document audiovisuel · Daarul Hadeethis Salafiyyah Citer
Kaddamar da Sashin Al-Qur'ani
- Type
- Enregistrement vidéo
- Editeur
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- Est une partie de
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Importance matérielle
- 175 minutes
- Support
- DVD
- Sujet
-
Coran
Annotations de valeur
- AI Model - NER
- Claude Haiku 5.5
-
Ibn Kathir
Annotations de valeur
- AI Model - NER
- Claude Haiku 5.5
- Théologie
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000009
- contenu
-
============================================================
[Part 1]
============================================================
[Segment 1/3 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yau asabar uku ga watan zulkaida hijiran manzon Allah tana da dubu daya da dari hudu da talatin da biyu daidai da daya ga watan October shekara ta dubu biyu da sha daya muna masu godiya ga Allah subhanahu wata'ala wanda ya tara mu a wannan makaranta ta darul hadis salafiya domin gabatar da sashin hadin alkur'ani mai girma da ilumu min shi da abin da ya shafi tafsirin shi da sauran abubuwa masu tarin yawa wanda kafin kai tsaye gabatar da malam da zai gabatar da wadannan bayani da izinin Allah zamu buga ci daya daga cikin dalibai ah Isa Abdul Karim yazo ya gabatar mana da karatun alkur'ani mai girma domin bude wannan taro mai albarka Allah ya gabatar malam bismillah
[Speaker seg1-spk:1]
Alhamdulillahi
[Speaker seg1-spk:2]Lire le texte intégral — 21 753 mots restants Réduire le texte intégral
Allah madaukakin sarki ya saka wa malam da alkhairi kai tsaye zamu gabatar da malam mu mu Abu Abdurrahman Muhammad Awwal Adam Albani Zaria saboda ya gabatar da wannan sashi da zai karantar da littafin Allah mai girma Allah ya gabatar malam bismillah yan uwa masu kallon mu da sauraron mu na kusa da na nesa da wadanda zasu kalle mu kuma su saurare mu ta kafofin yada bayani na zamani kuna sauraron mu ne da kallon mu daga makarantar darul hadis salafiya da ke number four Madarkaci Road Zaria jihar Kaduna a Najeriya wato a gaskiya layout quarters tarihin wannan makaranta na komawa baya ne zuwa ga ainihin wato tarihin da'awa da ni Muhammad Awwal Adam Albani Zaria na fara gwargwadan shekaru talatin da daya da su gabata wanda daga cikin manufofin wannan ainihin wato da'awa da nake yi akwai dawo wa alkur'ani mai girma wajen karanta shi da kuma karantar da shi da haddace shi da kuma haddatar da shi da fassara shi da koyar da tafsirin shi da aiki da shi da kuma koyar da aiki da shi sannan wadannan baki daya a bisa fahimtar malaman farko wadanda sune da larabci aka fi sani da mai son ji ko kuma gani ko kuma gaba daya dangane da wadannan manufofi na wannan da'awa da nake yi sai yaje ya samu jerangiyar wasu kasusuwa wadanda na sanya musu manufar da'awar salafiya salafiya ba kungiya bace salafiya ba dariqa bace kuma salafiya ba mazhaba bace daga cikin mazhabobi guda hudu ko guda biyar ko guda arba'in hasali salafiya ta farki ne wanda musulmi kan dauka wajen bin alkur'ani da hadisi wannan shine ta farkin da na yadda da shi kadai duk wani tafsiriki bayan shi bidi'a ne ba addini bane bata lokaci ne a karkashin wannan dukkanin abin da zanyi sai na tsaya na dubi ya dace da wannan ta farkin kuma shi wannan ta farki ne wanda yake ba a littattafai ne ake zuwa a karanta shi a koyar shi ba ta farki ne da sai kaje ka zauna gaban malaman da sun san shi kuma su karantar da kai in ba haka ba sai kayi ta daukan su alkur'ani da sunna din ne salafiyancin a'a salafiyancin qari ne wanda yake tabbata na tabbatar da salan da za ayi aiki da su alkur'ani da sunna din kamar yadda malam Samir yake fadi a cikin ainihin wato ta'alikin shi da sharhin shi da yawa littafin da yake cewa kar kuma ka taba zaton cewa wajabcin riko da bin ta farkin salafiyancin wani abu ne wanda muka kirkira bashi da dalili a qur'ani da hadisi a'a wajibi ne abin manhajin salaf wajen fassara fahimta karantawa ta qur'ani da ainihin wato hadisi ne idan mun fahimci wannan to gaskiyar lamari samar da makaranta wadda zata karantar da ilimi na qur'ani a bisa manhaji na salaf yana bukatan kyakkyawan shiri da kyakkyawan wuri da kuma jajircewa domin a tabbatar da haka din a bisa yadda hasken tafiyar zamani kuma tazo wannan yasa ina karantar da dalibai alkur'ani tun farko amma aka samu wani lokaci ganin wasu yan uwa sun tsayu da dauke mana wannan wajibin to sai na bada karfin abubuwan da kuma a wadancan lokutan suma ba damu da karantar da su ba sune aqida da kuma hadisi to sai ya zama a daidai wannan lokacin ne da'awar tayi karfi har sai ya zama wasu ma basu taba sani na a mai karantar da karatun qur'ani ko a mai karantar da hadda qur'ani ko tafsirin alkur'ani ba amma wani abin sha'awa shine da karantar da alkur'ani na fara da kuma makaranta ta ita na fara Allah madaukakin sarki ya taimake mu a yau safiyar ranar asabar da ta daidai da uku ga watan zulqa'ada hijiran annabi na da shekara dubu daya da dari hudu da talatin da biyu daidai da daya ga watan October shekara ta dubu biyu da sha daya ta bature zamu muna zaune zamu gabatar da sashin karantar da alkur'ani da haddashi da ilumu min shi a karkashin makarantar mu mai suna wanda ita kuma wannan makarantar yau shekarar ta ashirin da daya da yan kwanaki kamar sha takwas ko sha tara da ainihin kafawa domin na kafa makarantar ne a cikin watan sa tun ba na gashi a yau kuma daya ga watan October insha Allahu ta'ala daidai da uku ga watan zulqa'ada ina mai kaddamar wa da kafa makaranta ta hadda alkur'ani wadda ita kuma sunan da nasa mata shine ma'ana domin haddatar da kuma karantar da alkur'ani mai girma zan kara bayani dangane da wadannan insha Allahu ta'ala amma nake son in watsake mana kwakwalen mu da kuma ainihin tunanin mu da maganganun farko da yake fadi a cikin littafin shi da yake cewa Allah madaukakin sarki ya gafarta wa Allah madaukakin sarki ya gafarta wa wannan littafi ne dangane da ilimi na qira'o'i guda bakwai da riwayoyin su guda goma sha hudu da abubuwan da suka karu dangane da haka babban dalilin da ya sanya na sanya wannan makaranta sunan na sanya mata suna ne saboda malaman musulunci guda biyu da suka shahara da ainihin suna malamin farko da ya shahara da suna malami na biyu kuma da ya shahara da suna shi kuma cikin malaman tafsiri ya bayyana shi wannan na farko shine a cikin wannan littafi yake cewa wannan asalin sunan shi dan mutumin qasar Makka ne ana kuma ce mishi ma'ana sun fito asalin qauye daya da babban sahabi nan mai suna wanda a yanzu garin su yana karkashin jihar jihar a inda take a qasar Saudi Arabia nan ne asalin garin su malamai suka ce ana mishi alkunya da wasu kuma suka ce wasu suka ce ana ce mishi amma dai sunan shi wannan malami yana daga cikin malaman ainihin sunna a inda malamai suka ce ya manyanta kwarai da gaske furfura ta mamaye kanshi da gemun shi kamar yadda zamu zo mu ji yakan ainihin wato wannan furfura tashi da lalle mai wa'azi ne ainihin a qasar Makka yana daga cikin wadanda da aka kasabta su kashi uku na farko da na biyu da na uku to shi ya shiga cikin yazo a cikin littafin
[Segment 2/3 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
Yake cewa Shi wannan ya kasance dattijo ne babba. Kanshi fari haka kuma gemun shi. Ba dan komai ba saboda furfura. Mutum ne dogo. Mai jiki. Sannan fari ne. Yana da idanuwa dara dara amma sun fi bayyana zuwa gajaje gajaje. Yakan rina ainihin furfuren shi da lalle ko kuma da za'afaran. Mutum ne na tsatse. Wannan ita ce daga cikin sifofin Na tsatsu ne masu karatun alqur'ani zaka same su basu hayaniya. An haife shi a Makka. A shekara ta arba'in da biyar bayan hijira a zamanin sayyidina Mu'awiya. Kuma a Makka din ya rasu. Shekara ta dari da ashirin. A zamanin sarki Hishamu dan Abdul Malik. A lokacin yana dan shekara saba'in da biyar. Kun ji taƙaitaccen tarihin shi. Wanda na karanto mana daga Wanda ya rasu hijira na da shekara dari biyar da arba'in. A cikin mujalladi na farko na wannan littafi gashi daga nan ne na karanto mana. Dan haka kun ji na farko. Shine Mallam Shatubiyya ce ita kuwa Makka Abdullah nan ne ya zaɓa ta zaman mishi wurin zama. Shine wato Abdullah dan Kathir dan mai albarka. Wanda albarkar shi ta mamaye dukkanin al'umma tare da ɗaukaka. Yace ɗaliban shi da Ahmad Al Bazzi da Muhammad sune ɗaliban nashi. Amma sai yace Ba sun yi karatu ne kai tsaye a wurin shi ba. Sun karɓo riwayar shi ne da Yace Shi Muhammad din shine ake mishi laƙabi da Qumbul. In Allah ya so lokacin da aka zo tantance abubuwa a cikin waɗannan makarantata tamu ta A lokacin za'a ainihin tsaya a fayyace ire iren waɗannan baitoci menene imamu Shatubiyya ke nufi da su. Kun ji na farko kenan. Ma'ana makaranta ɗaya ce amma ta ci sunan malamai biyu. Waɗanda malaman kuma sun shahara da ainihin waɗannan ainihin wato abin nan sunaye na su. Da kuma Ainihin wato Wancan Al Makki wannan Ad Dimashqi. Wancan Abdullah wannan Ismail. Shi na biyu shi ko malamin tafsiri ne. Babban malami ne. Imam Ismail dan Umar dan Kathir. Ka ji yadda abun yake. Shi wancan Abdullah Kathir din baban shi ne mahaifi. Shi ko wannan Ismail Kathir din kakan shi ne da ya haifi uban shi mai suna Umar. Amma sai shi din ya shahara da Kamar yadda ya shahara da Hazmun din kakan shi ne. ya shahara da Abdul Barri din kakan shi ne. ya shahara da Taiyya din kakan shi ce. Haka wannan ma ya shahara da amma Kathir din kakan shi ne. Wancan ko ya shahara da amma Kathir din mahaifin shi ne. Shi kuwa wannan aka ce an haife shi ne a ainihin wato Daga cikin ƙauyuka na garin ainihin Busra ba Basra ba. Busra a ƙasar Sham take. Basra a ƙasar Iraki take. An haife shi ainihin wato shekarar hijira na da dari bakwai da daya. Ko kuma makamancin haka. An haife shi a gida ne na ilimi domin baban shi malami ne. Sannan baban shi mutumin kirki ne. Bayan da mahaifin su ya rasu. Sai ainihin wan shi. Wanda shine na biyu a cikin gidan. Domin asali shi mai tafsiri. Ya ci sunan babban wan shi ne. Babban wan shi Dan Umar. Shine aka haife shi ya haddace alqur'ani. Ya zama gogaggen malami yana dan shekara sha shida zuwa sha bakwai. Uban su Umar yana ta murnar cewa madalla ya samu magaji. Tsautsayi sai yasa yaron ya faɗo daga bene. Ko daga bishiya nan take sai ya mutu. Mallam Umar ya matukar baƙin ciki ƙwarai da gaske amma ya maida al'amari ga Allah. Ana nan sai wata matar shi kuma ba uwar wancan Ismail ba sai ta haifi wani ɗa. Sai ya sanya wannan ainihin ɗa To daga haihuwar wannan Ismail ba'a daɗe ba. Sai shi mallam Umar ya rasu. Sai ɗan shi na biyu mai suna Abdul Wahab wanda shi ma ya taso da tarbiyyar ilimi. Sai ya ga cewa to wannan ɗan uban su yana da manufa ne irin manufar da yake da ita akan babban ɗan shi. Dan haka sai ya ɗauke shi daga wannan ƙauye sai suka dawo cikin babban birnin Dimashq. Domin a nemi ilimi a hannun manya manyan malamai. Ismail ibn Kathir ya shagaltu da neman ilimi a hannun babban wan shi Abdul Wahab. Sannan kuma sai yasa ƙwazo wajen neman ainihin ilimi a hannun manya manyan malamai Irin su Ibn Taimiyya. Irin su Irin su Har ya aura mishi ƴar shi daga ƙarshe ya waye gari ya zama sarkin Ya kuma ainihin haddace alqur'ani mai girma. Ya cika ainihin haddashi Yana dan shekara goma. Ya haddace alqur'ani kuma ya kyautata ainihin wato haddar tashi. Allah maɗaukakin sarki Ya ƙara mishi ainihin wato ɗaukaka da daraja. Ya rubuta littattafai da dama bayan yayi karance karance a wurin malamai masu ɗimbin yawa kamar yadda ka ji munyi ishara. Daga cikin littattafan shi akwai Wanda asalin wannan tafsirin yayi wa ɗalibai shiftar shi ne wato yana zama yana karantar da su. Suka ainihin wato ruwaito daga gare shi. Sannan da littafin Littafin da a bangaren tarihin duniya Daga farkon ta har zuwa shekara dari bakwai na musulunci ba'a samu kamar shi ba. Da Da kuma wanda aka fi sani da A ƙarshen rayuwar shi ya samu ainihin ciwon ido wanda ta kai shi zuwa ga makanta. Ya rasu a ranar Alhamis. Wanda tayi daidai da ashirin da shida ga watan Sha'aban. Hijira na da dari bakwai da saba'in da hudu. Jana'izar shi kamar yadda yake cewa Jana'iza ciwon da yake ta tara gari baki daya. Kuma yayi wasiyya cewa in an tashi rufe shi a rufe shi a makabartar da aka rufe malamin shi shine Ibn Taimiyya. A wannan makabarta a nan ainihin aka rufe shi mai suna A ainihin wato babun nasr a garin ainihin Dimashq. Allah maɗaukakin sarki ya gafarta musu.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
Jama'a kun ji daga inda wannan makaranta ta samo ainihin sunan ta. Makaranta ta ta ta hadda alqur'ani daru ake sa mata. Daru ake sa mata. Ba madrasa ba. Abin da daru take nufi ita ce institute da turanci ko kuma cibiyar yada ilimi. Daru da za'a sa mata sai a dube abin da za'a danganta gare ta. Ma'ana shine yasa muka danganta ta zuwa ga waɗannan manyan malamai. Domin ka fahimci cewa ashe Kamar yadda Ibn Kathir Abdullah na farko malamin qur'ani ne. Ibn Kathir Ismail na biyu shi kuma malamin alqur'ani ne. Wancan ya ƙware a kira'a. Wannan ya ƙware a tafsiri da To wannan makarantar manufar ta kenan za'a karantar da zallar karatun alqur'ani. Da dukkanin kira'o'i waɗanda suka inganta domin kira'o'i da suka inganta sun wace guda bakwai. To za'a karantar in sha Allahu ta'ala da dukkanin kira'o'i da suka inganta. Da riwayoyi waɗanda suka tabbatar to daga annabi Jama'a ina fatan an samu kyakkyawar gamsuwar Daga yadda makarantar ta samo suna. Dan haka sunan ta Ma'ana cibiyar Ibn Kathir domin haddar alqur'ani mai girma. Daga cikin tsare tsaren wannan makaranta shine makaranta ce ta maza da mata. Yara da manya. Amma tsare tsaren namu zamu bi su sannu sannu ne. Har yau daga cikin tsare tsaren wannan makarantar Tana da full time tana da part time. Har yau daga cikin tsare tsaren wannan makaranta private school ce. Wato ba makaranta ce ta gwamnati ba. Ba kuma makaranta ce ta wata ƙungiya Mai ainihin wato zaman kanta ba sai dai ita makarantar ce mai zaman kanta shine ma'anar private school. Wato Makaranta ce wanda take mai zaman kanta. Daga cikin tsare tsaren makarantar Ltd akwai ɗaliban da da safe zasu yi karatu. Akwai waɗanda da yamma zasu yi karatu. Akwai waɗanda da daddare zasu yi karatu in sha Allahu ta'ala. Amma a yau zamu gabatar da tsare tsare guda biyu ne sune tsarin safe da tsarin yamma. Tsarin safe na samari da manya maza da mata tsarin yamma kuma na yara ƙanana maza da mata. Dangane da abin da ya shafi manya Duk wanda zai shiga wannan makaranta ya san cewa To full time ce wato cikakken lokacin ka zaka bayar. Domin shekara hudu ne za'a yi a sauke hadda da karatun alqur'ani. Kuma kwanaki shida ne a cikin mako ranar juma'a ce kawai hutu. Sannan tana da terms guda uku wato tana da zangon karatu guda uku a shekara. Sannan Duk bayan zangon karatu guda wato term To za'a bada hutu ne na mako biyu rack. Watan azumi da kwana goma. Kwanaki arba'in a jere. Sune abin da zai zama ainihin wato long vacation wato dogon hutu. Kwanaki arba'in kenan. Wato in daya ga ramadan ya kama to za'a rufe makarantar Har sai bayan sallah da kwana goma. Shine ainihin tashe na shekara. Za'a rinƙa fara karatu in sha Allahu ta'ala ƙarfe tara na safe daidai ana tashi ƙarfe biyu na rana in sha Allahu. Kullum Akwai Wato assignment da za'a rinƙa bayar Ko kuma karɓar haddar ko kuma a bada ainihin rubutu. Dukkanin assignment da za'a bayar na ka je ka yo bincike. A cikin waɗansu littattafai ko akan duniyar gizo ta internet. Wannan makaranta uwar wato ita ce Ta tattalawa ainihin wato Ɗaliban makarantar da malaman duk abin da suke buƙata Wanda basa buƙatar su fita waje domin neman wani abu in sha Allahu ta'ala. Domin a tsawon shekaru talatin da daya ɗin nan. To munyi ƙoƙarin mallakawa makarantar Duk wani littafi wanda za'a buƙata a kiyaye ba mu ce mun mallaki duk littattafan duniya ba amma dai duk abin da makarantar zata buƙata To makarantar tana da shi. Akan ainihin wato rubutaccen takarda ne. Ko ko a Ko kuwa akan ainihin fasahar zamani ne ta ainihin wato na aura computer. Ko ko wasu abubuwa ne da za'a tafi a lalibo su a duniyar internet makarantar tana da su in sha Allahu ta'ala dan haka Duk ɗalibin da ke wannan makarantar Baya buƙatar sai ya kallafa wa kanshi siyan littafi ko ƙwaya daya daga waje. Littattafan da zasu zama matsayin A makarantar za'a siyar da su. Su kuwa qur'anan To zamu ji ainihin ta yadda zasu kasance ga ɗaliban makarantar. Wannan shine abin da ya shafi tsarin wannan ainihin wato makaranta bangaren manya. A cikin wannan makaranta Harshen da za'a rinƙa yin darasi da shi shine harshen larabci. Amma a matakan farko Za'a dan rinƙa sirkawa da Hausa. Amma idan tafiya tayi tafiya To shikenan za'a daina magana da ainihin Hausa. Har sai in ka fita daga cikin makarantar gaba daya ka je ka nemi Hausar ko kuma wani yare amma da malamin da ɗaliban wajibi ne larabci zasu yi. Amma ba shi daga cikin abubuwan da za'a karantar a makarantar harshen larabci a karance sai dai za'a rinƙa karantar da shi a ɗabbakance. Ta hanya yi maka magana da kuma yi maka bayanin waɗansu abubuwa da harshen larabcin. In sha Allahu ta'ala wannan shine tsarin da aka ɗauka. Dangane da kuɗin makaranta naira dubu hamsin ne ainihin a shekara. Wato a shekara hudu kenan naira dubu dari biyu ne. Waɗannan kuɗin makaranta kuɗin makaranta ne da ake kiran su Zaka iya raba su a cikin shekara kashi uku ka bada naira dubu ashirin a zangon farko. Naira dubu sha biyar zango na biyu wata naira dubu sha biyar din a zango na uku. Ka ga dubu hamsin kenan in sha Allahu ta'ala. Littattafan da za'a karantar a wannan makaranta ƙananan littattafai ne waɗanda Ba masu yawa bane. Ba zasu wuce naira dari Naira dari da hamsin naira dari biyu ba. Ɗaliban makarantar nan Zasu rinƙa ainihin sayan su. Waɗanda suka biya kuɗin makaranta daga cikin waɗanda ba ɗaliban Duk waɗannan littattafai da za'a karantar a cikin kuɗin su ne za'a ba su. Ɗaliban kuwa Saboda asali su za'a su biya kuɗin makaranta ne da suka shaba na To sune kaɗai suke buƙatar siyan ire ire waɗannan littattafai a matsayin naira dari ko naira hamsin ko makamancin haka. Waɗannan littattafai Kaɗai Mun mallaka su ne domin ɗaliban wannan ainihin wato makaranta ta Dukkanin wanda ba ɗan makarantar bane ko da yana Ko yana Ko yana wata makaranta daga cikin makarantun mu Ba za'a siyan mishi da littafin ba. Ba za'a bashi kyauta ba. Ba za'a bashi aro ba. Ba kuma zai shiga library na waɗannan ƴan Wannan shine tsarin da mukayi. Dan haka littafin farko da zamu ainihin wato fara karantar da su a cikin watanni biyu ko uku masu zuwa Shine littafin Wani Alaramma ne Shugaban makarantun hadda alqur'ani na ainihin wato A cikin ainihin wato ƙasar Makka. Wato tsakanin Makka da Madina garin yake. To wannan littafin yana daga cikin littattafan da za'a karantar da su a cikin watanni uku masu ainihin zuwa in sha Allahu ta'ala. Sai bayani dangane da qur'ani. Bayani dangane da qur'ani ita ce za'a mu karantar kamar yadda ita ce nuska karɓar biya duk duniya Nuskar da sayyidina Abubakar da Umar Suka jagoranci sahabbai Bayan rasuwar manzon Allah Aka zauna aka rubuce ta. Ta waye gari bayan rasuwar Abubakar da Umar tana hannun uwar mumini Matar annabi A zamanin sayyidina aka ɗauke ta Aka ainihin wato buga ta da yawa aka yaɗa ta duk ƙasashen duniya. Wannan nuska ita ce nuskar da Allah yayi yarda da ita ita ce nuskar da annabi yayi yarda da ita ita ce nuskar da sahabbai suka yarda da ita dan haka ita ce nuskar da za'a mu karantar in sha Allahu ta'ala. Ita ce nuskar da Aka rubuta Mafi yawancin alqur'anan duniya a yau. Sai ƴan kaɗan da ba'a rasa waɗanda an rubuta su ne wanda kuma wannan haramun ne bidi'a ce. Ba'a rubuta alqur'ani da wani tsarin rubutu. Baki daya sai da ainihin rubutu irin waɗannan da su sayyidina Dan in buga misalin ka gane Ana
[Segment 3/3 | 00:40:00–end]
[Speaker seg3-spk:0]
da alif lan jaye sai zaira sai kaulasan sai wau sai ayi aluja a saman wau din sannan sai ayi takuri wannan na daga cikin ka'idojin da aka rubuta alqur'ani tun a gaban annabi wadanda suka rubuta sune su zaid da su aliyu wadanda sune sakatarorin wahayin manzon allah idan aka zo rubuta kalmar sallah za'a ga an rubuta da sai wau sai aluja a saman shi sai kuma ainihin takuri haka kalmar haka dai ire-iren wadannan sune abinda muke nufi da haramun ne a zo rubuta alqur'ani kamar yadda galibi za'a ga suna rubutawa a cikin bagadadi a rubuta kalmar sai a rubuta sai ayi lamalu sai ayi takuri wannan haramun ne kuma bidi'a ce wadda take malamai gaba daya sun hadu akan haramcin ta daliban da zamu karantar da su a zamu karantar da su wani ilimi mai suna wato wannan qur'ani shine ainihin qur'anin da daru bunul haisam suka ainihin buga kuma shine ainihin wato qur'anin da ya cika wadannan sharuda shine zamu karantar gashi gashi nan suka buga shi wadda suke wannan na daya daga cikin ainihin wannan makarantar zata fara da riwayoyi guda biyu ne riwayar daga sai kuma riwayar mai yiwuwa bana baza'a samu damar farawa ba sai da bangaren yan saboda karancin daliban mai yiwuwa amma ita dai makaranta a shirye take idan an samu wadattun dalibai abinda muke nufi da wadattun dalibai shine a ko wani aji a samu dalibi daga zuwa saboda azuzuwan dama anyi an gina su ne gini na musamman ba irin tsarin azuzuwa ba sai dan wannan aikin na musamman dan haka a bisa tsarin ginin da ma'aikatar ilimin gwamnatin tarayyar nigeria ta tsara girman azuzuwa to ko wani aji daya daga cikin wadannan azuzuwa namu madadin daya to daya da rabi ne dan haka madadin yaci dalibai to mafi yawa zaci ainihin idan da zamu samu daliban da zasu kai mana guda ainihin wato to zamu iya zuba su zama su zama inda zamu samu zasu zama su zama hakan inda za'a samu tare da cewa zamu ainihin kwadatar da daliban ne dangane da zabin kira'a kaza da kira'a kaza ko riwaya kaza da riwaya kaza ba tursasawa zamu yi ma'ana kai a nufin ka da wacce riwaya ka so ka haddace ita wannan hadda da zakayi da wannan riwaya guda daya a yadda muka tsara a makarantar shine idan ka haddace to kuma zamu ce maka akwai wani wannan akan kira'at ne banda ainihin kira'at da ai kira'ar da ka haddace ko riwayar da ka haddace za'a zo a koyar da kai kuma wasu riwayoyi da wasu kira'o'i ana mai jingina maka a jikin wannan da ka baka haddace darasi ne na musamman amma shi ne na tsawon shekara guda bayan ka haddace da ko ka haddace da to sai kuma a zo a koya maka sauran kira'at amma wannan sai ga wanda ya zaba kamar wanda ya kaga sai in ya zaba yayi in ba haka ba babu lallai babu dole to haka wannan abun yake wadannan qur'anai jama'a ni nine na siye su kuma na sadaukar da sune wakafi ga mahaifiya ta mai suna wadda yau shekarar ta kamar ainihin shida ko kuma bakwai da rasuwa nayi mata wakafin wannan wadannan ba kuma wadannan kadai ba a'a duk wasu da za'a karanta a wannan makaranta ta daga nan har wadannan qur'ane ni da kudi na zan siye su kuma a baiwa ko wani dalibi a matsayin an mallaka mishi shi kuma a matsayin wakafi dan haka wadannan qur'ane ba na siyarwa bane kuma ba na a dauka a bayar da su sadaka din bane ga wani domin asalin ni da nayi wakafin nayi sharadi wakafi ne ga uwata kadai kuma wadanda zasu yi amfani da wadannan qur'anan wakafi a matsayin an basu su kyauta dindindin sune daliban makarantar dan haka wadannan qur'anai basu daga cikin wadanda za'a lissafa a cikin littattafan da za'a siyar wa da daliban ko wani dalibi matukar yayi register a makarantar nan to rana fara karatu za'a kawo guda daya za'a ainihin mallaka mishi sai dai kuma sai yayi kokarin kiyayewa domin in ya batar da shi ko ya salwantar da shi kuma baza'a sake bashi wani ba kuma baza'a ainihin siyar mishi ba sai dai ya san ina ne zai tafi a kasuwa ya samu irin shi domin bazai zo da wani alqur'ani ba sai ainihin shi wannan kwaya daya irin wanda kowa yake rike da shi wannan na daga cikin ka'idar da muka lazimta dan haka qur'anan da za'a yi amfani da su a ko wani aji to irin su daya bugun su daya launin takardar su daya girman rubutun su daya wasalin su daya launin tawadar da ke ciki iri daya abinda ya shafi shafi da ke karewa da ke farawa komai daya ne duka daliban haka zasu kasance kuma duka haka qur'anan zasu kasance insha allahu ta'ala dan haka kunji bayani dangane da wadannan ainihin qur'anai kamar yadda na fadi wakafi ne nayi wa mahaifiya ta saboda itace malama ta farko tawa ta alqur'ani itace ta farko wadda ta saka ni a makarantar alqur'ani itace ta farko wadda ta bada muhimmanci dangane da karatu na na alqur'ani mai girma har zuwa lokacin da allah madaukakin sarki ya dauki ranta itace mutuniyar farko da ta fara dafa mini tawada da karo da zige itace mutuniyar farko da take samo gamba daga can kasar su ta kano tazo ta feke min alkaluma masu kyau itace mutuniyar farko da take samo mana allo wanda aka sassake shi da bishiyar duniya domin shine allon da yafi ko wanne kyau da dadin rubutu wanda baya sha wannan na kadan daga cikin dansa kamar kwanda zan dan iya mata a bisa dan kokarin da zan iya yi mata ba dan in iya biyan ta ba domin kamar yadda babban sahabi ibn umar ya bayar da fatawa ga wani da yayi aikin haji yana goye da uwar shi a baya sai yazo yake tambayar ibn umar cewa allah gafarta malam kana ganin na biya uwata sai yace ko yunkurin na guda daya baka biya ta ba to ba'a iya biyan uwa ko daga haihuwar da tayi maka kadai balle uwar da tayi hidima gare ni uwa irin tawa wanda yake in ba uwa irin ta imam ahmad ibn hambali ba da uwa irin ta imam shafi'i a duniyar tarihi ban karanta tarihin wata uwa wadda nake iya kwatanta ta da ta uwar ba ina fadin haka ne dan tsabar adalci da kuma gaskiyar da ni na sani gama da ita dan haka in nayi mata addu'a ta musamman allah madaukakin sarki ya gafarta mata
[Speaker seg3-spk:1]
amin
[Speaker seg3-spk:0]
allah ya dauka ka darajojin ta a cikin bayin allah madaukaka
[Speaker seg3-spk:1]
amin
[Speaker unknown]
babu mamaki idan tayi haka domin tun ina karami take kai ni gidan su gidan malamai ne ba abinda zaka hanga daga tarin kara sai tarin toka da alluna na almajirai wadanda suke nufowa ko ina ainihin a wadannan yankuna na kauye inda ake kira ainihin wato hawwadan bango a cikin ainihin wato kasar kano a yau ko hawwadan galadima ana dauka ainihin karatun alqur'ani dan haka ina addu'a ta musamman allah madaukakin sarki ya saka mata da alkhairi bayani dangane da tsarin makarantar yara kuma tsarin makarantar yara a cikin wannan makaranta ta ibn kathirin ko daru ibn kathirin shine yara muna daukan su tun daga yaran da suka fara magana baza mu ce yan shekara kaza ba saboda wani yaran allah zai iya karrama shi ya fara magana yana shekara biyu da rabi ko shekara uku dan haka duk yaran da ya fara magana ko da in an kawo shi za'a yi tayin karatun shi bazai ba gentleman kenan sai yaje gida zai yi nashi eh kun san akwai irin su gentleman kenan za'a yi tayi bazai yi ba amma sai yaje gida zai yi nashi to ya isa a kawo mana shi insha allahu ta'ala amma in ya zama baya magana gaba daya to wannan kuma bai isa a dauke shi ba kar kayi gaggawa bari in allah ya kai mu badi za'a ayi insha allahu ta'ala wannan abu ne da zai ci gaba duk shekara za'a ringa dauka lokacin daukar kuma shine watan shawwal bayan karamar sallah na dukkan shekara dan haka in danka bai isa ba bana dinki bai isa ba bana ki kwantar da hankalin ki allah ya kai mu badi za'a dauke shi insha allahu ta'ala haka yar ki sannan a yara to mafi yawan wanda ya kai shekara goma shine geji idan ya wuce shekara goma to kuma wannan wani tsari ne na daban za'a zo musu da shi dan haka daga yan shekarun da suka fara magana zuwa yan shekara goma to zamu kasafta su kashi uku da yan wadannan yan turagutsa yan mutsi mutsi da kuma tsaka tsakin su sune yan shekara biyar shida bakwai su kuma sune yan tsakiya da kuma yan shekara takwas tara goma su kuma sune manya dan haka zuwa yanzu zai zama muna da azuzuwa guda uku kenan kananan yara kace yan shekara hudu misali sai wadanda suke yan shekara biyar shida bakwai sai kuma yan shekara takwas tara goma wadannan nau'in farko kanana wadannan na biyu na tsakiya wadannan kuma na uku sune manya za'a ringa musu wannan karatu daga ranar litinin talata laraba alhamis dan haka kwanaki hudu sune ranakun karatu litinin talata laraba alhamis ranakun juma'a asabar lahadi sune ranakun hutu lokacin karatu kuma shine karfe hudu da rabi za'a ringa fara musu karatu na yamma kuma zasu tashi karfe biyar da rabi awa daya rak karatun alqur'ani ne zalla wato hadda alqur'ani ba lallai ma ya zama za'a sanya musu alqur'ani ba sai in sunyi nisa tukuna amma abu mai muhimmanci shine karatun alqur'anin da zasu yi hadda ne idan kuma idon su ya bude za'a basu ainihin qur'ani to suma yana daga cikin ainihin qur'ani wanda zamu ringa basu a karkashin wancan wakafi in allah ya so dan haka shi wannan wakafi da nayi wa ita mahaifiya ta ta alqur'ani na alqur'ani ya shafi duk wani wanda za'a karanta karatun alqur'ani a karkashin daru bunul kathirin idan ya kai za'a sanya musu juzu'a amma ne to zamu ainihin dauko juzu'a amma bugun madina zamu baiwa ko wani yaro kyauta idan ya kasance za'a karantar da su ainihin wato juzu'in tabara ne ko juzu'in ko juzu'in ko juzu'in to duk wadannan ainihin wato zamu basu ne a cikin wannan wakafi insha allahu ta'ala amma in ya zama za'a karantar da su wato littafi ne dangane da abinda ya shafi ka'idoji na koyan karatun larabci na alqur'ani shine kamar to wannan siye zasu yi kuma zasu siye bugu ne mai kyau wanda muke tahowa da shi daga ainihin kasar makka ko madina don muma siye muke yi idan ya kasance tare da ne ko haka za'a siyar musu gaba daya domin abinda muke koya musu a ringa komawa gida ana sanya musu ko kuma a ainihin wato ana sa musu domin ya ringa wasa tunanin su muna da wadannan abubuwan baki daya a bisa yadda kaji ainihin wato mun ambata idan ya kasance alqa'idatun nuraniyya littafi ne shima ka ganshi kamar bagadadi yake littafi ne gashi yadda ka ganshi haka ainihin ake buga shi ana siyar da shi ainihin kasar makka gashi nan suna sai da shi kusan real ashirin ne ko talatin wato kusan dubu daya da wani abu to kaga wannan littafin an rubuta shi ne domin karantar da yara alqur'ani tsarin shi kusan tsarin bagadadi ne yana tare da yana tare da to muna da su a wannan makarantar in kazo zaka siye wa danka zaka iya siye mishi inda zaka siya inda zaka siya inda duka zaka siya amma sai in yanayi ya kai za'a sanya musu dan haka ba ko wani yaro bane za'a ainihin wato sanya wannan din sai wanda yanayi ya kama insha allahu ta'ala wannan yana daga cikin ainihin wato tsare tsaren allah madaukakin sarki ya taimaka su yaran ba kamar manya ba suna da din su shine ainihin fari ga maza sannan mai ruwan kasa mai haske ga mata wato kwatan kwacin yadda kaga kalante burun kata kwannan da nake zaune ainihin akan shi wannan shine ainihin launin na mata din mata din doguwar riga ce mai dogon hannu da maballai tun daga saman ta har kasa wato botura da kuma botur a kwala hannun ta sa'annan kuma da hijabi dogo hijabin kuma mai ainihin wato hannu shima mai kwala da aljihun dama da hagu a jikin wannan ainihin rigar wannan din mata kenan din maza kuma
============================================================
[Part 2]
============================================================
[Segment 1/6 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Allah madaukakin sarki ya taimaka. Su yaran ba kaman manya ba suna da uniform. Uniform dinsu shine ainihin fari ga maza sannan mai ruwan kasa mai haske ga mata wato kwatan kwacin yadda kaga kalan teburin kata kwanan da nake zaune ainihin akan shi. Wannan shine ainihin launin na mata din. Mata din doguwar riga ce mai dogon hannu da maballai tun daga saman ta har kasa wato botura da kuma botur a kwala hannun ta sa'annan kuma da hijabi dogo hijabin kuma mai ainihin wato hannu shima mai kwala da aljihuwai dama da hagu a jikin wannan ainihin rigar. Wannan uniform din mata kenan. Uniform din maza kuma kamar yadda nace fari ne. Doguwar riga ce da dogon wando irin na sunna yankakke iyakar kwauri da kuma ainihin hula irin ta Makka sannan ga wadanda suka yi wa yau da kuma dan igal wato irin dan kallabin maza da larabawan Saudiya ainihin suke sawa. Amma wannan ga manyan kenan. Amma ga yaran kanana to hula ce kadai irin ta ainihin Makka. Wannan shine uniform din. Akwai baje wanda bajen mu na makaranta buga shi ake yi a jikin ainihin aljihun riga ko kuma a bayan hijabin 'ya mace. Wannan shine tsare tsaren ko wane da za'a dinka mishi uniform guda biyu mata ma za'a dinka musu guda biyu. A wannan makarantar ake sai da uniform din dan haka in aka dauki danka a makaranta za'a gwada shi a kuma fada maka kudin yadi da kudin dinki baza'a kara maka ko kwabo a bisa kudin yadi da kudin dinki ba da kudin baje. Sannan dangane da abinda ya shafi kudin makarantar su naira dubu daya ne rak a wata naira dubu daya a wata. Amma naira dubu dayan a wata abinda take nufi shine naira dubu goma sha biyu a shekara. Wato hatta watannin da ake hutu zaka biya kudi. Domin hatta wadannan watannin da ake hutu su malaman ba hutu suke ba. Aiki suke na shirya wa yaran jarabawa da fitar musu da sakamakon jarabawa da sauransu. Dan haka a shekara naira dubu goma sha biyu. A wata naira dubu daya a wata uku naira dubu uku. Uba na da zabi akan duk wanda ya so yayi. Zaka iya biyan kudin shekara zaka iya biyan na wata uku zaka iya biyan na wata daya zaka iya biyan na wata biyu ko wata hudu duk gwargwadon yadda ka so. Ma'ana duk wasu kudi da zasu zo kasa da naira dubu daya ne baza'a ansa ba. Amma za'a karbi naira dubu biyu za'a karbi uku za'a karbi hudu za'a karbi biyar. Baza'a karbi na wata daya da rabi ba wato baza'a karbi naira dubu daya da dari biyar ba. Sai dai wata biyu ko wata uku ko makamantan haka. Wadannan sune tsare tsare dangane da abinda ya shafi ainihin ita makaranta ta yara din jama'a. Ya rage wadannan yara baza mu juru latti ba. Yaran duk da yazo latti baza'a barshi ya shigo ba. To dan haka shawarar da muke baiwa iyaye idan har zaka wakilta wani wanda zai ringa kawo yaran ka ne kuma ya samu wuri ya zauna tunda darasin na awa daya ne rak har sai an tashi to zai fi. Sannan baza mu juru over time ba. Idan ka bar mana yara in ta kai magariba har sai an basu tuwo sun ci ko indomie to in kazo zaka biya don sunyi over time. Ina fata an gane. Dan yaro ya fashe da kuka baza mu barshi da yunwa ba. To kuma in muka ci da shi zaka biya mu don wannan bashi daga cikin hidimomin da muka ce zamu yi. Allah madaukakin sarki ya taimaka. Shawarar da muke bayarwa ga wadanda zasu ringa zuwa da babura da ke kuna domin daukan 'ya'yan su ko kawo 'ya'yan su sune su ringa biyo dasu ta kofar baya. Amma wanda zai zo da mota to ya ringa samun wuri can gefe yayi parking sannan ya kamo hannun yaran ya shigo dasu. Amma babu parking a kofar gate din makaranta ko kofar makaranta domin zaka takura na cikin makarantar da zasu fita ko wadanda zasu shigo kamar yadda kuma zaka takura mutanen da ke wucewa akan titi. Dan haka duk wanda ya zanda mota yazo da 'ya'yan shi sai ya samu can gefe yayi parking sai ya kamo hannun yaran a hankali sai ya shigo da su makaranta sannan sai ya tafi. Baza mu so ka sako su daga can ba gasu 'yan kanana yadda zasu iya zuwa wajen wucewa ko ketarawa mota ko babur ya kade su. Sannan masu ke kuna da babura da zasu kawo 'ya'yan su su kuma baza mu so su ringa ainihin towa suna tsayawa a nan ba don kar a ringa samar da gosulo ga masu wucewa. Sai a biyo ta kofar gate wato wanda take cikin unguwa sai kazo sai ka ajiye danka a keke ko a babur ko kuma sai ka ainihin wato zo domin jiran daukan shi. Wadannan sune ainihin wato tsare tsaren da muka yi wadanda muke fatan Allah madaukakin sarki ya taimaka mana kuma ya sa mana hannu a cikin wadannan al'amura din insha Allahu ta'ala. Sai abinda ya shafi ainihin wato biro da pensiri da littattafan rubutu wadanda in har ta kama za'a ainihin wato sai wa yara to a makarantar nan ne za'a sai musu insha Allahu ta'ala. Zamu sanya a buga littattafai wadanda zasu dauki sunan makarantar insha Allah wato Allah madaukakin sarki ya taimaka. Dukkanin yaran da aka samu baya kawo hadda to za'a ainihin wato kira uwar da kuma uban makaranta a zauna dasu domin su zo su amsa menene ke faruwa. Wannan ya kai mu zuwa ga wata magana wadda muka gabatar a wurin gayyatar wannan zama da kaddamar da makarantar nan muka ce muna kira ga dukkanin wanda ya san ya sanya dan shi ko zai sanya dan shi a wannan makaranta ya samu halartuwa wannan wuri da shi da uwar wannan yaro ko kuma markiyarsu wannan yaro idan markiyar yaran ta kasance kishiyar uwa ce ko kanwar uwa ko kaka ko makamantan haka. Kuma zamu kira taro na musamman. Ba dan komai ba saboda galibi lokacin da za'a kawo yaran makaranta iyayen suna kasuwa ko yaran zasu zo da kansu ko wani zai kawo su. Ita makarantar ba irin makarantar islamiyya ce ta Najeriya ba. Nace ba irin makarantar islamiyya ta Najeriya ba wato makarantar islamiyya ce domin ma'anar makarantar islamiyya makarantar musulunci to makarantar musulunci ce amma ba irin ta Najeriya ba. Wato wadda ake zuwa in anga dama kuma a ki zuwa in anga dama azo sanda aka gada ma da irin rigar da aka gada ma. Kaga yaran islamiyya zasu tafi wandinan su duk a dage sai ka dauka wandinan sunna ne a'a wandinan bidi'a ne amma tsabar dauda ce da sufurin tasa wandan ya dage har ya koma rabin kwauri. To gaskiya duk yaron da zai zo makarantar nan sai anyi mai wanka an shafa mishi mai an gyara mai jiki in namiji ne an fisa mai tirare an taje mai kai. Idan kansu yana bukatan aski a makarantar nan muna da wurin aski na musman wanda dama anyi ne kadai dan daliban makarantar maza. Manya zasu biya kudi naira ashirin. Amma yara duk wani yaro dake makarantar nan kyauta za'a ringa mai aski dan haka in har aka ga kansu ya kai ayi mai aski to baza'a yi shawara da uwar shi ko uban shi ba sai dai ki ga danki ya dawo da askyar kanka anyi mishi aski insha Allahu ta'ala. Wannan shine ainihin tsarin da muka yi. Ina fatan jama'a su fahimci wannan. Wannan tsari da muka yi tsari ne wanda yake baza mu karbi kazanta ba. Yankan kumba idan mace ce da yi mata kitso ado da tsafta da gayu da cakkarewa fiye da yadda ake yi idan za'a tafi makarantar naziri ko primary ko secondary da safe. Dan haka ko kadan baza mu juru dauda ba. Warin bakin yaro ko yarinya ko mutuwa hakora baza mu juru wannan ba. Dan haka uniform din nan za'a ringa wanke shi ana goge shi. Idan ya tsufa kazo ka sake bada kudi a dinka wa yaro yadda in zai taho makaranta zai taho da natsuwa da tsafta da haske da kyalli da kanshin tirare. Takalmi zaka samu takalmi mai kyau wanda zaka samu ka sa wa yaran ka bamu kayyade cewa sai takalmi iri kaza ba. Bamu ce kuma dole sai da safa fa. Amma dai lallai ne tsafta ga maza da mata mata baza'a sanya musu tirare ba saboda tarbiyyar su muke kamar yadda hadisin sahabi Abu Huraira a cikin sunanin Nasa'i ya haramta mace ta sanya tirare in zata fita to hadda wadannan kananan yara suma haramun ne zasu fita a sanya musu tirare. Amma maza kuma fa wajibi ne a sanya musu tirare. Al-imam al-shatubi yace Yace yace kaga babban malamin nan mai wani sirrin tirare da ake kiran shi nafi'u wannan shine ya zabi Madina a matsayin kasar zama. Al-imamu nafi'u daga cikin shine malamin Madina. Almajiran shi kuma guda biyu ne shine yake cewa da Isa kalun da kuma Usman warsh sune ainihin almajiran shi. To me yasa ake ce mishi Shine aka ce idan ya fara karatun al-kur'ani sai a ji kanshin tirare yana busowa daga bakin shi. Da zaran ya fara karatun al-kur'ani sai a ji kanshin tirare. Ba wanda ya san wannan sirrin sai Allah madaukakin sarki. Dan dai kai kasan ba'a cin tirare. Balle kace in zai fito ne yake fesa tirare a bakin shi ko yake shafa tirare a bakin shi tiraren da muka san kadai ana sa shi a abinci a ci shine tiraren al-misk. Shine larabawa zaka samu suna sanyawa a cikin ainihin abinci wajen ci. Har shine malaman fiqihu suka tattauna in ka karanta askari cewa ina hukuncin alhaji da aka haramta mishi sanya tirare a jika sai kuma yaje ya sanya a cikin miya ko a cikin abinci ya ci sai kuma yazo sakamakon haka sai kanshin tirare na fitowa daga cikin jikin tunda ya ci a cikin shi ne. Tafi can ka kara ta kai da malaman fiqihu amma abinda muke so mu ce maka a nan ka dai san ba'a cin tirare. To shi yasa malamai suke ce mishi babban malamin nan wanda yake da sirri na tirare wanda Allah kadai ya san wannan sirrin shine malam nafi'u. To dan haka kaga danka ba lallai ne ya zama yana da irin wannan karamar ba. Shi wannan nashi tiraren natural ne. To dole ka ringa sanya wa danka artificial tirare. Dan haka idan ka sanya danka a wannan makarantar ko da bakwa sa tirare a gidan ku saboda talauci ko babu to kamar yadda zaka tara kudin ka tara kudin siyan tirare ko da irin dan duri ne. Sai dai kar a sawo mai tiraren da kuma zai yi karfi ya rikita kan malamin mai karatu da kuma ainihin wato daliban makarantar don akwai tiraren da kuma in aka sa shi sai kaji kamar za'a tashi sama. To ba irin wannan tiraren ba mai dadin kanshi. Dan haka azuzuwan mu za'a ga suke cike da wani irin kwarfi gashi irin wannan wanda na zuba tiraren wuta ne wanda za'a ringa kunnawa ainihin wato aji yana tashi da kanshin tirare. Ina fatan an gane. Haka al'amarin yake in aka zo lallai ne kanshin tirare so ake a ji yana tashi ko ina. To kaga in aka samu tiraren ya zama wannan iri kaza wannan iri kaza wannan iri kaza ya hade sai kaji kuma ya haifar da wani kanshi wanda ba'a samun irin shi a kasuwa saboda iri iri ne yafi karfin dan goma kenan. Allah madaukakin sarki ya taimake mu. Daga cikin salan karantarwa da zamu bi shine salan karantarwa irin na annabi da sahabbai shine a karantar da dalibi malami ya karanta ya karanta ya karanta dalibi ya saurara. Bayan dalibi ya saurara sannan sai kuma malami ya ringa karantawa dalibi yana bin bakin karatun shi sannu a hankali. To baza mu yadda da irin abinda hatta Allah ya hana annabi ba wanda a yau zaka samu makarantu na hadda al'kur'ani da dama da makarantun islamiyya ana yi wanda hatta annabi Allah ya haramta mishi Haramun ne in malami yana karatu dalibi kuma ya ringa ainihin bi a lokacin sai ya saurara sai har malami ya gama. Dan haka lokacin da malam yazo yana cewa Dalibi zai yi shiru ko motsi da bakin shi bazai ba. Sai ya gama saurare tsaf sannan malam yace to in nayi kuyi malam yace Dalibi ma ya biya karanta haka a hankali in malami yaji bai daidai ba ya ainihin gyara mishi. A cikin tsaren karantar wata mu akwai bulala akwai duka amma ba duka na zalunci ba sai dai duka na tarbiyya. Ba duka wanda zai karya kashi ko kuma ya tayar da fata ta kumbura ba sai dai duka na horo saboda wannan yazo a cikin ainihin sunna sahabbai suka ce Sahabbai suna dukan mu saboda karantar da mu a Eh tabi'ai suka ce sahabbai sun kasance suna dukan mu saboda karantar da mu ilimi. Idan muka samu yaro kangararre mara ji to muna da mari mai karfi wanda za mu daure shi a ciki. Sakamakon haka shi zai waye gari ya zama bodin kenan shine yaran da kai in kazo ka ajiye shi ko ka turo shi sai ya gudu in ka turo shi sai ya gudu to in kazo kace yaran nan ya zama makala haula to mu bai zama mana ba. Zamu iya maganin shi har sai ya dawo yazo mutumin kirki da ikon Allah. In ya ki to shine sai mu kama shi sai mu daure shi. A cikin makarantar nan a nan zai ringa kwana a nan zai ringa wuni yanzu ya zama bodin kenan. Sai kai ka ringa kawo kudin abincin shi da sabulun wankan shi da na wanki mu kuma zamu dau nauyin a kama shi a daure shi in lokacin karatu yayi a fito da shi ya shiga aji. Har sai lokacin da ya sauka a cikin tabi'ai an samu wani mai kiriniya haka shine malam ikrimatu da kake ji din nan. To kiriniya ce da shi shima daure shi ibn Abbasin yayi bai natsuwa ya ainihin wato zauna lafiya sai da ya sauka sannan aka kwance shi. To saboda haka zamu kai ga daura yaro idan ta kai ga haka. Muna fadin wadannan ne domin iyaye su ji wace irin makaranta ce ka kawo danka ne. Gaskiya makaranta ce wadda ta dace da al'kur'ani da kuma sunna a bisa kuma fahimtar malaman farko insha Allah wanda in Allah ya so muna fatan baza mu yi abinda zai kauce wa wannan tsarin ba insha Allahu. Sai abinda ya zama kuskure wanda in mun fada ka ko an fadakar da mu insha Allahu ta'ala zamu gyara. Allah madaukakin sarki ya taimaka dan haka kaji wannan tsari na farko tsari na biyu duk abinda aka karantar za'a ringa fassarawa ana ainihin yin bayanai gamsassu kafin a wuce zuwa ga karatu na gaba. Ma'ana idan aka karanta wa yara Yara suka iya wannan sai ya zama wannan shine karatun su na yau eh to zuwa gobe an kara sa musu wannan sura ko jibi eh sun iya ta eh to baza'a tsallake a tafi sura ta gaba ba. Har sai an zauna an basu ma'anar ta a takaitace idan yara ne. Idan manya ne ku sai anyi musu tafsirin ta tafsiri gamsashen tafsiri tafsirin da in Allah ya so za'a iya daukar mako guda ko makamantan haka ana ci gaba da ainihin karantar da su wasu ilmomi na tajwidin dake cikin ta kuma a nemi musu tafsirin ta. Dan haka ga wadanda suke manya ne akwai tafsiri wanda zamu karrara musu a bangaren usul al-tafsir. Tafsir ne na cikin wannan makaranta na Dar ibn Kathirin wadda ainihin za'a ringa musu a abinda aka karantar da su shi za'a ringa musu tafsirin shi. Sannan daga cikin ka'idojin karantarwa da zamu bi akwai amfani da fasahar zamani wajen karantarwa zamu ringa amfani da computer da projector da kuma allo na bango irin wanda ake harba abinda ke cikin projector ko computer domin ya taimaka wa dalibai insha Allahu ta'ala. Kamar yadda in tafiya tayi tafiya akwai yanayin da zai kai daliban za'a ringa shigar dasu wasu azuzuwa wanda ko wane dalibi zai zauna a gaban shi akwai computer wadda za'a ringa nuna mishi aya ko harafi ko kalma ko surar da ake kokarin ya hadda ce. Computer kuma za'a ringa tana
[Segment 2/6 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
wato ta ne na nuna mishi ainihin hoton wurin da ake so ya yi. Wannan program ne wanda ainihin uwar makarantar wato mai suna ta tattalu waɗannan abubuwa tsawon shekaru na kafa makarantar. Wannan na daga cikin irin software wato na ururin computer wanda ainihin aka tattala gashi Gashi Wannan na daga cikin abubuwan da ke cikin wannan CD. Ma'ana hanya ce ta karantar da al qur'ani da tajwidi a zamanance ta cikkaken al qur'ani wadda zata nuna ainihin wato hoton al qur'ani baki daya akan computer shine kuma in aka harba akan projector zai nuna a bangon allo ka ga al qur'ani din dara dara ainihin a gaban ka da kuma irin wannan rubutun din wanda mukai bayani a baya. Sannan da jarabawa da za a ringa yi wa yara yaro yana zaune sai yaji computer shi tana ko kuma tana tana kara tana nufin cewa ya karanta kenan in yazo yana karantawa abunda ya karanta ba daidai ba sai yaji ainihin wato computer tana ce mishi kuskure ne kuskure ne gyara gyara dawo da baya dawo da baya misali. Sannan zai ringa ganin ka'idoji da hukunce hukuncen tajwidi da kuma ainihin rubutu waɗanda zasu ainihin wato haskaka akan abubuwa. Wannan program ne musamman aka yi shi dan manya. Sannan akwai kuma na yara. Wannan na yara shi kuma gashi Gashi nan shi kuma zai ringa nuna hoton yaro ne ba dan komai ba domin abun ya ya dauku ka ga yaron saboda yaro dan hoto ne. Duk abunda ke cikin can yana cikin ainihin wato nan sai dai akwai karin bayanai irin kamar abunda ya shafi duk wani abu da ake nema dangane da tarbiyyar yaro to wannan program din gashi makarantar ita take da shi mallaka da ainihin wato karantarwa in sha Allahu ta'ala a karkashin haka ne makarantar ta ta daru ibnu kathirin zata bi waɗannan tsare tsare in sha Allahu. Don haka zamu yi amfani da fasahar zamani wajen wannan karantarwa in Allah yaso. Kamar yadda muka fadi dangane da su kuma manya din akwai littattafai na tafsiri da sauran su in sha Allahu ta'ala. Duk baki daya waɗannan suna daga cikin tsare tsaren da zamu bi. Malamar da zasu karantar a wannan makaranta mun shugabantar da malam Musa Sahabi shine ainihin shugaban wannan sashi na daru ibnu kathirin. Ni ina gabatarwa ne a yanzu idan al'amari ya tafi shine zai rike duk wata ragama in sha Allahu ta'ala. Daga cikin aikin da zai yi shine akwai shugabancin makarantar ma'ana zai zama shine Ina fatan an gane shine zai zama mai kula da ainihin makarantar zai zama mai karantarwa a cikin makarantar da kuma wasu tsare tsare waɗanda malaman makarantar zasu hada gwiwa tare da shi in sha Allahu ta'ala. Ni kuma zan ringa tattara su lokaci zuwa lokaci in nai musu kwasakwasai na daura. Daga cikin waɗannan irin kwasakwasai akwai karantar da su sababbin hanyoyi da fasahohi na ainihin wato karantar da al qur'ani da haddatar da shi da makamantan haka. Ma'ana ba za a basu su yi sanyi ba sabanin yadda su da dama za a gama karantun bayan an kafa su sun taso da nishadi amma in tafiya tai tafiya sai ka ga ɗaliban sun yi sanyin jiki ɗaliban ma sun yi sanyi in sha Allahu ta'ala. Zamu ringa samar musu da kwasakwasai na karfafa gwiwa waɗanda zasu karfafa musu in sha Allahu ta'ala wajen wannan aiki. A karkashin haka su kansu malaman kenan zasu zama koyi ka koyar ana kara ɗura musu ilimi da fasaha da kuma hanyar karantarwa da kuma bayanai dangane da abubuwan da zasu shafi waɗannan ilmomi na ainihin al qur'ani. Ni din zanyi haka ne ta samun ainihin wato taimakon abubuwan da malaman mu suka karantar da mu a baya da kuma abubuwan da malamai suka cigaba da rubutawa daga ciki akwai littafin na malam ainihin Abu Zari A wannan littafi yana daya daga cikin littattafan da zasu taimaka mana in sha Allahu ta'ala. Sannan sai na ainihin wanda sai kuma buzaye na kasar Mauritania suna da wata hanya wadda ainihin suke karantar da hadda al qur'ani. Waɗannan buzaye na kasar Mauritania mai yawa Hausa basu sani ba su suka fara zuwa suka kawo mana makarantar allo a wannan ainihin kasar tamu. To in sha Allahu ta'ala zamu yi amfani da wannan littafi wanda Ibrahim ibn Abul Hasani Ash Shankiti ya rubuta shi gashi matakai na hanya wadda take za a haddace qur'ani hadda mai kwari da kuma hadda bayani dangane da tsarin yadda mai hadda al qur'ani ya kamata ya ringa cin abinci da yadda zai samu ya ainihin yi abunda ya dace. Sannan na wanda ainihin wato wani babban malami dake ya ainihin rubuta shi wanda ta ainihin buga wannan littafi gashi. Sannan muna muna karantar da su muna tsawatar da su game da abubuwan da ainihin wato basu dace da shari'ar musulunci ba a bisa haskakawar littafin na malam Bakar Abdullahi Abu Zaidin Allah madaukakin sarki ya gafarta musu. To littattafai ne dai ga sunan makaranta tana da su wanda in an karantar da ɗalibai sai kuma a nuna musu ga irin littattafan da zasu samu dan su taimaka musu su habaka wannan ilmi. Shi yasa ɗaliban da zasu shiga wannan makaranta to babu shakka akwai aiki mai girma akan su kwarai da gaske. Domin kamar yadda mukai ta fadi a lokacin da muke bayanan gabatar da daukar ɗalibai muna cewa waɗan nan abubuwa ne waɗanda babu shakka sai in ka shirya ka sadaukar da lokaci. Kamar yadda nace duk abunda ake bukatar za a karantar a makarantar makarantar tana da tarin littattafai a fagen wanda in aka bada asamin mai yiwuwa karfe biyu na rana aka tashi zaka zauna a makarantar kuma domin yin asamin din don gobe zaka zo da shi karfe tara na safe. Ka ga dole ka zauna a makarantar ko kuma kaje ka dawo domin kazo ga littattafai nan ka zauna kayi wannan asamin din. Ba za a yadda wani yayi wa wani asamin ba ba za a yadda wani yayi asamin wani ya copy ba. Dan littattafai ne a kowane abu daya da za a bada asamin in Allah yaso ana fatan makarantar tana da littafin da bazai gaza guda goma ba wanda zaka iya samu. To dama manufa asamin ba kopowa bane zaka je ka karanto ne a wani wuri abunda ka fahimta kazo ka tace ka rubuta. Shi yasa bai kamata har abada asamin din wane yayi iri daya da na wane ba. Daga cikin ire iren waɗannan littattafai ka ga dangane da abunda ya shafi ka'idoji na tilawa ga littafin makarantar tana da shi na ainihin wato wanda ainihin yayi mishi ainihin wato Wannan littafin yana daga cikin littattafan da zasu taimaka wajen sanin hukunce hukuncen tilawa. Akwai banbanci tsakanin tilawa da kuma tajwidi. Yanzu ba ka'idojin tajwidi ake magana ba a a ka zauna kana tilawa al qur'ani da Hausa ake cewa takara ko kana tilawar kanai da ka ko kanai da littafi to akwai ka'idoji da lalladubba waɗanda suka dace da sunna ba irin wannan wanda zaka ga yan ainihin wato ga sakaratun al qur'ani suzo su ne rangaji wani yana sa ainihin wato hannun shi a kuncin shi kamar dan anace zai fara waka. To ba ire iren waɗannan ba duk za a karantar da kai abubuwa in sha Allah. Sannan muna da littafin hukunce hukuncen da suka shafi al qur'ani mai girma. Ina hukuncin ka dauki wani littafi ka ɗora akan al qur'ani ina hukuncin shi al qur'ani in ka tashi ka kwantar da shi akan madadin ya zama ita take kasa suratul bakara ita take sama to sai ka kwantar da shi sai ta zama ita ce take sama suratul bakara ta zama tana kasa ko wani ainihin abu makamancin haka. Saboda haka in sha Allahu ta'ala abun duk da ya shafi waɗannan irin al'amuran ga sunan a cikin wannan littafin. Haka abunda ya shafi gashi malam ya rubuta ainihin wannan littafi Allah ya gafarta mishi. Ire iren waɗannan littattafai duk baki ɗayan su ga su muna da su. Sannan sai dangane da tajwidin ga ire iren waɗan nan littattafai duk ana da su. Sannan sanin ina ne harafi kaza ke fita in ya fita yaya sautin shi yake ya kara shi take duk gashi nan. Sannan abubuwan da zasu biyo baya na tsawatarwa dangane da ka fara karatun al qur'ani ka bari ko kuma tun farko kai dan tawaye ne ba ruwan ka ma da qur'ani tun da kake baka daukan qur'ani kana karantawa baka koyan karatun al qur'ani. Doktor gashi duk waɗan nan suna daga cikin littattafan da ɗalibai zasu mu'amalanta. Sannan Gashi sunayen surorin al qur'ani yaya ake surorin al qur'ani suke samun ainihin wato abunda ya shafi sunaye. Wannan littafin yana daya daga cikin littattafan farko da aka rubuta wanda malaman salaf suka rubuta dangane da sanin ka'idojin inda ake tsayawa da inda kuma ba a tsayawa a cikin ainihin al qur'ani. To akwai ɗimbin ire iren waɗan nan littattafai nan kowane fage na zaro guda daya ne a matsayin misali. Kusan ma da yawancin wasu fagagen ban dauko littafi ko daya a cikin su ba. Gashi wanda aka fi sani da Wannan littafi ne wanda yake dauko wasu matsaloli na tafsiri ko wasu kalmomi da zasu iya jawo maka ka kasa fahimta kyakyawa dangane da abunda ya shafi wasu ayoyi na al qur'ani. Ire iren waɗan nan littattafai har zuwa ga duk baki daya suna daga cikin ainihin littattafan da makaranta ta tattala. Duk ɗalibin da yake so zai shiga wannan makarantar to gaskiya idan yayi daidai da lokacin wata makaranta da yake to sai dai ya zaba ba zamu yadda da ya zaba wasu kwanaki yazo wasu kwanaki kuma yayi zaman shi ba. A tsari dole ne dukkanin ainihin wato ranakun karatun mu da dukkanin lokutan karatu ɗalibi zai zo. Idan ɗalibi ya fara makarantar mu babu maganar sai dai ya kori kansu. Don haka duk wanda zai shiga makarantar ya tsaya yayi tunanin nan da shekara hudu mai zuwa to ba fa dalilin da zai sa kuma yace zai ainihin wato daina karatun nan Allahu ma sai dai in shine da kansu bashi da lafiya ko kuma in shine da kansu Allah ya dauki ran shi. Amma gaskiya saboda Allah so muke ayi maganin wata matsala babba wadda take fama a cikin musulmi musamman ahlus sunna ta karancin mahaddata al qur'ani da kuma sakaci da lalaci da lalata da take neman ta shigo wannan fagen. Da kuma wata bidi'a wadda ita ma take neman ta yadu cikin ahlus sunna shine idan wani kwaya daya ko kwaya biyu ya haddace al qur'ani sai kuma yaje ta cika gari da doro da wuraren tarin rika da hayaniya ai ya hadda hadda ai ya hadda hadda har haddar ta watse bai sani ba yana can yana hayaniya har haddar ta rikice bai tsaya ya koyi ilimin tafsirin al qur'ani da sauran su ba. Saboda haka duk wanda zai shiga to gaskiya ya tsaya yayi nazari ba zuwa zaka yi kwana biyu kazo kace mana gaskiya wani uzuri ya taso maka ba. Zaka tafi kauyen ku saboda gonakin ku na gado zaku tsaya zaku kula da su ko zaka yi makamancin haka wannan bazai zama mana uzuri ba don haka tun farko in kasan cewa a gidan ku kai ne babba ko wani abu makamancin haka wanda in al'amari ya taso za a sa ka koma gida don ka rike gida to gaskiya wannan makarantar sai ka hakura. Kamar yadda kasan duk wanda ya tashi shiga A biyu zai karanta economics ko business admin ko engineering ko law ko pharmacy sai ya tabbatar da cewa zai gama shekarun nan hudu ko biyar ko kuma duk uzurin da ya taso mishi hakura ake da uzurin ko to gaskiya mu ma nan sai dai haka. Amma in har ka matsa to shikenan sai a ce to shikenan yanzu kai ka kori kanka daga makarantar kenan baka da certificate ko kwaya daya babu wani tsari da za a canza akan wannan. So da haka duk wanda ya san cewa bayan kwana biyu zai ji talauci ya dame shi ko kuma wata damuwa ta dame shi to bai cancanta ya shiga ba kenan. A nan ne zance abunda suka ce ya tabbata a cikin wannan ainihin makarantar. Ah mai bayani yace ba zaka samu ilimi ba sai da abubuwa guda shida. Sai kana da basira sai kana da kwadayin abun sai kana da juriya Ina fatan an gane sai kana da kudi guzuri tsawon zamani a samu gogaggun malamai. Don haka duk wanda yake son ya shiga wannan makarantar yaje ya tattalu kudin makaranta da zai biya. Mu a wannan makarantar bama bada scholarship kyauta bama karantarwa sai mutum yana biyan abunda aka sa. So da haka ba makaranta ce ta kyauta ba ba kuma makaranta ce ta kungiya kaza a cikin Najeriya ko a cikin kasar waje ba. Kamar yadda ba makaranta ce a karkashin gwamnatin Najeriya ko a karkashin gwamnatin jiha ko kamar yadda kasan cewa in ka tashi shiga jami'ar Ahmadu Bello sai ka tattali kudi in ma baka da su kafin registration zaka je ka nemo ko. To haka tare da cewa jami'ar Ahmadu Bello fa jami'a ce ta mai ta gwamnati amma dan abunda suka sa din nan a shekara in baka bayar ba zaka nuna cewa kai Basakkwace ne dangin Sardauna ne ko kai dan Arewa ne kana kishin Arewa eh to haka mu ma nan indai har baka da kudin makaranta da aka sa to muna maka fatan Allah madaukakin sarki ya yassare maka. A wannan ne zanyi kira zuwa ga waɗanda suke da hali su kuma suyi wa kansu ta hanyar taimaka wa ɗaliban da kudin makaranta. Kamar yadda ake samun wasu yan boko lauyoyi da injiniyoyi suke ware kudi duk wanda suka ji zai tafi karatu suke biya mishi. Ina bada shawara ga bayin Allah waɗanda suke da ainihin son alkhairi suyi kokarin daukar nauyin wasu ɗalibai. Sai dai kuma su sani in sunyi haka ba fa suyi wa Albani ba abun bazai kare ni da komai bane Albani bazai kare makarantar ta da komai ba. Kai zai kara sai wanda ka taimaka wa. Abunda yasa na fada haka don kada wani yaje yace Albani yace muzo wurin ku neman taimakon kudin makaranta a a baka taba ambatar kace shine ya turo mu wurin ka ranka ya dade saboda mu biya kudin makaranta ba zuwa kake ranka ya dade nazo ne a taimake ni da zan biya kudin makaranta kana ina ne sai kace kana Haka babu laifi zaka iya zuwa ranka ya dade nazo ne ka taimaka mini kudin makaranta wanda zan shiga ta a ina sai kace sunan
[Segment 3/6 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
amma karka ce makarantar albani ba makarantar albani bace domin saka albani a cikin abin to corruption ne rashin gaskiya ce wanda kake neman kayi shi zai je yana alfaharin yana turo dalibai makarantar albani dan haka yana taimakon albani shi kuma albani yana da galatsin magana wanda wataran zai iya fada uban kowa magana a duniyar nan yace bai rage kowa ba to sai yaji to shi yana tawa albani kokari a'a ba shegen da ya taba biyawa albani kudin makaranta duk duniya in ba uwar albani dincen da kaji an fadi ba sai uban albani duk duniya da lahira ma'ana har wadanda suka mutu dan haka albani ko gwamnatin tarayyar Najeriya bata biya mishi school fees ba makarantar kudi yayi har zuwa sanda yayi karatun shi gabadaya a karkashin wannan babu wanda zai ce a yanzu da albani ya zama ya kafa da'awa yace yana da minna akai babu minna tana ga Allah tana ga manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wasallama sannan sai uwar albani da uban albani sannan sai malaman da suka karantar da albani amma wani mai mulki ko wani mai kudi ko wani attajirin birni yace sune kaza kace albani yace alhaji karya kakeyi iyakarta kenan to kunga ina son ne mu tsaya mu tsara abinda yake gaskiya da gaskiya ne bana son muyi abinda yake daga baya za'azo ana cewa bai kyauta mana ba makarantar mu bata neman taimako a wurin kowa sai a wurin Allah amma kai a matsayin ka na dalibi da ka taho daga Katsina ko birnin Kebbi ko ta taho daga Gombe ko Bauchi zakayi karatu a nan zaka iya zuwa wurin wani ya taimake ka amma ba da yawun mu ba ba kuma da sunan mu ba kamar yadda in kazo zaka shiga Nuhu Bamalli Polytechnic dake Zaria kana zuwa kana ainihin neman taimako a wurin wanda zai taimaka maka ne ba da sunan cewa Rektar din shine ya turo ka ba kuma ba tare da ka fadi sunan Rektar din ba to haka itama wannan makarantar makaranta ba sunan ta makarantar albani ba a'a sunan makaranta in anaso a fadi sunan ta da Hausa sai ace makarantar in aka ce wane sai ace wanda ya rasu shekara kaza bayan hijira 125 da ta wuce ko 120 da ta wuce wato da hijira kusan yanzu shekara 1000 da 311 kenan da rasuwa ko kuma wanda ya rasu kamar shekaru kusan 700 da suka gaba ta sai kace wannan makaranta sunan makarantar kenan makaranta kuma ce kuma ba wanda ya mallake ta itace ta mallaki makarantar jama'ar musulmi wadannan ainihin sune bayanai na zan sassauta a nan in dan saurara saboda mu bude kofar tambayoyi ga wadanda zasu gabatar da tambayoyi musamman ainihin a fatar baki amma dai daukar dalibai yana nan yana ci gaba a kashin gaskiya saboda Allah a han abinda muka so shine asalatan abinda muka so shine ace zuwa yanzu an gama daukar dalibai zuwa yanzu an gama daukar dalibai yau dinnan a fara karatu da zaran an fita daga nan to sai dai daliban da aka dauka kaf din su basu wuce guda 20 ba su kuma guda 20 dinnan basu wuce kwarara guda biyar ba zuwa guda bakwai wadanda sune aka tabbatar da cewa sun tabbata cewa zasu yi karatun an samu wani bawan Allah da ya aiko cewa zai dauki nauyin wasu dalibai wadanda zasu bada suna yanzu to wannan labarin sai ya yadu sai kowa yayi ta kawo sunan shi da sunan yayan shi da tunanin wannan bawan Allah zai dauki nauyin mutane da yawa ne wannan bawan Allah ya aiko da kudin mutane biyu ne kadai kuma an bashi takarda ta sunayen dalibai guda 20 a lokacin da hannun shi yasa biro ya zabi guda biyu wadanda bai san su ba basu san shi ba yar manuniya yace kawai ta nuna kowa ta duba ko din mata ina fatan an gane sunan ya fada akan mutum daya namiji da kuma mace daya ya biya musu kudin makaranta dan haka wadanda suka bayar da sunan su da tunanin cewa akwai wani wanda zai biya to gaskiya ya riga ya biyawa mutane biyu sauran muna jiran su suzo su biya kudin makaranta in ba haka ba zamu ainihin cire sunayen su dan musan wadanda dalibai ne suka biya kudin makaranta kuma da wadanne ne za'a fara dan haka idan mun samu adadin dalibai da ake so daga nan zuwa kwana bakwai za'a fara in ba haka ba zamu jinkirta amma dai bazamu wuce karshen wannan ainihin wata na Zul Qa'ada ko kuma karshen wannan wata na October ba insha Allahu ta'ala kenan koda dalibai bakwai din ne to sai dai duk ranar da muka fara to koda rana ta biyu ce wani yazo register kuma sai dai badi dan an riga an wuce shi saboda haka dalibai dake nesa wadanda ba a Zaria suke ba za'a iya ainihin sanar da su domin su taho idan suna bukata sai kazo Zaria sai ka kama daki ko ka kama gida kai da matar ka ko makamantan haka matan aure matan aure ma zasu iya shiga wannan makaranta amma sharadin shiga wannan makaranta ga matan aure shine mijin ta ne zai zo da ita kuma ya tabbatar da cewa zata iya kuma ya tabbatar da cewa zai bata goyon baya da daurin gindin da zata ainihin tsayu domin wannan karatu domin dai kunji za'a tashi karatun karfe biyu idan an tashi karfe biyun nan abinda zai biyo baya tayi akwai assignment wanda bazai iya yiwuwa yayi a gida ba shi dalibin ko dalibar to kaga dole ne yasan haka tayi wata rana sai karfe hudu matar shi zata dawo in ta dawo kuma tana shirye shiryen ta huta tayi wanka tana shiryawa ana sallama garba sai ya ga ta zari Qur'ani kuma ta fara tilawa saboda zata bada ayoyi 10 da safe wadanda ainihin aka bata jiya kenan ga mutumin da zai sanya matar shi a zahiri to sai dai ya daukar mata yar aiki wanda zata rinka kula da yara da girke girke da shara amma a kashin gaskiya indai mace ce wadda uwar gida uwar gida ta gaske to bazata iya tafiya tare da wannan aiki na hadda na makarantar Ibn Kathir ba ina fatan an gane wannan itace gaskiya wasu mutane suna kokarin su ciro yayan su daga makarantun secondary domin su kawo su nan mu bamu goyi bayan haka ba abinda make goyon baya ka bar dan ka ya kammala a kalla makarantar secondary sa'annan sai ka kawo shi wato in aka ce za'a fara a bukar ka daukar wa kan ka mutuwa da rai ka dauka cewa bana tunda baka da dan da ya dace Allah ya kaimu badi badi in akwai sai ka in babu sai Allah ya kaimu badi waccen mai zuwa sai ka biya a hankali in ba haka ba in ya zama ba ra'ayin dan ka bane kaine kake da wannan ra'ayin to akuya ce fa kana iya kaita wurin shan ruwa amma baka isa ka tursasa ta ba ta shan ruwan dan haka ka raba shi da chan secondary da yake ka kawo shi nan ayi juyin duniya ya kiyin karatun me zai biyo baya karshe za'ayi biyu babu dan haka bashi ya kammala chan wannan shine babban abinda make ta nunawa jama'a ayi dangane da makarantar ta tahfiz din ta yara saka wa yayan musulmi sha'awa da son karatu da hadda Qur'ani tun suna yara in ba haka ba babu yaron da dan ya girma ance mishi ya shiga makaranta hadda Qur'ani zai kiya mata ko kuma zai ga cewa shi yaya kaza kaza amma in bai samo tarbiyyar yana karami ba za'a ga bashi da nishadi akan abun bashi da karsashi akan abun baya sha'awar abun amma da za'a buga wani music fa sai kaga jikin shi ya ya watsake yaji dadi saboda wannan yake da tarbiyya akai Allah madaukakin sarki ya kiyaye wadannan sune ainihin wato bayanai dangane da abinda ya shafi wannan makaranta daga cikin tambayoyi da ainihin aka rubuto ga su wannan yana ji wa ance ainihin wato bude taro da addu'a bidi'a ne haka rufewa indai addu'a ce jama'iyyan ina fatan an gane sai dai shikenan sai kowa ya kama gaban shi ina fatan an gane duk bidiyo indai duk addu'o'in da zakuyi sai kuyi su kafin wannan lokacin da anzo kawai shikenan Allah ya taimaka dan inyi tanbihi jama'a wannan abinda shima malam Muhammad Awal mai shago ya fara dashi wajen gabatar wan bidi'a ne fara jawabi da kunsan wannan ya zama al'ada a wurin malamai ba sunna bane jama'a mutum yazo zai fara bayani ya fara da Qur'ani ne aka ce haka ah in za'a karanta Qur'ani ne in ba haka ba ba inda aka ce ka ce ina fatan an gane so ba ba sunna bane galibi zaga yan siyasa ne dama suka sunnan ta a mutane wannan ka taba sai yace to ta eh to ai ba'a ce kayi ba tunda ibada ce sai inda aka ce kayi amma budewa da bismillah shine abinda yake sunna insha Allahu ta'ala na'am na'am ko anyi me a'a nayi maganan ne kafin kazo eh nayi maganan ne tun kafin a fara karatu wannan yana cewa wai yara masu suna Ja'afar dinnan za'a iya kawo su baza'a iya kawo su ba saboda duk yaron da karshe zai zo ya shiga wannan makarantar babu fa'ida kuma ka saka sha'awa ta makaranta ai duk wadannan abubuwan da kaji ana maganan makarantu ne wadanda basu samu daman shiga tsarin wanda yayi makaranta ne amma wanda ya zama yaro ne za'a kawo shi ko an riga an saka shi a nan mun riga mun tsara da wanda in Allah madaukakin sarki yaso babu sauran bukatan ka kai dan ka makarantar boko ka kai shi makarantar ka kai shi makarantar ka kai shi makarantar ka kai shi makarantar wadannan abubuwan sun yawa shi yasa karshe sai ya tubure ko kuma ya rinja ya ga abu daya makaranta daya itace aka tsara zata karantar da wadannan abubuwa Allah madaukakin sarki ya taimaka wannan amsar mun amsa ta da wani yake cewa shin yaushe za'a sake daukan dalibai duk shekara zamu dauki dalibai mun fadi komai da komai bawai sai an yaye wadannan ba Allah madaukakin sarki ya taimaka na'am na'am mene babu babu in an gama karatun Qur'ani an gama kawai sai kayi tafiyar ka ka ci gaba da harkan da kake yi babu da ake fadi dama bidi'a ce ba wani abu babu kawai an gama karatun Qur'ani shikenan kawai ina fatan an gane na'am na'am babu matsala amma abu mai muhimmanci shine a inda aka sa din a sa dan a saurare amma inda karatun ya kai ai kuma nan ba za'a iya mallakar wancan wurin ba so da haka in an sa kira a masallaci dan ta kai wani wuri wanda shi wurin da hayaniya babu matsala amma abinda ake cewa inda aka sa din wuri ne wanda yake da natsuwar da masu wannan wurin zasu iya saurare sauraran zai iya yiwuwa ta dayan hanya biyu ko dai ka zauna dafa'an domin saurare ko kuma mace ce a kitchen tana girki sai ta ainihin samo wani radio ko wani cassette ko wani MP3 ko wani technology sai ta sa tana aikin ta tana saurare amma ba inda ake hayaniya ba kamar yadda zaka ga ustazu yazo inda ake hayaniya shi kuma ya zauna ya ya sanya MP3 din shi su suna hayaniya shi kuma nan yasa karatun Qur'ani ba irin wannan ake magana ba Allah ya taimaka wa'alaikumussalam na'am na'am na'am a'a an basu ne yaya da su zasu koyi karatu an basu ne ai an basu ne a'a ai dama wakafin ana duban sharadi ne meye mai wakafin ya sharadan ta kawai haka ake yi na'am wa'alaikumussalam na'am na'am na'am a'a ai shine dama in baku manta ba makarantar nan muka ce ta manya da ta yara ta manya itace naira 50 itace full time ta yara kuma itace naira 1000 daya a wata itace naira 120 a shekara kenan so ita ta manyan daban ta yaran daban mun fadi tsare tsaren ko na'am wa'alaikumussalam kawai ran da adadin dalibai ya cika gare mu ai mu abinda muka so zuwa yanzu ace an gama daukan daliban ina fatan an gane abinda muka so kenan zuwa yanzu ace an gama daukar daliban dan haka da yanzu in muka fita dinnan kamar 12 ko 11 kawai shikenan za'a ce su shiga aji ne a ci gaba da raba musu Qur'ani a ci gaba da raba musu littattafai shikenan sai a ci gaba da darussa mu mun riga mun gama shiryawa amma daliban ne adadin da ake bukatan basu zo ba to shine muke ganin mun dan jinkirta nan da mako guda daliban da zaran sun gama haduwa insha Allahu ta'ala shikenan kuma in muka ga lokaci zai kure kawai za'azo a fara to in aka fara ne kuma sai badi za'a ci gaba da daukar dalibai daga karshe shawaran da nake bayarwa kamar yadda dalibai yan boko dake shiga Polytechnic da FCI da ABU sukan yi kokarin tattala kudin ustazai suma su rinka sabawa da wannan domin asalin abinda ya tare ustazai daga shigowa nan shine matsalar kudin makarantar to amma in ka duba yanzu su yan boko da yan gayu da nigogi eh abinda ke hana su shiga ABU shine cin jarabawar ma'ana su jarabawar ce take da wahalar shiga amma tunda dama yana son karatu yasan dole ya tattali kudi to su ustazai zama suke yi gaskiya basa neman kudin basa kuma tattalin sababbin su to dan haka duk abinda yazo tunani suke yi zai zama gaskiya a makarantar babu wani abu wanda aka ware da ake kira amma fa ita kanta amma a wurin Bahaushe to babu wannan a duk abinda ka gani a ko duk abinda kaji ance za'ayi to za'a sa kudi ne da ya dace ayi shi a bisa yadda ya dace saboda haka ita kanta kuma kuma amma ba irin ta Bahaushe ba dan shi Bahaushe abinda yake gani duk abinda aka ce to kyauta kenan to da haka ne galibi aka rusa muku addini dan haka ne galibi aka haifar muku da rudani saboda wasu kungiyoyi a cikin gida Najeriya da wasu kungiyoyi a kasashen waje na addini wadanda zasu zo su gina muku masallaci ko makaranta kyauta sai su haddasa muku da fitina tsakanin ku da jama'ar ku ko kuma ku da wasu al'umma gabadaya saboda haka ita gaskiya makaranta ce mai cin gashin kanta ba a gina ta da kudin sadakar kowa ba daga waje ko daga ciki ba a gina ta da kudin taimakon kowa ba daga cikin gida Najeriya ko daga kasar waje makaranta ce da ita da kanta ne ta gina kanta da kanta kuma ita da kanta ne take tsara saboda haka abubuwan da tsawon shekaru kaji muna cewa za'ayi kaza za'ayi kaza za'ayi kaza ana nufin ne kai kuma kaje ka dage da neman kudi ba kawai ka tattali kabbara ka cika bakin ka da ita ba in ance za'ayi kaza kace in aka ce to amma kaza dubu kaza sai kuma kace ai kai ka dauka da ai ya kayi kuskure da za'a kafa bayan wannan a cikin itace wadda in Allah yaso ba da jimawa ba za'a zo za'ayi magana dangane da yadda wannan cibiya ta zata kasance za'a rinka wanene wanene wanene itama din dai ba bace wato in nace ba a bisa harshen mutane ba kyauta bace amma in ba haka ba don abinda mu muka dauka abinda aka yi shi saboda Allah kuma to mun gina ne saboda Allah kuma aka gina ta wannan baya hana kuma a karbi wani abu kaga ai aikin hajji da kake zuwa kake a Makkah kana biyan kudi fa kai baka sani ba gani kake kudin
[Segment 4/6 | 01:00:00–01:20:00]
[Speaker seg4-spk:0]
ne kawai kake biya. Hatta wannan wanke ka'aban da ake da kudin ka ake yi. Hatta wannan ruwa da kake zuwa ka samu mai dimi a Arafat da Mina da Muzdalifa kana wanka a cikin kudin ka ne. Eh so duk abun da ake a cikin kudin ka ne ake yi. Soboda haka kaga da ace gwamnati zata ce maka naira dubu dari biyar ne kudin aikin hajji bana sai a baka din. Sai kaga ga kudin gida ga kudin mota ga kudin jirgi ga kudin kaza ga kudin kaza ga na abinci. To sauran kuma fa sai kaji ance maka sauran hidindimu sune sallar da kake zuwa ka'aba da ruwan alolan da kake amfani da tabarmi da ake shimfida maka da duk wadannan abubuwan. Eh baka ganin visa cewa ake visa zuwa kasar Saudi Arabia kyauta ne haka suke rubutawa. Amma kaje kaga nawa ake biya har dubu dari biyu biya ake yi. Amma kaga ba wanda ya taba cewa to ashe bane ma. To soboda haka muma tun farko bazamu zo mu cewa mutane kyauta ba dan mutane su shiga gari suna yaban mu ba. In ma sun yabe mu ma ba dadi zamu ji ba ban mu bamuyi dan a yabe mu ba. Balle in ma ance kyauta din kuma mutane kuma zasu ce to kyauta eh yaya kuma kyauta ma'ana duk abun da aka fadi sai sun fadi Soboda haka duk abun da kaji a bashi da banbanci da wata makaranta da kake ji a wajen mai yiwuwa ma na ba dan komai ba saboda mai yiwuwa ita waccen makarantar ta gwamnati ce. Mai yiwuwa wani dan siyasa ne ko wani sarki ya gina yake son ya gabatarwa da jama'a aikin alheri. To sai kaga irin abun da za'a karanta a a dubu hamsin ga irin shi can ana karantarwa a dari bakwai a wani wurin. So karka matsa wa kanka sai ka shiga sai kaje ka shiga ta dari bakwai din ko kuma ka shiga waccen din wanda ake kira wanda babu ko kwabo a ciki. Ina fatan an gane. Amma dai mu abun da muke cewa a sune abubuwan da muka fadi a farko. Makaranta ce aka tsara ta zata karantar da al'qur'ani da sunna a bisa fahimtar malaman farko. Malaman farko daga cikin sahabbai da tabi'ai da kuma mai gidan su annabi Kasantuwar a wadannan zamunna malaman da suke karantar da al'qur'ani ba'a samu gwamnati irin gwamnatin Umar ta rike su tana basu Malamai ne wadanda suke masu zaman kan su itama makaranta mai zaman kan ta ce. To wannan shi yasa sai musa kudi da yawa dan a biya malaman. Amma a zamanin sahabbai zaka samu shi yasa har fatawoyi aka ringa yi akan ya halatta ma a biya kudi wajen karantar da qur'ani ko bai halatta ba. Abun da ya ja shine duk wani malami kaf a zamanin Sayyidina Umar yasa mishi ana biyan shi haka siddan ba dan yana aikin komai ba. Sai dan shi malami ne sai dan shi sahabi ne sai dan shi muhajiri ne ko ansar. Duk wata sai ace mishi zo ka karbi naira dubu dari biyar. To randa wannan gwamnatin da take mai haka in tace dan Allah akwai wasu yara a can gefen tudun jukun aje a karantar da su qur'ani wannan malamin yana sa rai kuma gwamnatin tace mishi ga wani albashi daban. Ko kun fahimta jama'a soboda haka malamai idan zasu ringa fatawoyi sai su ringa suna lura da yaya asalin abu yake dan karka rabu da asalin. A zamanin Sayyidina Umar ba'a biyan malamai kudi. In ka karanta ya halatta a biya ko bai halatta ba wannan yace kaza wannan yace kaza wani yace haramun ne wani kuma yace shine abun ma da yafi cancanta a biya. To duk asalin abun da ya kawo wannan shine hakikanin maganar da na fadi. Gwamnati ce a zamanin Umar aka tsara duk wani malami ana biyan shi Ba fa dan yana yin aikin komai ba kawai kawai sai kazo in kace kai muhajiri ne aka tabbatar kai muhajiri ne ko ansari sahabi ne sai ace a rubuta sunan shi. Duk wata sai a dubi abun da yafi karfin cin ka na wata uku sai a baka a wata daya. To kaga wannan gwamnatin idan tasa ka aiki tana bukatan ta biya ka wani albashi na musamman akan wannan aikin. To mu a tun daga ni kaina har malaman kaf da zasu karantar babu wata gwamnati wadda ta taba biyan mu albashi ko Ko a Najeriya ko a waje babu babu wata karamar hukuma babu wani alhajin birni babu wani haka. Soboda haka mun kashe lokacin mu zamuyi zaman wannan aiki. To bazamu yadda mu ce bazamu karbi ko kwabo ba soboda jama'a suje suna taya ban mu amma kuma daga baya muzo mu kirkiro da rubutun sha guru da laya ya ladifu kafa dubu falaki da nasi maganin yan tsirku guda goma sha bakwai bakin allo allo mai kunnen fata allo mai kan zabuwa duk wadannan abun da ya ja aka kawo su a cikin malaman allo shine asali ba wata gwamnati take rike da su ba. Kuma da aka zo suna karantarwa sai basa karban ko kwabo sai ana ta musu kallon mutanen kirki. Shine sai suka bi sai suka bullo da wani ba'a sani ba. Duk kazalika da ya yanka sai ace wiya na mai yanka ne karya ne ba'a inda aka fadi haka a karatu. Amma wannan din ne ya kawo aka kirkiro wannan fatawar. Duk kazalika da malami ya yanka sai ace wiya na mai yanka ne. A ina aka fadi haka a ko a babu karya ce kawai to amma me yasa aka kirkiro wannan karyar soboda da nan ne zai samu duk kazalika da aka yanka a unguwar yana da wiya. In an so a kara mai ko ba'a kara mai ba amma dai yana da nashi Ina fatan an gane. To mu in sha Allahu ta'ala bazamu yadda mutun kudi zuwa ga haka ba musamman a wannan zamanin ne da mutane sun waye gari sun saba da biyan kudaden makarantun boko. Tare da muna cewa ba'a iya biyan na makarantun islamiya to amma mu a tsarin mu muna son duk wanda zai fara ya fara da ainihin sanin irin wannan tsarin namu. Dan haka tun farko ga wannan tsarin. Idan har Allah madaukakin sarki ya kai lokacin da zamuyi sanarwa idan kazo da danka kowane wata a farkon watan ne zaka ringa biyan kudin ba wai sai watan ya kare ka gama shan karatun banyi so ka gudu a'a kai zaka biya kudin. Soboda haka misali za'a fara wa yara karatu ma farko na watan yaran yara za'a fara musu abun nan mai yake da suna karatu a farko na watan Wato kaga kaman nan da makonni uku da rabi kenan kaman nan da kwana ashirin da bakwai din za'a fara wa yara karatu. To duk mutumin da ya kawo mana da a randa zai taho zai taho da naira dubu daya sannan zai taho da kudin dinkin uniform wanda a yanzu bamu san ko nawa zasu kasance ba. A yanka a dinka wa dan shi uniform guda biyu a bashi. Soboda haka yadda kaji kana jin jiki in zaka sanya danka eh ko sai kayi kyakkyawan shiri to nan ma ba islamiya bace kawai yadda in yamma tayi za'a tunka do shi ace ka damu mutane tafi islamiya a'a kafin ya taho din sai ainihin uwar ta tabbatar tayi aiki sai tayi mai wanka sai ta wanke mai sutura sai an goge suturar in yazo da riga ba guga zai koma. In ka dire shi ka tafi rigar shi ba guga muma sai mu dire maka shi a nan har kazo ka dauke shi saboda rigar shi ba'a goge ta ba saboda hular shi tayi datti ko kuma tayi irin fashe wannan ta rube a can sama irin na almajirai to nan ba makarantan almajirai bace. Ina fatan an gane ko kafar shi da kaushi kafar shi kazo da shi da kaushi ko kuma kazo da shi ba'a mishi wanka ba kafar shiga ta nan kaman bayan ka dangare duk in kayi haka a nan inda ka ajiye shi a nan zaka zo ka same shi sai yace an hanashi shiga. Wallahi jama'a akwai aboki na da galibin ku nan kun san shi dan Makka ne akwai randa muka je makaranta dauko yar shi karfe daya na rana sai muka same ta inda ya ajiye ta tun safe. Me yasa wata takarda ce kwa daya bata zo da ita ba. Kiri da muzu aka aka barta a nan bata shiga makarantan ba. Kuma wannan makaranta ta gwamnati ce amma saboda shi ba dan kasa bane yana biyan kudi to ya biya kudin takarda ce kwa daya babu a cikin takardun ya ajiye yarinyar ya tafi ya dawo nan ya same ta yace ya akai tace ba'a barta ta shiga ba ba'a kwai takardar da babu. Wannan a cikin garin Makka kenan garin gaba daya garin shi kanshi ne ma gaba daya ina fatan an gane soboda haka jama'a duk wanda zai sa dan shi a makarantan mu gaskiya soboda Allah zai biya naira dubu daya a wata. Amma bari in gyara mana tunani kaga wannan dubu daya da zaka biya ba ka biya kudin karatun bane. Kaga wannan dubu hamsin da zaka biya ba ka biya kudin karatun bane. Wannan shine abun da malaman suka yi tsawa ba'a iya biyan malamin da ke karantar da al'qur'ani amma kaman yadda muka ce za'a bada abubuwan dan aka hada ne za'a kyautata wa malaman. To ga kanan baka ganin kyashin kaje ka biya wa danka a ko a baka ganin kyamar duk wadannan abubuwan da zaka kai danka wurin wasu sun buda wani dan shago soboda zasu koya mai computer amma in abu ya shafi makarantan al'qur'ani kana ganin kyashi to nan makarantan to wurin gyarawa mutun zamani duk abun da kuka ji mun ce zamuyi a to ka fara tara kudi kar kayi tunanin akwai wani abu wanda za'a ce wannan abun kyauta ne. Sam ba kyauta bane komai za'a biya kudi to amma kudin da za'a biya shine tunanin da nake gyara maka karatun boko kam wannan mun yadda kace ka biya haka makarantan computer da zamu kafa nan za'a yadda kace ka biya soboda asalin makarantan computer ma da zamu sa kudaden da za'a ringa biya na kwasakwasan kiyasinsu a dollar ne domin kwasakwasan mu suna da sa ne a karkashin hukumar computer ta duniya zamu ringa fitar wa a karkashin wannan dollar ce in ta kama dollar goma sai a juya ta a kudin Najeriya sai ta zama kaza sai ace kaza ne. Dan haka zaka ji zaka ji shi dubu talatin kaza dubu arba'in kaza dubu hamsin har akwai a makarantan nan na naira dubu dari biyar ko dubu dari bakwai a cikin wata tara. In ka gama kuma tsaf an gama randa zakayi jarabawa sai ka sake siyan wanda bazai gaza dubu hamsin ba ka sake ainihin sawa akan na'urar internet sannan ka iya yin jarabawa. Ina fatan an gane wannan shine ainihin a bayani jama'a dan haka ina fatan yan uwa sunji wadannan bayanai kuma sun gamsu akan su. Allah madaukakin sarki ya taimaka. Na'am bari mu amsa tambayan ka mu gabatar da wasu baki namu guda biyu na'am. Wa'alaikumussalam warahmatullah. Na'am Babu gaskiya a zuwa yanzu ga wadanda suka haddace al'qur'ani babu wani tsari da aka yi musu sai in muna da duf'a ta farko na namu mahaddatan sune wanda mukayi bayani. Shine wanda ya haddace al'qur'ani an fahimta da kira'a daya ko riwaya daya ko makamantan haka. Shi in ka kawo shi nan to mai zai yi kuma? In kace mishi to yazo saboda sauran ilmo min madallah. Amma kuma in aka zo matsalar hadda to zai ringa jin jikin shi ya mutu ko makamancin haka sai dai dan sauran ilmo min. Idan akace bayan an yaye daliban mu shekara hudu za'a yi wancan na shekara daya in yace shi kuma zai shiga eh idan yace zai shiga to matsalar shi kuma ilmo min da aka karantar da su a baya shi kuma bai da shi. Soboda asalin matsalar da ke tattare da system din da ya biyo haddar galibi system din da ake bi ana yo hadda system ne na mai na tsabar karantar da haddar zalla ba fassara ba wasu ka'idoji babu ilmomi ire-iren wadannan. Wato bari in baku a shuarance in sha Allahu ta'ala abun da muke fata duf'ar mu ta farko ta huffaz in Allah yaso nagartar karatun su bazai gaza wanda yaje jami'ar islamiya yaje ya karatu ba in sha Allahu manhajiyya ce muka dauko kuma har mukayi kari akai in sha Allahu dan haka muke fatan shekara daya da zata biyo baya wanda wanda yaga dama zai cigaba da karatu sai a koyar da shi ainihin sauran ilmomi na kira'o'i kuma. Allah madaukakin sarki ya taimaka. Bako na farko da muke da shi Malam Isa mai aikin tashar talabijin da radio bama ce da kuma alheri radio kadai ba. Shi Malam Isa wakilin duk tashoshin radio ne da talabijin na duniya gaba daya dan in ka ganshi yanzu yana aiki a alheri radio gobe kuma zaka iya ganin shi yayi ruwaya ga BBC ko Malam Isa bismillah ka gabato. Akwai bako na biyu wakili ne shi kuma daga ainihin wato na'am eh Ahmad Muhammad Makarafi ya turo dan ya ainihin wakilce shi in sha Allahu ta'ala Malam yasa mune maka mara ba. Allah ya saka da alheri bismillah in sha Allahu. Abun dama da muka ce dangane da masu aikin jaridu da yada bayanai idan suka shigo in sha Allahu ta'ala zasu zo wannan wuri ne su saurari abubuwan da mukayi bismillah Malam bismillah Malam. Suka shigo zasu saurari abubuwan da mukayi kuma in aka tahi sai a basu a kaser in sha Allahu ta'ala assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuh Soboda haka jama'ar musulmi darul hadith da darul ibn kathirin ta gama nata gabatarwa. Zamu so yanzu Malam Abubakar ya gabato in sha Allahu ta'ala shine wakilin sanata Ahmad Muhammad Makarafi muji sakon da yake dauke da shi. Wato akwai sakonni ne da muka aika gidajen radio da jaridu da kuma text wanda ainihin aka yi ta turawa ta lambobin waya ina jin ta haka ne da dama wasu suka ainihin samu sakonni in sha Allahu. Malam Abubakar bismillah in sha Allahu ta'ala ka gabatar da kanka da kuma ainihin shi sanata da ya turo ka bismillah.
[Speaker seg4-spk:1]
Suna na Abubakar Bala Makada daga Muciya ina wakiltar sanata Dr Ahmad Muhammad Makarafi mu rabu da shi jiya yana mutukar son yazo nan wurin soboda mahimmancin da'awar da ake yi kuma yanayin yanda yake girmama shugaban da'awar watan babu shakka yayi yunkurin zuwan sosai har i zuwa dazun nan yake min waya cewar dan Allah lallai lallai a daure a zo domin shi da kanshi bazai samu zuwa ba. Amma a isar da sakon shi yafi na farko yana kara yin addu'a ga Malam Allah shi kara karfa fashi yayi mai jagora akan wannan abu da yasa a gaba na yada sunnar manzon Allah a doron kasa. Bayan haka yana kara jawo hankalin Malam akan cewar irin wannan abubuwan basa yiwuwa sai da hakuri. Soboda da haka ne magabata suka samu cin nasara har addinin ya kawo gare mu. Sannan yana jawo hankalin dukkan mabiya suyi bin yanda ya tabbata a sunnar manzon Allah daga lokacin da akace kana da shugaba to komar isuwar ka komai kan ba Makka to kana dakatar da ita ne ka saurare wanda yake shugabantar ka addinance. Daga cikin abun da sanata yake cewa yana bashi mamaki su da yawa za'a waye gari aga malami babban malami mai sai aga wasu da suke tare da shi suna da wani ra'ayi nasu yanda suka ga dama yace wannan abu yana bashi mamaki. Ace jagora yana wani umarni wanda yake bi shi kuma yana bin abun da yake so wannan ba tsarin addini bane Allah ka shiryar damu. Daga nan ya jawo hankalin yan uwa musulmi akan cewar a hada kai akan gaskiya kuma yace babu shakka yana tare da wannan tafiya kuma yana sauraron koyaushe a tuntube shi in Allah yaso duk irin gudunmawar da ake da bukata ta bangaren shi don cigaban addinin Allah in sha Allahu zai yi abun da zai iya.
[Speaker unknown]
Malam mun gode. To wannan wakilci biyu ne ya wakilci Dr Ahmad Muhammad 4
[Segment 5/6 | 01:20:00–01:40:00]
[Speaker seg5-spk:0]
makarfi kuma shima ya wakilci kanshi da nashi jama'ar da ke bayan shi. Malam Abubakar, Allah ya saka da alkhairi. Mun saurari sako daga kuma mun gode munyi farin ciki. Addu'o'i da shawarwari da nasihohi muna rokon Allah ya karba. Allah kuma ya taimake mu wajen muyi aiki da su. Babu shakka takaitattun sakonni ne wadanda suka zo a takaice amma suna cike da dimbin ilmomi kwarai da gaske. Wadanda ina ganin gaba daya sun tattara manufar addinin gaba daya da kuma manufar da muma muke son mu cimma wadda itace ta addinin. Na farko a hada kai akan gaskiya. Na biyu wanda yake jagoranci yayi kokarin hakuri da kuma adalci wajen bi da jama'a. Su kuma suyi hakuri da juriyar biyayya. Sannan da kuma nuna cewa yana ainihin shirye da ya kawo duk wani dauki da gudunmawa. Allah madaukakin sarki ya saka da alkhairi. A madadin daliban da ke kokarin shigowa musamman wannan makaranta da ake gabatarwa a yau muna ainihin godiya da wannan wakilci da sako da shi sanata ya turo. Kuma muna isar da gaisuwa ga sanata. Sannan a isar mishi da kukan wadannan dalibai dama suna neman su samu wani babba wanda zai zo wurin wannan kaddamarwa. Dan suce to lallai gwamnatin tarayya ta gaza game da harkar ilimi. To ana neman wasu bayin Allah wadanda zasu taimaka musu. Suna neman school fees. Suna kuma neman dan abun siyan garin kwaki da kuma sukari da zasu ringa jika garin kwakin. Da kuma ganyen shayi na lipton da ganyen bunu da zasu ringa jikawa in dare yayi hadda ta fara tsummuwa. Wannan a isar wa da ainihin mai girma sanata Allah ya saka da alkhairi. Malam Isa ni bana so in address naka da Malam Isa DITV. Na fi son in ce radio da television gaba daya da jarida. Dan shi duka in all ne. In kana jin shi wannan tashar gobe zaka ji shi a waccen tashar. Malam Isa ina tare da mu akan duk abubuwan da muke yi jama'a. Yakan biyo ni har cikin gida wani lokacin ya dauki rahoto na television da na abun nan. Abun da yasa galibin wani lokacin rahotannin da yafi bayyana akan su a shirin gari ya waye. Amma dai mu a makarantar nan muna ji ban san wace karama ce mu da mun daga FM a makarantar nan sai mu ji. Amma wasu bangarori a Zaria da yawa ba'a jin tashar DITV ko alkhairi. Mu nan ko dan mun dan yi sama ne mun dan yi tudu haka sai ka ji rangada dau tashar. Allah madaukakin sarki ya saka da alkhairi. Da sauran yan uwa yan jaridu wadanda suka ziyarto mu muna yi musu maraba. Malam Isa baza mu soka ainihin barorin nan ba duk da mun san cewa a yanzu din kana ta nadan rahotanni ne. Insha Allahu ta'ala za'a je a fada wa duniya duk abubuwan da aka kudurta na alkhairi a wurin nan. Amma muna son daga cikin wadanda zasu ka bada labarin sunyi magana harda kai kanka. Ka ruwaito kai kanka da kanka. Malam Isa bismillah.
[Speaker seg5-spk:1]
Jama'a assalamu alaikum. A kamar yanda malam ya fadi suna na Isa Abdullahi Gidan Kwako. Kuma kamar yanda malam ya fadi babu shakka mun dade muna tare da malam shekaru da yawa gaske. Kuma a bisa aiki tun ina jaridan gaskiya tafi saboda wayansu jaridu da yawa kusan kaman goma sha biyu haka da suka wuce. Babu shakka duk abun da aka ce abun da ya shafi aikin jarida in har za'a tuntubi malami na addinin musulunci a wasu lokuta zan ma malam waya a wasu lokuta zan mishi trace ne a wani lokaci zan fado ne kawai in ce malam ga abun da ya kawo ni. In nayin ne nan take ayi in ba nayin bane bazai ce bazai yi ba sai ya gama sai ya gaya mana hujja. Hujjan nan kuma ni kaina zan dauke ta a matsayin ni kaina a gare ni hujja ce. Saboda haka kamar yanda yake fadi a duk lokacin da mukayi tattauna da shi akwai kafafe da nake sawa. Daya daga ciki musamman shine inda nake aiki yanzu DITV Alheri Radio. Ta bangaren labarai ne da wayansu abubuwa wurare bangarori. Sannan akwai gidan rediyon muryar Najeriya Lagos. A kalla shekara takwas ko in ce tara da suka wuce nine wakilin ta a nan jihar Kaduna baki daya. Kuma gidan rediyon a Amerika wani lokaci in zasu yi wani shiri na musamman da ya shafi bangaren shi yanzu Zaria nan yawanci suna tuntuba na su ce in tsara musu yanda zasu kai ga nasara akan abun da suka tsara. Saboda haka a takaice kenan ina sarebi izinin Allah ta'ala kamar yanda malam ya fadi zanyi bakin kokari na zan cigaba da bakin kokari na akan abun da ya shafi abubuwan da muka ga malam yake yi. Musamman wata matsala da ta faru a lokacin da ta faru kafin zabe ne ko lokacin zabe kowa yasan wannan matsala. Allah ya sani malam yayi mun bayani mun zauna da ni da shi daga ni sai mahaliccin mu. Yayi mun bayani wanda na gamsu da shi kuma daga lokacin da Allah ya kaddara ido na bai kara ganin shi ba sai a wannan rana wallahi ba'ayi rana ta fito ta fadi ba tare da nayi wa malam addu'a Allah ya fito mana da shi lafiya ba. Abokan mu yan jaridu in mun hadu da su wadanda ma basu san wanene malam ba sanin da nayi mishi a kalla a cikin kashi dari nasan bai wuce in ce nasan malam kashi daya ba kashi ta sha inda tara. Duk wanda yasan malam kashi ta sha inda tara to gaskiya sai dai wanda yayi shi. Abun da in zan ajiye kenan musamman abun da ya shafi ilimin addini da ilimin zamani. In kazo ka samu malam yana magana akan ilimin zamani sai ka sai ka ga kaman bai san ilimin addini ma ba. Idan yana magana akan addini sai ka ga kai maka in bai san ilimin zamani ba. To saboda haka mu addu'ar da zamuyi a nan shine Allah ya kara masa lafiya kamar yanda sanata ya fadi Allah kuma ya kara mishi hakuri kamar yanda ya fadi Allah kuma ya kara mishi dauriya. Dan musamman mu dauka tafiyan da yayi kwanakin nan dan zamu ce tafiya yayi. Darussan da ya dauko da abubuwan da ya dauko hakurin nan ta je da shi hakurin kuma ta dawo da shi hakurin kuma ta sa yake cigaba da abubuwan da yake ba tare da ya waye ga baya ba. Saboda haka addu'ar da zamu cigaba mishi kenan Allah ubangiji ya kara mishi kwarin gwiwa ya kara mishi lafiya. Dan lafiya itace zata bamu tun dama yayi komai. To mu cigaba mishi da addu'ar Allah ubangiji ya kara mishi lafiya da kwarin gwiwa da hakurin aiwatar da abubuwan da Manzo sallallahu alaihi wa sallama yayi umurni Allah kuma ya cigaba mishi da jagora. Jama'a assalamu alaikum.
[Speaker seg5-spk:0]
Allah ya saka da alheri. Allah ya saka da alheri. Alhamdulillahi taro yayi taro lallai kam. Allah ya albarkaci taro da manyan malamai daliban ilimi yan siyasa yan jaridu to taro ya gama haduwa Allah madaukakin sarki ya sa albarka. Muna dab da rufe taro sai ga wani wanda shi in ma mun so zamu iya cewa dan jaridan Darul Hadith ne. Nan shi duk abun da aka tsuma aka tace a idon shi ake yi. Malam Mahamud Barwa ainihi na dauka zai zo wurin nan nema tun karfe bakwai. Amma dai in yazo jawabi ya kara kanshi. Ko kuma kasan ne zai wakilce shi ya ji wasu abubuwan da zai ruwaito mana. Shima dan jarida ne wanda kullum ana tare da shi tun farkon harkar nan yana daukan abubuwan da muke tayi yana isar wa duniya. Kullum shi yakan kawo mana bayanan gidan radio kaza zasu fara tafsiri za'a sa shiri kaza za'a sa kaza za'a sa kaza. Muna dai ta cewa a dan yi hakuri tukunna yanzu galibi duk dan canjin namu yana tafiya ne a wurin siyan bulo da siminti. In aka gama hada bulo da siminti da yashi gini ya tsaya shine lokacin za'a fara zuwa fa gagayen radio da television a fara siyan wurare insha Allahu ta'ala. Shi yasa cikin hikimar Allah sai ana ta ajiye darussan da ake yi saboda duk ran da aka tashi kawai to kunga dama bahaushe yana cewa mai uwa a maru hu. Ba yace to ba miya ba. Kusan duk inda zamu je insha Allahu ta'ala muna da wadanda da anje kawai mika musu cassette za'a yi a dan biya abun da za'a sai goro kawai shikenan sai a cigaba da sa program tun daga Radio Najeriya Kaduna rediyon nagarta abun da ya shafi rediyon jiha a taho zuwa ga ainihin alheri ko DITV ko makamantansu. Gaskiya duk jinkiri ko kuma rashin sanya karatuttukan mu da ake ji wato mune muke ta cewa a saurara saboda dalilan nan. In ba haka ba kullum Malam Mahamud yana kan hanya yazo yace to ga wata fa'ida ga wata dama tazo ayi amfani da ita mana sai mu ce to a dai dan kara saurara wa insha Allahu ta'ala. Muna rokon Allah madaukakin sarki Allah ya saka musu da alkhairi. Abubuwan da muka karanta a wurin nan na alkhairai Allah madaukakin sarki bamu ladan su. Kura kuren da mukayi Allah ya yafe mana. Allah ya ji kan iyayen mu da kakannin mu. Allah ya ji kan malamin mu da malamin malamin mu. Malam Mahamud Barwa muna fatan kaine na karshe da zamu saurari jawabi a wurin ka. Insha Allahu ta'ala sai kuma mai jawaban rufewa.
[Speaker seg5-spk:2]
A'uzu billahi minash shaitanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Yan uwa assalamu alaikum wa rahmatullahi ta'ala wa barakatuhu. A kamar yanda malam ya gabatar da ni a gare ku ga wasu fuska ta bakuwa ce. Ga wasu kuma fuska ta sun san ta. Yayi wasu sun san ina wannan aiki na yadan labarai yayi kuma basu san haka ba sai a yau da malam ya fada. So da yawa muka wani lokaci mukan dan boye kan mu. Bamu bayyanawa saboda akan dan kyamace mu wani sa'in idon harka ta neman labari ta asiri ta bayyana. Sai a dan boye mana. To shi yasa bamu son murka bayyana kan mu. Amma in yanayi irin wannan kaman malam ya bayyana mu to babu yanda zamu yi haka zamu fito muyi bayanin abun da ya kamata. Kamar yanda malam ya bayyana takaice Allah hakika yan jaridu a Zaria ko kuma a jihar Kaduna musulmai irin mu suna da yawan gaske. Amma masu manufa irin wannan zaka samu kadan ne daga ciki. To muna godiya ga Allah da ya bamu wannan dama har muka kasance daga cikin kadan din kamar yanda Annabi sallallahu alaihi wa sallam yake cewa musulunci ya tafiya da kadan ne. To muna gode wa Allah akan haka da yasa muna tare da wannan a dawa. Kuma Allah ya kara mana karfin gwiwa ne zamu cigaba da bada gudunmuwar mu gwargwado domin cigaban wannan addini namu duk kan mu gaba daya. Bazan tsawata bayani ba su saka kasancewan a shugaba na na taho duk dai lokacin da yake bayani wato Isa Abdullahi Gidan Kwako. Dan shugaba na ne. Yayi mun shugaban yan jaridu musamman a wannan shiya na Zaria. Sai dai shi an fada kafan yada labarin sa. To ni yanzu na zama kanin shi. Shi rooters ne. Yana shiga ko ya da ko ina. To ni kuma ina biye shi a baya. Da nayi aiki da kafan yada labarai na jihar Kaduna wato KSMC. Na shekara goma sha takwas da su. Daga baya na ajiye dan kai na shekara na biyu kenan na ajiye wa. To sai na bi na sahu shi shugaban nawa sai ya kasance ina baya a kafafen yada labarai labari daban daban. Wanda ina ganin basu fara lissafa ta su ba. In kuma an buqaci haka zan iya in lissafa su. Kila akwai buqatu ta wata sashin daban yana son ta nan ya ji an isa da sakon sa. To ba matsala ce ban Allah ya so. Kamar yanda malam ya bayyana muku na kan sadar da sako ga kafafen yada labarai na KSMC din har ila yau. Nakan ba rediyon tarayya na Kaduna. Ina ba rediyon nagarta labari har ila yau ni wakilin jaridan tarayyar ne da ke Kano a nan Zaria. Sannan ina ba leadership labari a daga nan Zaria. Sannan akwai wata kafan yada labarin ta fito ba'a ji ma ba ana ce mata Hamada International. To ni ba wakilin su ne kai tsaye ba amma wakilin su da ke Kano ni ke bashi labari daga nan shiyyar Zaria. To a takaice kafafen yada labarin da nake basu sakonni kenan a halin yanzu. Da fatan za'a cigaba da gudunmuwa mu hadu mu mu dinkula hannu mu dauka wannan addini da yaddan Allah. Ina godiya da wannan dama da Allah ya bani malam ya bani kuma ku saurare ni. Da fatan Allah shi mana jagoranci. Assalamu alaikum wa rahmatullah.
[Speaker seg5-spk:0]
Jama'a taro yayi taro saboda bamu so mu tsawata insha Allahu ta'ala. Muke rokon Allah madaukakin sarki ya mayar da kowa gidan shi lafiya. A karatu kuma daga yau an bude. Makaranta an dawo dan haka kowa zai fara karatun shi insha Allahu ta'ala daga yau. Masu ajin la'asar zasu dawo makaranta yau. Masu ajin dare zasu dawo yau insha Allahu ta'ala. Masu ajin safiya zasu dawo gobe. Haka karatu dai ya dawo dan haka da maza da mata gaba daya yan ajin Fatimatuz Zahra da yan ajin Sauda da yan ajin Abubakar da yan ajin Umar da Usman da ajin ainihin wato Abu Huraira makaranta ta dawo. Dan haka kowa ya taho da littattafan shi wurin karatu kuma lokacin karatun shi da ya sani. Daga yau kar ka ce baka san an ce makaranta ta dawo ba dama an ce za'a dawo makaranta yau asabar. To makaranta ta dawo insha Allahu ta'ala. Abun da ya shafi wannan daukan dalibai kuma daga yanzu din nan ana cigaba da daukar wadannan dalibai maza da mata da manya da yara. Sannan abun da ya shafi yara da muke dauka yan JSS 1 anyi common entrance an dauke dalibai. Mutane sun sake bulbulowa daga jihohi an sake yi an dauke dalibai. To mutane dai suna ta kara na cewa da muna tunanin ajin bazai wuce guda daya ba amma yanzu mun bada dama ajin ya kai guda biyu. Dan haka kofa a bude take har zuwa sanda zamu ainihin fara karatu a lokacin ne in muka rufe dauka kuma sai Allah ya kai mu badi. Dan haka dalibai muna kara sanar da ku. Karatun markaz yau ne zai dawo. Yau za'a dawo karatun Bukhari a markaz insha Allahu ta'ala. Karfe takwas da rabi na dare zuwa karfe goma. Dan haka masu wannan masallaci su je su shirya. Na biyu muna ainihin kara baiwa jama'a hakuri akan kaddamarwa da muka ce zamu yi ta karatun Sahihu Muslim a nan. Abubuwan ne sukai mana yawa lokacin jarabawa yaran. Lokacin jarabawa yaran nan muna zaton yaran bazasu wuce kwaya goma ba. Sai ga bugu daya an samu yara arba'in da wani abu. To wannan yasa dole kunga tsare tsaren sun dan karu. Anyi wannan kashe gari ma sai ga wasu yaran. Kai tun dai da mukayi jarabawa wannan sati biyu har zuwa jiya akwai yaran da aka kawo su ayi musu jarabawa. To wadannan shine sune dalilan. Mai yiuwa ranar Lahadi mai zuwa zamu gayyaci al'umar musulmi kaddamar da Sahihu Muslim din nan amma daga gobe ne zamu yi shawara in Allah ya so. Amma mun riga mun gama shiryawa tsaf. Hatta littattafan da zamu yi amfani da su daga batarwa duk gasu nan sai da muka zo da su muka tara su a wurin nan. Dan gane da daliban Darul Hadithi kuma wadanda ake karatun safe gobe karatun nan na safe zai cigaba. Zamu cigaba karatun Hamawiyya a gobe insha Allahu ta'ala. Dan haka karatun Hamawiyya ya dawo karfe goma na safe zuwa sha biyu. Dama Hamawiyya da Hikba to gobe kai riko Hikbar ka da Hamawiyya karfe goma na safe. To duk dai wani mai karatu dai kowa dai aji ya dawo kar wani ya ce bai sani ba. Yace ai yaji an ce a saurara a'a an ce a dawo. Saboda haka kowa ya dawo makaranta jama'a. Idan aka dawo zuwa gobe shine za'a yi sanarwar darussa irin su risala yaushe ne za'a dawo. Da darussa wadanda suka shafi kabairi yaushe za'a dawo da sauran su. Duk a gobe zamu fadi insha Allahu. Dan haka a yau za'a fara haduwa a wurin karatun markaz insha Allahu ta'ala. A yau daya ga watan October ko? Gobe biyu ga watan October. To Lahadi ta sama yaushe ake sa rai zai zama ga October. Takwas ko? To shi Lahadi tara. To kawai mu fara sanarwa duk wanda ke wurin nan yaji sanarwa ranar Lahadi ta sama tara ga October. To akwai muqaddima wadda za'a yi ta wadda ke dauke da tarihin Imamu Muslim da tarihin littafin shi da kuma takaitattun bayanan yanda za'a cigaba da karatun insha Allahu ta'ala. Dan haka ranar Lahadi mai zuwa itace ranar kaddamar da karatun Sahihu Muslim insha Allahu. Jama'a Allah madaukakin sarki ya dauka ka musulunci da musulmai Allah ya rusa kafirce da kafirai. Ga wata sabuwa dama na ce mana tun da muka tare a makarantar nan yanzu kuma duk wasu karatuttuka da suka saurara ko suka kwanta to zasu dawo. Kusan shekara goma sha shida da ta gabata ko sha bakwai wato a nan 1996 ko 95 afuwan shine yayi shekara sha shida zuwa sha bakwai. Akwai karatun littafin Nurul Albab wanda wannan karatu na Nurul Albab na Shehu Usmanu dan Fodio yau kaman shekara sha bakwai dai nake ji. A lokacin nan nake cewa insha Allahu ta'ala in Allah ya raya ni zan zo in sanya karatun littattafan dan Fodio da kuma littafin Malam Nasiru Dinil Albani. Wannan mashru'i ne wanda na daukar wa kai na. Insha Allahu ta'ala ina fatan kuma Allah ya taimake mu. To ina ganin Allah ya raya mu zuwa lokacin da nake nufi bayan shekara sha shida ko sha bakwai dai. Abu na farko nayi hidima akan littattafan dan Fodio
[Segment 6/6 | 01:40:00–end]
[Speaker seg6-spk:0]
wadanda suke buƙatar a yi hidima a kansu kamar yadda jama'a suka san na alƙawarta. Zuwa mako biyu da ya wuce na kammala abin da duk nake fatan in kammala a kan littattafan. Yanzu mun samar da littattafai wadanda abin da ya rage kawai zamu iya kai su a buga su a ko yaushe. Kuma in ba ku manta ba muna da kyakkyawar yarjejeniya da malam mashhur a kan zai buga mana littattafan nan a maɗaba'ar shi mai suna wadda take ƙasar Jordan. Na kammala na wasalce na yi duk abin da ya kamata in yi in banda ta'aliƙi da takhrijin ma'ana zamu iya buga su a yanzu a mujarradan su. Wato abin da muka yi shine mun rubuta littattafan a kan computer mun wasalce su mun gyara duk inda inji ko kurkuran hannu ya faru. Yadda za'a iya buga su a yadda suke. To dan haka daga ciki zamu riƙa printing da printer haka ana duplicating ana photocopy ana riƙewa ana karantawa. Sai dai wadannan karatuttukan zasu riƙa kasancewa da safe ne. Da safe zasu riƙa kasancewa wadannan karatuttukan in sha Allahu ta'ala. In ma bayan sallah asuba mubaasharatan wanda haka ba zata yu ba saboda zamu ɗan riƙa ɗaga ƙafa don masu tahowa daga nesa. Ina fatan an gane. Sai mu riƙa kai shi koda ƙarfe shida na asuba. Wadannan karatuttuka zasu riƙa kasancewa asabar da lahadi da alhamis da juma'a. Dan haka alhamis juma'a asabar lahadi kwanaki hudu a jere ƙarfe shida zuwa ƙarfe bakwai ko bakwai da kwata. Karatun na awa ɗaya za'a riƙa yi ko awa ɗaya da kwata a riƙa tashi in Allah ya so. Littattafan danfodiyo a zuwa yanzu ban fitar da wanene zamu karanta ba don suna nan da yawa wadanda na kammala sun wuce guda hamsin. Ina tunanin ko za'a karanta sirajul ikhwan ko za'a karanta ainihin wato ko makamantan haka dai in ba ku manta ba mun taɓa karanta guda biyu da kuma To mai yiwuwa yanzu zan sanya ko ko dai ɗaya daga cikin littattafan sai wanda hannu na ya kai kai amma dukkan su a shirye suke sai dai kawai a ɗauko a ci gaba da karantawa. Littafin malam Nasiruddin Al-Albani kuwa littafin da muka taɓa karantawa ne shima wajen shekara sha hudu da ta gabata. Amma a lokacin bamu karanta shi mun sa shi a video ba. Shine littafin Shi wannan littafi da ilimin da yake ɗauke da shi musulmi suna buƙatar su san shi musamman ilimi ne da ba kullum al'amarin yake faruwa ba. Shine dangane da al'amarin ya ake wankan gawa ya ake ɗinkal kafani ya ake saka mamaci cikin likkafani ya ake sa musulmi cikin ƙabari ya ake haƙar ƙabari ya ake shiga maƙabarta da fitar ta yaya ake tsara ƙabari da duk wadannan al'amura sannan wadannan bidi'o'i ne suka shigo cikin wannan fagen. Wadannan littattafai na wadannan malamai in Allah ya so sai dai a canza rana ko a canza lokaci. Amma dai ba a ɗauke karatun su ba in sha Allahu ta'ala ma'ana da zaran an kammala karatun wannan littafi na danfodiyo za'a ci gaba da wannan da an gama wancan za'a ci gaba da wannan da an gama wannan za'a ci gaba da wannan. Wato in Allah ya so muna da littattafan danfodiyo wadanda a bisa wannan karatun dai ko nan da shekara talatin ko hamsin mai zuwa muna da su a hannu. In sha Allahu ta'ala kaga in ma mun rayu mun yi tsawon rai kenan. Haka littattafan malam Muhammad Nasiruddin Al-Albani to wannan Kowa yayi ƙoƙarin ya samo shi ya siya. Za'a fara karatun in sha Allahu ta'ala daga ranar Alhamis ɗin nan mai zuwa duk Alhamis da juma'a ƙarfe shida na asuba zuwa ƙarfe bakwai da rabi. Duk Alhamis da juma'a asabar da lahadi kuma littattafan gidan fodiyo to in nace danfodiyo abin da nake nufi ba shehu kaɗai ba. Ina nufi shehu ɗin ina nufi Abdullahi Gwandu kuma ina nufi Muhammadu Bello. Wadannan guda uku dama sune ne aikin littattafan nasu. Yanzu da na kammala iya abin da na kammala a kan computer ko wanene na ware mishi nashi na ware littattafan Abdullahi daban na ware littattafan shehu Usmanu daban na ware littattafan Muhammadu Bello sarkin musulmi daban. To in Allah ya so abin da zamu yi idan muka zare ɗaya na danfodiyo muka karanta sai mu ɗauki ɗaya na Abdullahi Gwandu mu karanta sai mu ɗauki ɗaya na Muhammadu Bello sarkin musulmi mu karanta. Ɗaya bayan ɗaya haka zamu riƙa yi sai a riƙa kewaya wa. Ba dan komai ba saboda ɗimbin alhiran da ke cikin wadannan littattafan da kuma bayyana cewa mu ahlussunna da ke da'awa a Najeriya bamu zo da wani abu wanda yake sabanin abin da su danfodiyo suka zo da shi ba. Duk abin da wani zai faɗi a kan dan fodiyo rabu da shi duba me dan fodiyo ya rubuta da hannun shi. Duk abin da wani zai faɗi masoyi ne ko maƙiyi game da gidan fodiyo manta da abin da maƙiyin ko masoyin ya faɗi in kaji akwai iya wuri ko akwai rashin adalci a ciki ko ma ka karanta littattafan su me suka rubuta. Littattafan su da malaman mu na ƙasar nan suka karantar da mu muka karanta su muke son mu fara karantar da su. Suna cike da duk abin da muke kira zuwa gare shi cewa a dawo a bi alƙur'ani da hadisi a dawo a tsaya a kan tafarkin malaman farko. Kuma ma kamar yadda wani dattijon malami yake faɗi yau shekara ashirin da bakwai da faɗin wannan magana shine sheikh Ahmad Lemo daga jihar Niger a garin Mina an yi hira da shi a gidan rediyon Najeriya na Kaduna da la'asar 1984 ina zaune ina jin hirar har yake cewa abubuwan da 'yan izala suke yi ake musu musu idan haka buɗe littattafan su shehu sai an ga su kan su 'yan izala ma bidi'a suke yi. ce kenan ah haka ne wallahi ba kuskure yayi ba sai wanda ya karanta littattafan su dan fodiyo zai san haka. In aka karanta littattafan dan fodiyo har ɗan izala sai yace zagin shi ake yi. To izalatul izala kenan cab dijan ta kaga sai kuma gyaran ubangiji kenan tunda dai gashi zamu karanta. Kaga duk wanda zai ce ana zagin shi sai a ce to ai tun kafun ayi ka akai littattafin ashe ba da kai ake ba. Saboda haka in Allah ya so zamu fara karanta wadannan littattafai na dan fodiyo kuma duk littattafin da zan fara karantar wa sai na zauna nayi tarihin su dan fodiyo kaf in sha Allahu ta'ala sannan sai na kawo rubutun hannu na littattafin na nuna wa kowa ya gani in nuna kuma da wannan rubutun hannun ne amfani na sa a computer na wasalce sannan da website website na internet ɗin ban riga na kafa shi ba amma na raɗa mai suna shine f o d o d i o f o d i o wannan shine sunan da turawa suke kiran su da shi da yake sunan ya yaɗu shi yasa na bar shi a haka a kan website dan yayi sauƙin nema yadda koda search injin ka sa na computer ko ina zaka iya kamo wa. Amma in ba haka ba asalin sunan ba fodiyo bane ba fodiyo bane ko kuma yadda baushe yake cewa hodiyo a'a fodiyo ne fodiyo kalmar fulatanci ce fodiyo ma'anar ta shine babban malamin fiƙihu baban su ne da wannan sunan an gane Usmanu dan Muhammad fodiyo ina fatan an gane to fodiyo ne f u d u y e shine asalin spelling da yake daidai fodiyo to amma sai tura suke cewa fodiyo to da na tashi creating website ɗin da sunan fodiyo ɗin na sa amma yadda zai kasance duk littattafin da zaka nema in ka tafi kan wannan website ɗin zaka ga littattafan sai ka zaɓi wanda kake so. Akwai littattafan Abdullahi akwai littattafan Bello akwai littattafan shehu sannan akwai littattafan 'ya'yan su da jikokin su da almajiran su har zuwa yanzu. Akwai littattafai da dama da malaman suka rubuta hausawa fulani bare bari nufawa duk na bi wadannan ƙasashe na je na samo su sai na hada su zasu shiga cikin website ɗin daban. Misali gidan Yakubun Bauchi a nan ainihin wato a kafin mai yaƙi kenan za'a ce ko ina ne gidan masarautar zazzau su sarkin zazzau kwasau sarkin zazzau alu ɗan sidi su malam Jafaru ɗan Isiyaku duk littattafan da suka rubuta gaba ɗaya na zuba su a cikin website ɗin ne haka in ka tafi bidda ƙasan nufawa haka in ka tafi can kwararrafa wa can wajen kebbi da duka dai na bi littattafan na riƙa abin nan wato aiki ne lokacin na ɗaukar wa kai na wanda yake in ba dan bahaushe da yace su sa kai yafi bauta ciwo ba gaskiya in kuɗi za'a bani ba zan iya yin aikin ba. Don wannan tsohuwar motar tawa da ka gani duk inda ka ganni za'a ganni da generator a boot da injin photo start a ainihin kan seat. Kauye kauye na riƙa shiga wani wurin motar sai an zuba kata ko tukunna ma zata iya takawa da iya wuce wa saboda tsabar dausayi kofa dama da ke wurin. Har in je in hadu da wani malamin wani malamin zaka same shi kamar kullum wani mai sauƙin hali wani mai kaushin hali wani ma in kaje zai kalle ka wani bayahude ne. Haka wani zai gan ka don kace zaka ɗauki littattafan dan fodiyo ka zuba su a computer kai kasan dan fodiyo ko dan fodiyo in zaka sa littattafan shi a computer to wani in naje ma ya ɗauki littattafan ya bani sadaka wani kuma sai an tatta ta birza da ƙyar sai 'ya'yan shi da almajiran shi sun sa baki zai yarda ya fito ya tsaya a wurin a kunna generator da injin photo start ayi photo start. Da haka gani nan ni ne har cikin ƙauyukan kan giwa da ke jihar kebbi can ka buga wajen zuru ka buga ka dawo nan cikin bidda ƙauyuka gashi nan dai haka can in ka kaɗa wajen gombe su na faɗa daɗin kowa daɗin wanene duka dai haka to amma alhamdulillahi kamar yadda nace da ike na sa kai na ne zan yi na haka mun tattaro wadannan littattafai in sha Allahu ta'ala wadanda muke fatan Allah maɗaukakin sarki ya bamu ladan wannan aiki kuma Allah maɗaukakin sarki ya amfanar da wadanda aikin zai kai zuwa gare su. Ka ga yanzu ai akwai wani ɗalibi cikin ɗaliban mai duguri wanda yake jami'ar Islamiyya yanzu da ya tashi yin aiki a kan wasu littattafai kawai sai wani yace mishi ya neme ni. Yana nema na shikenan da mukayi magana shikenan sai nace shikenan ya turo email ɗin shi kawai a dare ɗaya sai na tura mishi. Ka ga shi yana zaune a ɗakin shi a iya condition kawai. Saboda na tuda na to dama wannan daga ciki shine abin da jiya nake faɗa muku. Tsoho ne yana noman dabino zai dasa dabino. Wani mai sarauta yace mishi kai wannan tsoho kana da wauta ka tufa ka zo kana da shan dabino to dabino da sai ya shekara ɗari tsoho yace to tunda dai an noma mana mun ci ai mu ma ya kamata mu shuka wa wasu su ci. Sai mai sarauta yaji daɗi yace kai wannan tsoho ka iya magana. To an shi wannan sai mu yi ƙo mai sai tsoho yace to ba gashi dabino har ya fara 'ya'ya ba tun yanzu. Ina fatan an gane. Shine tunda malamai sun yi mana wannan aiki mu ma mun amfana mu ma kaga ya kamata muyi wa wasu domin su amfana. Shi yasa wannan aikin a iya kar sani na shine aikin farko da ake yi ga littattafan gidan a bisa wannan sura ɗin. In ba haka ba akwai aikace aikace lokacin matar a bacha ta baiwa jami'ar dan fodiyo naira miliyan biyar suyi aikin tattara littattafan na na asma'u. To amma iya kacin abin da na san sun yi shine sun riƙa bin wasu littattafai ne suna photo start kawai sai aka hada sai aka yi printing. Har a lokacin ina da wani aboki lecturer a wurin nace mishi su bani miliyan ɗaya su su ci hudu. Su je ni ina littattafan zan yi musu aikin kawai sai in kawo musu. A su so suke su cinye duka. Nace su ban dubu ɗari biyar su su ci ɗari miliyan hudu da rabi yace a'a to shikenan dai haka dai suka je suka ɗan yi photo start ina nan da abin da suka yi photo start ɗin shi suka bata dai a matsayin shine aikin miliyan biyar ɗin wanda yake a lokacin ko naira dubu ashirin bai kai ba. Photo start ne kawai akai sai akai binding. Aka ce ga littattafan na na asma'u. Kuma sai da suka hada da wata bayahudiya ma mutuniyar Ingila sannan suka iya yin aikin. To alhamdulillahi mu mun yi saboda Allah ba saboda samun koko bo ba. Amma abin da muke fata shine mu taskance wa duniya don ta san wani aiki ne malaman mu suka yi a wannan nahiyar. Shi yasa na biyo baya da ayyukan sauran malaman ƙasar hausar kaf na fara tun daga kebbi wato Gwandu kenan har zuwa fodina itace adamawa ko yola ta yanzu. Na riƙa bi ina ainihin kar karɓo wa. Akwai littattafan ma da har yanzu wasu dattawa sun yi mun alƙawari ban je na karɓo ba. Akwai dattijon da mun hada da shi bara a Abuja wurin ta'aziya yake ce mun yau shekara biyar akai mun waya zaka zo zamu baka littattafan mahaifin mu. Nace ƙwarai da gaske nace kuma duk sanda nazo wuce wa garin ina tunawa. Shine malam yaya Arabi shugaban jam'iyyar nasirul islam ta jihar gombe babban ɗan malam Ahmadu Arabi wanda ajin su ɗaya da malam Abubakar Gumi a Sudan 1954 shine ya fara yi wa to sun tattara wadannan littattafan sun bani a gombe cewa zan je in ɗibo. Akwai littattafan a gidan doctor Ali Abubakar sarkin prime minister tafawa balewa wanda ke auren ƴar wanda ya aure ƴar tafawa balewa ta farko ya rasu doctor Ali Abubakar wanda ya rubuta littattafin shi ma har gidan shi na je ƴa'yan su kayi alƙawari suka aiko a koma a je a kwashe littattafan gaba ɗaya ma sun bayar in sha Allahu ta'ala duk zamu je mu karɓo su. Waƙafi ne suka yi. Wannan wurin namu mu ma waƙafi ne. Kun ga in sha Allahu ta'ala sai Allah ya kiyaye mana wadannan abubuwa da kiyayewar da yake wa addinin shi. Saboda haka muna roƙon Allah maɗaukakin sarki ya ɗaukaka musulunci da musulmi. Allah ya rusa kafirci da kafirai. Wadannan ayyuka da muke yi Allah ya sarkake zukatan mu ya karɓe su ba dan mu ba sai dan girman Allah. Allah maɗaukakin sarki muna roƙon ka Allah ka gyara zukatan mu ka sarkake zukatan mu ka gyara ayyukan mu. Da ƙarshe ina ƙara jin hankalin ƴan uwa a kan jajirce wa. Wannan wata tafiya ce wanda wallahi ba gudu ba ja da baya. Sabanin irin yadda su Abu Talib da su Abu Jahal suka riƙa tunanin musulunci cewa za'a yi ne kwana biyu a bari babu shakka da gaske muke yi. Kuma in sha Allahu ta'ala muna nuna wa Allah cewa da gaske muke yi kuma da gasken muke yi. Saboda haka wannan ba makaranta ce wanda an kafa ta kwana biyun aka gama zugugutawa shikenan ɗaliban su watse malaman su ma su tafi harkokin su a'a. Makaranta ce wanda in sha Allahu ta'ala ta kafo. Dan haka muna baka shawara ko muna kwaɗaitar da kai kayi ƙoƙarin a fara wadannan alkhairai da kai ko da ƴa'yan ka ko da matan ka. Allah maɗaukakin sarki ya albarkace mu Allah maɗaukakin sarki ya tsare mu muna roƙon Allah maɗaukakin sarki da tsarewar da yayi wa addinin shi Allah ya tsare mana wannan wuri. Abubuwan alkhairai nan duk gaba ɗayan su da muke gabatar wa muna roƙon Allah ya karɓa mana. Allah maɗaukakin sarki ya riƙe mana su da hannun shi na dama wannan amana ce muka bari a hannun Allah ba a hannun kowa ba kuma muka wakilta Allah ya zama wakili a kan hakaAnnotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani, et Daaru Ibn Katheer. Kaddamar da Sashin Al-Qur'ani. Daarul Hadeethis Salafiyyah. DVD. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15858.
Zaria, M. A. A., & Katheer, D. I. (s. d.). Kaddamar da Sashin Al-Qur'ani [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15858
Zaria, Muhammad Auwal Albani, et Daaru Ibn Katheer. Kaddamar da Sashin Al-Qur'ani. Daarul Hadeethis Salafiyyah. DVD. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15858.
Télécharger
Visualisations
Chargement des visualisations…


