabo. Domin computer scientist nake alhamdulillahi. Ni zanyi aiki da kaina in daura su akan CD ɗaya na computer yadda in ka riƙe wannan CD kana riƙe da wajen littattafai 300 a aljihun ka. Duk inda kaji aka soka shi a computer sai a bude a karanta abun da ake so a kwafi abun da ake so ayi printing aje a karanta wa jama'a su ji da'awar shehu. Wannan aiki bangare na biyu kenan. Ta iya yiwuwa akwai waɗanda ke nisan duniya zasu iya samun littafin ba ko CD. Suma sai muka ce har wa yau nan kuma a matsayi na na ɗan information technology yalam profesa dokta shek Sai aka ce ba'a hada profesa da dokta ai ko? Yalam profesa Mustafa sunan vice chancellor makarantar mu kenan. Toh a matsayi na na ɗan information technology harkar internet ta mu ta. Toh waɗannan littattafai zan daura su akan internet gaba ɗayan su da e-com Allah. Duk inda kake a duniya ko baka samu littattafan ba ko baka samu CD ba indai kana da computer ka hada ta da internet kai ko a tsakiyar daji kake da ƴan laptop ɗin ka ka hada ta da wireless model. Duk inda kake zaka kwafi littattafan ka karanta su duka baki ɗaya ta da'awar da kake so. Wannan aikin shi kuma zamu daura shi akan website akan duniyar gizo a fadi da harshen ƴan BBC ko? Website ɗin zamu creating ɗin shi a cikin wannan watan da zai kama na turawa na gobe daga cikin wannan watan in Allah yaso in ka duba wannan website ɗin zaka samu. Zan fara wannan aikin da zaran na koma yulama ko me zuwa zan fara shooting ɗin waɗanda na gama. Zuwa yanzu haka na kammala guda goma. Zan yi shooting ɗin su akan internet ina fatan nan da makobi ko uku mai zuwa insha Allahu yayi nisa tsawon ƙarshen watan nan. Ga ainihin address ɗin address ɗin shine www.fodiyo.com www ba za'a fadi da yadda ƴan BBC suke fada muku www. fodiyo.com .com Yauwa. www.fodiyo.com In ka sa www. sai ka sa fodio sai ka sa dot sai ka sa com. dot com wannan in ka buga wannan zai kai ka zuwa ga ainihin wannan website ɗin na ɗan fodiyo na fodiyo gaba 1/2 nayi ne da sunan uban su gaba 1/2 Amma in kana so ka shiga littattafan shehu ne kaɗai Toh in ka buga www.fodiyo.com sai ka sa slash Uthman usman Idan a cikin littattafan Uthman kana son hidaya ne sai ka sa slash Uthman slash hidaya h i d a y a slash Uthman slash hidaya misali www.fodiyo.com/uthman/hidaya sai kai ka kai tsaye zuwa ga wancan littafi Wannan bangaren wannan aikin kenan. Waɗannan ayyukan jama'ar musulmi sune nake kan yi a yanzu. A a saurara jama'a mun kusa tashi wa'azi insha Allahu. Wannan aikin sai naga akwai wani mutum wanda ya raya aikin ɗan fodiyo. Wannan mutumin shine Gumi Malam Abubakar Gumi Toh sai nace wannan mutumin ma baza'a barshi haka ba musamman shi ma yanzu almajiran shi suna neman su zama irin almajiran ɗan fodiyo. Su zama malaman bidi'a su zama ƴan gargajiya. Su watse gaba 1/2 su koma gindin azzalumai su daina aikin musulunci. Waɗannan Malam Abubakar Gumi shima yanzu littattafan shi har ma na kammala guda 1/2 chief Akwai littafin Ƴan bidi'a da turawa basa son wannan littafin zasu samu wani profesa ya fassara shi da turanci ƴan o Abdul Musa a jami'ar Ibadan duk da ya rasu yau kamar shekara 6 da suka wuce. Na gama zuba wannan ma shima zamu yi shooting ɗin shi akan website. Amma shi baza'a mu saka shi a wannan website ɗin ba. Na taɓa faɗar site ɗin da zan sa shi sai dai wani yayi min tanbihi da na duba sai muka ga wata tasha taccaniya su ta hau kan gurin. Muka ce da www.gumi.org www.gumi.org Toh in ka buga wannan yanzu a internet zata baka wata tasha ne a ƙasar Chinese dan akwai wani guri a ƙasar Chinese sunan shi Gumi sun bude tasha sun sa mai wannan. Toh al'amarin da yayi abun namu ɗan kura da kallon bin kize. Dama Gumi yace mana muje mu yi karatu. Insha Allahu muna nan muna yi ba ma munyi ba indai karatun kwamfuta ne alhamdulillahi. Saboda haka har yanzu zamu iya komawa www.gumi.co.uk wannan wata saba ce dake United Kingdom. www.gumi.co.uk Wannan muna fatan muyi shooting a wannan wannan kamar yadda nace zuwa ƙarshen wannan watan. Idan ta yiwu mun chanza waɗannan address zaku ji sanarwa a tashoshin BBC da sauran su yadda kowa zai iya ji. Jama'a wannan maganar kaɗai na faɗe ta ne wallahi dan abu ɗaya. Domin mu san Ina littattafan ɗan fodiyo suke a yau? Turawa sun kwashe wasu malaman bidi'a sun ɓoye sauran. Toh amma kamar yadda na faɗi yafi shekaru goma sha bakwai ina tara littattafan nan. Kuma na tara su yanzu aikin da nake kan yi kenan. Kuma waɗannan littattafai duk sanda naje yau da yanzu in na dawo wanda duk yake son ya fara samun su ma zai iya fara samun su. Amma kaɗan daga littattafan shehu ɗan fodiyo na faɗa a ɗazu irin su Nurul Albabi irin su Hidayattul Tullabi da Wasiƙattul Ikhwani da Najmul Ikhwan a cikin littafin Najmul Ikhwan ina son ku samu littafin Najmul Ikhwan shehu Uthman ya faɗi dalilin da yasa yayi yaƙin sarki Yunfa a nan ya faɗa da alƙalamin shi ya faɗi duk irin abubuwan da aka yi musu da abun da ya ja yaƙin. Idan muka dawo muna maganar mata da ƴaƴan shehu shehu yana da matan aure yana da ƙwara-ƙwarai bayi ƙwar-ƙwara Daga cikin matan shi akwai wata mai suna Muna sunan ta kenan Muna wannan Muna ta haifa mishi ƴaƴa maza guda shida mata guda uku mazan sune Aliyu da Mamma da Muhammadu da Umar da Mamma Haji da Hassan wannan ta gwaye ne ta raka haife su da Asma'u Hassan ita kuma aka sa mata Asma'u. A nan ɗakin akwai Asma'u akwai Hapsatu akwai Aisha waɗannan sune matan shi ta farko ta fara haifa mishi guda tara. Akwai wata matan shi mai suna Ita kuma ta haifa mishi ƴaƴa kamar haka guda takwas. Akwai Muhammadu Sa'ada Muhammadu Sa'ada ɗin nan yana ɗaya daga cikin ƴaƴan shehu waɗanda yasa musu ainihin Muhammadu amma ana cewa shehu Muhammadu ne saboda wancan ainihin wato Mamma na farko. Sannan akwai Muhammadu Sambo akwai Buhari cikin ƴaƴan shehu akwai wani mai suna Ina ɗaliban hadisi waye Almajirin Imam Bukhari wanda ya ruwaito Sahihul Bukhari nan dake hannun ka yanzu sunan shi Ɗan fodiyo yasa wa ɗan shi suna. Sannan akwai Khadija akwai wata Aisha akwai Juwariya akwai Amina. A cikin matan shi akwai wata mai suna Hawa ita ce ta haifi Muhammadu Bello sarkin musulmi. Ita ta haifi Abubakar Atiku ba wannan naku ba na labarin nan Abubakar Atiku wancan wannan Abubakar Atiku ba Atiku Abubakar ba. Akwai wata ƴar ta mai suna Fatima akwai ainihin Sa'adatu akwai Hannatu. Sannan akwai wata matan shi mai suna Haji Haji ita kuma ta haifa mishi ƴa ɗaya sunan ta Aisha. Akwai wata matan shi sunan ta Hajjio ta haifa mai ɗa Abdulƙadir da Fatima. Akwai kuma wata mata mai suna Janni Janni ita kuma ta haifi Halliru da Safiya. Sannan akwai kuma wata mai suna Shatumu Shatumu ita kuma ta haifi Ahmad Rufa'i da Ahmad Badawi. Akwai cikin su mai suna Mariya wato waɗannan na hada matan ne da Kuyangum. Akwai Mariya ita kuma ta haifi Ibrahim da kuma wani daban Ibrahim da su Giba Ibrahim da su wannan na kwanan nan ba. Da Isa wanda aka fi sanin shi da Auta da Amina da Hajaru da Maryamu da Hadiza. Waɗannan sune ainihin ƴaƴan shehu guda talatin da bakwai. Annabi yace kuyi aure da yawa ku haihu da yawa saboda inyi alfahari amma annabi baya nufin ku haifi ƴan iska masu kame abubuwan mutane suna cinyewa ƴan daba annabi yana nufin ku haifi salihai ne. Wani abun sha'awa duk cikin ƴaƴan shehu guda talatin da bakwai babu ɗan iska. Duk cikin ƴaƴan shi babu ɗan iska ko ɗaya. Malamai sai ku auna kan ku yanzu. Kun ga wannan wa'azin da sarakuna gaban su ya faɗi suke tsoro Albani yau zai wa'azi zai zage su har yanzu ma fa ba'a zo kan matsalar sarakunan ba tukunna yanzu malamai ake cewa malamai ku auna kan ku da'awar ku da da'awar shehu. Toh jama'a yanzu sai wata babbar magana. Wannan babbar maganar ita ce me ce ce sana'ar shehu? Abun da yasa zanyi wannan maganar saboda kar ka taɓa ɗaukar cewa shehu Uthman Allah ya yarda da shi ya zauna ne kawai yana zaman cin sadaƙa ko kuma jiran maula ta CD maula ta balarabe. Wallahi wannan a yau shi ya hana wasu malamai dayawa waɗanda sun dama ni sun shanye na ilimi amma baza'a su iya tsayawa a nan su yi magana ba. Suna tsoron gwamnati suna tsoron sarki suna tsoron masu kudi suna tsoron wane da wane. Toh da basu aikin fari sai na baƙi. Ba ji su da sana'a komai sai maula sai tumasanci. Ina rayuwa a addini zata tafi? Ga wani littafi na shehu da nake so ku same shi. Wannan littafin Gashi. Sunan littafin Shehu yace faɗakar da aboki gama da hukunce-hukuncen neman abinci. Shehu ya kawo ayoyin alƙur'ani da hadisai da suke magana akan kasuwanci. Toh dan Allah zai wuya shehu ya kawo ayoyin nan da hadisan nan da maganganun malaman su giwa amma kuma shehu ya zauna ya yi kasuwanci ya zauna yana jiran kawai a bashi sadaƙa. Jama'a bamu ce cin sadaƙa haramun bace. Amma akwai ƙasƙanci ka zauna baka da aikin komai. Sannan malamai da suke karantarwa ake basu albashi ko kuma iyaye kar ku ɗauka sadaƙa kuke basu. Kai malamin islamiya kada wani uba ya daga maka hannu yana baka sadaƙa haƙƙin ka yake baka. Kaje karantar da ɗan shi mana in ba za'a tsoro ba. Abun da nake so in ce jama'a menene sana'ar shehu sannan wacce waɗanne darussa zamu ɗauka? Tun farko ban ce sana'ar shehu ba kaɗai nace sana'o'in shehu shehu yana da shahararrun sana'o'i guda uku. Sana'ar farko ita ce sana'ar da duk wani bafulatani ya gaɗa kiwo. Toh abun mamaki shi shehu ba wai kiwon shanu kaɗai yake da'awa ki da tumaki ba. Hatta poultry farm shehu yana da ita yana da kaji da yake kiwo kaji kuma ba wai irin ƙwaya 1/2 da kaka take bayarwa in anje garin gida a ƙauye ba. Tarin kaji shehu yake kiwo da zabi da abubuwa shehu yana kiwon shanu yana kiwon raƙuma shehu yana kiwon a'awaki da tumaki. A matsayin wannan sana'a ce wanda dama duk bafulatani in ba harka ta ku wuce mishi ba yana gadon ta. Shehu yana noma noma sana'a ce jama'a. Da darajar shi da komai shehu yake duk ku sa a yi noma. Jama'a kun san wani abun sha'awa? Abdullahi Gwandu shi sana'ar shi ma kenan har aka naɗa shi gwamna kanin shehu Uthman yana gwamna sana'ar shi kenan yana ƙodago. Yana gwamna zai je ya karɓi gonar wani talaka ya nome mai ya biya shi. Garin wani noma da ya karɓa yaje zai yi girbi afuwan garin girbin da'awa da yaje zai yi kar dajiyar da'awa ta yanke shi jini ya ci gaba da zuba har ya mutu. A wajen neman halal ɗin shi annabin Allah annabi Dauda annabi Muhammadu yace Aiki yake da hannun shi ya ci abinci.
[Segment 4/6 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
Sannan shehu yana da wata masana'anta a gidan shi. Wanda a wannan masana'anta shehu yake saka ainihin igiyoyi da ake daura dabbobi tarnaki na jaki da igiyoyin daura awaki da tumaki da sauransu. To kun san wani abun sha'awa dake cikin wannan sana'ar ta karshe ta shehu? Itace kullum shehu zai zauna da safe karantar da mutane daga sallar asuba zuwa hantsi. In aka tashi sai a dibo shehu wannan kabar wanda aka jika ta sai ya zauna ya saka wadannan igiyoyi da hannun shi. Ya tubka igiyoyin nan da hannun shi. Zuwa sallar azahar sai a diba a kai kasuwa a aka sayar sai yace a kasa kudin kashi uku. Na farko a siyo raw materials shine a siyo kabar da za'a yi gobe. Kun ji ko? Kashi na biyu a yo mai cefane kashi na uku fa? Sai yace wannan za'a taimaki adinin Allah ne. Yanzu tukunna malaman mu suna da sana'ar ma da zasu taimaki adinin Allah da ita. Da suka rasa sana'ar in suka je suka wawasau sai Allah ya hana su su taimaki adinin sai ka je ka samu gabjajan malami kana jin labarin shi. Ana kunna nasu fika masallacin sai ka ji tana tsaki. Ta tsufa wayar din ya mutu. Amma yana da kudi sun fi miliyan goma. Sai Allah ya hana shi yi wa adinin aiki. Sai Allah ya maida shi irin yadda yan duniya ke rayuwa haka zai rayu. Tunda bai nemi kudin ta yadda ya kamata ba bai nema da manufa ba. Yau ya anru wannan gobe ya sake jibi yace ayi koran fenti zata yi ce yellow. Wata rana yace a hada. Ta wahala. Dama haka suka ce matukar baka yanka wa Allah horusuru ba sai ka yanka wa gunki taure ya sa. Ku duba irin wannan abu jama'a. Ku tsaya kuyi nazari cikin sana'o'in nan na shehu. In aka sayar da kanshi yake saka yake tubka wadannan ainihin wato igwai in aka sayar a yo mai cefane. Sannan a siyo abar da za'a saka a a a a tubka gobe sannan a sake. Koma a taimaka a adinin Allah ma'ana yadda kullum shehu zai taimaki gidan shi ya musu cefane sai ya taimaki adinin Allah. Malaman mu ku kama sana'a in ba haka ba ba zamu yi mutunci ba zamu yi ta fada da ku. Mu irin mu yanzu da muke independa bama karkashin kungiyar kowa bama karkashin kowa zamu zo zamu fadi gaskiya bama shakkan kowa mu ce a kai kasar ko ina. In muka zo muka fada sai a je a samu wani malami yace Allah ka fita bana kaji abun da yaran nan suka fada ko gasiya ne sai yace hawa na wannan zai shirme ne ai basu yi karatu ba. A ina suke karatu bafniya kake yi. Karya kake ko hasidin izala hasida ya san mun yi karatu. Gade zaku fada a mutane haka ku gaya mutane. Amma yanzu karya ta bayyana. Ya kamata jama'a. Malamai ku ji tsoron Allah. Ku dauki darussan dake cikin tarihin nan na dan hodiyo dan hodiyo yana da sana'a ina kara jaddada abun nan. Malami ka samu wata sana'a da kake. In ba haka ba bari mu baku wani sirri malamai magada annabawa. Bari mu baku fahimi. Bari mu baku fara. Mun kuma sadaukan muku zata yi aiki. Barar itace. In kana ganin kai malami ne ba zaka tafi ka shiga kasuwa kana harkoki ba. Saboda kana kyamar mutane kai waliyi ne. To shawarar da muke baka ga sana'ar zamani. A yau akwai sana'o'in zamani da yawa. Na daga cikin su irin tasi da achaba din nan. Ba wai kai kayi ba sai ka sayi babur ka bayar a rinka maka kullum sai a kawo maka return. Kana nan zaune kana ta wurdi a zaune. A zo da dubu biyu a je. Sai ka ga turfuraka tana sheki. Jama'a haka ne ko ba haka ba?
[Speaker seg4-spk:1]
Haka ne.
[Speaker seg4-spk:0]
Ka sayi tasi. Ana nan ana neman ka kabo kabo. Sai ka ga kana hadawa kana daki ba jama'a basu san sirrin ka ba to fahimi ne muka baka ka ji shi. To babban fahimin bari mu sakan maka shi. Ku rinka siyan hannun jari hannun jari nan da ake cewa ana siyar wa kuna ta barwa kafirai suna ta siyan hannun jari baku san abun da ake nufi ba. Wannan hannun jari da ake saye wani dattijo da ba zan fadi sunan shi ba a nan zariya ya sayi hannun jari yau shekara sha tara da ta wuce shi yama manta Allah sarki. Ka san bahaushe wani lokacin dan aidon kiya ne. Yana da kudi a lokacin aka zo aka ce mishi alhaji can sai hannun jari me nan ne hannun zariya aka ce tashi ka je ka je ka shige a bashi dai daddango la ya sa hoto sai ku tafi yana ganin kawai a cuce shi. Bayan shekara goma sha bakwai ba rawan can kenan. Aka zo aka samu shi alhaji ka manta da kudin ka ne da kake a da zuwa kamfanin mu. Yace wannan kudi nake da su yara. Yace ah alhaji kana da kudi gashi ka sa hannun a abu dan maka yace ku tsaya ku ji yara. In kun zo cuta ta ne bani da kudin yanzu na karye. Alhaji alhaji kudin ka ne ga sa hannun ka ga hoton ka. Aka fito da dattijon miliyan goma sha tara. Sha daya aka ce ko sha biyu. Yanzu don Allah dattijo ya fara makarkata sabo da bai cin naman kaza tsoho bai cin naman kaza makarkata yake sirrin kenan jama'a. Ku tambayi wadannan su gaya muku yadda yake shi. In ka tsoho baka cin naman kaza shine za'a kana kana yana makarkata ba wani alhaniji jikin ka ta ku Kaza ce baya ci. In da Allah ka yi shekarun sa bakwai kana makarkata aka ce ga miliyan sha daya. Yau ba shikenan sai ka ga an maida kai sabo ba malam. An yi maka garan bahaushe. I In ni ne kai inji da zan je du wannan tamojin a shashare. Sarauniyar ingila haka ake mata ta tsufa ta tsufa sai a je da ita wani inji di sai ya kakkau da tamojin nan a yanyan ke fata a zubar sai gatta ka ma sabo budurwa yau kana da kudi kuma yaya harka ai. Sai ka ga kana shafa rab malam yana shigewa wani dogo da Yau mun gane wannan da kyau. Ku rinka siyan hannun jari jama'ar mu malaman muna baku wannan shawarar. Amma galibi in mu mun zo mun kawo musu shawara da mun tafi sai a ce na fada su yan takarda ne kai kai hankali dan boko dan takarda ne dan farar ka zai yi. Shikenan sai ya zama baku da yanci kuna jin kunyar ku shiga kasuwa kuyi kasuwanci. Sannan ba zaku yarda ayi muku jagorancin haka kan ku ya waye ba. Sannan sai ku zauna haka. Yo in bahaushe na kanci da yaushe za'a ce wai gwamna ya tattara malaman jihar kaduna ya basu naira dubu dari su arba'in su raba naira dubu biyu akan maganar shari'a an shashantar da ita. In bahaushe na kanci ba me aka yi aka yi naira dubu biyu. Naira dubu biyu wata tsiya ce ranar da zasu tafi kaduna ina ganin su. Ina ganin su a mota na yauba taking din su ni zan tafi abuja su kuma zasu tafi kaduna za'a tafi maganar shari'a. Da aka je me ya faru? Aka basu naira dubu dari. Malam arsalan lokacin yace ba zamu karba ba ba abun da ya kai mu ba kenan abun da ya kai mu maganar shari'a suka ce ah mu muna bukata yace ai ba bukata ta kawo mu ba. Mu maganar shari'a ta kawo mu. Yana kaucewa kawai sai suka ce mu karbe suka kasauta abun su. Kafin ya dawo zariya shi din ya tafi shudushidun shi kaduna sirri gashi suka zo nan suka yi mai sharri suka ce an je ya zanzashi gwamna. Daga nan suka yi ta bata sunan shi dan kai yazo ya fadi gaskiya a kasa fahimta abun. Naira dubu biyu din akan maganar shari'a suka ci maganar shari'a gashi nan ta sha ruwa dubu dubu. A naira dubu biyu aka yi cinikin shari'ar musulunci aka zo nan suka ci. Me yasa ba sana'a. Ba aikin fari sai na baki. Yo yaushe don Allah rayuwa zata yo yaushe adini zai yo. Jama'a idan malamai basa iya fadin gaskiya kasa ba zata gyaru ba. Kasa ba zata gyaru ba in malamai basa fadin gaskiya. Gabar wa'azin mu karshe itace magana mai muhimmanci akan yanzu to ina matsayin almajiran shehu ina almajiran shehu ina yayan shehu. Na rantse da Allah wannan faslin zan tattauna shi amma ina mai jin kunya. Saboda maganganun dake karkashin su basu da kyau. Maganganun dake karkashin wannan gabar ba dadi. Tarihin shehu daga haihuwar shi. Zuwa lokuttan yayan shi na kusa irin su muhammadu bello tarihin yana da dadi. Amma daga lokacin da. Allah madaukakin sarki ya dauki ran shehu. Dalla yazo ya tafi su atiku suka zo saura duk sauran bayan Allah suka kare. Daga sa'ar da turawa suka zo jama'a sai sharri ya faru. A da. Har shallar larabci shine official language. Ga larabci ake tattaunawa. An ce ta kai ma hatta asma'u idan shehu ya kira ta zai aike ta larabci yake mata. Ta kai ma abdullahi bayar wa shehu fillanci shehu biya mishi sai inda ta kama larabci suke yi sai da larabci ya karfi har shi ya kai yau mafi yawancin kalmomin hausawa larabci sai ya shiga. Malaman hausava daga jami'ar bayero suka ce duk wata kalma da kaji a hausa ance al. To larabci ce misali albasa. Albasulu ce. Alkaki. Alkaku. Alkubus. Alkhubus. Irin wadannan kalmomin gasu nan burjik. Jama'a mun gane wannan da kyau? To da turawa suka zo suka karya wannan gwamnati. Wannan ba tarihin zamu tsaya a yanzu ba amma so muke mu kai ina matsayin yanzu wani hali yaya da jikokin shehu suka koma. Yaya almajiran shehu suka koma ina masarautun da shehu ya danka wa tuta a yau. Da wadannan mutane turawa suka ci yai. Sai suka ce sun soke larabci a matsayin official language fari na farko da suka fara kenan. Suka ce sun soke shari'ar musulunci a matsayin shari'ar dake jagoranci. Suka ce yanzu za'a hada wata kasa ne mai suna nigeria wannan sunan matar gwamna lugga. In kai tsoho ne gwamna mai wandan karfi. Ita ta sawa kasar wannan suna. Shehu shagari a 1947. Yana malamin makaranta ya rera wata waka yace sun kira wani kogi kwara. Sun kira wani kogi neja mu kwara muke ce wajiya daga sunan kogin nan daya suka sa ma kasar suka rataya dan kogin yafi cikin ta ne ya ratsa kasar ya zagaya. Shagarin ku wannan shugaban kasa shi wannan waka a 1947 yana malamin makaranta a. A sokoto. Wannan sunan na nigeria sai suka ce tunda suna ne da ya tattaro kasashe da suka fi fadi fiye da kasar shehu akwai kiristoci akwai yahudu akwai maguzawa akwai arna. Sai suka ce to shari'ar musulunci ba zata yiwu ba dole sai dai a samu final court. Final court din nan wai shi wata doka ce da zata yi surfin tsakanin arne da musulmi. Amma gaskiyar lamari. Shari'ar kiristoci ce aka dibo aka zuba. Aka dibo yahudawa aka zuba. Sai aka kauda shari'ar musulunci. A lokacin sai suka ce harshen hausa shine harshen da za'a amfani da shi a arewacin nigeria. Da farko sun dauki hausan sokoto turawa kenan. Shi yasa zaka ga duk wani dan bokon da in yazo rubuta kalmar malam sai ya rubuta mallam koda baba sokoto bane sai ya rubuta double l sabo da wancan tarbiyyar. Daga baya sai suka zo suka dauki hausan kano. Daga baya sai suka ce sun soke hausa a matsayin official language hatta a nigeria ta arewa dole turanci ne kawai. Kun ji makircin da suka yi mataki mataki. Jama'ar musulmi. Abin takaici kamar yadda na fadi yau. Wadanda suke daddanta kansu da shehu usmanu. Da sarakuna na gargajiya. Da malaman bidi'a. Duk sun narke a cikin abun da shehu ya mutu yana fada da shi. Zalunci da bidi'a. Malaman kasar hausa. A yau da dama daga ciki sun koma zalunci. Tsubbace tsubbace. Baba rayi sata sai sai sa'a. Guru da laya burudun sha da sauran duk wani tsubburce tsubburce abun da suke kenan. An waye gari yau sarakuna sun lalace. Ya jama'ar musulmi ina mai bakin cikin cewa wata hira da naji a radio nigeria kaduna. Ana da magajin shehu dan hodiyo. Jikan dan hodiyo. Sarkin musulmi na yanzu. Muhammadu macido ina mai jin kunyar fadin wannan maganar ina kuma mai jin takaicin ta tunda da zuciyar baki. Amma ya kama mu fada ne dan a gyara. Macido aka ce iya karkara tunka na muhammadiyya yaya yace iya kashe amma. Iya kashe amma na rantse da Allah wannan maganar ba'a bar dariya bace. Kuma idan na fadi wannan maganar da nufin wulakanci Allah ya wulakanta ni. Wallahi ta kama ni amma wallahi ina mai jin takaici ace. Sarkin musulmin da muke musulunci a zamanin shi. Iya kacinsa amma adinin mu ya shiga ru. Wannan shi zai sanar da ganin wata shi zai sanar da sanda za'a hau arafa ko kuma idi babba. Iya kacinsa amma. Yanzu ya ayyuhallazina amanu kutiba alaikumus siyama kama kutiba alal lazina min kablikum bai san ta ba. Tunda ko saukar zu'u bai mukan nan aya da tayi maganar azumi bai san ta ba. Wallahi azimi wannan ba karamin bala'i bane a gidan radio nigeria kaduna aka yi wannan tarihin. Da naji har sai da nace in fa ba dan ni naji wannan da kai na fada in aka fada mun ba zan yarda ba. To shikenan fa wani fa bai kai alam tara kai babba fa. Wani bai kai alam tara kai fa ba. Sannan wani abun takaici shi wannan sarkin musulmin na yanzu. Shine malaman mu suka zo daga madina su doctor zarban alghamidi suka bashi gamar. Ya kawo yayan musulmi da suka cancanta a kai su jami'ar madina su yi karatu. Sai ya dibi yayan shi guda biyu na cikin shi ya bayar. Wallahi da sun cancanta babu komai amma basu cancanta ba 1998 na je saudi arabia. Sai na samu ana koyawa daya daga cikin su huruful hija'iya wanda yake koyar mai huruful hija'iya shine malam ismail wanda yayi kulliyatus shari'a a wannan jami'ar tsohon almajirin dan gongo. Yan izala gangan sun san shi sanda dan gungun ya ta waye shine yazo yana kwaikwayon muryar dan gongo. Shima yana daga sama har kasa in kun manta shi to shine ismail sai na hadu da shi a nan masallacin jam'iyyar islamiyya mun yi sallar asuba na fito. Nace zo ka raka ni sai yazo ya raka ni sai nace wannan yaro kake koyawa huruful hija'iya haka a jami'a. Sai yace dan macido ne sai nace wannan macido yace sarkin musulmi nace ai bama wasa da kai yace ai ba wasa bane yace yayan shi. Yace su biyu ne aka kawo su saboda an ba baban su damar ya kawo mutane sai ya bada yayan shi. Bazo basu cancanta ba to a takaitce yanzu dai daya bazai iya. Zama a sakandare ba ma an koro shi daya kuma yanzu yana sakandare aji shi da tun 1998 yau shekara shida. Da yayan talakawa da suka cancanta aka tura dasu tuni basu yi sun dawo suna wa'azi ba. Wannan yana daga abun da na gaya wa zarban. Nace kuna da wata hikima wadda mu bama ganin daidai ce. Su wai abun da suke tunani in suka kwashe yayan sarakuna suka je suka yi karatun suka dawo zasu yi fiyayya da'awa. Yaya dan nigeria yayan talakawa sune mune nan muke ta kwamawa. Kun san duk wanda yake da'awa a nigeria in yazo sai dai ya maka karya. Dukkan mu dake da'awar sunna duk wanda ya bude baki yace baba na malami ne karya yake so yayi kawai. Ya fadi gaskiya. Nace baban shi sarki ne waye? Yayan talakawa ne. Mu din da ba'a so muje din mune kuma Allah cikin ikon shi sai ya sa zamu iya tada bakin kuma kuma sai a ce tunda mu ba yayan kowa bane bazamu je ba su kuma sai suje din gashi nan an bata yanzu wannan ainihin admission letters guda biyu. Wannan wannan kadan ne daga makomar jikokin shehu ba a yau shi wannan din nan shima jikan shehu ne. Akwai wani babban malami wadanda suka san zamanin sardauna a ilmance. Kun san shi. Wazirun sokoto malam junaidu. Wazirun sokoto malam junaidu gogaggen malami ne cikin lacan nan tawa yana daga cikin littattafan shi da na duba. Yayi iyakar kokarin shi malami ne kuma dan boko ya rubuta da larabci ya rubuta da hausa ya rubuta da turanci yayi hidima ga ainihin ayyukan dan hodiyo. Amma yau kaje ka samu yayan waziri. A cikin yayan waziri yau akwai wanda bazai iya karanta maka sunayen littattafan waziri kwaya biyu ba gasu yana gani a rubuce. Jama'ar musulmi wannan sharri ne. Wannan masifa ce. Wadannan bangaren malami kenan. To bangaren sarakuna fa. Duk kasar hausan nan tunda da kano har zazzau tun daga katsina har sokoto. Har ka buga adamawa duk inda ka buga wannan tutocin shehu ne. Wadannan sarakunan a yau. Sunayin aiki da shehu dan hodiyo kakansu ya bari. Suna da'awa. Suna kira mutane zuwa ga adini. Ku kuwa sun koma sun shantake. Yadda suka lalace suka lalatad da adinin Allah sai Allah ya wulakanta su yanzu ko kun san wani sharri sarakunan nan na gargajiya fa babu sunan su a kwansu to shehu. Yadda kake jobless baka da aiki yi haka fa suke a wurin gwamnati har yanzu suna gwagwarmaya ne a neman musu aikin yi a a gwamnati ba sunan su. Ba wani aiki ne ke karkashin su basu cikin lissafin gwamnati. Me yasa? Suka wulakanta adinin Allah sai Allah ya hada su da karmika yan boko. Suka wulakanta su yan boko sun ci mutuncin sarakunan nan kuma daidai da su kenan.
[Segment 5/6 | 01:20:00–01:40:00]
[Speaker seg5-spk:0]
wulakanta addinin Allah, sai Allah ya kawo karnuka 'yan boko suka wulakanta su. Yanzu ko kunsan kansila kansila yafi sarki da rai? Yanzu sarki mai martaba mai daraja duk darajar shi in zai fita daga lokal gwamnat dole sai ya nemi izinin ciyaman. Idan ciyaman ya hana shi dole ya hakura. Ciyaman dinnan fa koda arne ne bakin arne daga kan dutsen ku fa yayi sako yau, inda yaci ciyaman shi to gobe fa sarki da sallah da carbi da komai bazai duka ba sai wannan arnan ya yarda. Saboda sun wulakanta addinin Allah. Malamai kuji tsoron Allah. Kudawo kan addinin Allah kuzo mu hadu daku a fadi gaskiya abar gaskiya tayi aiki. Sarakuna kuji tsoron Allah. Ku hada kai daku muyi wa addini aiki inba haka ba Allah zai karya mulkin ku. Allah zai gyara kasa domin kasa ba tamu bace. Allah zai kawo bayin Allah wadanda da gaske suke. Tsaye da sallah bada zakka su umarni kyakkyawa su hana mummuna. Amma kasa ta lalace. Sarkin Zazzau Ja'afaru nan kurkusa a zamanin shi inka kama hannu kana tafiya da mace wai kaine dan iskan anguwa. Mara kunya a haife ka a tsakiyar muce nan amma sai ka riko budurwa wai ka wuce da ita, wai kai ai kayi boko. Wai kai dan wuta ne ka share kayan ka daga gaban mutunci ba ruwan ka da mutunci. Wai sai kayo zanzaro ka wuce da mace baka jin kunyar kowa sai kasa bakin gilas. A zamanin sarkin Zazzau Ja'afaru inkayi haka anan kasan Zariya budala goma ake yi. A yanzu kuma addini ya lalace. Yanzu ku dubi wani iskanci da yara suka dauko da sallah sallar musulmi yara suna buga nok aut. Da sallar musulmi yara suna buga nok aut, karamar sallah ko babba suna buga wannan gurnetin arna. In aka ce yau Ja'afaru gobe sallah sai kayi ta ji ta tas ta tas kuma 'ya'yan musulmi ne suke yi. Ina masu mulki wannan ba bata addini bane? Wannan baba da tarbiya bane? Da sallah kaga dan musulmi yasa hula sallah? Yasa kabi kunne a kunna hagu ya kawo sarka yasa kamar dan kwikwiyo kun zura musu ido wai kowa ya rayu yadda yake so. Wannan ba bacin tarbiya bane? Ina sarakunan arewa? Kunci amanar sardauna. Jihadin da sardauna ya dauko na kakan shi arna suka kashe shi me yasa bazaku ci gaba ba? Arnan kasan nan sun kashe sardauna ne saboda ganin ya tayar mu musulunci. Yana shiga lungu lungu yana musuluntar da mutane. Lungu lungu yana shiga yana musuluntar da mutane. Can wajen kasar Kafanchan wata rana na dawo harka ta nazo na tsaya na shiga wani kauye can surkuki na ja mota ta a bakin hanya can na shiga surkukin duwatsu na shiga wani kauye nace ina so inyi wa'azi wata tsohuwa tana daka nace kai na na ni musulma ce tun zamanin sardauna muke musulunci. Ta dauko mana a tamfa mai tabarma tace ka gani ma sardauna tunda ya bani na boye a nan tarihi ne. Wannan aikin sardauna ne sarakuna kunayin wannan? Ku je ku gyara in anje ance muku albaniya zage ku oho gobe ma albani zai saka wa'azi a wani wurin matsala bata kare muku ba gwamma ku gyara kawai ya fi muku. Kuji tsoron Allah kasa ta lalace. Yanzu in aka ce ana aure 'yan boko suke tafi Zariya suyi ta shan giya suna zinace zinace. To luwadi wannan ai ma ya zama wani abun alfahari yanzu. Drama nan da ake sa ta Hausa drama arna inyamurai da suke yi Nigeria film sai da suka zauna suka yi sai da suke tsayawa suka suka daina ta abun daidai da al'adar su. Ku kun bar wadannan 'yan mata karuwai na Kano sunje suna yin drama suna kwaso al'adun Indiyoyi sun canza muku dabi'a sun canza muku al'ada sun canza muku addini. Duk wannan ba lalata addini bane sarakunan gargajiya bazaku yi magana ba. Malamar kasar Hausa bazaku je ku kai wannan kara wurin fadar mai martaba ba sai in anyi sallar juma'a karfe tara ku matsalar kuke nan. Albaniya yayi sallah karfe tara zai canza malikiya kaji karya ko mukhtasar baka kai ba fa ko mukhtasar baka kai ba za'a canza malikiya ko mukhtasar bai iya ba. Ku dubi wannan jamal wallahil azimi wadannan abubuwa ne da ya kamata mu tsaya muyi nazari. Malamai kuji tsoron Allah. Sarakuna kuji tsoron Allah. Wannan hawan daushe da kukayi saboda wai jihadin nan audio ya shekara 200 wallah karya kuke. Ba wai da ya tusa ba wai da ya ne dan audio ya fara jihadi ba karya kuke su Hamfred sun gaya muku karya su Hamfred sun gaya muku karya da suka rubuta muku a tarihi saboda su Hamfred kafirai ne suka zo suka rubuta tarihi Nigeria aka samu wani zindikin baturan mulkin mallaka wai yana son ya fassara wannan littafin infakul maisur baya jin larabci sai dai yana jin Hausa wai sai a karanta mai da larabci a fassara mai da Hausa shi kuma wai sai ya fassara da turanci wai da haka ya fassara littafin infakul maisur da haka sai suka bi suka cancanza tarihin kasar Hausa. Duk duk karantarwa da jihadi da gwagwarmaya yada addini da alherin dan audio turawa sai suka wasap da wannan. Idan kuka je ana karantar da ku Nigerian history tarihin Nigeria abun da ake cewa wani bafulatani ne wallah muna primary bani manta hahoton shi akayi a wani littafi gashi na ya tsaga kafa daya haka ya yayi irin abun da fulani suke da sanda haka. Shanu suka kare mai takai ciyawa dashi shine ya tashe ta kashe mutane. In ba damun sa addini ba dole da haka zamu tashi ya ka iya tun kana aji uku an saba ka wannan addinin. To duk sai aka yanke sai aka ce wai dan audio ya fara jihadi ne daga hijirar bature tana da dubu daya da dari takwas da hudu dan haka yau shekara dari biyu. A wannan lokacin shehun dan audio ya shekara 39 fa yana jihadi yana da'awa duk ba'a bada labarin wannan ba sai randa ya fara yaki. To abun da kayi cin da da kuka tashi ku raya ko zaku tuna sai ku zauna sai ku dubi kan ku ku ga wace asara kuka yi wa kan ku wace asara ce ta shafe ku akwai kurkushin jihadin kuna aikin da kakan ku yayi da sai ku zauna ku rushe da kuka kuma ni na tabbatar har ga Allah da shehu zai dawo duniya yau da yawa daga sarakunan kasar Hausa sai ya yake su. Don in har shehu zai yaki sarki Yunfa ku je ku karanta wannan littafin Najimul Ikhwan a cikin ta hakika na shafi na dari daya da goma sha biyar dari daya da goma sha biyar a cikin nawa ta hakikin a ciki anan dan audio yake fadin dalilin da yasa ya yaki Yunfa sarakunan gargajiya da yawa a yau sun cika wannan dalilin shehu da sai ya yake su. Fada da addini rashin yada addinin musulunci. In anyi musu wa'azi suce an zage su to ku duba irin wannan to ya za'ayi da su kenan? Da karshe nace zanyi magana akan wasiyyar shehu duk dattijon in yazo rasuwa ko rasuwa ta taho gare shi zai yi wasiya ai ko? Shehu yayi wasiya guda biyu wasiya daya khas wasiya ta biyu amma wasiyyar shi khassa itace ga dan shi Bello ya kira dan shi Bello yace daga cikin 'ya'ya na kai na nura kafi dacewa da harkan mulki da siyasa abun da nake maka wasiyya zan kwanta in rasu amma zan barka cikin rigingimu yace don haka kayi hakuri ka daure kasan inka haifi 'ya'ya da yawa zaka ga wani yafi dacewa yafi kama da kai. Akwai wani rago ne lubu lubu ne to wannan me zaka gaya mishi? Sai dai kace to kai ka daina sa ma abun da zaka dinga kaya bakin ka Allah ya kiyaye ka da duniya lafiya to amma Bello namiji ne shi yasa yasa mai Bello din ai ma anan Bello da turawa ne suka canza ba Bello bane Ballo ne Ballo ne da fillanci Ballo ma'anar shi Nasir sanda aka haife su shehu yana kallon shi yace wannan Ballo ne wannan Nasir wannan shi zai taimake ne. Tunda aka haife shi shi ka kaga gare ke da jikin shi ba rago bane shehu ya zaunar dashi yace zan mutu zan barka cikin rigingimu naga kana da karfin zuciya kuma naga harkokin mulki da sarauta da siyasa kafi dacewa da su yace to duk abun da ya same ka na fito ka daure kayi hakuri kuma Allah ya sa maka albarka Allah ya taimake ka. Shehu yana mutuwa sai aka je aka gayawa Abdullahi Gwandu kafin Abdullahi Gwandu ya zo nan da nan sai aka yi wa Bello mubaya'a da daddare gari na wayewa anyi sallah asuba tun dare Abdullahi ya nemi a bude mai kofa aka yi sai kwance shi a waje bai doka yace ko da tsiya ko da arziki ba kuma shi dinnan ya girmi Bello ya karantar da shi kuma kanin uban shi. Amma da ya gane akwai makircin mahassada aka hana shi shigo a dan ya shigo daga gari shi za'a yi wa mubaya'a tunda shine mutum na kusa da shehu. To amma yana nesa an nada shi gwamna a Gwandu sai kwance shi a kofa gari ya waye aka bude aka yi sallah asuba aka ce an riga an nada Bello ya zama sarkin musulmi. Ana sa ido ne ya tada kayar baya gwamnatin ta wargaje. Sai shi Abdullahi yace to Allah ya sa albarka. Ya taso zai yi wa Bello ya taso sai shi Abdullahi yace koma ka zauna ai kaine shugaban mu. Yaje gaishe shi yayi mishi mubaya'a a bisa al'kur'ani da hadisi. A garin Zazzau mun samu limami daya mai irin wannan zuciyar shine Malam Hudu Cikaji Allah ya ji kan shi. Amin. Shine mai halin 'yan mazan jiya salafus salih aka cire shi daga limancin aka gimishi juyin mulki aka yi mishi duk abun da aka yi mishi ya juyo yayi wa Zariya kuma yace ba shikenan ba fitina. Sai naga zauna lafiya ba shikenan ba gashi mun yi mai mubaya'a da duk ta har ya gitsefa shine saboda haka kunji bayan wannan abun da ya faru nasiha khassa nasihar shehu amma gata a karshen wannan littafin shima a cikin ta hakikin da nayi a shafi na 16 zuwa na 17 shehu yace idan da zaka ce muni ni dan audio in bayyana muku abubuwan da zai haskaka muku rayuwa kul da sai ince jama'a wannan wasiyyar da nake karantawa gaskiya na yi wa dalibai alkawari da zata zama wa'azi ne mai zaman kanta domin wannan wasiyyar da shehu ya fada ya kamata ta zama wa'azi ne zaman kanta amma karanta ta a wani wuri mu ji ta wata rana zata zama wa'azi insha Allahu. Shehu yace wasiyiyoyi guda hudu kana son haskaka rayuwa kaine dan kabuwa kaine ma'aikacin gwamnati kaine dan makaranta aure kake nema ko dan takara ne kai indai kana son hasken rayuwa shehu yace ga abu hudu abu na farko shehu yace ka lazimci tilawatan tilawa al'kur'ani ta kara ka zauna kayi ta karanta al'kur'ani ko kana yin haka? Ko ko sai bala'i ya same ka dan yanzu har ya zama wani abun mamaki in aka ga mutum ya nannada kafa yana karatun al'kur'ani sai a ce lafiya? Saboda wai yanzu sai in ana damuna haka ake karanta al'kur'ani amma in duniya komai na tafiya anje ka kama motar mutum sai dai kaji disko twistan suna amsawa wannan sharri ne ace musulmi baya karatun al'kur'ani shehu yace ka rinka tilawa al'kur'ani da lura da ayoyin shi da kuma fahimtar ma'anonin shi. Jama'a kunji karanta hadisan manzon Allah Allah ya ji kan Malam Abubakar Mahmoud Gumi shekhul islam alqadis shar'i al'alimul allama Malam Abubakar Gumi yace karatun hadisi da aiki dashi shine zama lafiya ga musulmi ina 'yan uwa 'yan izala kuna karatun hadisi ku dubi kan ku da kyau kuna ta fada a masallaci kungiya tana ta bindiga tana fashewa kuna karanta hadisi duk inda ba'a karatun hadisi wallah sai kayi yara ku je mai duguru ku gani kaje na same su shekara hudu da suka wuce suna ta fada wannan ya dan je karanto wata takara yazo ya mike assalamu alaikum wanda duk bai bi wannan ba dan wuta ne wani yace karya kake ai ta dambe nace me zafi ana karatun hadisi masallacin nan aka ce ba'a yi nace to Gumi yace karatun hadisi da aiki dashi shine zama lafiya ga musulmi wallah ni na manta nayi musu wannan maganar so suke tuna mun wata uku da suka wuce wata uku da suka wuce naje mai duguru so suka ce tun shawarar da ka bamu fa ana saka karatun hadisin nan shikenan amma manta da fada yanzu karatun kawai ake yi nace wasiyyar waliyi kenan Gumi waliyi ne yayi sai ka zaba waliyi sai ana yana wasa kudi wasiyyar waliyi kenan Gumi yace karatun hadisi da aiki dashi in kun karanta in ba ku je ku zauna lafiya yanzu dayawan cin ahlu sunna basa karatun hadisin in ma suna yi in aka zo kan wani hadisi sai a ce ah to wannan fa ba manhajar mu bane wannan ne shehu ya rubuta wani littafi duk tayi Allah ya same ka wannan yana daya daga cikin ta fan da na gama aiki a kan su shehu yace mas'aloli goma mas'alar farko yace ka sani da cewa duk abun da yazo a cikin hadisin manzon Allah daga annabi ba'a kiran shi mazhaba sunan wannan abu shari'a dole kowa yayi yanzu maganar runguma hannu a sallah kana cewa mazhabar shafiyya ce sai a ce kayi zalunci tunda annabi ne kawai sai kace sunna ce don da kace mazhabar wane ce sai ka zo kayi wasa da hankalin mutane sai wani yace wai ni ba mazhabar nake bi ba amma in abu ya tabbata a hadisi to sai a ce wannan shari'a ce shehu yace dole a bi jama'a kunji wasiyyar shehu ta biyu karanta hadisan manzon Allah da karatun tarihin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama da fahimtar maganar annabi da bin sunnar shi ana karanta hadisan annabi ana karanta tarihin annabi ko sai ranar maulidi ana bin sunnar annabi ko ko sai wadda ta dace da 'yan komiti shehu yace wasiyya ta uku sanin labaran 'yan mazan jiya salaf wannan da muke danganta kan mu gare su mu daku ku kuke ce muna mu muke cewa kan mu salafiyya to shehu yace a rinka karanta labarin salaf wai su waye salaf ne daga cikin sahabbai da tabi'ai kuma a rinka kwaikwayar su kuma a rinka kwaikwayar su wasiyyar shehu ta uku kenan in kana son karanta tarihin salaf ga littattafai zan gaya maka ka samu littafin littafin ainihin sarki ya tabbata ga Allah zaka sha tarihin sahabbai a nan baki daya shine ka samu wadannan littattafai ka rinka karanta idan Allah yasa ka kware ka iya komputa kazo mu samo maka CD kwaya daya duk wadannan littattafai suna kan CD kwaya daya kuma naira dari biyar zamu siyan maka rack kaje ka gode kayi ta karanta kana ta shan hadisan manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama jama'a mun gane wannan da kyau ko?
[Speaker seg5-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg5-spk:0]
Sannan tsoron Allah da kuma tsayuwa akan da nisantar mummuna nan abubuwa sai shehu yace adadin nan abubuwa guda hudu suke haskaka kirji su kara ma basirar ka haske. Yanzu rayuwa kowa yana kuka tayi kunji 'yan kasuwa suce kasuwa ba abun da ke gudana sallah tazo ace to ba wani abu duk daya ne 0 ma'aikatan gwamnati komai ya rikice gulyan makaranta a Ubasanjaya ce dubu biyar da muke biya dubu hamsin zamu biya to ya za'ayi komai ya rikice to ya zaka yanzu wannan kunci da bala'i da ka samu kan ka wallah ka kama al'kur'ani da hadisi kayi ta tilawa kayi ta karanta tarihin sahabbai da sauran su shikenan sai kaga kaman ma baka tare da wannan zamanin sai rayuwar tayi maka sauki amma indai tarihin 'yan iska za'ayi ta karantawa su su gwamna Lugga su gwamna to wallah wahala ta same ka bakin ciki kuma yanzu ka fara Allah ya kiyaye. Jama'ar musulmi kunji wannan itace ainihin wasiyyar shehu Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Bayan wannan shehu Usmanu ya rasu ainihin wato safiyar litinin uku ga watan hijira na da shekara dubu daya da dari biyu da talatin da biyu daidai da ya shekara 63 a duniya daidai da halifancin daidai da shekarun annabi yayi halifanci shekara 13 da wata bakwai cif a duniya jama'a da musulmi wadannan kadan daga abubuwan da zamu fadi kenan na abubuwan da muka alkauranta muku cewa jihadin dan audio ba hawan daushe bane wannan itace sunan littafin da na shirya har na shirya irin ta da turanci sai mun samu lokaci zamu tafi Kaduna
[Segment 6/6 | 01:40:00–end]
[Speaker seg6-spk:0]
A tare yan boko a arewa haus gidan sarauta Gabatar da ita da turanci Don wannan aiki ne suka baro saboda in muka shiru sun lalata tarihi Duk shekarar da ta kewaya zasu ce suna murnar Jahar nan hudu ya shekara dari biyu da daya Su ta gudu akan da wa kai suna zufa Su dawo su cinye abincin mutane su ce sun dawo daga jihadi A ji karya Yan boko su yi tattara kudi suna neman taimako suna ta cutar mutane Wannan ba da haka zaku raya ba Yanzu jama'a ina matsayin mu game da waccan da'awa da shehu yayi Ina muka kwana ina zamu tashi Ba wani abu bane Da zan maimaita in bata mana lokaci Abubuwan da na fada a wuri wa'azi a saurara jama'a suna da yawa akwai wata magana mai muhimmanci wadda ake kanta a zamanin nan ina so in cika da ita insha Allahu Sannan da wata sanarwa mai muhimmanci ku saurare ta da kyau Wannan ainihin Maganar da zanyi Ita ce wannan lacca ta kare A gobe a saurara ga sanarwa jama'a A gobe muna gayyatar ku wata kasaitacciyar lacca Irin wannan ce Amma kuma da wani sabon salo da wani sabon take Wannan laccar a tudun wada za'a yita A tudun wada a markazus salafiyya Yanda yan salafawa kenan Karfe takwas ita ma zuwa iwar haka insha Allahu Taken laccar Ta su'a da ashura Ranan ko azumi ibadar Allah Ba ranakun bidi'a ba Ko kuma zagin magabata Ta su'a da ashura Ranan ko azumi ne Ba ranakun bidi'a ba Ko kuma ranakun zagin bayin Allah Jama'a gobe tara ga wata Gobe tara ga wata Gobe ta su'a Wanda ya samu iko mustahabbi ne yayi azumi Jidi goma ga wata Wanda ya samu iko ya dauki azumi mustahabbi ne Annabi yace yana kankara zunubin shekara daya da ta gabata da shekara daya da zata zo To meye tarihin wannan azumin Meye tarihin ai abubuwa da ake na bidi'o'i a cikin wadannan ranaku Sannan Yan shi'a suna cika titi suna zagayawa annabi sahabbai To gwamnati karka manta Yan shi'a kuma karka manta Mun fadi magana muka ce Bana A yi Saki a zagayawa annabi sahabbai Yauwa sai dai ku zagi bush Da yaron bush Karami da babba Amma kar a zagi sahabban annabi Abubakar bai ci bai sha ba kar a zage shi Mu'awiya bai ci bai sha ba kar a zage shi Yazidu bai ci bai sha ba kar a zage shi Ina malaman kungiyoyi da suke cewa ana zagin sarakunan gargajiya suna kai kara fada To yan shi'a ai suna zagin sarki a wani lokacin shine sarki Yazidu shima sarki ne ai In da gaske kuke nan ma sai ku kayi Saboda haka wannan lacca gobe kasaitacciya ce jama'a bata gaza ta yau ba Akan azumin ta su'a da ashura da bidi'o'i da ake na al'adun gargajiya da kuma zage zagen da ake wa sahabbai shine zamu yi cikakkiyar lacca a kai mu wayar wa da mutane kai Ya haka yayi wannan lacca insha Allahu ta'ala a gobe Zamu dan bada hoto kwana daya ko biyu a dan tsahirta kadan a goban zamu sanar da ranar da za'a yi wata lacca a nan tudun wada kuma Ita kuma taken ta Zai zama ainihin wate Aure bautar ubangiji Aure bautar ubangiji gwabare Magana mai muhimmanci a ku tsaya jama'a akwai wata danya a kasa Allurar riga kafi Allurar riga kafi jama'a baza muyi shiru ba Allurar polio Ku bamu minti goma Minti goma baza ya isa eh Jama'a kuna ganin wasu ma'aikata a saurara Kuna ganin wasu ma'aikata Da wata figaggiyar riga Suna yawo gida gida suna kwankwadawa yayan ku wani magani Ko kun san wannan maganin karya suke ba maganin allurar riga kafi bace Duk wani malami da ke fitowa yake magana Ace ni albani namu kabalance shi cewa karya yake yana magana ne da jahilci bai san abun da yake fada ba Wato kun ji abun da yake faruwa jama'a Cututtuka ne ake so a dasawa mutane a jika in sun girma su tashi Sai aka pake da wasu cututtuka da suke yawan damun jama'a Ana cewa an kawo musu maganin riga kafin su tun gaban su Irin wannan allurar irin ta ce aka yi wa yara kanana Da sunan lamba in baku manta ba lokacin muna primary Lamba da ake a zo a kafa maka wani abu kicket A hannu Ta wannan hanyar suka ainihin yada ainihin ciwon kanjamau da ake fama da shi a yau Karya suke ciwon kanjamau da ke yawo a yau a kasashen Africa Ba wai ya yadu bane ta hanyar zinace zinace kamar yadda suke fada Wannan ciwo an zauna an kire kire shi ne a cikin dakin bincike a America Amma ya aka yi yafi yawa a ainihin Africa A Africa kuma ya aka yi yafi yawa a kasashen Africa ta kudu da sauran kasashen gabashin Africa Ah Ana yaudarar malaman musulunci da aka san cewa basu san boko ba Sai a je a ce malam meye hukuncin riga kafi To akwai bambanci tsakanin maganar hukuncin riga kafi da hukuncin waccan allurar riga kafi da ake magana maganganu biyu ne ake Riga kafi a musulunci in bukata ta kama za'a iya yin wa cuta magani kafin ta auwama Ku karanta littafin Ana iya wa cuta magani wadda ake zaka zaka Babu laifi akan haka To mu abun da muke cewa yanzu Ba riga kafin muke magana ba wannan maganin da kuke diga wa yara ne bamu yarda da shi ba Guba ce kai da aka baka ka sanar da dubu biyar Wannan wai har wani wai ya je wai bai same ni ba wai ya zo ya wayar mun da kai Wai ya zo ya wayar mun da kai shugaban su nan jahar Kaduna gaba daya ya zo wuri na wani doctor Da ya zo wai shigo office ya zauna ya zallita dafe haka sai ya rude yace to ko da yake ma dai ni dama na zo ne in dai baka tarho lambar tarho dai ko kana neman karin bayani Nace ah amma an aiko cewa zaka zo gashi gashi za'a yi bayani kaza kaza kaza kaza Yace ah to ai tunda naga kai mai bincike ne shine dai naga ba sai mun tattauna ba dai ga dai lambar waya ne Kin gani Sun daina malaman mu ne Da su dan boko wai da ya ji ka iya Arabiya sai ya dauka wai shi kadai ne ya iya boko ba Na ga sai maka turo ko Abun da muke cewa shine Tsakani da Allah Malamai da ake tambayar ku kuke bada amsa Zan fito kararan fada To sunusiyyun gunguba bai san physics ba bai san chemistry ba bai san biology ba bai san Daran sai ya je ya karanta na akida Don haka kuna jin gashi nan ya karanta Kuna jin karatun yadda ake katarar makatarar Yaushe za'a ce wai sunusiyyun gungume zai fito yace wai ba komai wai kuma mafatawar sunusiyyun gungume ita ce za'a bi akan wannan Me zai fada akan wannan an cuti musulmin na Kwararrun likitoci da malamai sun je sun yo bincike a kasashen musulmi na Pakistan da sauran su sun dawo sun tabbatar da cewa allurar riga kafin nan tana cike da cutar wa An sa abun nan a BBC an sa abun nan a jaridu a hannu na nan a kalla jaridu guda uku ne Akan irin wadannan maganganun wanene Duk an tabbatar da cewa abun nan yana da cuta Amma kuna ta fitowa an hada kai da sarakunan gargajiya an kwashi wasu sarakunan gargajiya wai an tafi da su za'a je wai za'a sake bincike Wadannan sarakunan in an je su ce me Koda sunyi science suna secondary school ko kuma sunyi suna wata makaranta da suka tafi kwasa kwasan su da suke yi Yanzu duk sun manta formula saboda an daura kan zufa ta sa formula ya yi yawa An dauki sarakunan gargajiya a je a ce musu me In aka ji aka ce in aka ce musu babu guba sai su dawo su ce to bayan gansu wa babu guba Takalidu takalidi Takalidu takalidi an taba haka Su su buturawa malum bisu To kamar yadda wani ya text zuwa ga BBC rannan abun da muke cewa sarakunan da suka tafi karbo bayani Mu dai bayanin farko da aka yi ya gamsar da mu Amma in sun karbo su yi wa yayan su allurar riga kafi da bayin su da barorin su Amma kar wanda ya damu shi da gidan shi aka yi wa yayan shi riga kafi daya kenan na biyu Abun da yake ba da gaske ne Sarakunan nan aka yi ta maganar shari'a baku fito kun goyi baya ba Baku fito kun takarfafa ayi shari'ar musulunci irin takakan ku dan hodiyo ba Sai yanzu ne zaku fito ku matsa mana akan riga kafi riga kafi me zai amfani mu A dibi kudin riga kafin ko wata anguwa a gyara musu titi mana Ku duba muciya titi yafi karfin arzikin mutanen muciya can ga wani kwari can Duk wanda zai shigo muciya sai ya fada cikin shi gashi nan damuna tana ketawa Shikenan za'a fada kwari damuna tana kama duk dan muciya ya san shi Gashi nan zaka yi magana sai ka bi ta cikin sai dai in baza ka shiga muciya ba Allurar riga kafin da za'a yi wa muciya a cike wannan ramin mana mangala goma sha biyar ta isa ta cike Baza kuyi haka ba Sai ku zo kuna kwankwadawa yayan mutane guba A bara waccan yau shekara uku da suka wuce Gwamna ya fito yace wai malamai sun an zan kurege Wai suna magana ba tare da ilimi ba Suna cewa allurar riga kafi guba ce To muna gayawa gwamna sai dai irin malaman ka wadanda basu san komai game da rayuwa ba iyakar su Arabiyya suka sani kawai abun da aka gayawa musu shi za'a fada Amma mu ba kanzan kurege muke ba shi yasa ku nemi kaset din mu na tamanin da daya Karatun sarimul battar mun maida raddi ga maganar gwamna Wannan maganar da muke fadi ba kanzan kurege bace Idan tayi zafi a Zamu gabatar da dalilan da muka sa ta sa muka ce allurar riga kafin da ake An hada kai ne da ku za'a cuce mu baza muyi shiru mu bar ku cutu al'ummar mu ba Saboda kuna son kada George Bush ya zo ya yake ku ya kifar da gwamnatin ku Baza mu yarda ba don haka a bijire a buga takardu a yi ta aikawa kauyuka a yi ta zuwa kauyuka a ce kar ku sake ku yarda Yan boko ne da yan siyasa Suka daure wa turawa gindi zasu cuce ku Sannan munafukan kiristoci sun fito suna cewa wai su ba komai ba komai don ace wai su basu hadin kai ne Wanda duk rahotannin da jaridar Weekly Trust take bugawa sai ta fitar da maganganu daga manya manyan hamshakan su Ka samu jaridar Weekly Trust ta ainihin sha takwas zuwa sha hudu a ainihin wannan sha takwas zuwa sha hudu Na watan November shekarar bature da ta gabata A cikin shafi na biyar Sai da suka yi cikakken rahoto akan sharri da illa allurar riga kafi Ga ta ga maganar nan Sannan har yau jaridar Weekly Trust Wanda ita ce ta ainihin volume na shida lamba ta arba'in da hudu Waccan din dai da na fada gashi nan suka ce polio vaccine opposition vindicted anti pregnancy agent identified A karkashin wannan jaridar aka tabbatar da cewa an tabbatar da allurar riga kafi tana cutar da yaya da ciki tana cutar da mata masu ciki Har aka yi ta kawo misalin abubuwan da suka faru a wasu ainihin kananan hukumomi a Daga karshe yan boko Yan boko ko da ake huda ku tashi ku dinga bincike in ba haka ba wallahi ku kade Za'a ta gayawa muku karya mu zo mu tona asirin ku Duk wanda yake da access zuwa ga internet ya je ga wani site ya je ya duba ya gani zaku ga sharri da ke ga allurar riga kafi da kan ku ba ni zan gaya muku ba In wannan na fada ne wannan a dakin ka ka je ka duba www.thinktwice.com/secret.htm Zan maimaita www.thinktwice Ma na shi think twice kayi tunani sau biyu Sunan website din kenan bari in bari in yi spelling th i n kt w i c e dat com slash secret s e c r e t dat h Bari in fada h h t m Wannan shine website din ku je ku duba zaku ga cikakken sharrin allurar riga kafi In baka in baka da access da internet ka tafi binciken center naira goma sha takwas da naira dari da talatin ne zasu baka ka hau awa daya ko kuma in ba haka ba ka basu wannan website din ka ce da Allah ku fitar mun da wannan ku min saving a jair printing ka je ka samu Kowa zai iya zuwa ya samu Wannan website din su ne Allah ya kama su suka gano sirrin duk sharrin da suka kulla a ciki su suka rubuta gashi www.thinktwice.com/secret.htm Duk sharrin allurar riga kafi yana ciki Kuna nan kuna cewa malamai su yi wa'azi sai dai malaman ku da kuke ba zakka koro zakka fidda kai Da gerar ku na azini Da ragon layya da kujerar haji amma wallahi mu malamai ne masu zaman kan mu Bamu a karkashin kowa kuma bamu cin tuwon kowa kuma bamu da mai gida ba wata kungiya kuma da take karkashin mu ba wani malami da yake shine sarkin mu Muna zaman kan mu ne duk abun da ya zo gaskiya ne wallahi zamu fada kuma baza mu bari ku cutar da al'ummar mu ba domin mu muna nan muna karatu ne kadai don addinin Allah kadai ya samu su koro Amma don me za'a hada kai da ku a dinga kashe mutane Muna nan suna cikin wahala kun ji ku tausaya musu Muna nan sun shiga cikin kunci Yanzu duk sanda aka ce shugaban kasa zai yi jawabin karshen shekara duk dan Najeriya damuna na yake yanzu kuwa gaban ka sai ya fadi To wane bala'in kuma za'a fada Muna zaune wai makaranta sai aka ce to dubu biyar da kuke biya Ya koma dubu hamsin Irin ranan a yau nan na ce wasu na ce wallahi tayi kyau Ya ce in za'a fada haka na ce tayi kyau Dubu hamsin na ce tayi kyau na ce ba ilimi bane na ce muna da kudin da zamu biya yo in bamu da kudin na ce ba ku ku saka musu kuri'a ba Sanda muka zo muka ce ku saka ku saka musu kuri'a me kuka ce Ya kuka yi da To ba shikenan ba kuma yanzu kowa ya shigo uban shi mun muna da Wallahi ni ina da kudin da zan biya kudin register ko dubu dari aka sa register a makaranta wallahi zan biya Abun da ya shafi ni Ina da kudi nan da shekara goma in zan yi makaranta ina da kudin da zan yi abun da ya shafi ni Zalunci ai yanzu wani dan sanda ya tare ni a hanya a Abuja za'a shiga Abuja na nuna mai takardar mota komai ya ce wai sai na bashi wani abu na ce ko kwabo Wai wani zai tausaya musu ba ba albashi na ce kadan ma kenan Me yasa na ce ga kun ba mai gidan mu Wannan bindigar taku ba da ita aka yi amfani aka murda mulki ba Na ce to da kun bari an ba mai gidan mu da kowa ya samu albashi waye mai gidan ku na ce Buhari To go mai wandon Na ce albashi yanzu baza ka fara Don haka yanzu ma ana wata ga wata ga wani zaban ya zo in za'a ku sake zaban su su sake ci muku to Mu dai zamu fadi gaskiya a yi ta zagimu mu yi taAnnotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Jihadin dan Fodio... Daarul Hadeethis Salafiyyah, 2004. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15868.
Zaria, M. A. A. (2004). Jihadin dan Fodio... [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15868
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Jihadin dan Fodio... Daarul Hadeethis Salafiyyah, 2004. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15868.
Télécharger
Visualisations
Chargement des visualisations…


