document audiovisuel · Daarul Hadeethis Salafiyyah · août 2001 Citer
Adabul Mufrad #1-4
- Type
- Enregistrement vidéo
- Editeur
- Daarul Hadeethis Salafiyyah
- Description
- en Sheikh M.A.A. Albani teach us how to run our life with everyone without and tribalism or religious differences and how to obey parents from the Adabul Mufrad.
- ha Malam shaikh M.A.A Albani yana karantar da yadda za mu yi mu ba tare da banbachi komai ba da bin iyaye daga littafai Ablabul-Mufrad
- Date
- août 2001
- numéro
- 1
- 2
- 3
- 4
- Est une partie de
- Muhammad Auwal Albani Zaria
- Importance matérielle
- PT246M
- Support
- DVD
- Sujet
- Théologie
- Langue
- Haoussa
- Source
-
Abdoulaye Sounaye
- Identifiant
- iwac-video-0000008
- contenu
-
============================================================
[Part 4]
============================================================
[Segment 1/4 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yau asabar ashirin da biyu ga watan na da shekara dubu daya da dari hudu da ashirin da biyu wanda ya daidai da goma ga watan shekara ta dubu biyu da daya muna karatun littafin Allah ya gafarta mishi bamu gushe ba muna karkashin babin da ke bayani akan hukuncin saba ma iyaye laifi ne mai matukar muni munji hadisin farko a yau sai Al Imam Al Bukhari ya samo wannan hadisi daga malamin shi Muhammad dan shi kuma yace ya samo shi daga malamin shi Jarir Jarir daga Abdul Malik dan ainihin shi ko yace daga din sakatare ne na ainihin dan yayi ainihin governor a Kufa a lokacin ainihin mulkin su to shine sai shi ainihin wato din yace Muawiya ya rubuta takarda zuwa ga governor shi na kasar Kufa mai suna dan yace ka rubuto mini abubuwa daga abubuwan da kaji daga manzon Allah sai yace sai shi ya rinka mini ya rinka mini yana fadi ina rubutawa tunda nine sakataren shi yace da hannu na na rubuta cewa Ni na ji shi manzon Allah domin ana fada mishi ne abin da aka fada mishi ya rubuta Ma'ana ni dan na ji manzon Allah sai shi ya rubuta kamar yadda aka fada mishi na ji manzon Allah manzon Allah yana ainihin hani game da yawan tambaya yawan tambaya ainihin manzon Allah ya hana mutum ya rinka yawaita tambayaLire le texte intégral — 35 573 mots restants Réduire le texte intégral
musamman tambaya ta tambayoyi wadanda yake ba na neman fahimta addini ba tambayoyin jayayya da neman gaddama da neman kure da neman shari'ar musulunci ta hana wannan misali mako biyu da suka wuce wani ya bugo mini waya daga garin Bama can ainihin gaba da Maiduguri wai yana tambayar wai ina hukuncin shuwagabannin kasar nan a wurin Allah nace to ni dai karatu na bai kai ba amma da zan baka shawara da kai kayi kokarin sanin naka matsayin a wurin Allah da yafi kasan matsayin wani a wurin Allah don in kasan matsayin ka kai dan wuta ne to tunda baka riga ka shiga wutar ba sai kayi kokarin zama dan aljanna in kasan matsayin ka kai dan janna to kaza ne tun baka kai ba sai kayi kokarin zama dan janna to kaza to in ko kana tambayar matsayin wani shine Bahaushe ke cewa kowa ya daka rawar wani sai ya rasa turmin daka tashi irin wadannan tambayoyin a yau sune suka shagaltar da daliban ilimi suka kasa natsuwa su koyi ilimin da ake koya musu sai a yanzu kamar littafin gashi muna karantawa amma wani ba nan hankalin shi yake ba abin da hankalin shi yake shine wasu malamai sunce ba'a zakka a neran Najeriya wasu malamai sunce ba'a zakka a masara da tumaturin abin da yake so wannan matsalar yake so a tattauna mai wannan matsalar kuma tafi karfin shi dan in an bashi karatun da bayanan kwakwalwar shi yanzu baza ta dauka ba don haka in aka bashi sai ya zama ya dai ji abin da yake so ya ji wurin ka ko sai kuma ya tashi sai ya ketaracen malam ina hukuncin ana yi naira zakka wannan malami yace eh ko yace a'a shima ya bashi abin da ke wurin shi sai ya hada fatawoyin malamai gaba daya in kazo ka tambaye shi menene malam wane yace meye hujjar shi bai rike ba Al Adabul Mufrad kuma da ake kokarin a biya mai ya rike kuma bai rike ba sai ya tashi sai ya biyu babu batan bakatan ta bai iya karatun da ake koya mishi ba bai kuma ainihin iya waccan rikicin da ya shiga ba shi yasa da ace daliban ilimi zasu gane sai ka fahimta tun randa uwar ka ta haife ka tun daga sanda ka fara jin magana ka tashi kaji malamai yana rikici ina son ka tuna wannan da kyau sanda ka tashi a kasar ku ko waye kai dattijo ne kai ko matashi kaji malamai yana rikici akan wata matsala har yau kuma malamai rikici suke akan wata matsala to su malamai ne duk abin da sukai rikici akai sunsan mafitar da zasu fita su kwana lafiya in kaje ka kuga kanka a cikin wannan rikicin kwatan kwacin dan kasuwan da ke da jalin naira dubu biyar ne sai ya ga manya manyan yan kasuwa diloli wadanda ke da miliyan biliyan da sauran su suna gasar siyan motoci barka barka da gina manya manyan gidaje da auro a tsala tsaren amale sai ainihin yace shima mai jalin dubu biyar zai shiga cikin wannan zai yu to abin da nake cewa dalibai su san cewa dalibi ba malami bane kusan wannan dalibi daban malami daban in kai ba malami bane ka auna yanzu da ace za'a je a ajiye ka a cikin majalissar malamai da za'a tattauna matsalar zakka a nera ace za'a tattauna da Larabci ake so kowa ya wargaje dalilan shi yazo da hujjoji zaka iya zama a majalissar tsakanin ka da Allah ka amsa mini wannan tambaya amma a zuciyar ka zaka iya eh to shikenan to duk rikicin da ya taso ka shiga amma sai ya zan amsar wannan tambayar da zakayi shine a'a baza ka iya zama majalissar malaman nan ba misali su malam Abubakar Gumi zasu mike sai kayi awa biyu kana jawabi da Larabci kuma bazan fare ni uwar shi da uban shi ba Laraba bane amma da Larabci zai tashi yana jawabi misali da za'a ka kara ka tsakiyar irin wadannan zaka iya shiga bazaka iya ba me ya kai ka ka shiga cikin matsalar ka bari ana koya maka karatu ana nan sai azo kan babin zakka ta kudi sai kaji ance maka wasu sunce ana yi wa kaza zakka wasu sunce ba'a yi wadanda suka ce kaza sai kaga a natse anzo gurin ka fahimta amma ace bana ka shiga ainihin makaranta sai kace kana so zaka rinka zuwa wadanda suke wadanda suke zaka rinka zuwa kana sauraren lacchar su me zai amfane ka in ba rudani ba ba abin da zakayi sai rudani ana biya maka misali sai kaje ka shiga cikin manya manyan ainihin wato gardawa wadanda yake zasu je su rubuto ainihin kaza da ka suzo malam ya kwace allon su biya ba'a ci gyaran su ko kumsa ba balle kuri misali sai kai mai allon an baki sai kazo sai ka shiga cikin wannan tsari kace ai abin duk karatu ne duk muma muna son mu karu me zaka karu da shi ba abin da zaka karu da shi sai rudewa to dalibai ya kamata su gane duk sanda kake koyon ilimi abin da ake koya maka din yafi muhimmanci fiye da abin da ake rikici akai a gari amma kaje Bauchi kaje Maiduguri kaje Sokoto kaje ka samu irin tambayoyin da ke kan dalibai duk inda akaje akai wa'azi abin da akai musu wa'azi akai ba shine abin da ainihin suke tambaya akai ba shi yasa mako biyu da suka wuce na sanya mutanen Kubwa Dab da Abuja na sa musu karatun sai nace dokar farko daga cikin dokoki shine duk abin da bakaji baki na ya fadi a inda na zauna ba karka tambaye ni ko ka taba ji a wani kasar nawa karka tambaye ni sai abin da na fada a yanzu na zo koyar da ku to ku zauna ku koyi to amma in misali a wannan ranar fa na fadi wannan magana amma sai ga tambayoyi malam a cikin Sahihul Bukhari akwai hadisi da'ifi malam ya halatta a dauki hoto a bidiyo tunda kunce bai halatta a dauki hoto na na camera na abin nan ba ka gani in akai hakuri wannan karatun da yake tambaya akai yana nan a cikin amma ba'a zo kai ba in ka amsa mini in kace mai a cikin Bukhari babu hadisi da'ifi sai kai ta kawo mishi misalan hadisan da ake gani da'ifai ne kamar guda dari biyar wadanda ya ciku musu yace da'ifai ne duk sai ka warware mai zai iya dauka bazai iya ba me ya amfanin ka amsa mai sai kace mishi eh akwai sai ka kawo hadisan da ake gani masu illa sai kace duk wadannan suna da illa a Bukhari misali zai iya dauka ashe menene amfanin wannan tambayar ya kamata jama'a wallahil azimi mu rufa kanmu asiri natsuwa kake in kana koyin ilimi natsuwa kake yi kaje kayi sai ka zama murucin kan dutse tukuna amma ka zama shege dan masara ana goyon ka kana gemu zagin yara kenan da suke yi ko ma'ana kana yaro dan karami dalibi amma ka rika ba haka yara suke cewa ba dan masara zaka ga goyo dan yana goyo yana bayan uwar shi amma da gemu hadda furfura da sauran su saboda rashin kunya ba haka bane ma'ana baka baka zama malami ba kace zaka rinka kusa kai a cikin rigingimun malamai sai kaje ka ruda kanka sai kaji kullum mutum abin da yake sanyi tambaya matsalar da tafi karfin shi ne to haka suka rinka wa Annabi irin wadannan tambayoyin Annabi ranshi ya baci Allah ya saukar da Qur'ani yana zargin su yana hana su in Qur'ani na sauka ku daina tambaya Qur'ani na sauka dan in kuka tambaya za'a baku amsa zuwa sukai suka kewaye Annabi ya manzon Allah baba na ya mutu yana jahiliyya yana ina sai manzon Allah yace uban ka na wuta ya manzon Allah ni kuma nawa fa manzon Allah kaima uban ka na wuta wannan kuma ya manzon Allah sai mutum ya riko gari tun daga kauyen su ba kauye ya taho tun daga kauye wai abin da yazo tambaya wai uban shi ya mutu a jahiliyya yana ina sai manzon Allah yace uban ka na wuta to da yake ba kauye be da kan gado sai yace to ya manzon Allah na kafa sai yace da uba na da uban ka duk suna wuta kuma duk inda kaje zaka wuce kabarin wani arne ka tsaya kayi mishi albishir da cewa dan wuta ne to yanzu wannan wannan fitinar da wannan ba kauyen ya ja itace ake rikici har yau sai wadancan yan bidi'a daga cikin yan darika da yan shi'a sai su zasu ce ai Ahlussunna sunce iyayen Annabi na wuta duk ba wancan fitinan ba kauyen ne ya ja matsalar ba da bai yi tambayar ba haka su dan Annabi zai ce iyayen shi na wuta ne to abin da ake cewa babu wata fa'ida irin wadannan tambayoyin ka tambaya yanzu kai kasan farillan alwala da za'a datse ka na daya daura niyya na biyu wanke fuska da yan Islamiyya suke ka iya su a wakance din nan baka iya ba kaje kasan wadannan abubuwan rigingimun da kaji malamai ne Allah na sama ne ko yana kasa ko yana ko ina kace kai ba malami bane yanzu kake koyin karatu ana zakkar kudi ko ba ai kace baka sani ba ana zakkar masara ko ba kai kace karatun ka bai kai ba ka bar malamai da sha'anin karatu ka bar malamai da sha'anin saba ni da sha'anin rigingimu su suka san ina aka kwana su suka san inda za'a tashi amma kai baka san inda aka kwana ba baka san inda za'a tashi ba baka san inda za'a sa kai ba ba abin da ka sani sai ka shiga cikin rikici sai ka ruda kanka daga karshe sai kaga ya daina zuwa makaranta ya daina karatun addini ya daina zama da masu san addini da an taba shi sai yace sun cika rikici ne kai ka saka kanka a rikici musulunci bai da rikici bashi da rikici ko kadan amma kai ka saka kanka a rikici kamar kaine da jalin dubu biyar din can kaje ka shiga rikicin alhazancen sai kace kasuwan mata cika rikici ba dole kasuwa tayi rikici ba jalin ka na dubu biyar kace zaka auri tsaleleiyar mace kace kana son dandame mai yan mota kace kana son faske kyan gida ina zai yu bazai yu ba saboda haka an hana yawan tambaya an hana yawan tambaya to irin wadannan tambayoyi suna daga cikin irin su kuma koda tambayar da kake bukata akai sai ka tambaya nan ayi maka gamsashen bayani kuma sai ka ketarawa sai kuma kana son kaji ta bakin wane ka zama munafukin dan jarida kenan jama'a mun gane wannan da kyau ko in ba haka ba yana cikin hadisin Bukhari wani mutum yazo yace ya manzon Allah nazo in maka tambayar da in ka bani amsa bazan sake tambayar wani ba bayan kai ba shikenan ba haka yanzu in ka samu wanda ya amsa kai mai tambaya to kawai in ya baka amsa shikenan sai ka bi mukallidi ne kai dama imanin mukallidi yana rata yana jikin mujtahidi to duk abin da mujtahidi ya fada wa mukallidi sai ya dauka in ko ka baka gamsu ba shi din da ka tambaya sai kace malam baka gamsu ba sai ya kara warware maka ya fito maka da matsalar amma sai kaje kuma malam na tambayi wani malami yace kaza su kuma malaman saboda son girma sai yace a dan Allah wannan ai shume ne ai kaza kaza ai kaza madadin ka ce koma kaje can ka sake tambayar shi jama'a mun gane wannan da kyau to wannan littafi kar ku manta yana koyar da mu ladabi ne kunga yana daga cikin ladabi irin wannan tambayoyi na banza din nan ka daina yawaita su sannan da kuma ainihin tozartar da dukiya sannan kuma ainihin manzon Allah ya hana ance yace ance kuma yace sai kaje ka zauna ka bada labari tsaf a ace kai sahabi ne wajen iya bada labari sai ka gama jawabi sai ace ina kaji sai kace nima dai a bakin kasuwan ne na tsaya zan sai a yaba naji ana cewa yace a bakin kasuwa ko a bakin tasha zaka shiga mota zaka je Huntuwa ne kaji ance yace daga haka kuma kaji ga kanon kamar koje ka zauna ka bada labari kamar wahayi akai maka sai da ka gama ina kaji sai kuma a'a nima na tsaya ne wallahi zan sai a yaba sai naji ana cewa ai wane ne yace duk wadannan shari'ar musulunci ta hana Allah madaukakin sarki shi ya shiryar da mu yace wannan ainihin hadisi sahihi ne in kana son ganin bayani ka duba ta a karkashin lamba ta dubu biyar da dari biyar da casa'in da ainihin takwas jama'a musulmi an gane wannan da kyau ko to saboda wannan lafazin hadisin akwai akwai inda lafazin shi yazo da kuma cewa an hana saba ma iyaye akwai lafazin wannan hadisin don haka ainihin Bukhari ya kawo shi a nan me yiwa bai cika sharaɗin Bukhari bane don haka Bukhari bai kawo wancan shi ainihin lafazin ba amma alakar dai dake nuna ainihin me yasa kawo wannan hadisin tunda ana magana akan saba ma iyaye an hana saba ma iyaye ko saba ma iyaye yana daga cikin manya manyan laifuffuka to sai aka kawo ga wasu manya manyan laifuffuka ma da aka hana to zartar da dukiya wulaƙantar da dukiya yawo da tsegumi yawo da magana ka iya da bakin ka wannan harshe da ka gani inda kana da hankali wannan harshen wallahi yadda Allah ya iya maka shi da ka kara kiyaye shi ka duba can ciki aka saka shi can nisa shine na kurya a cikin baki sannan aka kawo kuso shi sama da kafa sama sama da kafa aka kakkafe wai kar ya fito sama da kasa kar ya fito amma sai ka turo shi yazo ya kai ka wuta ka duba can aka tura shi aka kawo aka fa mai shi ga kuso shi sama da kasa aka kawo labba akai mishi aka sake rufewa kar dai ya fito kar dai ya fito amma sai ka fito da shi ya kai ka wuta Annabi yace akwai abin da ke kifa mutane su shiga wuta suyi tunsara gudi gudi ko suyi kifa daya kwala da baya su fada ta kye su wuta ai ba abin da ke kai su sai abubuwan da harshen suke girbo musu yanzu yau wunin yau daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana karya nawa kayi kai ko bakai karya ba su rutu nawa kayi su rutun nan in ance tace mai amfani kai da kanka kasan mara amfanin yafi mai amfanin yawa daga nan zaka gane kaba ta kana iya zama kayi awa daya ba bacci kake ba ba komai ba baka komai kuma kayi shiru awa daya kayi shiru kayi shiru awa daya kayi shiru to kaga daga nan zaka samu cewa lallai kana girbowar kanka bala'i kuma ranar kiyama kasan sharrin wannan bakin sai a rufe shi wadannan ainihin bakin naka da ke su rutun a nan duniya da za'a barshi yayi jawabi a kiyama da sai kayi furi amma sai a rufe shi ace kafa kiyi jawabi hannu kayi jawabi sai sun gama sheda gaba daya kaje kaza kayi kaza kayi kaza kace kaza ka gama duk sun gama tona asirin ka kaf sannan sai kuma a buda bakin sai kuma kafa da baki da kafa da hannaye me yasa kukayi sheda akainu sai suce Allah dake iya sa komai yayi magana shine yasa mu muyi magana don haka ka rufawa kanka asiri yakai dan adam Allah ya shiryar da mu Imam Al Bukhari yace babin da ke bayani akan Allah ya tsine wa dan da ya zagi iyayen shi dan duk da ya tsine wa iyayen shi Allah ya tsine mishi albarka irin wadannan kalmomin a rinka fassara su da Hausa sunfi dadin ji sunfi fitar da ma'anar kalmar Larabci ce to Bahaushe bai jin zafin ma'anar ta sosai sai ance Allah ya tsine wa wane albarka to duk dan da ya tsine wa iyayen shi Allah ya tsine mishi albarka me yasa Sayyidina Ali aka tambaye shi aka ce shinku su Ali mutanen gidan manzon Allah ko manzon Allah ya kebe ku da wani abun nan musamman wanda manzon Allah bai keba mutane da shi ba sai Sayyidina Ali yace manzon Allah bai kebe mu da wani abu wanda bai gayawa sauran jama'a ba duk abin da ya karantar da jama'a shine ya karantar da mu
[Segment 2/4 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
yace saidai abinda ke cikin ainihin wato rufin ko kuma abinnan gidan wannan takobi nawa. Kube kenan. Sai sayyidina ainihin Ali sai ya fito da sahifa wata takarda. A cikin wannan takarda sai aka gani an rubuce. Allah ya tsine albarka ga duk wanda yayi yanka ba ga Allah ba. Boka kaiwa mai danko aljana wance duk abinda kaiwa yanka matukar ba Allah madaukakin sarki kaiwa yanka ba Allah ya tsine maka albarka. Allah ya tsine albarka ga duk wanda yasa ta iya kokin kasa anje an yanyanka filaye an aje bulo nan an aje iyaka nan an aje iyaka nan sai kaje da daddare sai ka sace ko kaje sai ka canza dan akwai wani lafazi na Bukhari. Sai kaje ka canza ka kara fadin filin ka ko ka rage filin wani to akace Allah ya tsine wa duk mai irin wannan aiki albarka. Haka kuma Allah ya tsine wa dan da ya tsine wa iyayen shi albarka. Allah ya tsine albarka ga duk wanda ya tattaro wata barna ya ainihin kawo bayan kasa. Wanda duk yake kawo barna a bayan kasa Allah madaukakin sarki ya tsine mishi albarka. Duk wanda ya taimaka wa wani dan ta'adda ko kuma ya tattara shi ya bashi masauki ya taimaka mishi ya tsare shi daga abokin husuman shi wani yaje yayo ta'adi a wani guri sai kai kuma sai kazo sai ka ainihin boye shi. Ya zan kasha makance wannan mutum ya sha makance tsakanin wancan da ya gudo yayi barna daga wanda zai ainihin rama zalincin da yayi to duk wanda yayi haka Allah ya tsine mai albarka. Ma'ana wani yaje yayo ta'adin da za'a tsai mishi da haddi sai kai kazo ka sha makance tsakanin shi da haddin ka boye shi Allah ya tsine maka albarka kai da kayi haka. Malam yace kuma ana ruwaito wa da fatha ga dal din To meye ma'anan Shine al'amarin da aka kirkiro shi da kan shi al'amarin duk da aka kirkiro. Allah madaukakin sarki ya ainihin wato la'anci irin wannan abu. Ma'anar tattarowa da akace tattarawa ka ka taimaka wa bidi'a ko ka ainihin taimaka wa wani azzalumi shine ka yarda da abun kuma kayi hakurin zama da shi dan bidi'a ne ka bashi shago ko dan bidi'a ne ka bashi gidan zama ko makamantan haka shine akace duk wadannan suna daga abubuwan da ke ja wa mutum la'anta. Domin in mutum ya yarda da bidi'a ya tabbatar da mai aikata bidi'a din ba'a samu wani yayi wa mai bidi'a musun bidi'ar ba ai ya taimake shi kenan. La budda sai anyi inkarin bidi'a sai anki taimaka wa 'yan bidi'a sannan duk wata barna da aka kirkiro aka jawo ta bayan kasa karka ga ka taimaka mata shiyasa a kashin gaskiya saboda Allah da wannan munasabar ce zamu yi wa 'yan uwa masu ainihin kokarin sana'ar sai da nasiha akan su san cewa shari'ar musulunci ta ainihin halattar da ainihin ciniki kuma ta haramta riba. Allah ya halatta ciniki kuma ya haramtar da riba to riba haramun ce to duk wani nau'in kasuwanci da zai kai ga barna mu tabbatar da cewa wannan abu fasikanci ne kuma ba daidai bane siyar da kaset ne na bidiyo ko kaset ne na audio wanda ake yada barna da ta'adi kada kada da wake wake iskanci ne da muna na tarbiyya wallahi duk wadannan abubuwan sun shiga karkashin irin wannan tsinuwar domin barna ce ka tattaro kai zaka je ka siyo kaset kaza anyi production kaza a gari kaza anyi production kaza kaje kazo da shi katan katan kaje kana yadawa kana sai ruwa duk wannan yana ja wa mutum ainihin tsinuwa domin yada barna ne bata tarbiyya ne shekarun baya da suka wuce da bahaushe bashi da ainihin fim da yake kallo nashi na Hausa sai wanda za'a sa a gidan talabijin wanda zaka ga ana yi nema kamar masu mutunci ne suke da kuma siffar mutunci da siffar fadakarwa. A lokacin sai India bahaushe zai gani da fim din America da sauran su a wancan lokacin wadannan fimafimai na India sun bata tarbiyyar samarin wancan lokacin daidai da irin wannan zamanin. Ashe wadannan samarin kos ne suke yi suna nan suna kosa kosa akan kasusuwan nan da suke kallo na India sai abun ya zama sai suka haifar da barnar da tafi wancan sharri shine duk wani tsarin fim da ake na kaset din India sai suka juye shi sai ya zama da Hausa da irin yadda ake wakokin da irin yadda ake rike hannun budurwa da saurayi ayi rawa da irin yadda ake runguma da irin yadda ake kaza duk gaba daya sai suka zo suka yi wannan wallahu alam sunzo sun kara kansu ko ya zama haka ne yake zuciyar su ko karya ce da munafunci wai sunce suna yi ne dan fadakarwa ka sani da cewa duk abinda kake yi koda a dabi'a anchi akan kalli abun. Ba addini bane wannan abun to sai a kalli abun barnar shi tafi yawa koko alherin shi. Lallai kuna cewa abubuwan da kuke nuna wa a cikin fimafiman ku kuna nuna ainihin me ke faruwa ne a yau a Nigeria ko me ke faruwa a duniya kuna fadakarwa a wannan lokacin kun manta cewa barnar da ke biyo baya na gurbatar da tarbiyya da lalatar da ainihin dabi'un jama'a yafi fa'idar da ake zaton ana samu in ma ana samun ta musamman matan hausawa dake kallon wannan fim din sunfi kowa rashin kan gado. Matar bahaushe in ta kalli fim taga sharri a ciki da wata ta hada wa mijin ta madadin ta wa'azantu wannan da ta hada sharrin ba'a gama fim din sai anga wani bala'i ya afka mata to ana wa'azantar da ke ne matar bahaushe ki wa'azantu amma matar bahaushe sai ta zama Bani Isra'ila. Ai ita tana ganin wannan sai taga to ai na miji dama haka ake mishi ai dama ba dan goyo bane sai taga wannan a fim din nan kuskure ne da tayi shi ya kai taga wancan muguwar karshe. Kuma ai fim ne ita ko zata iya tsarawa da gaske yadda zata tsara mugun abun ya gudanu ba tare da wancan sharri ya biyo baya ba sai ya zanka an karantar da ita ne mafi yawancin abubuwan da suke ainihin faruwa kenan. Allah madaukakin sarki ya kiyaye shiyasa jama'a sai su kiyaye wannan haka gidan haya ne bai halatta ka bai wa wanda yake dan bidi'a ba shagon haya ne bai halatta ka bai wa dan bidi'a ba duk irin wadannan abubuwan duk abinda zai tattaro 'yan bidi'a mabarnata 'yan iska masu lalatar tarbiyya ba'a hudda da su ya jama'ar musulmi saboda barnatar da tarbiyyar mutum ne wallahil azimi ba karamin ta'adi bane akan addini. Yanzu duk wani wa'azi da akai shekaru ashirin shekara kaza sakamakon irin wadannan fimafimai wallahi a cikin shekara biyu da suka wuce duk an lalata wa'azin nan. Duk matan da da basu biki basu suna basu rawa basu gwatso basu kaza a gaban makadi yanzu duk sun dawo suna yin abubuwan su. Me yasa za'a ce anga ga yadda ake a fim za'a yi dinkin sababbin kaya za'a yi kaza za'a yi kaza kafi suwa na tsoron Allah ne kafi kaza ne kafi aure nawa ne ya mutu wanda yake da ta hakura bata duk irin wannan fajirci amma yanzu an riga tana ga an haskaka mata fa ga abun da duniya take ciki don haka sai tace ita ko a bata 'yancin ta ko a bata takardar ta. Allah ya kiyaye.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
To dai sai ayi kokarin kiyaye wa kwarai da gaske. Malam yace sahihun wannan ainihin hadisi sahihi ne in kana son ganin bayani akan ingancin shi sai ka karanta littafin al mishka alambar hadisi na dubu hudu da ainihin saba'in sai yace Muslim mimun kenan mimun Muslim ya ruwaito wannan hadisi hadisi na arba'in da hudu da kuma hadisi na arba'in da biyar. Jama'ar musulmi wannan hadisi ba karamin hadisi bane daga cikin ainihin hadisan addinin musulunci wadanda malaman musulunci sun baiwa hadisin nan matukar muhimmanci ba dan komai ba saboda ya warware wata takaddama da wata gaddama dake tsakanin musulmi da ainihin 'yan shi'a domin 'yan shi'a suna da'awar cewa akwai abubuwa wadanda suke da su na ilmomi wadanda ahlul baiti da masu goyon bayan su sunsan wadannan ilmomi daga manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama wanda yake sauran jama'a basu sani ba sai ga wannan hadisi yadda kaji shi haka Bukhari ma ya ruwaito shi da lafazi kwatan kwacin wannan inda Abu Juhaifa wani tabi'i ne ya tambayi sayyidina Ali yace ranka ya dade ku mutan gidan manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ko akwai wani abu da manzon Allah ya kebance ku da shi wanda bai sanar da ainihin sauran mutane ba shine Ali ya bada ainihin amsa irin wannan to wannan ainihin sahifa ta sayyidina Ali Allah ya kara mishi yarda Allah ya tsare wa musulmi ita har zuwa yanzu dinnan da nake magana tana nan a duniyar musulunci sayyidina Ali hadisan da ya jiyo daga manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama sune wannan hadisin yana cikin wannan sahifa da sayyidina Ali ya jawo daga cikin kuben takobin shi. Sannan sai hadisan dake magana dangane da diyya cewa baza'a kashe musulmi ba dan ya kashe kafiri. Da dai hadisan dake wajabtar da da lallai ne ya girmama kuma ya bi ainihin iyayen shi su kenan hadisan dake ciki wannan sahifa kaga gata a hannu na. Gashi shine ya tsayaye hakkaka wannan littafi sayyidina Ali ya rubuta shi da hannun shi. Jama'ar musulmi mun gane wannan da kyau ko to itace sahifar ta sayyidina Ali a cikin ta ba'a ga wasiyyar da akace annabi yayi wa sayyidina Ali cewa shine ya cancanta ya zama khalifa a Gadir Khumba kuma kai kaje ka karanta babin dake bayani akan girmama ahlul baiti da kiyaye darajojin su dake cikin Riyadus Salihina kaje zaka ga hadisin da 'yan shi'a suke magana akan Gadir Khum din kaji shin akwai maganar wasiyya abinda akace manzon Allah ya tashi ya ainihin tsayu a Gadir Khum min 'yan shi'a saboda bakin jahilci sunan ma basa iya furta shi daidai sai suce Gadir Khum Gadir Khum wuri ne Khum din to Gadir ruwa ne sai ainihin annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallama ya tsaya a wannan wurin ruwa sai ya ainihin yi wa sahabban shi wa'azi ya kwadaitar da su gama da wajabcin bin littafin Allah ya nuna musu muhimmancin al'kur'ani sannan ya nuna musu muhimmancin mutanen gidan shi yace amana na baku amana ku kula da mutanen gida na ku kula da mutanen gida na kaje ka karanta littafin Riyadus Salihina kaga karya da suke yi maka suce wai wasiyyar sayyidina Ali da manzon Allah yayi tana nan a Riyadus Salihina inda shi'a yace haka kace Riyadus Salihina yana nan a kasuwa ko ina dari uku da hamsin dari uku dari da kaza kaza a bude a karanta ga hadisin tiriyan tiriyan ina ne wasiyyar take cewa wai nassin wasiyya annabi sallallahu alaihi wa sallama wai yace Ali wai shine ainihin zai zama shugaban kasa bayan sayyidina ainihin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam saboda haka hadisi dai kaji kuma kebance ahlul baiti da wani ilmi sabanin sauran musulmi gashi daga ainihin harshen Ali yace babu abinda manzon Allah ya kebance su yace sai dai wadannan abubuwan da ya ruwaito daga manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam sune hadisai ne guda hudu zuwa guda biyar a ciki wadanda suke tsoratar wa gama da taimaka wa dan bidi'a suke tsoratar wa gama da ainihin tsine wa iyayen shi suke nuna muhimmancin biyayyar iyayen suke ainihin nuna ba'a kashe musulmi dan ya kashe ainihin kafiri koda kafirin amana ne hukunce hukuncen diyya iya kar abinda ke ciki kenan gata sai da malamin ya tsayaye dirasar isnadin ta daya bayan daya ya kawo fikihun da ake cirewa gashi nan doktor ne guda a cikin fikihun musulunci daga Jami'ar Al Kahira bawai Saudi Arabia ba balle ku ce ainihin Saudi Arabia Wahabiyawa daga Al Kahira kasar ainihin Al Kahira kasar Masar in baka sani ba. Jama'ar musulmi mun gane wannan da kyau ko To wadannan ainihin da'awowi da 'yan shi'a suke suna nan suna nan a cikin ainihin littattafan su shi yasan nan nake so kadan daga ainihin abubuwan dake cikin littafin ainihin muji kadan daga abubuwan da suka fadi dangane da shin da gaske ne 'yan shi'a suna da wani al'kur'ani wanda suke da'awar sayyidina Ali ya ruwaito shi daga manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama wanda sauran musulmi basu da shi to ga dai littafin kaje ka samu littafin gashi zan fada maka ainihin shafin da zan ciro wannan magana insha Allahu ta'ala zan karanta maka kwatan kwacin gurare uku ne In kana son ganin bayani mu hadu da kai gobe a dogon bauchi insha Allahu ta'ala inda zaka ji bayani dangane da bambancin musulunci da addinin shi'a za'a zo nan in Allah yaso a wargaje bayanai tare da yi wa kowa adalci meye musulmi sukace a cikin littattafan su menene 'yan shi'a sukace a cikin littattafan su shikenan da zarar ka hada kai da kan ka ka iya banbance wa. Kaje ka karanta littafin a cikin shafi na dari shida da saba'in da daya ga abinda ainihin yace Yace babin dake bayani akan cewa babu wanda ya hada al'kur'ani baki daya shi sai wadannan limamai tun daga kan Aliyu har zuwa wannan limaman su goma sha biyu suka ce su kadai ne suka hada al'kur'ani cif din shi in basu ba ba wanda ya hada al'kur'ani. Jama'a mun gane wannan da kyau ko a cikin zaka duba a cikin Ga abinda aka ruwaito ainihin daga akace yace Daga cikin mutane abinda yake nufi da mutane nan sahabbai ba wani sahabi da yayi da'awar ya hada ainihin al'kur'ani baki daya kamar yadda aka saukar da shi sai tsantsar makaryaci duk wanda yace ya hada al'kur'ani cikin sahabbai kamar yadda Allah ya saukar da shi karya ike. Suka ce in ba Aliyu da sauran limamai goma sha daya da suka zo bayan shi ba babu wanda ya hada al'kur'ani cif ya haddace shi kamar yadda Allah madaukakin sarki ya saukar da shi. Jama'a mun gane wannan da kyau ko wannan maganar da na karanto tana cikin shafi na dari shida da talatin da tara na littafin a cikin In dai kai dan shi'a ne ya kamata ka mallaki wannan littafin kamar yadda ni dan sunna nake da bai kamata a barka da jarida ba ya kamata ya zama kana da littafi kuma ka iya karatu kuma karatu ba irin na shugaban ku zazzaki ba wanda zai ce littafin ba wasali ba zai iya ja ba kaje ka samu raddin da malam Mansur yayi mishi ta suniyar Kaji zazzaki ya jawo littafi zai karanta sai yace ap sai dai kuma ba wasali to to to a bari ba wasali bazai karanto ba bana hau bana hau ba sarf. Mu duba bala'i jama'a kana wai malami wai ana ce maka malami wai har ana cewa wai shehu dan fodio yayi ishara da zuwan shi wai an samu shi wai yana tashi a sararin sama to shaidanin aljanun nan duk a ina suke tashi wannan karama ce wannan ba karama bace ai amma ace shehi guda shehi bai iya karanta littafi ba ba wasali duk mutumin da bai iya karanta littafi babu wasali ba wannan bashi da rabo a cikin ilmi har abada shiyasa tafi tsohuwar jahar Gongola ta raba kenan da adamawa ta yanzu. In aka kai ka gurin malami ya koya maka karatun kur'ani randa za'a fara koya maka nahau sai baban ka ya kawo sa sai ace rannan za'a maida kai malami da mukallidi ne kai dan an koya maka baka san fassara ba Alhamdulillan aka rikita ta akace alhamdin ne aka kawo maka dabara zaka iya yarda to randa za'a fara koya maka nahau inda za'a ja ka ja ka kafe kai kayi jawabi rannan zaka zama mutum to sai baban ka ya kawo bijimin sa har yanzu haka ka'idar take a wurin fulanin dake dajin jahar Adamawa da ainihin jahar Taraba randa duk za'a koya maka nahau da sarf sai baban ka ya kawo bijimin sa ji ka Adamawa kaji. Allah ya taimaka.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
To don haka kaje ka samu littafin shafi na dari shida da talatin da tara gashi dai akace wai ba wanda ya hada Al'kur'ani ya haddace shi cikin mutane sai sayyidina Ali sai wadannan limamai da suka zo bayan shi da Hassan da Husaini da su ainihin wanene da wanene. Sannan Gashi kuma a baban falalar Al'kur'ani gashi abinda akace yace abinda yasa nake cewa akace yace jikokin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ne malaman sunna ne malaman alheri ne Ja'afar Sadiq ma malamin Imam Malik ne Imam Malik ya koyi karatun hadisi da fikihu da tarihi a gurin shi. Amma 'yan ta'adda ne wadannan 'yan shi'a da suka zo daga baya sai suka birkice haka'ik suka birkice abubuwa yadda suke to amma ainihin wato kifi mai jar koma yana ganin ka. Jama'a mun gane wannan da kyau ko ashe me ya kamata mu rinka tsayawa duk abinda 'yan shi'a sukace kamata yayi a koma tarihi a ga menene gaskiya abun kai kaje kana zagin ko limamai ne daga cikin limaman sunna. Amma 'yan shi'a runto ne da su sai suka jawo su sai suka jera su cikin wadannan limamai sai sukace limaman su ne kaza kaza kaza kaza to akace wai ga abinda Ja'afar Sadiq yace Idan mai mikewa ya mikewa to Umma Hadiya zo zai karanta littafin
[Segment 3/4 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
Allah madaukakin sarki dalla dalla. Wancan qur'ani da aka ce sayyidina Ali shi kadai ya rubuta a zamanin annabi ko? To aka ce Mahadi zai fito da shi in karshen duniya ta zo. Yayin da Aliyu ya gama rubuta wannan ya fito wa da mutane sai ya ce da su. Wannan shine littafin Allah kamar yadda ainihin wato Allah ya saukar wa da manzon shi Muhammad sallallahu alaihi ainihin wato Jama'a mun gane? Wannan salati fa inna ne kamar yadda musulmi suke amma yan shi a yadda yake zuwa a littafin su shine Yan shi'a basa cewa Wannan sai karatu wata ran zaka ji me yasa basa cewa Basa Jama'a mun gane? Sai yace Wai Aliyu yace na hada wannan qur'ani bango da bango daga bakara har nasi. Sai mutane su ce da Mahadi wannan qur'ani da ka fito da shi ka ce shine qur'anin da sayyidina Ali ya rubuta. Ai mu gamu da qur'ani fikakke a gurin mu izo 60 wani qur'ani zaka zo da shi yanzu ka daga ka ce wai gashi shine sayyidina Ali ya ruwaito daga manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Bamu da bukatan wannan sabo da ka zo da shi. Wai sai Mahadi yace To na rantse da Allah bayan yau ba zaku sake ganin shi ba. Shikenan sai ya gaba da abun shi. Ma'ana mutanen zamanin Mahadi yanzu ana nuna kenan Mahadi zai zo musu da wani abu wanda yake basu san shi ba har kuma suyi musu in kuma suka yi musu sai ya hakura shi da ya zo shiryar da su fa sai ya hakura daga shiryar da su shikenan har yayi rantsuwa da Allah ba zasu sake ganin qur'anin da ya zo shiryar da su ba. Bayan Mahadin nan ya tabbata a cikin hadisin Ahmad da Abu Dauda da Tirmizi cewa zai zo ne zai shiryar da jama'a bayan jama'a sun lalace amma ya zo musu da qur'anin gaskiya su daga nasu wanda suke da shi yace to tunda dai basu san wannan to shikenan basu sake ganin wannan ma'ana ya fasa shiryar da su kenan. Wannan magana ka je ka karanta ta a littafin na 661 da ainihin 71 Allah ya kiyaye. Ka ji wannan kenan. To bari kuma ka ji wata ainihin tatsuniyar tasu dai har wa yau. Don kamar yadda na ce gurare uku ne za a ainihin duba insha Allahu ta'ala. Gashi har wa yau a cikin dai littafin Karkashin wannan babin zaka je ka duba a cikin littafin Shafi na 146 Ga abin da Abu Basirin yace Na halarci churin Wata rana Sai na ce da shi Akwai wani al'amari fa na musamman ne tsakanin ni da kai yan gida ne ta yan gida ne za a yi na musamman ne amma sai tsakanin ni da kai. Ko akwai wani bari wanda ba namu ba a kusa? Sai shi Al Imam Ja'afar sai ya daga labulen da ke tsakanin mu da sauran jama'a. Sai muka ga bamu ga kowa ba to ba kowa kenan to zo muyi sirri Allah gafarta malam. Sai ya ce Abu Basirin ka tambayi duk abin da kake so. Sai nayi mishi tambayoyi masu yawa gama da ilimin da sayyidina Ali ya tara da ilimin sauran ainihin limamai na shi'a. Sai liman yayi mani bayani ma'ana Imam Ja'afar Sadiq yayi mani bayanin al'amuran da nayi mai tambaya gama da ilimin sayyidina Ali dalla dalla to wannan kissa tana da matukar tsawo tunda na baka shafin da zaka je ka karanta shafin na 146 na Je ka ka karanta amma jikarshen ta abin da take cewa A wurin mu akwai Ja'afar Sai na ce da shi To kuma menene Ja'afar? Sai ya ce Wani buhu ne na ainihin fata wanda duk ilimin annabawa na ciki. Duk ilimin wadanda annabawa suka yi musu wasiyya yana ciki. Duk ilimin annabi malaman Banu Isra'ila na ciki. Sannan sai ya ce Kuma a wurin mu fa akwai qur'anin Fatima Allah ya kara mata yarda. Sai na ce ah malam menene kuma Sai ya ce Wani qur'ani ne da Fatima take da shi wanda ya ninka wannan qur'anin naku kashi uku ya ninka qur'anin ku kashi uku. Kuma ka tsaya ka ji da kyau ya kai a babasir na rantse da Allah Ko harafi daya daga cikin qur'anin ku babu kuma ya ninka naku uku kuma qur'ani ne Fatima ta ruwaito ita ma daga baban ta annabi sallallahu alaihi wa sallam. Ya jama'ar musulmi ku rinka mana adalci. Wadannan abubuwan da muke fadi kamata yayi in abubuwan nan sun yi muku zafi a hada komitin majalisar malamai a neme mu mu zo mu kara kan mu a irin wadannan abubuwan. Raddi da bakar magana ba zai biya muku bukata ba saboda wadannan abubuwan iyakar karfi yada su muke yanzu jiya war haka ina gwagwala dattan gaba da Abuja ina ta yada irin wadannan abubuwan. Nan da mako mai zuwa ina wani garin haka muke ta yada wadannan abubuwan idan sharri ne muke yada wa in kuna ganin mu akan bata ku zo ku shiryar da mu. Idan alheri ne ku tabbatar da wadannan abubuwa domin me a hada karfi da karfe na ilimi a rugurguje sharrin wannan shi'a dan in kana ganin cewa kai ka kubuta yayan ka fa jikokin ka fa ta taba kunnen ka fa zuriyar ka fa Wannan ba sharri ne wanda yake saboda kungiyanci zaka je kai ne dan kungiyar Izala ka je ka hade kai da yan shi'a saboda zaku yi fada da su Albani ka je ka hade kai da yan shi'a kai ne dan darika zaku yi fada da su a wannan su Albani sun tashi suna kare addinin musulunci ne qur'anin da kake da shi kai Alaramma malam wane kai gwani wane kai gangaran wane ko wanene kai ka ji sun ce suna da nasu qur'anin wanda ya ninka naka uku. Sannan harafi daya daga cikin naka babu. Kasancewa dan da ka haifa ko yar da ka haifa ko jikan ka ko jikanyar ka nan gaba ba za a fito da irin wannan qur'anin a koya mata ba? Jama'a muna fahimtar abubuwan nan da kyau ko? Shi yasa wannan ba har mu ba kungiya bane mu ba kungiyar kowa bane duniya mu mu musulunci muke wa yaki. Don haka ko ka zo a hada karfi a hada karfe a tafi ko baka zo ba Baushe yace gaskiya dokin karfi Gaskiya dokin karfi bata bukata a bata ciyawa ko a bata mai a a da karfin Allah take tafiya tafiya ce wanda yake da i dubi yan shi'a irin ta taimaka musu fasikan masu kudi su taimaka musu amma har yanzu sun kasa kai labari duk kasan nan babu wani mai kudi ko gwamnati da take taimaka mana duk duniya babu wata mai kudi wani mai kudi ko wata gwamnati da take taimaka mana Allah ne kawai yake taimaka mana amma gashi har yanzu ba a jin labarin su amma karkashin kasa suke bi suna yada wannan sharrin. Karkashin kasa suke bi suna yada wannan sharrin yayan ku da kuke turawa Islamiyya ba ku ne yan darika ba kun ce ba zaku kawo yayan ku wurin mu mu karantar da su addinin musulunci ba kun je kun ware kun kai su can suna can kasancewa ko irin wannan qur'anin ake koya wa yayan ku? Ba zaka yi nazari ba amma kai kana jin haushin Albani dan yace darika ka ba addini bace dan yace kungiyar ka tana bidi'a kai wannan haushin kake ji ka manta yakin maimai din da ake kokarin ayi don a samu tabbatar da gaskiya. Gashi yanzu daga littafin su ne ake karantawa kai tsaye usulul kafi ana fadin shi dalilai duk dan shi'an da yace ba haka ba ka ce a dakko usulul kafin a duba a gani shin ba za a samu haka ba? Wadannan maganganun da muke fadi an kasa mu kabalanta mu kuna jin karya muke fadi da tuni ba a ga bayan mu ba babu malamai ne a kasar ina sheikh wane ina imam wane ina sayyidi wane duk ba suna nan ba? Saboda haka ka saurara ka ji wadannan abubuwa da kyau ka dai ji wannan duk kamar yadda na ce maka so mun tabi ne ake ka san aka ce yau jaji beri ana so ya kaji da daddare zaka ga yara sun je sun kewaye murhu ko ana dan gutsuran musu fufuke suna ci ana dan gutsuran musu hanta suna ci ma'ana so mun tabi ne gobe akwai lashe lashe kenan a gidan ko yanzu so mun taba ake gobe akwai jawabi Insha Allahu jama'a mun gane wannan da kyau ko? Allah madaukakin sarki ya shiryar da mu. To dan ka ji me ne misalin wannan qur'anin nasu bari mu karanto maka Alaramma ka haddace qur'ani yaushe kararka 30 ko 60 ka rubuta qur'ani kai ne Alaramma mai 60 ko Alaramma mai 80 ka tsaya ka ji wannan ayar ba zan karanto daga saman qur'ani ba muyi wa wasu yan Islamiyya karatun su bai kai ba za a karanto ne inda wannan in muka bar yan shi'a da yan Islamiyya kawai ta ishe su. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Gashi dai ainihin a cikin usulul kafi din nan shafi na 200 da 66 Abu Basirin yace aka ce yace daga baban Abdullahi amincin Allah ya tabbata gare shi shine Al Imam al Bakir kenan. Game da maganar Allah madaukakin sarki cewa Alaramma idan mu ne yan Izala suka karanta wannan wani sharri zaka yi mana? To ka ji yayan ku yan shi'a ka ji cikin littafin su gashi suka ce Yace yadda ka ji din nan Yace na rantse da Allah Jibrilu ya sauka da ita ga annabi Muhammadu. Shafi na 266 Wannan littafin usulul kafi kamar matsayin littafin Bukhari ne a wurin mu musulmi wanda malam Abdullahi Gwandu babban waliyin Allah kanin waliyin Allah yake cewa Wannan littafin Bukhari matsayin shi da ka ji malam Abdullahi Gwandu yace yace bayan al'qur'ani sai Bukhari to a wurin shi'a bayan al'qur'ani sai usulul kafi gashi usulul kafi ya ruwaito cewa Mai tambaya yayi tambaya gama da tabbatar ciyawar azaba da babu makawa sai ta faru. Kafiran da suka kafir cewa cewa Aliyu shi ya cancanta ya karbi halifancin manzon Allah wadanda suka kafir cewa wannan wilayar babu abin da zai tunkude musu wannan azabar wallahi wannan Wannan dugo ne daga cikin tekun sharrin da ke cikin usulul kafi sai gobe zan buga maka misalai akalla biyar zuwa goma. Kowanne a ne ana kawo maka shafi insha Allahu duba wuri kaza in an yi ruwa gobe mu hadu da kai lahadi in an yi ruwa lahadi a hada litinin Insha Allahu Jama'a an gane wannan da kyau ko? Saboda haka jama'ar musulmi wannan takaitaccen dan tabawa ne aka yi fa. To kun ji fa Karerayin kadan daga ciki kenan amma sai a je a ce muku shi'a son ahlul baiti ne mu bamu san ahlul baiti saboda kaunar ahlul baiti a Najeriya In aka haifi ta gwaye kai tsaye sai a ce sun zo da sunan su ne saboda girmama manzon Allah saboda girmama jikokin shi girmama Hassan da Hussaini da an haifi ta gwaye sai a ce ai da sunan su suka zo Hassan da Hussaini. Bamu kauna ahlul baiti? Saboda girmama ainihin ahlul baiti ba gidan da zaka je a Najeriya akwai yan mata guda biyar babu Fatima ina gaya muku Fatimo min da ke Najeriya na rantse da Allah da irin da Saudiya in ka tara babu su. Fatima da ke Najeriya Fatima Fatima Fati Fanta Batulu Binta duk sunan yar manzon Allah ne ake neman a sa Zara in ka je Kano duk in ka ju in ka tafi wajen yola in ka je an ce Batulu Fatima ake nufi in ka je mai duguru in ka je an ce Fati ko Fanta Fatima ake nufi tsakanin Zazzau Katsina Sokoto in ka je an ce Binta Fatima ake nufi duk gashi na Fatima Zahra'u duk yar ma'aiki duk Ba haka bane? To bamu kauna ahlul baiti? Sannan in kana ja wani ya mike yau ya zagi Fatima yar gidan manzon Allah ka gani ka ga aiki da cikawa Wani ya mike ya zagi Hassan ko Hussaini wani ya mike ya zagi sayyidina Ali ka gani Amma kun je sun gaya muku karya su baku littafi mana su karanta muku a littafi su koya muku mana yanzu ba littafin al adabul mufrad muka sa ba shekara 1200 da wani abu da rubuta littafin a saka muku littafi irin wannan na shi'a a karanta muku mana amma kawai an hada ku da jaraba jarida bayan shekara 10 shekara 20 wahalhalu sun maka yawa sai ka dawo ka natsu kana natsuwa kuma sai ka gane akan bata kake kuma ka riga ka yi asara Guda nawa ne yanzu suka yi irin wannan nadamar suna nan sun rayuwa ta rikita su su rasa gaba zasu yi ko yamma kudu zasu yi ko arewa kashe kan su zasu yi ko ridda zasu yi Ana ana fada maka gaskiya yanzu zafin kai ya shiga kan ka wai ana kin zazzaki waye waye zazzaki da za a ki shi wani menene zazzaki Me zazzaki da za a ki shi waye shi da za a ki shi malami ne ko mai kudi mai sarauta ne ko kuwa me yake da shi da za a ki shi Ba abin da Allah ya mishi baiwa wanda za a yi mishi hassada da shi ka kaba rayuwar shi Balle ka ce ana mishi hassada limanci in aka nada shi ba zai iya limancin ba bai iya karantun qur'ani ba sai kuri wai ya haddace qur'ani ya haddace qur'ani wasa ne Ana gaya maka gaskiya ka haukace soyayya da kiyayya su suke hallaka yan bidi'a kana son wane shikenan ka rufe ido baka san wane shikenan ka rufe ido. Allah ya shiryar da mu. So da haka jama'ar musulmi kun ji in kana son bayanin shi'a abin da yasa mun dade ba a yi bayani akan shi'a ba. Shi yasa ya kamata a tsaya a tattauna abubuwa gobe din nan insha Allahu ta'ala a natse za a kawo abubuwa dalla dalla Najeriya kuma kasuwa ce Ku kafa wa'azi kuma ku fadi naku mu ma mu fada jama'a sune ainihin alkalai sai suyi adalci su ga waye ke da gaskiya ku bude ku karanta kamar yadda muka bude muka karanta. Amma sai a zo wai da jarida wallahi ga Fahad da Cross ba Fahad ba Faisal ko Mas'udu karewar Saudiya kenan Mas'udu ko Faisal a ganshi da fafaro ma a ka Me ruwan mu me ya rage darajan mu? Fahad shugaban mu ne? Fahad sarkin gargajiya ne irin na kauyen ku. Dan Fahad ya sa Cross sai me wai wallahi Fahad ne da Cross To Fahad dan ya sa Cross sai me Ka je ka yi karatu wallahi in ba haka ba zaka yi nadama ba boko ba mahamadiya ba sana'a addinin musulunci ba addinin yan iska bane ba addinin masu tsiwa bane karatu ake zuwa ake sanda muke karatu a angon na lokacin ku kuna can kuna bakin sulman randa kuna iskanci kuna zina da yan mata kuna musu ciki kuna iskanci sai rana tsaka wai yaushe Albani ya karatu ka zo mana Kuma kai bude ka karanta mana muciya aka haife ka muciya aka haife ni sabon gira aka haife ka sabon gira aka haife ni zari aka haife ka zari aka haife ni ba zazzagi kake ba zazzagi kake bude ka karanta mana kai ma ka yada manufa yadda Albani yake yada wa. Ko hanaka aka yi an sa maka doka ne? Imam al Bukhari yace babin da ke bayani akan lallai da dole ne ya bi uwar shi da uban shi matukar dai ba sabon Allah suka sa shi yayi ba idan mahaifiyar ka tace sai ka je ka siyo mata giya ko mahaifin ka yace sai ka je ka ainihin shiga chacha ka je ka wakilce shi ba zaka bi ba amma ba zaka yi mai bakan magana ba ba zaka yi mai galatsi ba sai ka yi mai magana mai laushi amma ba zaka bi wannan magana ba. Ah ko? Ainihin wato Abu Darda'i sahabi annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallama ne yace manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yayi mani wasiyya da abubuwa guda tara. Sai kowa ya karkada kunnen shi wasiyyar gaskiya kenan. Wasiyyar gaskiya kenan ina ce maka fa ka je ka samu ne kasar din tatsuniyar wanda malam Mansur babban malamin hadisi ne a garin Sokoto yayi raddi ga zazzaki da wadannan sune yan sahun farko ma'ana sune lada nan zazzaki. Sune sahun farko su suke ta da ikama a ta da ainihin motar bata. Don haka duk wani tsohon kasat duk wata hayaniya ta shi suna nan da ita don haka gutsun shi a rike yake fam a hannun su suka tsaya suka yi kasat dalla dalla zaka ji inda ainihin aka dakko gashi wai yana karanta wasiyya fa wannan kuma kan ma ka ce tafiya da dadewa. shekara 6 da suka wuce shekara 6 da suka
[Segment 4/4 | 01:00:00–end]
[Speaker seg4-spk:0]
wai zazzabi bai iya karatu ba wasali Shekara shida da suka wuce a masallacin nan fiye da shekara goma mun karantar da na hauru wazi tuni na hauru wazi tuni yaran mu duk sun iya na hauru wazi sun iya na hauru Sun san Amma zazzabi wai ba sai yana ja sai malam Mansur sai yace a dan yorbas da kasar din sai kaji sai a ja sai kaji ya ja ya kasa kaje ka saurari kasar din da kyau don Allah in sharri muke zaka ji muryar shi ce in kasan muryar shi Wai sai wai kur'ani wai sai a Kur'ani Kur'ani wasa ne yaro Kur'ani Haba malam Kur'ani sai kaje ka koya malam Amma kaje ka karanta Mai sai da tumatur da albasa a bakin hanya ya iya boko ba wanda bai iya boko ba a Najeriya boko ba abun alheri bane da za'a ce dan ka iya shahar shikenan kai ka zama malami da haka zaka je kayi karanta abu da daddare kazo kawai da rana kana kallon harafin larabci kana dube daga Abubakarata wai Abubakarata ba ma Abubakarata ba daga Abubakarata Kaje ka koyi karatu Kaje ka koyi karatu In ba haka ba kaima abun da zai same ka kenan bayan shekara arba'in ace kaine amir din anguwarku amma baka iya tada baki ba Gashi dai wasiyyar gaskiya Abu Darda'i yace manzon Allah yayi mishi wasiyoyi guda tara Kaji wasiyyar farko yace kar ka sake ka hada Allah da komai koda za'a daddasa ka Koda za'a kona ka ka kafe sai kabi Allah ba shirka Annabi ya bada labarin wasu mutane guda biyu cikin Bani Isra'ila suna tafiya sai ainihin suka zo suka samu wasu jama'a sun kafa gungi a gefen hanya suka ce ba wanda zai wuce hanyar nan sai ya yanka wani abu ga gungi Aka kamo na farko to kai yaya zaka yanka koko mu dasa kanka sai yace a'a ku saurara ni ba abun yankan ne ai da da akwai sai a yanka ai larura Yace to to ko kuda ya gutsura kanshi da nufin gungi ya kama kuda ya gutsura kanshi da nufin gungi yana mutuwa Allah ya saka shi a wuta Wannan kuma kai yaya yace pau pau ba yadda za'ayi ba watta larura da zata sa a yi shirka Ko kuda bazaka tsinke kanshi ba don ka mutunta gungin mu eh to shikenan sai suka dasa kanshi yana mutuwa shi kuma sai ya shiga aljanna karanta littafin Fathul Majit Karanta ta Sirul Azizil Hamid Shi yasa gashi Annabi yace ahir kar ka sake kayi shirka ko za'a daddasa ka Kar ka sake ko za'a kona ka Ahir kar ka sake ka bar sallar farilla da gangan ahir manzon Allah ya ja kunnen ka Jama'a mun gane wannan da kyau ko to shikenan gashi lokaci yayi kuma muma lokacin sallar farilla yayi don haka zamu saurara in sha Allahu ta'ala bari mu saurara a nan In sha Allahu To kamar yadda muka ce jama'a
============================================================
[Part 7]
============================================================
[Segment 1/3 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yau asabar sha biyar ga watan na da shekara dubu daya da dari hudu da ashirin da biyu wanda ya dai dai da uku ga watan shekara ta dubu biyu da daya Allah madaukakin sarki ya gafarta mishi Wannan littafi ne daya tamkar da dubu akan babin shi domin ya karantar da ladubba na addini da na rayuwa wadanda rashin ladabi a musulunci ba karamin ta'adi bane ba karamar barna bace wadda zata iya rugurguza akidar ka ta rugurguza ibadar ka shi yasa malaman salaf da wadanda suka biyo bayan su ainihin wato sai suka dage suna ta rubuce rubuce game da tsarin ladabi da yadda mutum zai zauna lafiya tare da ainihin magabatan shi tare da sa'o'in shi tare da wadanda shi kuma yake sama da su yaya musulunci yace kaza tsari game da zamantakewar makwabtaka da musulmi ne da bamaguje ne da krista ne da bayahude ne da dan bidi'a ne yaya zamantakewa tsakanin kai da ainihin wadanda ka samu kanka a cikin mota maza da mata ne yara da manya a aji ne kafirai da makamantan su sallama musafaha da abubuwan dake da alaka da wadannan To yayin da muka dage ana ta karantar da mutane gwargwadon iyawar mu game da abinda ya shafi akida da al'amuran da suke da alaka da fannoni na ilimi sai ya zan wajibi ne kuma mu daga kai muyi waiwaye adon tafiya mu san cewa babu shakka akwai ladubba wadanda addinin musulunci ya ainihin nuna da tsare tsaren da suke da alaka da wannan to acan lokacin baya mun sanya littafin mun ainihin karanta shi duk da cewa wasu kasusuwa ne suka samu ainihin shiga cikin kaset wanda littafin shima yana daga cikin littafin dake karantar da ladubba da dabi'u na gari amma littafi ne tsari irin na malaman wadanda suka zo daga baya sai su fadi hadisi sai su fitar da malamin da ainihin ya fitar wannan dai dai ne alheri ne To wannan sai muka ga bari mutum uku tun daga asali irin su wadanda da dadewa su suka rayu to shine muka sanya wannan littafi nashi wanda shi kuma yana bin tsari ne irin na ainihin malaman magabata Shine a kawo isnadi tiryan tiryan shi kanshi littafin tukunna me ye isnadin littafin ta wace hanya aka same shi sai an kawo maka wannan sannan duk hadisi duk magana ta sahabi ko tabi'i ko wani malami sai an kawo maka isnadi to in aka kawo sai a ja baki ayi shiru a karshen shi ba dan komai ba domin a zamanin su Bukhari Malamai da daliban ilimi in har ka kawo musu isnadi to suna karanta isnadin sun san ya inganta ko bai inganta ba To da al'amari ya taho yayi rauni shine manyan malamai suka tashi suna ainihin bayyana matsayin kowane hadisi kamar yadda ainihin malamin Bukhari yake cewa da Allah zai mun tsawon rai irin shekarun da na baro a baya da sai kowane hadisi na rubuta shi kuma na rubuta matsayin shi a gefe ya inganta ko bai inganta ba To Imam al-Bukhari da ya taso sai ya biya ainihin hada littafi wanda tace hadisan annabi shine ainihin Wannan littafi karbabbe ne baki daya a wurin al'ummar musulunci cewa ingantaccen littafi ne ma a wanda yazo bayan al'kur'ani haka malam Abdullahi Gwandi ya fadi a cikin Malam Abdullahi Gwandu kanin shehu Usmanu dan hudu manya manyan waliyyan Allah kenan a cikin Najeriya manyan bayin Allah wadanda aikin su ya bayyana a wurin al'umma cewa wadannan mutane insha Allahu mutanen kirki ne shine yace Indai littafi ne a bayan al'kur'ani to Bukhari yafi duk wani littafin hadisi ko fikihi ko tarihi ko menene Bukhari yafi shi inganci bayan al'kur'ani Kowane littafi karshen makomar shi tana karewa ga Bukhari ne Sai kaji ance hadisi kaza hadisi kaza Wane da ya ruwaito hadisi kaza Muslim ne shi Abu Dauda Tirmizi Nasa'i in aka ce Bukhari ya ruwaito irin wannan hadisin sai a kara ganin na Muslim din da inganci da mutunci saboda Bukhari ma ya amince da shi Littafi ne wanda ya tattara sunnoni na shugaban halitta kuma ya kore duk abinda makaryata suke fadi suna dangantawa ga ainihin annabi A ina Bukhari ya rubuta wannan littafi sai malam Abdullahi yace A masallacin Ka'aba ya rubuta shi A wurin da aka haifi babban mutum wa kenan Manzon Allah Shine ya rubuta littafin asali a kasar su sai yazo Ka'aba ya zauna da musu waddar a hannun shi asalin sai ya bi duk hadisin da zai tabbatar sai yayi sallah raka'a biyu yayi addu'ar ya roki Allah in abin nan ya tabbata to babu shakka Allah ka natsar da zuciya ta a rubuta da yaji zuciyar shi ta natsu sannan sai ya bi sai ya haka ya hada wannan littafi Sallah dubu nawa raka'a dubu nawa kenan Duk hadisi daya fa akwai hadisi dubu bakwai da dari hudu da wani abu a littafin Haka Imam al-Bukhari ya biyayyi da ya gama sai ya daga sai yace Yace jama'ar musulmi ku bautawa Allah da wannan In anje lahira na yadda ku ce hujja nine nace kuyi na amince Kaji ba shehin darika ne da zai tashi yayi ihu yace a'a sai yace ma'ana gashi cewa yake daga malaman shi sannan zuwa ga annabi Duk wani hadisi in Bukhari ya ga yana ciwon kai ko yana girgidi shi sai ajiye shi gefe guda sai yace ba dai nan ba To da ya tayamma rubuta sauran littattafan shi sai bai ajiye wannan ka'idar ba irin su da da littafin shi da sauran littattafan shi irin wannan da zamu fara karantawa sai yayi tsarin kawai a dai kawo hadisi ya inganta ko bai inganta ba to shikenan ana nan sai wasu shekarun baya da suka gabata babban malamin hadisi Allah ya gafarta mishi Sai ya zaunar da matan aure yana karantar da su wannan littafi na ya neme musu wa'azi da shi yana koya musu ladabi da ladabin manzon Allah Ma'ana wadannan yara yan mata ne matan aure ne in aka ladabtar da su da irin ladabin manzon Allah shikenan sai al'amari yayi mana sauki duk yayan mu in suka taso sai iyayen sai su ladabtar da su da ladabin manzon Allah Baka ji kamar yadda ainihin ya ruwaito a cikin da isnadi ingantacce duba littafin ainihin yace Goggon mu Aisha ta kasance tana zaunar da mu tana koya mana tafiya Me yasa take koyar da su tafiya manzon Allah yayi tarbiyyar ta Abubakar as-Siddik yayi tarbiyyar ta yau ba gashi an huta ita take tarbiyyar ahalin Abubakar ba jikokin Abubakar ba ita take tarbiyyar al'umma ba to shine malam Muhammad Nasir Din al-Albani ya zaunar da ainihin wato mata yana karantar da su wannan littafi Malam Muhammad Nasir Din al-Albani yana da Wato ko kwanti ragi wanda ya daukarwa kanshi tsakanin shi da Allah akan har ya mutu Gabatar da sunna a gaban ainihin al'umma sunna da kake jin labarin tadda tayi nisa sai yace to gata za'a gabatar maka dan haka masallaci kaza yasa karatun hadisi masallaci kaza yasa karatun hadisi matan aure yan mata samari yana karantar da su da tafiya tayi tafiya babban malami Allah yayi mishi arziki ya samu kudi yadda zai iya zuwa gari kaza ya sayi gida ya gina masallaci sai kuma ya kafa karatuttuka kasa kasa shine kasan masar zai je ya kwana bakwai ko yayi wata guda kasa kaza yaje kaza haka shi yasa sai aka waye gari ya gama cin duniya da yaki indai game da yada sunna ne duk inda kaje sai kaji ance To yana nan yana karantar da wadannan mata sai ya zan acikin wannan littafi akwai hadisan da yake wasu basu inganta ba To sai yace wa matan wannan hadisin bai inganta ba wannan bai inganta ba wannan ya inganta ah to malam ba Bukhari bane sai yace ai wannan Bukhari wannan ba sahihul Bukhari bane shi kanshi Bukhari ba ya tattara ingantattu bane dan haka yace Ladubba ne kawai duk abinda aka danganta ga annabi sai dai koda masu raunin daga ciki ba rauni ne wanda yake rauni yayi tsanani kwarai da gaske ba don haka sai suka ce to me zai hana Bazai ainihin taimake su a gefen kowane hadisi a rubuta matsayin hadisin ba shikenan da yake manyan malamai ne Allah ya huwace musu abun Allah ya musu fatahi Shine malam malamin da ya zauna kawai sai ma yayi baki daya ya wara sahihan ya wara da'ifan shine nan dake gaba na gashi Gashi Acikin shi akwai hadisi dari tara da casa'in da uku dukkan su wadannan tsakanin ingantattu da kyawawa wadannan da aka ware ba abinda ya rage anan kawai sai aiki Don ko isnadin babu kawai kaza sai ace sahihi dan neman karin bayani da ilimi sai yace amma in kana son kaga ina aka kwana ina aka tashi koma ka karanta littafi na kaza nayi cikakken bayani yadda aka yi zama sahihi ko Hassan ko makamantan haka sai kuma yace dadin gushi Bukhari ya fitar da wannan hadisin a wuri kaza a littafin shi Tirmizi ma in ya fitar kaza haka aikin da yake nan sannan ya taho kuma hadisan kuma da basu inganta ba na cikin yazo ya ware Gashi shima dai su kuma hadisai dari biyu ne da goma sha bakwai a ciki Jama'ar musulmi mun fahimci wannan da kyau ko to wannan ainihin harkar sai ta zan Babu shakka kashe wutan nan malam Jama'a mun gane wannan da kyau ko sai ya zan wannan harkar tana da matukar bukata akan al'umma su tsaya su bi wadannan ayuka daya bayan daya to shine sai muka ga abinda ya kamata shine wannan littafin nashi azo a karanta To ana nan kuma ba da dadewa wannan ba sai dai har wa yau Dake ainihin kasar Saudi Arabia sai suka tayarma malam Muhammad Nasir Din al-Albani cewa Allah gafarta malam kai mana arziki aikin nan da kayi ka ware nan ingantattu nan kuma wadanda basu inganta ba ka hade mana aikin ka bar littafin a yadda yake sai ka rubuta mana matsayin kowane hadisi a gefen shi ko a karkashin shi sai a buga dan ya zama yanzu ga al asalin Tare da hukunce hukuncen yadda Bukhari yayi shi kuma gashi Shine malamin dai alkalamin shi bai gaza ba shi kuma bai gaji ba sai ya tashi yayi wannan gashi ainihin Ka ganshi gashi Jama'a mun gane wannan Shine wannan shine al Allah madaukakin sarki ya gafarta wa Imam al-Bukhari to wannan ainihin shine littafin da in Allah madaukakin sarki yaso zamu fara karanta shi daga yau din nan in Allah yaso ba dan komai ba domin mu ladabtu mu kara samun ladabtuwa mu sake ainihin wato fahimtar abubuwa wadanda suka zo na ladabin manzon Allah domin wannan shine kadai al khairi gare mu Shi dai al Imam al Bukhari An haife shi a halin mahaifin shi ya rasu ma'ana an haife shi maraya kenan ko talle kenan ko audi Audi kenan Imam al Bukhari audi ne kenan ko an haife shi baban shi na ciki kamar yadda aka haifi manzon Allah nashi mahaifin yana ciki Na'am shi yana ciki eh baban shi ya ainihin rasu Jama'a mun gane wannan da kyau ko to an haifi Imam al Bukhari ne a ainihin wato ranar goma sha daya ga watan Shawwal hijran annabi na da shekara dari daya da casa'in da hudu An gane wannan dari daya da casa'in da hudu Sannan ya rasu a daren karamar sallah wanda ya dai dai da daren asabar dai dai da ana cikin sallar isha shi kuma ya rasu To shikenan ba'a same mishi jana'iza ba sai kashe garin wannan rana ranar asabar kenan ana bayan sallah azahar akai mishi ainihin abin nan sallar jana'iza akaje aka rufe shi a garin Garin gari ne dake tsakanin su da sauran su din nan kabarin Imam al Bukhari yana nan a wannan wurin ya rasu hijrana da shekara dari biyu da hamsin da shida in ka lissafa zaka ga yau Imam al Bukhari shekarar shi dubu daya da dari daya da sittin da shida da mutuwa Dubu da dari daya da sittin da shida da mutuwa ma'ana wannan tsohon littafi ne kenan ko a ha don mutanen kasashen mu an batar da su sai ace wai ai an ance wai ku rinka karanta tsohon littafi to yanzu dai wannan tsoho ne dan duk abinda aka ce yau shekarar shi dubu daya da dari daya da goma sha shida da sittin da shida marubucin kenan da mutuwar shi ai tsohon dan duk duniya yau babu sa'an shi Ko ko akwai Jama'a mun gane wannan da kyau ko to a karkashin wannan ainihin ba hujja bace wannan ma magana ta tsuniya ce kawai wadda ake karantawa cikin ta'alimi ai mai ta'alimi yace a rinka karanta tsohon littafi ah da ake karantawa sabo ne ko tsoho To kuma menene tsoho tsoho ai shine in ya kasance bayan sabo yazo ne ake gane wannan tsoho ne ko shiyasa babu hujja duk gaskiya ana gane ta ne da kasancewar ta gaskiya da hujjojin ta ba wai dadewar ta ba In ba haka ba yau shekara dubu nawa ana kafirci a duniya Dadewar kafirci a duniya ya nuna shine gaskiya ah ah gaskiya tana tabbata ne saboda itace gaskiya saboda ainihin dalilan ta Allah madaukakin sarki ya shiryar da mu wannan bugu dake hannu na itace shekarar da malam Muhammad Nasir Din al-Albani din ya rasu kenan wanda tayi dai dai da hijrana da dubu daya da dari hudu da ainihin sha tara kenan Shi ko malamin namu Muhammad Nasir Din al-Albani an haife shi hijrana da dubu daya da dari hudu da talatin da uku wanda ya dai dai da aka haifi Muhammad Nasir Din al-Albani ya rasu kuma ainihin wato daren ashirin da bakwai ga hijrana da dari daya dubu daya da dari hudu da ashirin dai dai ana dai dai lokacin sallar magriba shi kuma Muhammad Nasir Din al-Albani Allah ya mishi rasuwa A wannan daren aka rufe shi shi yasa wasu ma dake layin da ya rasu basu ma san albani ya rasu ba sai da gari ya waye tukunna to da yake malamai ne na sunna daliban shi kuma daliban sunna ne ba ruwan su da alfahari ba ruwan su da abubuwa nan da nan aka kinkin tsashi nan take kawai ana cikin ana cikin gida ana wankan gawa ana abubuwa nan kuma suna nan suna bayyana a mutane a kofar gida ga yadda sunna tace ga yadda sunna tace shi kanshi malam ya karantar da mu ga yadda ya rubuta cikin nan da nan akaje akayi jana'izar shi sai da gari ya waye Sannan ma akaji ai Muhammad Nasir Din al-Albani ya rasu a kasar ainihin Jama'a mun gane wannan da kyau ko to shi Muhammad Nasir Din al-Albani ya ainihin wato rasu a wannan ranar kamar yadda kaji ranar Laraba ce randa ya rasu din Laraba ce randa ya rasu sannan dai dai dai da shida ga watan shi kuma ya rasu yana shekara talatin da biyar a duniya shekarar shi talatin da biyar ko da shida gwargwadon yadda lissafin kamariya ko shamsiya wato lissafin kalandar boko ko kalandar arabiya amma dai talatin da biyar zuwa talatin da shida shine ainihin shekarun shi a duniya Yau shekarar shi biyu ba wata daya da yan kwanaki kenan ma'ana wata mai zuwa in ashirin da bakwai saba'in wata da bahaushe ke cewa ya ko to saba'in wata nayi na watan gobe shikenan albani shekarar shi biyu kenan da ainihin rasuwa Allah madaukakin sarki ya gafarta musu baki daya A lokacin da ya rubuta wannan littafi su da zasu buga sai da suka je suka nemi izinin shi wannan shine rubutun hannun Muhammad Nasir Din al-Albani gashi Wannan shine asalin rubutun hannun nashi kenan shine ainihin ya basu izinin cewa ya mallaka musu wannan littafi suje su cigaba da bugawa da yawun shi Allah ya gafarta musu An gane wannan da kyau ko to sai zan ya tattaro kamar bugu uku na wannan littafi daba'a uku na wannan littafi akan su ne ya biye wannan aiki Wadannan bugu guda uku gashi bugun farko Sannan ga kuma Sannan kuma ga An gane wannan da kyau ko to wannan littafi saboda yadda yake da matukar muhimmanci malaman hadisi suna son wannan littafi kaje ka ainihin karanta littafin Zaka ga bayanai sosai an rungumi littafin nan a kasar India domin malaman sunna na kasar India kaunar manzon Allah ta kai musu matuka yadda in ka tashi auren da yarka zaka je ka siyo To wannan shine to shi
[Segment 2/3 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
mafi girma a duniya da ake wa 'ya musulma a Indiya.
[Speaker seg2-spk:1]
Allahu Akbar.
[Speaker seg2-spk:0]
Idan madadin ma'ana kai da kake sayan Honda Accord, ka sayi ka hala, ka sayi menene, duk abin da kai kake ganin ka gina wa 'yar ka gida, kayi kaza, kayi kaza, su ahlu sunnan Indiya sai mutum ya karantar da 'yar shi al qur'ani da sunna. Ranar kaita sai a dauko qur'anin nan sai a aza akan sahihul bukhari, sai a ce wannan ita ce wasiyyar da baban ki ya miki. Qur'ani da sunna, ba hala ba, babar su waja ba ba, a'a qur'ani da hadisi baban ki ya baki ki je gashi nan shi aka koya miki shi ne kan gidan ku.
[Speaker seg2-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg2-spk:0]
Mun fahimci wannan da kyau ko? Eh, ka san akwai irin wannan, sanda muka tashi muna hara sai mu ji kakannin mu wai kai ka sayo tinkiya kana kiwo, tinkiya ce kan gidan ku. Wai ashe abin da ba haushi yake nufi wai ta karbi kakan ku, indai kuna kiwon tinkiya tana albarka tana haihuwa, to mu kan gidan mu ya tashi daga tinkiya ko akuya ko kaba fara ya koma al qur'ani da hadisi shi ya karbe mu. Jama'a mun fahimci wannan da kyau ko? To shine sai aka samu wani babban malami mai kaunar manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama mai suna wanda A kasar Indiya, babban malami ne a kasar Indiya sai yayi sharhin wannan littafi a cikin mujalladi biyu sai ya yanko sunan shi sai ya hada da sunan ya sawa littafin suna, ya sawa littafin Gashi mujalladi biyu ne wannan kamar yadda ka gansu haka manya manya to wannan guda ne daga cikin guda biyu manya manya ga su. Sharhin da na wannan littafi Don haka duk sanda ka ji mun ce jilani to jilani ba wancan jilani na dangi kanawa ba da suke cewa jilani babu ta kaddama tun loton ai sama ai kasa Allahu ta'ala mai dika ya fifita kaza kaza to ba wannan jilanin ba ba siyyid Abdul Qadir ba siyyid Abdul Qadir shine jilani shima ana danganta shi jilan zuwa ga angon su jilan. Mun gane ko? To wancan siyyid Abdul Qadir al jilani Allah ya gafarta mishi to duk sanda ka ji mun ce to wannan muke nufi shine sunan da bahaushe ya mayar zailani. Jilani ne ana iya cewa jilani ko kailani gashi nan zaka ji almajirai a Kano suna waka Kanawa kenan. Jama'a musulmi mun gane wannan da kyau ko? To shine zamu fara karatun wannan littafi sai Bukhari yace Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Muke mai? Shine malamai suka ce sai a ce Malaman Kufa da malaman Basra sai suka yi sabani kun san kamar yadda a fiqhu ake da Hanabila a Hanaf, Hanabila sannan Malikiya Shafi'iya wanene to sai ya zan a nahawu kuma ana da manyan mazhabi guda biyu da Kufa da Basra a ce wane Kufi ne wane Basri ne mun gane wannan da kyau ko? To sai suka ce in aka zo sai a ce da sunan Allah mai rahama mai jin kai nake farawa ko farawa ta. Wasu kuma suka ce a'a tun farko sai ka ce ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jin kai ko kuma farawa ta da sunan Allah mai rahama mai jin kai. To duk sanda ake jayayya wace fassara ta kamata ayi sai a ce ayi To da akai kuma sai ya zan har yanzu da sauran matsala shin shi wannan wanda za a za a ko koko ko haka dai suka yi wadannan maganganu ga su nan mafi kurkusan inda zaka je ka samu tafi ka je ka samu sharhin littafin na ainihin wancan malami An nabhani wanda malam Yusuf an nabhani ko nan zaka je ka ga ina aka kai akan Ala ayyi halin duk yadda ka fadi daidai ne in sha Allahu. In kace ina farawa da sunan Allah mai rahama mai jin kai ko farawa ta da sunan Allah mai rahama mai jin kai ko da sunan Allah mai rahama mai jin kai nake farawa ko da sunan Allah mai rahama mai jin kai nake farawa ta duk daidai ne. An gane wannan da kyau? To mai kake farawa? Nake fara karatun littafin To shi Imam Bukhari yana da dabi'a shi baya mukaddima ga littafin shi mukaddima sai ya ce Allah ya ce annabi ya ce ita ce mukaddima. Domin mala'ika Jibril da yazo wa annabi sallallahu alaihi wa sallama ba wata mukaddima yayi ba ni ne kaza ni ne kaza ni ne kaza zuwa yayi kawai yace Yayi karatu. Da mai ya fara? Da qur'ani ba haka bane? Don haka Bukhari sai ya ce to mu dauki dabi'ar da Allah yake saukar wa da annabi wahayi. Da yazo sahihul Bukhari ma sai ya ce Fara wahayi. Allah ya ce annabi ya ce shikenan da ya gama sai kuma ya ce Tunda an saukar da wahayi ya rage mai? Imani. Bayan imani kayi imani sai ka zauna jaki ba karatu sai ya ce karatu ilimi. To sai mai? An yi ilimi sai mai? Sai aiki sai ya ce Shikenan karatu ya tafi karatu can da ya kawo ayyukan imani sallah azumi kiyamul laili sadaka biyayyar iyaye duk ayyukan imani ne. Karshen littafin kuma sai ya ce Akida tauhidi. Jama'a mun fahimci wannan da kyau? To nan kuma sai ya ce Babin maganar Allah madaukakin sarki Lallai mun yi wa mutum wasiyya dan adam mun ja kunnen ka mun umarce ka muna maka kasheidi lallai ka kyautata wa iyayen ka. Abin da yasa wannan littafi ladabi za a koyar da kai. Duk ladabin duniya to ya kare akan ainihin uwa da uba. Domin su shi Allah madaukakin sarki ladabi gare shi shine ka bauta mishi to sai Allah ya ce Allah ya riga ya hukunta lallai kar ka bauta wa kowa sai shi To ashe kyautatawa din nan ita ce ladabi to ka kyautata wa ogan ka a office, kin kyautata wa mijin ki, ka kyautata wa abokin zaman ka to duk wadannan kyautatawa daidai ce amma kyautatawa mafi girma ita ce ka kyautata wa iyayen ka. Jama'a mun ji yadda sunna take ladabi ko? Mun ji yadda al qur'ani yake karantar da tarbiyya ko? Duk mai neman tarbiyya da ladabi ya koma al qur'ani da hadisi zai samu tarbiyya da ladabi. In ya rabu da al qur'ani da hadisi shikenan ba tarbiyya babu ladabi. Yanzu baku gan wasu shaidanu da suka koma suka rabu da al qur'ani da sunna ba suka koma suka kama ladubban kafirai wai yanzu ana nan ana tunanin yaya za a dinga koya wa mutane jima'i. Shi wanda zai koyar da jima'in uban waye koyar wa uban shi sanda zai sadu da uwar shi yayi jima'i ya haife shi. Jama'a kun ga wannan duk rashin kunya ake son a karantar da 'ya'yan ku a makarantun sakandare da makamantan su wajibi ne iyaye su binciki wannan jima'i ana koyar da ladabi waye koyar wa binsuru yadda ake jima'i. A wane littafi ya koya? A wace sakandare? A wace jami'a? Waye HOD din su? Jama'a mun fahimci wannan da kyau? Wannan na daga cikin shedancin bature shi yasa kar ka ga ka sa dan ka makarantar boko ka sa dan ka ai kaza a'a lallai ne ka rinkai kana koyar da shi ainihin ladabi shi yasa ainihin ya fara kawo ladabin farko shine ayi ladabi ga uwa da uba saboda sune mutane mafi girma bayan Allah da manzon Allah sallallahu alaihi wa alaihi wa sallama Allah ya shiryar da mu. To a nan ne in ka gane wannan ya kai mai saurare na sai ka san cewa Ashe inda za a bi irin wannan tsarin a ladabtar da mutane da an samu 'ya'ya irin su Aisha. Domin Aisha tashi tayi kawai ta ganta an haife ta a musulunci haka ta ce Ta ce kawai tashi ne naga ainihin uwa ta da uba na Abubakar da Ummu Ruman tashi kawai ne na gansu suna addini suna sallah. Su Abdullah dan Umar tashi suka yi suka ga su Umar suna sallah. Ka duba yadda suka zama mutane masu ladabi masu mutunci su Ibn Abbas to haka gashi dai Imam al Bukhari yanzu ya karantar da mu wannan ladabi. Amma sai ya zan malamin da ya ruwaito littafin sai da yayi fara kawo isnadin shi yaya yayi ya samu littafin waye karantar da shi littafin a wace shekara a ina da yaushe Sai ya ce Wannan malami da ke ruwaito mana Bukhari yace Baban Nasr ya bamu labari wanene baban Nasr shine Ahmad dan Muhammad dan Hassan dan Hamidu dan Haruna dan Abdul Jabbar dan Bukhara. Bukhara din gari ne a yanzu yana cikin kasar Rasha yana karkashin tarayyar Soviet ko ya fada Bosnia ko ya fada Albania ko ya fada Kosovo yana dai karkashin tarayyar Rasha tarayyar Soviet din nan. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Dan haka Imam al Bukhari gashi da shi da almajiran duk da suka ruwaito wannan ba balarabe bane kamar yadda Shehu Usmanu ba balarabe bane ba fulatani ne Abdullahi Gwando ba balarabe bane ba fulatani ne Abubakar Gumi ba balarabe bane ba fulatani ne haka duk ga su nan manya manyan malamai wannan ya rage daraja? Bai rage daraja ba don haka duk wanda yazo yace bature ne sai ka ce gaskiya ne mai kake nufi da bature turanci ba yare bane? Koko turanci ba yare bane? Yare ne to fillanci mai? Yare Sokotanci mai? Yare ne Hausa mai ne? Yare ne in ya muranci ya rabanci nufanci duk menene to zaka kawo mana kabilanci ne cikin musulunci. Risala da kake aiki da ita ai mai risala ma bature ne mutumin Spain ne ba balarabe bane. Mukhtasar ba balarabe bane Spanish ne shima mutumin kasar Spain ne Andalus. Mai askari ne kadai balaraben kasar Iraki mai iziya kuma balaraben kasar Masar dukkan su ba balaraben Saudiya duk fiqhun da kuke bi ba balaraben Makkah ko Madina duk fiqhun naku. Jama'a mun gane wannan? Shi yasa ba kabilanci a cikin addinin musulunci gashi mutumin kasar al Bukhara ne yace An fi sanin shi da Ibn Nazzaki Sai shi wannan Abu Nasr din nan sai shi mai bamu labari wanda ya ruwaito wannan littafi sai ya ce Na ja baki ne Malam yayi min fassara kuma ya tabbatar da karatun nawa ma'ana ba malam ne ya ja baki ya fassara ba a'a ni ne na rinka karantowa malam ya nemi mu na fassara. To yaya akai sai ya ce Ya iso gare mu ne bayan ya dawo aikin hajji a ainihin shekara ta 300 da ainihin Shi wannan malami Abu Nasr sai ya ce Abu Khairi ya bamu labari waye Abu Khairi shine Ahmad dan Muhammad dan Jalilu dan Khalidu dan Hurais al Bukhari shima mutumin Bukhara ne. Al Karmani a kasar Bukhara din to dan garin Karman Karman din gari ne a cikin ainihin kasar Bukhara kamar a ce dan Najeriya dan ina sai a ce dan Ibada a Najeriya din. Al Abqasi sannan dan kabila Abqas al Bazzar sannan ainihin al Bazzar ma'ana sai aka danganta shi zuwa ga ainihin sana'ar shi. A shekara ta 322 ya karantar da mu To kun ji wannan shine almajirin Bukhari dan haka in aka ce waye almajirin Bukhari da ya ruwaito Ka gansu nan shine wannan. Shine ya koyo wannan karatun wannan littafi a wurin Bukhari. To sahih na Bukhari shi kuma firyabi ne ya ruwaito shi. Za a zo sai randa aka zo karatun Bukhari in sha Allahu nan kuma za a yi bayani akan wannan amma kowanne ka iya rike abubuwan daban daban kar ka ji ana karatu a ce ka dauka a'a ake karantawa. To shine shi kuma shi wannan Baban Abdullahi ya bamu hadisi waye baban Abdullahi shine Muhammad dan Isma'ila sunan Bukhari kenan dan Ibrahim kakan Bukhari sunan shi Ibrahim Ibn al Mughira baban kakan Bukhari sunan shi Mughira Ibn al Ahnaf kakan kakan Bukhari sunan shi Ahnaf al Ju'afi ba Ju'afi ya musulunta a hannun su ne shine ake danganta shi zuwa gare su kamar yanzu kai bahaushe a ce ka musulunta a hannun wani ba nufi in ka zo rubuta tarihin ka sai ka sa Ahmad dan Muhammad dan Idris dan wanene dan wanene bahaushe ba nufi sai a ce ya akai ka zama bahaushe ba nufi sai ka ce ni asali na bahaushe ne nufawa kuma iyayen gida na ne dan so suka musulantar da ni. Jama'a mun gane wannan? Al Bukhari mutumin ainihin kasar Bukhara To duk sanda ka zo yanzu zaka karanta wani isnadi tun daga kan wannan na farko da ka ji har na karshe to a ka'ida wurin malaman hadisi shine zaka yi dayan abu biyu. Duk isnadin da ka zo zaka karanta a farko sai ka ce Mai ake nufi da Don in ka zo kawai ka ce Sai ka ce yanzu kai ne almajirin wannan din kenan ma'ana matsayin ku daya da Bukhari amma tunda kana karanta littafin Bukhari ne to sai ka ce Ai wa Bukhari ya ce To ko kuma ka zo kayi shiru sai ka fara da amma ka san akwai ta a rubuce. Dan haka malamai suka ce duk irin tsakanin ko da babu a wurin a rubuce to dai akwai ta. Mun fahimci wannan da kyau ko? To shine ya ce Kun ga Imam al Bukhari sai ya fara da sarkin malamai kenan a kasar ainihin wato Basra ko a kasar Kufa a kasar Kufa in sha Allah babban malami ne kwararre wanda ya kai matuka a hadisi Na ji Abu Amr yana cewa Mai waccan nan gidan ya bamu labari. Domin kalmar ce mace ce. To dan haka To Hausawan Kano da Sokoto basu da ita da hausar su dan haka da sai bahaushe ya ce wannan. To wannan gwaranci ne zagi zagi zagi zagin kuma na kudu da zariya sune suke banbance wa duk da bobancin su duk da gwarancin su sun fi fasaha a nan sune ke banbance su ce wannan. kuma su ce waccan nan. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Yauwa Mai waccan nan gidan ya bamu labari. Mun gane wannan da kyau ko? Sai mu zazagance kenan tunda mu ma duk su ne. Ya ce to mai waccan nan gidan ya bani labari ya bamu labari sai ya karkatar da hannun shi ya nuna gidan Abdullahi duk sanda kake karatun hadisin annabi in ka ji an ce Abdullahi kai tsaye cikin sahabbai to shi ake nufi Abdullah dan Mas'ud. Sai ya nuna gidan Abdullah dan Mas'ud ya ce mai waccan nan gida ya bamu labari Daga cikin ayyukan musulunci wanene Allah bai bi wa da daukaka yayi fi so yanzu sahabbai sune wa manzon Allah tambaya ne menene Allah ya fi so mu aikata don mu samu matsayi a gurin shi. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Duk sanda kake neman kusanci ga Allah ka tafi ga Allah kai tsaye shi yasa babban malami Ibn Taimiya yayi littafi ya samu shi
[Segment 3/3 | 00:40:00–end]
[Speaker seg3-spk:0]
Dan ka tabbatar babu shamaki tsakanin kai da sanda zaka bauta ma Allah, babu buƙatar sai wani waliyi ya kama ka ya kai ka gaban Allah. Duk wanda zai bauta ma Allah ya bauta wa Allah kai tsaye, Allah yace Ya ku muminai ku ji tsoron Allah, ku nemi kusanci zuwa ga Allah. Duk baki daya malamai suka ce abinda ake nufi da a nan shine ayyukan alkhairi, ka karanta ainihin Mawaki yace ya ke 'yata naga fa samari suna son ki, mota kaza tayi parking, Alhaji kaza yallabai kaza sai yace ki rinka yin kunshi ki rinka sato zani. To me ce ce Naga samari suna son su matso kusa da ke, kaga ashe yadda tazo a haka haka ne ma'anar ta neman kusanci. Babu wanda yace wai ka kama wani shehi ko wani limami ko wani kaza, hatta waccen ayar da suke mata ta tun daga 'yan shi'a da sauran 'yan bidi'a Ranar alkiyama rana ce da za a kirayi kowace al'umma da littafin su, in aka jawo ku ne Bani Isra'ila al'umman Musa tare da ku ne Bani Isra'ila al'umman Isa tare da Injila, ku ne Muhammadawa tare da Alƙur'ani. Jama'a mun fahimci wannan da kyau ko? To wannan ita ce cewa neman kusanci zuwa ga Allah ta hanyar aikata ayyukan Amma kar kayi irin ta mushirkai, mushirkai ne da aka ce me yasa kuke bauta wa waɗannan gumaka sai suka ce Ai ba komai yasa muke bauta musu ba sai dan su kusantar damu ga Allah, asali ba su muka nufa da ibadar ba. To a ƙa'ida a cikin addinin musulunci kai tsaye ake ainihin wato neman kusanci zuwa ga Allah. To in ka tashi sai ka dubi to wani aiki Allah yafi so. Sai Allah yace daga cikin ayyukan duk dake kusantar da bawa na zuwa gare ni to babu kamar farilla. Haka yazo a cikin hadisin waliyi, a cikin ainihin hadisin Bukhari da Muslim. Duk abinda zaka yi wanda Allah zai kusantar da kai ka duba me yayi farilla, Allah yafi son farilla. Farilla ita ke kusantar da kai zuwa ga Allah. Duk sallah ce ta farilla, azumi ne, zakka, biyayyar iyaye, hajji, umra, duk abinda suke na farilla sune suke kusantar da kai zuwa ga Allah. To Allah maɗaukakin sarki yafi son waɗannan abubuwa. Sai Allah yace bawa na bazai gushe ba kuma yana matsuwa gare ni, yana matsuwa gare ni matuƙar yana kula da nafilfili, matuƙar yana kula da nafilfili. Ashe nafila tana ƙara kusantar da kai ne zuwa ga Allah. Amma kana son daga ƙofar gidan ku a kai ka gaban Allah kana son haka? To ka tsai da farilla da kyau. Jama'a mun fahimci wannan da kyau ko? Allah maɗaukakin sarki ya taimake mu. Shine suka tambayi Annabi Abdullahi dan Mas'ud yace sai na tambaye shi cewa menene wani aiki ne Allah maɗaukakin sarki yafi so? Yin sallah akan lokacin ta. Yin sallah akan lokacin ta jama'a. Da zaran lokacin asuba yayi idon ka biyu sai ka ainihin taso kaje kayi sallah. A'a kana bacci ne aka tashe ka sai kayi murmuje sai ka tashi kaje kayi sallah akan lokacin ta. Azahar, la'asar, magariba, isha duk sallolin nan kowace tana da lokaci Allah yace Sallah dai farilla ce muminai su tsai da ita kuma ainihin akan lokaci. To yin sallah akan lokaci na daga cikin aiki mafi daraja. Me yasa nace yana daga ciki? Saboda zaka ga irin waɗannan tambayoyin suna da yawa. Abu Musa ya tambayi Annabi ya manzon Allah wani ainihin aiki ne yafi kowanne? Sai kaji manzon Allah yace ciyar da abinci. Sai kace to kamar an samu rikici kenan? A'a duk sanda suka yi wa Annabi tambaya sai Annabi ya dube a yanzu menene abinda aka fi buƙata? To sai ace yin wannan aikin shi yafi falala. Dan haka babu rikici tsakanin hadisan. Sannan sai nace sai kuma me ya manzon Allah? Sannan sai biyayyar uwa da uba. Sannan sai nace sai me? Sannan sai jihadi wajen ta da addinin Allah. Ai jihadi jihadi ba wai zuwa kawai ku je ku samu kafirai ku karkashe su, a'a sai kun kiraye su zuwa ga addinin musulunci da wa'azi ne da kyawawan ɗabi'u. Sahabbai sun kasance garuruwa in suka shiga sai su zauna suna trader, suna nunawa mutane halaye na gari. In suka zo wa'azi sai ace 'yan kasuwan nan ne fa yau ga su can wai sun kafa wa'azi. Ai dama malamai ne to muje muje abinda zasu ce. In suka zo suna wa'azi Allah yace Annabi yace sai su ce jama'a kuyi kokari ku ga kuyi rinka yin yadda kuka ga muna yi ɗin nan. Don me? An yi huɗɗa da su, an gan su suna da amana, suna da mutunta mutane, suna da kula da ibada. To duk sanda suka haɗo maka aya suka haɗo hadisi sai su ce Ku zama irin mu kuyi kokari kuyi yadda muke yi. Me yasa? Saboda su mutanen kirki ne. Haka aka samu bayin Allah a yanzu daga cikin 'yan uwan mu ahalus sunna, daga ƙasashen Amman ne Jordan, daga ƙasashen Sham Syria, daga ƙasashen Saudi Arabia, daga Masar ne, daga ina? Sai mutum malami ne fa ko engineer ne, ko medical doctor, ko pharmacist, ko economist, ko accountant ko wani iri sai ya sai da kayan shi, sai ya samu ya sai mota sai ya nemi izinin zama ƙasar Ingila ko America ko Faransa ko Germany. Sai ya je sai ya tasi, yana tasi yana kabo kabo. Ya je da'awar musulunci ne. Sai ya manna a daidai sit ɗin da fasinjoji ke zama da bayan sit 1 gaba yadda da fasinja ya zauna a gaba ko a baya sai ainihin kawai kaga ya rubuta In kana da wata tambaya akan musulunci zaka iya tambaya ta. To da ka karanta sai kaga ka kallo shi Sai yace eh. To sai kaga an fara lura da ɗabi'un shi sai ya rinka kyawawan ɗabi'u. Ah ina za a sauke ka? Ai ai za a sauke ni ne nan. Ah to shikenan ina ne ƙofar gidan ka? Ai gashi can ma kusa da tasha to bari aje a kai ka. Madadin naira 200 sai ya karbi naira 100 sai yace ba komai ta isa wannan ai ta isa ba komai. To shikenan ka tashi fita to ga kati na mana tunda mun zama costomomi in zaka dan buga mana waya ga inda nake, in kuma zaka zo wuri na duk dai babu laifi. Mu kuma kana da tambaya ɗin duk zaka iya. In ma yanzu kake so sai in parking in ajiye ɗin sai a tsaya a yi. Amma kai dan a chaba oya oya malam Allah Allah kake ka an ce ku ɗin ka ka guda. Ba ruwan ka da'awa ko tayi da'awa ko ta da'awa ko ta To su abinda suke kenan bayin Allah ne Allah ya saka musu da alkhairi. Suna nan abinda suke kenan dare da rana zama suke a internet, kwana zasu yi, yini zasu yi, suna ta rubutu suna watsawa a cikin saƙonni na internet. Yana shiga duniya ko ina saboda wannan internet da Allah ya kawo shi ta hanyar computer alheri ne ga musulmi sharri ne ga waɗanda suke ba musulmi ba da kuma waɗanda suke fasikai ne. Amma internet ba ƙaramin alheri bane domin saƙo ne na da'awa ko manufa zai shiga gidan ka ya zauna ba sallama ba izini kuma daren dakan. Matuƙar kana da computer kana da internet to shikenan ya shigo ɗakin ka yana nan ya zauna bai yi sallama ba, bai nemi ɗakin zama ba, bai nemi izini ba da ka buga kuma sai yace gani. Yafi radio, yafi talabijin, yafi dish domin akwai inda tashar radio in nisa ya nisa bata kamawa. Internet kuwa in aka harba shi in saƙo na zuwa lahira daga duniya to zai kai. Ba inda bazai je ba domin kamar tarho ne ina ne bazaka yi taho a duniya ba? To haka jama'ar musulmi mun gane wannan da kyau ko? To ta haka suna nan suna ta da'awa sai suna ta sharhi game da musulunci. Sai su ɗakko wata shubuha da aka saka akan musulunci sai su bada amsa kawai sai su zuba a internet. Ba wani abu sai su ce kaza kaza kaza kaza ko kuma Muhammad manzon Allah ne sallallahu alaihi wa sallam ko kuma tarihin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam. Haka ake yin da'awa. Baku ganin wata baiwar Allah Madina Dauda na Dabo tana labarai a network news, tana labarai a ainihin sashin turanci. Baku ganin abinda take duk ran da ita zata yi presentation sai tayi sallama ta musulunci. Ga turanci a bakin ta kace gwamla lugga ne ba banta. Turanci malam kamar alwutsuwutsu ne ya karantar da ita karatu. Turanci a bakin ta. To in taje ana nan da aka zo sai tazo daidai lokacin maulidi su waɗannan suna ta hayaniya Suna can suna ta hayaniya basa da'awa ita ko sai taje sai ta rubuta Ma'anar sharhi bayan labarai akan waye manzon Allah? Aka yi tarihin manzon Allah ya shiga network news duk duniya kenan an kama an je. An yi da'awa ko ba ayi ba? Abinda ake so kenan dan jarida ne kai dan radio ne kai dan ina ne ko kowace harka kake kayi kokari ka kira mutane zuwa ga addinin ka. Jama'a mun fahimci wannan? Kasuwanci kazo da haka aka ce tarihin musulunci yazo mana nan ƙasashen baƙaƙen fata. Kasuwanci suke zuwa daga ƙasa kaza buzaaye ne daga tunishia ne daga Mauritania ne daga haka sai suzo suna kasuwanci kuma suna karantar da mutane. Shikenan sai addini ya ɗu. Haka kaima a yanzu ka waye gari ka gan ka a Lagos ko a Patakol ko a ina ne duk inda ka gan ka sai kayi kokari ka kiraye mutane zuwa ga addinin ka. Sannan kira zuwa ga addini da aiki yafi da surutu domin suka ce Karantar da mutane a aikace yafi karantar da mutane ainihin wato da bayani. Misalin wannan mutum ne ke jin ƙishi sai ya shigo da gudu ɗakin nan. Yana zuwa sai ya nemi randa ko fridge. Bai yi sallama ba bai ce komai ba kawai sai da ya ɗibo ruwa ya sha ya ƙoshi tuku na zufa ta tsatsafo mishi sannan sai yace jama'a dan Allah kuyi haƙuri na manta assalamu alaikum lafiya lafiya lafiya lafiya. Yanzu wannan bai ce mana yana jin ƙishi ba amma dai a aikace munga irin yadda ya girgince yazo ya sha ruwa har ya kasa sallama sai daga baya. Da shi da wanda yazo ya zauna yace jama'a ina jin ƙishi. Ana cikin hira sai yace jama'a ina jin ƙishi. Da shi da wancan naɗa zuwa nene zamu fi gane yana jin ƙishi? Na farko domin wancan action a aikace kawai sai dai muka ga da yazo ba sallama sai ya nufi ina randa take. Haka duk sanda kake dan kasuwa ne kai ma'aikacin gwamnati ne kai dan tasi ne kai dan a chaba mai sana'a ne manomi ko wani iri ne kai zaka kiraye mutane zuwa ga addinin ka ne ta hanyar ɗabi'un ka da ayyukan ka. To shine nan ainihin yake nuna mana cewa ainihin gashi jihadi ɗin nan yana daga cikin abu mafi daraja wanda ya takala matakala To in an nuna mutane an yi musu wa'azi, an lallashe su, an yi musu in suka ƙi to shine sai a tashi sai a yaƙe su. Duk da haka kaga asali musulunci ashe ba yaƙin yake so ba. Dan da yaƙin ne sai yace ku je kuyi musu yaƙin hotsi da tutsi. Ku je kuyi musu yaƙin ƙare dangi. Ku je kuyi musu kisan da ainihin sabiyawa suka yi wa bosunawa amma musulunci bai ce haka ba. Sai yace in kuka zo zaku fara yaƙin ku fara da sunan Allah. Kuma kan ma ku rinka fatan yaƙin ku rinka roƙon Allah ya zaunar da ku lafiya. In ya zama ba yadda za ayi to sai ku fara da sunan Allah sannan ku roƙi Allah Allah ya baku nasara. Annabi yace kar ku kashe mace, kar ku kashe yaro, kar ku kashe tsoho. Matuƙar mace ba fitowar tayi aka ganta da taƙarya ko da bindiga ba an same ta a ɗaki ko kuma ta gudu da yara duk sai ya ƙyale. Tsoho haka haka tsoho ne wani ne ke ibada yana zaune cikin chochi yana ibada rikici ya tashi malamai suka ce kar a taba shi har ma abinci ke shi in bai da guzuri sai a ɗibo kuɗi ko abinci a bashi. Ashe kunga ana buƙatar a san waɗannan abubuwan a ilmance. In ba haka ba sai aje jihadi aje ayi kwakyara. Mun gane wannan da kyau ko? Manzon Allah ne ya bani waɗannan ainihin labarai guda uku falaloli uku, falalar biyayyar iyaye, falalar ainihin sallah akan lokaci, falalar jihadi wajen ta da addinin Allah. Kuma ma da na nemi ƙari wurin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam da za da ni da ya ƙara mun dan manzon Allah bashi da ruwan karatu. Malam Muhammad Nasir Dinil Albani sai yace Wannan hadisi ingantacce ne. Yace ka duba littafin Lamba hadisi na 1001 da 98 sai kuma yace Me yake nufi da yana nufin Bukhari ya fitar da ainihin wannan hadisi a cikin kitabi na tara shine ma'anar tara ɗin nan. Littafin lokuttan sallah babi na biyar shine yace Babin dake bayani akan falalar yin sallah akan lokacin ta. Sai ya sa Ina ma'anar Musulmin ma ya fitar da shi a kitabi na farko littafin farko Hadisi na 137 da 138 da 139 da 140 Jama'a kunji wannan shine hadisin farko Imam Bukhari ya kawo shi ne saboda waccen magana da Annabi yace biyayyar iyaye ita ce ainihin aiki ko shine aiki mafi falala bayan yin sallah akan lokaci. Ko kana bin iyayen ka ya kai mai saurare na ko ko kana saba musu Baban ka da ya rasu ko babar ka da ta rasu ya kuka rabu da ita? Ka amsa wa kan ka wannan tambayar ya rage halin da kuka rabu da su to shine zai amsa maka ko zai taimake ka akan abinda zan faɗi. Mahaifin ka ya mutu kuna dutse hannun riga, ko mahaifiyar ka ta mutu kuna dutse hannun riga wallahil azimi ka gama yin asara, ka shiga uku ka lalace. Amma Allah ya soka tunda kaji wa'azi baka riga ka mutu ba ya zaka kai ka gyara yanzu? Sai ka ci gaba da yi wa iyayen nan naka addu'a, ka nemi musu sadaka, kana ɗiban kuɗi, kana ainihin baiwa bayin Allah suna ainihin gina masallatai ne, makarantu ne, waƙafi ne gidan baki, pamfo ne, rijiya ce wasu mutane ke buƙata da ayyukan alkhairai irin haka da nufin cewa ka ne haka ne dan Allah maɗaukakin sarki ya ɗauka ya kai gare su kuma Allah ya yafe matsalar dake tsakanin kai da su. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? In iyayen ka basu mutu ba to kai kam akwai sauran aiki akan ka har yanzu. Sai kayi yadda zaku kai ku rabu lafiya. Shine abinda ladabi na farko da ake so kenan. Duk wani wanda zaka girmama a office ne ka dubi ogan ka tace ranka ya daade ko yallabai ko wanene amma ka wulakanta uban ka ko ka wulakanta uwar ka to girman da kake girmama wancan girmamawar banza ce kuma ta munafunci ce kuma babu Allah a ciki. Domin inda girmamawar gaske ce to a hakku wanda ya cancanta da ka fara girmama mawa shine Allah manzon Allah sannan sai kuma ka kyautata kai wa iyayen ka ladabi. Duk sanda matsala ta faru tsakanin kai da mahaifan ka sai ka gane cewa kai ke da gaskiya su basu da gaskiya sai ka dubi matsalar. Shin matsalar nan haƙƙi ne da ya shigo daga cikin haƙƙoƙin Allah to anan kam shine bazaka saurara musu ba amma bazaka yi musu ainihin karansaye ba. Dubi Annabi Ibrahim yafi kowa sabawa mahaifin shi domin mahaifin shi bautar gunki yake. Shi kuma Annabi Ibrahim shine shugaban masu tauhidi cikin annabawa ma. In ka ɗauki Annabi sallallahu alaihi wa sallam amma duk da haka bai gaya wa uban shi ba kan magana ba, bai wulakanta uban shi ba. Haka kaima akan aƙida ne akan sunna da bidi'a kuka samu tan garda kai da mahaifin ka kai da mahaifiyar ka haƙƙoƙin su zaka basu amma game da haƙƙoƙin da suka shafi Allah anan bazaka saurara musu ba kuma bazaka gaya musu ba kan magana ba wannan ita ce ƙa'ida ta Alƙur'ani da sunna. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Kai kuma uba da kake saurare na a yanzu ko ke kuma uwa kar ki ɗauka tunda ance a bi ki a girmama ki kar ki je ki ɗakko rikicin da yafi ƙarfin ki. Kar ka ɗakko rikicin da yafi ƙarfin ka, ka rikice ka ce ainihin ɗan ka bazai tsai da gemu ba ko ɗan ka bazai sallah masallaci kaza ba ko ɗan ka bazai kaza ba wanda yake haƙƙoƙi ne daga cikin haƙƙoƙin Allah anan kuma kam ka nemo rikicin da ainihin yafi ƙarfin ka. Allah maɗaukakin sarki ya shiryar damu. Saboda yadda lokaci ya ƙure zamu saurara anan insha Allahu ta'ala. Sai kuma anzo ainihin jibi ranar lahadi za a ci gaba da karatun wannan littafi Allah maɗaukakin sarki ya gafarta mishi.
============================================================
[Part 8]
============================================================
[Segment 1/4 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yau litinin 16 ga watan na da shekara 1422 wanda ya daidai da biyar ga ainihin watan shekara ta 2001 Muna karatun littafin Muhammad dan Ismail Al-Bukhari Allah ya gafarta mishi. A inda muka fara karatun wannan littafi muka ji Al-Imam Al-Bukhari yace Wannan littafi ne da ke kawo ladubba na musulunci shi ya sanya ya sanya mishi A daina cewa a'a ladabi na kowanne mutum da ya kamata shi kanshi ya lazimta to ladabi mafi girma bayan girmama Allah da manzon Allah shine ladabi da biyayya ga iyaye da na gaba shine muka ji ainihin hadisin farko da ya kawo mana wanda ainihin annabi Biyayyar iyaye na daga cikin ayyuka mafi falala a cikin addinin musulunci. Ainihin wato shi wannan ainihin ya karbo daga malamin sa Adam yace Shuba ya bamu hadisin da yace Yace ya ainihin bamu labari to wannan na daga dalilan da ya sa malamai suke ayi wa littafi saboda kada lahani ya faru domin haka suka ce wajibi ne ga duk wanda zai karanta hadisin manzon Allah ya iya nahawu gwargwadon yadda in kuskure ya faru zai iya gyarawa. Yanzu kunga wannan abun da ya faru kuskure ne inji yayi da yace sai yace Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Sai To abun da ainihin badali ya dauka haka ainihin mu yake dauka. Ma'ana in kace Musa mai Duk wannan sunan ba na mutum daya bane? To in a larabci ne da Alhaji ya dauka shi Musa zai dauka shi mai zai dauka. In kace Muhammad dan Ahmad To da Muhammad ya dauka shi dan zai dauka domin Muhammad shine dan dan shine Muhammad. To hakan nan shine fa'ili domin shine ya bada hadisin. To sai ya zama amma kaga sai inji ya kuskure sai maida shi An gane wannan da kyau ko? Ahaa Ya karbo wannan hadisi daga To a kasa malam Muhammad haka yazo a cikin asalin rubutun Amma a cikin da shi da wani malamin ba wai dan Umar aka ce ba a'a cewa akayi Daga sai malam yace ka karanta zai zo ya gaya mana lambar shafi din da lambar hadisi insha Allahu ta'ala zai gaya mana lambar hadisi. Ma'ana yanzu Bukhari ya ruwaito wannan hadisi ta hanyar sai malam Muhammad yace haka yazo a Shin haka abun yake? Bukhari wannan hadisin ya same shi ta hanyar ne? Ko kuwa kuskure ne ya faru masu kwafewa wajen su su tabbatar da wannan Sai suka barshi basu tabbatar ba rashin tabbatar da sai kuma ya maida sahabi daga ya koma dan Umar da sunan da sunan Umar duk daya ne. Amma in aka so bambance wa to shine sai shi sai a sa tunda ba Don kar a bari Umar in ka gani sai ka Umar ne ko to sai malamai sai suka ce sai a sa da an sa to kai kana zuwa sai ka karanta To shine sai yazo nan amma yace a cikin da shi da wasu malamai duk sai ta zo cewa To duk ma dai wanda ta kasance ai sahabi ne na annabi In din ne ya ruwaito in din ne in kuma dukkan su ne suka ruwaito dukkan su dai sahaba ne na annabi Kala shi wannan ainihin sahabi sai yace yardar ubangiji tana cikin yardar mahaifi Fushin ubangiji kuma yana cikin fushin ainihin mahaifi matukar mahaifin ka ya yarda da kai ubangijin ka ya yarda da kai matukar mahaifin ka ya yi fushi da kai ainihin ubangijin ka ya yi fushi da kai to wannan magana kunga ne ya fada to a ita baza a kirata hadisi ba sai a kirata Baza a kirata ba sai a kirata Sai malam yace Wannan magana kyakkyawa ce a yadda kaji ta din nan cewa ya fadi ta shine kuma ta tabbata wato daga annabi In kana son ganin bayani sai yace ka duba lambar hadisi na Bayan da kaji bayani akan cewa lallai kayi ladabi ka bi uwa ka bi uba ka kyautata musu har in ka sake uban ka yayi fushi da kai Allah yayi fushi da kai in ka sake ainihin uban ka yayi in ka biyar da uban ka yayi yarda da kai Allah yayi yarda da kai duk wadannan abubuwa a bisa ka'idoji na shari'a domin wannan wadannan babuka Bukhari zai kulla mana su wajen babuka 16 da ni game da tsarin biyayyar iyaye. Yanzu nan ana nuna maka jumillar daraja da wajabci da falalar biyayyar iyaye ne to can gaba kuma za'a zo to in aka samu iyayen da suka taso da mas'alar da take tafi karfin su hakkin Allah ne fa to anan zaka ji kuma ya kulla babi su kutun da guda cewa baza a bi su akan wannan abun ba. Ina fatan mun gane? Yace babin da ke bayani akan biyayyar uwa meye dalilin Bukhari akan haka sai yace Wannan ainihin hadisi Imam Al-Bukhari ya ruwaito shi daga malamin sa Ana son kasan malaman hadisi daya bayan daya yadda da kaga wane kasan shine wane da kaga wane kasan shine wane. Shi kuma yace ya karbo daga To malaman hadisi sunyi sabani game da hadisin da hadisin ainihin Shin wadannan sun tabbata ko basu tabbata ba? To karshe dai da aka kai aka komo sai malamai suka tabbatar da cewa ingantacciyar magana dukkan su a sani da Isnadai ne kyawawa to amma Ahmad Shakir a cikin sharhin sunanin Tirmizi shi ya kai matuka ma idda har ya zan isna dan yake yi in yaga isnadi akwai sai ya in yaga isnadi akwai ainihin sai ya Amma indai kana son ganin gaskiyar bayani kaje ka samu littafin tare da ainihin sharhin shi na shi Ahmad Shakir din zaka ga bayanai insha Allahu ta'ala gamsassu. To ya karbo shi dan Hakim ya karbo wannan hadisi daga mahaifin shi mahaifin shi kuma ya karbo daga ainihin nashi mahaifin wato kakan To abun da ake so ka rinka ganewa kenan in kaji malaman hadisi yace To shi mai riwayar kamar ya karbo daga baban shi daga kakan shi to kakan shi wancan na farkon fa? Ma'ana wannan ya karbo daga baban shi shi ma baban ya karbo daga nashi baban kaga ba matsala kenan. An gane Hakim ya karbo daga nashi baban baban shi kuma ya karbo daga nashi baban wato kakan An gane? Kakan yace sai nace Wanene yafi cancanta da mahaifiyar ka maman ka babar ka ita ta fi cancanta a duniyar nan ka bi Sai nace to ya manzon Allah wa yafi cancanta dai in yi wa biyayya kuma naji wannan mahaifiyar ka ya sake cewa ya manzon Allah wa yafi cancanta da in yi wa biyayya sai annabi yace mahaifiyar ka a kasa sai malam ya sauke yace a cikin wato bugu wannan munyi ishara zuwa ga cewa malam ya dogara akan bugu uku ne yadda ya tattaro ya hado wannan littafi ko sai yace to a asalin wani bugu na ainihin sai aka samu Ma'ana anan an samu takararin cewa mahaifiya ita ta fi cancanta da ainihin bi a kyautata wa har kashi hudu. Mun fahimci wannan da kyau ko? To sai mu koma sama sai na sake cewa waya fi cancanta da in bi to mahaifin ka ma'ana yanzu in an kasa darajar uwa da uba kashi hudu uwa zata dauki kashi uku uba sai ya dauki kashi daya kenan. Uwa ita ta fi girman daraja a wajen biyayya kamar yadda zaka zo kaji domin itace ta sha wahalar daukan cikin ka tayi kaza tayi duk abubuwan da uba yake yi abubuwa ne wadanda yake duk harkokin da uba yake yi na wajen tattali ne suka fi yawa. Amma ka duba uwa ta sha wahala da ranta tayi kaza zaka ji wani yace yayi wa uwar shi kaza yayi wa uwar shi ko ya biya ta sai sahabi yace mishi ai ko yunkuri daya daga cikin yunkurin na guda ma baka biya ba. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Sannan sai kuma wanda yafi kusanci sannan sai wanda yafi kusanci bayan uwa sai uba bayan uba sai wa sai babban yaya sai babbar yaya sai makamancin haka haka dai biyayya daya bayan daya ma'ana a cikin addinin musulunci akwai na gaba kenan bin na gaba bin Allah da bahaushe yake cewa gaskiya ne matukar kabi na gaba lallai kabi Allah madaukakin sarki babu shakka akan haka musamman lallai ace shi ainihin na gaban nan ya ainihin jagorance ka ne akan biyayyar Allah. Sai malam yace wannan hadisi kyakkyawa ne in kana son ganin bayanin yaya akayi ya zama kyakkyawa kaje ka duba littafin a cikin lambar hadisi na 2232 da lambar hadisi na 1829 sai ainihin ya sake cewa ta to wannan ta da ya kawo me yake nufi kenan? Tirmizi Tirmizi kenan kuma ka sake duba Tirmizi a cikin kitabi lambar littafi na 25 shine Littafin da ke bayani akan biyayyar iyaye da kuma sadar da zumunci a cikin babi na daya Anan Tirmizi ya fitar da wannan hadisi. Jama'a mun ji wannan ko? Yanzu abun da ya faru shine sahabi Abdullah dan Abbas wani mutum yazo gurin shi yace Allah ya gafarta malam na nemi auren wata mace sai ya taki aure na tace bata so na. Sai wani na je nemi auren ta sai ta yarda zata aure shi. Sai kishin ta ya kama ni yaya zata kyau re na taje ta auri wani kawai sai na bi ni mata makami na kashe ta. In na tuba Allah zai karba? Sai Ibn Abbas yace Mahaifiyar ka na da rai? Sai yace a'a mahaifiya ta bata da rai ta mutu. Sai yace to shikenan Tafi ka tuba zuwa ga Allah mai biyayya da daukaka ka nemi kusanci zuwa ga Allah gwargwadon y`adda zaka iya ta hanyar sadaka ne ta hanyar sadar da zumunci Allah madaukakin sarki yace ya ku ji tsoron Allah ku nemi kusanci zuwa ga Allah kullum muna nuna wa mutane wannan kurba neman kusanci ga Allah yana faruwa ne ta hanyar biyayyar Allah madaukakin sarki ba wai ka kalewa wani shehi ko wani waliyi kace wai ya kai ka ga Allah ba a'a anan abun da ake so kai kanka kayi wani aikin alheri wanda zai sadar da kai zuwa ga mahaifi zuwa ga ainihin Allah madaukakin sarki kamar yadda zamu zo a cikin karatuttukan nan insha Allahu zamu kawo kissar wasu bayin Allah salihai daga cikin mutanen farko wadanda suka samu kansu a halin kunci suka rasa yadda zasuyi sai wani yace abun da za'a yi kowa yayi tunanin aikin alheri da yayi wanda zai sa ya roki Allah Allah madaukakin sarki ya samu ya kai mu kusa gare shi yadda zai sauraru kukan mu wannan yazo ya yi tawasuli da biyayyar iyaye wannan yazo ya yi tawasuli ya nemi kusanci ga Allah saboda kiyaye amana wannan kuma ya yi tawasuli saboda rashin sabon Allah sai Allah ya yayi musu bala'in da suke ciki to shine yanzu ga wannan mutum yaje ya kashe budurwa saboda tace bata son shi yaje ya kashe bazaura saboda tace bata son shi to yaya za'a yi sai kuma ya fara yawan fatawa yanzu malam yanzu yaya za'a yi yaya kenan sai malam yace uwar kana da rai yace a'a Sai yace to sai kaje ka tuba sannan sai kaje kayi ta ibadoji kayi ta sadaka kayi ta ayyukan alkhairi wadanda zasu kusantar da kai zuwa ga Allah madaukakin sarki mutumin yace sai na tafi Afwan shi wancan mutum wanda yake bamu labarin hadisi Yace to da naji irin wannan fatawa da malam Ibn Abbas ya bayar sai naje na tambayi shi Ibn Abbas Allah gafarta malam me yasa ka tambaye shi game da rayuwar uwar shi? Saboda ni bansan wani aiki ba wanda yake kusantar da mutum zuwa ga Allah mai biyayya da daukaka fiye da ainihin biyayyar uwa to naso da ace uwar shi na da rai sai ince yaje yayi mata wani alheri yaje ya kyautata wa uwar shi ya nemi kusanci da wannan kyautata wa zuwa ga Allah sai Allah yafe mai zunuban shi to tunda uwar shi bata da rai sai yaje ya tuba sannan kuma yaje yayi wasu ayyukan dai da zasu kusantar da shi zuwa ga Allah amma da uwar shi na da rai to hanya mafi kusa da zai bi baya da zai bi duk ya yanke wadannan sabon Allah ya kai ga fadar Allah kai tsaye shine hanyar uwar shi. To yanzu kaga kai da uwar ka take da rai ke da uwar ki take da rai ku da iyayen ku suke da rai duk sanda ka samu kansu a halin bukata kaine darakta kaza ko kaine shugaban kasa kaza minista kaza ne ranka ya dade wane ne kai madam wance ce ke sai kije sai ki kyautata wa uwar ki sai kaje ka kyautata wa uwar ka wannan ana nufin banda kyautata wa fa wadda dama kake yi. Ba wai da can kai dan iska ne ka gudu kana wulakanta uwar ka yanzu kuma kaji ana rabon minista sai kuma kaje gwaggo wallahi nazo kinga wadannan atampofi ayi mana addu'a wannan baza kayi wa Allah wa yau da danfara ka cuci uwar ka ba. A'a dama kana kyautata mata kane mata biyayya ma'ana in bala'i ya same ka ba kana kwashe wa da gudu ka tafi gurin malamai ba idan bukata ta kama ka ba rugawa kake kaje gurin malamai ba aka ce wannan hanyar ta malamai gaskiya ce indai malaman sunna ne amma tana da tsawo. Wacece tafi kusa itace uwar ka din nan da take gida je ka kai mata wani alheri tana da tsohon firiji ne sai kaje ka siyo sabo gal dakin ta a sake kafet a sake abubuwa a sake abubuwa duk a mutunta ta AC a samo mai remote control a sa mata tsohuwa farfesun kullum a ajiye yan mata da zasu rinka kula da ita suna gyara mata abubuwa to kaga wadannan abubuwan kari ne akan abun da dama kake yi ko? To shine sai kuma kayi tawasuli yanzu ka kara kusanta Allah kenan. Jama'a mun gane wannan da kyau yanzu da wanda yake mai duguri yake da bukatar yaje yaga shugaban kasa a Abuja da wanda yake a tafa ta jahar Naija wanne yafi kusa da shugaban kasa? Wanda yake tafa domin wannan ko da gudu zai taka ya ruga da gudu ba haka bane amma daga mai duguru fa ihun ka banza yan fashi da makami nawa ne a hanya misali? Haka ake nuna maka hanyar da zaka bi kaje gurin malaman sunna suyi maka addu'a su rokan maka Allah gaskiya ne malaman sunna suyi addu'a su karanta al'kur'ani Allah ya biya bukata gaskiya ne wannan amma hanya mafi kusa ga ta nan a kusa da kai. Shine kaje ka kyautata wa mahaifiyar ka sabon Allah kai sai kaje ka kyautata mata kuma wannan kar ku fahimci addinin musulunci da kuskure fahimtar da zaku yi da kuskure ta kai ku kuyi wa addini fahimtar irin fahimtar da khawarijawa da yan shi'a suka dawo suka yi sai suka zauna suna zargin malaman sunna. Kar ku dauka cewa wai tunda dai yanzu kana da uwa a gida bari kaje kayi ta sharbo ta da magarba sai ka shigo mata da leda guda na suwan wata da kaza da kaza to gwaggo da yau dai munyi sabon
[Segment 2/4 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
sai kuma a roƙa mana Allah. Gobe ma ka sake tafiya, ka sake sharɓo ta, to inna dai wallahi kinga dai wannan a tamfa, a dai ƙara roƙa mana Allah, kar dai a gaji da mu. Gada kuma ka sake zuwa kai ka toɓara, ka sake zuwa, inna ga mu dai mun dawo. A'a ba haka ake nufi ba. Dan kaɗei kana da kuɗin omo, kana da mai wanki a gidanka, da mai guga, wannan ba zai baka damar ka ga kwata ta kai ta komo kayi alkafura ka shiga cikin ta ba. Ka ce da an taɓa ka ka ce ai muna da omo, muna da masu wanki da guga. Kana yin haka?
[Speaker seg2-spk:1]
A'a.
[Speaker seg2-spk:0]
To haka wannan ma karka fahimci dan ance uwar ka in tayi maka addu'a, ko in kai biyayya ta hanyar ta, Allah zai ja ka kusa da shi. Karka ɗauki dama ce aka baka kaje kayi ta saɓon Allah, ka dawo ka kyautata uwar ka saboda abu ya wuce. A'a ba abin da ake nufi ba kenan. Domin waɗannan abubuwan su suka ja khawarijawa, da wasu ɓatattu daga cikin rafidha ƴan shi'a, sai suka koma suna cewa ahlussunna sun ɗaura gindin mutum yaje ya saɓon Allah saboda ga hanyoyin tuba sun kawo birjik. Sai aka ce a'a ai ba haka ahlussunna suke nufi ba. Abin da suke nufi shine ba shege ba ɗan banza a gurin Allah sai wanda ya shegantar da kanshi. Karka taɓa ɗaukar cewa kai Allah ya tsine maka albarka ba zai jika ba. Aka ce duk laifin ka Ya ku bayina da kuka yiwa kanku ta'adi, kuka cuci kanku, kuka saɓa mini, karku yanke tsammani daga rahamar Allah. Allah na gafara zunubai baki ɗaya. Babu wani laifi da zaka je gurin Allah maɗaukakin sarki da shi sai Allah ya gafarta maka. Ka miƙe hannun ka, ka roƙi Allah. To sai ake nuna maka wace hanyar ce in ka samu kanka a halin tsautsayi, za'a yi marmaza a karɓa maka, aka ce gata. Ashe kaga ba cewa akai dan kana da hanya mafi kusanci kaje ka saɓa Allah ba. Jama'a muna fahimtar waɗannan abubuwan da kyau ko? Allah maɗaukakin sarki ya shiryar damu. Malam Muhammad Nasiruddin Albani yace sahihun, wannan ainihin hadisi sahihi ne wato wannan asari sahihi ne. Sai yace in kana son ganin bayani ka duba silsilar sahiha a lamba hadisi na dubu biyu da ɗari bakwai da casa'in da tara. To wannan ainihin asari na Abdullahi ɗan Abbas ya raba wata gaddama dake tsakanin manyan malaman fiƙihu game da ina hukuncin mutumin da ya kisa. Mutumin da ya kisan kai da gangan ɗan ta'adda yaje ya kashe wani ko ya kashe wata ko ya kashe wasu. Shin in ya tuba Allah zai karɓi tuban shi? Mafi yawancin malamai suka ce Allah zai karɓi tuban shi. Ibnu Abbas sai ya tirje yace pau pau Allah ba zai karɓi tuban shi ba saboda ga irin narkon azaba da akai mishi alƙawari a cikin ainihin suratul nisa'i. Wanda duk ya kashe mumini da gangan, Allah maɗaukakin sarki ya tsine mishi albarka. Allah yayi fushi da shi. Allah ya mishi tattalin azabar da in ya shiga zai dawwama cikin ta har abada ba zai fita ba. Sai Ibnu Abbas yace babu wani laifi da Allah ya kausasa harshe akan laifi irin wannan bayan shirka. In ba wannan ba don haka in kai kisan kai da gangan babu tuba. To daga waɗannan asarai sai aka tabbatar da cewa to ashe Ibnu Abbas yanzu ya dawo daga waccan fatawar. An fahimci wannan da kyau ko? Don haka al'allamatul shaukani a cikin littafin nailul autar sai yace ko Ibnu Abbasi ya ko da ya tabbata Ibnu Abbasi yana kan wannan magana, ba zata zama hujja ba domin al'ummar musulunci sun haɗu akan cewa babu wani laifi da zai dawwamar da kai a cikin wuta dawwama da ma'anar dawwama ta har abadan abidina in ba shirka ba. To yanzu wancan khuludi da Allah yace sai ya zama me ma'anar shi kenan? To khuludi na ma'anar lugha kenan. Mun fahimci wannan? Ma'ana wannan mutum za'a zaunar da shi a cikin wuta. Amma baya nufin za'a zaunar da shi zama na har abada irin na mai baƙin laifi irin na shirka. To dai da wannan magana aka fahimci lallai Ibnu Abbasi ya sake ainihin waccan fatawa da yake akai, ya dawo akan fatawar da sauran jumhuru suke. To dama wasu nassoshin asali sahabban zasu faɗi magana kaza. Sai ya zan sun faɗa ne saboda ƙa'idar da malaman usulu suka ce in nassi yazo mai zafi to a barshi ɗimi ɗimin shi kowa ya ge gare shi. Saboda kar a sassauta, ka ji au ashe ma in anyi kisan kai da gangan, ashe ma za'a tuba kuma za'a karɓa. Eh to shikenan. Dama ni wane ya tsone min ido. Dama naji wane ana sanarwa a rediyo wai shine kansula mai jiran gado. To kuje ku gama da shi. To bayan kwana biyu shikenan a gafarta mu. Allah ya kiyaye. Kaza kaza aje ayi kafara. A sai aka ce in akasan mutumin da zai amfani da irin wannan damar yaje ya kisan kai. To in yazo maka tambaya, Allah gafarta malam. Yanzu in ni kisan kai, Allah zai ainihin karɓi tuba na daga baya? Sai ka ce wane mutum ina? Ai in ka shiga wuta to ka tabbata cikin ta kenan tashi ka bamu guri.
[Speaker seg2-spk:1]
Na'am.
[Speaker seg2-spk:0]
Sai ka jawo nassin da ɗimi ɗimi sai ka kauce sai su haɗa fuska da nassin. To shikenan sai wannan yafi firgita shi. Wannan ƙa'ida ce ta tahafiri. Jama'a mun gane? Saboda ana ganin kamar dama yake son ya samu yaje ya saɓon Allah don yaje yace ainihin in ya tuba kaza kaza. Anan ne Bukhari da Muslim suka ruwaito hadisi cewa wani ɗan ta'adda ya kashe mutum casa'in da tara. Sai yazo yana tambaya. Jama'ar gari ku nuna min malami. Su kuma jama'a duk wanda suka ga yayi naɗi da tasbaha da ƙasin ba sai su ɗauka shine malami. Sai aka samu wani zahidi gashi nan yana ibada. Sai aka ce ai ga wani akaran nan. Yaje akar makallahu na kashe rai casa'in da tara ne. Ko in na tuba Allah zai karɓa? Ashe jahili ne a cikin rigan malamai. Sai kawai sai yace ina? Ba yadda Allah zai karɓi tuban ka. Sai kawai wannan ɗan ta'adda sai ya kifar da shi sai ya haɗa ɗari kenan. Sai yace jama'a musulmi ku taimake ni. Nayi kisan kai yanzu ɗari na kashe. Yaya za'ayi in tuba? Sai aka ce to ai shikenan sai aka nuna mai malami da kuwa sai aka ce rahibi. Wani mai ibada gashi nan ya dukufa da tarbiyya yana ta zikiri ko yana ta tasbihi ko yaya ne. To sai aka ce yanzu sai aka nuna mai malami. Da ya tambayi malamin shin in na tuba Allah zai karɓi tuba na na kashe rai ɗari? Malamin yace me zai hana Allah ya karɓi tuban ka? Har ni ina ma baka shawara da ka tafi ƙasa kaza da ƙasa kaza. Akwai bayin Allah, akwai salihai suna bautar Allah kaje can ka tuba sai ka zauna tare da su. Saboda nisantar ka daga ƴan banza bayan ka fita daga cikin su yana dawwamar da kai a nagarta. Da can tsohuwar karuwa ce. To ta tuba karku batta tayi idda a gidan karuwai. In ba haka ba wallahi wani tsohon saurayin ta yana zuwa shikenan sai ya birkice mata hankali sai ya wargaza idda. Sai a kaita gidan liman tayi. Jama'a mun fahimci wannan da kyau ko? Saboda haka nan da nan sai ya tafi wannan garin. Ya tafi kafin ya shiga garin kawai shikenan sai ya faɗi matacce. To yanzu menene zai kwace shi? Kyakkyawar niyya kenan. Sai mala'ikun wuta suka zo zasu ɗauka. Ƴan mala'ikun aljanna suka zo zasu ɗauka. Ko wanne suka zo sai za'ayi jayayya sai Allah ya aiko da wani mala'ika asiffa ta ainihin mutum. Da yazo yace dan me za'ayi jayayya? A gwada mana. Aka gwada. Daga gari kaza da ya baro zuwa nan inda ya faɗi ɗani kaza. Daga gari kaza da zai je zuwa nan inda ya faɗi ɗani kaza. Aka ce sai Allah ya takura ƙasa. Sai ya zama asalatan asali ƙasar da ya baro To yafi kusanci zuwa ga ita ƙasar masu saɓon Allah. Ma'ana da in akai ƙiyasi kenan ƙarshen ta sai dai a barshi a je jahannama da shi. Amma saboda kyakkyawar niyyar shi sai Allah ya takura ƙasar sai ta zama ainihin yafi kusantar waccan ƙasar mutanen kirki da ya hara. Sai aka ce to a ɗauke shi ayi aljanna da shi. Saboda ƙa'ida rabbaniya Allah yace rahama ta tayal wace komai. Wallahi ba dan haka ba jama'a da mun shiga uku. Manzon Allah sallallahu alaihi wasallama yace ba wani daga cikin ku sai da ya zama ba zai shiga aljanna don aikin shi ba. Sai dai rahama Allah suka ce har kai ya manzon Allah yace wallahi ko ni sai dai rahama ta kai ni. Amma aiki na ba zai kai ni aljanna ba. Shiyasa wallahi ka daina ɗaga hanci kana hurawa kana ganin kai wata tsiya ce. Duk gaba ɗayan sallar da kake da azumin ka da zikirin ka da karatun alƙur'anin ka da biyayyar iyaye bai kai Allah ya saka ka a aljanna ba sai dai ƙa'ida ce da Allah yace Wannan rayuwar an halicce mu ne dan a jarabce mu wanene zai fi kyautata aiki. Wanda yafi kyautata aiki da ƙwazo sai a ɗauke shi a kai shi aljanna don kyakkyawar niyyar shi ba wai don aikin shi. Ya zan aikin ka ne yasa aka baka aljanna a'a. Allah ya shiryar damu.
[Speaker seg2-spk:1]
Amin.
[Speaker seg2-spk:0]
To dan kada uba yayi fushi yace to ai ma dai yanzu ma dai mu ba'a san darajar mu ba. An saka karatun littafi ance iyaye maza basu da daraja. Sai Bukhari yace dattijo kayi haƙuri. Babun biyayyar ka. Umm. Bukhari yace a bika kaima. Amma dai ance uwa ta fika. Shine kawai abin da aka ce dan haka kayi haƙuri. To ai kai kuma an baka gwamnati ko gwamnati a hannun ka take. Gwamnatin kace gidan amma kuma an fika daraja. Eh ba haka ba sai ka ga shugaban ƙasa da diploma ko mataimakin shugaban ƙasa da diploma ƙarƙashin shi kuma ga professor a ofishin shi. Ba haka bane?
[Speaker seg2-spk:1]
Haka ne.
[Speaker seg2-spk:0]
To haka nan ma kaine gwamnati amma kuma dai an fika daraja a gidan. Wannan ainihin almajirin Abu Huraira a cikin wannan hadisi kunga Abu Zur'a kenan ko? To karku ruɗe Abu Zur'a ba Abu Zur'atar Razi ba. Abu Zur'a wannan tabi'i ne. Akwai Abu Zur'atar Razi mutumin ƙasar Rayyu abokin abokin Abu Hatim Razi. Dan wasu suna ruɗewa saboda al'amarin sunaye yana kama da juna. Sai kaga suna kaza a cikin sahabbai ga mai suna kaza. A cikin ainihin malamai na fiƙihu game irin wannan sunan. To sai kazo ka ruɗe. Zaka zo kana karatu cikin fiƙihu misali. A cikin fiƙihu kana cikin karatu sai kaji ance ga wani mutum mai suna Ibnu Abi Huraira. Wani malamin fiƙihu ne ba Abu Huraira wancan da ka sani Addausi ba. An fahimci wannan da kyau ko? Amma wani ne daban da wannan ainihin laƙabin. Haka kana cikin karatu zaka ji wannan Abu Zur'atar Razi. To wannan wani malami ne cikin malaman hadisi. Akwai kuma Abu Zur'a shine wannan ainihin tabi'in. To shine almajirin wannan ainihin sahabi. Kamar Abdullahi Ibnu Zubair sahabi ne na annabi sallallahu alaihi wasallama. An gane wannan? Abdullahi Ibnu Zubair sahabi ne na annabi jikan Abubakar Siddiƙ. Shine ɗa na farko da aka haifa wa musulmi a lokacin da aka dawo Madina. Abdullahi Ibnu Zubair. To sai kuma in ka buɗe Bukhari hadisin farko a cikin sahihul Bukhari sai kaga Humaidi mai suna Abdullahi ɗan Zubair ya bamu hadisi. To karkace to ashe Bukhari ma yayi karatu gurin sahabbai. Ashe Bukhari tabi'i ne. To kai kuma kazo ma tabi'i ga jahilci. A'a abin da ake nufi sunan ne yazo ɗaya. An gane wannan da kyau ko? Wani malami ne mai suna Abdullahi Ibnu Zubair. To akwai kuma sahabi mai suna Abdullahi Ibnu Zubair. To sai ka rinƙa banbancewa shine yace ya karɓo daga malamin shi Abu Huraira. Aka ce ya manzon Allah wanene yafi cancanta da in fiwa biyayya shine asalin wannan kalma. Wanene yafi cancanta da in fiwa biyayya cikin iyaye na? Annabi yace ummaka. Mahaifiyar ka. Yace ya manzon Allah sai kuma wa? Manzon Allah yace ummaka. Mahaifiyar ka. Yace ya manzon Allah sai wa? Manzon Allah yace nace uwar ka ita ta fi cancanta da ka fi fifita wa wajen biyayya. Sai yace sai wa? Sai manzon Allah yace sai kuma mahaifin ka. To anan ma sai irin na ɗazu ɗin yace a cikin nuska wanda yayi da ba an samu ƙari da cewa Sannan sai ya faɗi Abu Jama'a mun gane wannan da kyau? Irin wannan abin da yake faruwa bari ku ji aiki ne na ta haƙiƙi. Idan kazo yanzu bari in maku misali da abin da kafi sani. Ace yanzu sai ka ɗakko littafin Nurul Albab na shehu Usmanu ɗan Fodio Allah ya gafarta mishi. Sai kace to abin da zakayi tunda yanzu ne za'a fara wa wannan littafin bugun inji. To bari kaje ka tattaro rubutun hannu irin wannan bugun rubutun sharƙiyya namu na gida. Sai kaje sai ka siyo. Ga wannan nuska a Kano aka kofe ta. Wannan a zari aka kofe ta. Wannan a ƙa'ida fa in zakayi ta haƙiƙi aiki ne. Zaka je duk malaman nan namu na soro na cikin garin Zariya sai ka rinƙa bin su. Akar makallahu ko kana da wani littafi Nurul Albab in yace eh sai ka samu kofin hannun shi. Sai ka gwada da waɗannan da kake da su sai kaga baka da irin shi sai kaje kayi photo start sai ka mayar mai da nashi. Haka zaka kewaye kamar cikin garin Zariya, cikin Sokoto, cikin Kano, Katsina, Bidda duk ƙasashen nan da kasan ana karatun ainihin soro sai kafi kayi waɗannan binciken. In ka tattaro waɗannan nuska sai ya zan ka tattara nusko kin nan kamar guda goma. Sai kafi sai ka karance su duka. Sai ka samu takarda kane kana kofe wa. To daga ciki sai ka dubi wacce ce tafi kyar rubutu da kuma tsafta da tsarin rubutu. Sai kace ka mai da ita ita ce asali. To in kazo sai ka sa mata suna da harafin da kaga dama. Misali sai kace kasa mata To duk sanda kace A cikin nuskar da ka mai da ita ita ce ta asali kaza ne. Nuskar da ka samo a Zariya sai ka sa mata To sai irin abin da suke nufi kenan zaka ga in kana karatun wasu littattafai da akai haƙiƙi sai kaga a ƙasa yace maka A cikin nun kaza aka ce wato yana nufin a cikin nuska kaza. Jama'a mun fahimci wannan da kyau ko? To a farkon wannan littafin ya ainihin wato kawo abubuwa kamar yadda na nuna mana ran nan nuska ta farko da ta biyu da ta uku. To duk sanda kaji yace To ita ce nuska ba wadda yake ainihin ishara akan ta. Allah ya mana taimako akai. Malam Muhammad Nasiruddin Albani sai yace Wannan ainihin wato hadisi sahihi ne. Ka duba A lamba hadisi na ɗari takwas da talatin da bakwai Ta hata a ƙarƙashin lamba hadisi na dubu huɗu da ɗari tara da casa'in da biyu. A ƙarƙashin nan ne da yazo yana maganar wasu hadisai da basu inganta ba. Har kuma ya kawo wannan yace amma shi wannan ya inganta. In kaji yace maka ka duba littafin shi Kuma ka nemi hadisi sahihi a gurin wato yazo kawo wani hadisi ne mai mai rauni. Sai bayani ya kama sai kuma ya kawo wani da ya inganta a ƙarƙashin shi. Sai yace to Asali kuma wannan hadisi yana nan a cikin Bukhari Babin dake bayani akan mutumin da yafi cancantar da kafi kyautatawa a cikin al'umma. Anan Bukhari ya kawo wannan hadisi. Mimun ɗin nan da yasa kuma yana nufin Muslim. Muslim ya fitar da wannan hadisi a lamba kitabi na arba'in da biyar. Shine ainihin Littafin biyayya da sadar da zumunci da ladubba a cikin ainihin wato lamba hadisi na ɗaya da na biyu da na uku. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Abu Zur'a yace malamin mu Abu Huraira ya karantar damu cewa wani mutum yazo gurin annabin Allah annabi Muhammad Wannan mutum yace ya manzon Allah me kake umarni na da shi? Sai manzon Allah yace ina umarnin ka da biyayyar uwa. Summa ko? Ada sannan sai ainihin mutumin ya sake cewa ya manzon Allah me dai kake umarni na da shi? Biyayyar uwar ka shi nake umarnin ka da shi. Sannan sai ya koma ya sake tambaya dai ya sake kumawa. Sai manzon Allah yace Mutumin da ya sake a karo na uku Manzon Allah yace ina umarnin ka da biyayyar uwar ka. Sannan sai ya koma karo na huɗu sai yace Sannan kuma biyayya da uban ka ga uban ka. Jama'ar musulmi ku saurara da kyau ku ji mune ƴan izala. Mu da kuka ji muna karatun nan mune ƴan izala. Kun ji irin karatun namu, kun ji darajar iyaye a gurin mu. Duk wanda yaje ya same ka a ƙauye kai ba ƙauye kaci dankali ka take cikin ka kana kwance gindin kargo yace maka ai wasu mutane ƴan izala sunce a wulaƙanta iyaye. To ka dai ji mu dake jawabin nan mune ƴan izala. Wannan jawabai duk da ake zuwa ake maka ta soƙeyar wanda ke maka ka ce ya nuna maka ɗan izala guda ɗaya wanda ainihin ya wulaƙanta uwar shi ko ya wulaƙanta uban shi da umarnin izala. Izala bata taɓa cewa je ka ka wulaƙanta uwar ka ko je ka ka wulaƙanta uban ka ba. Duk wanda ya wulaƙanta uwar shi ko uban shi da sunan ɗan izala ba ɗan izala bane ɗan iska ne. Mu ƴan izala mu muka faɗi haka. Ba namu bane nasu ne can. Dan haka ku gane wannan da kyau jama'a. Saboda har yanzu irin wannan faro fagandar ana nan ana yawo da ita a ƙauyuka kuma masu yawo da faro fagandar nan galibi wasu masu wa'azin neman na batir ne da masu tara ƙwona da masu wa'azin tirmi. Ba dan komai ba dan su karkato hankalin jahilai zuwa gare su. Suna zuwa kasuwar ƙauye sai su fasa salati To za'a yanke aljihun su kenan. Sai ace yanzu yanzun nan daga gari kaza muke. Yanzu yanzun nan wani ɗan izala ya ɗakko gora ya ainihin make uban shi. Shikenan don a kamo
[Segment 3/4 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker unknown]
hankalin su ne za'a faɗi haka, to waɗannan abubuwa duk sharri ne jama'a, ɗayan irin waɗannan abubuwa bai faru ba, amma mas'ala ce wadda yake, harka ce muka tashi mu ga kan mu a cikin al'adun gargajiya, al'amarin ya cude tare da ainihin addini, sai muka ce al'adar duk da ta saɓa wa musulunci, ba zamu yi ta ba, ma'ana ashe bamu ki al'adar hausawa ba, in ba haka ba yanzu kayan da kake gani na suke jiki na, ai al'adar hausawa ce baki ɗaya, amma me yasa bamu ƙyamace su ba? domin basu saɓa ma addinin musulunci ba, to duk al'adar da ta saɓa ma addinin musulunci sai mu ce ba zamu bi ba. To shikenan ba zamu bi wannan al'ada ba, to sai a koma ana cewa ai mun bi bin iyaye, to sai ya zama wata al'adar tayi karo da sunna. To kuma a ƙasar nan an saka wa mutane wani bala'i a karatun soro, in kana karatun soro karatun zaure, zaka ji ana Ai al'adar gari yaro kamar sunna ce, ma'ana in dai aka ce al'ada kowa yana bi to kaima ka bi don ka zauna lafiya da jama'ar garin ku, to mu ƴan izala da muka zo sai muka ce to duk abin da yake ya wannan ci addini, matuƙar ba addini bane, to ba zamu yi ba, to sai ya zama wani abu in muka ce ba zamu yi ba, sai kuma ya zama iyayen mu suna so mu yi, to sai mu dube ai Allah maɗaukakin sarki ne ya ce mana mu bi iyayen, ba don ma Allah ya ce mu bi su ba mu da bamu bi su ba, amma Allah ne ya ce mu bi su, to tunda Allah ya ce mutum mun ja kunnen shi ya kyautata wa iyayen shi. Sai kuma Allah ya ce Amma in iyayen ka suka nemi rikici da kai akan ka shiga harkan da baka da ilimi a kanta, ka shiga abin da yake ya saɓa mini, Allah ya ce ahir kar ka sake kayi musu biyayya, amma duk da haka sai Allah ya ce Iyayen ka ne, duk da ka ki bin su akan waccen ainihin abin da suka nema, amma ka kyautata musu a nan duniyar. Ashe har yanzu da ka ki bin su akan waccen maganar, kyautata wannan da ka saba yi, ka je musu gona, ka ɗaukan musu kaza, kayi musu kaza, wannan wajibi ka ci gaba ne koda uban ka ne sarkin maguzawa. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? to shikenan sai in waɗannan malaman turmi suka tashi saboda sharri, sai su ce ga annabi ibrahim yana wa uban shi tallan gunki. Gashi yana yawo yana tallan gunki, jama'a wanene zai sayi abin da ba zai amfanin shi ba duniya da lahira? wannan ƙarya ce, annabi ibrahim da ya je ya rusa gumaka, aka zo aka tambaye shi wanene ya rusa waɗannan gumaka? ya ce ah Wannan babban nasu da kuka gani shine ya karya ya su, ai wasu basu gama mutuwa ba wane ƙafar shi aka sare ku tambaye shi shi dange shi yake zai iya jawabi in dai suna magana. Allah ya ce sai suka tsaya su da kan su suka yi tunani, sai suka ce To ai kai kan ka ibrahim dan dai neman fitina ne kaima kasan basa magana, to kun ga ya biyo musu yadda ake wa'azi kenan, sai ya ce Ya ce yanzu nan abin da ba zai cuce ku ba bazai amfane ku ba, kuke bauta mishi, Allah wa dare da ku yanzu ku dube kalmar da Allah ya ce kar ka gaya wa iyayen ka ita ya faɗa. Allah ya ce Kar ka ce wa iyayen ka kash, ahir kar ka ce musu haka, amma kuma sai ga annabi ibrahim kuma ya ce Yanzu an nan ba ya faɗa musu haka bane a matsayin iyayen shi, ya faɗa musu haka ne a matsayin arna ne masu bautar gunki. Kun gane yadda ƙur'ani yake ƙur'ani ba rikici a ciki. Can umumin iyayen ka kuna magana kar ka ce Amma nan yana magana da wasu arna ne, ba a matsayin iyayen shi ba, a matsayin arna ne shi kuma annabin Allah. To in kuka gane haka, sai ku ga ashe waɗannan kisso shi na annabi ibrahim sun fassara mana waccen aya ta cikin suratul luƙmana kenan ko cikin suratul ankabu. Menene ashe ayar take cewa? lallai ka bi iyayen ka ka kyautata musu, amma in suka yi jahilci da kai ga abin da ya shallake ƙa'idar Allah, to anan kuma kam babu yadda zaka bi su, amma duk da haka saboda uwa uwa ce, uba uba ne sai Allah ya ce Ya ce ina jan kunnen ka fa ka fi kyautata wa iyayen ka a duniyar nan, to wannan shine taurin kan mu mu ƴan izala. Abin duk da ya shafi shirka ne in iyayen mu suka nemi mu yi ba zamu yi ba, abin duk da ya shafi bidi'a ne in iyayen mu suka nemi mu yi ba zamu yi ba, kuma abin sha'awa shine duk abubuwan nan da muka ce shirka, duk abubuwan nan da muka ce bidi'a, ba ƙirƙirar kan mu bane, budewa muke yi daga cikin littattafan manyan malamai, manyan bayin Allah, har daga cikin su akwai su shehu usmanu ɗan fodio, da shehu abdullahi na gwandu, da malam muhammadu bello sarkin musulmi, da nana asma'u, daga cikin littattafan nan zamu buɗe, gashi cikin ihyau sunna, shehu usmanu ya ce kaza bidi'a ne, cikin kaza shehu usmanu ya ce kaza ba kyau, to sai mu ce ba zamu yi ba, tunda shehu ma da kan shi ya ce ba kyau, to sai a samo wani uba sai ya ce sai anyi, to anan sai a je ana yawo ai ƴan izala suna saɓa ma iyayen su, kun ga duk propagandan nan da akai fa bata yi tasiri ba saboda me saboda ƙarya ce. Sai ka je dama turu, sai ka ji ana bada labari ai wani ɗan izala yana nan ya buge uban shi, a ina? sai a ce a gashuwa, sai a ce to a je abinci ka, ana zuwa gashuwa sai a ce a'a ina a fulatan ne, fulatan jahar kaduna, kana zuwa fulatan sai a ce ina? can manbila ne akai can wajen jahar taraba, haka zaka kewaye ƙasar nan baka samu ɗan izala ɗaya da wannan maganar ta tabbata gare shi ba, amma kafin izala ƴa'ya nawa ne suke saɓa ma iyayen su? amma baka taɓa jin an kira wannan da sunan wani addini ba, ashe ka ga nan ɓatanci ne, duk da izalar tana nan yanzu ƴa'ya nawa ne suke ƴa'yan iska suna saɓa ma iyayen su? baka taɓa jin an zarge su ba, amma saboda mu Allah ya taimake mu mun zama na gari, mun samu halin nagarta, shi yasa ake ƙoƙarin haɗa mu da iyayen mu don a ɓata tsakanin mu kuma a je cikin garuruwa a nemi mana sharri, wallahi azimi Allah ya fi ku. Amma mu dai ƴan izala muna bin iyaye, muna kyautata musu, domin mu biyayyar ma a matsayin ibada ce, kai ko da yake kasgi ne kana bin uban ka ne da ka kawai, da ka kake bi ba wanda ya ce ka bi shi baka san me yasa kake bi ba, amma mu ƙur'ani ne da hadisi ka je ya ce mu bi, saboda haka mu muna ganin in bamu bi iyayen ba wuta zamu je. Kai kuwa kana ganin abin ne da ka kawai, kana yi ne Al'ada ne kawai kai da gadon gargajiya, shi yasa duk irin biyayyar da ka samu yi kake, mu ko muna yi ne ainihin akan yadda shari'ar musulunci ta ce, to don haka iyayen su san wannan, kaɗai don ɗan ka ya shiga izala ai shikenan kai bala'in duniya ya same ka, a da da ɗan ka yake iskanci ya sha giya, ya je wa ƴan mata ciki, ya je yayi sata, ya cinye kajin mutane, ya buge agwagi, ya sace ainihin tumakai, duk waɗannan abubuwan sau nawa kana zuwa police station? Ka je ka karɓo shi, sau nawa ana kulle ka? sau nawa kana ɗiban rikici saboda ƴa'yan ka? amma duk waɗannan abubuwan sai ka ga kamar wai yaron ba wani abu bane domin me? kamar ya bi yadda ake rayuwa ne, amma da zaran ya ce addini wai duk sai a tara dattawan anguwa wai za'a tsine mishi albarka don ya shiga aure, ai dai dai dai ya shiga ainihin izala, da yanzu za'a ƙwace mata, za'a kashe aure, ba za'a bashi kaza ba, ba za'a bashi kaza ba, ƙarshen lokaci kuma sai ku dattawan da ake zugawa, da zaku koma kuyi nazari sai ku ga waɗannan da suka zuga ku ɗin su ƴa'yan su suna ina? Su ƴa'yan su mala'ika ne jibrilu koko mala'iku ne a saman bakwai suke tasbihi? A yayin da suka zuga ka kai faɗa da naka ɗan, shi kuma nashi yana can shine yake manajan sulma. Kai kuma nan ance naka ɗan iska ne shi kuma wancan ɗan aljanna ne ko sulma aljanna firdausi ce? Ka ga inda basira take ɓacewa mutane. Har wani har ya sallami ɗan shi da daddare ya ce in gari ya waye ɗan ya ƙwashe kaya tunda ya shiga izala, daddare sai ga shehin ɗariƙa babu ya zo yana ainihin karatun hadisi, yana karatu yana karatu, can da karatu yayi karatu, sai ya ce ita ɗariƙan nan da kuke ji fa tanfurari ce ba itace asalin addinin ba, to uban asali ya taɓa kasan mutum ya dan taɓa aikin gwamnati ko bai karatun boko ba ya san wasu kalmomi na turanci. To kowa ya san tanfurari, duk tanfurarin fa kwano ba zata daɗe ba ko? kaftin a kwashe in ya zo zai ce a kwashe ko? to saboda haka nan da nan sai uban ya kira shi, ai kai da akan tanfurari zamu rabu? Ya ce kayi zaman ka, ni na ɗauka addini ne ashe tanfurari ne. Ka gani? Allah ya shiryar da mu. To shine malam muhammad nasiruddeen albani Allah ya gafarta mishi ya ce sahihun, wannan ainihin hadisi sahihi ne. Ka dubi hadisin da ke kafin shi, ma'ana ka duba za'a ka je ka ga inda aka tattake wuri waɗannan hadisai ne ingantattu. Babin da ke bayani akan ɗa ya bi iyayen shi koda iyayen nashi sun zalince shi ne. Me dalilin bukhari akan haka sai ya ce Saboda abin da yasa yayi marmaza ya ce saboda hammadu guda biyu ake da su, akwai hammadu ɗan salama, akwai hammadu ɗan zaid malamin su abu hanifa. To kar ka ce hammadu, in ka ce hammadu galibi sai ayi tunanin ko wancan ne, shi yasa sai kayi marmaza ka ce wana fa ake nufi. An fahimci wannan da kyau ko? Daga shi ya ce ya karɓo daga Babu wani musulmi da zai zan yana da iyaye guda biyu musulmi Yegaggawa ya tafi gare su domin neman lada ya sammako shine Ba da ance ya kwana tare da su, amma mai wa gidan shi daban, gidan iyayen daban, gari na wayewa sai kayi marmaza rufe shi da ne, ka rufe bakwai ne, sai kayi marmaza ka je wurin iyayen ka wai inda wata buƙata tunda ɗumi ɗumi ka biya musu wannan buƙata. Shine aka ce annabi Babu wani musulmi da zai kasance haka illa Sai Allah ya buɗe wa wannan musulmi ƙofofin aljanna guda biyu In kuma iyayen nashi ɗaya ne ya rage to ƙofa ɗaya kenan za'a buɗe mishi. In har shi ɗan ya sake ya fi satar da ɗaya daga cikin iyayen nan, Allah maɗaukakin sarki ba zai taɓa yarje mishi ba, har sai ya dawo ya ainihin yardar da mahaifin nan nashi. Sai aka ce Ya manzon Allah koda waɗannan iyayen nashi sun zalince shi Koda sun zalince shi, sun cuce shi, Allah sai ya ce Koda ainihin sun zalince shi koda sun cuce shi. Sai malam ya ce Wannan isnadi mai rauni ne domin da ka ji ma'ana ba'a san shi ba, wanene shi? a ina yayi karatu? daga ina yake? su wanene malaman shi? ina ya fito? ma'ana dai kawai anji sunan ne kawai shi ake nufi da To in ka ji ance ba wai kai da ni in bamu san wana ba mu su waye? Ana nufin malaman duniya waɗanda su kan su hadisi ne a cikin ilimi, to in suka ce basu san wana ba irin su irin su irin su malam Allah ya ji ƙan maza, manya manyan bayin Allah da waɗanda su sun narke a cikin ilimin hadisi. To in suka ce basu san wana ba to shikenan magana ta ƙare. An gane wannan da kyau? kai ko don kace baka san wana ba malamin ango kuma baka san sunan shi ba. Ka ga ba mamaki, to sai ya zama wannan isnadi mai rauni ne, amma mas'alar da yake ɗauke da ita zamu zo mu samu hadisai da za'a mara mata baya, wato al'amarin koda ya zama akwai zalunci da kake ganin mahaifiyar ka ta zalunce ka, tunda zalunci ne tsakanin kai da ita. Misali kawai sai mahaifiyar ka sai kana da gida sai ta ce ta ƙwace gidan. Ko kuma kana tana zuwa gidan ka kawai sai ta samu ka tattara kuɗin haya sai ta ce kawo nan. Ka ce to ai sadaki zan je biya, ta ce ka kawo nan, ta ce to ni dai an zalince ni to wannan maganar ba bi halatta ka faɗa ba. Tunda ta murɗe ta karɓa ta ci halal. Jama'a mun fahimci wannan da kyau ko? wannan shine abin da hadisi yake hukunta to hukuncin haka yake amma shi isnadin nan shi yasa ka ji malam da yake ƙwararren malami ne sai ya ce Isnadin ne mai rauni amma a maganar fa ta inganta zamu samu tabbatar ciyar ta a gaba. Allah maɗaukakin sarki ya shiryar da mu. Babin da ke magana akan tausasa magana ga iyayen shi, in zaka yi magana ga iyayen ka sai ka riƙa faɗi da taushin murya, kana sauke murya ka ka neme musu magana ta cikin ladabi, ɗan shagwaba shagwaba ne, ɗan takwarkwashe wane haka, kar ka zo kana magana da mahaifin ka ko mahaifiyar ka kamar yadda kike magana da ƙawarki ko kamar yadda kake magana da abokin ka gatsa gatsa haka, koda mahaifin nan naka fa ya zo wurin ka ne da buƙata, ya zo wurin ka ya ce ka sai mishi kaza ko kayi mishi kaza sai ka ce ka ƙara haƙuri babu hali ko kiyi haƙuri babu hali, magana mai taushi dai, to me dalilin bukhari akan haka? Ko? Shi wannan ya ce na kasance Tare da ainihin Tare da An kira su ne ga haka kamar yadda malam ya faɗi su ne Mutane ne daga cikin ƙabila Wasu mutane ne su kuma wato mutane ne waɗanda suka yi husanci a musulunci. Da akai rikici tsakanin sa habbai Wasu suka zagi waɗannan wasu suka yabi waɗannan, su Suka ce kowa ma duka kafirai ne. To sai aka ce musu Ai sunyi wa shuwagabannin musulunci ta waye, sai suka fita sai suka kafa wani gari, sai suka je suka kafa gari a wata anguwa da ake kira To sai aka koma ana kiran su Ke baharuriya ce, kai baharure ne ma'ana To su a cikin aƙidar su cewa suke Duk wani saɓan Allah da mutum yayi to shikenan ya zama kafiri kuma in ya shiga wuta zai dawwama a ciki. Suna da zafin mazhabi, sun fi jin haushin habbai su kuma fiye da kowa, bukhari ya ruwaito hadisi wani sahabi na cikin salla, dattijo ne tsoho yana da dokin shi haka, sai ya daure dokin nashi da igiya doguwa sai ya jawo igiyar dokin shi sai ya riƙe a hannu sai ya kabbarta salla, ya ci gaba da salla makala da igiyar dokin shi doki na can na can ciyawa. In doki ya fusga sai wannan sahabi ya dan fusga sai ya ja haka. Yana cikin salla sai wani Allah ya tsine wa tsohon nan albarka, ciki tsine nan ne kaza kaza kaza kaza kaza, shikenan sai ainihin wannan dattijo yana idar da salla, sai ya ce babu komai ni sahabi manzon Allah ne Na san halin irin ku ku Ya ce in saki dokin nawa ya je yana kiyo, ya gudu Ina tsoho a idar da salla magariba ko isha kafin in je in kamo shi tsakar dare yayi, ya fi sauƙi haka saboda manzon Allah ya zo mana da sassauci, tunda in na bi waccen ƙa'idar zan wahala, yanzu ko in na rungume hannu na na riƙe igiyar nan, ina sallar nan wannan ɗan matsawa ka dan bai ɓata salla ta ba, 11 annabi ya zo da sassauci a salla amma ku kun ci ƙazafin ka. Kharijawa kenan, in kana son ganin yadda akai rugu rugu da su, ka je ka ɗauki kitabu Na ainihin Da abu dauda Sai da ya tasa su gaba ya ragaragar da su ɗaya bayan ɗaya, wani hamshaƙin malami ne ai malanta ta kai malanta in aka ce ka karantar da abu dauda da nasa'i kuma. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? to kun dai ji wannan ainihin al'amari shine sai ainihin shi wannan ko? sai ya ce na kasance tare da Sai na afka cikin wasu saɓannin Allah Ko? Ni a iya kar gani na waɗannan zunubai da na afka to manya manyan zunubai ne Sai na je na faɗa wa ibn umar na ce mishi Allah gafarta malam wallahi ni dai zama na da waɗancan mutane gashi dai mutane ne masu ƙyamar saɓan Allah matuƙa, amma ni kuma na afka cikin wasu manya manyan saɓannin Allah. Sai ibn umar ya ce waɗannan saɓannin Allah ne, sai na ce ka ji yadda ake hikima. Ai ya faɗa wa malamin saɓannin Allah, amma yanzu da ya zo yana ba duniya labari sai ya kauce. Sai ya ce kaza da kaza. Sai malamin ya ce ai waɗannan basu daga cikin manya manyan laifuffuka. Ai manyan laifuffuka guda tara ne ka tsaya ka ji su da kyau, na farko Haɗa Allah da wani wannan laifi ne wanda ya kai matuƙa wajen ainihin girma Da kuma kisan kai ka kashe wani ɗan ka ne ko ainihin ƴar ka ko wanene kisan kai ainihin wato duk zai iya zama haka. Da kuma gudu daga filin yaƙi. Ana cikin yaƙi ka juya da gudu ka ai shi yasa aka ce malaman fiƙihu musulunci suka ce in ana cikin yaƙi Muka tabbatar da cewa yawan kafiran nan ba ya kai yawan da aka ce In wani ya ji tsoro daga cikin sojoji ya falle zai gudu to ku sa bindiga ku harbe shi. Ko wane soja ya san akwai wannan ƙa'idar don haka ba damar ka gudu kenan. Domin in ka tsaya me kake tsoro? Kisa To ba tabbas za'a kashe ka ko ba za'a kashe ka ba, amma in ka juya ka gudu fa sai aka ce a sa bindiga a tashe ka a yi. Domin zaka wargaza mana taro, kana gudu mai yi wa kai wani sadauki ne sai wana ma ya sa kai, sai wana ma ya sa kai to ya ka sa an ci mu kenan, da wannan sai ainihin aka ce lallai gudu a filin daga haramun ne yana daga cikin manya manyan zunubai. Da kuma yin ƙazafi ga mata wadda take mutumin niyar kirki, kaman miya, kan malalliya, mai mutunci, sai kawai sai ka ce kai da Allah waɗannan sai
[Segment 4/4 | 01:00:00–end]
[Speaker seg4-spk:0]
in iska ne kaza kaza kaza, mu mai bamu sani ba a duniyar nan, dan kasan yar iska kuma kowace yar iska, kowace mace yar iska ce? To me yasa aka yi ta abiri da mace? Saboda an fi wa mace kazafi galibi fiye da namiji. Namiji an fi zargin shi da sata, shi yasa kuka ga da Allah ya tashi maganar barawo sai ya ce Da Allah ya tashi hukuncin zina sai ya ce Wajen zina mata sun fi yawa. Sata kuma da yake mai kaushin hali ke iya yi sai namiji shine zai zo ya same ka zafi yayi zafi ka tinko ka fito waje, shi kuma sai alkafura ya shiga dakin yaje ya dauko rediyon ka yazo yana harin ta ina zai kitare ka. In ba namiji ba wa zai iya wannan? To saboda haka sai aka fara da barawo a wajen yanke hannu namiji, amma a wajen zina saboda harka ce da mata sun fi yawa tayi sai aka fara da mace. To anan ne sai yasa wannan yake sa ana yawan zargin su. Wannan yawan zargin su da ake yi shine ya ja sai kaga duk inda za'a yi maganar manya manyan zunubai sai ace yana daga cikin babban zunubi yi wa ainihin mace kazafi wadda take macen kuma muhusina. Me ake nufi da muhusina? Ita ce wadda jama'a masu kirki zasu dube ta su ce wancan mutuniyar kirki ce. Sirrin ta kuma fa wannan Allah ya sani. Amma dai ka ganta ta wuce mutuniyar kirki da hijabi to mutuniyar kirki ce. In haka kace kai da Allah in za'a sa hijabin ba an ji masu zanzare da jins ka gani in kaga wata tana yin haka ita yanzu wannan da kake magana akan ta ka ganta a haka? Baka ganta a haka ba to wallahi sai ka saka kanka a wuta. Wadannan irin abubuwan sune zasu sa ranar kiyama sallolin nan da kake da azumin nan da duk biyayyar iyayen can sai a kwashe sai a biya irin wadancan da kake zagi kaga al'amari ya baci. Jama'ar musulmi mun gane wannan da kyau ko? To gashi kuma karatun ya karatu lokaci ya ainihin kure mana. Sai gobe insha Allahu ta'ala zamu zo sai a cigaba da wannan karatu
============================================================
[Part 9]
============================================================
[Segment 1/4 | 00:00:00–00:20:00]
[Speaker seg1-spk:0]
Yau talata 17 ga watan Jumada al Ula Hijira Annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallam na da shekara 1422 wanda ya daidai da shida ga watan August shekara ta 2001 muna karatun littafin al Bukhari Allah ya gafarta mishi a inda muke karkashin babin da ke bayani akan ɗa ya tausasa ainihin magana ga iyayen shi guda biyu na kasance tare da Najidawa wato Khawarijawa wannan hadisi jiya mun fara karanta shi mun yi duk bayanai akan haka sai lokaci ya ƙure aka ce ana kiran su waɗannan Najidat ne saboda malamin su mai suna Najidatu dan Amir al Khariji sune dai ainihin Haruriyya saboda lokacin da suka yi tawaye suka kafirtar da sahabban Annabi sallallahu alaihi wa sallama sai suka je ƙauye suka kafa gari a Hirawra shine sai ake ce musu ainihin Haruriyya to sai yace na kasance tare da waɗannan mutane sai na afka cikin zunubai masu yawa ainihin su waɗannan zunubai ɗin ni a iyakar gani na waɗannan zunubai manya manyan kabairai ne sai naje na faɗa wa Ibn Umar cewa Allah gafarta malam na zauna tare da ainihin Khawarijawa har al amari ya kai al amari gare ni na faɗa cikin zunubai na sabon Allah menene wai sai ainihin shi wannan ainihin sahabi yace waɗanne zunubai ne sai ainihin nace kaza da kaza ne kala sai yace ai waɗannan abubuwan duk da kace ka aikata zunubai ne amma basu kai ace manya manyan zunubai ba su ainihin kabairai ɗin nan ai guda tara ne na farkon su shine shirka ka haɗa Allah da wani wannan babban zunubi ne da kuma kisan kai da kuma gudu a ainihin filin daga da kuma yi wa ainihin mace mutuniyar kirki kammalalliya kai mata ƙazafi kace mata ƴar iska ko mazinaciya da cin riba to daidai nan ne jiya sai lokaci ya ƙure mana munyi bayanai akan ainihin waɗan can tare da cewa Abdullahi dan Umar yace manya manyan zunubai guda tara ne ɗin nan ba fa wai iya kacin su kenan ba inna ma kowane sahabi yana faɗin abun da ya sani ne shi yasa Ibn Abbasi yace sun fi kusanci da saba'in fiye da guda bakwai saboda akwai wani hadisi da Annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallama yace guda bakwai ne sai shi Ibn Abbasi yace ai sun fi kusanci da saba'in fiye da bakwai ashe can da Annabi sallallahu alaihi wa sallama yace guda bakwai wannan shine an batar wani ɓangare na daga cikin tarin abubuwa masu yawa baya nuna su kenan waɗannan guda kaza da aka faɗa amma yana ƙarfafa ya tabbatar da cewa lallai waɗannan fa suna daga cikin waɗannan jerangiyar abubuwa shi yasa kamar yadda kaji can cikin hadisin Bukhari inda Annabi ya lissafa mutane goma yace waɗannan goma ƴan aljanna ne shin Annabi yana nufin su kaɗai ne ƴan aljanna to amma ƴan shi'a saboda rashin fahimtar karatu za kayi mamaki sunna ce ta ƴan shi'a jahilci jahilci sunna ce da ƴan shi'a suka ga da tun daga na farkon su har zuwa na yau haka suka siffantu da jahilci in suka karanta nassi kawai suka ainihin ji menene iyakar fahimtar su ta basu sai yace iyakar ma'anar shi kenan basa duba ƙa'idoji na ilimin usulu basu duba ƙa'idoji na ilimin in ba haka ba Annabi sallallahu alaihi wa sallama tuni yace Fatima ƴar aljanna ce ba ma ƴar aljanna ba gama gari kawai sai yace ita ce ma sarauniyar matan aljanna Hassan da Husaini ƴan aljanna ne ba ma ƴan aljanna ba su ne kaɗai su ne shuwagabannin samarin gidan aljanna Fatima tace ya manzon Allah naji ana ta cewa wane dan aljanna su wane su wane uwa ta Khadija da aka fara musuluncin nan da ita yaya ita kuma sai Annabi yace ai wa Khadija albishir da gida ƙanƙarere a cikin aljanna gidan ƙarau da Allah yayi mata shi wanda iken na tsatstsen gida ne babu hayaniya a cikin shi ga ainihin wani sahabi Annabi sallallahu alaihi wa alihi wa sallama yace dan aljanna ne ga Bilal Annabi sallallahu alaihi wa sallama yace dan aljanna ne to shikenan waɗannan sai ya zan daga baya sai Annabi yazo yace yace ga mutum goma ƴan aljanna to ƴan shi'a saboda dindikwalon ƙwaƙƙwanya da suke da ita sai suka ce wai to waɗan can kuma fa misali alhaji wane ƴan labai wane duk shekara ya ɗauki wane da wane ya kai su hajji duk shekara mutum ɗaya mutum biyu ya kai su hajji sai kaji labari baya yaɗuwa sai aka samu bana sai yace mutum 200 duk yayi musu kujerar hajji ina ne labari ba zai je ba shin cewa yayi wa mutum 200 kujerar hajji ɗin nan tana nuna kuma waɗan can da da aka riƙa musu ɗai ɗai ɗai ɗai a da ƙarya ne abu ne mai sauƙin fahimta amma in baka yi karatu ba ko kuma kayi karatu kana da son zuciya sai kayi ta murɗa mutane kayi ta hallakar da su dama waɗan can su Khadija su Fatima su wane ne su wane su wance duk ance ƴan aljanna ne to amma me yasa labarun su bai yaɗu a gari ba saboda ɗai 1 1 ne aka rinƙa faɗin albishir yau sai ya hau kan minbari yace goma ƴan aljanna ba'a taɓa irin wannan a lokaci guda ba ya lissafa su Abubakar Umar Usman Ali sai ainihin Abu Ubaida Ibnul Jarrah gashi nan ya lissafa su waɗannan mutane guda goma da ya lissafa a lokaci guda sai labari sai ya yaɗu ko ina shikenan sai ƴan shi'a suka ce to Hassan da Husaini fa jama'a kun fahimta
[Speaker seg1-spk:1]
na'am
[Speaker seg1-spk:0]
to yanzu me yake da nauyin fahimta a wannan alhaji wane da aka biya mishi kujerar aikin hajji tun yaje ya dawo wanda ya biya mishi ɗin nan bana kuma sai yace ya biya wa mutum 60 a ƙauyen nan shikenan kuma sai ace to wancan kuma hajji shi bata yi ba ko an soke shi haka al'amarin ya faru an riga wa dan can an yi musu albishir da aljanna yau kuma sai Annabi yazo ya faɗi wasu guda goma sai yace ga su ƴan aljanna kaga labarin goma ɗin nan da ba'a taɓa irin su gaba ɗaya ba sai ya habbaka fiye da labarin ɗai 1 1 1 ɗin can ko kun gane
[Speaker seg1-spk:1]
na'am
[Speaker seg1-spk:0]
haka al'amarin nan nan da kaji Annabi ya ce waɗannan ainihin kabairai guda bakwai a wannan gashi Ibn Umar yana cewa guda tara to duk waɗannan kar kace ruɗani ne kamar inda zaka je kaje Annabi yace guda bakwai mutane bakwai Allah zai saka su a karkashin inuwar shi a ranar da babu wata inuwa sai tashi sai ya lissafa su waɗannan mutane bakwai kana nan wata ran kuma sai ka sake ganin wata falalar da zata kai mutum ga inuwar aljanna kuma ba daga cikin waɗan can bakwai ba to wannan ita ce wadda za'a ce ai wannan ma'ana cewa da Annabi yayi bakwai ɗin nan ba asali iyakar bakwai ɗin bane amma yanzu falalar bakwai 1 ce ta zo a yanzu amma a da fa falalar wane ta zo zuwan bakwai ɗin nan bata rushe ta wane ba ko mun fahimci wannan da kyau to shi yasa wajibi ne a je ayi karatu in ba haka ba wallahi sai kayi wa kan ka ta'addanci yanzu shekaru 15 da suka wuce waɗanda ake cewa sune hamshakan malamai a cikin ƙungiyar shi'a a nan Nigeria da suka dawo suka gane cewa shi an ci ba addini bane sai ga su kuma su ƴan shi'a nan da kan su da suke cewa wane babban malami ne bari muku misali akwai wani nan da suka zo suna wa'azi a unguwar nan lokacin yana tare da su da suka ɗaga shi sai suka ce duk duk Zaria ba wanda ya kai shi karatu ana nan shikenan sai ya rabu da shehin su sai ya dawo addinin musulunci da suka zo kuma zasu yi wa'azi shi ɗin nan sai suka sake ɗaga sunan shi sai suka ce jahilin banza jahilin wofi bai san komai ba sai nace sarki ya tabbata ga Allah wanda baya tufka da warwara
[Speaker seg1-spk:1]
Allah u Akbar
[Speaker seg1-spk:0]
Allah ba zai taɓa yin haka ba jiya kace yafi kowa karatu yau kuma sai kace kuma jahilin banza jahil ba ma jahili ba na banza na wofi kaga to ashe can da ake kambama wane ana cewa karatu kar ashe ƙungiyanci kenan saboda yana tare da ƙungiyar ne yau kuwa tunda bai tare da ita to ya zama jahili ashe babu alakar ilimi da ƙungiyar in kana tare da ita kai ne malami kana fita shikenan karatun ka ya ƙare Allah ya kiyaye to shine sai yace ne jama'a mutumin duk da ya ci riba ƙaramin misali da Annabi sallallahu alaihi wa sallama yayi a cikin hadisin Imamu Ahmad wanda yazo ingantaccen hadisi Annabi yace mafi ƙarancin misalin da za'a yi wa mutum dan ya gane laifin cin riba shine hukuncin mutumin da yayi zina da uwar shi mutumin da yayi zina da uwar shi ai mu muna ganin ya kai laifi matuƙa ko to wannan ƙaramin misali kenan na na riba ƙaramin misali kenan na riba jama'a mun gane wannan da kyau Allah ya kiyaye sannan ranar alkiyama kuma Allah yana cewa waɗanda basu ainihin daina cin riba a nan duniya ba ɗin nan basu tuba ba ba zasu iya miƙewa ba sai dai irin miƙewar wanda shaiɗan yake make shi in shaiɗan aljani ya shiga jikin mutum in yana farfadi yaya kake ganin shi ya miƙe ya faɗi ya buga wannan ya faɗi haka masu cin riba zasu miƙe ainihin a filin alkiyama sai Allah yace ba dan komai ba cewa suka yi ai da ai da ciniki da riba ai duk ɗaya ne yanzu in kuka dubi haka Yahuda da suka maida duniya ta zama suka ainihin hargitsa harkar duniya sai ya zan riba ta riga ta saje yanzu da riba da kasuwanci duk ɗaya ne kamar yadda Allah yace abun da suka faɗi kenan to shi yasa Allah yayi musu wannan mummunan sakamako da kuma cin dukiyar maraya an bar maraya a hannun ka ko marayu a hannun ki ko makamantan haka sai ka turmushi musu kuɗi ka zalunce su babu shakka ranar alkiyama zaka raina kan ka da kuma ainihin wato ta'adi ɓarna a masallaci ka taho masallaci masallacin ka'aba ne masallacin juma'a ne masallacin salloli biyar ne kazo kace zaka taɗa hankalin musulmi ayi tarzoma a masallaci wannan yana daga cikin manya manyan zunubai to kun ga duk wannan yana daga cikin aikin ƴan shi'a to amma sai Allah yayi musu daidai da irin yadda suke yanzu suka tashi zasu kai hari sai su kai hari masallacin iyayen su ƴan ɗari sai su tafi da ainihin makara cike da ainihin makamai sai su je sai su tsogali iyayen su ƴan ɗari ga da an fara faɗa shikenan sai su fito su sassara iyayen su sai su ɗau hoto kuma sai su aika Iran ace gashi nan ana jihadi a ƙaro kuɗi sai aiko da daloli masallaci fa jihadi amma a masallaci kaji fa duk ga arnan nan sun cika gari amma sai a tafi masallacin juma'a to sai kaga sai ya zama sai su tafi can masallacin iyayen su kenan haka kuma Ibn Umar yace da kuma mutumin da yake izgilanci mutumin da yake izgilanci kai izgilanci ga wani ainihin wato gatse ko habaici ko bakar magana ko izgilanci duk waɗannan ainihin suna daga cikin munanan laifuffuka sannan da kuma iyaye guda biyu saboda saɓa musu da ɗa yayi har su fashe da kuka duk ɗan da yayi irin haka ya aikata mummunan laifi saboda matuƙar yadda ka saɓa wa iyayen ka har ya kai suna kuka dubi iyayen Annabi Yaƙub inda suka saka shi a takaici ya rinƙa kuka har kuka ya kai mishi ga makanta wai madadin su ji tausayin shi suna zuwa sai suka ce har yanzu kana nan kana tunanin Yusuf har sai ka ainihin makance har ko kuma sai ka koma ka hallaka to waɗannan ainihin wato duk na daga cikin manya manyan zunubai laifi ya kai laifi saɓa wa ya kai saɓa wa harka tun zira iyayen ka su faše maka da kuka to ka aikata mummunan zunubi sai shi mai riwaya wannan ainihin wato mutum mai suna yace sai malami na Ibn Umar yace kana jin tsoron wuta ya kai an gane kana jin tsoron wuta ya kai shine ainihin kuma kana son ka shiga aljanna sai nace i na rantse da Allah kaga kalmar i an gane wannan da kyau ko to kaga larabci ne sai bahaushe ainihin ya ara mun fahimci wannan ko to kuma ko da hausa kazo dama haka dai zaka ce i in ma ba i kace ba in ma na'am kace duk dai larabcin ne sai yace i wallahi haka abun yake ina jin tsoron wuta kuma ina son in shiga aljanna kala sai yace in har kana son ka shiga aljanna kana jin tsoron wuta ga tambaya zan maka iyayen ka guda biyu ɗin nan suna da rai sai nace uwa ta dai tana nan da rai tana kuma guri na kala sai yace fa wallahi na rantse da Allah da ace zaka rinƙa tausasa mata magana ka rinƙa wa uwar ka magana da taushin kalmomi kalmomi masu taushi ladabi da biyayya kuma ka rinƙa ci da ita abinci lallai sai ka shiga aljanna matuƙar ka ne sanci manya manyan zunubai jama'a mun ji wannan da kyau ko kaji ƙa'idojin da zasu kai ka aljanna ka tausasa har shi ga ainihin mahaifiyar ka shine abun da dama Bukhari ya ƙulla babu yace tausasa magana ga ainihin iyaye to sai yace da zaka tausasa ainihin magana ga mahaifiyar ka ka rinƙa ci yadda ita abinci wannan abinci wane irin abinci kai kake ci kai kaji kaci abinci mai tsaɗar tsiya anje an turawa tsohuwa tuwo da miyar kuka wai ai su mutanen da ne basa son daɗi wayace basu son daɗi a ina ka karanta yaushe ta gaya maka bata son ka ci daɗi bata son ka ci daɗi waya koya maka cin daɗi ɗin ba ita ce ta sa bata sai kaza ta so ya maka tayi maka kaza tayi maka kaza ba Imamu Bukhari ya ruwaito hadisi ainihin Aisha tana zaune gida sai wata mata tazo tayi bara tace duk Allah ko da abinci a san mata gidan nan Aisha tace babu sai dai ainihin Dabino ƙwaya ɗaya sai Aisha ta fito da wannan ainihin Dabino shikenan ta fito da Dabino guda 3 afuwan sai wannan mata sai ta karɓa da ta karɓi Dabino nan guda 3 sai ta raba wa ƴa'yan nan nata guda biyu ta ba wancan ta ba wancan nan da nan yara suka lanƙwama Dabino sai kuma yara suka sa ido zuru sai wannan ƙwaya ɗayan kuma sai matar ta sake tsagawa sai ta raba musu sai manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yace wanda duk Allah ya jarabce shi da waɗannan ƴa'ya mata ya kyautata musu yayi tarbiyyar su ya koya musu ladabi har ya aurar da su Annabi yace haka zamu zauna ni da shi a alkiyama ka faɗa da ka faɗa saboda wahalar riƙon ƴa mace yafi wahala tarbiyyar ƴa mace tafi wahala zata zo da a tamfa yadi kaza shadda kaza namiji ko kana ɗinka mishi alawayyo sai ya sa ya shiga gari ba abun da ya shafe shi amma ita sai tace ai ana yayi ai in ba na yayi ba ita ba zata sa ba sannan kuma ita sai ka sa mata kan tsaro akwai wahala to shi yasa sai Annabi ya nuna falalar haihuwar ƴa'ya mata zamu zo mu samu waɗan nan hadisai a nan gaba insha Allahu ta'ala dan haka in Allah ya baka ƴa'ya mata ba bakin ciki zaka yi har bakin ciki yasa ka yi tarbiyyar su su je su lalace su zama maka sanadin shiga wuta ba a'a ƴa'ya mata sun fi ƴa'ya maza falala sai dai mutane sun fi son maza ɗin ne to kuma Allah maɗaukakin sarki abun da yake cewa so da dama kukan so abu sai ya zan sharri gare ku shi yasa abun da zaka roƙi Allah Allah ya baka ɗa na gari dubi lokacin da ai ainihin tayi roƙi Allah Allah maɗaukakin sarki ya bata ɗa ita abun da tasa rai shine ai kawai ɗa namiji ne ma zai zo kawai tana haihuwa kuma sai ta ga ainihin mace sai tace ya Allah da na yi alƙawarin abun da na haifa zai koma masallaci yayi ta maka ibada ba talla ba aike ba komai to sai dai kuma mace na haifa aka ce sai mala'iku suka ce mata ai ba duk wani namijin ne ma yake kamar wata macen ba sai tace to tunda haka ne na sa mata suna baiwar Allah ya Allah ina roƙon ka tsare ta ita da zuriyar ta daga shaiɗan wanda yake jefaffe daga albarkar Allah gashi nan sai Allah ya karɓa mata wannan addu'a wannan ƴa ita ce ta haifi Annabi Isa ɗaya daga cikin manya manyan manzanni shi yasa abun da ake so shine in ka samu ƴa'ya 1 nan sai kayi ƙoƙari kayi tarbiyya gwargwadon yadda zaka iya maza ne Allah ya baka mata ne Allah ya baka kar Allah ya taɓa baka wani ɗa kace tir kai dai baka so haka ba a'a ka roƙi Allah Allah ya sa wannan ɗan ta hanyar shi zaka samu rahamar Allah gashi dai kuna dai jin wannan yace lallai matuƙar dai ka ci da mahaifiyar ka abinci ka ainihin gaya mata maganganu masu taushi zaka shiga aljanna in dai har ka ne sanci manya manyan zunubai al Albani yace wannan hadisi sahihi ne in kana son ganin bayani kaje ka karanta alamba hadisi na 100
[Segment 2/4 | 00:20:00–00:40:00]
[Speaker seg2-spk:0]
Hisham dan Urwa yace ya karbo daga mahaifin shi Urwatu dan Zubairu yace. Me ce ce fassarar wannan aya da Allah madaukakin sarki yake cewa ka ainihin wato sassauta fukafukai na kaskanci da tausayi ga ainihin mahaifanka wato ka sauke ainihin girman kanka ka tausasa menene ake nufi da wannan da akace ainihin fukafukai na kaskanci na ainihin ka kaskantar da kanka ka tausaya mahaifinka me ake nufi da wannan ainihin aya aya ce tazo cikin suratul isra'i aya ta ashirin da hudu. Sai shi ainihin wato Urwatu dan Zubairu yace. Karka sake ka kiyin wani abu wanda iyayenka guda biyu suke son wannan abu matukar iyayenka guda biyu suka ce suna so kaje ka shiga ainihin aikin custom to karka ki matukar iyayenka suka ce suna son kaje makaranta ka zauna ka hafazi alkur'ani karka ki matukar iyayenka suka ce suna son ka tafi gona karka ki in abunda suka umarce ka ya saba ma Allah wannan kam Kasan wannan amma matukar abun nan ba saba ma shari'a bane to mai ake nufi da ka tausayawa iyayenka shine duk abunda kake so duk abunda suke so to karka sake ka kiyin wannan abun domin in ka duba haka al'amarin ya faru fa duk abunda kai kake so sanda kake karamin nan shi suke yi. In kace baka so ayi bacci a gidan ran nan ba wanda zai bacci. Hakane ko ba haka ba kai ta sandara kuka baka so ayi bacci so kake a rinka yawo da kai a hannu ana kewayawa haka baka ganin haka yaro tsakar dare sha biyu karfe daya karfe ukun dare sai ya tashi ya sandara kuka so yake a rungume shi a tsaya a tsaye. Haka kuma uban zai tsaya har sai kayi bacci. Ka duba fa a lokacin ya dauke ka ya jefar da kai ba wanda zai ji labarin ka a duniya. Sai akace yau gashi ya manyanta yana son kaza sai ya zama kai baka son kaza din nan tunda dai Allah baya kin wannan abun to dole kayi in kayi to sannan ne kayi aiki da wannan aya. Ka kaskantar musu da fukafukai na ainihin rahma ka tausasawa ainihin mahaifanka shine kaso ainihin abunda suke so to wannan kunga yana daga cikin inda ake samun fassarori daga salaf. In kana son ganin irin wannan sai kaje ka dauki tafsirin ibnu jariri shekhul mufassirina ko kuma tafsirin na anan ne zaka rinka ganin fassarori na ainihin malaman farko aya kaza me yace sahabi kaza ya fassara sai a kawo maka fassarar sai ainihin a kawo maka da isnadi to wannan dabi'ar ibnu jarir kenan dabi'ar suyudi shi kuma sai ya kawo maka sahabi ko tabi'in ko in ya kawo maka fassarar shi sai yace duba littafi kaza daga nan na dauko. yace wannan isnadi mai inganci ne jama'a mun gane wannan da kyau ko? babin dake bayani akan sakamakon iyaye guda biyu menene zakayi a matsayinka na da ya zanka biya iyayenka duk wahalhalun da suka yi. Shine wannan babin zai karantar ko akwai wannan abun in akwai abunda da zai iya yi ya zama ya biya iyayen shi menene wannan abu bari dai muji daga ainihin abunda yazo a cikin sunnar annabi da kuma jawabi daga ainihin manyan sahabban shi. Sahabi Abu Huraira in kun duba isnadin nan zaka ga isnadin shi Imam Bukhari ya karbo shi daga malamin shi Kabisa kuma yace Sufyanu ya ainihin bamu hadisi Sufyanu haka in kaga anan ana nufin Sufyanu dan Uyaina. Shi kuma yace daga Suhailu dan Abi Salih. To shi Abu Salih din shi Suhailu din sai yace ya karbo daga baman shi Abu Salih as-Samman ko az-Zayyat almajirin Abu Huraira ne ya shahara da riwaya daga gare shi. Shi kuma yace ya karbo daga Abu Huraira daga annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi annabi yace da bazai iya biyan uban shi hakkokin dake kanshi ba sai dai in shi dan ya samu uban shi a matsayin bawa sai ya siyi uban nashi sai ya 'yantar shi to in yayi haka lallai kam to ya biya uban hakkokin uban dake kanshi. Amma inda ba haka yayi ba to ba wani abu da zai iya wa uban shi ya iya ainihin biyan shi hakkokin. Wannan ainihin hadisi sahihi ne in kana son ganin bayani kaje ka karanta littafin lamba hadisi na dubu daya da dari bakwai da arba'in da bakwai haka nan Muslim kenan ya ruwaito shi a cikin kitabi na ashirin kitabul 'itki hadisi na ashirin da biyar da kuma hadisi na ashirin da shida mai yiwuwa mai saurare na daga nesa zai ce yaya yake jin ana cewa Albani yace bayan littafin Bukhari ne a Albani yayi aiki ne ainihin akan littafin shi yasa kake jin sai ainihin in akaga ma kawo hadisin sai Malam Muhammad Nasiruddin al-Albani sai ya fada ainihin nashi hukuncin dake ainihin ya tabbata mashi a cikin ilmi dangane da ainihin hadisin. Sahabi Abdullahi dan Umar shine yake ainihin ruwaito mana wannan magana amma wanda ya ruwaito ta daga gare shi shine Sa'idu dan Abi Burda jikan Abu Musa al-Ash'ari Abu Musa al-Ash'ari yana da da Abu Burda Abu Burda yana da da Sa'idu to Sa'idu din yace kala yace naji baba na yana bada labarin cewa Toh nefa kenan Shine sai ainihin shi wannan Sa'idu dan Abi Burda yace naji baba na Abu Burda yana bada labarin cewa ya halarci gurin Ibnu Umar wato yaje gurin Ibnu Umar Wani mutum mutumin kasar yaman yana ainihin kewaye dakin ka'aba ya dauki mahaifiyar shi a bayan shi yana goye da uwar shi a baya ya goye uwar shi a gadon baya yana kewayawa da ita yana dawafin ka'aba. Mai yiwuwa ko ta tsufa ne ko kuma dai yaji tausayin ta ne yaga cewa bari ainihin yayi mata haka sai ainihin yaji shi yana rera waka yana cewa nine horar rarraƙumin ta koda raƙuman ta sunyi mata ainihin hutsu ko sunyi mata ta waye to ni bazanyi mata hutsu ba ga alama mai yiwuwa ko uwar ta hau wani raƙumi ne raƙumin ya kada ita sai dan yace to zo in goya ki a baya ta in raƙumi yayi hutsu to ni bazanyi hutsu ba sai shi mutumin yace ya kai dan Umar kana tsammanin shine ma'anar da yace da yace kana ganin amma shin kana zaton ko na biya ta sai yace a'a ai ko yunkuri guda daya daga cikin yunkurin da tayi a wajen haihuwar ta baka biya ba in mace tazo haihuwa yunkuri nawa take to ko yunkuri daya baka biya ba sannan sai Ibnu Umar ya kewaye ka'aba shima yaje wurin sai yayi sallah raka'a biyu sai yace ya kai dan Abi Musa Abu Burda kenan tunda da shi ake maganar an gane wannan da kyau ko shi yake ruwaito hadisin yanzu wancan mutum an gama bashi fatawar shi sai shi kuma ake baiwa sai shi sahabin yake sanya tattauna da shi da mai riwaya almajirin shi cewa ya kai dan gidan Abu Musa wato Abu Burda dan Abi Musa al-Ash'ari duk ainihin wato wasu raka'o'i guda biyu tana kankare ainihin wato zunuban da akayi kafin su duk sanda mutum ya kewaye ka'aba da ya kewaye ka'aba sai yazo ya ainihin ya sallah raka'a biyu to duk laifuffukan da kayi gabanin wannan dawafin da wadannan sallolin to za'a gafarta maka su. Wannan isnadi mai inganci ne to kaga inda gafara kake nema to ga yadda za'a ayi lada kake nema ga yadda zaka samu in ka kewaye ka'aba akwai hadisi sahihi da annabi yace ma in ka kewaye ka'aba kazo kayi raka'a biyu din nan sai ainihin a rubuta maka lada tamkar kayi umra yasa falala tana can ka'aba malam sai a dage in ka samu kudin umra kaje kana da kudin aikin hajji kaje akwai lada a wannan guri akwai Allah madaukakin sarki ya saka wurin albarka. Don Allah ayi wayar nan magana jama'a don Allah ayi wayar nan magana akace Abu Huraira Allah ya kara mashi yarda ya ainihin kasance shi Abu Huraira ya kasance yana ma'anar mahaifiyar Abu Huraira asali kafira ce krista ce mutuniyar kasar yaman asalin uwar Abu Hanifa ai uwar Abu Huraira sai ainihin yaje yayi mata wa'azi yaje yace mata shi fa ya musulunta shikenan sai tayi ta waye ta hau babbakin fada kaza kaza yayi juyin duniya ta musulunta tace ita bazata musulunta ba shikenan sai daga baya sai yaje kai kuka ga annabi sai annabi yace ka tashi ka koma zaka jije ka samu ta musulunta Abu Huraira sai yaje ya samu uwar shi kawai ma tana sallah mutuniyar kasar yaman ce daga kasar yaman su mutanen kasar yaman ne to ya koma kawai sai ya samu ta na ainihin sallah to shine anan ake bamu labari cewa Abu Huraira ya kasance Marwanu yakan nada shi gwamnan wucin gadi Marwanu yana gwamna a Madina to in zai yi tafiya sai ace to an baka riƙon gari kamar yadda sarki in zai tafiya sai ace an bar sarauta wa'an bar kula da fada a hannun wane ko gwamna ace a hannun mataimaki ko makamantan haka to Marwanu sai ya nada Abu Huraira to shi Abu Huraira yakan kasance a sai yaje ainihin can miƙatin mutanen Madina waje da Madina ne haka to sai ya zan Abu Huraira ya dawo da mahaifiyar shi Madina amma tana wani gida shi kuma yana wani gida daban idan shi ainihin Abu Huraira ya nufi zai fita office sai ya tsaya a ƙofar gidan ta ko ƙofar dakin ta ma'ana abunda ake nufi sai yaje gidan ta ya gaishe ta kenan wa kala in yaje sai yace amincin Allah ya tabbata gare ki ya mahaifiyata wannan kalma ce ta ainihin tausasawa an gane da makamantan su amincin Allah ya tabbata gare ki ya mahaifiyata haka rahama da albarka Allah su tabbata gare ita kuma sai tace amincin Allah ya tabbata gareka ya dana da rahama da albarka Allah sai Abu Huraira yace Allah ya jikan ki ya 'yantar mahaifiyata kamar yadda kika yi mun tarbiyya ina ƙarami sai tace Allah kaima yayi maka rahama kamar yadda kake mun biyayya gaka da girmanka da komai amma kake bina haka in yayi nufin zai tafi gidan shi sai ya sake koma ya biya ta gidan mahaifiyar ya sake gaishe ta. Malam Muhammad Nasiruddin al-Albani yace isnadin wannan ainihin asalin da kaji mai rauni ne mai yasa sai yace a cikin isnadin akwai Sa'idu dan Abi Salih din nan ya samu rikicin ainihin kwakwalwa a karshen rayuwar shi to irin wadannan in suka samu irin wannan rikicin to al'amari yakan zama matsala matsalar da take faruwa abunda ake nufi da babban malami ne mahaddaci karshen rayuwar shi sai ya samu wata jarabawa koda ya makance in ya makance sai ya zama yana bada karatu daka madadin da a littafi yake bayarwa ko kuma da din ma daka yake bayarwa amma kafin ya fito bada karatu zai yi nazari to yanzu ya makance babu yadda zai yi kafin ya fito yayi nazarin abunda zai fada to sai ya zan yana baku hadisai sai a rinka aunawa da hadisan da ya bayar da sai aga in ya bada wani hadisi wanda a da ya taba bada shi sai aga ya rikice to sai a fara fahimtar to yanzu kwakwalwar malam ta fara rikicewa domin da ga abunda ya fada yanzu dai makance kuma ga abunda ya fada an fahimci wannan ko ko kuma yana da iyayen shi yana matukar son su sai su mutu ko yana da 'ya'ya wadanda yake so sai dan ya mutu ko 'ya'yan ko yana da mata wanda ya jarabtu yana so sai ta mutu ko gidan shi ya kama da gobara ko wata larura makamancin haka to sai ya zama baya iya bada karatu daidai to sai malamai suce ai marmaza a kafa kwamitin bincike na ilmi a gane suwanene almajiran shi kafin ya samu wannan matsala sune suwane to duk sanda suwane suka zo suka ruwaito hadisi a wurin shi to sai ace wannan hadisi ya inganta ko ya kyautatu da gwargwadon yadda isnadin ya kama a hukunta shi amma dukkan dalibin shi da aka tabbatar cewa yayi karatu a guren shi ne bayan da ya rikice sai ace to baza a karba ba domin tabbas wane yayi karatu ne bayan malamin ya rikice to dalibin kuma da aka kasa tantance wa shin yayi karatun ne kafin malamin ya rikice koko sai bayan da malamin ya rikice sai ace to ayi bincike in aka bincika aka kasa ganowa sai ace to yanzu a dauko hadisin wannan dalibin da ba'a gane ba shin yayi karatun ne a makarantar kafin malam ya rikice ko bayan ya rikice sai a sake duba wata makarantar shin ko an ruwaito irin wannan hadisin a wata makarantar in aka gwada wannan riwayar da waccen ta makarantar akaga tayi daidai sai ace to duk da dai yayi karatu ne a hannun malamin ainihin ana tunanin bayan ya rikice ko kafin ya rikice tunda gashi hadda tayi daidai da abunda aka haddato a wata makarantar to sai a karba jama'a an gane wannan da kyau ko to wannan na daga ainihin cikin ƙa'idojin da malamai suke bi dangane da ainihin akwai buƙatar ainihin wato ka tsaya sai ka natsu akan wannan kamar Imam Abdurrazak as-San'ani mai littafin ya samu karkashin a karshen rayuwar shi saboda ya makance hakanan wannan malami Abdullahi Ibnu ya samu to an iya ware malaman da ainihin suka yo karatu a wurin shi daga wadanda basu yo karatu ba kamar dai yadda nake fadi kullum wannan matsala ce wanda tana buƙatar ne kaje ainihin ka koya a wurin ainihin malaman da suka santa Allah ya shiryar damu na'am jama'a mun gane wannan da kyau ko to kamar yadda na fadi karka dauka fa wai tunda Bukhari ne ya rubuta wannan littafi yaya za'ace akwai da'ifin hadisi a'a Bukhari bai sharadin inganci a cikin wannan littafin ba a cikin littafin shi daya kwaya daya anan ne ya sharɗanta duk abunda ya kawo yake ganin cewa ingantacce ne amma bayan haka sauran littattafan shi yayi su ne kamar yadda sauran ainihin malamai suka yi su ku dan rage fankannan malam tayi yawa sa ta karshe ne kawai Abdullahi dan Amru yace wani mutum yazo wurin annabi dan yayi mashi mubaya'a akan cewa zai hijira sai ya baro iyayen shi guda biyu suna ta kuka basu yarda da wannan hijira tashi ba sai annabi yace ka koma wurin mahaifan naka ka ainihin yi tattaunawa dasu har ka kwantar musu da hankali yadda har sai kasa su sunyi dariya kamar yadda kasa su kuka jama'a mun gane wannan da kyau ko domin a wannan halin ka tsaya ka kula da mahaifanka yafi ainihin muhimmanci a musulunci fiye da wannan hijirar da zaka yi malam yace ainihin ka duba littafin ainihin wato sahihi ne wannan ina zaka duba kaga yadda ya tattauna shine wannan littafin Allah ya rufa asiri Malam Muhammad Nasiruddin al-Albani dab da zai mutu sai aka ganshi in baku manta ba na baku labari akwai wasu littattafan shi wadanda daga gama rubutawa sai suka bata daga ciki akwai littafin da babban mahaddaci Malam Abdul'aziz Ibnu Abdulƙawi al-Munziri ya rubuta shi littafi ne zai ce maka babin dake bayani akan kwaɗaitarwa akan yin sallah akan lokaci sai ta kawo maka hadisai daga annabi sai kuma yazo yace babin dake bayani akan tsoratarwa game da barin sallah akan lokaci sai ya kawo maka hadisai akan haka to sai ya zama malamin ya rubuta littafin ne nesa daga littattafan shi bashi kusa da littattafan shi ya rubuta ne daka shi wannan malami sai ya rinka kuma takriji hadisi kaza sai yace sahabi kaza ya ruwaito shi daga kaza kamar yadda kaga tsarin to sai ya zan wannan littafi an samu kurakurai masu yawa a ciki wadanda kurakuran sun kai matuka hadisin Aisha sai ya jefa shi cikin hadisan Abu Huraira hadisin da yazo cikin Bukhari sai yace Ibnu Maja ya ruwaito shi hadisin Ibnu Maja sai yace yana cikin
[Segment 3/4 | 00:40:00–01:00:00]
[Speaker seg3-spk:0]
Irin wadannan kurakurai sai suka yi yawa. Sai ainihin shi malam Muhammad Nasiruddin Albani sai yazo, sai ya ainihin dauka sai ya fasa littafin biyu. Sannan kuma To wannan an buga shi a yanzu mujalladi biyar. Mujalladi biyar. Uku sahihai biyu da'ifai. Ya fito kwanan nan bai wuce wata biyu da fitowa ba. Wannan kenan. To sai bayan da ya gama wannan aikin sai kuma yazo sai ya bar littafin yadda yake. Sai yayi rinka yin ta'aliki a jikin shi yana danyen sharhohi yana ishara game da hadisan da muka manton haka. Sai ya sa mishi Ta'aliki sharhi da ake kwadayi To wannan din sai ya bata kafin Aje a buga shi. To daga baya sai Allah madaukakin sarki ya taimaka sai aka ganshi shine har aka buga gashi kaji yanzu yana hujja dashi. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? To a cikin Sai shi malam Muhammad Nasiruddin Albani yace yana cikin bincike yana yalle kyalle kyen shi a cikin library na Jami'al Islamiyya dake Madina. Sai ya gano wani littafi da wani kwararren malamin hadisi yayi shi. Da yayi shi ba'a taba buga shi ba. Wani mutumin kasar Sham ne mutumin garin ainihin Halab. Da ya dau littafin Amma sai ya ajiye shi ba'a buga ba don yayi shi da dadewa ne. To shi naji da yazo yana gyare gyare da yaga ta'adin yayi yawa. Kaga malaman hadisi zaka ga kamar wato gyare gyaren sun yawa su abin da suke so shine A bar ka'ida yadda take. To in kai kurakurai da yawa sai sun bi duk kurakuran nan sai suce a bi a gyara tunda yadawa zakayi ga jama'a. To da yazo yana gyare gyare Sai yake cewa wannan irin matsala dake cikin littafin matsala ta kai matsala. Ina ma da mutum bai wahalar da kanshi yace zai gyara wannan ba. Ina ma da nashi ya rubuta da kanshi da yafi mishi sauki. To wadannan kalmomin ina fadin su ne saboda in kana da littafin to kayi takatsantsan ya kamata ka samu ainihin wadannan aikace aikace Da kuma ainihin wancan ainihin Da kuma Akwai kuma wani aiki wanda wasu malamai ainihin suka yi ba da dade wannan ba a cikin mujalladi hudu. Sun dibo da dama daga cikin ayyukan da shi Muhammad Nasiruddin yayi sun zuba ainihin a cikin nasu. Wadannan duk zasu haskaka maka wajen ka gane ainihin cewa kar ka sake. Ka tinkari rubutu game da ilimin da kasan cewa baka da garanti a kanshi. Don ilimin nan ba harkar copy bace. Kuna ganin Amma ku duba irin abubuwan da ake gani sun samu a cikin littafin. Balle kai da zuwa zakayi ka kofo. Mutane sun kosa kowa ina son a zamanin nan wai ace ya rubuta littafi ya rubuta littafi. Rubuta littafi jama'a kana magana ne da mutanen zamanin ka. Da wadanda kuma zasu zo bayan zamanin ka. Kar ka rinka ganin wai zaka rubuta ne dan yan Islamiyyar unguwar ku, ko dan yan Islamiyyar garin ku, ko dan yan Islamiyyar kasar ku, ko dan mutanen kasar ku. Ka dauka kana magana ne da duniya. Yanzu ga wannan littafi dake gaban mu. Fiye da shekara dubu daya da rubuta gashi har yanzu ana karanta shi. Yanzu in shirime me shi yayi yaya? Malamin hadisi kamar tarihi suke basu hakura duk inda suka gani sai suce kaza ne. Yanzu wannan hadisi da muka gama karanta na Abu Huraira dincen nada su. Amma zamu zo mu samu kuma wani ainihin wato wata riwaya ta wannan hadisin gashi yanzu ba da dadewa ba zamu karanta. Ita kuma kyakkyawar riwaya ce. To inda abin da son zuciya ake ko da jahilci da sai ace ah to tunda dai wannan ainihin Hassan ne to wancan kuma ace Amma ba irin wannan ne ake cewa ba. Domin wannan din nan da muka gama karantawa da'ifi ne Domin duk riwayar da ta zama ainihin riwaya ce ta To da'ifi ya ce. To wannan sai ya zama ba'a samu wannan din a ciki ba. Don haka sai kaji ainihin an karba in sha Allahu ta'ala. Malam yace ka duba littafin a cikin mujalladi na uku shafi na dari biyu da sha uku. Sannan Abu Dauda ya ruwaito wannan hadisi a kitabi na goma sha biyar wato Babi na talatin da daya shine Babin dake bayani akan ina hukuncin mutumin da zai tafi yaki amma iyayen shi basa so. Nasa'i ma ya ruwaito wannan hadisi shine ishara da Kitabi na talatin da tara shine Littafin dake bayani akan muba'a akan jihadi. Shine ainihin babi na goma kenan Babin dake bayanin muba'a akan hijira. Sannan sai ya sa Menene Shine ainihin alama ta Shi kuma ainihin kitabi na talatin da hudu Babi na goma sha biyu Babin dake bayani akan mutumin da zai tafi yaki a halin yana da iyaye guda biyu. Lamba hadisi na dubu biyu da dari bakwai da tamanin da biyu. Abu Hazimin yace lallai Abu Murra to kun ga inda ainihin wato ake gane yanzu yadda zaka dauko wannan sai ka dauko shi da wancan. Sai ka auna kaga. A chan gurin aka ce Shi Lais Da yace To Akace shine matsala a isnaidun ko? To sai ka dawo wannan isnaidun sai kaga gaba daya babu din ma gaba dayan shi. An gane? To amma sai kaga kuma Malamin shi shine a chan ko to kuma ga malamin nashi a nan. Wato ashe malamin nasu Abu Hazim ya karantar da Musa Musa kuma ya karantar da ainihin Chan kuma shi malamin ya karantar da Sa'idu shi kuma ya karantar da Khalid dan ainihin wato To kaga a nan da yake babu wancan matsalar shine zaka ji malam ya Sai yace Wani mutum mai suna Abu Murra bararren bawa ne na Ya bada labarin cewa Abu Huraira yana da ainihin gona a Sai shi wannan ainihin wato bararren bawa na yace sun hau dabba sun tafi gonar Abu Huraira wanda ke Idan Abu Huraira ya shiga gonar tashi sai ya daga muryar shi yayi magana. Amincin Allah da rahamar Allah da albarkar Allah su tabbata gare ki ya ke babata. Wato babar tashi sai ya mata gida a nan inda gonar tashi take. To da yazo wurin gonar sai ya daga murrya ya mata sallama. Amincin Allah da rahama da albarka Allah su tabbata gare ka. Allah yaji miki rahama ya ke mahaifiya ta kamar yadda kika yi mun tarbiyya ina karami. Kaima dai Allah ya maka sakamakon alkhairi. Allah ya yarda da kai. Dan haka in kaine tsinanne baka yi wa Abu Huraira Bazaka cewa Abu Huraira wai kana jin haushin shi ko? To uwar shi tace mishi Magana ta kare ko bata kare ba? Ka tuna kai da nake magana da kai uwar ka ta taba ce maka Wacce ta taba gaya maka tsakanin ka da Allah. An gane wannan da kyau? Saboda haka ko baka cewa Abu Huraira ba wai kana jin haushin shi. Don me don ya rike mulki a lokacin da wadanda kake so suyi mulkin Allah bai basu ba. An gane wannan da kyau? Domin matsalar yan shi'a kwaya daya ce. Duk inda kaji surukicin su na siyasa ne duk wanda bai shiga rikicin siyasan nan da akai ba zaka ji basa zagin shi. Sai dai su dan gaya mai bakan magana kamar su Abdullahi dan Umar ace to ai dai ko da dai bai ce komai ba akwai alamar munafunci. Ka gani? To amma wai duk mutum me yasa kaji suke zagin Mu'awiya suke zagin su Mughira saboda sun rike sarauta a wadannan lokutta. Duk wanda ya rike sarauta a wadannan lokutta shikenan. Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Domin Humaini a cikin littafin shi yana cewa Wadannan zamunna daga mutuwar annabi Har zuwa sanda Sayyidina Ali ya karba halifanci sun zauna ne Kasan aka ce kaset na video ne aka ce Ma'ana in kasa baka ganin komai din din. To suka ce haka wadannan shekaru suka zauna shiru ba'a mulki. Yace sai sanda Aliyu ya karbi mulki lokacin ne aka fara ainihin halifanci. Don haka duk yan shi'a daga kan Aliyu suke fara ainihin lissafi. In suka lissafa Aliyu, Hassan, Husaini har shine sai su kai kan ainihin mahadi sai suce limaman su guda goma sha biyu kenan Sai suce to wadannan limamai guda goma sha biyu to sun fi annabin dake manzon Allah daraja a wurin Allah. Sun fi mala'ikan dake kusa da ainihin Allah daraja a wurin Allah. Sai Mu su muna kafirtar da yan shi'a yanke wadanda ke cewa din nan limaman su goma sha biyu sun fa annabawa da manzanni ainihin darajar. Hakanan Hakanan malamin Bukhari In kana son ganin tattake wuri ko kaje yadda aka tattake wuri mu hadu da kai a dogon Bauchi ranar asabar in sha Allahu ta'ala. Muna da kasaitacciyar laitawar da za'a yi akan bambanci tsakanin musulunci da ainihin shi'a. Bambanci tsakanin shi'a da ainihin musulunci. Menene musulunci? Sai a bayyana ga musulunci ka kuma ji akidar musulunci kuma kaji akidar musulumi. To sannan mecece akidar shi'a game da Allah, game da annabi game da sahabbai, game da al'kur'ani, game da sunna, game da malaman duk zamu kawo wadannan abubuwa da izinin Allah. Bazamu zalunci kowa daga ciki ba. Zamu bude littafin musulmi mu karanta. Me musulmi suka yadda da shi game da akidar su? To me musulunci daga sheda littafin su? Sannan mu bude littafin yan shi'a mu karanta. Menene musulunci su kuma a wurin su? Shikenan aka ce Duk abin aka kawo aka sun shi yanzun nan sai kaga ka gane dayan. Ana cikin duhun aka kawo wuta kasan sunan nada zo ya sha bamban da na yanzu. Hakane ko ba haka ba? To haka al'amarin yake in sha Allahu ta'ala. Shine ga dai Abu Huraira kaji dai uwar shi tana cewa Allah ya saka maka da alheri. Allah ya yarda da kai Abu Huraira kamar yadda gashi da girman ka da komai amma kana bi na. Sai shi Musa almajirin Abu Hazimin yace Sunan ainihin wato Abu Huraira wato sunan shi meye hakikanin sunan Abu Huraira? Tunda yace Asalin sunan shi a jahiliyya ake magana. Asalin sunan shi a jahiliyya an tattauna. Wasu ce Abdushamsin wasu ce ainihin Abdullahi dan Amr shine shi yake cewa yana ganin dai sunan Abu Huraira Abdullahi dan Amr ne. Amma a musulunci aka dawo aka tattauna to a musulunci meye ta kamar man sunan shi? Karshe dai na wau yace yana kyautata ainihin wato ganin cewa Abdurrahman ne ainihin sunan shi. Saboda an kawo maganganu wajen guda goma in kaje ka karanta littafin To Bayan da ka gama jin cewa lallai ne kai da baka da abin da zakayi wa iyayen ka ka biya su. Matukar ba dai ka samu mahaifin ka ko mahaifiyar ka a kangin bauta ka siye su ka yanto su ba nan ne kawai za'a ce in ma akwai abin da zakayi ka biya iyayen ka nan ne kawai. Amma bayan nan fa babu wani abu da zaka iya wa iyayen ka kace ka biya su hakkin su. Tunda gashi dai anji wani ya goya uwar shi yana kewar Ka'aba da ita. Yace ya biya aka ce ai ko nishi daya daga ciki nishin da tayi yayin da take yunkurin haihuwa baka biya ba. To saboda haka duk abin da kayi wa iyayen ka kar ka dauka kayi kaza kayi a'a ka dai abin da zaka iya Allah ya saka maka da alkhairi kuma Allah ya karba amma hakkin iyaye yana da girma. Babin dake bayani akan saba wa iyaye ina matsayin saba wa iyaye a musulunci? Haramun ne. Abdurrahman dan Abi Bakrata yace ya karbo daga mahaifin shi sahabi Abu Bakrata. Abu Bakrata daban Abu Bakkar daban. Abu Bakkar as-siddiku sunan shi Abdullahi dan Abi Kuhafa shi kuma wannan Abu Bakrata alkunya shi ce sunan shi ainihin Nufai. Dan haka ka banbance to Abdurrahman yace ya karbo daga mahaifin shi Abu Bakrata Yaku jama'a bana baku labarin zunubin da yafi kowanne girma ba. Har su uku annabi sallallahu alaihi wasallama yace wa sahabbai sai suka ce Muna so ya manzon Allah a bamu labari Wani zunubi ne yafi ainihin kowanne zunubi girma daga cikin laifuffuka. Annabi yace ai zunuban suna da yawa amma dai gasu kadan daga ciki. Hada Allah da wani ko wani abu wannan laifi ne mai girma. Da kuma saba wa iyaye guda biyu. Ka kangare wa iyayen ka kafi karfin su kayi wa iyayen ka tawaye babu shakka wannan laifi ne mai girma. Mahallun shaidin kenan a hadisin dake babin. A da da annabi yake fadin wadancan maganganu yana kashin gida ne. To sai ga wata magana mai matukar muhimmanci annabi zai fadi. Sai ya tashi zauna dan jama'a su san aikin aiki ne. Annabi yace Jama'a ku saurara ku ji. Hadda fa dan zur fadar karya baka ji ba baka gani ba ka kirkira ka fada. Abu Bakrata yace annabi bai gushi ba yana ta maimaitawa har sai da har sai da nace kai ai da annabi yayi shiru ma munji ai mun fahimta. Annabi yana cewa A wata riwaya yana karawa Jama'a har da fadin karya har da sheda da karya baka ji ba baka gani ba sai ka kirkira ka fada. Kai kuma baka ji ba baka gani ba sai kace ka sheda. Wannan mummunan laifi ne. Allah ya kiyaye.
[Speaker seg3-spk:1]
Amin.
[Speaker seg3-spk:0]
Malam Albani yace wannan hadisi sahihi ne. Ina za'a ga yadda aka yi ya zama sahihi sai yace a duba littafin shi Littafin Littafi ne da Albani yayi Shi kuma tarihi littafin Wani babban malami ne da duniyar musulunci take ji da shi a yau din nan. Allah yayi mishi dinbin ilimi Balara be ne mutumin kasar Masar. Amma a yanzu yana nan a zaune a ainihin To sai yana zaune sai ainihin tun a kasashen su chan na Masar. Sai aka ce akwai musulmi da dama suna musulunta a Amerika. Ko kasan yanzu cewa addini na biyu a Amerika shine addinin musulunci. Kuma yafi ainihin nagarta fiye da duk wani addini. Domin ina son kusan cewa An daina yin Kiristanci bashi ba'a jin labarin kiristanci a kasar Turai. Kasashen Ingila, kasashen Faransa da makamantan su. Choci ce katuwar choci sai a a kada kararrawa azo service sai a je zuwa. Sai a fitowa kada mata kararrawar gwanjo dole a siyar da ita. Sai musulmi su siye ta sai su mayar Islamiyya ko masallaci. Abin da yake faruwa yanzu a kasashen Ingila kenan choci sai ka samu shekarar ta dari ana aikin choci a cikin ta amma an daina yanzu an koma ana sallah a cikin ta. Haka tafiya iya ta iya aka ce to kuma choci karanta littafin aka ce sahabbai lokacin in suka shiga kasar suka ci ta da yaki. In suka rasa inda zasu yi masallaci sai ya zama choci tayi saiti da alkibla kawai sai a share ta a maida ita masallaci. Yana cikin Jama'a mun gane wannan da kyau ko? To haka al'amarin nan sai ya kasance abin da yake faruwa kenan a kasashen Ingila Faransa. To sai kasar Amerika yanzu yan iskan yan rawa din nan da sauran su tuba suke tayi suna ta ainihin shiga addinin musulunci. Sannan da sun tuba sun shiga addinin musulunci zagewa suke suyi karatu. Tafi Jami'al Islamiyya zaka je ka gansun. Gasu nan turawan Amerika ne da Caribbean bakaken fata da sauran su. Ga ya musulunta. Amma yanzu Yau shekarar shi talatin da daya da musulunta. Amma yayi farko akan addinin musulunci. Akida da tauhidi yayi na biyu a Jami'al Islamiyya kuma a Madina. Ya koma Ya koma kasar su ya koma chan kasar Turai kasar Ingila kuma ya samu ma'ana uku akan addinin musulunci. Har an bashi yanzu Ya zama Jama'a mun gane wannan da kyau ko? Da gaske suke yi hakanan shekara tara da suka wuce zuwa shekara goma. Wasu turawa suka musulunta daga ainihin kasar Amerika sai suka ce suna son su kewar kasashen musulunci. Suka kawo ziyara Kano garin musulunci aka taho ainihin suka kawo ziyara. Sai suka zo Amerikawa ne sai aka sa su sahun farko suna ainihin sun zo ziyara. Malam da aka fara sallah sai suka ji karatu irin namu na gargajiya ake yi. Ana idar da sallah kawai malam sai guda daya ya tashi ya tada ikama sai suka tura daya daga cikin su kawai ya sake musu sallah. Sun musulunta a lokacin watan su shida sun shiga wata na bakwai da musulunta. Amma har sun gane tsohon liman bai iya karatu ba. Saboda mu da gargajiya muke su ka koyo suke yi. Zama suke suna koyo. Yaron nan da aka zo dashi dan Tanzaniya yana zalunci ana cutan mutane wai ga wani yaro an haife shi ya haddace kur'ani yayi menene yayi menene. Yana karanta wakar Islamiyya fa Wai ana wai kur'ani ne wannan wakar Islamiyya ce. Ka gani duk sai muka wai mu nan saboda jahilci ya kai mana kas. Sai aka kasa gane wai wannan fa ba kur'ani yake karantawa ba. Yaron nan yana zuwa a chan Amerika an kai shi. Sai aka je ana tattaunawa da manyan daraktan da kanshi yake fadin haka yau kamar wata guda anyi hira dashi a tashar Yace sai muka zaunar da manyan da suka zo dashi muna tattaunawa da su. Yace sai muka same su turun jahilai ne. Shi kuma yaron ashe yana chan yaran mu yan Islamiyya sun kure shi. Aka ce ya akai sai ai an yara ne suka ce
[Segment 4/4 | 01:00:00–end]
[Speaker seg4-spk:0]
to kai ance ka haddace qur'ani to karanta sura kaza sai yace ai shi bai san ta ba to karanta sura kaza shi bai sani ba sai yace kai shi fa daga to ance ka haddace qur'ani yace a shi iya abunda ya sani kenan kawai yawo ake yan damfara ne kawai haka al'amarin nan yake to wadannan tura da suka yi ta musulunta sai aka ce wanda tura wannan zasu ainihin fahimci addini a ciki to amma turancin bai kai karfin da zai iya rubuto a kai ba to sai ya rubuta da ainihin larabci sai aka to hadisan da yake kawowa a ciki shine sai ya baiwa kaiwa matuka ga abun nema sai albani yace ka duba wannan lamba hadisi na cewa babin da ke bayani akan saba wa iyaye guda biyu din nan babba ne daga cikin ainihin manya manyan zunubai muslim ma ya ruwaito wannan hadisi a cikin kitabi na farko kenan lamba hadisi na jama'a kunji saba wa iyaye haramun ne shiyasa in kasan yanzu da kake saurare na din nan cewa ka saba wa iyayenka kaje ka tuba bahaushe yace durkusawa wada ba gajiya bane ko to iyayenka ba wadanni bane gamji ne an gane wannan gamji ne kasan bishiyar gamji na da tsawo ko bata da tsawo to iyayenka sun wuce nan gare ka don haka kaje sai ka roke su su yafe maka sai ku ainihin daidaita kuma kullum kamar yadda muke fadi su kuma iyaye kar su ji haka suje su dauko hakkin da yafi karfin su suce su kuma lallai ne sai an basu wannan hakkin a'a anan kuma ka nemo rikici ainihin baza a bika ba akan wannan shiyasa daidai ruwa daidai gari haka bahaushe yace ko in aka yi waita gari ya yawa sai ya zama kunun zaki ko idan kuma ainihin ruwan ya yawa in ruwa ya yawa sai ya zama kunun zaki ko in gari ya yawa fa sai ainihin tufke to amma in aka sa daidai wa daida sai ya zama tuwo wanda zai ciyu a bakin kowa da kowa hakkokinka da aka baka ka tsaya anan kai kuma dan lallai ne kabi ainihin iyayenka to da ana dabbaka wadannan abubuwan sai kuga an zauna lafiya yanzu kasar amurka dincin da nake bada labari abun sha'awa idan da ya tashi musulunta sai yaje ya gaya baban shi sai yace kawai yana so zai musulunta ne sai uban yace to shikenan muje in raka ka sai kaga uban ya rako danshi yace ya kawo danshi ne wurin imam zai musulunta shi kuma sai a sawa uban kujera sai yaga gashi nan ana nuno su in kana kallon tashar saudi two sai kaga ga uba yazo ya kawo danshi ya musulunta shi kuma yana ji duk abunda za'a in aka gan musulunta shikenan danshi de ya shaida musulunta danshi dan haka ba matsala amma afirka bakar fata akwai matsala eh akwai matsala malam shiyasa natsuwa ya kamata ka rinka yi gama da harkoki in ba haka ba sai abubuwa da dama sai kayi ta asarar su zamu saurara anan insha allahu ta'alaAnnotations de valeur
- AI Model - Transcription
- Gemini 3.5 Transcribe
Comment citer ce document
Zaria, Muhammad Auwal Albani, et Adabul Mufrad. Adabul Mufrad #1-4. Daarul Hadeethis Salafiyyah, août 2001. DVD. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15857.
Zaria, M. A. A., & Mufrad, A. (2001, août). Adabul Mufrad #1-4 [DVD]. Daarul Hadeethis Salafiyyah. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15857
Zaria, Muhammad Auwal Albani, et Adabul Mufrad. Adabul Mufrad #1-4. Daarul Hadeethis Salafiyyah, août 2001. DVD. https://islam.zmo.de/s/afrique_ouest/item/15857.
Télécharger
Visualisations
Chargement des visualisations…


