document audiovisuel · Daarul Hadeethis Salafiyyah Citer
Hadisai 100
- Type
- Enregistrement vidéo
- Créateur
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Editeur
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- numéro
- 1
- 2
- Est une partie de
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Importance matérielle
- 200 minutes
- Support
- DVD
- Sujet
- Hadith
- Langue
- Haoussa
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000017
- contenu
-
[Segment 1/11 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Godiya ta tabbata ga Allah muna gode mishi muna roƙon Allah ya taimake mu. Allah ya ƙara tsare mu daga sharrin kawunan mu da miyagun ayyukan mu. Wanda Allah ya shiryar babu mai ɓatar da shi wanda kuma ya ɓata babu mai shiryar da shi. Ina shaida babu abun bauta da gaskiya sai Allah shi kaɗai bashi da abokin tarayya. Kuma lallai annabin mu Muhammad bawan Allah ne ko manzon Allah ne. Allah ya daɗin tsira gare shi da mutan gidan shi da sahabban shi da waɗanda suka zo bayan su da kyautatawa har zuwa tashin alƙiyama. Ƴan uwa musulmi masu kallon mu da sauraron mu. Da waɗanda za su kalle mu su saurare mu ta hanyoyin yaɗa bayanai na zamani. Kuna sauraron mu ne daga masallacin juma'a na Muciya. Da ke sabon gari. A Zaria jihar Kaduna a Najeriya. A yanzu safiyar asabar ce wadda ta dai dai da. Safiyar ashirin da bakwai ga watan Shawwal hijra annabi na da shekara dubu ɗaya da ɗari hudu da ashirin da tara. Wanda ta dai dai da ashirin da biyar ga watan Oktoba shekara ta dubu biyu da takwas. Wannan ainihin karatu ko wa'azi da kake saurare ko kake kallo shine na farko. Wanda za a fara a yanzu bayan ƙaramar sallah kamar da muka yi mata alƙawari. A wannan ainihin wato masallaci namu. A ƙashin gaskiya saboda Allah. Littafi ne daga cikin littattafai waɗanda suka tattara hadisan annabi guda ɗari ingantattu daga cikin WandaLire le texte intégral — 21 785 mots restants Réduire le texte intégral
wani babban malami a ƙasar Makka. Shugaban makarantar Wadda take ainihin wato kan shari'ar Mansur a Makka. Mai suna Ya rubuta wannan littafi. Wannan littafi. Hadisi ne guda ɗari ya tara dangane da akida da kuma tauhidi. Shine zamu fara karantawa a yau. Haka gobe ma zamu karanta shi in Allah ya so. To sannan sai kuma ƙarshen wata. Duk asabar da lahadi na ƙarshen wata zamu riƙa taruwa a wannan wuri domin karatun wannan littafi da mata insha Allahu ta'ala. Muna roƙon Allah maɗaukakin sarki Allah ya taimake mu. Malam yace shimfiɗa. Malam yace Godiya ta tabbata ga Allah godiya mai yawa kamar yadda Allah ya umarce mu. Ma'ana Allah maɗaukakin sarki ya umarce mu a wurare da dama a Qur'ani. Daga ciki akwai inda yake cewa Kace To muna godewa Allah godiyar mai yawa. Kuma Allah maɗaukakin sarki yayi shela. Ya sanar da cewa. Duk wanda ya godewa Allah maɗaukakin sarki ya yaba da alherin da Allah yayi mai to Allah zai ƙara mishi. Haka abun yake. Ina godewa Allah. Godiya wadda take ba a iya kance ta kuma ba a ƙididdige ta. Allah shine guda ɗaya wanda ake nufi da buƙata kowa ya tashi buƙata wurin Allah yake nufi shine ma'anar Allah shi ya cancanci yabo. Da kuma ainihin girmamawa. Allah ya daɗin tsira ga annabi Muhammad. To bayan haka. Malam yace To musulmi ga ka dai a matsayin ka na musulmi. Ga kuma maganar annabin ka Wannan shine annabin ka Muhammad Maganar annabin ka ita ce addinin ka ma'ana ba zaka yi addini ba sai abun da annabin ka ya faɗi. Shi annabin naka. Baya furuci baya magana ta son zuciya. Duk abun da yake faɗi to wahayi ne aka yi mishi. To ko tunda haka ne me yasa ba zamu riski wannan sunna ta annabi ba. Wanda take da haske. Wanda take ita ce tsira. Ita ce shirya. Ma'ana in dai mun yadda cewa maganganun annabi sune addinin mu me yasa ba zamu je mu neme su mu yi aiki da su ba sune tsira sune shirya. Duk wani hadisi. Shi ibada ne duk wani hadisi da kake gani. Karanta shi da aiki da shi ibada ce. Shi ko mai aiki da hadisin manzon Allah to kullum yana cikin ƙari ne game da alheri yana ƙaruwa ne game da alheri. Kuma yana cikin ɗaukakar sha'ani Allah zai riƙa ɗaukaka shi. Kuma zai riƙa samun haɓaka da bunƙasa. Ita ce maganar da tafi kowace falala. Bayan maganar Allah ma'ɗaukaki. Don haka kau da kai. Da kuma mantawa ko kuma sakar cewa ko watsi da sunnar annabi Waɗannan bala'o'i ne guda biyu a ce mutum ya kau da kai. Ya zama ɗan ba ruwan mu game da sunnar manzon Allah To bala'o'i ne guda biyu daga cikin manya manyan bala'o'i. Kuma ƙasƙanci ne guda biyu Daga cikin ƙasƙanci mafi girma a ce kana rayuwa a duniya ba ruwan ka da manzon Allah A ce kana rayuwa ka kau da kai game da manzon Allah. Kana rayuwa kana ganin cewa baka buƙatar abun da manzon Allah ya zo da shi to ka shiga ƙasƙanci da bala'i kada Allah ya nuna mana. Yace to ya kai ɗan uwa na. Ga wani abu na daga cikin sunna ta annabin ka ina miƙo maka. Mafi yawancin wannan sunna waɗannan hadisai. To mafi yawancin su a cikin ainihin akida ne. Gaskiya kamar yadda malamin yake cewa Mafi yawancin hadisan nan sun zo ne akan akida. Kuma malamin ya nemi maka tayi ne dangane da ka zo ka karanta su kuma kayi aiki da su. Kuma hadisai ne masu amfani. Don haka kayi gaggawa wajan haddace waɗannan ainihin hadisai. Kayi gaggawa wajan sa iyalan ka da kake riƙe da su suma su haddace domin Shine nauyi waɗanda kake ɗauke da nauyin su. Iyalan ka ma da kake ɗaukan nauyin su kayi gaggawa wajan ka sa su haddace. Malamin ya sa an karanta wannan littafin gaba ɗaya a karantawa zalla babu fassara. Kuma tun bara na karɓo tare da littafin. Muna son sai mun gama karanta littafin zamu zo muku da wannan a buga shi ko wacce ta je tana karantawa. Tana ainihin saurare ana karantawa ta haddace. Domin ya bamu dama za a zo ayi gasa ta haddar wannan littafi. Kuma yace zai ayi ko da kyauta mai tsoka to. Malami ne babban malami a Makka. Kuma Allah ya azurta shi. Da ainihin dukiya mai ɗimbin yawa. Yanzu haka ƴa'yan Hausawa ya kafa wa makaranta a Makka. Mafi yawancin ƴa'yan makarantar ƴa'yan Hausawa ne na Makka marayu. Waɗanda iyayen su sun rasu. Suna watan gaririya a titinan Makka sai ya je anguwar Hausawa a Makka sai ya gina ƙatuwar makaranta wajan aji talatin da bakwai. Ɗibo su ina karantar da su. Za tashi zaka tafi gida sai ya auno shinkafa tiya biyu tiya uku da kuɗi sai ya baka yace ka kai wa mahaifiyar ka. Malam Salih Allah ya saka mishi da alheri. To wannan ainihin malami yace to kai gaggawa wajan hadda wannan littafi da kai da iyalan ka. Ya zama kana da wani ƙwazo kenan Wanda ainihin wato ƙwazo na wajan yaɗa wannan littafi. Ta ɗulu sai ya zama kana da wani hannun alheri mai tsawo abun da yake nufi in ka haddace wannan littafin. Mai yawa ka zama hanyar da za a isar da waɗannan hadisai zuwa ga wani garin ko zuwa ga wata ƙasar saboda ka haddace. Shine sai kawo da yadda Larabawa yake cewa. Mai yawa ya zama kana da dogon hannu game da yaɗa wannan littafi wato ya zama kana daga cikin waɗanda za ka yaɗa wannan alheri. Kada Allah ya hana maka lada da sakamakon wannan aiki in ka yi shi ma'ana in har ka yi wannan aiki Allah ya baka lada kada Allah ya hana ka. Kuma in yi maka addu'a Allah ya datar da kai ka fahimci sunna kuma ka fahimci littafin Allah. Allah ya datar da mu da kai. Da kuma waɗanda duk suke taimakawa wajan buga wannan littafi. Don samun sakamako mafi girma shine Domin ita rayuwa. To dama fa wata ƴar sa'a ce guda gaba ɗayan rayuwar. To ɗan lokaci ne ɗan ƙarami. Don haka To kayi ƙoƙari ɗan wannan lokacin na rayuwa ka maida shi ya narki a ɗa'a. Yace ba zan manta ƴan uwa na mata musulmi ba. Domin sune iyayen gwaraza. Gwarzo. A Larabcin aka ce Ma'ana yana so ya muku addu'a ne ko mata cewa duk inda aka samu wani gwarzon malami ko kuka haife shi. Inda aka samu wani gwarzon shugaba ko kuka haife shi duk inda aka samu wani ko wanene a duniya wacece ta haife shi. Mace. Don haka mawaki yake cewa. Duk ɗan da mace ta haifa ko mai tsawo da wata ran ka ga an ɗauko shi a makara abun da wannan maganar take nufi dai. Bayan da malam ya gama addu'a ga dukkan al'ummar musulmi sai yace ba zai manta da iyaye mata ba domin su iyaye mata sune iyayen da suka tsuguna suka haifi duk wani jarimi. Kuma su mata sune masu kula masu ainihin taka tsantsan da tsare addini. Yace haka ƴan uwa na samari suma ba zan manta da su ba. Allah maɗaukakin sarki shine mai datarwa kuma Allah shine mai taimakawa. Mai buƙata zuwa ga ahuwar ubangijin shi shi ya rubuta wannan magana kuma mai buƙata zuwa ga gafaran Allah shine Da ya haifi ɗan shi ƙwaya ɗaya raƙ a duniya sai ya sa mai sunan baban shi don haka Allah ya taimaka. Ya fara da hadisin farko hadisin niyya wanda Na so a ce duk mutumin da zai fara rubuta littafi a duniya to ya fara da wannan hadisin. Domin ya nuna cewa duk aikin da kayi in baka sa tsarkin niyya ba Allah ba zai taimaki aikin ba. Wannan hadisin in karɓo shi daga Umar ɗan Khattabi Allah ya ƙara mishi yarda Manzon Allah yace Lallai dai ayyuka da niyyoyin su suke tafe. Ina ma'anar wannan maganar idan kin tashi yin abu don Allah niyyar ki da kika yi ta don Allah sai Allah ya baki lada. Idan abun da ake yi don Allah ne sai kika yi ba don Allah ba sai Allah ya hana ki lada ranar alƙiyama sai ya tattara masu irin wannan aiki sai ya ce to ni ina da lada ne ga wanda yayi abu don Allah ga wanda yayi ba don Allah ba ko sai ya tafi wurin wanda yayi domin shi ya biya shi. To wannan rana rana ce ta ainihin hadari ƙwarai da gaske saboda haka duk abun da zaki ki sa tsarkin zuciya ki sa tsarkin niyya sai ki ga Allah ya albarkaci abun. Sai yake cewa Wanda hijran shi ta ƙasance ya tafi ne zuwa ga Allah ya tafi ne zuwa ga manzon Allah To lallai hijrar tashi ta tabbata ga Allah kuma ga manzon shi kamar yadda yayi niyya. Wanda ko hijrar shi ta ƙasance saboda duniya ne don ya samu duniya. Ko don ya auri wata mace. To hijrar shi tana nan zuwa ga abun da yayi hijrar zuwa gare shi. Wannan hadisi malamai nau'i biyu suna amfani da shi a cikin littattafan su. Nau'in farko na malamai sune malaman tauhidi da tazkiya. Sune malaman da ke wa'azi akan a bautawa Allah kar a bautawa kowa bayan shi. Malaman da suke cewa duk abun da zaka yi kayi don Allah su in suka kawo wannan hadisin suna nufin duk abun da zaka yi ka kyautata niyyar ka ta zama saboda Allah. Nau'i na biyu na malamai da ke kawo wannan hadisi a cikin littattafan su sune malaman Su ko suna kawo shi ne don su nuna cewa niyya ana amfani da ita wajan bambance ibada misali sallah a zahar raka'a huɗu ce sallar la'asar ma raka'a huɗu ce. Assirrance ake karatun sallah a zahar la'asar ma assirrance ake yi duk abun da sallah a zahar take da shi shi sallar la'asar take da shi to kenan me bambanci tsakanin sallah a zahar da la'asar niyya to malaman suka kawo wannan hadisin suna nufin bambance tsakanin ibadoji. Don haka sanda Imam al-Bukhari zai kawo wannan hadisi a babin alwala sai ya sake maimaita shi a babin wanka sai ya sake maimaita shi a babin abun nan misali sallar juma'a me yake nufi idan zaka yi alwala sai kayi niyya in baka yi niyya ba alwalar da kayi ta zama ƙwaskwarima ta zama wanke jiki kawai. Idan ka zo wankan janaba in baka yi niyya ba ba zai bambantu daga wankan jin daɗi ba idan kika zo wankan haila ba zai bambantu daga wankan janaba ba sai in kinyi niyya don haka niyya ana amfani da ita a wurin malaman wajan bambance ibada. Niyya a wurin malaman tauhidi su kuma a nuna cewa duk abun da zaka kayi niyya cewa Allah ya baka lada. An yabe ka ko an zage ka ba zaka damu ba. Ka samu ainihin buƙatar da kake buƙata a wurin mutane sun bi ko ko sun ƙaryata ba zaka damu ba saboda niyyar ka saboda Allah ce. To alaƙar wannan hadisi da wannan karatun da muke shi ne kar ku manta muna magana akan tauhidi ne kar ku manta muna magana akan akida ne. Kenan wanda duk zai yi wani abu don Allah to ya tabbatar da cewa bayan yayi ƙoƙarin kyautata abun dai dai To yayi ƙoƙarin fita daga siffofi guda uku waɗanda suke rugurguza aiki siffar farko ita ce shirka. Cewa wannan abun da kake yi yadda kake yi wa Allah haka kake zuwa kake wa wani wanda ba Allah ba. To kar kayi haka ya zama Allah kaɗai kake wa. To in kuma Allah kaɗai ɗin kake wa kada kana cikin yi. Sai ya zama in ƙira'a ce kana ɗaukaka murya kana gyara murya don mutane su ji su ce ka iya to an samu kenan kana so a ji. Riya sallah ce in kai kaɗai zaka yi zaka yi fača fača amma a gaban mutane ne zaka tsaya kayi ta kyakyawa kenan kana yi ne don mutane su gani. Dukkan mutumin da ya bari ɗayan waɗannan siffofi suka shiga cikin aiki shi to aiki ya lalace. Da riya da shirka duk abu ɗaya ne sai dai ana cewa riyar shirka ne ƙarama saboda an gwada ta ga Babban shirka amma da riyar da shirka ɗin duk abu ɗaya ne shirka ce. Kenan duk abun da zamu yi mu yi don Allah.
[Segment 2/11 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
Abinda kai dan Allah shine Allah madaukakin sarki yake baka lada, kuma shine Allah yake sawa wa albarka ya barshi a duniyar nan. To dai kun ji dalilin fadin wannan hadisi kamar yadda malamai suka bayyana, lokacin da Annabi ya dawo ainihin Madina sai aka dinga samun matsala. Mutanen Madina suna da alheri su baka gida su baka jali su kawo mata su baka su kawo gona su baka a kai ka kasuwa a baka rumfa, a kawo jali a baka, da ka ce wash sai mutum kaza sai su taso kanka me ya dame ka? Wannan irin hidimar sai ta sa aka samu yan duniya sai suka shiga musulunci ba dan Allah ba, dan in sun zo Madina za su samu mace, za su samu gida, ga gona, ga jali, wannan sai zan ba dan Allah suke ba, to sai abun ya fara yawa. Wani kuma yana da budurwa ne ya fara neman ta sai ita ta musulunta, sai ya ga in fa bai musulunta ba to in ta tafi Madina shi kam yayi asarar ta, sai ya taho Madina ba dan Allah ba, sai dan ita shine Umar yace sai manzon Allah ya hau kan minbari ranar Juma'a yayi wa'azi ya fadi wannan hadisi cewa wanda duk yayi hijira dan ya samu duniya ko dan ya auri wata mace to in ya samu macen ya aura ko yayi wannan hijira dan duniya ya samu duniyar to iya rabon shi kenan a lahira ba shi da rabo. Wanda ko yayi hijira saboda Allah ya tafi wurin Allah yayi hijira zuwa ga manzon Allah ya tafi Madina wannan mutumi ko da a hanya ya mutu bai kai Madina ba Allah ya tabbatar mishi da ladan shi. To sai hadisi na biyu malam yace Abu Huraira Allah ya kara mishi yarda yace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace Allah madaukakin sarki yace Daga cikin duk mutane da ake wa shirka da sauran halittu da ake bauta musu ake hadawa da ni Allah yace to gaba dayan ni nawa da ta daga shirka. Wato idan wani gunki zai yarda a bauta mai a je a bauta wa wani idan wani da ake bauta wa zai yarda a bauta mishi a hada da wani sai Allah yace to shi bai yarda ba, ko dai ayi mai bauta shi kadai ko kuma to in har sai an hada shi da wani to ya bari baya bukata. Don haka yace daga cikin wadanda ake bauta wa ana hada su da wasu sai Allah yace to shi ya wadata, baya bukatun ibadar da za a hada ta da shirka. Wanda ya aikata wani aiki ya hada wani na da ni a cikin wannan aiki zan barshi da shi da shirkar ta shi. To daga ran da aka ce Allah yace bashi baka to ka kade. Daga ran da aka ce Allah yace ya barka da aikin ka kaje can ka kara ta, kaje can wanda ka hada da Allah ya biya ka shi Allah baya so to shikenan ka gama asara. Allah ya kiyaye. Al-Imam Muslim ya ruwaito wannan hadisi. Wannan hadisi yana fada mana hadarin da ke tattare da shirka da kuma muhimmancin da ke tattare ga dayan ta Allah shi kadai bai da abokin tarayya. Hadisi na uku Daga Anas Allah ya kara mishi yarda yace Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace Imani yana da rassa guda sittin da wani abu, abinda ake kira shine abinda kake dorawa akan lissafi ba tare da ka ambace shi ba, shine kace goma sha wani abu wato baka fadi yan kan ba ashirin da wani abu baka fadi yan kan ba to shine Laraba sai su ce Imani yana da rassa kamar yadda kika ga bishiya take da rassa rassa rassa haka, to haka imani gashi nan bishiya ce guda daya amma yana da rassa wadanda ake bi a tabbata a kan shi har guda sittin da wani abu. Mafi daukaka daga cikin kalmar imani Daga cikin rassa na imani mafi daukaka reshen da ya fi kowanne sama shine na kasa wanda ke kasa mafi kasa daga cikin rassan imani shine Kawar da abinda ke cutar da al'umma daga kan hanya sai manzon Allah kunya reshe ce daga cikin rassan imani Allahu Akbar. Wannan hadisi ya tabbata kamar yadda malam yace da Muslim suka ruwaito shi. A cikin wata riwayar Annabi yace rassa saba'in da wani abu, gashi nan ko ita ce na tsallake yanda yace A wata riwaya aka ce rassa saba'in da wani abu ne, wannan riwaya ma ita ce ta fi karfi da nagarta. Ina son ku tsaya ku fahimci hadisin nan da kyau ku duba nayi sharhin wannan hadisin a wannan wurin yau kusan shekara goma da ta wuce ko shekara takwas muna karatun Na dauko littafin Wani malami ne aka samu babban malami daga cikin manya manyan malamai da suka gabata yau fiye da shekara dubu daya Allah ya gafarta mishi. Wannan littafi wajen mujalladi ashirin da biyar ne. Shi wannan littafin yayi sharhin wannan hadisin ne kawai. Annabi yace imani kamar bishiya ce to ita wannan bishiya tana da rassa reshe reshe reshe. Reshe mafi sama shine me? Kenan duk mutumin da ya fadi ya yarda da ita to ya hau kololuwar reshe na imani. Wannan reshe ne kasa kasa shine kina tafiya sai kika ga fasashiyar kwalba a hanya sai ki dauke ta, in har kika yi wannan yana nuna kina da mafi karancin wannan imani, to in ya zama ga fadin ga yarda da ita, ga ganin cuta akan hanya ki dauke ta to kin hada imani kenan tun daga sama har kasa. Me zaki yi kokari? Sai ki yi kokarin sauran rassan kuma suma ki bi ki cika su. Saboda wadannan rassan da ake nufi ba wasu abubuwa bane ayyuka ne na musulunci, misali ciyar da miskinai reshe ne daga cikin rassan, yin sallama ga musulmi reshe ne daga cikin rassan, yin sallah reshe ne daga ciki, bada zakka ma reshe ne. Kenan in aka wayi gari musulmi yana ayyukan musulunci gaba daya to ya mallaki bishiyar imani kenan gaba daya. Abu na farko kenan. Wannan hadisin yana nuna mana daraja da falalar Na'am Allah ya kira ta a cikin Alkur'ani yace Yace ita ce kalima ta tsoron Allah, babu wanda yake iya fadin ta sai wanda yake da tsoron Allah. Abu na biyu wata rana Annabi Yayi wa dan shi wasiyya da ainihin fadin Aka ce abinda ya faru kuwa cewa Allah ya Allah ka karantar da ni zikiri wanda ya fi na kuwa, sai Allah yace ka dinga cewa Annabi Nuhu sai yace ya Allah aini ina son wani zikiri ne na musamman. Kowa ai yana fadin ta sai Allah yace mishi ai ka sani da cewa da za a rubuta a jikin takarda a tattara halittu tun daga na saman bakwai har na kasan bakwai har halittun da ke tsakiya a tara su wuri guda sai a dora akan To dake rubuce jikin takarda duk zata rinjayi halittun Allah. Kar ku manta ita ce kafiri yake fadi sai ya zama musulmi. Ita ce kalmar da musulmi zai fadi sanda zai rasu ya zama yana mutuwa ya cika da imani aljanna zai wuce kai tsaye. Manzon Allah Manzon Allah yace in mutum yace sai ya shiga aljanna ko yayi sata ko yayi zina, Abu Zarri yace Ko yayi sata yayi zina manzon Allah yace Ko yayi zina yayi sata manzon Allah ya maimaita Abu Zarri ya maimaita karo na uku sai manzon Allah yace Abu Zarri ko baka so mutumin nan sai ya shiga aljanna indai ya fadi Wannan hadisin ba ya daura gindin mutum yaje ya fadi yaje ya sata ne ko ya zina ba a'a, hadisin yana nuna mana Ina fata an gane. A cikin wani hadisi na Bukhari manzon Allah wanda ya shaida ba abun bautawa da gaskiya sai Allah kuma ya shaida Muhammad manzon Allah ne ya yarda cewa Isa bawa ne na Allah kuma rai ne daga cikin rayukan da Allah ya halitta, ya yarda da aljanna gaskiya ce, wuta gaskiya ce, sai manzon Allah yace sai ya shiga aljanna komai kankantar aikin shi na alheri. Duk karancin aikin ki na alheri indai kin yi imani da kin yarda aljanna gaskiya ce wuta gaskiya ce, kin yarda Isa cewa bawa ne cikin bayin Allah, halitta ne cikin halittun Allah, ba dan Allah bane, ba Allah bane ba wai dayan alloli uku ba, matukar kin yarda haka manzon Allah yace komai kankantar aiki sai mutum ya shiga aljanna. Sai wani hadisi yazo ya fassara manzon Allah yace sai yan aljanna sun gama shiga aljanna kakaf yan wuta sun gama shiga wuta kakaf sai ya rage saura wani mutum kwaya daya Duk duniya shi kadai ne shi bai shiga wuta ba shi bai shiga aljanna ba. Abinda yasa shi dai wannan mutumi ba shi da aikin alheri ko kadan. Balle ya shiga aljanna, ita ko aljanna sai da aljanna to shi bashi da abun alheri ko kadan bai taba aikin alheri ba. To ba zai shiga aljanna ba. Shi kuma bashi da wani aiki da ya aikata na sharri wanda zai kai shi wuta, don haka sai aka jepar da shi a a tsakar lahira kenan. A san sai Allah madaukakin sarki yace a je a ajiye shi tsakanin wuta da aljanna, in ya kalli aljanna ya hadiye yawu amma ba zai shiga ba, kun ga nan ma azaba ce. Ka ga da kwalanka aji sun soyu, ga yunwa saboda Allah, ka kalla a hara ka Sawa. Nan kuma in ya juwa ya kalli wuta kun ga nan ma musiba ce. To da yake Allah mai rahama ne sai Allah yayi mai izini yayi magana, ina son kusan lahira ba irin duniya bace. Manzon Allah yace Ranar lahira manzanni ne kawai suke iya magana, suma ba su rutu za su yi ta yi ba sai Allah yace suma kawai cewa suke Allah ya kiyaye Allah ya kiyaye Allah ya kiyaye basa iya fito fa wata magana. Duk wanda yace haji yayi mana hidima ranar alkiyama zamu kama hannun ki mu ke rike siradi rabu da shi kice a nan ka sai mun kati na JSM yafi mni kai mun wannan alkawarin. Ku duba a ranar lahira babu wanda ya isa yayi magana. Ga maganar da manzon Allah Kur'ani ya bayyana mana wannan maganar wuri daban daban daban daban cewa babu wanda ya isa yayi magana. Ba zaka yi magana ba sai Allah yace yi magana in ka tashi magana kuma sai Allah yace ga abinda zaka fada. To wannan mutumi da Allah ya so shi da rahama sai aka mai izini yayi magana can sai ya buda baki yace ya Allah kar ka sa ya zama ni ne matsiyaci cikin halittar ka, kowa ya shiga aljanna ni an bar ni a waje. Sai a ce me kake so? Sai ya ce arziki yake so ayi mai a juyar da fuskar shi ya kalli aljanna kawai ya daina kallon wuta. Sai Allah yace arzikin da kake so ayi maka kenan eh, in aka yi maka wannan arzikin ba zaka roki wani ba sai yace wallahi tallahi na rantse da gir, ba zan sake rokan komai ba in aka yi mun wannan arzikin sai Allah ya ce wa mala'iku ku juwa shi ya kalli aljanna ya daina kallon wuta. To in ya kalli aljanna manzon Allah yace hangi la gwada da bahaja ado dake ciki sai kuma ya sunkuyar da kai sai yace ya ubangiji sai Allah yace ya aka yi? Sai yace kar dai in zama ni ne matsiyaci cikin halittun ka. A kusantar da ni kofar aljanna kofar kawai sai Allah yace kai dan Adam ka cika yaudara yanzu ka gama rantsuwa sai yace ya Allah kada in zama ni ne matsiyaci a taimake ni. To in aka yi maka wannan ba zaka sake roko ba yace wallahi tallahi duk ya ci layin rantsuwa sai a ce a kai shi sai a kai shi kofar aljanna. To can kuma sai wasu wasi kenan to ni yanzu na ce ba zan sake rokan arziki ba yanzu kuma in sake roko to amma ya zaka yi kai bawa talaka ne Allah ne wadatacce to talaka ko menene don ka buda baki ka ce wadatacce ayi mun baka kaskanta ba ya Allah a shigar da ni cikin aljanna sai Allah yace dan Adam ka cika yaudara wato kadan kadan kadan kadan dan Adam wai Allah ma zai wa wayo a ranar lahira kadan kadan sai Allah yace a shigar da shi to yanzu ina son ku gane wannan mutumin manzon Allah yace bai taba aikin alheri ko amma a zuciyar shi ne aka samu akwai imani daidai da ya yarda da Allah dan wannan yardar da yayi da Allah da yake bai taba yin shirka ba sai Allah yace a shigar da shi aljanna, in aka shigar da shi aljannar Allah yace manzon Allah yace sai sai a ce dubi abinda kake so in ya fada sai a ninka mai sai a ce to ka manta kaza ka manta kaza ka manta kaza ka manta kaza, bayan an gama bashi aljanna hadaddiya sai Allah yace to an ninka maka so goma. Wannan bai taba yin sallah azahar ba ko talasar amin ba abinda ya taba ba sai dai bai taba shirka ba bai zalunci wani ba bai gulmar wani ba bai tsegumin wani ba yaje lahira bai da aikin alheri kuma bai da nauyin kowa a ka amma yayi imani da Allah sai Allah ya mishi wannan. Saboda haka gaskiya saboda Allah ku kiyaye wadannan rassa da ake magana sannan sai sai aka ce a ango ku ga wani kwatami wanda idan yara sun zo suna tanjamawa sai kice a je a samu kafin ta yazo yayi gada a wannan wurin. Wannan yana daga cikin kawar da cuta a a kina tafiya sai kika ga yara sun farfasa kwalabe sai ki tsaya a share kwalbar kina tafiya sai kika ga wata kusa mai yiwuwa wani ya taka da kafa ko da mota ko da babur sai ki cire sai kika ga wani reshe ya taho yana tara mutane, haka manzon Allah yace wani mutum yana cikin tafiya sai ya ga wani reshe yayo akan hanya haka sai ya tsaya ya karye shi saboda reshen yana kawo mutane cikas. Manzon Allah yace sai Allah ya gode mishi ya yafe mai zunuban shi sannan ya saka shi a aljanna. Abu uku Allah ya gode maka ya yafe maka zunuban ka sannan ya baka aljanna. Saboda haka duk inda kuka ga wani abu da zai cutar akan hanya sai a cire shi to wannan dalili ne na cewa kina da imani. Allah ya taimake mu sannan Annabi yace kunya imani ce wanene yake to godewa shi mara kunya ne, shi fitsaren rai ne, shi bai da kunya kamar yana cewa kenan bashi da imani. Saboda haka kunya daraja ce ya kamata lallai mutum ya zama yana da kunya domin siffa ce daga cikin siffofin mumini, Allah ya taimake mu. Malam yace wannan hadisi an karbo shi daga Abu Huraira Allah ya kara mishi yarda Abu Huraira yace manzon Allah yace wanda ya mini karya da gangan haka sddan ki sharbo karya ki danganta ga manzon Allah Manzon Allah yace sai ya tattali mazaunin shi a wuta. Karya ga manzon Allah rusa addini ce to wannan rusa addini kuma matsayi ne da ya tabbatar da mutum a cikin wuta kuma yin karya ga mutumin da yake mai daraja ba kamar yin karya bace ga mutumin da yake ba ya da daraja balle yin karya ga mutumin da yake maganar shi da aikin shi da rayuwar shi ta zama abun koyi. Idan kika yi wa Annabi karya kika gina wannan karya ta ginu wato mutane zasu zo suna bauta wa Allah da karya kenan. Amma abun mamaki fiye da shekara dubu daya da ta wuce bayan zamanin ta bai ayi an ta samu mutanen da suka maida karya ita ce hanyar samun cefa ne. Wani malami irin malaman bidi'a malaman gwamnati yazo wurin sarki Almahdi sai ya samu sarkin yana wasa da tantabara a hannun shi haka can sai malamin yayi shiru sai fadawa suka ce Allah gafarta malam yau ba za a karantar da sarki hadisai bane sai ya shiru yace to Annabi bai halatta ayi wasa da komai ba sai da ainihin kibiya sai da doki sai kuma wasa da mutum zai yi da tantabara. Sai ya fadi hadisi wanda asalin hadisin gaskiya ne Abu Dauda ya ruwaito shi Annabi yace ba a wasa da komai sai wasa na koyon harbi, sai wasa da doki sannan sai yace sai kuma wasa da tantabara. Yanzu kenan sarki ya shigo ciki
[Segment 3/11 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
Shine sarki ya kawo kyauta ya bashi, bayan ya tafi sai sarkin ya dubi kiyayen yace na rantse ga Allah wannan kiyayen makaryaci ya kiyayace kiyayen makaryaci ce. Shine malamai yace ai wannan kuskure ne tunda ya gano cewa makaryaci ne bai kamata ya dibi dukiya al'umma ya bashi ba. Karya ga annabi babu kyau. Wasu suna yin karyar ne dan me dan su burge matan su. Wani ne matan shi tana nakiya sai ya zama malami ne mai wa'azi, nakiya ai an san ai an san nakiya ko? To nakiya kuma in ta kwana za a samu matsala wani lokacin za ta yi tsami. To almuru tayi likis ga nakiya tayi kwantayi. Matan malami tayi ta sababi. Tayi ta sababi malam ya shigo ya same ta tana sababi ya akai tace nakiya bata kare ba in tayi kwantayi za ta yi kaza kaza kaza. Yace zaki sai da nakiya ki tace yaushe za a sai da nakiya almuru tana kara yi. Yace nace miki kiyi hakuri zaki sai da nakiya ki. Magariba nayi malam yaje sallah a masallaci kawai sai ya mike yana wa'azi, wa'azi yayi wa'azi can sai yace Ai manzon Allah yace nakiya tana maganin ciwon mara. Iye nan da nan sai mutane ina ba a samu nakiya da almuran nan aka shiga aka fita sai aka ce ai gidan malam akwai nakiya. Nan da nan nakiya ta kare ana wawasantama ana salati ba a samu ma. Yace ba na ce miki zaki sai da nakiya ki ba? Yanzu yayi wa annabin mu karya ne dan matan shi ta ta sai da nakiya. To akwai irin wadannan fitsararru suna nan da yawa. Har kullum kuma suna ta wadannan karya rayin dan haka malamai suka zauna suka tsara ilmomi daga cikin ilimin akwai ilimin hadisi, akwai ilimin wanda wannan ilimin shine ke taimakawa da ikon Allah wajen a gane ingantattun hadisai a gane wadanda basu inganta ba. Dan haka ya jama'a bashi daga cikin abin da yake daidai baki san tabbas ba game da hadisi kizo kina dangantawa ga annabi sallallahu alaihi wasallama. Wannan yana daga cikin kuskure duk littafin da kika san akwai hadisai masu rikici a ciki to ki samu wani malami ya tantance miki tukunna kafin ki karanta dan kake wayi gari kine wa annabi sallallahu alaihi wasallama karya. Kun dai ji in mutum yayi wa annabi karya tun a nan duniya ma ya samar wa kanshi sit. Kamar jirgin saman zaka shiga tun kafin ka shiga za a ce kaine lamba kaza. Tun kafin ka shiga tun kafin ka ga jirgin mai yiwuwa ma tun kafin ranar kasan cewa ga kujerar ka. Dukkan mutumin da yayi wa annabi karya a nan duniya to shima yayi wa kanshi lamba. Yace daga iblis to shine na uku. Kawai Allah ya kyauta da muslim suka ruwaito wannan hadisi. Wato yadda malamin yake yi yana tattara hadisan sahabi wuri guda ne yanzu ya ta kawo mana hadisai zaku je yana ta kawo hadisan abu huraira abu huraira abu huraira yana daya yana dan surkawa da na anas sai an tafi kuma zaku je yana kawo hadisan wasu ainihin daga cikin sahabbai kamar abu saidul khudri kamar aisha da makamantan su. Allah madaukakin sarki ya taimaka. Daga abu huraira Allah ya kara mishi yarda abu huraira yace manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace wanda duk yayi mun da'a to Allah yayi wa wanda duk ya saba mini to Allah ya saba wa. Jama'a kun ji doka. Duk wanda manzon Allah yace bari ya ki bari to ya saba wa Allah ya saba wa manzon Allah. Wanda duk ya ainihin wato yayi wa manzon Allah biyayya to Allah yayi wa ta'a. Allah yace wanda yayi wa manzo ta'a Allah yayi wa. Sai yace wanda yayi bi sarkin garin su ko shugaban garin su ko jagoran tafiyar su hakika ni yayi wa da'a ma'ana in aka ce kuna da wani shugaba a wata tafiya ce a wata kungiya ce a'a shugaba ne na gwamnati a'a sarki ne a'a dagaci ne ko hakimi ne a'a gida ne aka ce akwai wani shugaba amma aikata ce aka ce akwai shugaba makaranta ce aka ce akwai shugaba sai shugaban nan ya bada doka sai kika bi ko kabi dokar to wannan ainihin doka da kabi annabi sallallahu alaihi wasallama yace shi kabi shi kai wa biyayya. Amma mu san cewa sharadin shine ya zama ita dokar bata yi karo da dokar Allah da ta annabin shi ba. Kuma dokar ya zama an bada ita ne da nufin doka ce ta Allah ba wai doka ce aka bada ita ta san zuciya sai ta dace da dokar Allah ba. A'a doka ce da sunan musulunci da sunan Allah aka bada ita kuma ya zama ta dace da dokar Allah din. Misali yanzu sai mijin ki yace indai zaki fita a matsayi na na mijin ki mai gidan ki wanda nine shugaban ki da shugabantarwar da Allah yayi mini sai kinsa hijabi ke kuma sai kice a'a ado zaki chaba kisa gyale to yanzu wannan biyayya in kika daure kika yi mai to kinyi wa manzon Allah sallallahu alaihi wasallam dan biyayya ce da biyayyar Allah. Amma in miji yace sam yaushe yanzu zamu tafi yawo za a tafi abuja ko za a tafi kaduna garin yan bariki zaki dauko mana hijabi da nikabi ai sai dai ki tambala ado ki kawo gyalen ki yafa to anan sai kice a'a to in kika sake kika yi mishi biyayya a wannan halin to kin ainihin wato sabawa manzon Allah sallallahu alaihi wasallam. Manzon Allah yace duk wanda ya saba wa shugaban shi to ni ya sabawa. Muttafakun alaihi bukhari da muslim suka ruwaito wannan hadisi. Masu surutu a daina surutu da Allah. A daina surutu Allah ya kyauta. To kun ji wannan. Abu huraira Allah ya kara mishi yarda yace manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace shine cuta bata tashi daga jikin wani ta fada wani. Abin da a cikin Wato cutar da za ta tashi daga jikin wane ta fada wane kamar misali idan kina ciwon ido sai su ce idan kika kalli wata itama ta daga kai ta kalle ki kuka hada ido sai ciwon idon ki ya tashi ya harbu waccan sai manzon Allah yace karya ne ba ciwon idon ne yake tashi ba Allah ne yake sawa in ya ga dama. Idan kuturu na da kuturta sai a ce in kayi hannu da shi zaka zama kuturu sai manzon Allah yace a'a karya ne. Allah ne yake daukar kuturta kai ya sa in ya so in ba haka ba dan kuturu da yar kuturwa guda nawa ne basu zama ku tare ba. Ashe kun ga ba cutar ce take tashi da kanta ba. Da cutar ce take tashi da kanta mahaifiyar shi kuturwa ce za ta haife shi ta sa hannun kuturta ta mishi wanka. Kuma kuturta ba za ta kama shi ba ashe da kuturta ce ke kamawa da ta kama ashe Allah ne ke nufa dan haka manzon Allah yace cuta bata iya harbin mutum da kanta shine aduwa. Aduwa shine cuta ta harbi wani da kanta ita cutar to bata iya haka. Babu champi. Me ye champi shine kina fitowa in kika ga zomo sai kice Me yasa zomo yana da gudu to yau kasuwa za ta yi kyau kenan. Kina fitowa sai kika ga agwagwa sai kice yau ba sa'a. Kun fahimci wannan jama'a champi kenan. Ko kuma a ji idan mujiya tayi kuka da daddare sai a ce sai a kawo wani champi. Ko kuma kin bude shago sai wani yazo yace miki wance a bani bashi sai kice wato tunda aka fara da bashi yau kasuwa tayi muni. Muna nan shago akwai wata mata in ta dauko ta lamburedi ta champa cewa akwai wani yaro indai ta sauke ya daura ta to za ta siyar. Da ta zo cikin wasa da dariya sai ta sauke bredin ta kamar ta tsaya ta gaishe mu ne. Shikenan to wane yazo ka daura ne ashe ita ta champa ne. A yana cikin din ki rabu da shi barwa ne daura ki sai tace a'a ku bari ku bari ku manya ne wannan dai. Ita ta champa ne indai ya daura ta to da ta shiga cikin mijin nan bredi zai kare. To wannan ba daidai bane. Champi ba kyau jama'a. Champi ba kyau cewa in aka dibi ruwa da ri'a a rijiya da daddare kaza zai faru cewa in akai kaza in akai shara da daddare kaza zai faru duk wannan champi ne babu kyau. A'a ai in ka auru wance zaka talauce in ko ka auru wance zaka yi kudi duk wannan champi ne ba daidai bane. Shine babu champi manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace babu champi. Kun san wani champi da ya zama bala'i a duniya wanda duk shekara in muka je hajji sai mun tawa alha zai wa'azi wani lokacin basa fahimta shine duk sanda aka hau arafa ranar juma'a to sai wani babban mutum ya rasu a wannan shekara ko kusa da wannan ba gaskiya bane. To amma ya zaka yi annabi ya hau arafa ranar juma'a yana dawowa bai dade ba sai ya rasu. Sardauna ya hau arafa ranar juma'a yana dawowa bai dade ba aka kashe shi. Murtala ya hau arafa ranar juma'a bai dade ba aka kashe shi. An hau arafa ranar juma'a yau shekara biyu muna wayar gari sai aka kashe saddam sai suka champa mutanen duniya cewa indai aka yi arafa juma'a to manya za su mutu. Dan haka duk shekara idan arafa ta zo juma'a sai ku ji ana cewa za a jawo ta baya ko za a wai dan kada wani ya mutu wannan champi ne. Ga daidai bane. Ga daidai bane. Sannan yace babu abin da ake nufi shine wani abu mai mugun nufi ko wata mai muguwar nufi ko wata muguwar manufa da zaka ce ai indai wane ne ka hada mu'amala da shi to yana da kashin tsiya. Zaka tsiya ce to babu ainihin sannan babu watan menene watan safar shine wata na biyu na musulunci kun san suna cewa in aka daura aure a watan safar ba zai albarka ba in ka tare a gida a watan safar ba zai albarka ba sai su ce watan safar wata ne mai shu'umci wannan duk jahiliya ce. Ina fata an gane duk ba daidai bane wannan da muslim suka ruwaito wannan hadisi. To kun ga in baku yi a hankali ba mutane suna yin shi a hankali a hankali a hankali a hankali. Har ya kai yanzu akwai wani zobe ko wani warwaro da ake sawa a hannu. Shine har wani malami ya rubuta littafi yana bayyana sharrin da ke tattare da wannan. Mutane sun champa da wane yasa zobe kaza in ya fara kasuwanci kasuwanci zai yi kyau aikin gwamnati zai yi kyau da budurwa ta sa shi yanzu samari sa taso ana ta rigima wane na so wane na so da zaran saurayi yasa yanzu yan mata sa ya ta rububi a kan shi da zaran mai direba yasa yanzu fasinjoji sai ta rigima sai motar shi sai motar shi. Wannan ba daidai bane jama'a. Ga daidai bane ba musulunci bane karku yi Allah ya kiyaye. da muslim suka ruwaito wannan hadisi. Jabiru yace naji manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yana cewa lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci shine barin sallah. Ina ma'anar haka kina barin sallah kin zama kafira. Kina daina yin sallah kin zama mushrika domin dama banbancin mu da mushrikai da kafirai shine sallah to da ka bari kaima ka zama kafiri. Babu shakka zahirin wannan hadisi yana nuna kafircin duk wanda ya bar sallah amma hakikanin ma'anar itace wanda ya bar sallah a bisa musu ya ki yin sallah saboda yace sallah karya ce wannan ya zama kafiri. Amma wane yayi sallah sai ya ta kasala yayi ta kasala yayi ta kasala ko dai baka yarda da sallah bane yace ya yarda. Aka ce wannan ba za a kafir tashi ba sai dai za a bashi kwana uku. Ana lallashin shi wane kayi sallah fa in har ya ki bayan kwana uku to za a kashe shi. Amma wane yace sallah karya ce aka ce sallar yace karya ce to wannan yanzu ne za a tabbatar mishi da hukuncin ki sa matukar alkalin musulunci ya zaunar da shi. Allah ya kyauta. Jama'a sallah tana da girma. Muslim ya ruwaito wannan hadisi. Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yace Har sai na kasance na fi soyuwa gare shi wato har sai ya fi so na sai ya fi so manzon Allah fiye da iyalen shi da dukiyar shi da mutane baki daya. Sai ya zama duk duniya da lahira da za a hada ta wuri daya sai kace kafi kaunar manzon Allah fiye da kowa kafi kaunar manzon Allah fiye da matan ka fiye da yayan ka fiye da baban ka fiye da babar ka fiye da duk mutanen garin ku sai ya zama manzon Allah yafi kowa a zuciyar ka to in ka samu wannan to lallai ka dandana zakin imani. Muslim ya ruwaito wannan hadisi. Abu huraira Allah ya kara mishi yarda yace manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace kowanne da ana haihuwar shi ne da tsarkin zuciya me ake nufi da fitara itace farar zuciya zuciyar da yake babu abin da ya bata ta. To kowanne da kuka ga an haife shi ko kafirai ne suka haihu ko musulmi ne suka haihu komai kafircin su a duniya in suka haifi da zuciyar dan fara ce. Sai yace Uwar shi da uban shi ne suke mai da shi bayahude. Bayahude shine mara kunya game da Allah. Bayahude shike zagin Allah yace Allah talaka ne mune masu wadata. Yace Allah marowaci ne sai dai iyayen shi su mai da shi bayahude ya koma yana kafirci ga Allah ko kuma in iyayen shi kristoci ne su mai da shi krista banasare ya koma yace isa Allah ne. Allah Allah ne maryamu Allah ce ya koma yana cewa Allah uku ne ya koma yana cewa isa daya ne daga cikin alloli duk wannan iyayen shi ne za su bata shi amma in ba haka ba fa an haife shi ne da farar zuciya wanda yake zai iya yarda Allah daya ne. Ko kuma iyayen shi su mai da shi majusu shine mai bautar wuta. Ya ki bauta wa Allah ya koma yana sujjada ga wuta saboda iyayen shi su lallata shi. Sai wani mutum yace ya manzon Allah to da a ce kafirai za su haifi da kafin su bata shi ya koma ya zama kafiri yace Allah uku ne ya koma yana zagin Allah yana bautar wuta to inda zai mutu fa kafin wannan lokacin me kake gani? Sai manzon Allah yace Allah shi yafi sanin me za su aikata inda sun girma dan haka ni yanzu ban sani ba. Malamai suka ce manzon Allah ya fada haka ne kafin Allah ya tabbatar mishi da cewa dukkan yaro in ya rasu a aljanna ike. Domin akwai hadisi sahihi da ya zo cikin sahihul bukhari da ke tabbatar da cewa arna ma idan suka haihu daya rasu kafin ya balaga to aljanna za a kai shi. In aka kai shi aljanna sune manzon Allah yace ya shiga aljanna sai ya ga wani mutum dogo kyakyawa yana karantar da yara islamiya a aljanna. Cewa nane ne wannan sai aka ce wannan baban ka kenan annabi ibrahim. Wadannan yayan fa sai aka ce yayan da ke rasuwa ne basu balaga ba yayan musulmi da yayan kafirai sai a kai su aljanna sai annabi ibrahim yayi ta koya musu islamiya a cikin aljanna. Kun ji har aljanna ma ana islamiya lallai islamiya babban makaranta ce. Ina fata an gane to dan haka in har ya rasu dan kafin ya zama yana da wannan muguwar akida kafin ya balaga to shikenan aljanna zai tafi. Allah ya taimaka. Daga abu huraira Allah ya kara mishi yarda haka ne ko? Abu huraira yace manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace Manzon Allah yace bawan dinari ya shiga uku ya kade me ake nufi da bawan dinari wanda in kika dauki kudi kika bashi a zauna lafiya in kika hana shi ayi tashin hankali to ya zama bawan kudi kwandala kudade wadanda suke na karafuna da kuma bawan alkatifa shine mayafi wanda in aka dauki mayafi aka bashi a zauna lafiya da shi da riga bawan riga in an dau riga an bashi a zauna lafiya da shi in ba dauka an bashi ba ayi fitina. Manzon Allah yace in an dauka an bashi sai yaji dadi ya yarda a zauna lafiya in ko aka hana shi ba zai yarda ba sai ya ta da fitina.
[Segment 4/11 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
abin da wannan hadisi ke nuna mana shine kar ki zama kawai ke kudi kika tasa a gaba. Ba ruwan ki da addini. Ba ruwan ki da mutunci. Ke kawai abin da ya dame ki ya za ayi a samu kudi. In aka zo aka ce wance eh abin da muke so da ke mu makwabtan ki ne zamu jingina gida a jikin naki ki ce ki tada masifa ki tada bala'i. Amma ana zuwa aka ce hajiya eh wallahi tallahi ga yar wata dubu goma kaza kaza dai kaza to Allah ya rufe asiri a sai suka ringa azumi kwana biyu kuma sai a zo a ce hajiya za a hada da ki ce ah hada mana nan ba gidan ku bane? Amma ba dan Allah kika yi wannan ba sai dan an baki wata toshiyar baki. Ina fata an gane. Ya kamata mutane su gane cewa kudi basu daga cikin ma'unai da kake gane mai son ka, mai baka kudi baya nuna mai son ka ne, wani yana baka kudi ne dan ya yaudare ka. Wani yana baka kudi ne dan yana da wata manufa a kan ka. Ina fata an gane. Misali yanzu wasu da suka bullo da wani sharri sai ku ga mutum ya sai wayar GSM sabuwa tungal sai ya ajiye a mota. Da ya ga yarinya budurwa yana son ta kawai abu na farko da zai bata sai ya kawo wayar sai ya bata. Sai tayi ta murna ya bata GSM ne ya bata ne dan amfanin kan shi. Yana nan sai ya ringa buga mata har sai ya yaudare ta. Yanzu GSM din amfanin ta ce ko amfanin shi? Dan amfanin kan shi. Dan haka daukar kudi a baka ko abin duniya ba shike nuna kauna ba, kauna a zuci ta ke. Wannan hadisin yana nuna daga cikin mutane akwai mutanen da kawai kudi suke bautawa kuma mai cece bautar kudi ita ce in an baka kudi ka yadda in ba baka ba fa ba zaka yadda ba. Allah madaukakin sarki ya kiyaye. Bukhari Bukhari ya ruwaito wannan hadisi daga Imran dan Husaini Allah ya kara mishi yarda. Manzon Allah ya ce Manzon Allah ya ce Daga cikin al'umma ta mutum dubu saba'in zasu shiga aljanna ba tare da an bincike su ba. Idan kika tafi airport na jirgin sama sai ki ga akwai wani layi dogo ana ta bincikan mutane tun daga kan ka har ko ina sai an shafa wata na'ura a jikin ka ana bincikar ka. Jakar ka sai an bincika komai sai an kwakule ka yau in a airport na jirgin sama na London ne ma kana zuwa wani wuri takalmin ka ma sai a ce cire takalmin ka, safar ka ma a cire sai an goga wata na'ura a tafin kafar ka. Akwai inda za a kai sai an cire rigar ka an gwaggoga na'ura a cikin wandon ka da ina ina. Duk ana bincikar ka ne a nan saboda kai talaka ne. Amma kuma sai ki ga wata hanya gashi wanda kuka shigo jirgi daya da shi shi saboda wane ne da shi da jakar shi sai a ce su wuce ba za a bincike su ba. Dan haka kana nan a ne maka kwakudubab bincike shi har yana can an kai shi gidan shi ya kwanta yana hutawa. To abin da wannan hadisi yake cewa ranar lahira za a samu wasu mutane dubu saba'in haka Allah zai musu. Suna tashi daga kabari sai a ce musu ga hanya ku shiga aljanna. Su baza su tsaya dangalin kiyama ba ma da sun tashi daga kabari to ku wuce ku wuce mutum dubu saba'in. Ta Allah yasa muna ciki.
[Speaker seg4-spk:1]
Amin.
[Speaker seg4-spk:0]
To kun san aka yi irin wannan maganar dole akwai tambayar da zata biyo baya. Su waye ya manzon Allah sahabbai suka ce Sune wadanda basa neman ayi musu rikuya. Wato idan ciwo ya same su aka yi musu asiri ko kanbin baka ko aljani basa neman kowa yayi musu rikuya. Ko dai su suyi da kan su ko kuma su dake su ce suna rokon kawai Allah ya basu sauki. Wannan shine matsayi mafi daraja idan larura ta same ka kar ka gaya wa kowa a duniya. Kar ka nemi komai a wurin kowa sai a wurin Allah. In zaka iya kaiwa wannan matsayin to zaka shiga aljanna a ranar alkiyama babu bincike. Amma fa da wahala. Aljani ya kama ka ya goga ka ya goga ka ga malami da zai maka rikuya a ce ka dake kawai ka je kayi ta rokon Allah. Wannan hadisin ba yana nuna cowa rikuya ba kyau bane a'a rikuya tana da kyau amma in larura ta same ka ba zaka iya daurewa ka dogara ga Allah gaba daya ba je ka ayi maka. Babu laifi domin annabi ma in bai da lafiya in ya gaza mala'ika Jibrilu yayi mai. In mala'ika Jibrilu bai zo ba sai ya ce a Aisha tayi mishi. To amma matsayi mafi daukaka shine mai? Ka bari kar ka nema wurin kowa kawai ka ce Allah ka warkar da ni. To in har zaka iya haka to ka taka matsayi mai daukaka babu laifi a nan kana sa dai zaka zama cikin dubu saba'in din nan. kuma basa canfi. Wadanda basa canfi suma zasu shiga. Abin da ake nufu da lalas shine a ce wannan wurin yana da ciwo sai mai magani ya ce a kawo garin magani a sa. In aka sa sai a samu dan makodi bakin karfe sai a saka shi a wuta sai yayi jajawur sai a zo a dadana a kan maganin nan a danna har sai ya lime. Wannan yin magani ne. Amma a musulunci ana kyamar irin shi saboda akwai azabtar da jiki da wuta. Shi ko jiki manzon Allah yana cewa Allah bai yadda a azabtar da jiki da abin da yake azaba da shi ba. Allah ne kawai yake azaba da wuta. Dan haka idan kwaro ya bata miki rai ya cije ki da kendir kusa da ke sai ki ce bari ki diga mai ruwan kendir. To Allah zai rama mai a ranar alkiyama ba ramuwar kisan ba ramuwar kisa da wuta ba a kisa da wuta sai Allah ba a azaba da wuta sai Allah. Shi yasa kun ga kafirai yau saboda zalunci sai suka yi wani abin horon masu laifi wanda wuta ce. Idan kayi laifi aka dake ka aka dake ka ka ki fadan gaskiya sai a dakko wata hular kwano sai a cire hular ka sai a sa maka. Sai ka ji duk kwanyar ka tana ta farfasa jije jikin ka sai kayi ta surutu har wanda ba a tambaye ka ba ma su nemi maka dariya. To wannan irin azabar bai halatta ba saboda da wuta ce. Akwai kulki yau na wuta kulki ne na wuta wanda in aka dodana maka shi sai ka ji yana shokin din jikin ka to sai su je su bi dare duk mai laifi sai su je suna shafa mai a jikin yana ta ihu. To wannan bai halatta ba a musulunci ba a azaba da wuta domin annabi sallallahu alaihi wa sallama yayi ce wani annabi daga cikin annabawa ya zauna jikin bishiya yana hutawa sai cinnaka ya zo ya cije shi sai ya dakko kananzir ya barbadawa dukkan cinnakun gaba daya sai kyatta a shana sai suka kone. Sai Allah yayi mai wahayi ya ce a'a me yasa guda daya da taimaka baka kashe ta ba kuma me yasa da zaka kashe su kai musu da wuta? Ba a azaba da wuta ba kyau. Ba kyau. To amma kun ga abin takaici akwai matar da aka nuna ta a tashar talabijin yar kishi ya ta dauka ta ringa dadanawa wuta sai da ta kona jikin yarinya karkaf. Bakin wuta zata dakko sai ta dadana mata yarinya tayi ta ihu tayi ta ihu. Ta sake dakko wani bakin wuta sai da duk ta kone jikin yarinyar gaba daya haka aka nuna a news line. Me yasa wai yar kishiyar ta ce ko da kishiyar da suka yi kishin bai halatta tayi mata haka ba balle yar kishiya. Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yayi ce wata rana ya shiga gidan wuta sai ya ga wata mata mage tana cizon ta kuliya kyan wane cizon matar tana yakushin ta tana yagar ta. Manzon Allah da kan shi sai da ya ce sai da ya ja baya yaji tsoro ya ce me tayi? Sai aka ce kyanwa ta daure. Bata barta ta je tayi ya wuta ci abinci ba kuma bata bata abinci ba har ta kashe ta da yinwa. A yau mata nawa ne? Matar zata kwanta ta mutu sai ya auro wata ko kuma wannan matar da ta rage sai ta dauka wannan kyan ko wannan daya zama abokin gaban ta sai tayi ta azabtar da shi. Duk azabar da kika yi yanzu Allah ba yana kallon wannan daya a matsayin dan kishiya bane Allah yana kallon shi a matsayin dan adam. Kin azabtar da dan adam da bai ci miki ba bai sha miki ba ko da uwar shi tayi miki. Wallahi ma kwan da ya wuce yarinya ce ta zo tana kuka sharaf sharaf. Ta ce ta zo ne a kashe mata aure ta zauna a koya mata girki sannan a samu wanda zai aure ta na ce ya akai sai ta ce uwar ta ta rasu tana karama. Sai kishiyar uwa ta rike ta ta fara ganawa yarinya azaba har yarinya ta kai shekara sha bakwai aka aurar da ita saboda azaba da mugunta yarinyar bata iya girki ba. Yar shekara sha bakwai ta ce ko taliya ba a barta ta ga ta ce kai ko alaiyah hu a ka mika mata bata san ya ake yanka shi ba. Daga talla sai duka sai wanke wanke sai ta ce ba a koya mata komi ba. Wanda ya zo zai aure ta ya ce zai aure ta yana da mata biyu zasu koya mata girki. Aka tafi mata su kuma suka juwa mata baya. Eh suma suka yi nasu kishin azaba kun ga ita gaba daya ta kare a kan kishi da kishiyar uwa da kishiyoyin ta. Ranar girki sai a zo a tile mata cefane sai su shiga dakka suyi ta dariya. Su dafa taliya da indomie su ci su da yayan su. Ita kuma fa a barta ta kwana da yinwa. Shine abin duniya yayi mata yawa ranar juma'a da ta gaba ta jama'a ina zaune a office da abokai na sun zo daga Lagos. Muna tattaunawa muna abin nan sai kawai ta ta leko tana kuka kukan in kika ga kukan ba kukan ido bane kukan zuci ne. Kukan zuci ne. Ta ce bata da kowa a duniya sai uban shi kuma ga abin da ya faru gashi gashi gashi ga dan haka kawai ta yanke shawara ne ta zo ne a kashe auren ta zauna a koyar da ita girki sannan a samu wani da zai mutunta ta ya aure ta. Na lallashe ta sai na bata hakuri na saka ta a mota sai na kai ta gidan mijin. Ya ce duk abin da ta fada gaskiya ne na ce to kai dole ne ka samu ka san matakin da zaka yi tunda ba karya tayi ba. Da karya tayi sai a ce to tayi karya za ayi kaza amma duk abin da sai ya ce duk abin da ta fada gaskiya ne. To yanzu ya za ayi kenan? To shine ni kuma a irin yar tawa shawaran na ce sai ka samu dattijuwa sai ka dauke ta aiki. Sai ka hada ta da ita ta nemi mata girkin kuma tana koyo. Girki kan ko mu ma za ayi a wata uku zuwa wata shida zaka dauki hannu ko? Balle yan mata kuma balle abin da takaici kun san abin aka yi maka gori kafi zagewa. To Allah madaukakin sarki ya kiyaye. Ina gaya wa matan da suka san an mutu ko an fita an bar musu yaya da ba na kowa bane sai wanda ya mutunta shi. Ku kiyaye wannan in kika mutunta shi karshe sai in manta da uwar ya zama kece uwar shi. Dan a duniya babu halittar banza irin kare. Amma kare ya san mai kyautata mai. To balle dan mutum ya tashi ya ga kece wankan shi kece cin shi kece shan shi ana nan sai a waye gari ya manta cewa uwar shi ta rasu ko uwar shi ta fita. Ba shi daga cikin sunna abin da mata suke na cin amanar wasu yaya saboda sunyi zama na rashin lafiya da uwa kuma uwar ta rasu ke baza ki ji tausayi ba marayan Allah ne Allah ya bar miki. Maraya da zaka shafa kan shi ka samu lada maraya da zaku zama a gidan ku in akwai maraya Allah bai barin ku ku wahala. Inda mutane sun san fa lalan marayu bani tunanin in za a samu gidan marayu a duniya. Wallahi yanzu nake gaya muku labarin wannan malamin. Wallahi malami ne na sakandare amma wallahi millioniya ne. Allah ya azabta shi me yasa? Kullum abin da ya dame shi shine talakawa marayu mata da mijin su suyi rasu. Sai ku ga wadannan yara na gaya muku ga makaranta ya zo ya gina. Sannan sai ya je yayi wata ma'aikata haka ya gina ta makekiyar ma'aikata ce. In yi muku misali tafi masallacin Haruna Danja girma. Wannan wurin ya sa mishi Wato ma'ajiya ce ta sadaka sai ya je ya samu masu kudi tunda shi mai kudi ne yanzu ba talaka ba in ya je bazai ji kunyar gaya maka ba. Sai ya ce na zo ne daga cikin abin da Allah ya baka ajiya ka dibo ka bamu. Sai a je a tara kaya wane zai aurar da yar shi bai da hali sai ka zo in ka fada duk abin da kake so za a dauka a baka. Wane zai aure bai da hali sai ayi ma wane bai da sana'a sai ayi ma wane bai da kaza saboda haka wurin in kika je zaki ga har motoci gasu nan sababbi an kawo sadaka. Saudiya ce. Wani zai zo shi direba ne ya ce wallahi tallahi Allah gafarta malam ni direba ne na hadari mota ta ta kone wallahi na shiga halin kaka ni kayi. Sai ya ce to gashi daga cikin dukiyar Allah wasu suka kawo an baka. Sai ku ga mutum ya fashe da kukan dadi. Wani sai ya kasa tuka mota aka yi aka yi yaya ka ce kai direba ne ya ce dadi ya sa jikin shi ya mutu ya kasa ya kasa tukawa. To haka abin yake jama'a kun ga sai Allah yasa albarka a cikin rayuwar shi. Dan haka jama'a ku daina mugunta babu kishi a musulunci. Babu cin zalun dan kishiya. Balle a ce maraya ne ta mutu ta barshi sai kiyi tunani ke kuma gobe in kika mutu fa. Ina fata an gane. Allah ya kiyaye. Na'am. Yayin da kuma kun ga akasun haka zamu zo mu karanta a cikin hadisi wata kuma karuwace take tafiya kawai sai ta ga kare yana jin kishi. Ta shiga ta sha ruwa ta fito a rijiya sai ta shiga ta dibo a takalmin ta ta ringa baiwa karen nan ya sha Allah ya gode mata ya gafarta mata ya saka ta a aljanna. Allah ya manta da zunuban ta ya gafarta mata saboda ta sha yarda kare. To balle a ce mutum ne aka bar miki sai kiyi kokarin mayar da shi ya zama naki. Ai ba mai dadin sha'ani ma irin yaro. Duk wanda ke bashi shine nashi. Abin da uwar tana gidan ke kina gidan in gari ya waye ya lura kece kike kawo da faffan shayi kece kike kawo dan danbin nama ki danka mai kece kike sa mai kaza yana nan sai ki ji ya ce kece ba bar shi. Yayi ta waye can ana ta bayani ya kasa fahimta ga inda duniya ta ke nan ana ana hidima ke kuma kawai zaki ce kece kika haife shi. To Allah ya taimake mu. Saboda haka kun ji. Sannan sai ya ce ga uban gijin su kadai suka dogara wadanda duk suka dogara ga Allah basa kai wata bukatar su ga kowa sai ga Allah sune zasu shiga aljanna ranar alkiyama kai tsaye. Allah ya saka mu dan rahamar shi. Na'am Muttafakun alaihi Bukhari da Muslim su suka ruwaito wannan hadisi. Kasantuwar bamu fara karatun da wuri ba to zamu saurara a nan sai gobe za a ci gaba insha Allahu ta'ala. Dalilai biyu ne suka sa bamu fara da wuri ba dalilin farko akwai registration da ake can na makaranta dalili na biyu kuma dan a raba littafi dan haka gobe lallai ne karfe tara daidai za mu fara insha Allahu ta'ala. Idan akwai tambayoyi sai a miko su mu dan cike lokaci da su in kuma babu tambayoyi to zamu yi addu'a sai mu tashi in Allah madaukakin sarki ya so. In kuma tambayar ta baki ce to in ba rubutacciya duka dai muna saurare. Na'am. Mata masu biki. Na'am. Na'am. Ta ce mata masu dafa ruwan wanka na haihuwa sai ka kunna wuta sai ka ga kwari a ciki sai kayi sauri ka kashe. Kayi kokarin zazzage su. Ka tabbatar cewa babu a ciki. Shi yasa haramun ne saka wa daji wuta da mutane suke saboda sanda zaka sako wutan nan wata kwaruwar ko wata dabbar tana nan duk inda ta sheka da gudu a iya gudun ta wutan zata fada. Saboda haka wuta ta cinye ta danya ba daidai bane. Allah ya kiyaye. Na'am. Na'am. To shi kananzirin an dube shi wuta ce shi kan shi. Inda zaki gane kananzirin wuta ce in ya zuba jikin dan adam ko ba a kunna wuta ba kwayewa take. Kenan a samu maganin da zai zama shine maganin kwarin shi yafi dacewa a sa musu fiye da a ce a sa maganin da yake asalin shi wuta ce. Amma kananzir wuta ce. Da dan adam zai daure ya sha kananzir hanjin shi tsintsinkewa zai yi. Na'am. Na'am. Fiya fiya ai dama shi an yi shi dan kwari ne. Babu laifi insha Allahu. Na'am. Fiya fiya a hada shi da kananzir. To Yafi kashewa in aka hada da kananzir to kun ga kuma nan ne aka shigo tsala. Allah ya kiyaye amma dai ni abin da nake gaya muku inda yadda zaku kauce wa kananzirin nan ku kauce mai. To. Na'am. Akwai magani irin wanda ake in kuka je wurin masu sai da magungunan gona. Akwai maganin wanda dama an yi shi saboda kwarkwasa ne ana fesawa zaku ga ta bace. Sai dai ina son ku san wani abu daga cikin nau'in kwarkwasa akwai kwarkwasar da ba kwarkwasa bace tana wahal da bahaushe bai gane ba aljanu ne. Zaku ga duk yadda zaku yi na samu irin wannan matsala a gida na a Yola. Yanzun nan zaku ga gidan lafiya lau kafin minti biyu sai ku ga kwarkwasa tafi kace million ko ina kwarkwasa ce. Muka kashe
[Segment 5/11 | 01:20:00–01:40:00]
[Speaker seg5-spk:0]
muka ga jiran nan sai na tsaya sai nayi nazari ai daga cikin nau'in kwarkwasa akwai aljanu. Shikenan sai mukayi addu'a a ruwa muka yafa, shikenan har muka taso Allah ya raba mu da su. Sai na gane ashe ba kwarkwasa bace aljanu ne kawai. To gida ne dama ance an gina shi wajen shekara biyar kowa yace da aljanu a ciki. To wai ni da akaji zan kama sai akace ku barshi tunda malami ne shi yasan yadda zaiyi, wallahi haka sukai sai daga baya naji labari sai daga baya naji labari kawai Na'am. Suma maganin kwari ya kamata a sa musu kenke sai dake damun mata a kitchen ko? Shine. Har gida sai a gansu sai wato dai ku kauce wa wuta ku kauce wa wuta wata tace dan Allah malam ina hukuncin daliban dake zagin malaman su wannan rashin ladabi ne. Ai ba wai malamin ka ba zagi gaba daya ma bai halatta ba. Allahumma ace kuma malamin da ya karantar da kai shi zaka zaga wannan rashin ladabi ya kai matuka domin bari kuji malami matsayin uba ne bari kuji babu laifin da baban ka zai maka a duniya ya halatta ka zage shi babu laifin da mahaifiyar ka zata yi maka a duniya ya halatta ka zage ta haka malamin ka malami ba abun wasa bane Allah ya kyauta. Wannan kuma tana tambayar cewa to ina hukuncin hadisin da akace a ringa yin lalas ko bai inganta bane? Asalin hadisin ya inganta sai dai matsalar itace wato annabi sallallahu alaihi wasallama ya dubi lamas a matsayin shi na magani to ya halatta a nan kuma ya dubi lalas a matsayin shi na azabtarwa ce da wuta dan haka yace bai halatta ba. Shi hadisin ba bai inganta bane sai dai malamai sun bada fatawar cewa a karkata wajen aiki da wannan hadisin cewa kada ayi lalas din shine yafi. Allah ya taimaka. Wannan yace taimako eh malam ina neman taimakon yan uwa musulmi da addu'a da wadansu azzalumai suka tawe mun suka tawe mahaifi na hakkin sa Allah ya kwantar masa Allah ya kwatar masa amu to wata ce tace wai wasu azzalumai ne suka danne wa mahaifin ta wani hakkin sa shine take neman mu taya ta addu'a Allah ya kwatar mishi hakkin shi, Allah ya kwatar mishi hakkin nashi. Su kuma azzaluman Allah ya sa su tuba su dawo da wannan abu kafin a je lahira dan kunsan ka zalunci mutum a nan duniya kana ganin ba komai ranar lahira sallolin ka na azahar da la'asar da magariba da isha da azumin ka na ramadan da na shitta shawwal duk su za'a kwashe ayi ta biyan mutane sai ka wayi gari kafin yamma a ranar lahira baka da komai. Wa'alaikumussalam warahmatullahi. Na'am. To bismillah eh bismillah bismillah Na'am. Wannan kuma tace wannan tace ana yin azumin nafila ranar asabar to tambayar ta gaba ce tace ko yayi ranar juma'a wato ba'a yin azumin nafila ranar asabar koda asabar din ta dace da ranar arafa ce abunda yasa hadisi ne yazo sahihi a cikin sunan abi dauda annabi sallallahu alaihi wasallama yace karku yi azumi ranar asabar sai dai azumin da aka farlanta muku idan misali azumin ramadan ne in yazo da asabar zaki iya yi a'a da watan azumi ne kinyi al'ada bakiyi azumi ba sai kika zo zaki rama bayan sallah sai ranar ta fado har da asabar zaki iya yi dan duk farilla ne azumin ka fara zaki iya yi ranar asabar saboda duk farilla ne amma azumin nafila kamar azumin shitta shawwal kin dauko kina yi sai aka zo asabar sai ki tsallake ta sai kiyi lahadi babu komai a'a azumi ne kika dauko kina yi azumin annabi dauda yau kiyi azumi gobe kiyi sai ya zama kinyi azumi ranar alhamis ranar juma'a bazaki yi ba kenan to ranar asabar tayi daidai da zaki yi kenan to bazaki yi ba sai ki tsallake ta sai ki kai lahadi ba'a yin azumin asabar eh nafila ranar asabar annabi sallallahu alaihi wasallama ya hana ita kuma juma'a ba'a ware ta da azumi ita kadai ma'ana ya zama ke bazaki yi azumi ba sai ranar juma'a kadai amma in ya zama ya dace da ranar azumin ki ne misali kinyi azumi ranar laraba sai kika sha ranar alhamis sai ki tashi da azumi ranar juma'a babu laifi amma ace ita bata yin azumi sai ranar juma'a to wannan ba kyau ko kuma ace ita bata sallar dare sai daren juma'a to wannan ba kyau na'am. Eh bism.
[Speaker seg5-spk:1]
Wannan gamin ranar asabar din na dauka laifin ne na gama asabar din na dauka
[Speaker seg5-spk:0]
Babu komai tace to kafin taji wa'azi ta riga tayi azumin ranar asabar babu laifi yayi ita doka tana aiki ne akan wanda yaji ta ya karya ta wanda bai sani ba ya aikata bashi da laifi jama'a na'am wannan tace akan maganar maraya to malam in baka da halin halifa kuma gidan ku akwai to to ban gane dai wannan tambayar ba in mai tambayar tana kusa sai yayi ta magana insha Allahu wannan tace tana tambaya wannan annabi ne ya kona ainihin wato wannan cin naku annabi bai fadi sunan shi ba cewa wani annabi daga cikin annabawa annabawa ko yawa ne da su wannan tace menene hukuncin in an karanta fatiha ba'a sallah ba'a ce amin a'a a sallah ne kawai ake cewa amin in ba'a sallah ba babu cewa amin sai a cigaba da karatu kawai wannan tace suma ta zasu hada duk duniya da duk duniya a sa hun sallah eh mata in suka zo yin sallah kamar yadda maza suke yin sahu su hada duk duniya da duk duniya wato kafa da kafa a hadu haka ya kamata suma suyi na'am wannan tace yaya matsayin wda take hudda da kirista sama da shekara takwas in an kora ta zan barta tazo gida na har ta kwanta ta ci abinci saboda naso in jawo ra'ayin ta zuwa ga addinin musulunci kuma tana so ta musulunta ba mai bata abinci in ta samu aiki zata samu yadda zata ci abinci don tayi karatu ya halatta haka daidai ne ma'ana kirista ce sai ya zama iyayen ta na wulakanta ta sai tazo wurin ki kika bata abinci ta kwana wurin ki kika bata sabulu tayi wanka kika karbe ta hannu biyu biyu kina kyautata mata dama ai ba wa'azi ne yake shiryar da mutane ba hali na gari ne yake shiryar da mutane in ba haka ba duk najeriya da an shiryu wa'azi kan kullum gidan rediyo da azumin nan har asuba ake yin wa'azi shi kanshi rediyon baya hutawa ba haka bane amma kunga karshe sai kuga duk abun abinda dama ake bukata mu mu kyautata musu ina fata an gane mu mu kyautata musu ace yau sallah ne kuna da makwabta kristoci in aka dafa abinci sai ku ce a kai musu ina fata an gane idan suka zo suna da wata bukata wanda suke so ayi musu sai ayi musu babu laifi ina fatan kun gane Wa'alaikumussalam warahmatullahi. Na'am. Na'am. Na'am. Na'am. Na'am. Yayi daidai. Yayi daidai ki rike maraya sai ki roki Allah ya sa miki kauna ke ki so shi shima yaji yana son ki daidai ne domin in ya tashi babu soyayya ai bazai biyayya ba kwarai da gaske lallai dai ku lura da rike maraya rike maraya yana da falala lallai rike maraya yana da falala na'am. Na'am. Na'am. Na'am. Karatun. Mm. To kamata yayi a samu wadanda zasu rike shi kuma waccan maganar da kika fada ai ba karya bace cewa in ya girma zai kashe uwar wannan kan abu ne sannan ne dama gare su amma dangane da abunda ya shafi yaron tunda ke kinyi kukan baki iya rike shi to kamata yayi kuyi tunanin wanene zai iya rike shi ana bukatan dai a samu wani wanda yana wurin uwa amma za'a ringa kula da shi muna rokon Allah madaukakin sarki ya kawo mishi wanda zai kula da shi ba komai Allah zai kawo mishi in Allah ya so kuna ga annabi abunda Allah yace mishi Allah bai same ka maraya ba ya rungume ka me yake nufi yaro ne yana ciki uba ya rasu uwar ta haife shi shekaru kadan sai kuma ta kwanta ta rasu kaka ya rike shi ya rasu kawu ya rike shi ya rasu sai Allah ya hada shi da mata mai mutunci itace wa itace ya aure ta tun kafin ya zama annabi ta dibi abinci ta bashi tayi kaza tayi kaza tayi kaza tayi kaza dan haka da qur'ani yazo mishi sai yace Allah bai same ka maraya ba sai rungume ka ina fata an gane ina ma'anar wannan maganar lallai ne maraya yana bukatan a samu wanda zai rike shi wato a hankali masu kudin mu zamu yi ta wayar musu da kai su gane muhimmancin rike marayu a kudu in kuka je kasar yarabawa ko kasar iyamare zaku ga wasu abubuwa na ban sha'awa gwamnati ta bada izinin zaka iya siyan fili ka gina gida ya zama gidan marayu ka ringa dauko su sai ka dauki ma'aikata in ka dauki ma'aikata sai su ma'aikatan su ringa kula da marayun kai kuma kana kawo musu abinci kunsan cewa yanzu a kudu samari da yan mata hada kansu suke in sun gama jami'a basu samu aiki ba sai su samu gida su kama haya sai su maida shi gidan marayu suna taimaka wa marayun su kuma suna samun kudi saboda zasu rubuta ma'aikata kaza ma'aikata kaza sai kuga ana aiko musu da miliyoyin kudi sai kuga su kansu suna daukan mutane aiki ne ba da aiki itama bata da aiki sai su hadu sai su kama gida sai su biya miliyan daya kudin haya a shekara sai suji su tsuntsunto marayu sai su rubuta wa kamfanin ban bita kamfanin dangote na sukari kamfanin sabulu cewa muna rainon marayu dan haka ku kawo taimako mu mu yi aikin taimakon marayu sai kuga an kawo abunda marayun su ci masu rikon marayun ma su ci sai kuga kowa yayi ku mari to Allah ya taimaka to saboda kure wani lokaci zamu saurara a nan sai Allah ya kaimu gobe insha Allahu ta'ala muna rokon Allah ya daukaka musulunci da musulmai Allah ya rusa kafirci da Allahu Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh.
[Speaker seg5-spk:2]
Wa'alaikumussalam.
[Speaker seg5-spk:0]
Yanzu da muke magana safiyar ranar lahadi ce wanda tayi daidai da ranar ashirin da takwas ga watan oktoba hijiran annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallam na da shekara dubu daya da dari hudu a wato ashirin da takwas ga watan oktoba shekara ta dubu biyu da takwas wanda tayi daidai da ashirin da biyar ga watan shawwal hijira na da shekara dubu daya da dari hudu da ashirin da tara wannan shine kasan na biyu daga cikin jiran gyar wa'azozi da karatu tuka da muke wa mata a wannan masallaci na juma'a nan muciya littafin da rubuta Allah ya gafarta mishi ya sa mishi wato hadisai dari gama da ainihin wato hadisai da suka shafi akidoji Allah ya taimake mu zamu tashi akan hadisi na sha biyu ko na malam yace Abu huraira daga sahabi Abu huraira Allah ya kara mishi yadda shi Abu huraira yace ya karbo daga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi manzon Allah yace ina rantsewa da ran ina rantsewa da ran wanda wato ran wanda wato ina rantsewa da wanda ran muhammadu yake a hanne shi wato ina rantsewa da Allah wanda shine ke rike da ran annabi muhammadu sallallahu alaihi wasallama wani daga cikin wannan al'umma bazai ji labari na ba ko ba yahude ne ko kirista sannan kuma bai yadda da abinda aka aiko ni da shi ba sai ya zama daga cikin yan wuta ya ruwaito wannan hadisi da farko ina so mu gane annabi sallallahu alaihi wasallama yana danganta al'umma zuwa gare shi ne da dalilai biyu dalilin farko itace al'ummar da annabi sallallahu alaihi wa alihi wasallama yake kiran su zuwa ga addinin musulunci a nan da kiristoci da yahudawa da maguzawa da majusawa dake bautar wuta da sabi'awa dake bautar taurari da duk wani kafiri a duniya dukkan inda mutum da aljani yake to annabi yazo zuwa gare shi ne yazo mishi da sako daga Allah to wadannan in aka tattara su sune ake kira to a cikin wannan taro na halittu mutane da aljanu sai aka samu wasu mutane sukai imani da annabi sallallahu alaihi wasallam wasu aljanu sukai imani da annabi muhammadu sallallahu alaihi wasallama to wadannan sun tashi daga kafirai sun zama muminai musulmi to su yanzu wadannan sai a kira su al'ummar da suka amsa wa annabi muhammadu sallallahu alaihi wasallama to so da dama annabi in yazo sai yace al'umma ta ko kuma wannan al'umma yanzu wannan kalmar da ya fadi a cikin wannan hadisi da yake cewa ina rantsewa da Allah wanda ran annabi muhammadu yake a hannun shi babu wani daga cikin wannan al'umma to wacce al'umma yake nufi yana nufin duniya gaba daya duk duniya gaba daya mutane da aljanu wanda duk yaji labarin annabi yazo ya cigaba da yahudanci to in ya mutu wuta zai tafi wanda duk yaji labarin annabi yazo ya cigaba da kiristanci har ya mutu to wuta zai tafi wanda yaji labarin annabi sallallahu alaihi wasallama yazo ya cigaba da bautar wuta ko bautar taurari ko bautar gunki ko ya cigaba da wani nau'i na kafirci to wuta zai tafi wannan yake nuna ashe da annabi ya danganta wannan al'umma yana nufin wato al'ummar da yazo yake kira zuwa ga addini to kenan wannan hadisin yana nuna mana a zahiri wanda bai ji sakon annabi muhammad ba ya mutu yana kafircin shi shikenan Allah bazai azabtar da shi ba na'am wannan shine zahiri kuma wannan shine abinda malaman musulunci suka tafi a kai domin Allah yana cewa bama azaba sai mun aiko da manzo mutumin da yake zaune bai taba jin sako na Allah yazo gare shi ba saboda babu manzanni saboda babu malamai saboda sako bai je gare shi ba har ya mutu aka ce irin wadannan abinda yafi inganci shine ace suna cikin nufin Allah abinda Allah yayi so shi zaiyi da su wasu malamai suka ce ranar alkiyama Allah zai musu jarabawa ne sai ya kunna wutar jahannama sai yace musu kuje ku shige ta to sai a samu wasu sai su tsaya gaddama cewa ah Allah ya zamu shiga wutar jahannama ai mu bamu saba maka ba dan baka turo mana da manzanni mun kafirce musu ba sai ace to su koma gefe guda wadancan ko da suka sallah ma aka ce kuje ku shiga wuta suka kama hanya zasu shiga wuta sai ace ku dawo sai ace wannan dalili ne akan cewa da kun samu manzon ku zaku bi ku kuma zaku kafirce a nan take sai Allah ya hukunta wadancan da tafiya aljanna wadancan da tafiya wutar wasu malamai sun fada haka gaskiyar lamari Allah madaukakin sarki shi yafi sanin yadda zaiyi da irin wadannan mutane wadannan mutane su ake kira mutanen da suka rayu lokacin da babu manzanni ko kuma ga manzannin amma su kuma basu ji labarin su ba amma mutanen makka tun kafin a haifi annabi sallallahu alaihi wasallama har
[Segment 6/11 | 01:40:00–02:00:00]
[Speaker seg6-spk:0]
zuwa zamanin Isma'il da Ibrahim wanda duk yayi kafirci wuta zai tafi. Abinda yasa tunda Allah madaukakin sarki ya aiko annabi Ibrahim da Isma'il Makkah suka zo suka gina Ka'aba, suka karantar da tauhidi, to duk wanda ya lalace yaje yana bautar gunki ko yaje yana tsafi ko yana maguzanci, yana mutuwa wuta zai tafi. Dan haka annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallama wata rana suna hira da matar shi Aisha taji labarin wani dattijo mutumin kirki a jahiliyya ya dafa abinci ya tacyar da talakawa, yayi ta ayyukan alheri, yayi ta yin abubuwa, yayi ta yin abubuwa sai Aisha ran nan sai tace oh Allah yaji kanwa ne sai manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yace ka ci karki sake cewa Allah yaji kan shi domin tunda yake har ya mutu bai taba cewa Allah ka gafarta ni ba. Wato ya mutu yana maguzanci yana bautar gunki, sai dai mutumin kirki ne yana ba talakawa abinci, yana taimakon gajiyayyu, yana ayyukan alheri amma maguzanci yake yi. Kenan wannan ayyuka na alheri da yake yi basu isa su kankare mishi wancan kafirci ba domin shi kafirci ba abinda ke kankare shi sai ka bude baki kace na tuba. Da ace wanda yafi kowa kafirci a duniya zai waye gari kuma yafi kowa sadaka to wannan sadakar ba zata amfane shi ba har sai ya dawo ya shiga addinin musulunci. In ba haka ba fa wannan ladan sadaka sai a tattara shi a ranar alkiyama sai a watse shi yabi iska, shi kuma sai a kama shi ayi wuta dashi. Allah yace sai mu tattara duk ayyukan da suka aikata sai mu sheke shi sai yabi iska, su kuma sai a kama su ayi wuta dasu. Allah ya kiyaye. To wannan hadisi kuma yana nuna mana muhimmancin musulmi su rinka da'awa suna yada addinin musulunci domin na daga cikin matsalolin da ake samu shine akwai da dama daga cikin yahudawa da nasara sakon musulunci bai zai gare su ba jama'a. Akwai wani malami bature ne amma bakin fata ma'ana Caribbean, bakin fata America ne. Allah madaukakin sarki yayi mishi hikima ta fasahar bayani tunda bature ne ma'ana bakin fata America ne. Nayi kokarin na tattaro sidinan shi da kasusuwan shi wanda muna so a tashar talabijin ta Zaria zamu sa za'a rinka sawa zamu kintaci rana kun Juma'a da ranakun Asabar da ranakun Laraba za'a rinka sawa. Ba dan komai ba dukkan wa'azozin da muke yi da Hausa muke yi. Wani yana nan baya jin Hausa. Haka ne ko ba haka ba?
[Speaker seg6-spk:1]
Haka ne.
[Speaker seg6-spk:0]
Yanzu wanda baya jin Hausa duk bayanan nan da nake yana fahimtar su? Baya fahimtar su. Ashe yana daga cikin hakkin masu da'awa lallai ne suyi da'awa da yarukan da mutane suke fahimta. Amma matsalar da muke fuskanta ne shine yanzu zaka tara mata ne a muciya ko cika ji ko daurawa ko dogon bauchi ko tudun wada kace zaka musu wa'azi da turanci ba duka za'a fahimta ba za'a samu matsala. Zaka je ka tara mutane ne yanzu a wadannan irin anguwanni namu kace zaka musu wa'azi da turanci ba duka zasu fahimta ba. Sai dai in muka samu Allah ya taimake mu mukayi lecture tiyata sai mu samu auditorium, mu samu wani dan daki sai a rinka tara wadanda suke zalla 'yan boko ne sai a rinka yi musu darrusa da lectoci da turanci to wannan sai a rinka yada wa sai a rinka wakiltar da'awar mu. Amma yau wani yana nan yana rayuwa a Zaria yana jin dai ana cewa su Albani su Albani amma mai su Albani suke cewa bai sani ba domin shi turanci yake ji. In ba haka ba fa sai in ya muranci, in ba haka ba fa sai ko ya rabanci, in ba haka ba sai wani yare to lallai ne mu isar mishi da sako da yaren da yake ji. Dan haka nake cewa mutumin da ya samu kanshi a kudancin Nigeria kana zaune Akwa Ibom ko kana zaune Kalaba ko kana zaune Lagos ko Potakort ko kana zaune a Benin ko wani gari irin wannan ana bukatan a rinka yin tafsirin al'kur'ani da broken. Lalataccen turancin nan da za'a ce na my father sai make a bitter. Wannan irin turancin shine yaren wani. Wani yana nan baya jin wani ainihin yare sai wannan. To in muka zo mukayi wa'azi da turanci mai kyau ce wadannan kalmomin sun maye wa baya fahimta. Sai an dawo ana cewa Allah yace annabi yace da irin turancin da yake fahimta. Sannan sai anje an samu Fulani a riga yau akwai Fulani suna nan basa jin Hausa duk wa'azozin nan da muke basa ji. Sai munje mun bisu har riga munyi musu wa'azi. Dayawa ci Fulani dake riga wasu basa sallah. Basa sallah. Sai mutum ya kai shekara 40 sai ya biya kujerar hajji yaje yayi hajji to in ya dawo sai a zo ayi biki ya tsai da gemu kuma sannan zai fara sallah. Ya kai shekara 40. To in bai kai shekara 40 ba ya mutu fa ya mutu baya sallah. Can naje na same su a wani tsibiri can tudu garin Maya Balwacen abin nan a cikin kasar Adamawa naje da la'asar haka na same su samari ne da 'yan mata gasu nan na fara tattaunawa dasu. Sai nace kayi sallah la'asar? Sai yace ai bai fara sallah ba tukuna a gidan ma baffen su ne kawai yake sallah. Nace ya baffe ne yace eh baffe ne kawai yake sallah. Ina masallacin ku yace ya basu da masallaci saboda baffe ne kawai yake sallah a gidan. Su duk basu fara ba amma fa ya kai shekara 20 da wani abu. To idan kunga laifin shi sai kuga laifin mu mu masu wa'azi. Domin shi an haife shi a daji iyayen shi ba malamai bane kuma tunanin da iyayen shi suka tashi akai shine ba'a fara sallah sai an kai shekara 40. Abin tambaya malamai sunje sunyi musu wa'azi sunce ba haka abin yake ba? Ba je anyi ba. Amma kunga in kuka shiga kasar Adamawa da kasar Taraba zaku je ku samu kiristoci shekara 40 da ta wuce sunje sunyi musu wa'azi sun saka su a addinin Kirista. Naje na samu bature a yau shekarar ta kusan 80 a duniya ta tsupar ta kyau ba irin fulatancin da bata je a duniya. Tace tun tana budurwa aka turo ta daga kasar Italia take aiki a wannan tsirkukin. Kusan shekarar ta 60 tana aikin yada faropaganda ta christianity da fulatanci ta iya fulatanci. Fulani ne ta zuba su sun zama kiristoci gasu nan. Sai kiji pasto ja'e reverend Julde kinga al'amari yaba ce. Wadannan gobe sune za'a hada su gaba da kiyayya da musu dawo suna yakar mu. Shiga kasar Ikara, shiga kasar Giwa, Hausawa ne gasu nan suna Hausa fiye da tamu. Maguzawa ne amma an shigar dasu cikin addinin Kirista. Laifin mu ne domin bamu je mun gaya musu addinin ba. Idan suka yunkuri suka zo suka ce zasu shiga addinin ada me ake yi? Sai a ce sai ya kawo rago sai ya kawo goro, sai ya kawo atampa, sai a loda mishi wani haraji wanda bazai iya ba. Sai kaga cewa to tunda musuluncin nan ya zama yana da tsada bari ya hakura. Allah yaji kan malam Abdul Hamid limamin masallacin Juma'a na Ahlus Sunnah na Hanwa ba dan ya mutu ba shi yake bamu wani labari yace ya dauki babur din shi ya shiga kudancin Zariyan nan wajen samu naka can cikin tsirkuki yaje ya samu katuwar fada gasu sarki na sarauta da sutura kamar musulmi sai zan ashe ba musulmi bane. Yace sarkin ya karbe shi ya kyautata mishi ya mutunta shi yayi mishi alheri. Da yaji dadi sai yace mishi to amma lokacin sallah yayi sai a tashi ayi sallah sai yace ai shi ba musulmi bane. Malami yace hankalin shi ya tashi ga rawani akan sarki ga babban riga ga alkebba ga komai a fada yaya ga kuma masallaci a fadar. Yace shi ba musulmi bane yace ya aka yi? Yace yana karami mahaifin shi yayi yunkurin ya shiga addinin musulunci a garin sai limamai suka ce to zai kawo raguna guda biyu zai kawo atampofi zai kawo goro. Haka sai da yayi shekara da shekaru yayi noma ya tara kudi sai ya sayi rago daya sai ya kawo sai su cinye. Haka har sai da ya gama biyan duk wadannan dues, wadannan tara da suka dora mishi sai aka ce to kuma sai ya noma wata katuwar gona sannan a fada mishi kalmar shahada. Madadin a fada mai in yaso a cigaba da cutar shi hisabi yayi sauki ko? Sai aka ki fada mishi kalmar yana cikin wannan noman ya mutu. Ba'a musuluntar dashi ba ba'a fada mishi kalmar shahada ba. Ya mutu. Sai shi dan yake bada bayani yace a daidai wannan lokaci sai turawan mishin suka zo shi sai suka dauke shi suka tafi dashi suka je suka saka shi makarantar boko yaje yayi karatu har Ingila da ya dawo garin sai ya zama babu mai ilimi da kudi da karatu da iyawa kamar shi shine aka nada shi ya zama sarki. Sai yace dan haka shi da addinin musulunci har abada. Yace da ace kun so in musuluntar da kun musuluntar da baba na tabbas tashi zanyi kawai ni musulmi ne babu wata wahala da zaku sha. Wannan fitinar har yau muna fuskantar ta jama'a sai mu shiga tsirkuki zamu je muyi wa'azi sai mutane suce zasu musulunta sai mu musuluntar dasu sai wasu shaidanu sai suzo suce musu musuluncin ku bai yi ba. An yanka muku rago suce a'a an bada goro a'a nawa kuka bayar sadaka babu sai a ce musulunci bai yiwu ba. Haka kawai zaku shiga musulunci ba sadaka ba ragon suna ba wani abu babu inda aka fada haka a duniya. Musulunci ba trader bace, musulunci ba shago bane da manzon Allah ya bar mana mu rinka diban kudin mutane muna ci saboda mu basu musulunci. To kuji dai abinda hadisin nan yake cewa ina rantsuwa da Allah wanda ran Muhammad yake a hannun shi babu wani daga cikin wannan al'umma da zai ji labari na ba yahude ne ko ba nasari sannan ya mutu bai yadda da abinda aka aiko ni dashi ba sai ya zama daga cikin 'yan wuta. Lallai ne to muje mu yada sako jama'a mu yada busharar manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallama lallai aikin da'awa jama'a ya dauki salo iri-iri yanzu musamman yadda ainihin al'umma suka zama nau'i nau'i. Yanzu in mata ne zaka yi wa'azi irin yadda zaka bisu daban. Idan kaje ka samu samari daban, 'yan mata daban, in 'yan boko ne daban, in 'yan Arabiyya ne daban, idan matan aure ne ka samu daban, idan karuwai ne ka samu daban, kowa da uslubin da zaka bi saboda duk sanda ka kasa kaya kana son ka sayar kai kasan irin kalmomin da kake fade har mai sha'awa ya taho. Haka ne ko ba haka ba? To wannan hajar Allah ce kake talla. Sannan duk sanda kaga 'ya kana so a gidan nan kai kasan hanyoyin da zaka shiga ka fita kaje a yadda a dauka a baka haka ne ko ba haka ba? Haka duk sanda kaga wani kafiri kana so ka shigo dashi cikin addinin musulunci sai ka tsaya kayi tunani kar kace kawai ai na dauki littafin musulunci na bashi ya karanta, ai na zauna nayi mishi sharhin addinin musulunci me yasa kaza kaza kaza kaza. Mun zauna a yola da wani kafiri wallahi tunda aka fada mishi suna na baya sona ko kallo na baya son yayi, kallo na baya son yayi. Amma ni kuma ban gaji ba yau in dauko kaset in bashi sai ya karba ya kau da kai yana jin nauyi na amma yana ki na. Shi da kanshi yake fada mana haka bara zaku yi mamakin Allah bara sai gashi kawai mun hadu a wurin safa da marwa. In na bashi sai ya kau da kai yace bazai iya wulakanta niyar ki karbe ba amma in ya karba sai yaje ya jefar. Haka haka haka ran nan sai Allah ya taimaka na bashi wani kaset na Ahmad Deedat cewa shin Bible littafin Allah ne? Yace da yaji kaset din sai hankalin shi ya tashi baccin da bai yi ba kenan. Ya shiga nan ya fita nan ya shiga nan ya fita nan yana nema na bai same ni ba. Yace haka ya hakura. Yace sai ya cigaba da muwasala yana jin kasusuwan da da nake bashi wadanda da na bashi zubar wa yake a daki da 'yan littafan da nake bashi na bashi lambar intanet yace bai taba duba ba yace lokacin sai ya tashi wurjan da. Ai shikenan kawai na riga na bar yola lokacin sai ya je musulunta. Ya musulunta ba da dadewa ba mutanen garin shi sai suka tsai da shi takara sai ya zama dan majalissan dokoki. Shine bara kawai sai ya taho aikin hajji. Kawai ni ina safa da marwa kawai sai naje an dafa ka fada ta. Yace ya ustaz sai nace wanene? Sai na duba to sai kai na ya kasa fahimta wanda ka barshi bakin kafiri kuma kazo ka same shi farin mumini a Makkah sai ka kasa gane wanene. Yace Jonathan ne nace Jonathan Jonathan ina yace Jonathan na futi nace Jonathan na futi. Nace ban gane ka ba. Yace to muje dai muka zauna yayi ta mini bayanai har na yadda dai amma kwakwalwa ta tana ganin kamar akwai kuskure. Yace ikon Allah kenan. Ya karba addinin musulunci. To abinda kadai nake so in nuna mana ba wannan labari na so in bamu ba sai ina son ku gane kamar yadda nace in kaga 'ya kana so ko in ka kasa kaya kai kasan kalmomin da kake kai kasan shiga da ficen da kake ko haka idan kaga motar mutum kana so kai kasan yadda zaka bi ka lallabe shi yadda ya siyar maka haka duk wani abu da ka gani kana so ai bazaka zo kana son 'ya a gidan nan ba kazo kace dan Allah kana son 'ya mayun nan. Zai yiu ka fadi wannan kalmar? Zaka ce kai shiga ka kira mini 'ya mayun nan? Bazaka yi wannan kalmar ba koda duk gari ana ce musu mayu kai bazaka yadda ka fada ba. Haka ne ko ba haka ba? Sannan bazai yiu ki zo ki kasa a tampo kina siyar wa ki zo kina cewa wa zai sayi a tampo mai kodau? Zaki yi wannan tallan? Bazaki yi ba. Cewa zaki original a tampo original wax wanene wanene bata zuba bata duk ki geggyara abubuwa. Haka in kazo zaka yi da'awar musulunci sai kayi tunanin wadannan kalmomi zaka fadi wadannan hanyoyi zaka bi wani littafi zaka bashi wani in ka tashi kaset zaka bashi wani abinda yake bukata shine kawai gari ya waye in kun hadu kawai kace mishi hi good morning. Kawai abinda yake so barka barka da asuba. Sai wannan kalmar ta rinka mishi dadi kana girmama shi kana gaishe shi. Wadannan hanyoyin ya kamata musulmi su rinka tsayawa suna nazari a kansu. Ina fatan kun gane. Amma dai gaskiya saboda Allah jama'a akwai alhakin mutanen duniya akan musulmi suje su isar musu da sako dan kunga sahabbai ba yadda muke din nan ba haka sahabbai suka yi ba. Sahabbai bi suke in suka je garin da ba'a jin yaren su sai su samu mai tafin ta suna yin wa'azin da Larabci ana musu fassara. Ina fatan an gane. To Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Malami yace rawahu Muslim Muslim ya rawaito wannan hadisi. Malami yace hadisi na 13 daga sahabi Abu Hurairah Allah ya kara mishi yarda yace annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace Allah madaukakin sarki yana cewa wannan shi ake kira alhadisul kudsi. Shi ya sha banban da al'kur'ani kuma ya sha banban da alhadisun nabawi. In kuka ji a cikin hadisi manzon Allah yace Allah yace to wannan irin maganar ita ba kur'ani bace, ita kuma ba hadisai ne da kika saba jin su ba. Allah yana magana da annabi ne ta zuciyar shi kai tsaye ko kuma ta ainihin wato bacci ko makamantan haka. Amma in kuka ji al'kur'ani shi al'kur'ani ba a mafarki yake zuwa ba a ido biyu yake zuwa kuma mala'ika Jibrilu yake kawo shi. Alhadisun nabawi kuwa maganganu ne na hikimomi da ilimomi wadanda manzon Allah Allah yayi mishi izini ya fada. To amma wadannan maganganu ne wadanda Allah yake saka wa annabi shi yake fada mishi shi ta zuciyar shi ko kuma a mafarki ya gansu. To shine manzon Allah yace Allah madaukakin sarki yana cewa ni ina nan idda bawa na yake zato na. Me wannan hadisin yake nufi? Duk inda kike zaton Allah to Allah yana nan haka in kina zaton Allah zai miki gafara to zai miki. Allah zai azurta ki zai azurta ki. Allah zai baki lafiya saboda baki da lafiya. Allah zai baki haihuwa saboda kina son haihuwa. Allah zai rufa miki asiri saboda kina neman rufin asiri. Allah zai miki duk alherin da kike zaton Allah zai yi. Haka kike zaton Allah to zai yi din. Idan kuma kika waye gari kina zaton cewa wannan ciwon da kike fama dashi bazai yiu ki warke ba to kin muna na zato ga Allah kenan to sai Allah ya bar ki haka. Bawai dan bazai iya ba amma tunda haka kika dauka to bari ya bar ki haka. Idan kika dauka cewa talauci yayi miki yawa yawan da kina ganin bazaki taba fita daga talauci ba bama zai yiu ace ke kin fita daga talauci ba haka kike zato eh sai Allah ya bar ki haka. Idan kina zaton cewa ke din nan bazai yiu ki samu haihuwa ba haka kike wa Allah zato eh sai Allah ya bar ki haka. Dan haka ku gane. Akwai mugun hadari musulmi ya rinka zaton Allah bazai mishi wani abu ba. Duk abinda kake tunani a duniyar nan ka dauka cewa Allah zai iya maka shi indai na daukaka ne, indai na daraja ne sai kuma kaga Allah yayi maka. Amma in ka dauka cewa ni ban isa in samu kaza ba, ni ban isa, ni bazan iya kaza, ni bazan iya kaza ba shikenan sai kaga Allah ya bar ka inda kake tunani. Dan haka duk wanda take da bukata a zuciyar ta a wannan wurin da wadanda zasu saurare ne ta kafofin yada bayanan zamani ta dauka da cewa dukkan abinda ya dame ta Allah zai mata magani. To in kika dauka haka sai Allah ya miki maganin abun. Amma in kika dauka cewa bazai yiu Allah yayi miki ba shikenan sai Allah ya bar ki haka. Allah ya kyauta. To Allah dai yace ina nan inda bawa na ke zato na sannan kuma ina tare da bawa na duk sanda ya ambace ni. Ina ma'anan haka? Zikirin Allah yana faruwa ta dayan hanyoyi guda uku. Hanya farko itace ambaton Allah da baki. Duk sanda kika fada Allah da baki koda cewa kika yi subhanallah ko bismillah
[Segment 7/11 | 02:00:00–02:20:00]
[Speaker seg7-spk:0]
Kin ambaci Allah ko? To a nan ambato da baki, to Allah yana tare da ke. Me kike bukata yasa kika ce Allah zai miki wannan abun da kike bukata. Me kike bukata yasa kika ce Allah zai biya miki bukata. Wannan nau'i na farko na zikirin Allah kenan, nau'i na biyu shine zikirin Allah da gabobi duk abun da gabar ki zata aikata kar ki sai abun da Allah ya yarda da shi. Sannan sai zikirin Allah da zuci shine ki rinka tunanin Allah. Duk abun da zaki aikata sai ki tsaya ki ga. Wannan abun da zan aikata. Ya halatta ko bai halatta ba? Bai halatta ba sai ki bari to kin yi zikirin Allah da zuci. Duk abun da zaki aikata sai kika yi tunanin ya halatta ko bai halatta ba? Sai kika ga ya halatta sai kika aikata wannan abu, kin yi zikirin Allah da zuci sannan kuma kin yi da gabobi. Saboda haka ana ambaton Allah da baki. Ana ambaton Allah da zuci shine tunani game da Allah sannan ana ambaton Allah da gabobi. Duk mutumin da kaga ya durkusa yana sallah yana sujjada me yake yi? Zikrullahi yake yi. Haka Allah madaukakin sarki ce wa Ya ce Ka tsai da sallah saboda ambato na saboda tunani na dan haka munafukai Allah ya ce In sun tashi sallah munafukai tunanin da suke na Allah dan kadan ne saboda su sharri ne a zuciyar su, in suna kabbarta sallah sai sharri ya ta zuar musu, tunanin Allah kadan yake zuwar musu to abun da nake so in nuna muku a nan shine duk sanda kika ambaci Allah Allah yana tare da ke. Ku duba mace ce a kasar ina? A kasar Sham, kasar Syria. Tsakanin kasar Syria da Madina jama'a kamar tafiya ce daga Maiduguri zuwa Potiskum. Wato zaka yi awa 24 kana tuka mota baka tsaya ba sannan ka kai. Tsakanin Maiduguri da Potiskum. Tafiya ce ta wuni daya da kwana daya ma'ana da daga Maiduguri mutum zai fara tuka mota yazo ya wuce ya tafi Potiskum. In ya fara tafiya tun karfe bakwai na safiyar yau Laraba misali. To sai karfe bakwai na gobe. Sannan zai kai. Kenan wannan maganar me take nunawa? Tana nuna tsawan nisan tafiyar da ke tsakanin Sham da kuma Madina amma mace ce wasu suka fado gidan ta zasu ci mutuncin ta. Sai ta rinka Ta rinka cewa wayyo sarki Mu'utasim. Wayyo sarki Mu'utasim. Wannan yana Iraqi. Wata kuma tana cewa Tana cewa wayyo Amirul Mu'uminina wayyo tana kiran Sayyidina Umar. Umar yana Madina yana bacci sai Allah ya kawo wannan kukan cikin kunnen shi. Tun daga can ba warai GSM ba. Ba satellite ba babu wata na'ura kuka take a can. Amma sai Allah ya kawo kukan. Sai da Umar ya hada rundunar yaki. Aka yi tafiyar kwana da kwanaki sai da aka je aka gano matar nan aka zo aka kwato mata hakkin ta akan wadanda suka zalunce ta. Abun da nake so ku gane. Shine duk sanda mutum ya ambaci sunan Allah. Lallai Allah yana nan tare da shi. Ka samu wannan yakinin. Sanda Annabi yayi hijira shi da Abubakar ne Siddik kogo suka shiga. Suka shiga cikin kogon dutse. Da suka shiga cikin kogon dutsen suka zauna. Nan take sai Allah ya kawo gizo gizo sai gizo gizo yayi yana. Kafiran nan ga kafafun su a kofar kogo Abubakar yana ganin kafafun su yana cewa ya manzon Allah kada su durkusa fa su gan mu. Sai manzon Allah yake ce mashi Kar ka damu Allah yana tare da mu. To wace irin mai'iya ake nufi wace irin tare cewa Allah yana tare da mu da zatun shi? A'a Allah yana tare da mu da ilimin shi Allah guda daya ne yana sama amma duk abun da kake yana sane da shi. Wannan itace akidar musulmi. Idan musulmi ko idan bawa ya ambace ne a cikin ran shi kunga kamar yadda na fadi akwai zikiri a cikin rai ko a zuciya. Allah ya ce nima zan ambace shi zan tuno shi a cikin rai na. Idan ya ambace ne a cikin tarin jama'a masu yawa. Sai in ambace shi a cikin tarin jama'ar da suka fi jama'ar da ya ambace ni misali. Da zaka tara mutane ka nai musu wa'azi sai ka ambaci sunan Allah sai Allah ya ji dadi shi kuma sai ya tara mala'iku sai ya ambaci sunan ka. Yanzu da jama'ar ka da jama'ar Allah nawa suka fi alheri? Jama'ar Allah to duk sanda ka tara jama'a a cikin taron jama'a ka ambaci sunan Allah sai Allah madaukakin sarki sai ya tara mala'iku bayin Allah ne tsarkaka ku sai ya ambace ka. Idan bawa ya kusanto ni daidai da dani guda abun da ake nufi da dani guda shine in kika bude yatsin ki kamar kina da kuwa haka to ta zarar da ke tsakanin babban yatsa zuwa yatsa na tsakiya ita ake kira dani guda shibr. To idan ka matsa kusa da Allah ko daidai daidai daidai haka ne sai Allah madaukakin sarki yake cewa. Ko? Ni kuma sai in matsa kusa da bawa na zira'i guda wato kamu guda kamu guda kuma shine daga gwiwar hannu zuwa ainihin yatsan tsakiya. Ma'ana in ka matso kusa da Allah kadan sai Allah madaukakin sarki sai ya ninka kamar ninki uku sai ya matso kusa da kai. Sannan Idan bawa ya matso kusa da ni daidai da zira'i guda Ni kuma sai ainihin wato in matsa kusa da shi wato gaba guda idan kai ka matso kusa da Allah daidai da zira'i guda haka shi kuma Allah sai ya matso gar gare ka haka fadi gaba guda shine a mike hannaye biyu haka kunga yafi naka tsawon ya ninka. Yawwa ana nuna cewa Allah Karim ne Allah yana da alheri in kai mishi kadan sai ya maka mai yawa. In kai mishi kadan sai ya maka mai yawa yanzu zaka dauki naira goma ka bayar sadaka in Allah madaukakin sarki ya tashi sai ya ninka naira goma sau goma sai ya ninka ta sau 700. Shiyasa zaku ga indai ba tsautsayin shirka ba da wahala musulmi ya zauna a wuta. Saboda ka taba yin aikin alheri ko dan yaya to duk sharrin ka indai baka yi shirka ba ana nan ko an kai ka wutan ba a nife a yafe maka ba manzon Allah ya ce wata rana za a waye gari wutan jahannama ba kowa cikin ta. Me ake nufi? Wutan jahannama ma'aikata ma'aikata ce kashi kashi. Akwai Wannan bangaren wutan jahannaman mumine masu sabon Allah su za a zuba. Akwai inda za a zuba maguzawa akwai inda za a zuba kiristoci akwai inda za a zuba munafukai sune can kasa. To duk wanda yake kafiri ne har abada zai zauna a cikin wutan jahannama. Amma wanda yake mumini daidai da imani kwayar zarra in yana da shi sai an waye gari wata ran ya fito shine manzon Allah ya ce za a waye gari watan ba kowa a wutan jahannama me yake nufi? Shine wutan jahannaman da aka zuba musulmi masu laifi. Domin manzon Allah ya ce hankali na ba zai kwanta ba. Ba zan zauna lafiya a aljanna ba in ya zama akwai musulmi daya da ya taba yin sallah ko sau daya ne yana wuta. Annabi ya ce ba zai zauna ba. Zai shiga ya fita. Ya je yayi fadanci a wurin Allah. Yayi zikiri ya girmama Allah. Shine wata rana Annabi na zaune haka suddan sai ya tsage da kuka sai mala'ika Jibrilu ya ya taho ya ce Allah na gaishe ka bayan gaisuwa ya ce me yasa ka kuka ga ka kai dan gata ne ai dan gata baya kuka ko? Yana fara kuka sai a kawo dambun nama nan can sai a kawo juice nan nan sai a zo ana shafa shi to in yayi abun nan sai a dauke shi a dora kan katifa haka ne ko ba haka ba? To me yasa ka kuka kai da kake fiyayyen halitta kai da kafi kowa daraja duniya da lahira? Sai ya ce abun da ya saka ni kuka shine jin cewa wasu cikin al'umma ta zasu shiga wuta. Shine sai Allah ya miki wahayi. To kayi hakuri. Allah zai maka kyauta wadda sai kaji dadin ta wannan kyautar ita ce ranar lahira sai Allah ya ce to shiga cikin wutan jahannama. Duk inda kaga ina ka ina ka ka kwaso su an yafe musu. Kunga ai a ce an dibo maka abu an baka bai kai dadin a ce shiga ka dibo da kan ka ba. Yawwa da cewa za a yi to bari a fito maka da ina ka ina ka sai ya koma yana tunanin me yayi wa akwai saura amma ce mishi za a yi shiga ka kwaso ina ka ina ka sai sahabbai suka ce to ya zaka yi ka gane ina ka ina ka sai ya ce gabobin sujjada. Goshi tafi kan hannaye gwiwoyi da gefen yatsu. Sai ya ce saboda Allah ya haramta wa wuta ta ci duk wata gaba da ta taba kwanciya ta wa Allah sujjada. Dan haka in kika saka goshin ki a kasa to ki bari goshi ya san me yake yi. Ba a dan dandana kadan haka a daga a'a goshi a dandana shi a kasa saboda wannan goshin mai yi wa tsautsayi in ya kai ki jahannama kada Allah ya nuna mana jahannama Allah ya tsare mu Allah ya tsare kowa. Amma da wannan alamar sujjada ce manzon Allah ya ce zai biya ya gaggano ina shi ina shi sannan sai alamar alwala. Kina yin alwala ke musulma ce sai ki tsaya ki rinka wankewa da kyau kar ki rinka tsimbire ko ana sanyi. Alwala tana da alhirai masu yawa daga cikin alhirar ta shine sradi da za a tsallaka duhu ne da shi ba a gani shi. Kuma siriri ne kamar gashi. Kuma gefen shi dama da hagu wutan jahannama ce to ya muka iya wannan alwala ita ce zata tashi tana haska maka dama da hagu. Mumine suna Allah ka cika mana hasken mu Allah ka yafe mu haka zasu taso mumine suna tasowa suna ganin haske har su tsallaka munafukai zasu tashi da haske pau suna zuwa tsakiya sai hasken ya gintse. Sai su juyo baya sai su ga ga wata kofa an kafa ba damar wucewa sannan dama da hagu kuma wuta ce sannan ga mala'iku a ciki kowa ya rike kugiya yana kokarin jawo duk wanda yake kan sradi. Shiyasa Hassanul Banna yaga wani saurayi yana ta tunsura dariya yana buga kafa yana tafawa irin yadda gayu suke in duniya tayi dadi. Sai ya kira shi yace Ka tsallake sradi ne kake irin wannan dariya yace a'a. Yace amma kake wannan dariyar? Yace to ka sani sradi na jiran ka sannan zabaniyawa suna nan Allah ya tattale su. Mala'iku ne wadanda basa jin magana. Basa gani. Abun da suka sani kawai cika umarni in aka ce su fara dukan ka kawai duka zasu ci gaba da yi. Ko kayi salati goma ga Annabi basu sani ba basu ji ba. Ko ka fadi kayi sujjada basu gani ba abun da suka sani kawai su su cika aiki. Allah ya tsare mu. Saboda haka jama'a kun ji idan ka matsa ga Allah daidai da zira'i kamu guda sai Allah ya matse ka kai kuma gwargwadan ainihin gaba guda. To kun ga ko in Allah ya tarbe ka haka ai sai kuma a rungume ka kenan kai kan kasa mu shiga. Allah ya ce idan bawa na ya taho gare ni yana tafiya a hankali Ni kuma sai in zo wurin shi cikin gaggawa da sauri idan ka taho gurin Allah a hankali a hankali sai Allah ya tarbo ka cikin gaggawa shi kuma wannan hadisi yana tabbatar mana da cewa Allah yana da rahama ga bayin shi domin duk abun da kai shi kuma sai ya maka fiye da haka. Allah ya mana da kyau. Hadisi na 14 Jabiru dan Abdullahi Balansari Allah ya yarda da shi ya ce Wani mutum yazo wurin Annabi Ya manzon Allah Wadan na abubuwa guda biyu ne suke mutum shiga aljanna da kuma shiga wuta abubuwa guda biyu ne daya yana sa lallai ka shiga aljanna. Daya kuma na sa lallai ka shiga wuta wadan na abubuwa ne Sai manzon Allah ya ce Wanda duk ya mutu baya shirka baya hada Allah da komai zai shiga aljanna. Jama'a kun ji. Duk wanda ta san ta taba zuwa gidan boka ko dan tsubbu ko dan sihiri ko anje an bata wani magani ance ki makala wannan a cikin farjin ki ya kwana in gari ya waye ki kawo shi za a yi aiki sai yadda kika ce da mijin ki. Duk wanda tayi haka jama'a. Da ita da bama gujiya fa wanda bata taba sallah ba duk daya ne imaninta ya lalace. To lallai sai ta tuba. Idan ko bata tuba ba to matsala ta faru. Allah ya kyauta. Wanda ya rasu yana hada Allah da wani abu shi ko wuta zai shiga. Daga Abu Huraira Allah ya kara mishi yarda ya ce Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gare shi ya ce Allah ya kara wa Abu Huraira yarda ya ce Manzon Allah ya ce Musulunci ya fara yana bako sanda aka fara musulunci jama'a musulmi ana ganin su baki ne. Ana cewa sun zo da wani bakon addini misali wata rana Annabi da sahabbai suna tafiya a cikin daji sai lokacin sallah yayi aka zo babu ruwa kuma a lokacin hukuncin taimama bai sauka ba aka rasa ya za a yi sai manzon Allah ya cewa Aliyu kai Aliyu zo nan sai aka kira wani mutum aka ce ku je duk inda ruwa yake ku samo suka shiga daji suna cikin tafiya sai suka ga wata mata. Ba musulma bace gata ta dibo ruwa dama da hagu tasa a cikin jakunkunan salka ta dauko ruwa akan rakumi. Sai sayyidina Ali ya ce da ita ke baiwar Allah ina kika samo ruwa? Sai ta ce cap dija. Ta ce kun ga tsakani na da inda na samo ruwan nan suka ce eh to tun jiya iwar haka nake tafiya. Ta ce to ai mukan dai yanzu muke son ruwa dan haka kenan wato naki za muyi amfani da shi. Sai ya ce mata mu je. Ta ce ina? Sai ya ce zuwa ga Annabi Sai tayi shuru sai ta ce Wannan da aka ce yazo da sabon addini? Sai Aliyu bai ce eh ba sai ya ce wannan dai da kike nufin domin ita mushirka ce zata iya cewa Annabi yazo da sabon addini amma Aliyu ba zai yarda da wannan maganar ba. Dan haka in yace mata eh ya yarda kenan sai ya ce wannan dai tun da kin gane shi to mu je. Aka tasa kiyar ta aka kai ta ga manzon Allah aka je aka durkusar da rakumi ta sauka ta koma gefe guda ta zauna. Annabi yasa aka kawo wani katon baho sai aka zazzage ruwa sai ya dibo ya guntsa a baki ya kurkura bakin shi sai ya mayar da ruwan da ke ciki sai yayi addu'a sai ya ce jama'a kowa yazo ya dibo. Wannan yazo da bokiti ya kandama kana dibo sai ruwa ya koma yadda yake. Suka dibo suka yi wanka suka sha suka biya bukatun su gaba daya aka gama sai aka dibo ruwan ta sai aka mayar mata yadda yake sai manzon Allah ya ce ki dubi ruwan ki da kyau bamu rage miki komai ba. Ita dai baiwar Allah tana zaune tayi shuru to manzon Allah mutumin kirki ne manzon Allah yafi kowa alheri a duniya da lahira jama'a. Idan da dan ta manzon Allah ne ma fa ba wanda zai shiga wuta kowa ma sai a bude mai aljanna kawai ba হিসাব ma. Eh shine mawaki yake cewa Manzon Allah tunda yake baya cewa la sai dai Duk abun da kazo kace ya manzon Allah a bani kaza manzon Allah baya cewa babu. In babu sai ya ce zauna. Allah zai kawo ana nan ko sai kuga Allah ya kawo. Shiyasa duk wanda aka kuntata mishi sai ya gudu ya tafi wurin manzon Allah Wani mutum azumi ya shiga yayi wa matar shi zihari cewa wata guda ba zai sadu da ita kaza kaza kaza kaza can kuma ya ce sai bukata kawai sai ya je ya fada to yanzu tsautsayi ya faru ya za a yi ya je malamai suka ce zaka yanta wuya guda na bawa ya ce ba hali suka ce zaka ciyar da miskini 60 ya ce ba hali suka ce to zaka yi azumin wata biyu ya ce ba hali. Suka ce to ba halin ka je kayi laifi sai sai ka san yadda zaka yi. Ba rahama ba tausayi iya karfatawa kenan malamai suka hada mishi bango. Sai ya gudo daga kauye sai gudo Madina yazo wurin manzon Allah ya ce ya manzon Allah ga abun da ya faru. Manzon Allah ya ce kana da wuya guda da zaka yanta aka ce mutum ne mai barkwanci mai wasa da dariya sai ya ce ya manzon Allah duk duniya in ba wuya na ba ba wuyan da na mallaka. Maganar yanta bawa bata taso ba bani da shi. To zaka iya ciyar da miskinai 60 ya ce cap dija jiya gida na da yinwa aka kwana ma'ana nima miskini ne ina zan na kasa ciyar da gida na zan ciyar da gida guda 60. Manzon Allah ya ce mishi to yanzu abun da za ayi zaka iya yin azumi na wata biyu a jere. Sai ya yi dariya ya ce cap manzon Allah kenan azumin wata daya ne ya saka ma a wannan rikicin an kasa fita in muka ce za muyi na wata biyu kuma rikici ai zai kara rikicewa. To yanzu ya za a yi sai manzon Allah ya ce ka tafi kauyen ku akwai mutumin da na sa ya tattara zakka ka ce ya dibi zakka ya baka idan ya baka ka je ka ci da iyalan ka ita ce kaffara. Ku duba mutumin da ya fito kauyen su da laifi ance ba gaffara ba yafewa sannan sai yayi sadaka sai yayi azumi ya ce ba hali sunce dole sai yayi yanzu ya komo kauyen da farin ciki ga
[Segment 8/11 | 02:20:00–02:40:00]
[Speaker seg8-spk:0]
abinci buhu buhu shine da ya koma kauye, kun san mutanen kauye in aka in aka maka abun haushi, in ka koma asirin ka ya rufe, sai kaje sai kaje ba dala wato irin inda ake shan rake din nan da rana inda ake cin alala in yamma tayi, inda ake shan koko gari ya waye, kauye kenan, kofar kauyen kenan, da yaje sai ya daga hannu yayi ihu mutanen gari duk suka fito lafiya wane yace lafiya ta kawo haka yace na samu kunci da muguwar fatawa a wurin ku, naje wurin manzon Allah na samu rahama manzon Allah yace a dibi zakakkwa a bani in ci kun gani manzon Allah sallallahu alaihi wasallama mutumin kirki ne mai alheri ne wani yazo ya gaishe shi da ya tashi zai tafi sai manzon Allah yace ku bashi raguna, guda nawa sai yace ku bashi guda dari mutumin kauye a bashi rago dari tsaraba da yaje shima ya tsaya a bada la kauyen su yayi ihu jama'a duk suka fito aka ce lafiya yace ku duba, aka ce eh mun ga raguna ina ka samu su yace ku je ku musulunta wurin Muhammadu Muhammadu na diban dukiya yana bayar wa baya tsoron talauci yace kun ga gaishe shi naje nayi kun ga tsarabar rago dari manzon Allah bai san bai san ainihin sharri ba sai alkhairi maganar da nake fada mana itace siffa daga cikin siffofin manzon Allah sallallahu alaihi wasallama itace karimci itace alheri, itace kyautatawa, to abun da ake so musulmi ko baka da hali ka dan samu wani abu da zai bayyana kaima kana son alheri yadda za'a gane randa ka samu hali zaka yi alheri ma'ana a cikin gida ne kuna zaune sai wance ya zama bata da a shana, sai kika ji tana ci giya a shana, kafin tazo ta tambaye ki sai ki ce mata ga a shana ba abun da alheri zai rage ki fa sai dai ya kare ki saboda manzon Allah yace Allah yana da wasu mala'iku guda biyu, kullum gari ya waye addu'a suke suna cewa ya Allah duk wanda ya dauka ya bayar Allah ka mayar mishi kuma ka ninka mishi kuma addu'a suke suna cewa ya Allah duk wanda ya maki ya ki taimakawa Allah ka dora mishi asara, sai kuga mutumin da baya taimakawa sai kuga kullum asara yake yi to Allah ya tsare mu Allah ya taimaka to kun dai ji jama'a sai yace wanda kuma ya mutu yana hada Allah da wani abu to zai ainihin shiga wuta kamar yadda nace babu shakka a son manzon Allah to ba wanda Allah zai azabtar kamar annabi Isa ne alaihis salam ku saurara kamar annabi Ibrahim ne wadannan annabawan suna daga cikin annabawa masu taushin hali su basa son Allah ya azaba ko ka saba musu annabi Isa cewa Allah yake ya Allah in kai musu azaba to ba yadda za'ayi bayin ka ne amma da zaka gafarta musu kai buwayayen sarki ne Allah kafi karfin ko menene wato annabi Isa yana da laushin zuciya, yana da saukin hali, abun da yake nufi koda ka saba wa Allah in Allah ya maka azaba to daidai ne dan ba'a cewa Allah yayi ba daidai ba, amma kuma in Allah ya yafe maka ai dama Allah ya mafi karfin yafewar shi mai yafewa ne annabi da ya tashi sai ya kwatanta Abubakar ne Siddiku da annabi Isa da annabi Ibrahim Abubakar ne Siddiku mutum ne mai saukin hali Sayyidina Umar kuma fa to shi kuma lallai kan in kayi to ayi maka shiyasa da akayi yakin Badar aka kama kafirai saba'in aka daure su, aka kashe saba'in, sai aka kira Sahabbai Abubakar da Umar da Aliyu neman shawara, kun ga dai mutanen nan su suka kore mu daga kasar mu, su suka wulakanta mu, su suka ci mutuncin mu, yau gashi mun kashe saba'in mun kama saba'in, me kuke ganin za'ayi sai Sayyidina Abubakar yace ni abun da nake gani wadannan mutane yan uwan mu ne mun zo da addini sun kasa fahimtar mu kuma Allah ya ga cewa mu mutanen kirki ne ya bamu nasara a kan su dan haka kada mu kashe su mu dora musu fansa yan kudi kadan su biya mu, mu sake su su je in Allah ya nufe su da musulunci zasu zo suyi in Allah bai nufe su da musulunci ba su tafi dai mun riga mun karya lagon su kun ji fatawa Abubakar, kun ga ai akwai saukin hali a nan to Umar kai me kake gani yace a'a ra'ayin Abubakar ba daidai bane mutanen da suka dake mu suka kashe mu, suka kore mu daga kasar mu, yau mu samu iko a kan su mu kyale su, ni abun da nake ganin ma za'ayi mu zagaya cikin su kowa in yaga dangin shi daga ciki to ya kama ya danne shi ya yanka kawai cewa to anji taka kai kuma Umar to kai kuma Aliyu fa sai yace ai duka ra'ayoyin ma sun yi sauki da cewa ma wai a a sake su a karbi kudi da cewa ma kowa ya dubi dan uwan shi daga ciki yace ni shawaran da nake gani a je a samu daji wanda ya bushe rani ya dake shi, itatuwa sun bushe, a je a dora mutanen nan a ciki a kunna kalanzir da a shana, baki dai su su kone, Allah ya san da gaske muke yin musuluncin nan manzon Allah kullum aka kawo abubuwa sai ya dubi mai sauki sai ya dauki fatawa Abubakar aka dora mutanen fansa aka sake su, amma sai ga aya tazo, tana nuna cewa da ace an karbi ra'ayin Umar da haka Allah yafi so shiyasa lallai ne manzon Allah yana son sauki, amma kuma ba kullum ne sauki yakan ainihin dace da wasu nau'in mutanen ba saboda wasu mutanen jama'a sai an fesa musu attarugu a ido sannan suke gane ina aka fuskanta alkibla to wannan kenan ko ai mun wuce wannan hadisin ma ko ashe ina kan yauwa har na kawo kissa waccen mata ko, yayin da wannan mata duk aka gama wannan al'amari tana mamaki sai annabi yace a shimfida zani jama'a, da aka shimfida zani sai yace jama'a kowa ya tara mata kyauta, wane yana da kudi sai ya kawo ya zuba, wane yana da abinci, aka tara mata kudi da abinci buhu guda haka sai manzon Allah yace a dora ta akan rakumi aka dora ta, aka kawo ruwan ta aka mayar mata sai yace baiwar Allah kinga dai bamu rage miki komai daga ruwan ki ba tace eh sai yace to wannan kuma alheri ne ni da jama'a ta mukayi miki Allah ya sauke ki lafiya ta tafi mamaki ya cika ta kawayen ta da suka dibo ruwa suka taho bayan ta sai suka zo suka wuce ta, suka isa gida, suka tambaya ina wance aka ce bata iso ba, amma ai ta riga mu tahowa, ana mamaki sai ga ta, wance lafiya kin riga mu tahowa mun riga ki isowa sai tace kun ga mutumin nan da yazo da sabon addini to indai ba matsafi bane to tsakanin sama da kasa a duniyar nan ba wanda yafi shi gaske suka ce ya akayi sai ta basu labarin abun da ya faru haka matan nan ta zauna sai Allah yasa mata son musulunci a zuciya to abun da nake so ku kiyaye ku tuna magana ta ta dazu da nace kyautatawa mutane yana jawo su cikin addini kyautatawa mutane yana jawo su cikin addini yanzu a Lagos ana da wasu fitsararrun yara sunan su Area Boys sun gagaru kowa suna iya zuwa su kashe anguwa guda duk abun da suka ga dama zasu iya yi amma menene abun da muka bincika a kai bara na tafi naje nayi bincike akan yan Area Boys sai na gane mafi yawancin su musulmi ne ashe idan watan azumi yayi in suka tare ka zasu kwace maka kudi ko zasu dake ka ko suyi abun nan in suka ji kayi kalma ta musulunci sai suce Allah ya soka kana azumi ina azumi sai yace amma in aka sha ruwa na hadu da kai ka shiga uku eh in aka sha ruwa ya hadu da kai ka kade Allah ya kyauta shine sai nace kun ga har yadda za'ayi a tara kudi masu yawa a je da watan azumi a bi masallatai ana kai abinci ana kiran Area Boys din nan suna cin abincin dan zaman da zasu yi minti biyar minti goma sai a rinka musu nasiha zasu dawo su gyaru abun da ya kai su ka zama Area Boys irin maganganun da na fada jiya wani uban shi ya mutu kishiyar uwa mai azaba ce sai ta azabtar da shi sai ya gudu karkashin gada in ya gudu karkashin gada shikenan sai su dafe shi sai suyi training din shi sai su koyar da shi yadda ake iskanci zaku je cikin su zaku ga mata a nan karkashin gada nan ne gidan su, bata da kowa a nan za'ayi mata ciki ta haifi yaya biyar ita ma ta tsallake ta gudu ta bar su ita ma bata san dangin ta ba balle yayan da ta haifa a karkashin gada barna kara yaduwa take yi amma gwamna Buba Marwa da yazo sai da yayi aiki wajen dawo da Area Boys ya za'ayi a ci amfanin su babu wani gagarrarre sai bararre rashin aikin yi yana damun matasa maza da mata shi yasa suke kirkiro wa kan su mafita to kuma duk sanda aka bar yaro ya samar wa da kan shi mafita to zata baci shi yasa babu shakka wannan mata da annabi ya kyautata mata sai ta rike kyautatawa nan a rai ashe annabi ya gano kauyen ta idan ya tura Sahabbai yaki sai yace in kun je karku shiga kauye kaza a cikin kauyen akwai wata mata ta taba mana alheri ita wannan mata mai basira ce ita kuma ta lura in Sahabbai suka taho kawo hari sai su tsallake kauyen ran nan sai ta tara mutane a kofar fadar daga cin su tace ranka ya dade mutanen nan masu zuwa suna kawo yaki suna tsallake mu saboda na taba musu wani alheri ne me yasa bazamu rama alheri da alheri ba mu je mu shiga addinin su sai sarki da jama'a aka amsa mata gaba daya sai aka ji aka shiga addinin musulunci wallahi jama'a mutane daawa suna bukatan a kyautata musu, yanzu sarkin musulmi na yanzu Muhammad Sada yawo yake yi kasashen arna har America sai da yaje aka tara manya manyan kafirai hadda ra'asul kufri hadda bushi ya mike yayi musu bayani yace to shi jikan dan Fodio ne kakan shi yazo ya yada addinin musulunci a Nigeria yau ya waye gari shi yake zaune a kan kujerar kakan shi, shine yake yawo duniya dan ya tunasar da su gama da aikin da kakan shi yayi na yada musulunci haka ya rinka bin kasa arna kasa arna bara muna Lagos aka bugo mana waya aka ce ai akwai wani sarkin arna Hamshaki a jihar Delta ya karbi addinin musulunci bayan kwanaki uku ko hudu da zuwan da sarkin musulmi yaje yayi mishi wa'azi abun da muke so manyan mu suyi kenan Allah cewa yayi abun da Allah ya baka a nan duniya ka nemi lahira, duniya ba wurin zama bace kayi gida, ka sa kaza, ka sa kaza, kwana biyu sai a fasa hannu a kawo a ce ya mutu, shikenan shi yasa wani yace wa malamin shi Allah gafarta malam me yasa mutane basu san basu san mutuwa ne sai yace kamar mutum ne ya taho cirani, yaki komawa gida, yasan bayada gona, yasan bai gyara gida ba, yaushe zai yadda ya koma, yace duk wanda kuka ga baya son mutuwa yasan cewa bai shirya lahiran bane haka ne ko ba haka ba haka ne in aka ce ana ruwa kuka ji mutum yana tsoron fitowa bashi da laima ne in yana da laima baya tsoron fitowa kenan wannan addinin musulunci jama'a lallai ne mu je mu yada shi amma ina gaya muku wannan sanda musulunci yazo duk duniya yawo ake ana cewa yazo da wani sabon addini yazo da wani sabon addini amma abun da yazo da shi ba sabo bane domin annabawan da suka wuce shi suka zo da shi sai yace kuma addinin zai koma kamar yadda ya fara yana bako to haka zai koma ina ma'anar wannan maganar, za'a waye gari idan kayi aiki da musulunci sai a ce ya kawo bakuwar sallah, ya kawo bakon azumi, zakkan ma ko
[Segment 9/11 | 02:40:00–03:00:00]
[Speaker seg9-spk:0]
Eh
[Segment 10/11 | 03:00:00–03:20:00]
[Segment 11/11 | 03:20:00–end]Annotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Hadisai 100. Daarul Hadeethis Salafiyyah. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15866.
Zaria, M. A. A. (s. d.). Hadisai 100 [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15866
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Hadisai 100. Daarul Hadeethis Salafiyyah. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15866.
Télécharger
Visualisations
Chargement des visualisations…


