document audiovisuel · AA Rasheed Electronics · 2004 Citer
Hajji da Umrah (Hajji camp Yola)
- Type
- Enregistrement vidéo
- Créateur
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Editeur
- AA Rasheed Electronics
- Date
- 2004
- Est une partie de
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Importance matérielle
- PT149M
- Support
- DVD
- Langue
- Haoussa
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000015
- contenu
-
============================================================
[Part 1]
============================================================
[Segment 1/3 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Ya yan uwa na masu albarka bakin Allah ina muku gaisuwa irin ta addinin musulunci Kamar yadda muka ce ga malamin mu abokin mu masoyin mu Malam Muhammad Albani Zaria yana nan tare da mu a nan don yayi bayani a yau zai yi bayani ne akan umra practical zai yi magana ne akan yadda zaka yi umra zai nuna kuma ga harami a nan yadda zaka dauka da kuma zai yi bayani akan umra din don a fahimci ababen din daki daki don haka ya yan uwa a matso kusa don a sami amfanin nan insha Allah kuma Allah yasa zamu amfana Malam muna maka maraba da zuwa Allah ya saka da alheri Kamara ne ko?
[Speaker seg1-spk:1]
Na'am
[Speaker seg1-spk:0]Lire le texte intégral — 16 213 mots restants Réduire le texte intégral
Yan uwan mu musulmi mahajjata bakin Allah madaukakin sarki zuwa ga daki mai alfarma dakin ka'aba muna masu matukar farin cikin haduwa da ku a wannan fage na ainihin a dandalin alhazai dake nan ainihin yola babban birnin jihar adamawa muna yi muku addu'a ta musamman Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya Allah ya baku dacewa wajen bin aikin hajiyar da shari'a tazo dashi muna yi muku addu'a ta musamman Allah yasa hajjin ku da umarar ku karbabbu ne Allah ya kankare zunubai ya wanke ku kamar yadda jariri yake fadowa daga cikin mahaifiyar shi godiya ta musamman zuwa ga Santafo Islamic Thought da take daukar nauyin wadannan shirye shirye na gayyato malamai domin bayanai dangane da abunda ya shafi jumillar a musulunci da kuma ayyukan hajji a yau nazo domin in bada tawa gudunmawar a amma na kasafta tawa gudunmawar kashi biyu kashi na farko bayani akan umra wanda shine zan gabatar yau insha Allahu ga yan uwa iyaye yayye da kanne da sauran jama'ar musulmi gama da umra a yau maza insha Allahu sannan an jima kadan kuma ayi wa mata suma bayanai dangane da umra idan Allah madaukakin sarki ya kai mu gobe kuma muyi bayanai insha Allahu dangane da aikin hajji a bayanai da kuma aikace insha Allahu ta'ala jama'ar musulmi aikin hajji ibada ce mai girma daga cikin ibadojin addinin musulunci wadanda duk mutumin da ya sami yin aikin hajji yadda ya kamata yaje ya dawo annabi sallallahu alaihi wasallama yace an kankare mishi ainihin zunuban shi zai dawo kamar yadda mahaifiyar shi ta haife shi wannan kadan daga cikin falalar aikin hajji ce aikin hajji ibada ce wadda Allah madaukakin sarki ya farlanta ta daga cikin ibadoji wadanda suke farillai rukunai na addinin musulunci wadanda rukunin farko na addinin musulunci shine kalmar shahada rukuni na biyu sallah rukuni na uku azumi rukuni na hudu zakka rukuni na biyar aikin hajji shi aikin hajji a cikin al'kur'ani Allah yana cewa aikin hajji Allah yace ya farlanta wa mutane ga duk wanda ya samu ikon zuwa gare shi ga wanda bai samu ikon zuwa ba hajji bata zama farilla ba na daga cikin ainihin ikon zuwa shine lafiya da wadatar guzurin da zaka je ka dawo lafiya baka tafi kana roko ba ko kana maula ko bara sai Allah yace amma wanda ya kangare yaki zuwa aikin hajji a halin yana da sarari to Allah ya wadatu domin Allah yana da wani daki a sararin sama ta bakwai sunan shi yana saiti da ka'aba ne a kowace sa'a akwai mala'iku dubu sabain wadanda suke kewaye dakin nan in suka wuce bazasu dawo ba har duniya ta tashi to idan munje munyi aikin hajji a ka'aba bamu kara Allah da komai ba alherin yana dawowa kan mu ne idan kuma bamu je ba to bamu rage Allah da komai ba domin Allah wadatacce ne yana da bayi masu tsarki wadanda zasu cigaba da mishi tawafi da sa'ayi har duniya ta tashi aikin hajji yazo da ainihin wato nau'uka guda uku wadannan nau'uka guda uku shahararru akwai akwai kira ne akwai shine mutum yayi hajji da umra amma ya fara yin umrar idan yayi umrar nan ya warware ya zama kamar dan kasa in dan kasuwa ne yaje da harkokin kasuwancin shi ya cigaba da yi idan mai neman ilimi ne ya shiga wurin malamai yayi ta neman karatu idan kuma mai son shakatawa ne huta bawai shakatawa ta sabon Allah ba a'a ya huta baya kasuwanci baya neman ilimi ya zaman shi bayan ya gama umra sannan daga ranar takwas ga watan hajji watan ita ce ake kira zamu yi bayanai akan ta gobe insha Allahu ta'ala sai kuma ya dauki haraman hajji ya cigaba da hajji to wannan mutumin yayi domin sai da ya gama umra tsaf sannan ya warware ya fita daga cikin haramci ya shiga cikin halacci sannan daga baya yazo ya sake dauka ainihin yazo ya sake daukan harama aikin hajji wannan shi ake kira mutumin duk da yayi aikin hajji irin wannan to akwai yanka akan shi a matsayin hadaya wannan hadaya ita ce rago ko tinkiya ko akuya ko bunsuru ko sa ko saniya ko rakumi ko rakuma idan haka bata samu ba sai ya aikin ainihin wato sai ya azumi guda uku a kasar makka idan ya dawo gida Najeriya kuma a sai ayi ainihin azumi guda bakwai idan yayi haka ya samu guda goma kenan to wannan a takaice shine tsari na farko kenan wanda mutum zai iya yin aikin hajji a haka tsari na biyu shine kira ne kusan basu da banbanci da wannan sai dai shi sabuzarce ne idan mutum ya dauki umra to bazai ainihin warware ba daga ainihin kayan haramin shi koda ya gama umra zai cigaba da ainihin zama a cikin haramin shi amma idan dai haramin shi yadda yana da yancin ya cire mai dattin ya dauko wani mai haske ya daura zai zauna a cikin ibadoji karatun al'kur'ani zikirori salloli tawafi da makamantun haka har zuwa sa'ar da lokacin aikin hajji zata zo kuma ya cigaba da ainihin aikin hajji wannan babu ainihin wato a maganar warwarewa da zai yi a tsakiya akwai aikin hajji na kira ne tsari na ifradi aikin hajji na ifradi shi wannan babu umara hajji ce kawai mutum zai dauka daga ranar takwas ga wata sannan babu yanka akan shi sai in wata fidiya ce ta kama kamar yadda bayanai zasu zo insha Allahu ta'ala sannan akwai bayani dangane da mai kira ni da mukayi magana a baya to yana da wani sharadi mai girma shine zai yanka dabba amma dabban nan ya koro ta daga wajen harami ya koro ta daga wajen harami shi yasa kusan a wadannan zamanin wani lokacin kiranin yakan ainihin yiwuwa domin mutum sai ya koro dabba daga ainihin wajen harami yazo ya ainihin shigo da ita cikin harami sannan kiranin shi zai tabbata mafi falala daga ciki kamar yadda malamai suka fadi shine kuma shi shine yafi sauki shine nake so yanzu zan fara da bayanai dangane da ainihin umra umra farilla ce kamar yadda aikin hajji take ainihin farilla saboda Allah yana fadi a cikin al'kur'ani yana cewa da ainihin hajji da umara kuyi su cikakku ga Allah madaukakin sarki idan wata larura ta tsare ku wanda bazaku samu damar cika hajji ba ko umra a yadd ya kamata to sai ku yanka ainihin hadaya gwargwados a sai ku yanka fidiya gwargwados abunda ya saukaka zamu zo muyi bayani kamar yadda na fadi insha Allahu akan fidiya a zan fi bada karfi a wajen kwatance fiye da bayanai saboda galibi bayanai dinnan ya kamata ace ya kai alhaji tun daga sa'ar da kasan cewa zaka tafi aikin hajji to ya kamata kaje wurin malamin ka ya biya karantar da kai wasu ka'idoji a rubuce ne koko yana zaunar da kai ya nemi maka bayanai yanzu da yake mun samu kan mu a halin kurewar lokaci sai mufi bada karfi wajen kwatanta abubuwan a aikace yayin da kai haramar tafiya aikin hajji ya kai yan uwa na abin girmamawa musulmi ana bukatan ka da ka tabbatar da cewa kudin da zaka je aikin hajji kudi ne masu tsarki domin gaskiyar lamari kazaman kudi basu da alaka wajen a karbi aikin hajji ka ka tabbatar da cewa kudin da zaka yi aikin hajji dasu kudi ne masu tsarki ba kudi ne da ka samu ta hanyar murdiya ko danniya ko kasuwancin da Allah ya haramta sannan ka tuba ka koma zuwa ga Allah daga dukkanin zunuban ka sannan ka mayar da hakkoki ga masu su in wani na bin ka bashi kayi kokarin ka biya shi bashi kafin ka tafi aikin hajji wani zalunci da kasan kayi wa wani ka nemi yafe war shi kafin ka tafi iyalan ka ka shirya su gama da guzurin abunda zasu ci su sha da yadda zasu zauna su rayu lafiya har kaje ka dawo sannan kai kuma ka tattali guziri na kudi wadanda zasu wadatar da kai zuwan ka da dawowar ka ba tare da kayi bara ba ko kayi roko domin wadannan wasu abubuwa ne wadanda an haramta su musamman a yayin aikin hajji ko umra bayan wannan ya kai alhaji abin girmamawa yana da matukar muhimmanci gare ka ka tabbatar da kasan abubuwan da zaka je kayi a wannan kasa mai tsarki kar kaje kana aikin hajji da ka ko da jahilci wannan mummunan abu ne wanda munin aikin hajji ko umra da jahilci yafi munin aikin sallah da jahilci domin sallah yin ta da jahilci in an samu wani kuskure yana haifar da kabli ko ba'adi amma a hajji babu kabli ko ba'adi dayan abu biyu ne ko dai ace hajjin ka ta bace ko kuma ace hajjin ka ka aikata haramiyar da ake bukatan kayi fidya ka tuba ga Allah kun ga wannan masala ce mai girma yana daga abubuwa masu girma wadanda Allah madaukakin sarki ya haramta su a lokacin aikin hajji kwarkwasa basa neman aure daura aure gare ka koda kana can aikin hajji a daura maka aure a nan kasar ku ko kaga wata budurwa ko bazawara ka neman wa kan ka ko ka nemar wa wani an hana maka wannan a lokacin aikin hajji kai mai aikin hajji a matsayin ka na namiji an haramta maka in kana aikin hajji bayan ka sanya haramin ka ka shiga cikin alfarma aikin hajji an haramta maka ka rufe kan ka abunda ake nufi da rufe kai nan ka jawo haramin ka ka rufe kan ka saboda sanyi amma babu laifi zaka iya sa laima kayi amfani da ita babu laifi dan zobe yana hannun ka babu lefi dan agogwana hannun ka duk anyi ahuwa gama da wadannan abubuwa saboda abubuwa ne na amfanin yau da kullum an kyale maka zaka iya ainihin wato daura jaka wadda zata zama kamar a gaban ka ka rinka daura kudin ka a ciki in kana da bukata ka zaro ka ainihin kashe abunda zaka kashe mai halatta ga mai aikin hajji ya sanya dinka kunti fafi ba in munce dinka kunti fafi muna nufin tifafin da suke da kusurwa tifan da yake da hannu ko kafa ko wiya an haramta mai aikin hajji ya sanya wannan mai aikin hajji bazai sanya wando ba dogo ko gajere bazai sanya kampai ba dan diras ko makamantun haka mai aikin hajji bazai sanya singileti ba bazai sa hula ba bazai sa rawani ba amma mai aikin hajji babu lefi zai iya sanya nazara wato glass madubi na ido wannan babu lefi ga mai aikin hajji zai iya sanyawa mai aikin hajji bazai sanya tirare a jikin shi ba ba kuma zai sanya tirare a jikin tufafin shi ba mai aikin hajji bazai yi aski ba ba kuma zai yanke kumbaba amma dangane da tirare akwai halaccin mai aikin hajji ya sanya tirare kafin ya shiga cikin harama yadda in ya daura haramin shi yaje mikati ya shiga cikin harama sai ya zama akwai tiraren ne a jikin shi bawai a yanzu ne bayan ya shiga cikin harama zai shafa ba to wadannan kadan daga abubuwan da mai aikin hajji da umra zai kula dasu kenan wadansu bayanai kuma zasu zo yayin da muka zo kwatantawa insha Allahu yana daga cikin abunda na lura yana baiwa yan uwa na maza wahala dauran gyauto dinnan wajen aikin hajji musamman malam yana wani bayani wanda yace wata shekara yaje aikin hajji tafiya ya rinka yi kamar an sanya mishi a abinnan igiya a kafa wato wajen daura harami yan uwa na alhazai yana da kyau mu gane cewa ba daurin zani ake mishi irin na mata ba shi yasa yake subaliya mata ne mana dariya an kira shi gyauto izar kun ga yadda ake daura shi abu na farko haka zaka yi ka ja shi dama gare ka ina fatan yan uwa na alhazai su lura da wannan domin so ake in ka daura shi ya zama a kwankwasan ka ko gudu zaka yi bazai warware ba kuma zai baka alawus na yin gudu kanna kashi biyu kayi haka dashi sai ka jawo sai ka rike nan haka na idan ka jawo ka rike sai ka dawo da wannan nan dinka haka haka gashi ka rike haka to wannan dinnan sai kayo gaba dashi haka to sai ka nade shi haka haka to kaga haka kaga akwai balance sannan nan dinnan kuma ya dauru dam to in ka kawo jaka kudin ka kuma ka daura sai kuma mai kara zama daidai ina fatan an gane wannan shine abunda ake kira izar a a duk yadda ka daura shi baza ace maka bai ba amma idan balarabe yace izar galibi haka yake nufi yadda kaga gashi ko kwance yafa kai insha Allahu asirin ka a rufe amma so da dama yan uwa sukan daura shi daurin zani yadda in aka zo sai kaga wani lokacin ana tafiya gefe na delewa mutum na kwance ya sai a ganshi to wannan a takaice itace kaifiya da ake abinnan zan sake maimaita ta insha Allahu don fa'idar ta ga mai gaba daya idan ka dakko wannan ainihin wato zani haka kanna kashi biyu sai ka komo dashi bangaren ka na dama gaba daya haka sai ka rike shi haka ina fatan an gane in ka rike shi haka sai ka zo daidai nan jikin ka daga daidai inda mata ke daura zani kai kuma sai ka rike shi haka in
[Segment 2/3 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
ka riƙe sai ka yo kwana da wannan cuna ta dawo nan haka. Idan ta dawo sai kuma ka ainihin riƙo wannan haka nan, sai ka yo kwana da shi haka, to sai ka naɗe shi. To in kai haka insha Allahu ta'ala shikenan komai ya zauna. Larabawa suka ce haka asali shi ake nufi da abun da ake kira kwarjalle. Wani malami na ya koya mana haka tun ina ɗan makaranta a malami ne yanzu a Jami'ar Musulunci da ke Madina. Ka ga haka ɗan uwa kana da To ko ina ga ba tafiyar da za ka yi ta wadda za ta kai ta zara haka ba. To insha Allahu ta'ala wannan shi ake kira Ah ban san ko an zo da ɗaya ba? Akwai wani? Dama ɗaya ne ko? Cikin alhazan babu wani da ke da Eh
[Speaker seg2-spk:1]
Amma mu a ruwan abun nan
[Speaker seg2-spk:0]
Babu ko? Insha Allahu Akwai wanda yake da wani ne? Yauwa to Na'am to a riƙe da yayi ko? Ah Wannan an so mutum yayi shigar kayan haramin shi tun kafin ya isa miƙati idan zai yi. Saboda Annabi ya sanya haramin shi tun a gida. Aisha ta bi ta shafa mishi turare duk a jikin shi har da kan shi. Bayan yayi wanka ta shafa mai turare ya sanya kayan haramin shi. Da ya isa wurin ɗaukar miƙati kaɗai sai yayi alwala yayi sallah raka'a biyu. Daga nan ne sai ya ɗauki haramin shi a Wajen ɗauran shi wannan na sama idan baka riga ka isa Ka'aba ba wasu suna yin kuskure tun farko suna buɗe kafadun su ta dama. A'a wannan kuskure ne ya kai Alhaji. Sai in ka isa lokacin da ka je wurin Ka'aba za ka fara aikin a to a lokacin ne ake so ka ainihin ɗago hannu matar ka ta ƙasa ka sako wannan haka. Amma a yanzu tunda kana nan misali airport a ce daga nan za a tashi to in ka riga ka sa haramin ka sai ka bar shi a haka. Babu wando a ƙasa nan saboda ina misalta wa ne ba riga ba singlet ba In ka sa ka tafi haka idan aka isa idda miƙati yake an so ayi wanka idan aka yi wankan nan ayi alwala mutum ya fito yayi sallah raka'a biyu. Ita wannan sallah abun duk da ya sauƙaƙa ka karanta yayi sai dai malamai sun ce an so ka karanta qul ya a raka'a farko a raka'a ta biyu ka karanta Idan kayi wannan sallah aka tashi aka hau mota daga wannan lokaci mota tana fara tafiya sai kayi ko abun da kake cewa ya Allah na amsa kiran da kai mini in taho aikin hajji to gani na amsa a matsayin na taho amma zanyi hajji ko zanyi ko zanyi wannan bakin ka ne yake faɗi wannan ba ita ce niyya ba, wannan sunan ta a lokacin da kake faɗin wannan a daidai lokacin ake so zuciyar ka ta ƙudurce irin nau'in aikin hajji da za ka yi. Kwata-kwata ce sallah malaman fiqihu suka ce sanda bakin ka yake cewa kabara harama farko lokacin ake so zuciyar ka ta ƙudurce sallar da za ka yi a zahar ce ko la'asar ko ko magariba ko isha. To dole lokacin da kake cewa ko ko a daidai lokacin ana so zuciyar ka ta ƙudurta wannan abun da kake faɗi. To da zaran ka faɗi haka sai ka ci gaba Wannan zikirin ana so kowa yayi na shi ba tare da sai an samu jama'a sun dunkule wani yana faɗi suna faɗi ba. Kowa sai ya tsayu gayin na shi. Ana cikin tafiyar nan wani lokacin kafin a kai Makkah gajiya bacci zai iya taso maka an yi maka izini za ka iya tsai da talbiyar ka yi baccin tunda ana tafi a mota ne. Idan ka farka daga baccin ka sai ka ci gaba da talbiyar ka amma dai ka sani ya kai Tunda yanzu ka riga ka shiga cikin harama to bai halatta ba fa ko da ka ji sanyi ana tafiya a mota ka jawo mayafi ka rufa kan ka. Idan ka jawo mayafi ka rufa kan ka to fa matsala ta faru. Malamai za su ce to za ka yi fidiya kuma. Saboda haka sai kayi a hankali. Kana nan kana tafiyar nan ana talbiya, kana tafiya ana talbiya kar a riƙa tafiya ana Tarfiya ake ana talbiya Kana yin wannan talbiyar idan ka gaji da ɗaga murya za ka iya rage muryar ka kayi daidai da gwargwadon da za ka ji. Ma'ana ibada ta musulunci ba a buƙatar kayi yadda za ka gajiyar da kan ka. Za ka yi yadda yake ba za ka gaji ba ba za ka gunduru ba. Ina fatan mun gane wannan. To idan kayi wannan ana isa Ka'aba idan kana da alwala shikenan sai ka shiga. Idan baka da alwala to sai ka samu wuri sai ka je kayi alwala. Idan ka je kayi alwala za ka shigo ainihin Ka'aba Idan ka shigo Ka'aba Ka'aba tana da kusurwa guda hudu. Ina so zan ɗan yi misali da yadda teburin nan yake a a matsayin alal misali don jama'a su fahimta. Na'am To ah ƙofofi wani ɗan uwa yana magana wacce ƙofa ya kamata a shiga. Eh malamai sun kawo maganganun ƙofar Banu Shaiba ƙofar kaza in ka samu shiga Ka'aba ta ko wacce ƙofa ina son a gane yayi. Sai dai sun kawo cewa an fi son a shiga ƙofar ta ainihin Ka'aba ta ƙofar Banu Shaiba ah ba zan iya tuna wanne suna ne a yanzu wannan ƙofar take da shi ba a ƙashin gaskiya. Amma dai abun da na fi sani shine duk duk duk ƙofar da ka shiga Ka'aba yayi. Ina fatan mun gane wannan. Duk ƙofar da ka shiga Ka'aba yayi insha Allahu ta'ala. Yadda Ka'aba take tana da kusurwa hudu gabas da yamma kudu da arewa. Ɓangaren gabas yana ɗauke da abubuwa ga su kamar haka. A daidai gabas gabas maso kudu akwai inda ake kira Wannan dutse ne wanda yake mai matuƙar albarka. Daga kan shi ne ake fara yin Za ka ga an ja layi daga ainihin wannan kusurwa haka an danganta har ta tafi inda ƙofar Safa take. Don a nuna maka daga inda ake fara ɗawafi za mu zo muyi magana a wannan wurin. Idan ka taho daga ɓangaren gabas na Ka'aba in ka fuskanci yamma kana kallon Ka'aba kenan nan kuma ga ƙofar Ka'aba nan. Idan ka sake kewayowa ɓangaren arewa daga tsakiya akwai indararo sannan in ka kewayo Ka'aba ta wannan ɓangaren arewa da muke magana akwai wani gini wanda ake kiran shi Wata katan gace wadda asalin wannan katangar Ka'aba ce. Duk faɗin Ka'aba ne gaba ɗaya don haka ka kula da kyau ya kai ɗan uwa in ka zo ɗawafi ba a yin ɗawafi a shigo ta cikin wannan katangar ana bi ta bayan ta ne. Ana bi ta bayan ta ne amma in sallah ce ya halatta za ka iya shiga ciki kayi sallar nafila amma wajen ɗawafi ba a yin ɗawafi a bi ta cikin wannan katangar sai dai a bi ta bayan ta. Wannan katanga ita ake kira Idan ka kewayo Ka'aba ta ɓangaren yamma maso kudu wannan wuri kuma shi ake kira To idan ka fahimci Ka'aba a yadda na bayyana ga ga kana shigowa Ka'aba ya kai ɗan uwa za ka ga layi da aka ja daga jikin wannan wanda har ya tafi dangana da ƙofar Safa daga wannan wurin ake fara ɗawafi. Idan ka samu yadda ake so shine ka je ka sunbanci wannan Ka je ka sa baki ka sunbance shi haka in ka samu shine Hausawa suke cewa wai ana tsotsan nono ba nono ake tsotso ba shari'a ce ta shar'anta a sunbanci wannan wuri. Idan baka samu damar sunbanta ba saboda cikuwa da turereniya kar ka ce duk yadda za ayi sai ka bangaje mutane sai ka tura mutane a'a don haka aka ja layi mai tsawo don a nuna maka daga kan layin nan duk inda ka fara ɗawafin ka ɗawafin ka yayi ya kai Alhaji. Don haka babu matsala In ka samu damar sunbantar shi ka sunbanta Idan baka samu damar sunbanta ba sai ka sa hannun ka na dama sai ka taɓa. Idan baka samu dama ba sai ka samu sanda ƙwagiri sai ka ainihin nuna. Idan ka nuna sai kayi Idan wannan bai samu ba da hannu ɗin ma sa ka nuna haka saboda can in ka duba jikin shi akwai cincirindo akwai jama'a in ka ce sai ka kutsa ka sunbanci dutsan zai yi wa a karya ka ko ka karya wani ko wata wahala ta faru a'a sai ka tsaya daga nesa sai kayi To yanzu za ka fara ɗawafi kenan za ka fara ɗawafi to a yanzu da za ka fara ɗawafi ya kai Alhaji a yanzu ne ake so wannan wannan ainihin cuna ta dama ta mayafin ka to ake so yanzu ka ɗage ta ta biyo ƙarƙashin haramin ka sai ka yaba ta haka yanzu da za ka fara ɗawafi. Tun ɗazu da ka shigo Ka'aba ɗin nan ba za ka yi haka ba sai yanzu yanzu za ka fara ɗawafi. Za ka kewaye Ka'aba so uku. Uku farko da za ka yi za ka yi da sassarfa sannan sauran guda hudu za ka yi da tafiya ne yadda ƙasa ba. In ka haɗa uku da hudu ya zama nawa kenan? Bakwai to a uku farko ne ake sassarfa sassarfan nan ba gudu ba ce ba sauri ba ce ba tsalle bane amma tsakanin haka shine kana tafiya kana haka haka. Ina fatan an gane. To wannan ibada ce ko ranka ya daɗe ne kai yallabai ne kai mai sarauta ne babban malami ne ibada ce don yanzu kana gaban Allah ne.
[Speaker seg2-spk:1]
Eh ɗawafi ta clockwise counter clockwise za ayi
[Speaker seg2-spk:0]
Eh
[Speaker seg2-spk:1]
Sannan ta hagu ta hagu
[Speaker seg2-spk:0]
Yauwa za ka Ta hagu ne ai shi yasa yanzu nake kwatanta wannan yanzu misali kun gane tambayar shi jama'a yake cewa ta ina za ayi? Wato wannan ɓangaren dama shine a waje. Tarihin shi ya fara ne daga sanda Annabi ya ɗibo sahabbai za a zo ayi umra kafirai suna gulma cewa ya ɗibi ƴan jama'a sun rame a Makkah shine sai Annabi ya ce to kowa ya fito da cinyar shi nan in suka zo suka kewaye mu a ga power ta yara ko? Jama'a mun gane wannan? To ah za ka sanya Ka'aba tana hagu gare ka. An fahimci wannan sai ka zo sai ka fara daga sa'ar da za ka fara nan kamar yadda muka ce kayi kabara Allahu akbar. To wajen kewaye ɗawafi za ka iya talbiya labbaikallahumma za ka iya kabara za ka iya karatun qur'ani za ka iya salati za ka iya duk wani zikiri da ka sani a duniya. Jama'a an gane wannan da kyau? Kana cikin yi wasu suna kuskuren runguma hannu a ba a runguma hannu don ba sallah ba ce za ka saki hannun ka kana tafiya. Idan ka ga wani abokin ka za ka iya gaisawa ana yi ana gaisawa. A Alhaji an iso yayi salamu alaikum lafiya lafiya lafiya to Allah ya karɓa mana Allah ya karɓa bismillah lafiya labbaikallahumma labbaik misali za a iya haka babu laifi ah an yi sassaunci akan wannan. Ukun farko daga cikin bakwai kamar yadda na faɗi su ake yi wa sassarfa. Idan ka gama waɗannan guda uku to sauran kuma duk da tafiya za ka yi su. To wannan ɗawafin shi ake kira ɗawafin kudu. Ɗawafi ne na isowa shi kaɗai ne ɗawafin da ake ɗage kafada jama'a. Shi kaɗai ne ɗawafin da ake ɗage kafada. Duk sauran ɗawafi da za ka yi na aikin hajji da da babu sauran ka sake ɗage kafada haka duk sauran ɗawafan za ka yi su kafadar ka tana rufa ne haka. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? To wannan shine ina ga a sa ido a fahimci wannan ne. Ɗawafin farko na kudumi shi ake haka sauran ɗawafai ana rufe ainihin jiki ne gaba ɗaya ayi su. Na'am Alhaji
[Speaker seg2-spk:1]
Wanne
[Speaker seg2-spk:0]
Ta A'a A'a tambayar da Alhaji yake ɗawafin nan da za ayi na kudumi yana daga cikin sunna ko yana daga cikin ah farilla yana daga cikin farillai ne. Eh abu ne wanda yake wajibi ne ayi shi ƙwarai da gaske idan har mutum bai yi shi ba saboda wani uzuri to sai yayi yanka ƙwarai da gaske ina fatan an gane wannan. To wa alaikumussalam wa rahmatullahi
[Speaker seg2-spk:1]
Farkon mutum ya zo ya kama daga ya zo ya kama Alhaji
[Speaker seg2-spk:0]
Na'am Na'am Ita ce ta farko wadda zai yi Eh Ita ce ta farko da mutum zai yi ita ce To wajen ne Ah Yauwa ita ce za a buɗe kafada amma sauran da za ayi Duk ba za a sake buɗe kafada ba sauran duk wanda ka zo kawai kafadar ka tana haɗa haka shikenan za ka yi abun ka. Na'am wa alaikumussalam
[Speaker seg2-spk:1]
Kamar su bani daga baya za ayi tambayoyi sai a ci gaba da karatun daga baya mai tambaya sai
[Speaker seg2-spk:0]
To ah malam yana cewa a ɗan yi haƙurin tambayoyi za a ba da lokacin tambayoyi. Na'am akwai wani bayani jama'a bana so in manta tsakanin wannan wuri da na faɗi ɗazu inda ake kira Da Wato bangwan kudu na Ka'aba idan ka zo wannan bangwan ana so duk zikirin da kake kana zuwa wannan wurin sai ka tsaya sai ka koma kana Ana so daga wannan zuwa nan kayi ƙafa uku. Jama'a mun gane? Idan ka taho kana zuwa wannan wurin amma sai kayi ɗawafin farko tukunna ka tafi ka tafi ka tafi kana zuwa nan idan kana cikin Kana zuwa daidai nan sai ka canza Ka kabara kayi biyu kenan sai ka sake kewayawa da sassarfa kana sake zuwa waccen Idan kayi wannan ƙafa uku ka zo nan to kayi ɗawafi guda uku wanda yake da sassarfa a ciki to sauran ɗawafin ka duk zai zama a hankali za ka riƙa tafiya haka. Ka'aba wuri ne na cuɗanin maza da mata. Abu ne wanda ba yadda za a iya yi to amma ana so mutum ya kiyaye da gwargwadon ikon shi. Addu'o'i zikirori hailala salati istigfari duk za ka iya da karatun qur'ani kana kewayawa. Kamar yadda na faɗa mana sai dai tsakanin Idan ka gama wannan shuɗi bakwai shuɗi bakwai to ka gama abun da ake kira Bayan wannan Akwai sallah da za ka yi raka'a biyu. Wannan sallah akwai wani gini da za ka gani daga nan ɗin ka haka wato gabas da Ka'aba amma daga ɓangaren dama wannan wuri akwai glass za ka gani akwai sawun ƙafar Annabi Ibrahim Wannan shi ake kira Wani tubali ne da Annabi Ibrahim ya riƙa takawa sa'ar da yake ginin Ka'aba sai Allah ya fidda hoton sawun shi a ciki kuma Allah ya wanzar da abun haka. Idan ka samu so za mu yi to ana so ka tasa wannan gaba kayi sallah raka'a biyu. Allah ya ce Ku ɗauki In ka samu idan baka samu ba duk inda kayi wannan sallah raka'a biyu ta yi. Amma in so samu ne ka zo inda ka kabarta sallah raka'a biyu fatiha da qulya fatiha da qulhuwallahu idan sun samu in basu samu ba duk abun da ka karanta na qur'ani daidai ne. Idan ka idar da wannan sallah abun da ya rage maka sai shan ruwan zamzam. Shan ruwan zamzam na daga cikin sunna. Idan ka idar da wannan sallar a yanzu daidai wurin rijiyar zamzam ɗin ba a samun kaiwa gare shi. An kawo ruwan zamzam ɗin a cikin tuluna da butoci kusa. Na'am Yana yi ko? Yana yi An kawo ruwan ah zamzam ɗin kusa Yaya Yayi Yayi Eh Na'am To jama'a mun gane wannan da kyau? Ruwan zamzam ana so idan ka idar da wannan nafila raka'a biyu ka sha ruwan zamzam. Idan ka sha ana so ragowar abun da ka sha ka ɗibo ka zuba a kan ka. To ga wata
[Segment 3/3 | 00:40:00–end]
[Speaker seg3-spk:0]
da game da shan ruwan zamzam jama'a. Ba wai a Makka ba ko a Najeriya ka sha ruwan zamzam kayi addu'a. Saboda a cikin hadisi sahihi da Ibn Maja ya ruwaito annabi yana cewa Ruwan zamzam in aka sha shi duk manufar da ka sha ruwan zamzam da ita Allah zai biya maka bukata. Don haka idan ka sha ruwan zamzam din nan sai ka dauko kuma sai ka dan zuba ragowar a kanka kadan haka. Sannan sai ka daga hannu sai ka fuskanci Ka'aba. Kayi salati ga annabi Sannan ka gabatar da bukatocin ka da addu'o'i masu yawa da kake da su. Idan ka yi da wadannan addu'o'i sai ka sake yin salati ga annabi Toh ka gama ibadojin da ake a wurin Ka'aba. Yanzu abun da ya rage maka Sai kuma Safa da Marwa. Allah madaukakin sarki yace Safa da Marwa wurare ne wadanda na bautar Allah madaukakin sarki. Wanda duk yaje hajji ko yaje umra Allah yace babu laifi yaje yayi dawafi yaje yayi sa'ayi a wurin. Safa da Marwa idan kazo zaka fara da dutsen Safa ne. Wadannan duwatsu suna hannun riga ne da Ka'aba haka suka yi wa Ka'aba. Marwa tana can Arewa da Ka'aba daga gaba. Safa tana nan kudu da Ka'aba daga ainihin baya haka. Idan ka bar wannan wuri na Ka'aba zaka tinkari gabas maso ainihin arewa nan ne zaka ga wata kofa zaka ga an sa wannan kofa tana kaiwa zuwa ga Safa. An so idan ka fuskanci wurin Idan ka hangi dutsen Safa ka karanta farkon wannan ayar kace An so ka karanta haka. Idan haka bata samu ba babu laifi amma an so kayi haka. Idan kaje ana so ka fara da dutsen Safa Idan kaje ka hau kan dutsen Wasu mutane basa hawa in mun ce a hau kan dutsen kuma ba muna nufin can kololuwa ba A'a ka dai tabbatar da ka hau jikin dutsen. Wasu suna tsayawa kawai daga kasa a gefen su minti wannan kuskure ne. A'a ka samu ka hau kan dutsen toh idan ka hau kan dutsen ya kai alhaji Ba sai ka gangaro ba kuma dan wasu da sun hau sai su gangaro a'a idan ka hau kan dutsen sai kuma ka dawo ka biyo su ka kalli saitun Ka'aba sai ka daga hannu. Ga irin zikirin da zaka yi Wannan zikirin zaka yi shi kamar yadda kaji haka kafa daya kenan toh zaka yi kafa uku. Idan kayi shi sannan in kana da bukatu wanda na san bazaka rasa ba sai ka gabatar da su a wurin. Idan ka gabatar da bukatun ka sai ka sakko daga kan Safa sai ka tafi Marwa. Toh mai yi wa'azi tambaya toh yanzu idan ban iya irin wadannan zikirorin ba fa musulmi ne kai ai in kai kalmar shahada ta isar Kalmar shahada ta isar jama'a mun gane wannan? Bayan kayi addu'o'in nan sai ka sakko daga kan Safa. Idan ka sakko daga kan Safa zaka taho a hankali ne wasu suna sassarfa a wannan wurin ba'a sassarfa. Amma akwai idda ake yin sassarfa din. Zaka ga wani wuri ne da aka sanya alamomi kwarra amma daga sama in kana tafiya in ka kalli sama a cikin ginin inda Safa yake zaka ga an yi koran fenti daga idda koran fentinnin nan yake toh an so kadan daga kafa ka kadan yi sassarfa. Kana zuwa wurin koran fenti na gaba kuma sai ka tsaya da sassarfar sai ka cigaba da tafiya. Idan kaje kan Marwa kan Marwa sai ka fuskanto saitun Ka'aba duk da anan gini ya sha makance bazaka hangi Ka'aba ba amma ana so sai ka hayo juyo saitun ta sai ka daga hannu anan ma sai kayi Nan ma sai kayi addu'o'i da suka saukaka sannan sai ka sakko daga kan Marwa a hankali. Ita ma Marwar idan kazo zaka ga inda aka shafa koran fenti wannan koran fenti da aka shafa Idan kazo sai ka daga kafar ka daga wurin sai kayi sassarfa kana cikin yin sassarfa zaka sake ganin wani wuri da aka shafa koran fenti kana zuwa sai ka tsaya sai kuma ka cigaba da tafiyar ka kamar yadda ka saba. Duk sa'ar da kazo kan Safa ka tabbatar ka hau kan Safa din ka juyo Ka'aba sannan sai ka sakko in ka sakko ka gangara kana tafiya a hankali da zaran kaje inda aka shafa koran fenti nan sai ka dan yi sassarfa zuwa daya alamar koran fenti sai ka tsaya sai ka sake tafiya in ka kai kan Marwa sai ka sake ainihin juyowa ka sake fuskantar Ka'aba sannan ka sake sakko wa in kazo ka sake ganin koran fenti ka sake dan dagawa ka dan yi sassarfa in ka wuce ko kana zuwa koran fenti na biyu sai ka tsaya sai ka sake dawowa sai kayi Marwa a ka kai kan Safa ka'idar yadda abun yake shine daga kan Safa idan ka dauka ka tafi Marwa toh kayi daya. Daga Marwa idan ka dawo kayi Safa kayi biyu Daga Safa in ka dawo ka tafi Marwa kayi uku Daga Marwa in ka dawo kayi Safa kayi hudu Daga Safa in ka dawo ka tafi Marwa kayi biyar Daga Marwa in ka dawo ka tafi Safa kayi shida daga Safa in ka dawo ka tafi Marwa kayi bakwai toh ka cika abun da ake so. Toh kana cika wannan ka cika umarar ka tsaf yanzu a umarar ka abun da ya rage abu daya ne shine aski. Aski kana da yanci ga kofa nan daga kan Marwa ka fita nan take ga wanzamai nan na zamani su yi maka aski za'a iya maka askin baba ko kwaryan molo duk daya ne amma amma a wannan halin an fi so tunda kai mai aikin hajji ne Yanzu umara kai an fi so kayi saisaye Saboda ka bar su Makka lokacin aikin hajji sai ka aske ta duka sai kayi kwaryan molo kayi abu biyu kenan kayi saisaye kuma kayi kwaryan molo an fi so haka. Ina fatan mun gane. Za'a iya maka aski anan Idan kaso kuma zaka bari sai ka koma masaukin ka gidan da ka sauka sai kaje ka samu abokin ka ya maka aski kaima kayi mai in kuka yi haka duk daidai ne babu laifi akan haka. Jama'a wadannan sune takaitattun bayanai game da ainihin umara insha Allahu ta'ala Allah ya karba mana ibadojin da za'a je ayi zamu dan tsaya anan kadan saboda mu saurari tambayoyi ko na'am daidai da bismillah.
[Speaker seg3-spk:1]
Ana cewa
[Speaker seg3-spk:0]
Na'am Na'am
[Speaker seg3-spk:1]
In sun je kan ainihin Marwar su kamma laƙoran su sai a taɓa nan a taɓa nan a taɓa nan a taɓa nan yayi?
[Speaker seg3-spk:0]
A'a Tambayar duk dattijo yake yi wasu in suka je kan Marwa madadin a je ayi saisaye sai a dan taba gaba a dan taba baya a dan taba dama da hagu ko wannan yayi aka ce a'a don baza'a kira wannan saisaye ba abun da ake bukata a rage wa mutum gashin shi daga yadda yake yayi kasa toh an yi saisaye kenan na'am. A ce tun anan Najeriya ya riga yayi aski in ya isa can toh shine mai gashi wani alhaji ya buga yace kamar misalin yadda kaina yake din nan. Eh duk da haka za'a samu abun askewa in dai ba yau ne yayi askin ba ya tafi can dan gwargwadan abun da ya rage din nan in aka je wurin mai aski shi yasan abun da zai dan kankara dan kadan din aka aska yayi insha Allahu na'am. Ah wata matsala itace mai aikin hajji bazai yanke kumbawa ba amma kuma wani lokacin kana aikin hajji zai zama kumban ka ta dan karye haka toh ya zaka yi malamai suka ce anan babu laifi ka samu reza ko almakashi sai ka kara sa yankewa anan babu laifi amma in haka siddan ne ka dauki reza ko almakashi ka yanke farce ko kumba toh nan kuma ka tabo zaka yanka zaka yanka rago na'am sai wa kuma na'am wanene na'am bismillah dai. Wa'alaikumussalam na'am bashi da suma gaba daya toh mai saiko kenan shikenan mutum na da saiko shikenan aski ya fadi a kanshi yana da automatic aski kenan. Na'am Na'am Toh duk daya ne kamar yadda muka fadi a wajen Safa da wajen Marwa da wajen sa'ayin dawafi wajen Safa da Marwar sa'ayi kenan in mutum ya samu sai ya cigaba da talbiyya idan talbiyya bata samu ba sai yayi duk wani zikiri da ya samu karatun al'kur'ani salati addu'o'i zikirori duka daidai ne sai yayi ah babu wasu zikirori da ake yi in anje tsakanin wannan koran fenti zuwa wancan koran fenti a'a duk zikiri daya ne dai mutum zai cigaba da yin abun shi kamar yadda na fada in ana sa'ayi ma aka hadu da wani da aka san shi za'a iya tsayawa a gaisa amma a tsaya a gaisa in nace a tsaya a gaisa ba ina nufin a tsaya a koma gefe guda ana ganawa ba a'a ana tafiya din ana salamu alaikum alhaji lafiya lafiya lafiya an iso lafiya lafiya toh ya shi kuka iso a ranar talata toh Allah ya karba mana Allah ya karba bismillah ba na'am
[Speaker seg3-spk:1]
In mutum ya kewaya a dawafi
[Speaker seg3-spk:0]
Na'am
[Speaker seg3-spk:1]
Yayi dawafi ma'ana kewaya wani biyu na uku zai alwala ta karya Marwar ne.
[Speaker seg3-spk:0]
Na'am Ehe wannan matsala ce mai muhimmanci dattijo ya dagoo mutum yana cikin dawafi jama'a musulmi ko sa'ayi sai alwala ta karye bayan yayi daya ko yayi biyu ko yayi uku ya zai yi kenan idan ya dawo zai dauko sabo ne ko kuwa zai isti'inafi ne zai dora ne idan ya dawo sai ya dauko sabo sai ya cigaba da ayi wa in ya
============================================================
[Part 2]
============================================================
[Segment 1/2 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
ko za'ayi alwala ta karye, in yaje yayi alwala ya dawo. Zai daura ne ko zai sa sa zai sako sabo, sai ya sako sabon dawafi ko sa'ayi. Jama'a mun gane wannan? Ah ina fadin wannan maganar ina sani akwai fatuwar da take cewa babu laifi zai iya dorawa daga idda alwalanshi ta karye. Amma ah koda sallah ana iya dorawa idan alwala ta karye akace da sharadin in mutum bai surutu ba bai fuskanci alqibla ba. Toh abubuwan da zasu kai dawafi ya warware gaba daya sun faru, shine warwarewar alwala. Don haka idan ya dawo sai ya daso sabon dawafi ko sa'ayi shi yafi mishi. Ah ina so inyi wani tanbihi. Idan ka gama umararka in ka gama umara in ka tafi gida sai kaje ka cire wadannan kayan haram. Don kuskure ne bayan mutum ya dauko tamattu'i kuma ya gama umara kuma ya cigaba da yawo da wadannan babu wata ma'ana. Sai in mutum yana kirani ne wannan kuma wani abu ne da mun fara bayanin shi dasu. Sai kaje ka warware sai kasa kayanka kayi wanka ka cigaba da sanya tirare. Idan dan kasuwa ne kai kaje da goro ko kaje da yaduka zaka iya shanya abunka kaje ka siyar. Yanzu kai ka zama kamar mutumin makka. Duk wata harka zaka iya yi wadda da aka hana ka. Idan kazo ka'aba zaka cigaba da nafilfili zaka iya yin dawafi. Yazo a cikin hadisi annabi sallallahu alaihi wasallama yace duk sa'ar da mutum yazo ka'aba da alwalanshi ya kewaya yayi dawafi guda bakwai a matsayin nafila yazo ya fuskanci ka'aba yayi nafila raka'a biyu sai an rubuta mishi ladan umara. Duk sanda kayi wannan za'a rubuta maka ladan umara. Dawafi ka kewaya sau bakwai nafila raka'a biyu sai an rubuta maka ladan umara. Toh amma ba'a yin nafila ta sa'ayi. Ya kamata jama'a su gane wannan. Wasu suna zuwa sai ka ga mutum yana yin sa'ayi da doguwar riga. Kuskure ne wannan. Ah dawafi ne ake zuwa ayi tayin nafilar shi. Nafilar shi kuma shine in kai guda bakwai sai kayi raka'a biyu kayi daya kenan in kai bakwai sai toh duk sanda kayi bakwai kayi raka'a biyu sai an rubuta maka ladan umara. Amma sa'ayi bazaka sake yin sa'ayi a matsayin nafila ko mustahabbi ba. Angane wannan da kyau ko? Toh Allah ya taimaka.
[Speaker seg1-spk:1]
Yana tambaya
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
Tsakanin rukuni yamani da hajiral aswad za'ayi sassarfa ne ko tafiya?
[Speaker seg1-spk:0]
Eh tsakanin hajiral aswad da rukunul yamani tsakanin rukunul yamani da hajiral aswad ai in ba'a manta ba tun a farko munce a dawafi uku na farko gaba daya za'ayi su da sassarfa ne gaba dayan uku. Toh amma daga na hudu har zuwa na bakwai dukan kewayan za'ayi shi da tafiya ne yadda aka saba. Don haka hatta wajen hajiral aswad da rukunul yamani babu bambance shi da sassarfa tunda an riga anyi wadancan guda uku tun farko. Na'am wa'alaikumussalam.
[Speaker seg1-spk:1]
Tunda dawafi nafila yana mutum zai yin shi da suturansa na gida?
[Speaker seg1-spk:0]
Eh dawafin nafila ane da sutura ta gida. Na'am. Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
Duk wata tambaya na ta shafi mu da muke gida ne?
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
Ina so malam mana bayani ne kamar yadda lissafi yake in sallah a rafa
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
In mutum yayi ziyara
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
yana shakka biyar ne ko shida ne
[Speaker seg1-spk:0]
Eh.
[Speaker seg1-spk:1]
biyar ne ko shida ne
[Speaker seg1-spk:0]
Eh. Na'am. Toh alhaji ya sake sako wata tambayar mai muhimmanci. Yauwa mutum yana dawafi sai shakka ta shige shi biyar yayi ko shida biyar yayi ko shida idan zayi kokarin tunanin ya tabbatar da hakika sai yayi idan idan ko ya kasa tabbatar da hakika sai ya gini a mafi karanci biyar ne ko shida sai yace toh biyar ne kawai yanzu sai yayi na shida yayi na bakwai. Eh ama mu yi insha Allahu. Na'am. Na'am. Na'am. Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
Idan ka kewaya
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
idan ka dawo ka yi Na'am.
[Speaker seg1-spk:0]
Ah duk sanda ka kewaya daga hajiral aswad bayan kayi kabbarar farko in ka sake dawowa ta biyu sai ka sake yin kabbara Allahu akbar sai ka sake cigaba.
[Speaker seg1-spk:1]
Har in gama?
[Speaker seg1-spk:0]
Eh har ka gama kabbara bakwai kenan.
[Speaker seg1-spk:1]
Wani tambaya na wanda ya yi
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
Tsakanin rukunul yamani da
[Speaker seg1-spk:0]
Da hajiral aswad Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
Ah ita rafa na ai tana da zaka karanta
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
in zaka karanta ka wuce
[Speaker seg1-spk:0]
Eh.
[Speaker seg1-spk:1]
abun da rukunul yamani
[Speaker seg1-spk:0]
Eh. Eh. Eh. Eh a sassarfar duk za'ayi ta a wannan shudi uku na farko. Na'am. Faddal bismillah.
[Speaker seg1-spk:1]
Wani tambaya na
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
Ita dawafi
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
bayan ka gama da umara
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
Ita idan ka yi ita rukunul yamani ita ma za'ayi za'ayi kabbara ne ko ba kabbara ita hajiral aswad
[Speaker seg1-spk:0]
Hajiral aswad ban gane ba fa. Ko wane nafila da mukayi bayani haka yake. Duk sanda kazo duk abun da kayi a wancan zaka yi a wannan. Duka daya ne Allahumma bambancin shine yanzu baka da suturar harami ne kawai. Eh. Na'am. Toh alhamdullilahi toh akwai sauran sauran mata ko? Yayi daidai insha Allahu. Toh muna muku murna Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya. Allah ya karba ibadojin mu da naku gaba daya. Sai dai wa'alaikumussalam wa'arahmatullah. Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
Lokacin da akayi dawafin ku zo
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am.
[Speaker seg1-spk:1]
za'ayi yin sa'ayi ne ko sai lallai sai bayan sai lokacin da za'ayi
[Segment 2/2 | 00:20:00–end]
============================================================
[Part 3]
============================================================
[Speaker spk:0]
A irin wannan halin kayi duk wani abu wanda yake ya haram ya halatta ga wanda yake zaman gida. Shi yasa masu aikin hajji na kirani Allah madaukakin sarki ya shara'anta musu cewa masu aikin hajji irin na kirani ko aski ba zasu yi ba ba zasu cire ihramin su ba har sai ranar sallah ranar da hadaya ta halatta a yanka ta. Ah zaka zauna a cikin harami baka da damar ka fita kaje ka kasa kayan ka kana kasuwanci baka da damar ka sadu da matar ka tunda kana kirani bayan ka gama umra. Idan har ka sake ka sadu da matar ka bayan ka gama umra a halin kana kirani to sai ku tattaro kayan ku ku dawo iyalin ku dawo Najeriya hajji ta bace sai baki saboda kayi jima'i. Ba damar jima'i ba damar duk wani abu wanda ya halatta. Idan ka yanke kumba da gangan ko kaje kayi aski da gangan ko ka shafa tirare da gangan to hukunce hukuncen duk da suka shafi fidiya sun hau kan ka zaka yanka rago akan haka amma idan da mantuwa ne babu komai. Kana ainihin cikin zaman kiranin ka kana jiran a fara aikin hajji sai ka manta sai ka dakko tirare wanda ka siya zaka yi tsaraba sai kace bari ka gwada kaji tiraren nan sai ka fesa shi sai da ka fesa sai ka tuna an yi maka sassauci babu komai akan ka tunda mantuwa ce. Ko kuma sai ka dakko almakashi ka fara yanke farce sai ka tuna sai ka bari tunda mantuwa ce. Ko kuma sai kaje wurin masu aski aka fara maka aski sai ka tuna sai a tsaya tunda mantuwa ce amma idan da gangan ne kana sane to hukuncin da yake akan ka shine zaka yanka fidiya. Ina fatan mun gane zaka yi ainihin wato yanka dabba da gwargwadon irin wannan ainihin laifin naka. Ga mutumin da yake mai tamattu'i kuwa dama bayan yayi sa'i na umra zaje yayi aski idan yayi aski zaje ya cire kayan haramin shi to shi zai zauna a kasar Makkah yanzu shi ya zama kamar mutumin Makkah. Idan yaje da gorone ko yaje da kayan sayarwa shi zaje ya kasa kayan shi ya ta kasuwanci ya zama mutumin Makkah. Idan dalibin ilimi ne zai shiga cikin garin Makkah wurin malamai ya ta daukan karatu duk abunda mutanen Makkah suke zai tafiya yana yi. Idan leburane ma zai iya zuwa ya samu aikin leburanci ya tayi shi yanzu mutumin Makkah ne. Idan aka ce ranar takwas ga watan sallah tayi ranar jajibarin Arafah kenan ita ake kira an kira ta ne domin tun a jahiliyya suna yin aikin hajji. Idan wannan ranar tayi sai su tafi su cika ainihin tulun su da butocin su da ruwan zamzam ruwan zamzam da zasu sha a wurin Arafah to sai aka kira wannan ranar shayarwa ita ce ranar takwas ga wata. Wannan rana ta tarwiyya idan tayi ita ce ranar ana gobe jajiberi. Daga cikin abubuwan da mutum zai yi a wannan rana ga su kamar haka na farko sai ya dakko haramin shi ya sa ina gani yana da muhimmanci mu sake kwatanta bayanin harami din nan. Ko malam
[Speaker spk:1]
Eh wannan
[Speaker spk:0]
to a dakko shi ina yake? Eh zamu sake kwatanta harami musamman ga yan uwa mahajjata wadanda a jiya basa nan. Yanzu zamu kaddara yau takwas ga wata yau ce ranar tarwiyya. Gani a Makkah misali to amma kar kuga wadannan kayan ba haka za'a sa ba yanzu dan ina ina Najeriya ne ta in zaka sa abun ka zaka sa a daka ne kai kadai ba riga jikin ka ba wando ba jampa ba ba dan diras ba zaka yi tsarara ne sai ka dakko wannan mayafi naka sai ka sa shi kamar yadda na kwatanta a jiya. Wannan shine izar haka zaka daura shi. Ina fatan yan uwa mahajjata ku duba da kyau. Haka zaka sa shi in ka sa shi sai ka kawo sai ka rike nan. Mahajjata a kiyaye wannan domin yan uwan mu maza al'amarin yana da ban wahala so da dama sai a daura zani sai ayi ta tafiya ana tadiyewa ana faduwa. Mata kuma in sun ga musu su yi mana dariya tunda aikin ba namu bane to haka ake daura izar kwarjalle na wurin aikin hajji din nan da ake cewa ko umra in ka daura shi haka sai ka juyo wannan sai ya dawo nan haka. Idan ya dawo wannan abu da ya jaka sai ka tattaro shi haka to sai ka rike shi haka sai kayi haka. Haka haka haka haka. To in kayi haka ya kai alhaji zaka ga ka samu balas zaka iya tafiya a cikin sukuni ba tare da kaji kamar an maka da baibayi a kasa ba sannan nan kuma ya dauru in ka kawo jakar kudin ka ka sake dauraya sai kaji ka zauna kamar soja. Ina Ina fatan mun gane wannan ita ce siffar sai mayafi. A ranar tarwiyya din nan zaka daura wannan zani haka ranar takwas ga wata idan ka daura sai kuma ka kawo mayafin ka ka sa. Mun yi bayani a jiya a wurin umarar ka randa ka iso a dawafin ka na farko dawful kudum anan ne ake fito da kafada haka. Bayan haka duk wasu wurare da zaka sake sanya haramin nan babu sauranka sake yin haka wannan yana daga cikin kurakuran da alhazai suke yi wasu alhazan zaka gansu har a cikin gari ma suna yawo kafadar su haka a waje. Wannan kuskure ne a dawafin farko na isowar ka na umra shine kadai ake yin haka a duk sauran dawafin ka ba zaka sake ainihin wato a dage kafadar ka ba a duk sauran ibadojin ka na aikin hajji ba zaka sake dage kafadun ka ba yanzu sai kawai sai ka ainihin rufe haka to yanzu ka shiga cikin ainihin kayan harama kenan. To da yake yanzu kayi hukuncin ka mutumin Makkah ne a gidan da ka sauka a Makkah idan a hotel ne aka sauke ku idan a masauki ne in a Ka'aba duk inda kake daga nan zaka yi haramar ka nan ne mikatin ka. To daga inda kake din nan sai kayi alwala in ya samu kayi sallah na filar raka'a biyu yayi in bai sauka ka ba sai kayi alwala sai kayi ainihin yi talbiya da hajji sai kace ya Allah gani na amsa kira akan zan zo aikin hajji labbaika ya Allah na amsa kiran aikin hajji to daga nan sai ka ci gaba labbaika zaka iya ci gaba da wannan talbiya kana daga muryar ka da gwargwadon abunda ya samu kar kayi yadda makogoron ka zai zafi ko yadda zaka sike ko kuma kar kuyi a jama'a kar ace a samu wani mutum guda yana fadi wasu suna amsa a'a kowa yayi tashi. Jama'a mun gane wannan da kyau ko wannan abu na farko da zaka yi kenan daga masaukin ka to daga nan ina zaka tafi tunda yanzu kana cikin Makkah ne sai ka kintsa sai ka tafi Mina. Idan ka tafi Mina zaka ainihin yi dukkanin salloli a Mina din. Wannan shine mataki na biyu zamu zo muyi bayanin yadda zaman Mina zai kasance amma yanzu daga gidan ka da ka sauka kayi wanka a wannan wankan da kayi zaka iya shafa mai a wannan wankan da kayi zaka iya shafa tirare a jikin ka a wannan wankan zaka taji jikin ka ka gyara jikin ka tsaf domin baka riga ka shiga haramar ba tukunna to sai ka kawo wadannan ka sa to amma daga sanda kace to daga yanzu sunan ka Alhaji bai halatta ka dakko tirare ka sa ba bai halatta ka yanke kumba ba bai halatta kayi aski ba ko wani abu makamancin haka amma duk sanda kayi wanka na yau da kullun da ka saba zaka iya taji kayi ka sa ka sa zaka kuma ka iya shafa mai amma man da yake bashi da kanshi zaka iya shafa mai amma man da yake bashi da kanshi to yanzu zamu kaddara cewa a matsayin ka na Alhaji kayi ainihin wato ah ka dauki harama da aikin hajji. Kamar yadda muka ce sai ka tafi ainihin Mina idan ka tafi Mina zaka yi sallah azahar akan lokacin ta zaka yi sallan la'asar akan lokacin ta zaka yi sallan magriba akan lokacin ta zaka yi isha itama akan lokacin ta sannan sai kayi sallah asuba akan lokacin ta to idan kayi sallar asuba din nan sai kuma sai ka taso da safe sai ka taho ranar Arafah kenan sai ka taho zuwa filin Arafah kana tafe kana kabbara ko kana yin talbiya ko wani zikiri daga cikin azkaru wanda ya samu zaka iya ci gaba da zaka iya kabbar bari irin wadanda ake ranar sallah anan zaka iya wannan a halin ka taho daga ainihin Mina ka taho zuwa Arafah kenan. Idan kazo Arafah na daga cikin abubuwan da ake a Arafah sune za'a hada sallah ta azahar da la'asar amma wannan jam'i da za'ayi ana kiran shi Lokacin da zaka hada sallah azahar da la'asar lokacin azahar ya tayi amma la'asar bata yi ba to zaka jawo sallah la'asar baya sai ka hada ta da azahar idan aka yi sallah azahar da la'asar to sai kuma a tashi sai liman yayi hutuba. Ya jama'ar musulmi idan ana yin hutuba din nan mu rinka saurarawa domin ita hutubar nan ana fadin abubuwa muhimmai ne wadanda suke da alaka da al'ummar musulmi sannan akwai addu'o'i da ake a cikin hutubar nan sannan akwai yan uwan mu malamai ne wasu dalibai ne daga jami'o'in musulunci irin jami'ar Madina da makamantan su suna yi wa alhazan mu to yana da kyau ka saurari hutubar in anzo kuma ana bayyana ma'anar hutubar ka tsaya ka saurara don ya zama ka halarci hutubar kuma kasan me aka ce mai hutubar take ciki. Bayan an gama hutuba za'a yi ifada za'a sakko daga ainihin Arafah amma ina son in jawo hankalin yan uwa idan akaje Arafah lokacin da ake hawan Arafah din nan wasu suna kuskure saboda ance hawa sai wasu suke daukan hawan Arafah to za'a je a hau dutsen Arafah wani zai je ya hau dutse garin hawa dutse ya fado dutse ya gangaro ya danne shi ya makamantan haka ya dan uwa na kuskure ne bashi daga cikin aikin hajji kaje ka hau dutsen Arafah sannan yana daga cikin kuskure da wasu yan uwan mu suke yi da suke zuwa suna yin kashi akan dutsen Arafah wai ance in akai kashi a dutsen Arafah wai mutum ya taho zai yi kudi. Wannan kuskure ne jama'a babu inda aka fadi wannan a cikin karatu karya ce laifi ne wannan kuskure ne ina fatan mun gane saboda haka kai malam ah kuskure kan dutsen kaje ainihin kayi kashi akai don Allah alhazan mu ku kula da wadannan abubuwa suna daga cikin abubuwa na jahala basu daga cikin abubuwan ibada. Abunda ake so jama'ar musulmi a wannan rana ta Arafah yayin da ake hawan Arafah din bayan anyi sallah anyi hutuba to ana so duk wanda ya halarci wannan guri ya tsaya yayi addu'a. Siffar yadda ake addu'ar nan zaka iya addu'ar a tsaye zaka iya yin addu'ar a zaune amma la dubban addu'a da ake bi kirari da yabo ga Allah madaukakin sarki sannan sai ka daga hannu sai ka fadi ainihin bukatun ka ka daga hannu sai ka fadi ainihin bukatun ka ga Allah madaukakin sarki kuma ana so kayi ilha kayi naci a wajen ka ka ka nace ka fadi bukatun ka duk kalmar da ka fada ana so ka nanata ta sau uku Allah ka shiryar da yaya na Allah ka shiryar da yaya na Allah ka shiryar da yaya na Allah ka bamu zaman lafiya Allah ka bamu zaman lafiya Allah ka bamu zaman lafiya Allah wulakancin da musulmi suke ciki a duniya Allah ka dauke mana ya Allah ka gafartawa iyayen mu kaji kan malaman mu ka zaunar da mu lafiya misali ana son ka ka ka ka kai maimaita kowace addu'a daya sau uku sau uku sau uku yana daga cikin abunda ake so da kai. Bayan wannan ah yana daga abubuwan da ake bukatar alhazai su fahimta a wannan wuri na Arafah wuri ne wanda yake shine babbar rukuni daga cikin rukunai na aikin hajji ko shine babban sharadi daga cikin sharudan aikin hajji domin a cikin hadisi annabi yana cewa Arafah ita ce hajji duk wanda yaje hajji bai je Arafah ba bai yi hajji ba. To idan ka gane wannan ya kai dan uwa a ranar Arafah ne annabi sallallahu alaihi wa sallama yace a wannan rana shedan yana wasawukan shi sosai saboda ya batar da musulmi saboda ya bata musu ibada amma idan musulmi suka taru a filin Arafah sai Allah yace wa mala'iku ya ku mala'iku ku dubi wadannan mutane yayan Adam saboda wa suka taru sai mala'iku suce sun taru ne saboda kayi sai Allah yace to ina kafa ku shaida ku zama shaida duk na gafarta musu. Jama'a mun gane wannan da kyau ko saboda haka idan ka halarci wannan hawan Arafah ya kai dan uwa musulmi alherin Allah ya tabbata gare ka kuma abun a tayi ka murna ne. Wannan al'amari da ya shafi ainihin hawan Arafah kenan bayan haka sai ainihin mutum ya taso daga Arafah bayan rana ta fadi sai ya taho Muzdalifa a Muzdalifa anan kuma zai hada sallar magriba da isha amma kuma wannan hadawar da zai hadawa ce a Makari domin lokacin sallar magriba ya wuce a daidai wannan lokaci zai ainihin wato hada sallar magriba da isha bayan lokacin magriba ya wuce lokacin isha ya riga yayi. To wannan sanarwa ace Wasu alhazan mu da yawa basa yin wadannan sallolin saboda zasu ce sun taho a gajie sun gaji saboda haka sakamakon wannan gajiyar ba zasu ainihin yi sallar magriba ba ba zasu yi sallar isha ba sai gari ya waye. Wannan kuskure ne ba'a ki ba ka dan zauna ka huta idan ka shakata sai ka tashi kayi sallar magribar ka da isha amma kace bazaka yi ba sai gari ya waye gari na wayewa kuma kace zaka gangaro ka baro wurin to kaga wannan wata matsala ce daban saboda haka alhazan mu dole su kula da wannan. Bayan mutum yayi sallar isha wannan dare shi ake kira daren sallah jama'a babu wasu ibadoji da ake yi na musamman a ainihin wannan dare. Bayan kayi ainihin sallar ka ta isha zaka iya shafa'in ka da witiri sai ka ainihin koma sai ka kwanta sai ka huta saboda ibadojin da zaka zo ka fuskanta daga ranar sallah zuwa kwanaki uku wadanda zasu biyo bayan sallah babba. Idan mutum ya kwana a ainihin Muzdalifa gari ya waye zai yi ainihin sallar asuba idan yayi sallah asuba abunda ake so ya zauna a wannan wurin yayi ta ambaton Allah ya tsayu kafin rana ainihin ta fito dabda rana in an kusa rana zata fito sai ya ainihin fito daga ainihin Muzdalifa din. To anan idan mutum yayi sallar asuba ba zaman hira za'ayi ba mafi yawancin alhazan mu in anyi sallah asuba zaman hira suke wannan kuskure ne. Wasu kuma da zarar sun yi sallar asuba tun gari bai yi haske ba sai su baro goro wannan ma kuskure ne. Idan kayi sallar asuba ka samu wani abu na Qur'ani ka zauna kana karantawa ka samu kayi salatin annabi sallallahu alaihi wa sallama addu'o'i da sauran zikirori sai ka tsayu kayi a wannan wurin ne Allah madaukakin sarki yake cewa ku tsaya ku ambaci Allah madaukakin sarki kamar yadda kuke ambaton iyayen ku ko kuma fiye da haka ma saboda a wannan gurin a jahiliyya in suka zo aikin hajji kowa yana tsayawa yana yabon mahaifin shi da mahaifiyar shi da kakannin shi da iyaye sai Allah madaukakin sarki yace to yanzu an dauke wannan yabo da kuke wa iyaye a wannan wurin amma ku tsaya ku yabi Allah ku ambaci Allah kamar yadda kuke yabon iyayen ku ko kuma mafi da haka. Allah madaukakin sarki yace wasu in sun tsaya a wurin nan duniya kadai suke roko amma mumini yana rokon Allah ya bashi kkyakyawa a duniya ne Allah ya bashi kyakyawa a lahira don haka a wannan wurin zaka yawaita addu'o'i Idan rana ta kusa zata fito bayan gari ya waye gari ya haske ana dabda rana zata fito sai ainihin mutum ya bar wannan ah abun nan idan ya bar Muzdalifa zai kamo hanyar da zata kawo shi ne zuwa ga ainihin idan yazo zuwa wurin jifan shedan. Jama'a kuyi hakuri na kira shi da wannan sunan ban so in kira shi ba sai dai haka aka fi sanin shi ana cewa wurin jifan shedan. Wannan maganar da ake fadi ta cewa wurin jifan shedan wasu mutane sai suke dauka shedanin hakika yana nan cikin ramun don haka wani sai kaga ya cire takalmin shi ya zindima ashar yace dan kaza kaza ah ba sai kaga ya bata rai wannan kuskure ne ya Alhaji ba haka ake ba. Sakuwace zaka samu tsakon kumin nan da za'a samu guda bakwai ne sakuwar nan ba katuwar sakuwace zaka samu wanda zaka yi jifa ka fasa a wani kai a'a sakuwace wanda take kamar sakuwar da ake sawa wajen jifa da gwafa yar karamar sakuwava guda bakwai sai dai ana so ka tafi da kari ka tafi da extra don mai yiwuwa ka samu kuskure a wata daga ciki sannan kayi a hankali ya kai Alhaji in kaje jefawa kar ka jefi kan wani don haka ba jifa ne irin jifan fasa kai ba ko jifan ka dangare ko jifan kuciya jifa ne na wurgawa so ake wannan da'irar da akai rawn haka aka kewaye da siminti to akai wani gini dake tsakiya abunda ake so so ake ka jefa yadda zata je ta daki ginin nan sai ta fadi don haka ba dagiya zaka yi kayi haka ba ka shallaro ta a'a haka zaka yi ka wurga ta in ta shiga ciki sai kayi sai ka sake dakko daya sai kayi Allahu akbar sai ka sake jefawa Allahu akbar sai ka jefa Allahu akbar sai ka jefa in ka gama guda bakwai nan sai kuma ka taso shikenan. Ba sai lallai kaje bakin abun ba dan wasu suna matsawa cewa sai sunje bakin abun a'a in ka tsaya sai ka jefa idan ka jefa guda bakwai shikenan kayi sai ka dawo. Ina fatan mun gane wannan da kyau. Wannan shine zikirin da ake wajen jefawar ayi kabbara a jefa ayi kabbara a jefa ayi kabbara a jifa ba'a zagi ba shedanin ne kake jifa ba a wurin kai yanzu ibada kake ina fatan an gane wannan to ibadar da kake yi ba'a shara'anta maka kazo yin ta kayi ashar ba to don haka dole ne sai mutane sun cire tunanin cewa shedan suke jifa ba shedan ake jifa ba ibada ce ake yi ana so a nuna maka aikin hajji wata ibada ce wanda babu shakka ta kai ta komo yadda duk girman ka sai an maida kai kai ba kowa bane a gaban Allah ka dauki tufafi daidai da na talakawa ka sa akwai inda za'a saka kayi gudu akwai inda za'a saka kayi sassarfa akwai inda za'a saka kayi jifa don kasan kaima fa bawa ne daga cikin bayin Allah. Duk sarautar ka duk mukamin ka da zaka je wannan wuri kace kaima zaka sanya riga da jampa da wando da rawani sai yace to ranka ya dade in kayi bata yi ba duk malantar ka in zaka ce zaka daura rawani irin na malamai da menene za'a ce bai ba sai kayi yadda kowanne talaka zai yi duk yadda ka kai da mukamin ka bazaka ce ayi maka jifan ba sai dai kayi da kanka ina fatan mun gane wannan. To wannan ainihin jifa ah mutum bazai yi shi ba sai bayan rana ta fito sai dai mata da yara kanana. Mata da yara kanana anyi musu sassauci zasu iya yin jifa tun kafin rana ta fito wato saboda cikowar jama'a amma da ni da kai da makamantan mu da muke da karfi da lafiya ba yara ba ba mata ba to muyi hakuri cikin cincirindo da cikowar din muje muyi jifa bayan rana ta fito amma mata da yara kanana zasu iya yi kafin rana ainihin ta fito. Mai yiwuwa mutanen mu na Najeriya zasu yi mamaki har da yara yara suna zuwa aikin hajji amma ka'ida idan yaro yaje aikin hajji hajjin shi tayi a matsayin nafila sannan kai uban shi ko uwar shi ko waliyin shi da ka dauki nauyin shi yaje yayi za'a rubuta maka cikakken ladar hajji shima za'a rubuta mai ladar hajji amma ta nafila idan ya girma bata dauke mishi hajjin shi ta farilla ba sai yaje yayi hajjin farilla. Ina fatan mun gane wannan da kyau to daga nan abunda zai biyo baya a wannan rana ta sallah ita ce ibadoji ga su kamar haka akwai ibadar aski akwai ibada ta yanka to amma mutumin da ya jinkirtar da daya daga cikin wadannan to sai yayi daya. Sa'ar da ka gama jifan nan kamata yayi sai ka dawo sai kazo sai kayi yanka to amma ace kai daga zuwan ka kawai sai kaje sai kayi yanka to babu komai sai kaje kayi jifan yanzu babu komai. Ko mun gane kamata yayi kazo kayi jifa tunda farko sai baka je kayi jifa ba sai kazo ka fara yin yanka to baka yi laifi ba babu komai sai kaje yanzu sai ka ainihin yi abun nan na'am na'am Ban gane yayi bada a ranar sallah din daga zuwan shi aikin hajji eh to eh na'am yauwa tambayar da Alhaji yake tana da muhimmanci jama'a idan ka isa kasar Makkah akwai mutanen da suke tattara kudaden wurin alhazai don suyi musu hadaya akwai mutane wadanda suke zaman kansu akwai ita ma gwamnatin Saudiyya tana yi. Ya halatta ka bayar da kudin ka ga mutumin da ka amince wa ko ga gwamnati don ayi maka hadaya amma fa ku sani hadayar bawai ana yin ta ne kafin sallah ba sai ranar sallah idan ko har aka yi ta kafin sallah bata yi ba idan har aka yi ta kafin sallah bata yi ba kamar mutum ne yanzu ya yanka ragon layya yanzu ko kuma yanzu mutum ya sallar magriba yanzu ga rana tana ido biyu to ina fatan mun gane saboda haka idan har akai maka hadaya kafin ranar sallah bata yi ba fa koda yanzu ka gane haka bayan kayi hajji shekara goma da ta wuce to sai ka samu kudi ka ba alhazan nan yanzu in sunje su sake maka bata yi ba ana nan tana nan bashi akan ka don kun san matsalar aikin hajji jama'a ba irin matsalar ba'a ji ba ce ba'a ji in ta kama ka malaman fikiwu sunce in tsawon lokaci ya tsawon lokaci tana faduwa ko kuma kaza kaza amma fa al'amarin aikin hajji in ya kama ka to komai daren dade ya shekara goma da ta wuce in ka gane kayi wani kuskure a hajji har yanzu yana nan tsawon lokaci bai sa an yafe maka ba sai ka samu alhazai da zasu tafi yanzu sai kace aje a siya ayi maka a yadda ya kamata. Ina fatan an gane wannan. Eh to bazan amsa mishi ba na'am na'am na'am haka a'a tambayar nan tana da muhimmanci sai dai
============================================================
[Part 4]
============================================================
[Segment 1/2 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
akwai yanka akan shi mai suna hadaya. Toh malamin nan yace idan ya zama guzurin da naje dashi kadan ne, in na kwashe guzuri na nayi hadaya. Bazan samu abinci ba ko makamantan haka. Shin na iya yin azumi eh zaka iya yin azumi. Sai kayi guda uku acen guda bakwai in ka dawo kasar ka Najeriya. Wanne fa? Eh dama mana sai bayan an gama aikin hajji sannan zaka yi wadannan azumi guda uku. Ina fata an gane. Toh Toh bayan wannan maganar aski kamar yadda mukayi magana a jiya. Aski yazo siga biyu ko aski kayi saisaye ko kayi talkwabo. Saisaye kamar yadda muka ce in kayi sha umra toh ya kamata in aka zo wurin aikin hajji yanzu kayi kwalkwabo. Ayi maka aski ta dai ta dai aje ayi maka kwaryan molo saboda a cikin hadisi Annabi sallallahu alaihi wasallama yana cewa Allah yaji kan masu yin talkwabo, Allah yaji kan masu talkwabo, Allah yaji kan masu talkwabo, sai wani yace har da masu saisaye sai Annabi yace har da masu saisaye. Don haka masu yin kwalkwabo a aikin hajji da umra sun fi samun falala fiye da masu yin ainihin saisaye. Shi yasa Aisha tace Annabi yana tara gashi idan zai tafi umra ko aikin hajji saboda gwargwadon yawan ladan ka gwargwadon gashin da ka aske. Idan zai tafi aikin hajji zai tara suma ya tara ta ya tara ta saboda in yaje ya aske da yawa to yayi lada yayi yawa. Jama'a an gane wannan da kyau ko? Toh bayan mutum yayi wannan ranar ainihin sallah kenan sai kuma ya ainihin wato kwarara zuwa ga dakin Allah madaukakin sarki. Idan yaje dakin Allah madaukakin sarki zai yi Tawaf al ifada dinnan jiya munyi bayanin tawafi amma yana da kyau mu sake yin bayanin tawafi jama'a. A yadda mukayi bayanin yadda ka'aba take muka ce ka'aba tana da kusurwa hudu. Ka'aba tana da kusurwa hudu jama'a. Gabas da yamma kudu da arewa. Ina so mu dauki teburin nan dake gaban mu a matsayin misali. Nace wa ka'aba ne ga misali. Mu dauki wannan kusurwa dake wajen gaba na itace bangaren gabas. Wancan bangaren yamma wannan bangaren arewa, wannan bangaren kudu. Toh daga gabas da ka'aba ga abubuwan da suke. Gabas da ka'aba daga bangaren hagu in kana kallon yamma kenan in ka kalli ka'aba daga bangaren hagu ta akwai kofar ka'aba. A jikin kofar ka'aba dinnan a wannan kwana kwanar da ake kira gabas maso kudu wannan kwanar akwai wani wuri da ake kira Al hajarul aswad. Wannan dutse ne wanda shine Hausa ake cewa ana tsotson nono ba nono ake tsotso ba shari'a ce tazo da cewa idan mutum ya samu dama in yaje aikin hajji to ya ainihin sa bakin shi ya tsotsa. Tsotsan nan da zakayi ba wani abu ba ba nono ake tsotsa ba jama'a dutse ne. Tsotso kawai zakayi haka kamar yadda kake kiss haka shikenan yayi ce. Daga daidai wannan wuri akwai alama da aka shata haka zaka ga fenti anyi zane haka ya tafi zuwa kofar safa. Wannan alama itace wurin da ake fara yin tawafi. Idan ka kewayo baya kuma nan daga kwanar yamma maso kudu wannan kwana itace ake kira a ar ruknul yamani ar ruknul yamani. Idan ka zagayo bangaren arewa anan ne mizabul ka'aba yake shine in dararon ka'aba yana nan na gold na na zinare. Toh idan ka shigo ka'aba zaka fara tawafi. Abin da ake so shine ka sanya ka'aba hagu gare ka. Ka'aba tana hagu gare ka. Wannan wuri na ar ruknul al hajarul aswad idan ka samu sarari sai kaje kasa bakin ka ka tsotsa. Idan cikuwata yayi yawa ya dan uwa sai ka kyale. Daga nesa sai ka tsaya inda wannan layi yake sai ka sa hannun ka na dama sai ka nuna in ka nuna sai kayi kabbara Allahu akbar. Idan da sanda a hannun ka zaka iya sanya sanda ka nuna. A jiya nayi wani tuntuben harshe akan cewa baza a tsotse hannun ba ko baza a tsotse sanda ba a yazo cikin hadisi in Annabi sallallahu alaihi wasallama ya nuna yakan sumbance hannun shi ko in sandan shi yakan sumbance ta saboda haka babu laifi in ka nuna haka Allahu akbar sai kayi haka. Toh daga nan zaka fara tawafin ka. Tawafin nan da zaka fara akwai abubuwa guda biyu da muka fada a jiya a wajen tawaf al kudu to wadannan abubuwan basu a wannan. Na farko a jiya mun ce tawaf al kudu zaka fito da kafadar ka. Toh wannan tawafin babu zaka rufe kafadar ka. Na biyu tawafi guda uku na farko a jiya mun ce zakayi su da sassarfa a wannan tawafin babu. Na gaya mana sirrin da yasa haka a jiya lokacin da Annabi sallallahu alaihi wasallama ya taho zai umra shi da sahabbai sai mutanen Makka sukai ta tsegumi cewa ya dibi 'ya'yan jama'a ya kai su daji Madina yunwa ta rarake su zasu zo basu da karfi ku fito mutanen Makka ku ga 'ya'yan ku sun rame. Sai Annabi yace toh kaga mutanen nan tunda 'ya'yan siyasa ne bari ayi maganin su. Sai Annabi yace kowa ya fito da kafadar shi. Sannan in muka zo a kewayawa uku farko kowa yayi abin nan haka yayi sassarfa dan a gan mu muna nan da lafiyar mu. Sannan gashi har tsalle ma muke yi kaga ko mutumin da bai da lafiya ina tsalle? Toh wannan shine sirrin to tunda wannan matsalar ta wuce yanzu wannan tawaf al ifada babu wannan tsallen guda huku babu kuma fito da kafada kana zuwa sai ka ainihin bar kafadar ka a rufe haka. Sai kayi Allahu akbar sai ka fara kewayawa kana labbaik allahumma labbaik labbaik la sharika laka labbaik innal hamda wan ni'imata laka wal mulk la sharika lak idan kabbara ce ta samu idan karatun qur'ani ne dan uwa har qur'anin ma zaka iya rikewa. Kana kewayawa kana karantawa misali. Kana kewayawa a hankali sai kaga wani mutumi da ka sani ah sai ka tsai da karatun ka ko zikirin ka ko addu'ar ka ah assalamu alaikum Alhaji an iso lafiya lafiya toh Allah ya karba mana Allah ya karba shikenan sai a ci gaba kuma amma kar kuma a ci gaba da hira ah to Alhaji ginin nan yaya sun baka izini ka ci gaba toh Allah ya kiyaye Allah ya ah wannan matsala sai an dawo Najeriya tukunna. Ina fatan mun gane amma ah yanzu matsalar gaisuwa ya halatta ai toh idan aka kewaya in kazo daidai wannan kwana da muka ce ar ruknul yamani jiya na daga cikin mantuwa da nayi wannan kwana ana taba ta. Idan kazo ar ruknul yamani zaka sa hannu zaka shafe ta. Na'am. Yauwa eh zaka shafa toh amma ita idan cikuwata yayi yawa baka samu damar shafa ba bazaka nuna ba ma zaka wuce ne kawai in ka samu dama zaka shafa toh daga wannan kwanar ta yamma maso kudu zuwa wannan kwana ta ainihin gabas maso kudu itace zaka yi daga wannan kwana zuwa wannan kwana kana zuwa nan toh kayi tawafi daya. Daga nan sai ka sake kewayawa. Idan ka sake kewayawa ka sake dawowa nan kayi biyu toh sai kayi haka har so bakwai wannan shi ake kira tawaf al ifada tawaf al ifada. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Wannan wajibi ne farilla ne ga ainihin mai aikin hajji idan mai aikin hajji bai yi shi ba labudda ya koma yayi shi idan bai samu damar komawa yayi shi ba to babu shakka sai yayi fidya sai ya yanka dabba akan ainihin wannan abin da bai yi ba. Toh wannan na daga cikin abubuwan da mutum zai yi a wannan rana. Bayan nan kuma sai ya koma ainihin zuwa mina a daren sallah kenan. Wato a ranar sallah sai ya koma zuwa mina yaje ya kwana ainihin wato a mina wadannan dare raki na tashrik ayyam ut tashrik sune kwana uku bayan sallah ko kwana biyu bayan sallah. Zaka je ka kwana kwanan da ake a lokacin zaman ayyam ut tashrik ki jama'a. Wadannan kwanaki uku gaskiya mutanen mu na Najeriya mu gyara halin mu sabod da mu ma mu dace da abin da yake daidai. Mutanen mu suna zaman gulma a wannan lokaci. Mutanen mu ana zaman ado har kaji mata suna ainihin suna gasa a tsakanin su wacce ta samu samari biyar wacce taje ta samo dala dari uku wacce taje ta samo kaza wata har mata ce ainihi na bata wa wasu alhazan mu aikin hajji. Wallahil azimi wannan fajirci ne jama'a kuma duk fajirci haramun ne amma fajirci mafi girma shine fajirci a kasar Makka dan kasar Makka ce kadai kasar da zakayi tunanin sabon Allah tunani na sabon Allah Allah ya rubuta ka cikin 'yan wuta. Tunanin in kai in kaga mace kayi tunanin kayi kaza da ita sai a rubuta ka cikin mashiga wuta. Jama'a wannan kasa ba karamar kasa bace fa mu tsarkake kasar nan jama'a. Ba irin kasashen mu bane jama'a. Wannan zama na mina zama ne na karatun al qur'ani addu'o'i ibadoji. Amma wallahi akwai lokacin da naje kawai naga wasu kawai malam yadda kasan ana gidan kulab anka shin gidan kowa ya ya kunna taba ana ta hurawa ana hira. Nace jama'a sahabbai ba haka suke zama a wurin nan ba kuyi hakuri. Ba haka sahabbai suke zama ba wuri ne mai daraja jama'a. Kuma Allah ne karrama kai kai ka wannan wuri mai yiwuwa 'ya'yan ka da kakannin ka basu samu wannan darajar ba. Bazaka gode ma Allah ba ka bauta kwana nawa ne? Kwana biyu ne ko kwana uku Allah yace Mutumin da ya gaggawa kwana biyu ya tafi yayi mutumin da ya kai kwana uku yayi matukar dai kwana biyun nan da kai ba kayi ne domin wofantar da abu a'a kwana biyun nan kayi ta saboda Allah ne tayi in ka daure ka kai kwana uku tayi. Amma ba daidai bane kuma a wannan gurin aje ana zantuttuka wadanda basu dace ba. A zauna ayi karatun al qur'ani a yabi Allah ayi zikiri ayi wa Annabi salati sannan muyi addu'a muyi wa kan mu addu'a muyi wa kasashen mu addu'a jama'a. Addu'a bata faduwa banza a kasar nan. Tun a jahiliyya mutanen jahiliyya sun san darajar Makka in aka cuci mutum daga garin su sai ya kullo kayan shi ya taho Makka. Yazo cikin Makka ya durkusa gaban ka'aba ya roki Allah. Yaya yanzu muna sallah muna salati bazamu yi addu'a a wurin nan ba. Sannan muyi addu'a mu ma Allah ya sawa kasar mu albarka mu daina tsine wa kasar mu jama'a. Muyi addu'a mu ma Allah ya sawa kasar mu albarka wannan kasar ma Annabin Allah Ibrahim yayi mata addu'a ta zama mai albarka. Mu ma da bamu kai darajar annabawa ba mu yi gwargwadon abin da zamuyi na addu'a mu ma Allah ya albarkaci kasar mu domin bamu da wata kasar da tafi ta. Allah madaukakin sarke ya taimake mu. Toh wadannan na daga cikin ainihin wato abubuwan da mai aikin hajji zai ainihin kula da su. Idan ya gama ainihin ayyukan aikin hajji abin da ya rage yanzu sai tawaf al wada'a. Wannan tawafi shine tawafin ban kwana. Tawafin nan na ban kwana duk wanda yayi aikin hajji zai yi shi sai dai matar da take mai haila ce. Mai haila an dauke mata wannan tawafi shima kamar yadda kaga mun kwatanta tawafin nan haka zakayi shi guda bakwai kazo kayi sallar nafila guda biyu toh in kayi wannan kayi tawafin ban kwana kana da 'yancin kuma sai ainihin ka taho kasar ka. Wani kuskure da wasu alhazai suke shine tafiya fita daga ka'aba da baya da baya. Akwai alhazan da suke fita daga ka'aba da baya da baya. Wani zaka ga ya fita yana kuka yana haka yana mata bye bye toh wannan ba daidai bane ba addini bane gaskiya zaka iya fita daga ka'aba daga ba kuma ran da Allah ya dawo da kai shikenan in kuma Allah bai dawo da kai ba kayi abin da yake shine farilla akan ka. Wadannan sune kadan daga abubuwan da zamu iya bayyanawa anan insha Allahu sai dai wasu abubuwan zasu kara sa fitowa idan an gabatar da tambayoyi Allah ya datar da mu na'am. Ya kamata muyi bayanin ziyara ko a ha na'am. Haka yake an fadakar da ni akan ziyarar Madina da kuma ziyarar masallacin Annabi sallallahu alaihi wasallama da kuma ziyarar kuba da kuma ziyarar ainihin wasu kaburbuka da wasu wurare masu daraja na'am wa'alaikumussalam wa rahmatullahi.
[Speaker seg1-spk:1]
Wa'alaikumussalam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
[Speaker seg1-spk:0]
Na'am. Wani sa'a yayi nace toh naga munyi bayani jiya amma za'a maimaita shi a yau insha Allahu bari mu kara sa maganar ziyara. Jama'a Madina Madina kasa ce wadda take mai daraja Allah ya albarkaci Madina saboda hijirar da Annabi sallallahu alaihi wasallama yayi a cikin ta da kuma zama da Annabi yayi a cikin ta sannan da kabarin Annabi da sauran manyan bayan Allah suna wannan wuri a yanzu. Ziyarar Madina sunna ce. Sai dai ina son 'yan uwa na alhazai ku san cewa mutumin da yayi aikin hajji koda bai je yayi ziyara ba bazaa ce hajji shi ta baci ba. Hajji shi tayi. Sai dai an so kaje ka ziyarci Madina ka ziyarci masallacin Annabi sallallahu alaihi wasallama ka ziyarci kabarin Abubakar da Umar da Usman ka ziyarci kaburbukan mutanen ah su Hamza ah Uhud sannan an so ka ziyarci masallacin kuba toh ga yadda ziyarar take. In ka shiga masallacin Annabi sallallahu alaihi wasallama zaka shiga da alwala ka shiga da ainihin kafar ka ta dama kayi addu'a bismillah allahumma salli ala muhammadin wa sallim ko wani nau'i na salatin Annabi sallallahu alaihi wasallama kayi addu'a allahumma iftah li abwaba rahmatik Allah ka bude ni kofofin rahmar ka. Idan ka shiga masallacin kaje ziyara ba kabarin ba a yanzu sai ka wuce kayi sallah tukunna. Idan ka samu damar yin sallah a rauda wani wuri daga gaba gaban masallacin yana nan an sa koriyar darduma toh an fi son haka saboda wannan wurin aljanna ce a karkashin wurin. Annabi sallallahu alaihi wasallama yayi ce Yace tsakanin minbari na da gida na yace dausayin aljanna ce aka kawo aka ajiye. Toh wannan wurin shine zaka ga an samu shi koriyar darduma. Wannan koriyar darduma da aka kawo aka sa don ayi makin ne a nuna maka inda rauda din take. Toh idan so samu ne ka samu yin ainihin sallah mafi karancin nafila raka'a biyu a wannan wuri. Ina fatan an gane wannan da kyau. Wannan abu ne wanda yake yana da matukar falala. Idan ka idar da wannan sallah sai ka taho inda kabarin Annabi sallallahu alaihi wasallama yake kaburbukan guda uku ne jama'a. Kaburbukan guda uku ne. Ga kabarin Annabi sallallahu alaihi wasallam yamma dashi yamma dashi sai aka kawo kabarin Abubakar amma sai suka dan saba haka. Wasu malaman mu da mukayi karatu hannun su Hausawa sunce wai don haka ba Haushe yake cewa Abubakar garba wai saboda kabarin sayyidina Abubakar yana Garb wai saboda haka ba Haushe yake cewa Abubakar garba kabarin Abubakar yana yamma da na Annabi amma daga baya sannan kuma ya dan zoba haka toh daga nan kuma sai ga kabarin Abu Umar haka shi kuma daga daga wancan gefen shi kuma ya zoba haka kaburbukan guda uku sune alfaza zi yake wa'akyan su ashirin ne yayi ce Allah ya dadin tsira ga kabarin Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam da kabarin Abubakar da kabarin sayyidina Umar. Toh wadannan kaburbuka in kazo ziyarar su ya kai dan uwa ba'a taba shabbakin karfen ba sai ka taba ba. Zaka tsaya cikin ladabi ba'a daga murya a wurin in ka daga murya duk ayyukan ka sai su lalace. Allah yace Ladabi zaka in kaje da ladabi zaka sunkuya da muryar ka. In kaje sai kayi sallama ga Annabi sallallahu alaihi wasallam. In kayi sallama ga Annabi sallallahu alaihi wasallama sannan sai kayi salati gare shi. Kayi salati kamar yadda ka san yadda ake salati sai ka sake matsawa gaba sai kayi Abubakar kuma ba salati zaka yi mishi ba addu'a zaka yi mishi. In baka iya da larabci ba yi da Hausa idafin lanci idaka nuri idaka duk yaran da ka iya Allah ka jikan Abubakar Allah ka kara Abubakar ya yarda Allah ka saka Abubakar da alheri sai kuma ka sake matsowa Shima kayi mishi addu'a da sauran makamantan kamar yadda kayi wa Abubakar toh idan kai wadannan abubuwan toh ka gama ziyarar Annabi da Abubakar da Umar ba wata addu'a da zakayi a wurin idan kana da addu'a sai ka dawo wani bangaren na masallaci sai ka zauna sai kayi addu'a amma ba a wurin ba. Jama'a mun gane wannan da kyau? Babu wani sako da ake isarwa domin naji mutanen mu da dama in zaka tafi aikin hajji sai a baka sakon gaisuwa. Toh Allah in anje a gaishe mana da manzon Allah sai kaga mutum ya tsaya wallahi Alhaji ya tace in gaishe ka in gaishe ka eh. Babu wannan alhazai babu babu babu idan dai mutum yace don Allah in anje ayi mana addu'a toh in kaje ka'aba kayi mai addu'a in kaje masallacin Annabi kayi mai addu'a amma ba wani sakon gaisuwa da za'a ce don Allah ka gaishe mun da manzon Allah sai kaga wasu har rubuta suna ake Hajiya wacce tace a gaishe ka Alhaji mai goro yace a gaishe ka Alhaji na bakin titi yace a gaishe ka in kace Alhaji ba haka ba sai sai kuyi fada sai a hankali. Jama'a mun gane wannan da kyau? Wannan kabarin Annabi kenan da Abubakar da Umar Allah ya kara musu yarda sallallahu alaihi wasallam. Bayan wannan akwai masallacin kuba jama'a. Wannan masallaci na kuba Allah ya yabe shi a cikin al qur'ani Allah ya yabi masu sallah cikin shi. A cikin masallacin kuba akwai bayin Allah masu son tsarki
[Segment 2/2 | 00:20:00–end]
[Speaker seg2-spk:0]
Kuma Allah, Allah yana son wadannan mutane. Wannan masallacin quba kenan jama'a. Idan kaje masallacin quba. Zaka ainihin yi sallah. Gwargwado koda raka'a biyu. Kayi addu'o'i saboda annabi yana ziyarar wannan masallaci. Sai dai akwai wata makabarta a jikin masallacin quba. Mutane suna zuwa ziyara malamai sunce wannan bata dake cikin abubuwan ziyara. Sai dai dukkan musulmi zaka iya ziyarar shi da manufan musulmi ne kayi mashi addu'a amma kar a taba daukan cewa akwai wani wannan makabarta bata sahabbai bace wanda ke quba. Bata tabi'ai bace wannan makabarta bayan tafiyar annabi da sahabbai da shekaru kamar dari bakwai ne ma aka same ta. Ya kamata mu gane wannan. Bayan quba akwai masallacin akwai uhud dutsan uhud. Dutsan uhud in kaje zaka ziyarci kaburbukan su hamza ne. In ka tsaya. Zaka yi musu sallama. Za kuma kayi musu addu'a. Idan kayi musu sallama. Amincin Allah ya tabbata gare ku ya ku wadanda kuka samu darajar mutuwa a yakin uhud sannan ka daga hannu kayi musu addu'a shikenan sai ka bar wurin ka gama abinda ake yi. Kar kaje kace ya saidina hamza ban taba haihuwa ba ka taimake ni a'a saidina hamza bani da da bani da jali ba a wannan jama'a Allah ake roko sai ka dawo kazo ka roki Allah a masallaci. Bayan wannan. Wasu wurare da Ziyararta. Haka ku sani babu wani sai quba ita Ina kallon baitul makaddisi Suna cikin sallah suna kallon. Su ake kiran masallacin Sallah Kalli yan mu. Ina fatan kun gane. Akwai wasu masallatai. Wani Wallahi duk wannan shari'a bata lissafa su wajen ziyara ba. Sannan kayi anan hankali akwai wasu mutane masu mutawaffai. In kaje ziyarar baki'a makabartan baki'a. Kawai mutum zai tare ka yace ziyara ya haji ya zo yana nuna maka abubuwa wannan duk bashi daga ciki ziyaran quba. Uhh makabartan baki'a makabartan baki'a tana nan gaban masallacin annabi sallallahu alaihi wa sallam kana fitowa daga masallacin annabi in kayi gaba kadan. Zaka ganta sai kaje ka tsaya kayi musu sallama kayi musu addu'a sai ka tafi kaburbukan su Aisha suna wurin. Kaburbukan su abu huraira suna wurin. Kaburbukan su ummu salama suna wurin to sai kayi musu sallama kayi musu addu'a abinda ake yi kenan. Kar wani yace maka kazo ga addu'ar da ake yi ga addu'ar da ake yi zaka bashi riyal goma duk yar riyalan naka sai a cinye maka a wajen abinda bai da asali. Don haka ka kula da kyau ya kai alhaji. Wadannan sune takaitattun bayanan da zamu yi a kan game da quba. A game da ziyara. A madina akwai wani campy da mutane suka yi. Game da tantabaru madina. Tantabaru nan na madina da tantabaru makka ana cewa tantabaru binta yan ma'aikin Allah wanda ya ciyar da su yana da kaza a'a in dai tantabara duk tantabara ce duk inda tantabara take ka watsa mata abinci taci zaka samu lada. Wasu sun campa wai wanda ya kamo wannan tantabarar. Ya taho da ita ya yanka ya ci to Allah zai mai kaza zai mai kaza zai mai kaza wallahi duk ba haka bane. Shiyasa zaka gani in kaje kamawa sojoji sai su kama ka. To ya kamata a loro da kyau. Bayan wannan alhaji yayi mana tanbihi akan maganar sa'ayi. Jiya munyi maganar sa'ayi sai dai wasu yan uwa alhaji basa wurin nan. Sa'ayi. Shine ibadojin da ake a tsakanin safa da marwa. Safa da marwa duwatsu ne wadanda suke sunyi wa ka'aba hannun riga. Uhh Safa itace ta farko. Marwa ke biye da ita wadannan duwatsu ne. Wadanda kamar yadda mukayi bayani a jiya. Idan kaje zaka yi sa'ayi abinda ake bukata da kai ya kai alhaji. Shine ka tabbatar idan kazo ka hau kan dutsan kar ka tsaya akan siminti. Kuma in mun ce ka hau kan dutse ba muna nufin ka taka ka hau kololuwan dutse ba kaje ka fado a'a. Ka dai taka falalen dutsan in ka taka falalen dutsan. Sai ka tsaya sai ka fuskanto ka'aba. Domin so da dama alhazai idan suka hau wannan dutsan suna dayan abu biyu wanda duk ba daidai bane abu na farko wani da ya hau sai ya sauka. Abu na biyu wani da zaren ya hau sai kuga kawai yana daga hannu yana haka. Saboda galibi mutanen mu. Suna ganin mutanen kasar India da Pakistan da makamantan su. Kar kaga jar fata kai dan Nigeria ka dauka wai yafi ka wani abu. Wannan wuri kowa daidai da kowa ne kamar yadda yake sai wanda yafi wani tsoron Allah. An koya maka abubuwa anan kar ka watsar kaje kaga wani yana yin nashi kai kuma ka kwai kwai nashi ka barshi ya nashi kai kuma kayi wanda aka koya maka. Galibi mutane in sun hau dutsan safa sai kaga kawai sunyi wa ka'aba haka da sun dan yi mata haka haka sai su sauka ba haka ake ba ya dan uwa idan ka hau dutsan safa sai ka ainihin daga hannayen ka. Sai ka fuskanto ka'aba. Idan kayi wannan kafa daya kenan sai ka sake yi ka sake kafa uku sannan sai ka gabatar da addu'o'in ka sannan sai kayi salatin annabi sai ka rufe sai ka sauka. Sai ka tafi marwa. Idan ka tafi marwa kafin ka kai marwa ka rinka lura daga dama da kai daga hannun ka na dama zaka ga wani koran fenti. Daidai inda aka shafa koran fentinnan ana nufin kayi sassarfa. Idan kaje wurin sai ka dan daga kadan sai ka dan yi sassarfa haka kadan. Kana tafiya sai ka sake ganin koran fenti a gaban ka sai ka sake tsai da sassarfa ka sai ka ci gaba da tafiya yadda ka dauko da farko. Idan kaje kan marwa. Ba daga hawa zaka sauka ba itama idan ka hau kan marwa itama sai ka juyo sai ka ainihin sake fuskanto ka'aba to anan bazaka ga ka'aba ba domin akwai katanga da aka gina. Tunda bazaka ga ka'aba ba sai kayi kintace saitin ka'aba sai ka daga hannun ka nan ma sai ka sake irin wannan zikirorin. Ka sake yin addu'o'i sannan kayi salati sai ka sakko daga kan marwa. Idan ka taho daga kan marwa kana tafiya kana tafiya ka rinka lura da hannun ka na dama daga sama zaka ga wani koran fenti an shafa. Kana zuwa daidai wurin nan ma sai ka dan daga sai ka sake yin sassarfa haka. Kana tafiya sai ka sake ganin wani koran fenti sai ka tsaya sai ka ci gaba da tafiyar ka. Wannan talbiyya zaka rinka yi a halin kana tafiya wajen safa da marwa labbaikallahumma labbaik idan ba haka ba kabbara in ba haka ba salati in ba haka ba wani zikiri wanda ya saukaka ko addu'a gare ka anan ma in kaga wanda ka sani. Zaka iya tsayawa wato in nace tsayawa ba ina nufin tsayawa tsayawa ba a'a. Dakatar da zikiri. Yana ibada. Harkoki. Haka da irin. Jama'a. Idan ka kam. Zai zama. Daga safa kaga. Kuri. Sannan daga safa ka tafi marwa kayi daya. Daga marwa in ka dawo sara kayi biyu daga safa ka tafi marwa kayi uku daga marwa ka dawo safa kayi hudu daga safa ka tafi marwa kayi biyar daga marwa ka dawo safa kayi shida daga safa ka tafi marwa kayi bakwai daidai kenan amma haka kaga ka fara da safa ka gama da safa. To ko kayi takwas. Ko kayi goma ko kayi sha hudu. To kayi kari kayi kuskure kenan to amma tambayar itace da zai zama mutum yayi takwas. Ko goma da kuskure ko makamantan haka fa babu komai tunda dai har ka kai adadin da ake so. Amma in ka gaza ne to sai kaje ka cika in ba haka ba kuma to an samu matsala. To wadannan sune takaitattun bayani da zamu yi insha Allahu ta'ala Allah yasa mana albarka na'am. Na'am. Na'am. To malam yana tambaya ace daga madina ko daga jidda an dauki alhazai za a tafi. Zuwa makka. Bayan an dauki harama kenan. Sai sanyi ya kama mutum sai da yaji sanyi sai ya ja mayafi ya rufe kanshi. Idan da mantuwa ne da zaren ya tuna sai yayi sauri ya cire babu komai a kanshi. Amma idan da gangan ne ya ja ya rufe kanshi bayan yayi harama to sai ya yanka dabba. Kaga wannan yaji dumi mai tsada kenan. Na'am. Na'am. Alhaji yana tambaya ne wani cewa yayi shi mutum da bashi Na'am. Wani yana tambaya mai muhimmanci wai idan mutum yana da bashin azumi. Kamar ya tafi da bashin azumi daga nan Nigeria sannan ga wancan azumi ya kama shi guda uku a can bakwai anan. To yanzu ya zai yi a'a sai yayi wancan din in ya dawo kuma sai ya hada da na da da sauran bakwai din nan sai yayi. Na'am. Na'am. Na'am. Na'am. Na'am. Duk daya ne tambayar da yake da hadayyar da zaka bayar ayi maka da wanda zaka yi da wanda zaka ba gwamnati matukar dai anyi ta ranar sallah duk daya ce. Kwarai da gaske. Na'am. Na'am. Na'am. A ha malam yana tambayar idan mutum ya ainihin sanya mayafi. Sai ya sanya fil wanda zata rike mashi babu laifi wannan. Babu laifi anyi ahuwa akan haka na'am alhaji wa alaikumussalam wa rahmatullahi. Na'am. Na'am. Eh kowa da kanshi zai yi. Eh to maganar gajiya in ya gajiya bari ya huta tukunna. Amma maganar bai da lafiya shine zai zama uzurin sai ya wakilta wani yayi mashi eh na'am. Haji eh. To mutum ne ana binshi basussuka anan kasar su sai kuma gwamnati ta bashi kujera ko kuma alhaji wane ya bashi kujera haji. Idan so samu ne a siyar da kujera a bashi kudin shi ya biya basussuka yayi bukatu yafi. To amma in aka ce bazaa siyar ba fa. Sai ya kira masu binshi bashi yayi musu bayani. Kuna bi na bashi amma ba na samu kudi bane alhaji ne ya biya mun kujera. Nace ya bani kudin inje in biya ku bashi yace a'a don haka don Allah kuyi mana hakuri har in dawo. In suka mai hakurin ya dawo sai ya biya su. Na'am na'am alhaji. Daga muzdalifa. Na'am. Na'am. Na'am. Na'am. Na'am. Na'am. Na'am. Eh sai kaje kayi tunda iyayen da ka iya isowa kenan tunda da kafar ne. Kwarai da gaske na'am. Allah ya taimaka na'am wa alaikumussalam. Na'am. A'a a makka ne. A makka ne kwaryar moro tafi wanda yayi saisaye amma a halin yau da kullum in kana bukata zaka iya yin saisaye eh insha Allahu. Na'am to ga malam zai yi sanarwa. Wa alaikumussalam. Wa alaikumussalam wa rahmatullahi wa barakatuhu. To wannan suAnnotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Hajji da Umrah (Hajji camp Yola). AA Rasheed Electronics, 2004. DVD. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15864.
Zaria, M. A. A. (2004). Hajji da Umrah (Hajji camp Yola) [DVD]. AA Rasheed Electronics. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15864
Zaria, Muhammad Auwal Albani. Hajji da Umrah (Hajji camp Yola). AA Rasheed Electronics, 2004. DVD. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15864.
Télécharger
Visualisations
Chargement des visualisations…


