document audiovisuel · Daarul Hadeethis Salafiyyah Citer
Illar bara da tumasanci da bambadaci da maula a musulunci (Wa'azin Zaria)
- Type
- Enregistrement vidéo
- Créateur
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Editeur
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- numéro
- 1
- 2
- 3
- 4
- Est une partie de
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Importance matérielle
- 164 minutes
- Support
- DVD
- Sujet
- Wa'azi
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000016
- contenu
-
[Segment 1/9 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yan uwa masu kallon mu da sauraron mu da wadanda zasu kalle mu kuma su saurare mu ta kafofin yada bayanai na zamani. Kuna sauraron mu tare da kallon mu ne kai tsaye daga babban dakin taro na ainihin makarantar mu mai suna da ke nan Zaria a Nigeria. Yanzu da muke magana karfe goma na safiya ta ranar asabar ta wuce wadda ta dai dai da ashirin da hudu ga watan Shawwal. Hijira na da shekara dubu daya da dari hudu da talatin da hudu. Wadda ta dai dai da talatin da daya ga watan Agusta shekara ta dubu biyu da sha uku. Wannan wa'azi da kake kallo da saurare da kuma wannan lacca yana da wani dogon tarihi. Na daga cikin dogon tarihin shi ne gayyata ce wadda na samo kusan watanni biyu da suka gabata. Daga yan uwan mu Ahlussunna matasa na garin Rigachikun da ke ainihin karkashin Igabi Local Government a nan jihar Kaduna a Nigeria. A karkashin jagorancin shugaban majalisar malamai ta kasa Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun Allah ya saka mishi da alkhairi.
[Speaker seg1-spk:1]
Amin.
[Speaker seg1-spk:0]Lire le texte intégral — 21 576 mots restants Réduire le texte intégral
Na'am samu su cewa zan yi wannan lacca in Allah ya so wadda an sa ta ashirin da shida ga watan Ramadan ko ashirin da bakwai. Kuma Allah cikin iyawar shi ya bani iko na je na gabatar da wannan lacca. Taken laccan ya kawatad da ni kwarai da gaske. Shi yasa na ga cewa wannan lacca ya kamata in zo nan makarantar mu maimaita ta kuma in kara fada ta in kuma kara mata armashi da karin wasu dalilai da tattauna wadansu bayanai. Sannan kuma wannan laccan in sha Allahu ta'ala na yi alkawari zan cigaba da gabatar da ita a mafi yawancin bangarorin arewacin Nigeria musamman. Wannan laccan in Allah ya so na yi alkawari zan gudanar da ita a cikin garin Makkah a tsakiyar yan uwa na Hausawa. Ba dan komai ba saboda na san cewa wannan lacca lallai in ta shafi kowa to tafi shafar yan uwa na Hausawa wadanda ke arewacin Nigeria da kuma wadanda ke wasu bangarori musamman ainihin a cikin garin Makkah a unguwannin da Hausawa suka ainihin fi yawa kamar Shari'ar Mansur da ainihin wadansu unguwanni wadanda ke kusa da ainihin harami kamar Misfala Nakkasa da Kunkariya da makamantan su. Allah madaukakin sarki ya taimaka. Taken ainihin wato lacca tawa shugaban malamai na kasa na ce ko? Shi ne na kasa ne ai ba na jiha ba. Mataimakin shugaban malamai na kasa na'am. Taken lacca tawa shi ne da tumasanci da roko da maula da bambadanci a musulunci. Illar bara da tumasanci da roko da maula da bambadanci a musulunci. Ita dai kalmar kalma ce ta Larabci amma Bahaushe ya areta ya shigo da ita Hausa saboda irin karfin da harshen Larabci ya samu yi a cikin harshen Hausa da kuma tasirin shi. Kuma malamai masana ilimin fassara suka ce dukkan san da wani yare ya ari wata kalma kuma ta samu gindin zama a cikin wannan yaren to in ka zo kar ka yi wahalar fassara ta. Dan dai duk inda ka samu Hausawa ka ce to shikenan sun gane abun da ake nufi shi ne da barna da kuma matsala da kuma hadarin da wannan abun ke haifarwa. Na haka Ita kuwa kalmar to kalma ce ta Hausa wadda ba wani abu take nufi ba shi ne roko da sunan addini. Shi ne Bahaushe yake nufi roko da sunan addini. Idan rokon ba da sunan addini bane Bahaushe baya kiran shi bara. Na haka duk inda ka ji an ce bara to roko ne ake nufi amma da sunan addini. Na haka zaka ga rokon ya dauki salo iri iri. Zaka ga almajirai yara kanana in suna yawo bara ake cewa saboda almajirai ne. Wadanda suke koyon karatun Alkur'ani ka ga suna da alaka da addini. Na haka sai a ce suna bara. Idan ka ga kutare da makafi da sauran masakai sai a ce suna bara domin kalmomin da suke amfani da su kalmomi ne irin na malamai da almajirai. Zaka ji suna cewa Wato ainihin Allah shi ne Sannan shi Allah shi ne To amma saboda rashin iya Larabci sai ka ji sun ce Ina fata an gane to ka ga wannan bara ce roko ne da sunan addini to dan haka sai aka kira ta bara. Na haka duk inda ka ji an ce bara da Hausa to ana nufin ainihin roko wanda ake amfani da wasu kalmomi na ainihin addini. Shi yasa zaka ji yara kanana suna cewa Zaka ji yana cewa Yanzu da karfi a cikin musulmin Nigeria ta arewa har sai ta yi tasiri akan bara da yara kanana suke. Sai ka ji in yaro ya je zai yi bara sai ya ce To wannan tasirin ne a cikin yan arewa. Allahu akbar. Ina fata an gane. Dan haka wannan bara zamu yi magana akan ta wato bara da sunan addini ko roko da sunan addini. Tumasanci kuwa abun da ake nufi da shi a harshen Hausa shi ne mutuwar zuciya ta haifarwa da mutun zaman banza. Zaman banzan kuma sai ya haifar da roko. To kawai shi ne ake nufi. Tuma shi ne gashi nan Abundant wato gashi nan kawai ya ya mutu zuciyar shi ta yayi watsi da kanshi shi kanshi to shi ne Bahaushe yake cewa tuma. To tumasanci ana siffanta abun ne amma sai ya koma ana kiran shi da sunan abun. Ma'ana mutumin da zuciyar shi ta mutu sai ya je tuma a kofar gidan wani mai kudi ko attajiri ko mai mulki ko dan siyasa ko dan boko. Idan mai gidan ya fito sai ya kara tumasancewa shi ne sai ya kara takwarkwasewa ya kara kwanciya. Da in yana zaune ne ya mike kafar shi da mai gidan ya fito sai ya zamanta hiya sai ya kwanta haka. Shi ne tumasanci. Zuciya ta mutu kuma ya zo ya jepar da kanshi a wuri guda kuma yana roko da sunan wannan mutuwar zuciya shi ne ake kira tumasanci. Kalmar roko kuwa dama ita ce asalin kalmar. Amma sai Bahaushe ya ringa duban salon da ta shiga sai ya ringa kiran ta da wadannan suna bara tumasanci da sunan su. Shi ne tambayar abun hannun wani kawai tambayar abun hannun wani shi ake kira roko. Ita kuwa kalmar maula ita ce kalmar bara. To amma Hausawa sun areta daga Larabawa saboda sun ji yayan Hausawa in suna bara kamar yadda na fada ya dazu suna cewa To sai ta zaman maula din asali abun da take nufi shi ne mai gida na ne kai na zo ina rokon ka shi ne ma'anan maula. Kai mai gida na ne to amma da yake rashin sanin Larabci sai aka juye ita kalmar maula din sai ta zaman ita ce kan ta rokon ko barar. Na haka sai suke cewa Ina fata an gane. Na haka kalmar maula din abun da kawai suke nufi da ita roko amma asalin ta abun da take nufi na zo roko a wurin ubangida na. Bambadanci kuwa ma'anan shi roko. Amma fulatanci ne sai Bahaushe ya aro shi. Shi ne zaka ji an ce wane bambado ma'ana maroki kawai. To maroki a kasar Hausa ba da sunan addini yake yi ba. Yana yi ne da matsayin al'ada ce daga cikin al'adu na kasar Hausa da kuma wadanda suka shafi Hausawa. A gidan suna da gidan biki kuma ba da sunan addini yake ba. Amma saboda tasirin da addini yayi wa Hausawa daga baya baya din nan sai maroka suka koma suka dena bambadanci sai suka koma suna ainihin yin roko da sunan addini sai ya koma ya zaman bara. Har ma wani marokin sai ka ga ya tsuguna gaban ka ya ce In an je gidan suna ko gidan biki ya nemi maka da nufin raha ne amma da gaske yake yi. To wannan kalma ta bambadanci da Bahaushe ya aro ta da fulatanci to bai barta a wannan ma'anar kadai ba. Abun da Bahaushe yake nufi da bambadanci shi ne roko wanda ya hada da kirari. Roko wanda ya hada da kirari ana ana cewa wane dan wane jikan wane dan gidan kaza mai kaza to shi ne sai Bahaushe ya ce ga yace yana bambadanci. Ina fata an gane. Bara da tumasanci da roko da maula da bambadanci a cikin wannan lacca tawa na ce zan yi magana dangane da illar su in sha Allahu a cikin addinin musulunci. Wato wadannan abubuwan gaba dayan su suna da illa. Illa tun daga nan duniya har kabari har lahira. Illa tun daga wannan rayuwar taka har yayan ka har jikokin ka har tattaba kunnen ka wadannan abubuwan suna da hadari. Jama'a kun ji taken lacca tawa. Dan haka abu na farko da zan yi magana a kai kenan gashi nan na kawo maka wadannan bayanai yanzu ka ji abubuwan da zan yi wa'azi a kan su. To amma dan kada wani ya kuskura fahimtar wa'azi na ya ce to su Albani sun koma suna suka dangane da sadaka kenan dan ka san akan yi haka wajen kuskuren fahimta. Abun da wa'azin ka ya dosa daban inda kuma wani zai karkata ya fahimce shi daban. Sai na ware zan yi magana dangane da falalar sadaka amma da dukiyar halal. Ke nan wannan wa'azin nawa baya nuna cewa haramun ne ka bada sadaka kuma baya nuna cewa haramun ne kai ka karbi sadaka. Amma ana cewa haramun ne ka mai da bara ta zaman maka ita ce hanyar rayuwa ko kuma hanyar tara arziki. Amma in wata larura ta kama ka shiga daya daga cikin wadanda suka halatta su ci sadaka to in an baka sadaka zaka iya ci. A karkashin wannan kun ga na yi kokarin daidaita tunanin kenan in nuna illar da ke tattare da bara amma kuma in nuna cewa sadaka tana nan tana da falala a cikin addinin musulunci. Sannan in sha Allahu ta'ala zan yi magana dangane da falalar kamewa kana fama da babu da talauci da rashin da kunci amma sai ka daure ka kame ka kara rufawa kan ka asiri a bisa rufin asirin da Allah yayi maka. To akwai falala dangane da haka in sha Allahu ta'ala zan yi magana a kai. Sannan abu na hudu da zan yi magana a kai shi ne hadarin roko da bara da bambadanci domin ainihin tara dukiya. Wato wasu ba su ne ne dan su samu abinci ba. Wasu suna yi ne domin su tara dukiya. Na haka zaka ga akwai yan uwan mu da yawa a Lagos da Ogomosho da Ilori da Makkah da Madina. Akwai su da yawa a filin Arafat akwai su da yawa a Mina da Muzdalifa in an taso aikin hajji. Zaka gan su suna bara. Amma in ka dawo birnin Kano ko Sokoto ko Katsina ko Zaria zaka same su da gidaje masu yawa. Suna ainihin yin barar suna ainihin turo da dukiya nan gida domin a ajiye musu. Zaka ga daga cikin irin wadannan mutanen akwai wadanda suka mai da bara ta zama company. Suna diban yayan musulmi daga garin Bidda suna zuwa garin Kwantagora suna zuwa nan kasar Zazzau da Katsina da Kano suna diban yaya suna kai su aikin hajji. Da sharadin cewa wadannan yayan za a biya musu za su je su yi hajji. Amma kuma za a daddasa su a filayen Arafat da Muzdalifa da kofar Ka'aba su ne suna bara sannan an sanya musu wani ainihin wato manaja wanda shi ne yake tsaye idan ya hangi wancan tayi tari sai ya je ya karbi. In ya hangi wane yayi tari sai ya karbi. Har da bulala a hannun shi. Idan ya lura cewa wane yana da wani aljihu da yake soke wani abu sai ya ga yana tsula mishi yana horan shi. Duk akwai irin wadannan in sha Allahu ta'ala. Allah madaukakin sarki ya kiyaye. Saboda tattalin wannan lacca jama'a har wani documentation har camera na sa na ringa daukan su a wani lokaci na aikin hajji jama'a saboda tattarawa da ire ire wadannan bayanai. Yayan Hausawa ne Hausawa ne matan aure ne karti ne wasun su ma sun san mu dan akwai wata da ta san ni wadda ta ta hange ni da lasifikata ina wa'azi. A ainihin dai dai wurin jifon shaidan sai ta karce a guje. Gudu na fita hankali sai na zo na tambayi sauran almajiran sai ta ce ta ce ta san ka ne ita yan Zaria ce. To kun ga duk irin wannan shi yasa za a gan su da nikabi. Allah madaukakin sarki ya kiyaye. Sannan dan kar ka fahimci cewa fa haramun ne cin sadaka ga kowa da kowa zamu tattauna wata matsala mai muhimmanci ita ce wanda duk ke zaune ba bai roka ba bai yi bara ba bai kallafa ran shi ba sai aka kawo dukiya aka bashi kyauta ko sadaka to in yana bukata babu lefi zai iya karbe shari'ar musulunci bata haramta ba. Sannan daga karshe zan yawaita magana in sha Allahu game da halarcin bara sannan kuma in cike lacca tawa game da falalar neman halal. Amma ta hasken ilimin addinin musulunci. Halal tana da falala ka neme ta ya kai dan uwa musulmi. Amma kuma lallai ka san cewa wajibi ne ka je a koya maka mai Allah ya ce mai annabi ya ce. Dan haka wa'azi na zan faro shi daga wadda ita ta sauka ne ainihin a garin Madina. Gari na Madina gari ne na kwama chalar kabilu ka ga dai akwai Larabawa Qurayshawa Zalla sune su annabi da Abubakar da Umar da Usman da Ali. Wadanda wadannan asalin su muhajirai ne. Amma sun wayi gari suma sun zama a Madina suke. Akwai wadanda suke Larabawa ne ba Qurayshawa ba. Suma muhajirai ne kamar Ash'ariyawa su Abu Musa al-Ash'ari daga Yaman suke. Da kuma Dausawa sune su Tufailu da su Abu Huraira. Akwai wadanda suke kuma ainihin su Larabawa ne ba Qurayshawa bane kuma su ba yanci rani bane a garin Madina. Sune kabilan Ausu da Khazraj wato Ausawa da Khazrajawa. Ausawa ba Hausawa ba Ausawa da Khazrajawa. Akwai su a Madina sune su Jabir su su Anas dan Malik da makamantan su Allah ya kara musu yarda. In ka dube Madina ta bangaren abun da ya shafi addinai akwai musulmi sune annabi da sahabbai muhajirai da ansarawa. Idan kuma ka ainihin koma bangare guda zaka ga akwai Yahudawa da Kiristoci. Sannan a tsakanin musulmi da ainihin Kiristoci da kuma Yahudawa akwai wasu wadanda ke kai da komo sune munafukai. Sama da su shi ne Abdullahi dan Ubayyu dan Salul. Allah madaukakin sarki ya tsare mu daga makircin su. Sannan ka dawo ka dube Madina ta wani bangaren kuma zaka ga cewa Madina babban birni ne na ainihin kasuwanci. Domin duk wani kasuwanci sai da ya zama ana yin shi ainihin a Madina sannan kuma duk wasu nau'i na yan kasuwa suna ainihin tahowa daga mafi nisan wuri suna zuwa suna raya ainihin wato kasuwancin Madina. Akwai manya manyan kasuwanni
[Segment 2/9 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
wadanda ke ci yau da kullum. Akwai kasuwannin mako, akwai kasuwannin wata, akwai kasuwanni na kwata, wato kasuwanni na bayan watanni uku ko hudu. Akwai kuma kasuwanni na shekara. Sa'annan kuma akwai kasuwanni wadanda yanayi ne yake haifar da su, kamar lokacin aikin hajji da makamantan su. Akwai kasuwanni na lokacin kalon kuwa, wasu bukukuwan shekaru da sauransu. Don haka Madina birni ne na kasuwanci. Ta wani gefen kuma in ka dubi Madina, Madina cibiya ce ta ainihin Akwai harkan noma da ainihin harkan ruwa, da habbaka abubuwa na arziki dake bubbugowa daga kasa. Duk wannan Madina ta dauki irin wannan salon. A cikin sahaban Annabi Akwai duk wadannan nau'uka. Wasu sahabbai manoma ne. Wasu sahabbai yan kasuwa ne. Sama da su akwai Annabi Annabi duk yayi wadannan bangarorin. Annabi yayi kasuwanci tun yana ainihin Makka. Ya dawo ainihin Madina, ya ci gaba da harkan kasuwanci amma ba kai tsaye ba, ta hanyar ana juya mishi dukiyar shi A karkashin wannan Tana dauke da duk wadannan abubuwan da na fadi. Ta sauka ne a garin Madina, farko farkon isowar Annabi da sahabbai. Zan karanto mana aya ta 267 a inda Allah yace Ku ciyar Ku bada sadaka Daga mafi tsarkin abinda kuka tsururuta. Ma'ana kasuwancin da kukayi kuka ci riba. Aikin gwamnati da kukayi kuka tara kudi Allah madaukakin sarki yana cewa kudi ba ku ciyar matukar kunsan cewa dukiyar mai tsarki ce. To yanzu wannan aya tana alamta mana Ashe ba'a yin sadaka sai da dukiya wadda take ta halal. Ibn Mas'ud ko cewa yake yi Ya kai mumini Duk inda kaji Allah ya kira ka da wannan suna a Qur'ani to ka natsu Mai yiwuwa alheri ne Allah zai nuna maka. Mai yiwuwa sharri ne Allah zai kwabe ka. To dai Allah yace Ku ciyar Daga mafi tsarkin dukiyar da kuka nema Ta hanyar kasuwanci Ko kuma aikin gwamnati. Daga cikin sahabbai Abdullahi dan Abbas ya fassara wannan aya da wannan fassarar. Daga cikin tabi'ai akwai almajirinsa Mujahid ya fassara ta da wannan fassarar. A cikin littafin shi a nan ya ruwaito wadannan fassarori da isnadi ingantacce. Cewa abinda ake nufi da kasab shine kasuwanci ko kuma wani aiki da zakayi na karfi a dauka a ainihin a baka. Ina fata an gane. Sannan kuma Allah yake cewa haka ku ciyar Ku bada sadaka Ku taimaka Daga arzikin da muka fitar muku daga cikin kasa. Har wayewar wadancan malamai na sahabbai da tabi'ai suka fassara wannan wuri da noma. Kenan a cikin wannan wuri Allah yana umarnin manoma Da cewa dukiyan nan tasu da suka tara ta hanyar noma mai tsarki To su ciyar su yi sadaka. Amma sai Allah madaukakin sarki yayi kwaba da jan kunne da cewa Kar ku nufi dukiya wadda take kazama Ku je ainihin ku dibe ta kuyi sadaka. Wadda in an dauki irin wannan dukiyar an baku sadaka Ba zaku karbe ta ba Sai kullun tsai do. A lokacin da zaka dauki tuwo Wanda yara suka mai da shi dan dagwa dago Sukai dama dama da hannun su a ciki. Wani ya fyace majina a ciki, wani ya kaza. A lokacin da zaka dauka ka bayar Kayi tunani. Idan da zaka shiga irin halin da almajirin ya shiga in aka miko maka zaka karba kai tsaye kana murna koko zaka karba cikin rintsa ido. Allah yace kar ka bada irin wannan. Wannan rigar da zaka dauka ka bayar fasasshiya Da wannan fasasshen wando Da zaka dauka ka bayar Duba ka ga Idan da kaine ka samu kanka a halin bukata aka dauki wannan riga aka baka. Zaka karba kai tsaye koko zaka karba ne a halin larura da rintsa ido. Zaka karba ne a halin larura da rintsa ido. Kaji ma'aunin kenan. Don haka ma'aunin bada sadaka Shine duk lokacin da zaka bada sadaka sai ka duba da za'a kawo irin wannan abun a baka in kaine ka shiga wannan halin. Zaka karba cikin murna koko zaka karba cikin rintsa ido. Idan zaka karbi wannan cikin murna to ka bayar da irin ta ake so. Idan ko ya zama zaka rintsa ido ne saboda ka shiga halin kaskanci to ka sani da cewa Allah madaukakin sarki ya hana ka ka bada irin wannan. Kaji abu na farko. Abu na biyu Kar ku nufi dukiyar da take kazamar dukiya ce. Dukiya ce ta haram. Fansho ne na ma'aikata sai ka tattara shi sai kaje sai ka dibe shi sai a juya maka shi a kasuwanci. Bayan wata biyu wata biyar an fitar maka da riba ko riba. Sai ka ainihin je sai ka basu kudaden su. Kai kuma sai ka rike wannan riba ko kuma ka rike wannan riba. Ka sani da cewa Idan kayi haka haramun ne. Kuma Allah ba zai albarkaci abinda ainihin ka tara a dukiyar ka ba. Don haka nake tunanin Mai yiwuwa Zan cike wadannan ayoyi A garshen wa'azi na da wata aya wadda take da hadarin tarawa da dukiya Ta haram. Ko da kana sadaka sadaka bata tsarkake dukiya haram. Kuma kaji misalin da Allah yayi Yanda cewa garin banza ne Kuma a farau faron banza zai kare. Ba zai albarka ba komai daren dadewa. In bei watse a hannun ka ba zai watse a hannun zuriyar ka. Ba zai albarka ba don haka kar ka tara dukiya haram. Allah madaukakin sarki ya kiyaye. Allah yace Allah mawadaci ne Kuma Allah mai godiya ne ta hanyar sakayya ga duk wanda ainihin yayi abinda yake umarni da shi. A karkashin wannan aya da Allah ya cike ta da cewa Allah mawadaci ne Yana nuna cewa sadakar da kuke dauka kuke bayarwa ba zata tsine nawa Allah komai ba don Allah wadattacce ne. Don haka tunda kake sadaka Baka taba ganin an ajiye wani wuri ance aje Allah zai zo ya dauka ba. Sai ace dauki ka ba wani dan uwan ka mutum Ya dauka ya ci. Baka taba ganin wani hannu ya zuro daga sama Ya karba cewa Allah ne ya wakilta wani a karba mishi ba. Don haka in ka dauka ka bayar kar ka dauka cewa ka taimaki Allah ka taimaki kanka ne. Jama'a kunji ainihin wannan aya wadda yake da itace zanyi sharar fage Na wannan wa'azi nawa Domin a tabbatar da cewa lallai Allah yayi umarni da yin sadaka. Allah yayi umarni da ciyarwa. Allah yayi umarni da sadar da zumunci. Allah yayi umarni da zakka. Allah yayi umarni da taimako. Amma kuma gaba daya sharadin shine a dubi dukiya wadda take ta halal. Daga cikin wadda ka samu da gumin kanka ta hanyar kasuwanci Ko wani aikin karfi ko kuma ta hanyar aikin da kayi na noma ko makamantan haka. Don haka ba'a tara dukiyar haram a musulunci. Tara dukiya haram haramun ne. In kuma ka tara ba'a sadaka da dukiya haram. To kenan ya zakayi in ka tara sai dai ka mayar da ita inda kai ka san kaje ka dibo ta. Allah madaukakin sarki ya kiyaye. Jama'a to kunji wadannan ainihin nassoshi na Alkur'ani wadanda ainihin suke tabbatar mana da dukkanin maganganun nan da nayi sharar fage na ainihin fadi su. Sa'annan kuma bayan da muka ji daga Alkur'ani jama'a Dama taken mu mu ahalus sunna shine Alkur'ani da hadisi amma a bisa fassarar malaman farko Daga cikin sahabbai da tabi'ai da wadanda suka zo bayan su da kyautatawa. Da dumidumi kaji dai aya Alkur'ani na ja. Ina cikin fassarar ta sai kaji nace a duba fassarar Ibn Jarir al-Tabari. Ga wata fassara daga wani malami cikin malaman farko Ibn Abbas Da almajirinsa Mujahid. Wannan shine taken mu mu ahalus sunna To sa'annan bayan haka sai kuma hadisin manzon Allah Sallallahu ta'ala alaihi wa alihi wa sallam. Hadisan suma ingantattu a bisa fassara da aka samo daga malaman farko daga cikin sahabbai da tabi'ai da wadanda suka zo bayan su da kyautatawa. Don haka zan fara da littafi mafi inganci bayan Alkur'ani shine Sahih al-Bukhari. Malam Abdullahi Gwandu balaraban mutanen yamma yace Yace Sahih al-Bukhari shine mafi inganci bayan Alkur'ani. Yace duk wani littafi in yakai ya komo sai kaji ance Yace Imam al-Bukhari ya rubuta wannan littafi ne A Ka'aba a garin Makka inda aka haifi manzon Allah Shafi'i yace duk wani ilimi bata lokaci ne, shirme ne In dai ba'a ce Alkur'ani ba in dai ba'a ji ana cewa Wane ya bamu labari daga wane shi kuma daga manzon Allah. Yace haka nan duk abinda ba wadannan ba yace to bata lokaci ne. Sai kuma kokarin fahimtar addini ta hanyar menene malaman farko daga cikin malaman fikihun sahabbai da tabi'ai suka fadi. Yace to duk inda zaka nemo dalili a musulunci in ka wuce wadannan matakai guda uku Yace to shaidan ne kawai yayi maka kururuwa a cikin kunnen ka. Allah madaukakin sarki raba mu da kururuwar shaidan. Ibn al-Qayyim shi kuma Yake cewa Yace ilimi shine ace Allah yace Manzon Allah yace Sahabbai sun ce yace ilimi kenan. Yace amma in aka ce Allah yace manzon Allah yace sahabbai sun ce To in aka samu wani malami yayi wata magana da ta saba wata Allah ta saba ta manzon Allah ta saba ta sahabbai. Yace to wauta ne ma ka kawo wannan maganar. To kunga a nan Kunji yadda mu muke ahalus sunna muna aiki ne da Qur'ani. Muna aiki ne da hadisi. Muna aiki da fassarar da malaman farko daga cikin sahabbai da tabi'ai suka yi. Sannan dukkan malaman da suka biyo bayan su daga cikin malaman fikihu mun yadda da fassarar su. Yo amma in aka samu wani malami da ya biyo baya Yayi fassara wadda ta saba wata malaman farko To bama daukan ta. Saboda haka in ka tattara wadannan maganganu na Imam al-Shafi'i Da yake cewa Imam al-Shafi'i yace ilimi muje ance Duk abinda ya saba wa Allah yace Annabi yace Yace to wannan waswasi ne na shaidan, kururuwar shaidan ce. Yace babu laifi kuma koyan fikihu a cikin addini. Kenan mu ahalus sunna mun yadda da malaman fikihu. Amma kuma bamu tsarkake malaman fikihu daga yin kuskure ba. To idan suka yi kuskure To sai mu ajiye maganganun su mu yi musu addu'o'i na alheri. Amma ba zamu dauki maganar malamin fikihu ba in ta saba ta Allah, in ta saba ta Annabi To Ibn al-Qayyim kuma abinda yake nuna mana Ilimi shine ace Allah yace Annabi yace sahabbai sun ce babu laifi. To a nan in aka samu wani malamin fikihu yayi magana da ta saba wa ta Allah ta saba wa ta manzon Allah to ba yayi da gangan bane don haka ba za'a zarge shi ba. Sai ace mai yiwuwa akwai abinda ya kai shi ga yin wannan maganar. Amma ba wai yana ganin Allah yace ai shi kuma yace kada ai ba. Ba'a taba samu malamin fikihu da yawa Allah haka ba. Manzon Allah yace kaza sunna ne, wani malamin fikihu yace bidi'a ne. Ba'a taba samu wani malamin fikihu da yayi haka ba. Shi yasa daya daga cikin malaman mu na ahalus sunna Wanda ya zama jagora wajen bin ta farko da kuma karantar da Ta farkin malaman farko da muke a kai Shine al-imam Ahmad Yace dauke zargi daga manyan malamai. Ba'a zargin Imam Malik. Ba'a zargin Imam al-Shafi'i ko Imam Ahmad ko Ibn Hanbali ko ainihin Imam Abu Hanifa ko Ibn al-Mubarak ko wani malami cikin malaman fikihu sun fi 40 wa ike maganar hudu. Ba'a zargin su. Dukkan su Limaman shari'a ne. Ba'a zargin su. Karanta Zaka ga ba'a zargin su ko kadan. To amma kuma da ike malamai ne. Ilimi kuma yana da limit. Ilimi yana da iyaka. Akwai abinda ba zaka gano shi ba, akwai abinda bai bayyana a zamanin ka ba, akwai abinda ya zo maka amma bai zo maka ta hanyar da zaka karbe shi ba. To in aka samu sun yi wata magana ta saba dalili sai a ajiye ta. Sai ayi musu addu'a ta gari. Sai kuma ainihin a ci gaba da riko da abinda yake daidai. Wannan itace akidar mutum da kasan mu Har zuwa yau. Kuma itace akidar da muke fatan mu hadu a da Allah da ita domin a kanta ne. Malamin da suka gabace mu suka ainihin riga yayi mu lahira. Don haka ya Allah ka dauki ran mu a kan bin Alkur'ani da sunna. Da tsayawa a fassarar malaman farko daga cikin sahabbai da tabi'ai da wadanda suka zo bayan su da kyautatawa. Allah kada ka taba bada dama a kan mu bi wata magana wadda take kuskure ce a cikin son zuciya. Wannan hadisai ko wadannan hadisai da zan karanto mana duk gaba daya gasu a cikin A cikin ainihin Zan fara karatu daga babi na 30 Imam al-Bukhari yace babun Dan uwa musulmi don kar ka ce to su Albani suna suka ayi sadaka A abbara muke suka a rinka yin bara a mai da ita sana'a ta zama an daina komai zuka ta sun mutu. Amma har Kaji ance muna suka sadaka Allah ya tsare mu saboda Qur'ani yayi umarni da sadaka. Hadisai sun yi umarni da sadaka. Malamin musulunci kaf sun hadu a kan cewa sadaka addini ce. Wannan babi Imam al-Bukhari yace wajibi ne ko wani musulmi yayi sadaka. Imam al-Bukhari yace wanda bai samu abin yin sadaka ba to yayi aiki na gari. Daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana dole ne kayi sadaka ya kai dan uwa musulmi. Dole kayi sadaka. In baka samu abin yin sadaka ba fa Ka samu wani aikin alheri kayi. Amma kar ka sake rana ta fito Rana ta fadi baka yi sadaka ba kuma baka yi wani aikin alkhairi ba. Bukhari ya samu malami hadisin nan daga malamin shi Muslim dan Ibrahim Shi ko yace ya karbo hadisin daga malamin shi malam Shu'uba dan Hajjaj Abul Bistan. Shi ko yace ya karbo wannan hadisi daga Sa'idu dan Abi Burda. Shi ko yake cewa ya karbo daga mahaifin shi Abu Burda. Shi ko Abu Burda yace ya karbo daga nashi mahaifin shine Abu Musa al-Ash'ari sahabi. Shi ko yace ya karbo daga Annabi Annabi yace Lallai ne ko wani musulmi yayi sadaka. Sahabbai suka ce ya Annabin Allah. Wanda bai samu abin yin sadaka ba gashi kace lallai Yaje yayi aiki da hannun shi. Ya amfanar da kan shi Yanzu kunga wannan hadisin abinda yake ce mana Idan gari ya waye lallai kaje kayi sadaka. Sai kace to ai baka da sadaka sai Annabi yace je ka ka nemi inda ake aiki. Je ka gashi can ana diban leburori. Je ka gashi can ana diban mutane zasu tafi gona. Je ka ka samu wani zai kai shara ka dauka ka kai. Kayi aikin da za'a biya ka kaje ka amfanar da kan ka. Kaga abinda Annabi Ka amfanar da kan ka. Sannan kayi sadaka. Wannan yana nuna mana addinin musulunci ba sadakar kadai yake umarni da ita ba. Yana fada da zaman banza. Me yasa baka da naira 50 da zakayi sadaka? Baka da ita. To tashi kaje kayi aiki. Baka da aiki tafi ka nemi aiki. Kaga addinin musulunci yana nuna yadda ake yunkurar da kai. Ka tashi ka amfana, ka tashi ka amfanar. Sahabbai suka ce to ya manzon Allah Mutum ya kewaya kaf bai samu inda zai aiki ba. Yaje ya samu wani wanda yake da tsananin bukata ya taimake shi. Shiga cikin tudun wada Shiga cikin daurawa Shiga anguwar Madaka Shiga cikin anguwar gwargwaje Shiga cikin tukurtukur Tafi kauye kaza zaka je ka samu wani yana nan da tsananin bukata ya tsufa bashi da yaya. Bashi da lafiya. Je ka ka zauna ka share mai daki. Je ka ka
[Segment 3/9 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
bi wannan ainihin kudin cizo da ke damun shi. Je ka ka wanke mishi kayan shi. Je ka ka samu waccan tsohuwa ga ta nan ta makale, ta kasa yadda zata fita ga tsufa ga makanci rike mata sanda, fito da ita sarari zaunar da ita inda take so. Je ka ka samu wani katon gashi ta zibe. Ya rasa yadda zai yi ya tada ita. Amma ga kasa je ka ka kwaba mishi kasar. Duk wannan yana daga cikin abun da zaka yi a wuni guda a tabbatar da cewa ka samu kayi sadaka ta dukiya in ba haka ba kayi wani aiki wanda zaka zan ka tsai da shi a matsayin sadaka. Sahabbai suka ce ya manzon Allah. Idan mutum duk ya kewaye anguwanni da kauyuka da gidaje bai samu inda zai taimaka wa wani ba. Ya je yayi wani aikin alheri. Je ka ga kakanka can a kauye kaza je ka ka gaishe ta. Ga kanin mahaifinka can a anguwa kaza je ka ka gaishe shi aikin alheri ne. Je ka kayi ziyarar wani aboki naka saboda Allah. Wannan aikin alheri ne. Annabi yace ka yi shi a matsayin wannan wuni guda kuma ya kame daga sharri. Daga fitowar rana zuwa faduwar ta kar kayi wa kowa sharri. Kar ka je ka kulla wa wani makirci. Kar ka je ka ainihin yi sabobin saka wani a cikin kunci da damuwa. Manzon Allah yace Yin haka ma sadaka ce kaji. Wuni yayi baka samu kudin yin sadaka ba. Baka samu aikin yi ba. Ka rasa inda zaka je ana ginin masallaci kaje ka kai gudunmawa. Ka rasa abun da zaka yi manzon Allah yace kayi wani abu na alheri. Zauna kayi salati. Karanta alkur'ani. Sannan ka kame daga sharri kar ka cutar da kowa a wannan yin ne. Ka zauna lafiya ka bar mutane su zauna lafiya. Yin haka ma sadaka ce. Wadannan maganganun na annabi Ana bukatar su a kowane zamani. Amma munfi bukatar wadannan maganganun a wannan zamani. Kunji addinin musulunci ne ke cewa in gari ya waye baka samu sadaka da zaka yi ba. Baka samu aikin yi ba, baka samu kaza ba. Ka rasa abun da zaka yi eh to kaje ka zauna lafiya kar kayi wa kowa sharri. Yin haka ma sadaka ce. Yanzu musulmi da suke da wadannan nassoshin sune ake zargi da cewa yan ta'adda. Ayi kokari dai a gano yan ta'adda na gaskiya. Mutanen da aka umarce su da kamewa daga yin sharri da bakin ka da zuciyar ka da gabar ka an hana ka kayi sharri. Aka ce in ka wuni baka yi sharri ba. Matsayin daya kake da wanda ya dauki dukiya ya bayar sadaka. Matsayi daya kake da wanda yaje yayi aikin karfi ya samu yazo yayi sadaka. Wannan shine addinin musulunci jama'a. Jama'a kunga wannan hadisi yana kwadatar da mu game da yin sadaka ko? To dan haka jama'a ko da muka ce zamu yi wa'azi dangane da cewa bara haramun ce ba muna nufin cewa to kuma bada sadaka haramun bane zamu zo zamu warware maka zaka fita daga duk cikin rudani insha Allahu ta'ala. Sa'annan a cikin wannan hadisi munji inda manzon Allah yake karfafan musulmi dangane da wannan jiki naka kar ka zauna da tumasanci. Gari ya waye ka sake jan mayafi ka kwanta. Gari ya waye kaje ka zauna zauran wane ko kofar gidan wane ya fito kuma ka kara zubewa. Addinin musulunci cewa yayi tashi kaje ka nemi aikin yi. Dan haka kunga wannan hadisi yana tabbatar da cewa tumasanci bai halatta ba. Shine kar ka bar zuciyar ka ta mutu. Tashi kaje kayi wani abu wanda zaka samu abun da zaka rufa wa kanka asiri har ka ainihin taimaka wa wani. Zamu zo zamu ji. Annabi ya taba yin wa'azi. Irin wannan wa'azin daga haka ne wasu sahabbai suka samar wa da kansu aikin yi. Dan ka gane cewa baka kai darajar su ba. Dan haka baka da dalilin da zaka ce ba zaka je ka tura baro ba. Ba zaka je ka dauki kwangiri ba. Ba zaka je ka dauki ice ba. Ba zaka je kayi kaza ba. Baka da dalilin yin haka. Ina fatan an gane. To sa'annan imamul bukhari ya sake ainihin wato kulla wani babi kafin wannan da ya kira shi da babun Babin dake bayani akan cewa sadaka tana kankare zunubai a nan ba kuskure ba uhm uhm kuskure ai ba laifi bane balle a kankare maka shi. Zunubi ake nufi. Zunubi zunubi da ka aikata to in ka bada sadaka sadaka zata ainihin kankare maka shi. Sahabi huzaifa yace wata rana sayyidina umar ya mike yace jama'a cikin ku wanene ya taba jin manzon Allah yayi wa'azi dangane da fitina dangane da bala'o'i wadanda zasu faru a duniyan nan. Wanene ya taba jin wani wa'azi daga manzon Allah ya rike mana shi. Kalla sai huzaifa yace Huzaifa yace na haddace wa'azin manzon Allah game da fitintinu kamar yadda manzon Allah ya wa'azin haka na haddace. Sai ainihin sayyidina umar yace Ai indai wajen haddan maganar annabi ce ai kai in garma ne. Kana da kwazo indai wajen haddan maganar annabi ce kai kai gwarzo ne. Fada min yaya manzon Allah ya fadi. Kulta sai nace da shi Yace fitintunun da mutum yake fama da shi game da yayan shi fitintinu game da mata fitintunun ka game da iyalan ka da kake kwaramniya da su fitintunun da ke samun ka game da makwabcin ka to sallah da kake yi da ainihin wato sadaka da ayyukan alheri duk suna kankare ire-iren wadannan fitintinu. Me ake nufi fada ya hada ka da matar ka ka buda baki ka zage ta. Kaci zalin ta. Dan ka ka zalince shi. Ka zage shi ko ka tsine mai ba a inda ya dace ba. Hakanan makwabcin ka ka cutar da shi ko kayi mishi wani abu wanda bai halatta ba. Duk wadannan zunubai ne sai manzon Allah yace sallah da sadaka suna kankare wadannan zunuban. Sai kuma manzon Allah yace Hakanan ayyukan alherai da kake yi sadar da zumunci duk suna kankare ire-iren wadannan zunubai da suka shafi zunubin da ke tsakanin ka da matar ka zunubin da ke tsakanin ka da yayan ka zunubin da ke tsakanin ka da makwabtan ka. Sannan sai annabi sai yace Imamul bukhari yace Wani lokacin ma yace manzon Allah yace sallah da sadaka da umarni da kyakyawa da hana mumuna samar da alheri a zamanta kewa samar da zaman lafiya samar da cigaba a zaman takewa yin wa'azo zi nasiha sune ake tattarawa a musulunci ana kiran su Wadannan ayyukan na alheri da kake yi to suna kankare maka ainihin zunubai hakanan sallah hakanan sadaka. Kalla da umar yaji wannan wa'azi da huzaifa yace shi ya haddace sai yace Kai ba fitintinu irin wadannan kanana ba dan mutum ya zage dan shi dan mutum ya zage matar shi dan ya cuce eh duk wadannan fitintinu ne. Ba irin wadannan fitintunun nake nufi ba. Jama'a cikin ku waye ya taba jin manzon Allah yayi wa'azi dangane da bala'o'i wadanda zasu samu wadanda zasu hargitsa al'umma kamar yadda kunfatte ku take hargitsa ruwa. Kamar yadda igiyar teku take hargitsa ruwa. Ka dubi igiya a teku sai ta dauki ruwan dake gaba sai ta dawo da shi baya. Sai ta dauki ruwan dake gaba sai ta challa shi tsakiya. Na tsakiya kuma sai ta challo shi ya yo waje Allah yasa ka taba zuwa ka ga teku. Sai in kaga teku tukuna zaka gane wannan. Kuma daga nan zaka gane mu'ujizar manzon Allah. Kaji manzon Allah ya buga misali da teku. Amma manzon Allah bai taba ganin teku ba. Manzon Allah bai taba ganin teku ba. Fitintinu wadanda suke rikita mutane na gaba ya koma baya. Kana musulmi da safe kafin magariba ka zama arne. Garin ku na zaunar lafiya da daddare kafin gari ya waye gidaje goma su rushe bom ya tashi. An fahimta jama'a?
[Speaker seg3-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg3-spk:0]
An waye gari shine shugaban kasa. Kafin la'asar yana kurkuku. Anyi juyin mulki. Yanzu shine senate president. Anjima EFCC ta jefa shi a cell. Fitintinu wadanda yanzu sai kaga sun hargitsa al'amura. Ko kun fahimta jama'a? Irin wannan nake nema waye taba jin jawabin manzon Allah akan haka. Ran sarkin musulmi ya dade ran ka ya dade umar. Wadannan fitintunun ko sun zo ai ba zasu shafe ka ba ba ruwan ka da su dan me kake tambaya. Wadannan fitintinu lallai annabi yace zasu faru. Al'umma zasu hargitse nan gaba. Amma tsakanin kai da wannan fitintunun akwai kopa wanda take rufappiya ce. Ita kofar da take tsakani na da fitintunun da zasu faru umar yace Karya ta za'ayi ko ka bude ta za'ayi. Huzaifa yace a'a. Annabi yace karya ta za'ayi ba bude ta za'ayi ba. Indai fitina har tayi fitina ta karya wannan kopa to baza a sake rufe wannan kopa ba har abada. Ka duba da kyau ka gani in iska ta taso a guje ta karya kofar ka. Yaushe zaka nemo kafin ta ana iskar. Gudu zaka yi kai kanka.
[Speaker seg3-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg3-spk:0]
Bala'i yayi bala'i yaci kopa dan haka kai ma yanzu yake nema. Amma idan iska tayi iska ta buda kofar ka da karfi me kake kokarin yi in bata karya ba. Kokari kake ka maida ita ka rufe sai ka ga bala'in ya kwanta. To akwai bala'o'i da zasu zo su faru bayan annabi ya rasu shine umar ya san da su. Amma bai san lokacin ba shine yake tambaya. A zamanin shi za'ayi ko kuwa sai wannan sahabi yace a'a ai tsakanin kai da fitintunun akwai kopa. Wato ba a zamanin ka za'ayi ba. Sai yace to naji. Amma ita kofar bude ta za'ayi fitintunun su fito ko karya ta za'ayi sai aka ce a'a ai ran ka ya dade karya ta za'ayi sai yace to ko in aka karya ta baza ta rufe ba har abada. Huzaifa sai yace kwarai da gaske shima annabi haka ya fadi. Indai aka karya kopar to baza ta sake rufuwa ba. Sai muka ji kwar jinin malamin mu muka kasa tambayar malamin mu Shin wai wanene kofar. Wanene wannan kofar Allah gafarta malam. Da malamin ya gama musu hadisin Kamar su ce wai Allah gafarta malam me ake nufi da kopa kuma me ma'anar karya kofar. Sai muka ga kwar jinin malamin sai muka kasa. To amma cikin mu akwai wani dan yaro karami. Sunan shi masruk sai muka ce wa masruk salhu. Tafi ka tambayi malam. Sai ya tambayi malam. Umar Allah ya kara mishi yarda shine wannan kopa. Wato zaman umar a kujerar shugabancin musulmi to wata garkuwa ce daga bala'o'i su abko wa musulmi. To idan umar kwanciya zai ya mutu ma'ana hadisin in kwanciya zai ya mutu to za'a nada wani shugaba cikin lumana kuma ya cigaba da tare bala'in kenan. Amma idan kashe umar za'ayi to karya kopa kenan. To ba wani shugaba da zai sake zuwa ya zauna kuma gwamnati ta sake zama har duniya ta tashi irin umar. Abun da hadisi yake nufi kenan. Abun da hadisi yake nufi kenan. Shi umar ya san kashe shi za'ayi. Saboda mai gidan shi ya gaya mishi. Shine manzon Allah Wata rana manzon Allah yana zaune akan wani dutse hadisin yana nan cikin sahihul bukhari da muslim. A cikin wata gona dutse ne haka kututturan dutse manzon Allah ya haukan shi haka. Sai aka zo aka cewa annabi Abubakar yana sallah. Annabi yace ku ce ya shigo kuma ku ce albishirin shi shi dan aljanna ne. Aka je ran ka ya dade eh annabi yace ka shigo kuma yace ayi maka albishir da aljanna. Abubakar yace masha Allahu madallah nagode Allah ya shigo. Can sai aka ce ga umar na sallah. Manzon Allah yace ku ce ya shigo shima ku ce dan aljanna ne. Aka je ran ka ya dade eh annabi yace shigo amma yace kai ma dan aljanna ne umar shima ya godiya ga Allah ya shigo. Can sai aka ce ga usman na sallah. Manzon Allah kuyi mishi izini. Ku ce mishi shima albishirin shi dan aljanna ne. Amma akwai bala'i da zai same shi a lokacin mutuwa. Shine a musulunci ba'a taba kashe wani ba kisan farko akan usman aka fara yi na wulakanci. Ba'a taba danna mutum anyi mishi yankan rago tun daga zamanin annabi ba sai akan usman danne shi akayi akayi yanka shi yankan rago. Ba'a boye ba ba da daddare ba a'a har cikin gidan shi. Umar kuwa a masallaci ne a boye aka zira wa jiki aka soke shi aka nema a gudu. Amma usman an tare shi ne. Yana azumi zai sha ruwa. Suka hana shi sha ruwa. Yayi sabi zarce. Suna nan sun kewaye gidan. Gari ya waye ya leko yace musu ina gama ku da Allah kun san ni sahabi manzon Allah ne suka ce kwarai da gaske. Kun san lokacin da a garin nan musulmi suka rasa ruwa suna siyan ruwa a wurin bayahude ruma sunan bayahuden kenan ruma. Ba ruma ba kar kace baka tsine da garin ku a ke a'a ba ruma ba ruma sunan bayahuden kenan. Idan yaga lokacin sallah yayi kawai sai ya kulla rije shi sai ya tafi ya shi. In ya gane yau musulmi suna da wani sha'ani suna bukatar ruwa sai ya kulle kawai sai ya tafi ya shi. To da yake bayahude capitalist ne. Bayahude dan gurguzu ne dan jari hujja ne kudi. Ran nan sai yace zai siyar da rabul rijiyar shi. Radi an taba sai da rabul rijiya i statistic ne. Yau diban shi gobe diban wanda ya siya waye zai siya saboda tsabar neman kudi kawai. Sai usman sai ya aika yace ku je ku ce mishi zan siya duk abun da ya fada ku ce na siya. Usman da hausa sunan shi kundila. Abun da ake nufi da kundila da hausa shine wanda duk garin nan an kasa siye shi zai siya sai in ba yadda bukata shi ake kira kundila da hausa. Kundila da kaji ta kano ai sunan wani ba kano ne attajiri duk abun da ya ga garin kanawa siya sai a ce a je wurin shi. Indai yana so sai ya siya shine sai suka sa mai kundila suna ne na na na mukami. Kowa ya kasa siye in aka je shi zai siya shine sai a kira shi kundila to usman kundila ne. Yace ku je. Duk abun da ya fada ku ce na siya. Yace nawa yace kaza yace mai gida na ya siya. Yace yaushe zai kawo kudi sai yace ga su daman an bashi kudi a je kunkuna kawai sai aka kirga aka bashi. To yaya abun zai kasance sai yace yau diba na gobe diban usman. Aka rubuta takarda aka yi sign shikenan. Sai usman ya tara musulmi yace to shikenan. Duk ranar da take diba na ku je ku diba kyauta. Sadaka saboda Allah. Kuma kuyi guziri ku cika bokitai da jarkoki wanda zai ishe ku har gobe. Dan haka baza ku sake bukata ba sai jibi rana ta. Haka. Su usman tsoffin yan kasuwa ne in ba dan kur'ani da hadisi ba duk mugunta sun iya. Amma kur'ani da hadisi shi ke Saboda haka yanzu ba mugunta sukai ba. Yayi daidai ne shine yayi mugunta. Dan haka musulmi su cika jarkokin su ranar diban usman kyauta Ranar diban bayahude ran da za'a siya yazo yasa goga ya kada yayi ragi ba wanda zai siya. Yau da kowa ya wadatu. Bayan makonni sai yace Usman ya kashe ni. Ku kira shi yazo yayi siye sauran rabon.
[Segment 4/9 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
To kunga a cikin harkar kasuwanci ko?
[Speaker seg4-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:0]
To yanzu bazai siye ta yadda ya siye ta da ba.
[Speaker seg4-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:0]
Haka ake yi. Da in an siyar mai da rabin miliyan daya ko? To yanzu tunda ya gane in bai siya ba ba mai da bukata. Don haka yanzu sai ya siye ta siyan gaskiya. Aka koru Ruma kunji. Sai Usman yace to da guga shi da gugar duk wani musulmi daya ce a cikin wannan rijiya kowa ya sha. Shine Usman ya leko da suka zo kashe shi yace kunsan a garin nan an taba samun lokacin da ba ruwa ni na sai rijiyar Ruma kowa ya sha rijiya kyauta. Suka ce Yace amma yau kwana uku ina azumi kun hanani in sha ruwa makwarwa daya. Suka ce kwarai da gaske. Khawariji ne, boko haram.
[Speaker seg4-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:0]
Boko haram na farko kenan.
[Speaker seg4-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:0]
Yes. Ka saurari wani nawa in Allah ya so wajen shafi dari ne da turanci zamu zo kowa zai same shi ka kwantar da hankalin ka zamu yi Na riga na gama rubutun gaba daya kawai zamu yi Insha Allahu. Zaka ji wannan kisan a ciki. Farkon farkon su kenan. Musulmi ne amma suka zo da makami zasu kashe sahabi. Yana gaya musu ayyukan alheri suna cewa gaskiya ne amma sai mun kashe ka. Saboda mu mun hukunta kayi ridda. Yasa ake cewa ina gama ku da Allah kunsan sanda za'a je yakin Tabuka musulmi basu da abun hawa basu da abinci. Nayo order kaya a garin nan sun shigo abinci da man gyada da man shanu. Duk garin nan aka taya. Amma nace an bani ribar da tafi wannan? Na'am. Yaya tarihin yake? Za'a je yakin Tabuka musulmi suna cikin yunwa da talauci da rashin abun hawa lokacin zafin rana ne. Sai ga kayan Usman sun shigo yayo order daga kasar waje. Trailer trailer ka kalla abun a zamanin nan. Jiragen ruwa to a wancan zamani ne na rakuma. Shinkafa, hatsi, manja, man gyada, man shafa komai akwai. Yan kasuwar Madina suka zo sukai ta tayawa. Usman yana cewa an bani riba fiye da wanda ka bani. Sai aka je aka nemo kundilar Madina. Wanda daga kanshi to sai dai Usman din.
[Speaker seg4-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg4-spk:0]
Aka kira shi yazo. Ya ninka abun da wadancan mutane suka siya don Usman ya siyar mai sai Usman yace an bani riba fiye da wannan. Sai shi kundilan ya tambayi Usman don Allah mai gida kasan wannan kalmar ma a kasuwanci mukami ce? Eh mai gida je ka yan goro ka tambaya. Mai gida mai gida a kasuwanci itama mukami ce. Yace mishi mai gida waya baka riba sai yace Allah. Dama alaranma ne sai ya ja aya Allah yayi cinikin rayuka da dukiyar mumini akan zai basu aljanna sai yace kaji inda Allah ya siya ya biya. Don haka bazaka iya bani abun da yafi aljanna ba yace kwarai da gaske mai gida yace tashi ka tafi. Waccan kalmar da na fadi ka karanta wani littafi Je kan kana da wani kaka wanda ya sana'ar goro kaje zai fassara maka mai ake nufi da mai gida haka suke cewa Ina fata an gane. To mu dawo kan hadisin Usman sai Usman yace wadannan Ina gama ku da Allah kuna da wannan tarihin suka ce muna dashi. Kunsan mai Usman yayi sai yace wannan dukiya da abinci gaba daya da rakuma duka yace a ba sojojin musulmi su ci su sha su barwa iyalan su guzuri su hau dawakan da rakuman su je suyi jihadi. Mun san Allah na gida rana tsaka aka zo aka ce ga abun da Usman yayi. Manzon Allah ya jawo mayafinsa a guje taho masallaci aka kira sallah aka tara musulmi. Manzon Allah yace Manzon Allah yace musulmi daga yau duk abun da Usman yayi wa Allah Allah yafe mishi. Usman bazai sake laifi a wurin Allah Allah ya kama shi ba. Usman yace musu don Allah kunsan anyi haka? Suka ce Mun sani. Yace amma bazaku barni in sa kwallon dabino kwa daya a baki na ba yau kwana uku suka ce bazamu bari ba. Me yasa suka ce kayi ridda? Sai mun kashe ka. Sai yace Ana cikin haka sai su Sayyidina Ali suka ci karfin su sai suka buda sai suka shigo cikin gidan Usman. Suka ce Usman yaushe kana khalifan musulmi zamu bari a danne ka a yanka kamar rago. Sai Usman yace ku barshi su kashe ni. Don ni kadai zasu kashe. Idan yanzu kuka taya su mutanen da za'a kashe tare da ni suna da yawa. Don haka haka yawar ta kisan Aliyu suka fita yace ku barni ni zaman shi shi kadai akan buzu. Sukai kururuwa suka ce mai ake jira ne suka je suka danne shi suka yanka shi yankan rago. Sayyidina Usman kenan Allah ya kara mishi yarda. A lokacin shekarun shi 84 a duniya. Don haka idan yan boko haram sun kashe Janaral Shuwa mu bazamu yi mamaki ba Kuna da tarihin Janaral Shuwa bai kai shekara 84 ba. Khawariji sun kashe Sayyidina Usman shekarun shi 84. Janaral Shuwa Janaral ne a Nigerian Army. Sayyidina Usman fa field marshal ne. A cikin sahabban manzon Allah So karku damu jama'a tarihi ne mu musulmi duk muna da tarihin a hannu. Yan boko ne masu karatun tarihi da wadanda basu karatun addini ba sune wannan hayaniyar ta zaman musu bakiwa. Amma duk wanda ya karatun musulunci gata nan Canza suna da zatai bazai sanya ta canza siphofin ta ba. Shiyasa a cikin wannan makala tawa da zaka ji ta zaka ga zan kawo maka Menene siphofin yan boko haram tun wancan zamanin zaka ga ga sunan ga sunan ga sunan kuma mune muna kawo dalilai daga manzon Allah kamar kullun dai Allah ya taimaka. Jama'a kunji Almajirai suka tambayi Huzaifa na dawo hadisin nan ne. Yanzu nan Umar yasan wanda kake nufi da kofar Huzaifa yace kwarai ya sani. Kamar yadda yasan cewa bayan yau sai gobe daga yanzu sai mai sai dare daga dare sai wayewar gari ai kasan duk sanda gari ya waye mai ake jira? Dare yakinan ko? Duk sanda rana tayi ayi dare mai ake jira? Wayewar gari to kamar yadda Umar yasan haka yasan shine kofar yasan randa duk aka rasa shi kuma yasan za'a rasa shi ne ta hanyar mai? Ta hanyar kisa to bari in karasa mana wani hadisin don hadisan suna shiga juna amma kowanne ina sanar da yadda nake kawo shi. Annabi yana zaune akan dutse in baku manta ba cikin gona Abubakar ya shigo Umar ya shigo Usman ya shigo akan haka muka tsaya. Da Usman ya zauna akan dutse sai dutse ya tangadi haka sai manzon Allah yace ki dutse yace In ba manzon Allah ba duk wanda ya haka ku kaishe Akwai tabuwa. Eh dutse kayi magana da dutse sai annabawa suke magana da dutse duk wanda dutse yayi rawa haka sai manzon Allah yace Yace kai kana tsumana Annabi ne yake zaune akan ka da Siddiki shine Abubakar da shahidai guda biyu. A ina manzon Allah ya fada haka? A gaban Abubakar da Umar da Usman don haka da Umar da Usman sun san kashe su za'ayi. Shiyasa kullun sai Umar yazo da wata addu'a sai ta ruda musulmi. Kullun sai aji Umar yana cewa Allah ka dauki raina Allah ka bani darajar shahada. Allah ka bani darajar shahada Allah ka sa in mutu a Madina sai mutane kullun suna cewa to ai akwai tufa da warwara. Allah ya bashi shahada kuma Allah ya dauki ran shi a Madina to Madina ai garin musulunci ne za'ayi yaki a Madina ne? Shi yasan cewa manzon Allah yayi mishi bushara kuma ya fada mai tarihin cewa shahada zai yi. To amma kuma yasan falalar mutuwa a Madina. Hadisi ya tabbata cikin kayi fatan ka mutu a Makka ko Madina ko birnin Kudus. Shiyasa kaji mawakin hausawa shekara 30 da wani abu da suka wuce yake cewa Allah kaini Madina in mutu can. Daidai ne kayi addu'a Allah ya ya kashe ka a Madina kawai dauki ranka a Makka ko a birnin Kudus. Annabi Musa ya taba addu'ar haka manzon Allah ya bada labari hadisin yana nan cikin A karkashin wannan. Ashe Sayyidina Umar yaji abun da yaji ne daga manzon Allah yake fatan Allah ya tabbatar mai da mutuwar shahada. Kuma ta zama mutuwar shahadar a cikin ainihin garin Madina. Kuma haka ta faru. Yana cikin sallah asuba a raka'a ta farko masallaci ne da duhu a lokacin sai ga ainihin Wani zindiki arne Bafarishe. Bawa ne dama aka kawo su aiki Sayyidina Umar ya gansu sun fara yawa a gari har ya tsaya yana gargadin mai gidan shi. Kuna dibo wadannan mutane in suka yi yawa a garin nan garin bazai mana dadi ba. Sai Abu Lulu'a ya harare shi yace aikin banza zamu hadu ne. Umar ya duba sahabbai yace jama'a ina sarkin musulmi shugaban kasa bawa dan kasar waje yana gargadi na a garin ku kuna ji? Bayan kwanaki kadan da Abu Lulu'a da Fairuz dukkan su Farisawa ne. Sai suka zauna suna hira da wata wuka a tsakiyar su suna caccaka ta a kasa suna ganin wani da daga cikin yayan Umar wani saurayi sai sukai shiru. Ya wuce suka harare shi haka. Bayan kwana biyu sai ga Abu Lulu'a ya shigo masallaci sahu na biyu da asuba. Amma ya rufo alkyabba. Ashe ya taho da wannan wuka ne. Wannan wuka zindimeemiyar wuka ce ga kaifi ga tsini sannan a tsakiyar ta tana da kunnuwa guda biyu ita Larabawa ke kira Ya riko ta. An san ba musulmi bane amma yau da aka ganshi cikin masallaci sai aka tsammaci ya musulunta ne. Kunji fassarar da musulmi sukai. Ana fara sallah Umar ya fara sura kenan sai aka ji yana Ashe wannan kafiri yayi tsalle ya tura wanda ke gaban shi yaje ya samu Umar ya zindima mishi ita a ciki amma sai ta goce sai ta sauka a marar Umar. Da ya soka ta ya tabbatar da tsinin da kaifin sun shiga sai ya jawo ta sai kuma ta farki dama da hagun tunda tana da kunnuwa. Sai Umar ya fadi sai yayi ishara yazo ya cika sa wannan sallah. Akai kokarin kama shi sai ya ringa ainihin daukan wukan yana sara dama da hagun. Sai aka samo wani musulmi sai ya dauki rigar shi burnus itace yar maroko riga mai hula sai ya dauke ta sai ya jefa mishi sai ya shake shi sai suka kawo dashi. Ya tabbatar da asirin shi zai tonu sai daddabawa kanshi wukan shi ma sai ya mutu. Har ma ya riga Sayyidina Umar mutuwa. Ku dubi yadda kafirai suke da Yasan in aka kama shi za'a ji su waye suka turo shi. Don haka da ya bari haka kuma yasan karshen ta mutuwa zai to gwam mai ya mutu da wuri don kar ya tonu asirin iyayen gidan shi. Suna rike bayani suna rike sirrin su. Yaya kuke ko musulmi? In aka gaya muku magana a masallaci har tsuma kake a gama wa'azin kaje ka fade ta kaje ka rubuta ta a Facebook. Jama'a kuna ji? Kunji kisan kisan Sayyidina Umar kenan. Bayan kwana biyu aka kira likita yazo ya dinke wannan wurare na cikin Umar. Sai Umar yasa dan shi Abdullahi ya miko mai nono yana shan nono sai ya ga nono ya dawo ta inda akai dinki. Sai yace to rayuwa ta kare ku saurara yanzu abun da ya kamata ayi tattalin ina za'a kwanta? Yace Abdullahi tashi kaje wurin Aisha matar annabi Kace mata Umar karkace mata sarkin musulmi kace mata Umar na ganshe ta bayan gaisuwa yana rokon wannan fili da ya rage a dakin ta ga kabarin annabi ga kabarin Abubakar to akwai wani dan fili da ya rage haka to don Allah tunda dakin ta ne Umar na rokon ta azziki in ya mutu a kawo shi a rufe shi ya zama gashi ga abokan shi. Yace amma in kaje karka ce mata sarkin musulmi don kar taji cewa akwai iko a cikin kace mata Umar. Da yaje yace ranka ya dade Umar ya aiko ni. Yace bayan gaisuwa ga arzikin da yake nema sai tace kash. Gaskiya da na tattali wurin nan ne don ni kaina in na mutu a rufe ni nan miji na nan uba na ni kuma in zama nan. Amma wallahi tunda Umar na so kaje kace na bashi. Umar na kwance cikin jini sai aka ce ranka ya dade ga Abdullahi na ya dawo sai yace ku tada ni zauna sai aka tashe shi zaune yace yaya mai kazo dashi yace taimaka izini sai ajiye zuciya yace Yace a duk duniya yanzu ba abun da ya rage min shine ayi min alfarma ga kabarin annabi gani Abubakar ni kuma in zama gani nan. Abun da nake so kenan. Yace to amma Abdullahi yace in na mutu a dauki gawa ta aje a tsaya kofar dakin ta a sake mata sallama a sake mata gaisuwa ace to ga Umar fa yana sake rokon alfarma yace ta yiu tayi izini ne jiya. Taga ina da rai yanzu tunda ban da rai zata iya canza haka ayi mata karfi da yaji. Jama'a kunji wadannan sune shugabannin musulunci. Wadannan sune shugabannin musulunci domin dakin na ta ne. Kuma abokan shi ne a kwance madadin ya rubuta takarda yayi wa kanshi na wurin yace ya mallakawa gwamnati. Amma yasan cewa zalunci ne. Manzon Allah yace in kaci kasar wani da ni guda ranar kiyama za'a nan nado ta tun daga kasar ta daya har ta bakwai a dora maka a wuya a kada ka kayi wutar jahannama hadisi ne sahihi yana cikin Don haka dai ya rasu aka dauki gawa shi aka ji aka gaida Aisha aka ce ga Umar. Yana sallama ranka ya dade bayan gaisuwa kin bada izini cikin farin rai tace ai nayi izini. Shine aka je aka haka aka rufe shiyasa sai kaburbukan suka zama ga sunan haka. Ga kabarin annabi Ga kabarin Ga kuma kabarin ainihin Kaburbuka guda uku a cikin dakin manzon Allah Dakin a cikin ishiriniya yace Yace Allah ya dadin tsira ga kabarin Ahmad shine manzon Allah. Da kabarin Abubakar da kuma kabarin Umar kaji yadda tarihin yake zaka ga cikkaken tarihin yadda wadannan kaburbuka suke Allah madaukakin sarki ya kara musu yarda. To jama'a kunji karshe dai Huzaifa yace Ai abun da yasa Umar yasan maganar da na fadi gaskiya ce Hadisi ne na karanta mishi na annabi shi yasan ba shirme bane. Annabi ne ya fadi duk wadannan maganganu to ko da ike bance annabi ba amma yasan duk maganganun annabi ne don haka ya tabbatar da cewa shi Umar shine kofar kuma in kashe shi akai to za'a nada sabon khalifa lafiya kuma za'a zauna lafiya in mutuwa yayi. Amma in kashe shi akai to za'a nada sabon khalifa amma zaman lafiya bazai samu ba. Don haka har yau duniya bata sake komawa ta zauna lafiya yadda annabi ya barta ba har zuwa Abubakar da Umar kuma bazata sake komawa ta zauna lafiya ba. Ba wai addu'a muke ba a'a haka abun yake. Ana gamawa da kaza sai kaji kaza ya taso ana gamawa da kaza sai kaji kaza ya taso. Fitina ta yau daban ta gobe daban. Shekaru goma da suka wuce iri daban wata shekara goma ta ta daban haka fitin
[Segment 5/9 | 01:20:00–01:40:00]
[Speaker seg5-spk:0]
shine muna son muji cewa sadaka tana kankare zunubai, amma garin haka shine sai muka ji karatu mai yawa. Dan haka kar a manta har yanzu muna bayani ne dangane da falalar sadaka da kuma muhimmancin ainihin sadaka, da kuma bayani akan cewa lallai sadaka tana ainihin share dukkan zunubi, tana wanke musulmi daga dukkanin ainihin wani lefi. To jama'a bayan da kaji falalar sadaka da kuma bayani ainihin akan alherin sadaka zamu tsallaka zuwa ga kanun lacchan mu na gaba. Shine bayani dangane da muhimmancin kana da talauci amma ka kame. Kana fama da babu amma ka daure, ka cije, ka aji buƙatar ka. Abin da ke bayani akan mutum ya kame daga roƙo ko tambaya ko banbanci ko bara. Sahabi Abu Sa'id al-Khudri ya ce wasu mutanen Madina ne suka zo suka roƙi manzon Allah, ya manzon Allah bamu da abinci fa ne, bamu biya wa yara kuɗin makaranta ba, katanga ta rushe ɗaki na zuba, ya manzon Allah bamu yi abincin sallah ba, ya manzon Allah ana bin mu bashin kuɗin haya. Larurori ga su nan suka zo da manzon Allah iri iri. Manzon Allah ya ɗiba ya basu. Da suka ji daɗi kuma sai suka sake dawowa. Sai ɗiba ya basu. Suka sake dawowa. Sai ɗiba ya basu. Me yasa? Manzon Allah a cikin dikshinarin shi babu no. Babu babu. Babu a'a. A cikin karatun manzon Allah shi ba'a zuwa a ce ya bayar ya ce babu. Ko ya ce na hana, manzon Allah baya haka. In kazo in akwai sai ya ɗauka ya baka. In kaje ka yo kwana ka dawo ka ce baka sai ya ɗauka ya baka. In ka sake yo kwana sai ya ɗauka ya baka, shi baya cewa babu. Jama'a kun fahimci wannan shine manzon Allah. Duk duniya ba'a taɓa yin irin shi ba. Shi kaɗai ne kar cikin annabawa yafi kowa farar zuciya, yafi kowa alheri, baya tsoron talauci. Ko manzon Allah bai taɓa tara dukiya ba, bai taɓa ajiyewa ba. Hadisi yazo sahihi cikin Sahih al-Bukhari. Manzon Allah na zaune sai wata mata ta saƙo zani sutura ta sawa sabuwa kar zaran ma na musamman saboda wannan saƙan manzon Allah zata yi wa. Ta ce ya manzon Allah ina da masaƙa ne shine nayi maka saƙa ta musamman. Manzon Allah ya ɗaga mayafi ya kalle shi yaji daɗi sai ya shiga ciki sai ya cire. An fahimta jama'a? Ya shiga zai cire sai wani ya ce ya manzon Allah ina da magana, manzon Allah ya shiga. Ya fito kenan ya sawo yana murna. Sai wani ya ce ya manzon Allah don Allah ka bani wannan zani da ka sa wannan mayafi. Sai manzon Allah ya ce ina zuwa. Sai ya tashi sai ya shiga cikin gida. Yana shiga sai sahabbai suka ce kai dai baka da mutunci. Kana ganin mutumin nan an bashi yana murna yasa zai karɓa ya ce wallahi na roƙe shi ne don ayi mun likafani da abun, gashi sabo gashi ya taɓa zufar jikin shi. Shine nake so in ada na a lillibe ni ciki nima in samu rahama ta nan. Manzon Allah rahama ne. Fitsarin shi ma in ka sha aljanna zaka tafi, fitsarin manzon Allah. Balle zufar manzon Allah wadda take ƙanshi. Hadisi yazo sahihi cikin Abu Dauda da Ahmad da Ibn Maja da Tirmizi. Manzon Allah yayi fitsari a ƙoƙo da daɗare ajiye a ƙarƙashin gado, da safe sai ya tuna ya kira baiwa Barira e je kiki ɗakko fitsari yana nan a ƙoƙo ki zubar. Barira da taje sai ta tsuguna a gaban gado ta shanye. Sai ta fito sai ta ajiye ƙoƙo, manzon Allah ya ce ina fitsarin? Ta ce a na shanye ya manzon Allah, ya ce kije aljanna ta tabbata gare ki, wuta bazata ci ki ba. Fitsarin manzon Allah in ka sha aljanna zaka tafi. Amma ba'a ƙiyasi. Kar ka sake ka sha fitsarin wani wallahi. Ba wanda yake da wannan karamar duk duniya. Babu wallahi. Kar kaje ka sha kar ka sha gonoriya. Gonoriya siflis. Kar kaje ka sha ciwon fitsari. Kaje ka ka ka ka abun nan ka sha ciwon sanyi. Ko kaje ka sha aids kanjamau. Ba'a shan na kowa na manzon Allah ko ana shan shi. Saboda haka wannan mutum ya ce wallahi na roƙi annabi ne ba don komai ba don dai ayi mun likafani. Yana fitowa ko ya mi manzon Allah sai mutumin ne ya kuɗinda na abun shi. Ya maƙale, yaje gida ya ɓoye. Sahabi mai ruwa ya ce wallahi da shi mukayi mai likafani ko mutum. Saboda munafuki da Allah ya ce zai saka shi a wuta a qur'ani. Da ya mutu ɗan shi ya roƙi manzon Allah ya ce ya manzon Allah baba na kasan matsayin shi munafuki ne ɗan wuta ne. Amma kuma saboda tausayin uba ya manzon Allah ka taimake ni riga ka da kake sawa ta ciki jamfa wadda take taɓa jikin ka da zufa. Ka taimake ni ka ɗan lillibawa baba na. Ko zai samu sauƙin azaba. Manzon Allah ya ce insha Allahu, shi manzon Allah baya cewa a'a. Musamman wannan munafukin duk da munafuncin shi ya taɓa wa manzon Allah alheri. Da Hamza ya rasu sai ya kuɗunduno mayafi babba ya ce gashi kayi wa kawun ka likafani. To yau kuma shi kuma ɗan shi yazo ya roƙa, kuma ɗabi'ar shi baya cewa a'a balle gashi mukafa'a ce anyi mai alheri zai rama da alheri. Sai yaje ya ɗakko sai ya ba ɗan. Sai ɗan ya ce ya manzon Allah kar ka gaji dai. Yi haƙuri. Taso muje. Ka lillibawa baba na da kan ka. Kuma kayi mishi addu'a ka tufa mishi don dai ya ɗan samu sauƙi a dai ciccika dai haka. Har an saka shi a ƙabari aka ƙwaƙulo shi. Manzon Allah yayi tofi ya tufa mishi. Aka kawo aka nannada mishi don dai ya samu sauƙi. Shine Allah yake magana kanshi a qur'ani ya ce Wanda ya ɗauki nauyin yi wa Aisha ƙazafi yana da azaba mafi girma. Don haka tun a nan duniya Allah ya tabbatar da zai mai azaba. Amma manzon Allah saboda laushin zuciya manzon Allah saboda alherin shi ya ɗauki tufafin shi ya ba wannan kafiri munafuki zindiki wanda tsawon rayuwar shi gaba ɗaya ya ci gaba da cutar da manzon Allah ne. Manzon Allah baya cewa a'a. Jama'a kun fahimci wannan? Ɗaya kenan. To in aka zo wannan babin kam manzon Allah kuma hadisan shi basu ƙarewa. Sai dai bari mu kawo misalai guda hudu kawai kaji ɗaya. Misali na biyu manzon Allah Wani mawaki yayi zambo ya zage shi, sai manzon Allah ya ce a je a ciro kan shi. Kanin shi mawakin ya musulunta sai kanin ya rubuta takarda sai ya aika wa da wan shi to kai eh manzon Allah ya bada fatawa a kawo kan ka. Don haka ina baka shawara ka san yadda zaka yi in ma ka gudu in ma ka gudu kazo ka musulunta. To sai ya ɗauki shawarar ya gudu yazo ya musulunta. To amma ya zai ya kawo ga manzon Allah wani bai hadu da shi ya kwamtse shi ba. Sahabbai kuwa ya wa sauƙa shi tunda manzon Allah ya ce a kawo kan shi. To kafin ka iso daga tudun wada ka iso gwargwado wani ya hadu da kai ya cika da kai. Saboda haka sai rawani sai amawali irin na buzaye ya rufe jikin shi kaf ya rufe fuska. Sai ya taho gidan Abubakar ya ce nazo wurin ka ne ka saka ni cikin alfarmakka. Ya ce to waye ka ne ya ce a'a sai ka saka ni cikin alfarmakka tukunna. Ya ce na saka ka. Sai ya cire amawali, sai Abubakar ya ce amma mayaudari ne kai ya ce a'a. Naji anyi fatawa ne a kai na shine nazo in tuba to kada kafin in kai wani ya hadu da ni ya buge shine nazo in shiga alfarmakka kai kuma ka kai nurin annabi sai annabi sai Abubakar ya ce to mayar da amawalin ka kasan akwai sojojin Muhammadu suna a nan. Mayar da amawalin ka sai mai da amawalin shi sai abun nan. Ana tafiya ana ganin Abubakar da shi da wani buzu ne wannan wanene ne daga Nijar ne ko daga kwata ne eh? Abubakar ya kai shi ya zaunar da shi gaban annabi sallallahu alaihi wa sallam. Annabi ya ce Wanene faɗi waye ka ne ya ce a'a bashi amana dai. A bashi amana a saka shi a cikin jiwari ayi mai alfarma cewa ko an gane shi ba zai annabi ya ce an saka ka. Sai ya buɗe manzon Allah sai ya ce ka amma kai mayaudari ne sai ya miƙe tsaye. Sai ya ce Ya ci gaba da yabon manzon Allah. Yana ɗibo sunan kakannin manzon Allah ya nemi manzon Allah kirari. To kaji fa lefi ne ance a kawo shi, kuma yanzu yayi hikima yazo da manzon Allah yaji wannan mutum yana yabon shi yana faɗin gaskiya sai manzon Allah ya cire riga shi fa. Mayafin shi sai ya fa mishi. Ma'ana yanzu na yafe maka kai ga kyauta ma. Kun ji fa? Kai ka taɓa jin inda akayi haka? Anyi lefi an tuba an kawo maka mutum kazo yanzu ana son ya shiga beli ne ko ba'a karɓa ba ko yaya. Kuma daga ƙarshe mutumin ya tashi da kyauta mafi girma itace rigar ka. Duk duniya sai manzon Allah yake da wannan farar zuciya. Misali na biyu, misali na uku. Wani baƙauye yazo yayi musulunta wurin manzon Allah ya tashi zai koma garin su manzon Allah ya ɗibi raguna guda ɗari ya bashi. Wannan tsara ba ce, wannan guzuri ne. Da yaje badalar garin su sai ya tsaya yayi ihu a ƙofar gari ihu. Jama'a sai suka taru wani malak lafiya me yasa meka? Ya ce lafiya lau. Ya ce kuje ku musulunta a wurin Muhammadu. Muhammadu yana kyauta kyautar wanda baya tsoron talauci. Aka ce yaya jawabi ya ce ku duba na musulunta ne. Zan taho ƙauyen mu shine manzon Allah ya bani waɗannan rago ɗari. Jama'a ku duba. Baƙauye rago ɗari. Ka taɓa jin da akai kyautar rago ɗari duk garin ku? Sai a Madina manzon Allah yayi. Wani shi kuma misali na hudu azumi yayi shi kuma yana saduwa da matar shi da dare kuma ya sadu da ita da rana, kuma baya iya haƙura sai yaga tofa da watan azumin nan bazai iya haƙuri ba don haka sai yaga bari yayi zihari. Ya ce wa matar shi in ma ya sadu da ita da azumin nan to shikenan ta haramtu a kan shi. Ya ce ran nan ko sai ya ga matar shi kawai tayi wa wa kwanciya. Da daɗɗare don ya haramtu a kan shi ita ne gaba ɗayan da azumin ayi. In ba haka ba da daɗɗare ta halatta to gaba ɗaya ta haramtu a kan shi. Sai ya ga tayi wa wa kwanciya yayi sai ka sa haƙuri sai ya sadu da ita. To yanzu kuma tunda ya natso sai ya dawo cikin taitayin shi. To dama a ƙauye ne. Malamen ƙauye kuma karatu bai ishe su ba don zaka je wani ƙauyen duk ƙauyen ba wanda ya san ƙawa'idi har liman. To da ya za'ayi fatawa? Aka je aka samu liman, liman eh ga abun da is liman ya ce eh eh. To zaka enter bawa. Ya ce liman bani da hali. Ya ce baka da halin kaje kayi kai ka saɓa Allah. Ya ce to azumi sittin, ya ce liman eh talatin fa ta ja mana haka ya ce ba ruwa na dole kayi. To kana da yadda zaka ciyar da miskine sittin. Ya ce liman miskine sittin eh jiya da yunwa aka kwana gida na, liman ya ce tashi. Tashi ka tafi. Ka iya saɓa wa Allah baka san yadda zaka yi sadaka ba tashi, liman ya kore shi. Shine sai yayi tunani. Dama annabi ya ce Madina itace alheri. In ƙunci ya maka yawa tafi Madina. Matsala tayi yawa wallahi tafi Madina. Wallahi jama'a ko littafi ne ya mana tsada wani lokacin sai mu tafi Madina. Sai kaje ka same shi real 700 a Makka. Kana zuwa a Madina sai kaje ka same shi a wani bookshop real 780. Gata a aikace kun ganta. Kun ganta yau kusan shekara 15 Muna Makka mu rasa yadda zamu yi ta fito real 780. Ba kuɗi ɗalibi. Kawai sai muka shigo mota daga Makka zuwa Madina kawai da daɗɗare kafin gari ya waye kawai sai muka zo muka samu wani malami ya kaɗa mata bonanza real 780. Madina tafi alheri fiye da kowane gari. Duk matsala in ta same ka gudu Madina. Manzon Allah ina ya tafi? Madina kaima tafi Madina. Don haka kawai mutumin nan sai ya gudu Madina. Yana gudowa Madina aka kawo shi wurin manzon Allah sallallahu alaihi Yana zuwa wurin manzon Allah yazo ne da na shiga uku na lalace, manzon Allah ya ce kai zauna babu shiga uku a nan zauna. Me matsalar ka? Kazo ba matsala. Kazo Ba matsala me damuwar ka? Ya ce wallahi ya manzon Allah bani haƙuri sai nayi jima'i ne ko yaushe. To azumi ya kama nayi mata ta zihari cewa ma kaf azumin in na taɓa ta to kamar na taɓa uwa ta. To kuma tsautsayi ya kama ni jiya kawai gashi gashi. Manzon Allah ya ce kana da yadda zaka enter bawa mutum ne mai barkwanci sai ya dafa wuyan shi ya ce ya manzon Allah duk duniya in ba wuya na ba ban mallaki wuyan kowa ba. Manzon Allah ya ce to kana da yadda zaka yi azumi sittin mutum ya ce manzon Allah kenan duk wannan rikicin ai kwana 30 ne ya saka mu. To kuma in haka ce zamu yi kwana 60 to ai kaga rikici ya ƙarasa rikicewa. Bazan iya ba. 30 ma na kasa haƙuri ya manzon Allah balle sittin. Sai ya ce kana da yadda zaka ci da miskini sittin ya ce taɓ dai jan. Wallahi jiya da yunwa aka kwana gida na. Sai manzon Allah ya ce zauna. Ina ne garin ku? Ya ce gari kaza. Ya ce to kaje wurin wane. In kaje shine na sa ya tara zakka a gari. Kaje ka same shi ka ce na turo ka cewa a ɗibi zakka a baka. Ka ci zakkar a matsayin sadaka da kaffara da kai wa kan ka. Baƙauye a guje ya kwashe a guje. Ya tafi ƙauyen su, yaje ya tsaya a ƙofar ƙauye yayi ihu aka taru. Ka ƙaddara sai ya fara da zagi kenan tunda ya sha wahala a garin. Ya ce musu mugaye na hadu da ƙunci da wahala da muguwar fatawa a wurin ku ba rahama. Naje wurin manzon Allah na samu sassauci. Manzon Allah ya ce a bani zakkar ku in ci. In kunyi mun baƙin ciki to manzon Allah ya fanso ni. Jama'a kun fahimta? Wallahi kowane zamani suka ƙuntata maka ko ka gudu wurin manzon Allah. Shine me manzon Allah ya ce rabu da nasu kawai ka ɗauki na shi. Kar ka sake wallahi su baka wahala. Su ɗin ne su ɗin ne kuma manzon Allah shi ɗin ne shi ɗin ne har duniya ta tashi. Ga hadisan shi nan. An tara maka su, an tace su. Ka karanta shikenan kar ka yadda wani ya baka wahala a addini. Manzon Allah babu tsanani a cikin addinin shi. Jama'ar musulmi kun ji wannan. Hadisin nan da muke karantawa yana cewa ne an tambayi manzon Allah sun roƙo shi sun kawo buƙata ya basu, sun kawo buƙata ya basu, sun kawo buƙata ya basu. Baya cewa a'a. Wata rana anzo za'ayi ɗawafi a Ka'aba. Sai wani jikan manzon Allah yazo zai ɗawafi sai mutane sai suka ce bari su girma mashi gaba ɗaya kowa ya tsaya a barshi shi kaɗai yayi. Sai yazo yana kewaye Ka'aba shi kaɗai. Sai kawai wani da baƙan magana sai ya dube shi ya ce yasan ko waye. Kawai wulaƙanci ne sai ya ce wai waye wannan don Allah duk aka tsaya da Ka'aba saboda shi. To akwai wani mawaki yana zaune kusa da shi. Sai ya ce Ɗan gidan Fatima ne, jikan Fatima ne in baka san shi ba. Ya ci gaba da yabon wannan ɗa har ya kawo kan annabi a cikin yabon ne sai ya ce Kaga kakannin shi tunda yake bai taɓa cewa a'a ba. Ba don da kakannin shi yake cewa ba to da laɗin shi ma zata zama na'am ne. Don haka manzon Allah baya cewa babu. Baya cewa a'a. Baya cewa da matsala. Manzon Allah babu To amma duk da baya cewa babu ko baya cewa a'a amma ai yana nasiha. Bari ku ji. Sai da ya zama dukiyar da ke wurin shi kaf ta ƙare. Da da wani abu a wurin na bazan ɓoye muku shi ba. Ya ƙare duk abun da kuke tambaya ya ƙare, an tambaya ya kawo, an tambaya ya bayar, an tambaya ya bayar. Ya ce kuma wallahi daga wannan ya ƙare in akwai bazan ɓoye bazan kawo in baku. Amma sai musu wa'azi. Wanda duk ya kame baya roƙo Allah zai rufa mishi asirin yadda za'a ganshi a kammale.
[Segment 6/9 | 01:40:00–02:00:00]
[Speaker seg6-spk:0]
Wanda duk ya samu wadatuwar zuci. Allah zai wadata shi wadatuwar aljihu da hannu. Kai zaka sakawa kanka wadata zuci. Shi kuma Allah sai ya wadata hannun ka. Ku cire ku sa direct kawai. Duba duba bari kawai. Zauna kawai kai dai. Kai dai zauna kawai. Ka kashe ne?
[Speaker seg6-spk:1]
A'a.
[Speaker seg6-spk:0]
To. Wato muke nufi ku hakura da shi. Eh? Mmm kawai a hakura da shi. To shikenan sa. A danyi hakuri jama'a an dan samu rawa ne daga wuta din. Allah ya taimaka. Wanda duk yake hakuri. Da babu. To Allah zai rinka bashi abun da zai hakurtar da shi. Baka da shi sai kake hakuri ko? To Allah zai rinka dauka yana baka abun da za'a ganka mai hakuri din. Manzon Allah yace ba'a taba baiwa wani kyauta da tafi alheri da yalwata fiye da hakuri ba. Kyauta. Wanda tafi kowace itace hakuri. Kyautar da tafi kowace yalwata itace hakuri. Wannan hadisi yana nuna mana muhimmancin. Ka rinka hakuri ka rinka kamewa. Amma ba ya zama duk abun da ya taso maka an yi maka haihuwa. Sai ka nemi taimako. Zaka aurar da 'yar ka sai ka nemi taimako. Damuna tayi gidan ka na zuba sai ka nemi taimako. Dan ka bai da lafiya sai ka nemi taimako baka da hakuri baka da juriya komai ka gaza. Saboda zuciyar ka ta riga ta mutu. Bayan da Imam Bukhari ya kawo wannan sai kuma ya kawo wani hadisi Manzon Allah yace. Manzon Allah yace na rantse da Allah wanda raina yake a hannun shi. Dayanku ya dauki igiya. Yaje ya daso ice ya doro icen a gadon bayan shi. Yin haka shine mishi alheri. Ba wai yaje ya roki wani ba. Ya bashi ko ya hada shi. An baka. Kaji kunya balle kuma an hana ka. In an baka ma ka karba da hannu na kaskanci shine hannun ka na kasa. Balle ace an hana ka. Imam Bukhari ya sake kawo wannan hadisi cewa. Manzon Allah yace lallai daya daga cikin ku ya dauki igiyar shi. Yaje yayi ice kai guda ya doro shi a gadon bayan shi. Shine yaje ya siyar da ice. Allah ya kare mishi mutuncin fuskar shi da wannan ice. Haka shine alheri gare shi ba yaje ya roki mutane ba. Jama'a kunji maganar manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Ka dauki igiya. Kaje ka daso ice ka dauro shi dauri guda ka doro a gadon bayan ka shine maka alheri kadai. Ba wai shi yafi alheri ba karka fassara hadisin da aka kawo a'a. Haka shine alheri. Ba wai kaje kana rokon mutane ba. Su bashi ko su hana shi. Jama'a kunji wannan? To a cikin wannan hadisi akwai darussa masu yawa. Na farko annabi yana kara fassara mana waccan maganar. Gari ya waye kaje kayi sadaka. Baka da abun yin sadaka. Tafi kaje ka samu aikin yi. A'a baka san aikin da zakayi ba kaji daga cikin abubuwan da zakayi. Dauki igiya. Shiga daji. Daddaso ice ka dauro shi ka doro a gadon bayan ka. Dorowa a gadon bayan karya alkadarin girman kai ne. To amma. Wannan karya alkadarin girman kai kuma wajibine akan iyaye su fara wa yara tun daga kanana. Domin kun fari ya gama secondary. Duk 'yan matan anguwa ya gama musu karya. Yaje polytechnic. A'a yaje jami'a. Duk yaran department ko faculty ko kuma 'yan matan campus. Yana da wajen 'yan mata bakwai a campus din. Saboda haka duk inda ya kewaya a garin automatically akwai wata yarinya da zata ganshi ko kawar ta. Zai yarda ya yi wa ice? Kun fahimta jama'a? Zai yarda a irin wannan halin. Ya zauna yana kwankwasa kujeru ya kafinta. Zai zauna gaban keken dinki. Ba zai ba to hanya ta farko ta karya alkadarin girman kai. Ga 'ya'ya in sun girma shine tun suna kanana kai uba ka rinka daukan su kana tafiya da su wurin sana'ar ka kowace iri ce. Kowace iri ce. Kana aikin kafinta ne? Tafi da yaran ka. Da ya fara wayo kasa ayi mishi wata guduma ko da ta wasa ce. Samu wata karamar kusa ko yaya ce kasa shi ya rinka hada wani katakon. Ya saba ana wucewa ana ganin shi gashi nan shine kafinta. To ko ya kai shekara 60 ba zai ji cewa kaskanci bane ya ganshi. Tun yana dan shekara bakwai dauke shi ka dora shi akan keken dinki. Ko ya kai shekara 30. Ba zai ji kaskanci a ganshi a kanshi ba. Tun yana dan shekara goma kana zuwa da shi gona. To ko ya shiga jami'a ba zai ga cewa abun kunya ne. Wannan me yasa jiya baka zo lecture ba sai ya ce wallahi naje zuba taki ne. Kaga wata yarinya ta kalle shi taki eh a ina? Yace a gona. Yace ah. Saboda me? Yana cike da alfahari yana da confidence. Yana da izza yana jin daraja ce. Amma yanzu kai kaje ka samu wadannan yara. Yana jami'a ko yana polytechnic ko yana FCE. Ya cika 'yan matan gari da karya. Duk inda wata mota ta wuce ya gaida mai motar sai ya ce wannan karamar mamana ne fa. Eh wannan karamar mamana ne. Ina fata an gane? Yaje ya dauki hotunan gidaje masu kyau. Ya zuba a cikin lecture note. Wacce ta karbi arrow note din shi sai ta duba ah. Wannan fa wannan gidan ku ne yace ah wannan wasu gidaje ne ma baban mu ya haya zai bayar. Haya zai bayar. Eh duka. Saboda karya. Amma an jima sai ya zo yana cewa haya dai. Dan Allah baby ko akwai dan bom bita a dakin nan naki? Ke da kina da wayo sai ki hada masu sababbin gidajen haya shine yazo yana nokon ki bom bita? Daga nan zaki gane karya ce amma. 'Yan matan basu da wayo. Ina fata an gane? Saboda haka hanya ta farko ta karya alkadarin girman kan mutane shine tun suna yara a dora su akan abun da yake abun nan shine daidai. Jama'a kunji wannan hadisi na annabi sallallahu alaihi wa sallam. Wani sahabi ne dattijo sunan shi Hakimu dan Hizam yazo wurin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yace. Na roki manzon Allah sai manzon Allah ya bani. Na dawo na sake rokon shi ya dauka ya bani. Na sake rokon shi sai ya dauka ya bani. Sannan sai manzon Allah yace dani. Ya Hakim ya kai Hakimu. Kaga dukiyan nan kyau ne da ita a ido koriya take shar. Sannan zaki ne da ita a baki kamar alewa. Wanda duk ya karbi dukiyan nan cikin farin ran wanda ya bashi. To za'a samu shi albarka. Jama'a kunji sirrin albarkar? Ka karbi dukiyar a hannun shi yana fara'a yana baka. Haka duk wanda ya karbi dukiya a hannun wani. Cikin farin rai daga wanda ya bashi. To Allah zai albarkaci dukiyar. Wanda ko ya kwallafa ran shi akan dukiya saboda kwallafa rai. Har wannan mutum ya dauka ya baka. Ba za'a taba albarkatar shi akan haka ba. Shine ka sa a ido. Yanzu dubi yadda almajirai suke. Mutum ne yazo ya zauna. Ya sai tuwo kwaya biyu. Sai kaga tuwon kamar girman gwaiba. 'Yan tsugul tsugul an zuba mishi miya a sama. Da namayan ka daya. Kai kuma almajiri sai kazo sai ka tsuguna sai ka aje kwanon ka haka sai kayi haka. Dan Allah shi me yaci balle ya san maka. To amma ka kura mishi ido duk wata lauma kana kallon shi daga sama kana kasa. Ya dawo kana. To ka kalla fa rai. Sai ya dan rage wata 'yar loma sai ya mika maka ba zata yi albarka ba. Saboda ka kalla fa ran ka. Har kalla fa ran ka. Ah ka gano wane yana da kudi. Kai kenan yau kazo kofar gidan shi. Gobe jibi kana ina kana ofishin shi. Gata kana buga mishi waya. Ka kalla fa ran ka sai kaci wannan dukiya. Ko an baka manzon Allah yace. Ba zata yi albarka ba. Annabi sai yace sai ka zama kamar wanda yake ci baya koshi. Ku dubi wadannan almajiran namu. Akwai almajiran da zaka samu ta shekarar 30 tana bara. Akwai almajirin da zaka san ya shekarar goma yana bara. Ya kalla fa ran shi akan dukiya. Sai ya zama kamar mai ci ne baya koshi. Sai annabi yace. Sannan kuma hannun da ke sama yana bayarwa. Shine alheri. Fiye da hannun da ke kasa yana karbe. To Hakimu da yaji wannan wa'azi na manzon Allah. Sai Hakim yace. Sai nace ya manzon Allah. Ina rantsuwa da Allah da ya aiko ka da gaskiya. Nayi maka alkawarin bazan sake karban komai a hannun wani ba har in rabu da duniya. Ana nan sai manzon Allah ya rasu. Abu Bakr ya zama khalifa. Sai Abu Bakr ya kira. Hakim Hakim u zo ka karbi kyauta. Sai ya karbe. Har zamanin Abu Bakr ya kare shekara biyu. Hakim u bai taba karban kyautar shi ba dan yayi wa annabi alkawari. A zamanin Sayyidina Umar yanzu ba kyauta bace. A'a. Dukiyar gwamnati ce ta kai ta kasaita kamar yadda lokacin gawan aka ci odoji. Duk dattijo dan shekara 40 50 60 yasan me nake fadi. Dan shekara 30 kai ba'a ci da kai ba yi shiru. Zamanin gawan ne aka samu kudi. Kudi suka yi yawa a kasar. A lokacin kuma ana da karancin masana harkar tattali. Na am wannan ni nake wannan ta'alikin muna da karancin masu ilimi game da tattali. Aka tafi kasar Liberia aka biya musu albashi na shekara biyu. Shekara biyu duk ma'aikatan Liberia gwamnatin gawan ta diba aka biya musu an rasa ya za'a yi da kudin. Kuma ba masu shawara da za'a ce to ga abun da za'a yi. Da sai abu kowace karamar hukuma ko wane kauye sai a gina jami'a. Abun da sarki Fahd yayi kenan sarki Fahd ya samu haka a zamanin shi ya samu kudi da ba'a taba samun su a kasar Larabawa ba kaf. Sai bi duk wani gari. Ba local government ba fa gari. Ko ayi FCE ko ayi polytechnic ko ayi university. Duka a Saudi Arabia haka aka yi.
[Speaker seg6-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg6-spk:0]
A zo Zaria city ko sai ayi university. Sai a taho sabon gari sai ayi polytechnic. Ina aka tafi kudan sai ayi FCE. Haka aka yi duk Saudi Arabia makaranta ce yanzu ko ina akwai tashri'in su ciki ko wane gari ba wai local government ba. Saboda suna da mashawarta mu kuma a lokacin akwai karancin karatu musamman zamanin soja ne in kai magana ma sai a daure ka. Shikenan. Sai aka samu wani ina jin ya muri ne ko mutumin kalaba a lokacin wani masani sunan shi Odoji. Shine wakilin gawan akan haka sai aka ce abun da za'a yi duk ma'aikatan Nigeria a raba musu kudi. Ma'aikatar railway. Ma'aikatar Nitel PNT ma'aikatan talabijin duka aka yi ta raba musu kudi malam. Ka ga mutum ya shigo kasuwa. Sai ka gan yace wannan nawa aka ce su biyu sai ya ce a bashi ashirin. Ina fata an gane? Muna yara a babban titin Muciya. Wani ma'aikacin railway yaji ya karbo irin wannan Odoji malam su a babban kudi 'yan biyar biyar ya zubo su a aljihu. Ya aje sauran a gida wannan yaji ya sha giya ne ya taho ya wuse ya kado cikin Muciya. Da 'yan biyar biyar din shi malam. Yazo ya samu wani mahauci a tayi. A tayi yana gasa yana gande kan a waki. Yace ah to yana sai ya sai ya dauki 'yan biyar su biyar irin ta da sai ya gata ya sha giya ne in ya ya gasa sai ya wasa mana mu kuma sai ayi bindo sai a karba. To kai ka karbi rabi ni na karbi rabi muje a jona. Sai a je ayi chanji haka ake yi sai ya ga ne sai ya jefa. Chan sai ya zo kan ganda a tayi. A tayi nawa nawa kan awaki to a tayi ya ga yana zubar da kudi a banza? Sai ya ce su biyar sai ya ce a tayi dan ka ga na sha giya ai ina nan da hankali na. Duk a lokacin Odoji aka yi wannan shigan ta kar misali ne nayi muku kawai jama'a. Ina fata an gane? To. An fahimta jama'a? Kudi. Sun samu haka a zamanin Sayyidina Umar amma shi Sayyidina Umar sai bai almubazaranci ba. Sayyidina Fahd duk wani wanda ya zauna da manzon Allah namiji ko mace. Sai sa aka yi mishi designing payroll system. Ko ma'aikacin gwamnati ne ko ba ma'aikacin gwamnati ba ma'aikata suna nan da albashin su amma duk wani sahabi namiji ko mace. Sannan duk wasu 'ya'yan sahabbai. Duk wasu marayu. Duk wasu wadanda mazajen su suka mutu yasa aka yi mishi takarda gaba daya aka rubuta sunan su. Sai aka ainihin zuba musu ainihin allowance da za'a rinka basu duk kwana ashirin zuwa ashirin da biyar ga wata. Duka. Shine Aisha tace bamu cinye na tsohon wata ba sai na sabon wata yazo. Shekara uku da ta wuce ina jin ko shekara hudu kasar Saudi Arabia ta sake samun irin wannan kudin. Muna Saudiya a lokacin nan. Wani abokin mu an bashi kudi haka. Yazo ya baza su sai ya gigice. Ya kasa kirgawa yace nawa ne nan nace a kirga mana yace ai bazai iya kirga wato ya zare ne bazai iya kirga ba. Ya rude bazai iya kirgawa ba. In yayi kaza yayi kaza yayi kaza sai ya ce. Ai. In ya in ya kamar zai kirga sai ya ce. Sai ya ce sarki Abdullah sarki Rahma ne sarkin mutunci ne. Wai sai yace mu me kake bukata ne malam sai in ce mishi sai in ce la. Ina fata an gane? Malam a primary school. Yana karban real dubu goma sha bakwai sai ka buga dubu arba'in so dubu goma sha bakwai. Sai ace an ninka mai so biyar. To shine in yazo gida sai ya rikice. Ko an fahimta? Wani yace zai yi retire ayi ta lallashin shi yace a shi ya samu abun da yake so haka. To shine da suka samu wannan kudin jama'a shine kuka ga wadannan abubuwan da suke yi. Da sarki Abdullah yazo ya tsaya. Anan daidai babu Malik Fahd. Daidai kofar sarki Fahd sunan kofa ce kawai. Sai ya ce yana son ayi titi tun daga nan har Jidda kawai a haka a tsaye kawai. Kamar kace tun daga nan har kawo ma'ana in ce ina son ganin tashar kawo haka. Gida nawa za'a buge yace ba komai. Aka kewaya filin Arafat yace yana so ayi titin jirgin kasa. Amma bazai
[Segment 7/9 | 02:00:00–02:20:00]
[Speaker seg7-spk:0]
hana masu aikin hajji komai su cigaba duk wani gini kuma. Don haka kawai sai aka tada filoli, filoli. Sai aka tayar, sai aka tada titin jirgi a sama. Aka dawo Ka'aba. Shine yanzu aka zo aka yi mata wani irin ƙari, tsarki ya tabbata ga Allah. Da na san misalin zai kai mu ga haka da na ɗauko muku bidiyon kun gani akan komputa. Wato abun ba roba bane ba kata ko bane balle kace siminti ko dutse a'a. A cikin kwana biyu za'a iya zuwa a haɗa shi. In aka hațashi an sake haɗa wani wurin sabon ɗawafi hawa biyu. Kuma in an so za'a iya cire shi sai Ka'aba ta koma yadda take. Ba abunda zaka gani. Har sun riga sun gama. Shi yasa bana suka taƙaita bada visa da sauransu saboda wannan aikin da ake. Sannan su rusa waɗannan hotels suna son su fitar da waɗannan tituna da ake magana. Toh ba nan ba. Wannan riba ce aka samu irin taku ta PTF ta zamanin a bace raran man fetur. Riba ce aka samu ba wasu kuɗi ne daga saman bakwai ba, kuma kun samu irin su a ƙasan nan. Shine sai aka ce za'ayi wata jami'a. Kun ji ta a BBC ko? Har an gama jami'a an ɗauki ɗalibai. Sai aka koma Jami'ar Islamiyya ta Madina wadda duk duniya ba'a taɓa ƙafar jami'a da take karantar da addinin musulunci na gaskiya irinta ba. Aka koma aka rusa ta. Aka ce ba sauran ɗalibi biyu a ɗaki suka ce haramun ba'idin. Kowanne ɗalibi kwana shi daban. Kowanne ɗalibi ɗakinki daban, lokarka daban, komai naka daban. An faɗi wannan ko? Wallahi shekara ta kewaye na shiga Jami'ar Islamiyya kawai wani ɗannan yace mun sai na ganshi ɗakinki daban nace oh. Allahu Akbar. Tsarki goma, zamani goma. A da haka za'a zube su haka gashi nan kowa daga ɗanshi kana jin mun sharin wani. Amma yanzu kai kaɗai a kwananka ka rufe ka fita. Duk da suka gama wannan sai suka ce bai ba sai aka dubi wani ƙwari jama'a kaga kubanni ko? Yadda kaga kubanni ɗinnan ƙwarin kubanni ɗinnan a jikin Jami'ar Islamiyya shine Gaba ɗaya sai aka share shi kawai sai aka ce ayi Jami'ar Islamiyya kuma ta Turanci. Jami'ar Islamiyya ma ta Turanci yanzu za'a riƙa karantar da Jami'ar Islamiyya ce amma Turanci ne kuma goko. Kuɗin ne ba an rasa yadda za'ayi dasu ba amma shine ake ta ƙirƙiro irin wannan. Duk da aka gama sai aka ce toh ai cikin garin Makka akwai matsalar ruwa. Cikin garin Makka akwai matsalar ruwa. Wannan irin matsalar ta cikin garin Makka ai ita ta faru a lokacin Sarki Fahad aka rasa ya za'ayi a samar da ruwa. A Mina da Muzdalifa da Arafah. Kun sun Sahabbai sun sha wuya shi yasa suke cika jarkokinsu jajibarin Arafah sai su tafi da ita shi yasa aka sawa ranar Ranar cika buta da ruwa. Sarki Fahad a zamanin shi sai yasa akai Yasa a binciki ƙasar a gano ya za'ayi a iya tono ruwa a wurin. Sai aka gano duk dutsan da yake nan haka kuma yake ƙasa fiye da yadda yake a sama. Aka ce babu injin da zai fasa shi sai yace aje ayo mai injin da zai fasa shi, shi ayi mai injin da zai fasa shi. A haƙo mai ruwan wurin yake so a sha. Shine aka je akai mishi da suka fasa. Aka je akai a ƙasan Mina da Arafah da Muzdalifa sai yasa ba alhajin da zai ce maka yaje Mina da Muzdalifa bai yi wanka da ruwan ɗumi ba. Ba dafawa ake ba daga can ƙasan ƙasan dutse ne. Kuma awa ashirin da huɗu in ka buɗe zaka ganshi tar ya zubo. Amma a zamanin Sahabbai babu ko ɗigo guda. Shi yasa har Sayyidina Abdullah Ɗan Umar yake cewa Yace duk ranar kuka ga ruwa a Mina kuma duk ranar kuka ga tantunan Mina sun shallake duwatsun Mina yace toh duniya ta kusa tashi ku jira saura kaɗan. Shine wannan zamanin da muke ciki. A wancan zamanin zasu kafa tantunan su ne in kazo ba abunda zaka kalla sai me? Sai duwatsun amma a yanzu fa Tantunan kawai ake kallo. Mun shiga da wani dattijo muna zuwa yace nan ƙaburbuka ne nace rumfunan da zamu zauna ne. Sannan ba wannan ba, kaga waɗannan tantunan ko? Toh wuta bata cin su sharifai ne. Ko anyi gobara su basu aƙonewa sharifai ne. Wuta bata cin su. Saboda gobarar da aka taɓa yi a lokacin Sarki Fahad wajen shekara bakwai da ta wuce ko makamantan haka sai yace toh yana son aje ayo mishi tantunan da wuta bata cin su. Shine aka je aka yo sharifan tantuna. Ka san sharifi ance wuta bata cin shi. Ance nace bance ba. Ina fata an gane. Toh jama'a kun ji. Abdullah Ɗan Umar yace duk randa kuka ga tantunan nan sun fi duwatsun girma toh ku jira tashin gyau. Yace duk randa kuka ga ruwa a Mina toh wallahi jama'a yanzu in kaje ka kunna kan pamfo ko shawa ko in baka kauce ba sai ta ja maka matsala a kanka da ƙarfi. Daga can ƙasan ƙasan dutse akai wiring. Kun ji aikin da ake da kuɗi jama'a. Sannan kar ku manta maganar da na gaya muku ku ƴan Najeriya muma sunyi mana irin yadda akai ɗin ne. Sunyi mana muma irin yadda mukai walaliberia. Ƙasar Saudi Arabia a zamanin Umar u Musa ƴan adua Allah ya gafarta mishi. Aka je aka zauna da shugabannin mu na kawo muku wannan tarihi kaf na faɗi suna kuje ku nemi kasusuwa na 53 54 zuwa da biyar har zuwa 60 na fiqhu sirah duk na tattauna wannan matsala. Aka je aka zauna da shugabannin mu aka ce meye matsalar wutan lantarki a Najeriya? Aka ce ita kanta wutar ce matsala. Da injinan da da injina irin waɗanda suke Aka ce duk abinci ko abunda zai wadaci Najeriya daga zamanin ƴan adua zuwa shekara ɗari an rubuto aka rubuta. Aka tafi aka je aka kai musu hadda palwaya gaba ɗaya suka baiwa Najeriya. Shine Umar Musa Ɗan adua shi kuma ya fitar da kuɗi naira wuri na gugar wuri naira biliyan goma sha ɗaya. Aka sace kuɗin aka rabe su duka ba'a bar kokwabo ba. Sannan aka fitar da kayan kayan kuma zasu shigo ƙasar akai kwana dasu aka je aka sai dasu a wata ƙasar. Ita kuma hukumar NEPA ɗin fa aka zo aka kaɗa mata gwanjo aka siyar da ita a matsayin Saboda mu gunta sai aka siyarwa da waɗanda sune jami'an siyar da ita. Kuma aka siyar musu da kuɗin da kowanne ma'aikacin NEPA a yanzu dake ciki komai ƙanƙantar shi da sai a siyar mai da shi ya shima yana da kuɗi yana bin NEPA kuɗi kuɗin da shima zai iya siyan hannun jali saboda an siyar da ita ne a matsayin wato a matsayin fasashen buhu. Kaga fasashen buhu baya ɗaukan kaya. Ba'a shimfiɗa shi a kwanta sai dai a cusa shi a kasko a tada wuta da shi a haka aka sai da hukumar NEPA. Aka siyar da ita da Aka cinye biliyan goma sha ɗaya na Umar Musa Ɗan adua waɗanda suka cinye aka kai su kuje friji in suka yi kwana ashirin da takwas zuwa da tara. Sarakunan mu masu alfarma suka je suka karɓo su. Sannan su kuma waɗannan dukiya fa ba'a shigo dasu Najeriya ba akai kwana dasu aka je aka siyar dasu a wata ƙasar. Na faɗi wannan a karatutukan nan duk na bayyana muku komai na faɗi sunaye ni ganau ne ba jiau ba nasan mutanen ɗaya bayan ɗayansu duk da akai wannan abu da waɗanda aka kai kurkukun da komai kuma aikin ni da hannu na ne typing ɗin shi muka saka shi a internet. Daga baya duk suka zo suka janye waɗannan abubuwan akai musu komai. Muma ƙananan alhaki da mukai aiki muna bin ƴan miliyan talatin da wani abu aka cinye. Aka ƙi biyan mu. Kai Najeriya Najeriya Allah ya gyara mu. Toh jama'a kun ji. Allah mai maɗaukakin sarki ya gyara al'amuran mu.
[Speaker seg7-spk:1]
Yau Sayyidina Umar alkawarin cewa bazai ƙara karɓar
[Speaker seg7-spk:0]
Eh na'am shine hadisin yau Sayyidina Umar alkawarin cewa bazai sake karɓe ba tunda yaki karɓe a zamanin Annabi da Abu Bakr. Toh meye faru? Yaki karɓan kuɗi daga Umar kuma kuɗin nan right ne ba ba kuɗi ne na kyauta ba irin zamanin Abu Bakr irin zamanin Annabi a'a wannan dukiyar gwamnati ce aka ce a raba wa kowa. Misali Zaku ga inda chairman na EFCC wanda ya gabata Nuhu Ribadu yake cewa Daga 1960 zuwa 2005 Shugabannin Najeriya sun sace dala biliyan dala ba naira ba dala biliyan dubu 500 Da masu ƙididdiga suka fitar sai suka ce duk Ɗan Najeriya a ƙarƙashin wannan kuɗin wanda mun kai miliyan 550 mun mafi suka ce za'a iya ba kowa miliyan goma sannan ta rago. Kowa miliyan goma. Malam Ahmadu ya in ka samu miliyan goma? Darul hadisi sai dai mu ji ka a internet sai dai ka Eh Ko kun fahimta jama'a? Aka ce kowanne Ɗan Najeriya har wanda aka haifa ana cikin lissafi ana cikin bada kuɗin sai wanda ta haihu sai ace miliyan goma. Tun ba'a san sunan shi ba miliyan goma. Aka ce kuɗin zasu rago. Waɗanda aka sace ne waɗannan banda waɗanda ake dasu gasu nan. Kai in ka kalli abunda akai akan wutan NEPA ɗinnan kawai ya isheka ka gane halin da ake ciki. Sannan kaje ka sake buga Ko kuma ka tafi kan YouTube Sai ka tafi search bar ɗin sai ka sa Zaka ga da masaka wadda ta faru a zamanin mulkin Obasanjo a nan zaka ji yaran Obasanjo ne gasu nan ya rabawa ne yaran Obasanjo kai tsaye Baba ma suke ce mai amma suka ce saboda ɗin NEPA Obasanjo yasa aka kashe Bola Ige yasa aka kashe wane da wane duk gashi nan. Video ne nan bama text ba ba karanta zaka yi ba zaka saurara ne da Turanci tashar talabijin ce akan internet ƴaƴan ya rabawa ne kuma suka yi shooting nata kai tsaye suna magana akan mai gidan su Obasanjo. Toh jama'a wannan shine halin da muke ciki a ƙasar amma duk da haka kaga mun rayu har muna magana yanzu. Mun karya kuma mai yiwuwa ma in jima zamu sake ce insha Allahu. Toh mu gode wa Allah kuma mu cigaba da addua Najeriya zata gyaru. Amma zata gyaru kayi ƙoƙari ka zama ɗaya daga cikin Na'am Najeriya zata gyaru. Amma kayi ƙoƙari ka zama ɗaya daga cikin waɗanda Allah zai aiki dasu wajen gyara ƙasar amma fa wannan baya nuna kaima zakai zalunci. Kaima sai ka haƙura da zalunci don baza'ayi ja ya faɗo ja ya ɗauka ba. Shine abunda yake faruwa a irin ƙasashen Congo abunda yake faruwa a irin ƙasashen su Liberia da Sira Leon an kori wane azzalumi ne wane kuma ya dawo ya fishi zalunci. Tambaya ita ce ina kuɗaɗen da aka karɓo a hannun ƴaƴa da zuriyar Abacha? Shine ja ya faɗo ja ya ɗauka. An ce wane ya sata. Bayan an karɓo kuma sai ace toh shikenan wane ya ɗauki kaza ɗauki kaza toh haka bai fi ba? Toh shi can ya sata ba'a sani ba kai kuma sai da aka sani tuku na. Toh Allah ya kiyaye. Sayyidina Umar yana kiran Hakimu zo ka karɓi kuɗin ka. Alawans ne naka ba kyauta bace ba ni Umar na baka ba gwamnati ce ta tayi kuɗi aka ce kai sunanka ya fito zo ka karɓa. Yaki sai Umar yace Musulimi ku zama shaida ta dangane da Hakim. Dukiya ce ta gwamnati gashi ina bashi Hakimu dama yayi alƙauri bazai karɓi kyautar kowa ba bayan manzon Allah ko? Duk da wannan ƙafa shaida da Umar yake Hakimu har ya mutu bai karɓa ba. Sarki ya tabbata ga Allah. Kun ji waɗanda ke faɗe kuma su cika abunda suka faɗa. Jama'a kun ji wannan. Bayan wannan sai mu tsaya da kyau mu dubi waɗannan na soshi jama'a suna nuna ka mewa ko basu nunawa? Suna nuna. Hakim ya roƙa Annabi ya bashi ya roƙa an bashi ya roƙa an bashi sai Annabi yayi mai wa'azi toh da yayi mai wa'azi shikenan sai ya kame. Sai yace toh bayan kai bani sake karɓan kyauta ma wurin wani. Shikenan bai sake karɓe ba. Abu Bakr ya bashi ya ƙi karɓe, Umar ya bashi haƙƙin shi ne amma yace ai yayi alƙauri bazai sake karɓe ba. Haka ake so ka kame. Jama'a mun fahimta? Toh sa'annan sai kuma Imam Bukhari sai yace Mun yi magana dangane da ina masu neman dukiya masu roƙo masu bara masu tumasanci don tara dukiya. Je ka ka samu ƴan uwan mu Hausawa gasu nan tur a Lagos. Suna bara amma in ka taho Zaria ko Kano ko Sokoto ko Katsina zaka ji wannan kuturwar dake bakin hanya tana da gida biyar. Ta samu gidaje ta gina da kuɗin bara da take a Lagos amma kuma ta koma tana cigaba da bara. Tana sake tarawa zata sake siyan gida kaza zata sake siyan gida kaza. Gasu nan sune a Makka. Zaka ga Baushe ne ya nann da hannun shi haka a cikin riga ya miƙo shi ta alkyabba yana lilo haka. Yana tafiya yana ɗangash . Zaka gansu gasu nan kamar yadda na faɗi da zaka ga da kaina ne shooting ɗinsu na ɗauki hotonsu a ainihin kemara. Gasu nan a wurin jifon shedan a wurin hawan Arafah gasu nan a Muzdalifa gasu nan a ko ina a cikin gari. Suna roƙo. An ɗibe su ne an kai su da nufin cewa duk abunda suka tara toh suna da rabi. Ko kuma an ɗibe su ne an kai su cewa in suka biya kuɗin jirgi da guzuri da aka basu toh shikenan za'a bata passport ɗinta shikenan sai ta shiga gari. Don haka wata in ta shiga gari zata cigaba da bara. Amma wata wallahi karuwanci zata cigaba. Ina faɗin wannan magana wasu abokaina waɗanda yake asalinsu Hausawa ne a cikin garin Makka suna jin kasusuwan nan suna cewa basa jin daɗi toh nan asiri ake musu. Sai da na taɓa sawa wata rana suka taru kusan su arba'in a gidan wani abokina nace ina da magana dasu. Nace idan zaku kare Baushe a garin nan ku kara mutumin kirki nace amma ko mu a Najeriya da muke tsakiya Hausawa bama kare ɗanyan aikin Baushe. Amma duk abunda Baushe yayi sai ku ce zaku je ku tsaya mishi zaku je ku abun nan zaku je ku abun nan. Akwai wanda Hausawa suke da gidan giya a cikin Makka. A cikin garin Makka suna da gidan giya burkutu ana burkutu ana sha. Akwai gidan karuwai akai ƴan Daudu akwai kawalai. Wannan a cikin garin Makka ake magana in aka taho Jidda ko wannan bata da babbanci da ita da Sokoto ko Katsina ko Zaria. Duk shegantakar da ake ana yi a Jidda amma nan ana magana a cikin garin Makka. Zaka je ka samu sunayi. Sannan da yawanci ƴaƴan sai suke karatu. Fa abunda zasu yi sai su yi dako. Sai gadi sai abubuwa na ƙasƙanci. A daidai lokacin da ƴan Sudan baƙaƙen fata in suka haifi ƴaƴansu a Makka gwamnatin Saudiya zata basu dama suyi secondary. Na'am duk wanda ya haifi ɗanshi a Makka ko yaje na da takardar izinin zama gwamnatin Saudiya zata ɗauki nauyin karatun ɗanshi tun daga nursery primary har secondary school kyauta baza'a karɓi komai ba. Matukar uban shi yana biyan harajin da aka ɗora mishi na iƙamar zaman shi. Toh amma bazai jami'a ba sai dai yayi ta kuɗi. Toh ƴan Sudan sai suyi dako sai ya turo ɗanshi Sudan. In Ɗan yazo yayi karatu in ya koma kuma sai gwamnatin Saudiya sai ta bashi aiki babba. A mutunta shi sai ace saboda shi yana jin Larabci irin na ƴan ƙasa yasan al'adunsu don haka in aka ɗauke shi likita ko engineer sai kuga ya samu babban muƙami. Na ga bata wa da ƴan uwa na Hausawa mutanen Makka wannan. Amma ina? Abunda suke gani kawai abunda wani ya miƙe sai yace mun toh ku ce su fidda kuɗi su gyara ƙasa tuku na sannan mu zo ina suka zuwa mu sha wahala? Nace Sudan babu wahala? Nijar babu wahala? Duk akwai amma suna turo ƴaƴansu suzo suyi sai kuma su koma kuma ku turo i ce a ina muka je mu sha wahala? Toh su zauna yanzu gashi nan duk unguwannin nasu gwamnati ta bada
[Segment 8/9 | 02:20:00–02:40:00]
[Speaker unknown]
doka gabaɗaya a kore su a rushe unguwannin. Sai mu gani da zasu zauna. Rayuwa ba zata yiwu ba jama'a. Ace ana jiran sai an yanka hadaya. Ko kuma wasu alhaze sun zo sannan ko kuma zaku rayu a jikin su a sadaka. To sa'annan sai mu dube yaya rayuwar mu take a nan. Yanzu akwai mutanen da su kuma zaka gan su ba almajirai bane. Maroka ne su kuma smart maroka. Su ba zuwa suke wai su tsaya suna ta roko a gidan suna ko biki ba a'a. Zasu shiryo ne da manya manyan riguna. Da mota ta alfarma. Sai suzo gidan ka sai suce suna sallama da kai. Kana fitowa. Sai a gaishe ka ace kawai wai anzo maka fatan alheri ne. Idan ka fahimta ka kki ka fahimta. Ko kuma tun farko baka fahimci waɗannan maroka bane. In ka juya zaka tafi sai suce sai dai akwai magana da Allah. Wallahi su sun zo daga unguwa kaza ne ko daga gari kaza ne. Don Allah abunda suke so shine don Allah suna so a basu kaza a basu kaza sai ka dube rigunan jikin su. Sai ka dube irin motar da suka zo da ita. To wannan nema ne na bara. Da bambadanci da tumasanci takasuran haramun ne a musulunci. Don haka 'yan uwa musulmi kusan wannan. Haramun ne kayi bara. Ko roko don neman tara dukiya haramun ne bai halatta ba. Shine Imam Bukhari yace babu man sa'ala. Ina matsayin wanda ya nemi mutane su bashi kudi. Domin kawai yana son ya tara dukiya. An fahimta jama'a? Waɗannan mata da kake ganin su suna yawo a cikin garin Makkah. Ka ganta tana yawo da yara. Tana bara wuri wuri. Da zaka taho nan garin su sai kaji ance tana da gidaje uku. Sai kaji tazo ta kashe auren kanwar ta. An sai da kayan ɗaki an biya mata tikiti an tafi da ita. Barna iri iri babu wanda ba'a yi. To waɗannan abubuwa jama'a haramun ne. Kuji maganar da Annabi ya faɗi game da mutanen da suke bara. Ko roko. Ko bambadanci da tumasanci. Annabi yace Mutum bazai gushe ba. Yana ta rokon mutane. Yana ta tambaya. Yana ta bara. Ashe naman fuskar shi yana ta kwakulewa yana raguwa. Naman fuskar shi yana ta zarewa yana fita. Har yaje ranar alkiyama in ya tashi sai ya ga abun ya bayyana mishi a gaske. Sai ya ga fuskar shi ta zama kwarangwal gabaɗaya babu nama. Domin nama. Cikkon mutunci ne na fuska. Don in aka ce babu shi to babu mutunci. Don in aka wayi gari haka fuskar ka take a ranar alkiyama wuta zaka don alama ce ta 'yan wuta wannan. Don haka jama'a musulmi kunji wannan hadisi na manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. To duk da waɗannan bayanai ina so in karkare bayanar nan nawa da cewa. Ka sani da cewa ya kai 'yan uwa musulmi. Idan har. Dukiya ce Allah ya kwararo maka ita ba Baka roka ba. Baka bayyana buƙatar ka ba. Baka tambaya ba kawai aka kawo aka baka to shari'ar musulunci ta umarce ka da ka karɓa. A nan shine Imam Bukhari yace babun. Mutumin da Allah ya bashi wani abu ba tare da ya roka ba. Sai kawo ayar da Allah yake cewa Masu kudi. Su sani da cewa Allah ya wajabta haƙƙi a cikin dukiyar su. Ga wanda ya roka. Da kuma wanda ya kame bai roka ba. Kenan wannan aya har yanzu kenan tana nuna mana. Ashe ba dukkanin roko ne haramun ba. Ba dukkanin bara ce haramun ba. Haka abun yake to shine abunda yasa muka ware wata tattaunawa da zamuyi. Muji wani irin hali ne zaka shiga a cikin addini wanda zai halatta maka. Ka iya rokon mutane. Ko ka ainihin tambayi mutane. Saboda Allah madaukakin sarki yana cewa dukiyar masu dukiya. Su rika fitar ruwa ga waɗanda suke roko. Da kuma waɗanda suka kame basa roko amma an fahimci suna da buƙata. Bari kuji Abdullahi Ɗan Umar. Da ya kwankwaɗi irin wannan tarbiyyar. Manzon Allah sai ya ɗibi dukiya sai ya bashi a matsayin kyauta. Sai Ibn Umar sai ya cewa manzon Allah ya manzon Allah ka dubi wanda ya fini buƙata ka bashi. Umar. Umar manzon Allah ya ɗibi dukiya ya bashi kyauta. Sai Umar sai yace ya manzon Allah dubi waye fini buƙata ka bashi. Sai manzon Allah yace ka karɓa ba ruwanka da wanda ya fika buƙata kai Allah ya bashi. Karɓi kawai. Manzon Allah yace. Kaga wannan dukiya. Idan abu yazo maka daga cikin ta. Baka kwallafa ranka ba. Baka roka ba ka karɓa. Kana zaune sai wani yace maka ungo. Karka yi kara karɓi. Baka kwallafa ranka ba baka ma san da zai baka ba sai ya kawo ya baka karɓi. Manzon Allah yace in kuwa ba haka ba. Karka sake ka kwallafa ranka. Kasa zuciya. In an baka kaji daɗi in ba'a baka ba fa ka koma kana faɗin baƙaƙen maganganu. Jama'a kunji waɗannan hadisai. Da babuka waɗanda dukkanin su na karanto mana su daga cikin littafin ainihin Sahih Bukhari ne. Na karshe nake fatan zan cike ainihin wannan wa'azi nawa. Da waɗansu hadisai na Annabi sallallahu alaihi wa sallam. Waɗanda suna nan cikin ainihin littafin Kaman yadda ainihin Gabaɗayan waɗannan hadisan kaje ka duba su a cikin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam a cikin hadisi na farko. Da zan karanto mana. Wanda ainihin sahabi Abu Sa'id al-Khudri ya ruwaito manzon Allah yake cewa Sadaka bata halatta ga mawadata ci ba. Sai nau'i biyar na mawadata. Dukkan wanda yake da wadata. To haramun ne ya ci sadaka sai ɗayan mutum biyar. Wanda aka saka shi a matsayin hukumar tara zakka. Zakka ta farilla ko zakka fidda kai. To za'a iya cirewa daga ciki a bashi abunda Allah yace a bashi. Kunga mawadaci ne. Kenan ana iya daukar mawadaci a sanya shi a hukumar tara zakka. Ko dan ya iya aiki ko dan yana da amana ko dan yasan sirrin masu kudi. Kun san masu kudi wata duniya ce daban. Kai in ba mai in ba mai kudi bane ko. Baza su yadda su buɗa maka ba. Misali lokacin da ake seniority kuna jin ɗan form one. Yayi sai yaje ya zauna cikin 'yan form five. Baka ka mutu. Haka su ɗan ma ba'a ganka ba kawai wani zai tsaya a wata kwana yace wani shege yazo. Wani shegen. Kawai sai kaga ka rugo da gudu kazo kayi sujuda a gaban shi. Saboda in ya ganka kana kusa. Ya kira ka wani shege baka zo ba to ka shiga uku balle kazo suna zauna ka zauna. To haka masu kudi suke masu kudi wata duniya ce wanda in kai ba mai kudi bane ko. Baza su yadda ka san su ba. Balle ka san mai suke. Balle ka san sirrin su. To idan aka gano haka to sai a dauki ɗaya daga cikin su wanda aka san yasan addini. Ya iya aikin tara zakka sai a ainihin saka shi cikin hukumar zakka. Wannan na kawo muku daga cikin dalilan da zai iya halatta mai wadata misali za'a iya yi wa a samu waɗansu dalilan. Don aka fitar ko daga cikin haƙƙin da Allah yace a bashi a Qur'ani to za'a bashi kar ace a to wane kai tunda mawadaci ne ka haƙura mana a'a kudi baku bashi. Kunji na farko kenan cikin biyar. Ko kuma an dauki sadaka. An ba wani talaka. An bashi sadakan golf talaka ne. Shi kuma sai yace gaskiya shi baya son mota gida yake so. Sai ya kawo maka kai mai kudi sai ka sai wannan golf ɗin. Kaga sadaka ce. To yanzu kana amfani da sadaka ne ba a matsayin sadaka ba a matsayin kasiya ne amma dai sadaka ce kaji hanya ta biyu da mai kudi ko mai wadata. Zai iya amfani da sadaka. Ko kuma mawadaci ne. Mawadaci ne a garin su. Mawadaci ne a da. Mawadaci ne a jiya. Yau sai aka tamfatsa wata asara. Misali duk kuɗin shi suna banki. Sai aka ce bankin yayi liquidating. Bankin ya rushe an rufe bankin kun san aka rufe banki ba'a mai maka da kotaro. To kuma kuɗin ka duk suna banki. Ko ka zuba kuɗin za'a yi kasuwanci ranar juma'a. Ranar Laraba zaka tafi Kano zaka ɗibi kuɗin kaje kayi siyayya ranar Litinin sai CBN sai ta rufe bankin. Shikenan waɗannan kuɗin da kasa zaka dauke su a Kano nan da kwana uku sun tafi. Kuma su kenan maka ɗaka da waje. To kaga mai mutane ke kallon ka. Mawadaci amma a haƙiƙa a wannan lokaci ya halatta a ɗibi sadaka ko zakka a baka. Ko kuma mawadaci ne sai ya shiga cikin masu jihadi. To za'a iya dafa abinci za'a iya kawo sadaka da duk abunda ake na ainihin zakka da sadaka da ake wa masu jihadi duk za'a iya mishi. Ko kuma. Talaka aka dauka aka bashi sadaka. Sai ya dauka ya bai wa mawadaci. Kaman yadda Barira baiwa ce a gidan Annabi sallallahu alaihi wa sallam. To Annabi kuma a matsayin darajar da Allah ya bashi zamu zo mu ji suna daga cikin nau'ukan waɗanda bai halatta su ci sadaka ba sune nake lissafowa yanzu. Annabi da shi da zuriyar shi basa cin sadaka. To sai ya shigo cikin gida sai aka kawo mishi waina da miya. Amma ya wuce ga tukunya guda ana ɓararaka nama. Sai yazo ya same su Aisha matan gidan nan me yasa kuke min haka? An wuce nama tukunya guda ana farfesu. Amma a zubo min waina da miya kawai. Sai manzon Allah yace Aisha tace ai. Naman na Barira ne aka bata sadaka kai kuma baka cin sadaka yace ƙwarai. Amma ina cin kyauta yace to ita an bata sadaka ni kuma ta bani kyauta ki dan Allah je kiki zubo min nama da Allah. Je mana kawai zaki min wayau kiki min fatawa da kai na. Tafi ki zubo min nama kawai ni kyauta zan ci ita kuma sadaka aka bata to kenan da wannan ne malamai suka ce kaga inda dukiya take dukiya ba stagnant bace. Tana kwana. Ita an bata sadaka to kai kuma zata iya baka kyauta. To da wannan in karuwa tazo ta sai abinci a wurin ka zaka siyar mata. Zaka siyar mata. Saboda bai da alaƙa da karuwancin ta. Amma da karuwa ce tazo ta same ka kai tailor tace matsanar. Rage nan. Ah. To bazaka yi ba don yana da alaƙa. Ko an fahimta jama'a? Karuwa ce sai tazo sai tace zata siyar wa uban ta gida. Shi uban ne yanzu ake maganar rashin halaccin ya karɓa. Amma yanzu kai da kake da fili fa ba ruwanka da cewa dukiyar ta ta karuwanci ce. Ta karuwanci ce haramun ce gare ta ta karuwanci ce haramun ne ta baka kyauta amma tazo tayi sayayya abunda ya halatta fa. Ya halatta ka siyar mata saboda haka dukiya in tayi kwana ta ɓullo a haramun to tana iya komawa kuma sai ta zama halal. Amma ba a kowane hali ba ku kiyaye a waɗansu halaye ne. Don haka kaga gashi. Talaka ne aka dauka aka ba sadaka shi kuma sai ya dauka ya baka kyauta kai mawadaci to shi kuma mai wadata ana bashi kyauta saboda ita kyauta bata nuna talaucin mutum. Kyauta tana nuna girmamawa ne ga wanda aka ba. Wannan hadisi Ahmad da Abu Dauda da Ibn Maja suka ruwaito shi hadisi ne sahihi na biyu wannan hadisin ainihin. Yace wasu mutane guda biyu suka bashi labari cikin sahaba suka ce Sunje wurin manzon Allah. Suka je suka ce ya manzon Allah a ɗibi sadaka a bamu. Annabi ya ɗaga ido ya dube su. Yaga kai. Sai ya gansu haɗaɗɗun ƙarti ne. Yaga wannan murɗaɗɗun ƙato ne. Yaga wancan ma haɗaɗɗe ne ga jijiyoyin nan hararar juna. Annabi ya ɗaga kai ya kalle su sai yace to. In kun so. In ɗiba in baku in baku amma dai haramun ce. Domin ita sadaka bata halatta ga mawadaci ba. Hakanan mai ƙarfi wanda zai iya nema. To kai ka dubi wani marokin jama'a. Idan yayi kururuwa a gidan suna sai kaji hanjin cikin ka na motsawa. An fahimci wannan da kyau? Dafa dukkan aka kawo ta suna ta mutum takwas yake ci shi kaɗai. Ƙato ne malam. Ko kun fahimta jama'a? In yace ashe daru ku jama'a sai kaji gaban ka ya faɗi. Ko kun fahimta jama'a? To yanzu sasare ran ƙato irin wannan zai zo ya tsuguna gaban ka don ya gan ka kai ustazu ne. Wai zai maka wayau sai yace maka kun san ku ustazai ne ba'a yi muku roko Don dauki ka bani ko ɗan yaya dan Allah dan Allah ustazu ko ɗan yaya don Allah ustazu don Allah. Ina fata an gane. Wannan hadisi hadisi ne sahihi Imam Ahmad shima ya ruwaito shi da Abu Dauda kunji sahaba ne suka zo. Ƙarti guda biyu haɗaɗɗu. Suka ce a ɗiba a bamu ya manzon Allah manzon Allah ya ɗaga kai ya kalle su yace to. In kun so in baku in baku amma dai haram ne. Domin bata halatta ga mai wadata ba ko kuma mai ƙarfin nema. To dan girman Allah kai kaje Abuja. Duk da yadda 'yan rufa iya fasa su har yanzu suna nan. Je ka iya riya one. Je ka iya riya three. Kaje ka samu mace gwarjejiar mace. Bata wuce shekara talatin ko ashirin da takwas ba. Taje ta samu wani junction kawai ta zauna. Tayi wani haka da kan ta wallahi ƙarya kake yi. Duk wanda ya kalle ki yasan ki lafiyayyiya ce. Tafi cikin Republic. Tafi Mr. Biggs. Kaje kaga sarkaceciar ba fulatana ba ta wuce shekara ashirin da biyu ba da ɗan yan goyo. Tazo ta tsaya kana parking da motar ka zati kaci abinci sai ta taho maka. To ba nan ba. Da watan azumi. Matan aure ne suke fitowa daga unguwannin irin tudun jukun mufiyaci kaji daurawa sai ka gan su wajen su hamsin. Sai suje sai su tare a gidan wani mai arziki. Ƙarfe shida na asuba sun taru suna dambe da juna. Zai fito wai zai rarraba musu shinkafa kofi biyu biyu ko zai rarraba musu a tamfa. In kuka je kuka ji irin wannan wa'azin da nayi a garin Riga Cikun da na faɗi ɗazu. Wani yazo da computer iPad yana nuna mana gashi a wannan ranar da muke wa'azin. Anan Riga Cikun sun tsallako titi zasu shigo cikin Riga Cikun mota ta niƙe wata daga cikin su. Matan aure ne masu ƙarfin jiki. Mai suke gayawa mazajen zasu je nema. Ina suke shiga GRE suke shiga. Da unguwanni na masu kudi da gidajen 'yan boko da maka mantan su. To kai idan da sharrin ya tsaya ga wannan ko. To wallahi yayi kyau jama'a bara. A cikin unguwannin nan namu rahotannin da muka samu shine. Akwai wanda zai fito ya rarraba musu ɗin. Amma a ciki ya aje yaran shi waɗanda su ba rabo suke ba suna tsuntsunto cikin matayen ne wacce ce aka ganta wannan lafiyayyiya ce. Sai ace ku ku saurara ku ku saurara ku ku saurara bayan an gama raba musu. Sai ayi ƙoƙarin samar da alaƙa tsakanin ta da mai gidan. To sauran abunda zai biyo baya kuma Matan aure ne. Sun baro mazajen su anan cikin tudun jukun wasu daga cika ji wasu daga mace ya wasu daga tsugugi wasu daga sabon gari wasu daga unguwar Fulani ga su nan sun zo sun taru. Kuna kwance irin bacci mai daɗi na ƙarfe shida bayan kunyi sahur kunyi sallah asuba sai kaji sun wuce ta bayan wunden ka kace yaƙi ake yi. In ka leƙo sai ka gan su wajen su tamanin. Suna tafe matan aure ne zasu tafi bara. Zasu tafi roko zasu tafi bambadanci zasu tafi tumasanci. Hakanan wasu mutane uku suka rika yawo unguwannin nan namu jama'a. Kana zaune kawai ƙarfe shida kana baccin hutawa ranar asabar lahadi sai a buga maka ƙofa. Sai ace wasu mutane suna sallama kana fitowa sai su faɗi ƙasa.
[Segment 9/9 | 02:40:00–end]
[Speaker seg9-spk:0]
alaji wallahi mun zo neman na masara ne. Shine wata ran nace kai bawan Allah ai ba abunda kake nema sai na masara? Sai yace toh ai masaran ne yake wahalar damu nace kai baka da sana'a ne? Yace yana da sana'a. Me kake yana sai da kayan miya? Nace toh ya aka yi? Yace jalin ne ya kare. Nawa ne jalin? Yace dubu biyar. Wallahi dubu goma na dauko na bashi. Toh ban sake ganin sa a unguwan nan ba. Shekaranjiya malam ka tuna munje muna sayayya a nan cikin GRA a wani shago? Ka tuna mutum da yazo yana rokon mu? Shine da ya kalli fuska ta ba ga ya baya ba. Shine shiru ne kawai ban gaya ma ba. Shekaranjiya bayan shekara uku. Yace dubu biyar ne jalin shi sai na kawo goma na bashi. Tunda dai kana da sana'a toh bari a raya ka akan sana'ar ka. Na'am. Idan aka gane mutum yana da sana'a sana'ar ta kare ana gina shi jama'a wannan ba haramun bane. Domin musulunci addini ne dake son a habaka mutane, a raya mutane. Kaga yaje ya kashe kudin. Wannan shekaranjiya ne jama'a ba fa wata kaza ba. Shekaranjiya muna zaune a kofar wani shago a GRA. Munje sayayya ana fito mana da kayan da muka siya. Mun zauna akan kujera sai ya sake zuwa toh sai ya zama nine nake saitun waje. Yana gama fadin na masaran nan da muka hada ido sai kawai sai naga yayi baya. Wallahi malam. Shiru ne kawai banyi magana ba. Har ina zamu je jama'a? Wadannan na soshen suna nuna mana kana da karfin nema dan haka matasa ku duba. Yanzu nan ka shiga cikin garin Zaria dinnan tamu. Karfe bakwai na safe sai kaga matasa wajen guda talatin a gidan suna. Wani saboda kankanta sai ya ribi sai sai ya dibi riga hudu sai ya zuba dan ta kara mai girma. Ya samu rawani a cukwikuya mishi. Sai kaji yazo yana ce maka dan girman manzon Allah wai na wai wai ya ganka ustazu ne kai mai dan gemu haka dan girman manzon Allah. Can kuma in ya tafi ranka ya dade Allah ya daukaka ka Allah ya kaza Allah ya kaza. Bayan kwana biyu sai ya gani yazo yana siyan awaki, yana siyan kaza sai kaji a cikin gida ana cewa toh kasan kowa da sana'ar shi. Shi kuma ta hanyar roko ne Allah yayi zai ci abinci. Wallahi tallahi inna kun daure wa karya gindi. Wallahi ba sana'ar shi bane. Ya tafi alhuda huda a bashi admission. Ii yaje ya fara daga form two ko JS two. Yaje ya karasa secondary. Wallahi tallahi wannan shi ya kashe mu a Arewa. Kuma wallahi sai anyi gyara akai. Wannan gini da suka zo suna yi da nufin cewa wai makarantar almajirai. Tambayar da muke shin wadannan almajiran ne ake sake promoting almajirancin su? Kowa ya koma garin su yaje a gyara makarantun garin su a baiwa uban shi jali ya rike shi. Amma babu inda makarantar almajirai take surviving a cikin tarihin duniya. So daurewa karya gindi ne saboda haka gashi nan sun gama yi. Kap dama haka BBC ta tattara mana su. Akai hiran mu kuma muka kofe muka ajiye saboda mun san zamani irin wannan zai zo insha Allahu. Malamai irin su malam Isa Ali Pantami duk su aka tattaro akai hira da su. Aka dibo wannan Allah ramma daga Sokoto wannan daga Kano. Aka dibo masana da wadanda ke kara gwamnatin duk da aka gama. Da aka fitar da naira biliyan kaza. Sai suka ga kai hauka ake a turawa almajirai wadannan. Tuni sunyi kwana da kudin. Yanzu sun zo nan gashi akwai cikin wadanda aka dauka ma'aikatan akwai wani dalibin mu na yaje yayi karatu economics a university Malaysia. An dauke su da aka ga sun shirya gaskiya za'a yi kawai shikenan duk sai aka kore su. Aka ce an canza manufar wannan scheme din. Shikenan awala an dauke shi an tuni sun kore su. Tuni sun kore su. Kowa ya tafi kawai kudi sun fito kawai bayan an gama wahala shikenan. An gama program a radio shikenan. Har zuwa yaushe zamu tafi a haka? Sannan kai in makarantar almajirancin ma. Yanzu kenan ita gwamnati tana promoting a cigaba da kawo yaya daga wani gari suna almajiranci. Wannan ba musulunci bane jama'a. Musulunci shine in har da gaske ne za'a tafi ne a samar da wurare da zasu zama tsangayu na gaskiya. Kuma su masu malaman makarantar su za'a karfafe su su kafa tsangayu tsangayu.Annotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Illar bara da tumasanci da bambadaci da maula a musulunci (Wa'azin Zaria). Daarul Hadeethis Salafiyyah. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15865.
Zaria, M. A. A. (s. d.). Illar bara da tumasanci da bambadaci da maula a musulunci (Wa'azin Zaria) [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15865
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Illar bara da tumasanci da bambadaci da maula a musulunci (Wa'azin Zaria). Daarul Hadeethis Salafiyyah. [DVD]. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15865.
Télécharger
Visualisations
Chargement des visualisations…


